Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 148
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 148: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 148. Motar shiru tunda suka ɗauki…
4,092 words
Motar shiru tunda suka ɗauki hanyar airport har suka iso. Yaya Fawzan ya samu waje yay parking. Basu fitoba kowa yayi shiru kusan minti biyu babban Yaya yay gyaran murya. Duk kallonsa sukayi har Mamy data sha kuka harta godema UBANGIJI. Muryarsa da rauni sosai ya ce, “Mamy bazamu ƙiki ba. Dan duk abinda kika zama ke mahaifiya ce, muna kuma sonki muna ƙaunarki duk da kin ɗaukemu tun muna ƙanana a zanen haihuwa kin bama Oum saboda biyan buƙatar kanki. Alhamdullahi Oum ta mana riƙo irin na uwa mahaifiya ba uwar riƙo matar uba ba. Muna alfahari da wannan kamar yanda muke alfahari da haihuwarmu da kikayi. Komai daya faru mun yarda mun karɓesa matsayin jarabawarmu kuma ƙaddararmu. Amma dan ALLAH muna roƙonki a karo na farko kije kiyi nazarin komai da ya faru. Tun daga aurenki da Abanmu har zuwa yau minene suka aikata miki na cutarwa? Wanne kikai musu ke na cutarwa?. Mu wanda kikai mana mun yafe miki shi kuma muna roƙon ki yafe mana wanda muma muka aikata miki ko ƴan uwana?”. A tare AA da Yaya Fawzan suka jinjina kawuna. Ya cigaba da faɗin, “Idan har kece mai laifi Mamy ki zauna ki nazartu da yanda ƙarshen yazo, ki daure ki shirya canja zuciyarki zuwa kyakkyawa kamar yanda matar can ta faɗa. Ba zamu so rayuwarki ta ƙare da hakkin kowa ba musamman iyayenmu Abah da Oum da suka kyautata rayuwar. Ki koma ga UBANGIJI Mamy shi mai gafara ne, kiyi tuba na gaskiya ALLAH zai yi alfahari dake. In sha ALLAHU zamu cigaba da sauke dukkan hakkinki dake a kammu. Zamu dinga zuwa dubaki a kai a kai, duk abinda kike buƙata ki gaya mana zamuyi miki shi in har baifi ƙarfinmu ba. Idan kun sauka in sha ALLAHU muma zuwa jibi yanda jikin Maanal ya kasance zamu biyo bayanku muga mazaunin naki. Ki riƙe a ranki muna sonki, muna kuma yi miki fatan shiriya, za kuma mu cigaba da roƙon ALLAH ya baki ikon neman gafarar duk wanda kika cutamawa”. Ya kai hannu ya ɗauke hawayen da suka cika masa idanunsa. Yaya Fawzan kam share-share suke zuba. Shima AA hawayen da suka ciko masa idon yasa yatsa ya ɗauke. Sannan ya kamo hannunta ya matse a cikin nashi, kafin a hankali ya kaishi wajen bakinsa ya sumbata. Daga haka ya buɗe motar ya fita. Suma su Babban Yaya duk suka fita. Haka suka kamata suka saka a wheelchair ɗin. Kamar yanda AA yay mata Babban Yaya da Yaya Fawzan ma haka sukazo suka kama hannunta duk suka sumbata. Sannan Aunty ta kama keken nata suka shige dan jirgin su zai tashi nan da mintuna..........✍️213
.......Nuratu da Saheeba ma haka suka shige suna waigen su AA suna kuka kamar ransu zai fita. Haka ma Aunty kuka take sosai. Su Babban Yaya basu bar airport ɗin ba sai da jirgin su Mamy ya ɗaga zuwa Kano sannan. Koda suka fito kuma driver ne kawai ya wuce gida su Mawaad Company ma suka tafi, suka kulle kansu a office ɗin AA. Ba wani hira suke ba ba komai ba kowa yana zaune ne shiru kawai. Sai lokacin salla yayi suje massalaci suyi su sake dawowa su zauna. Basu bar Company ɗin ba sai kusan goma na dare. Shima Baba Sardauna ne yay kiransu a waya yay musu nasiha sosai data ratsasu....
Washe gari mutanen Kano suka wuce suma da safe saboda jikin Maanal Alhamdullah da sauƙi babu wani damuwa sai fatan ƙarasa murmurewa. Nibras ce dai ƴan uwanta ma sun yanke hukuncin fita da ita waje saboda illar da ƙugunta ya samu.. Sai Oum da itama dai bata jin daɗi saboda damuwar tafiyar Mamy data sakama kanta. Dole aka kwantar da ita asibiti itama.....
__________★
Anan ɓangaren Hajiya Basariyya rayuwa ta mata zafi sosai. Komai babu daɗi. Tun tana tunanin kuɓuta a rayuwar Alhaji Balala harta fahimci al'amarin fa bamai sauƙi bane ba. Ta rame ta lalace tai baƙi kamar ba ita ba. Tun tana hawayen aikin yin tuwon gidan Alhaji Balala a ranar girkinta harta saba. Jini ko tunda Alhaji Balala ya fahimci na asiri ne ya tattara matansa ya musu tas, da yake shima sun san hatsabibin kansa ne babu arziƙi sukaje suka karya asirin ya cigaba da ragargazar amarcinsa. Sai ga Hajiya Basariyya da ciki. Wannan abu ya sake ɗaga mata hankali matuƙa. Tana tsaka da wannan laulayin jaraba suka samu baƙuncin Maman Yaseerah tazo bibiyar bashin kuɗinta. Itama dai Baban su Najma tuni ya tasheta a gidansa ganin iskancinta na ƙara gaba, yanzu haka yaran suna wajen uwargidasa ita kuma ta shiga buga barikinta da hatsabiban yan iskan bariki. Sun kuwa buɗe mata ido dan yanzu haka ma sune suka rakota har nan garin da Hajiya Basariyya ke aure. Babu mutunci suka dinga shekama Hajiya Basariyya dariya wai haka kuma duniya ta maida ita? Ita dai bata tanka musu ba, dan tsoro ma suka bata. Maman Yaseerah tace kuɗinta take buƙata. Hajiya Basariyya bata da su, babu mutunci tai waya da wani akan yazo ya sai kayan ɗakin Hajiya Basariyyar. Haka kuwa mutum yazo da ƙatuwar motar ɗibar kaya daga kankia. Akai cinikin kujerunta dake a waje rufe har yanzu babu wajen sakasu, da yake sayen mugunta ne kuɗin bai kai ba. Suka kuwa haɗa dana ɗakinta, haka suka sauke mata katifa a ƙasa suka zazzage mata kayanta daga wadrob a katifar suka kwashe komai sukai gaba suka barta da kuka da dana sanin sanin Hajiya Jumai a rayuwarta. Kishiyoyi kuma suka samu nayi da dariya da habaici har suna gayyato matan ƙauyen. Aka saka Hajiya Basariyya gaba harda waƙa idan ana luguden daka. Ko'a jikin Alhaji Balala duk da yaji haushin an rage masa jin daɗin hawa katon gado, amma tunda katifar na nan ai ba damuwa a ɗan shana ai rigijib-jib inji (Hadiza Kabara😂). Hajiya Basariyya bata gane ALLAH ɗaya bane sai da aka fara aikin gona. Ashe Alhaji Balala tattara matansa yake kaf da ƴaƴa da jikoki aje gona aiki. Tana kuka tana komai ga laulayi babu tausayi haka ya sakata a gaba kuwa itama aka tafi. Tun bata iya ba harta zage tana aiki. A wannan halin yayanta da su Madeena daya kwasa suje dubata suka sameta. Kuka su Madeena suka dingayi dan da farko wlhy basu gane Ummy ɗinsu bace ba ganin yanda ta ƙomaje ta tsofe ta fita a hayyacinta. Shi kansa Yayanta ya girgiza. Ga ciki, wlhy da babu ciki sai ya raba auren nan, amma yaya za'ayi da ikon ALLAH. Asibiti kawai suka kaita tai kwana uku, Alhaji Balala nata fushi amma yaya zaiyi. Ta ɗan murmure, Ƴaƴanta ya sake siya mata kayan ɗaki dai-dai zaman ƙauyen ba irin wanda ta rasa ba, ya bata jarin yin sana'a. Data kalla yaranta sai hawaye. Ko maƙiyi ya kallesu yasan suna jin daɗi suna kuma cikin kwanciyar hankali. Da zasu tafi ta basu kayan kuka kuɓewa daddawa sunkaima su Ammie. Haka suka tafi tana kuka sunayi. Bayan tafiyarsu da kusan wata guda Sageer ya tilasta Huznah suka zo suma. Suma hankalinsu ya tashi da ganin makomar Hajiya Basariyyar amma yaya zasuyi. Huznah na kuka Hajiya Basariyya nayi da neman gafararsu ita da Sageer. Da zasu tafi ya kawo alkairin mai yawa yayi mata. Ranta fal mamakin yaushe Sageer ya jiƙe haka, ga mota mai ƙyau ga kuɗi, kallo ɗaya tai musu shi da Huznah ga ɗan yaronsu kamar ta cinye dan kyau tasan hankalinsu kwance suke. Ga Huznah ɗin ma kamar da ciki a tare da ita. Suma haka suka wuce suka barta cike da jimami dan basu kwana ba. Labarin da su Madeena sukaje suka bama su Ammie akan halin da Umminsu ke ciki ya ɗagama su Ammien hankali sosai. Haka Yazeed ya shiryo shima yazo ya mata alkairi sosai, a ransa kuma ya kudira sai ta ɗauketa a garin nan ko bajika koba daɗe. Koda ya koma shima ya labartama Daddy komai ko tari baiyi ba balle ya nuna ya jishi, dole ya tsuke bakinsa dan wargi ma waje yake samu......
★ Bisa tirsasawar Daddy su Basira duk sun fidda mijin aure suma. A yanzu haka an tsaida rana harda Yaya Yazeed da Khadijah da suka daidaita kansu. Ƴan uwa nata farin ciki da wannan al'amari. A tsakanin ne kuma Amaal ta haihu. Kasancewar Maanal na asibiti bataje ba, hakama Oum na fama da kanta. Sai Ameerah da Najma. Su Umma ma sun zo daga Kano. Ta haifi namiji abinta.
_________★
Su Mamy an isa Kano lafiya, gidan babu laifi da ɗan ƙyansa gwargwado amma dai ƙarami ne dai-dai zaman mutum ɗaya. Su Saheeba da sunce bazasu zauna ba. Dan haka suka wuce gidan Babansu wai can zasu zauna. Haka suka wuce can kayansu ma can aka sauke. Kamar gaske matar babbansu ta tarbesu da farin ciki da murna. Suko suna sha mata ƙamshi saboda ganinta ƙarama. Basu san kwantar musu da kai tayi ba kawai. Tun suna nuna isa har suka fara sakkowa ganin ita babu ruwanta, shima Babban yana sake ji da su saboda tausayin halin da suke ciki, duk da ya yarda su masu laifi ne dan har kiran Abah yayi ya sake bashi hakuri da su AA. Amma yayi imanin duk laifin uwarsu da yar uwarsa Turai ne da Mamy da suka ɗorasu a kan hanyar banza. Da wayo da wayo sai da sabbin ƙawayensu suka sakasu salwantar da komai da suka zo da shi, na kayan ɗaki da sutura da duk wani kayan adonsu. Sai da komai ya ƙare aka fahimci harkar shaye-shaye suka shiga, aiki matar babansu tace bazata zauna da su ba dan sun fara mata ƴan sace-sace. Rikicin yau da ban na gobe daban babu arziƙi suka bar gidan dan baban nasu ma ya daina raga musu. Komai matarsa ta gaya masa sunyi yarda yake dan ta fisu gaskiya, duk kuma rantsuwar da zasuyi baya saurarensu sai yace dama haka suke da baƙin hali kamar uwarsu. Ganin fa abin bana wasa bane babansu na neman tsine musu suka tattara suka koma wajen Mamy da tuni Uwangale ta gudu ta barta. Sai wata mai aikin da su Babban Yaya suka ɗauka mata dan sun zo har sau biyu sun dubata. Sai dai ranar suke suwa su koma dan har yanzu Maanal da Oum na asibiti. Amma suna saka ran a satin nan za'a sallamesu. Idan kuma an sallamesun ƙasar zasu bari dan samu su huta zuwa nan gaba sa dawo ko hakan zai sa su sami sauƙin zuciya dana al'amura.
Da farko Mamy taƙi amsar su Saheeba. Sai da Aunty Babba ta saka baki tare da mata nasiha sannan. Dan Mamyn kam yanzu ba tada bace. Tayi laushi sosai kawai dai har yanzu ALLAH bai bata ikon kwantar da kanta ta nema gafarar kowa bane. Amma har kiran Oum take taji yaya jikinta. Ta kuma kira AA a haɗasu da Maanal itama tai mata yaya jiki. Hakan na ɗan saka musu jin farin ciki a ransu. Suna kuma mata addu'ar shiriya da ƙara gane gaskiya koda anan gaba ne kafin dai lokaci ya ƙure mata.. Dawowar su Saheeba gidan kuma sai rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, kullum faɗa ita da su. Wani lokacin tana zaginsu suna zaginta. Basa raga mata sam. Bata isa sakasu aiki ba. Dan kai tsaye zasuce bazasuyi ba. Ga yawon darensu na tsiya. Ga kudi data ajiye su sace. Tun tana iya daurewa harta fito fili ta sanarma su babban Yaya saboda wani duka da Saheeba da Nuratu suka haɗu suka laƙaɗa mata saboda Saheeba tayi shaye-shaye tazo ta musu amai a falo Mamyn tayi magana. Babu ma wanda ya sani babban Yaya ya zo Kano. Shi kansa yanda yaga su Saheeban sun koma sai da mamaki ya kamashi. Kallo ɗaya zaka fahimci shaye-shaye suke yi. Basu da wata maraba da karuwai wlhy. Ga uban ƙarin gashi, ga ƙarin farce dana girar ido. Idanu duk sun juye saboda shaye-shayen ma na hauka sukeyi komai aka samu ɗorawa ake yi. Aiko ya lakaɗa musu shegen duka ya korasu, ya kuma saka yan bijilanti duk randa suka gansu a jikin gidan ma su musu dukan tsiya. Sai ya samu mijin Aunty Babba ya roƙesa akan ta dawo nan ta zauna tunda dama can gidan ya musu kaɗan ita da kishiyarta, yaranta kuma sun kaisu karatu waje shi da su yaya Fawzan ita kaɗai take zaune. Sai kawai ya amince Aunty ta dawo nan kusa da Mamy ɗin. Aka samo musu mai tayasu aiki. Duk wata zasu dinga aiko mata da maganinta na HIV, ƙafa da ido dai an riga da an rasa su sai haƙuri. Koda ya koma Abuja bai bama kowa labarin nan ba. Dan yanzu har kunyar kawo zancen Mamy suke gaban Abah da Oum dama matansu. Abin farin ciki kuma ya samu ma an sallami Oum da Maanal daga asibiti, bayan jiyyar kusan sati uku. Dan Maanal gaskiya ta wajigu matuƙar wajiguwa. ALLAH dai ya ƙaddara tana da sauran kwana ne a gaba da yanzu wata maganar akeyi.........✍️214
.......A washe garin da aka sallami Oum da Maanal suka bar Nigeria gaba ɗayan su. Kuma da alama wannan tafiyar mai daɗewa ce. Dan ƙasar Chaina suka dira. A block ɗaya suka kama wajen zama. Sai dai kowa da apartment ɗinsa, amma floor ɗaya suke kuma a jere guda huɗu reras. Kowanne a nashi akwai bedroom ɗaya, kitchen, falo, sai wajen karatu. Komai dai tsaff, babu takura babu gajiyawa. Tsarin kuma duk iri ɗaya ne. Duk a gajiye suke, dan haka kowa yaja matarsa suka shige nasu. Oum ta amshi ƴan biyu ita da Abah, idan akai musu wanka a maido su. Hakan ya bama AA damar jan hannun Maanal suka shige nasu suma. Dan shekaran jiya ƙiri-ƙiri da aka sallamosu asibiti taƙi zuwa sashensu ta wuce wajen Oum. Haka ta barshi ya kwana shi kaɗai, sai a jirgi ne suka zauna waje ɗaya. Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe ya mannata a jiki. Kallonsa take fuskarta babu walwala sam, ga idannunta sun ɗan ƙara fitowa saboda ramar da tayi ta jiyya. Shima kallon nata yake cikin wani yanayi mai wahalar fassara, kafin a hankali ya motsa lips ɗinsa cike da raɗa ya furta, “Besty bazaki yafe ma Ajwaad ki daina fushin nan ba?”. Kanta ta ɗan kawar gefe kaɗan, idannunta na tara ƙwalla, ALLAH har yanzu taƙi daina ganin yanda yake dukan Nibras a idanunta da yanda take tsirara sai kimono a jiki, da yanda ta dinga roƙonsa akan yaransu amma taurin kai irin na mutumin nan ko. Hummm. Hannu yasa ya dawo da fuskar tata inda yake, sai kuma a hankali ya matsar da tashi gab yana busa mata numfashi. Cikin sake sauke murya ya ce, “Yanzu minene laifina anan? Ko sai yanzu kike jin kishi?”. Hannayenta biyu ta saka ta turashi, dan wlhy da gaske fa sai yanzu take jin kishin abinda Nibras ɗin tayi, dan tun bayan lafawar komai zuciyarta ta kasa nutsuwa, tana matuƙar son tasan minene ya faru har yay ma Nibras dukan nan, musamman data ganta tsirara sai kimono a jiki. Amma babu wanda ya gaya mata komai har shi. Bata zarginsa, kuma ai tasan Nibras ɗin ce ta kawo masa kanta, amma idan ta tuna ko wani abu ya faru zafi zuciyarta take mata. Yanda take turashi shi kuma ko gezau baiyi ba ya sake fusatata tasa hannaye biyu tana dukan ƙirjinsa. Tsayawa kawai yayi yana kallonta yana danne dariya da ƙyar, sai da tayi iya iyawarta har ta gaji dan kanta ga hawaye sannan yay murmushi da kamota ya rungume tsam a jikinsa. Sai ta sake sakar masa kukan kawai. Baice mata komai bai har tayi shiru dan kanta sai a jiyar zuciya kawai take saukewa, sannan ya ɗagata cak ya nufi bedroom, saman haɗaɗɗen gadon ɗakin ya kwantar da ita ya fita ya jawo akwatinsu ɗaya jal sai dai babba ne sosai, sai bag ɗinta da bag ɗin laptop ɗinsu ita da shi dan aiki kam dole a cigaba da yinsa daga nan. Har lokacin tana a kwance inda ya barta. Baiyi magana ba ya shiga bayin ya dudduba sannan ya dawo bedroom ɗin ma ya dudduba, ya fita falo da ko'ina na gidan ya sake dawowa ya shiga bayin ya haɗa ruwa a jacuzzi mai ɗumu da ƙamshi sannan ya zo ya ɗagata ya cire mata kaya ya cire nashi ya wuce da ita. Cikin ruwan ya saka su, a tare suka sauke ajiyar zuciya. Sai kuma yanda ya ɗan ƙanƙameta ta ɗago tana kallonsa. Murmushi yay mata ƙasa-ƙasa fuskarsa a shagwaɓe ya ce, “Please Besty ki huce mana”. Kafaɗa ta maƙe masa tana tura baki da kauda kai. Ya riƙo haɓarta cike da lallashi yace, “Mizan miki ki huce to?”. “Ka faɗa min abinda ya faru a ranar”. Ajiyar zuciya ya sauke, sai kawai ya shiga bata labarin komai bai ɓoye ba. Kai tsaye ta ce, “ALLAH ya isa ban yafe mata hawa min jikinka da tayi ba wlhy”. Dariya ce ta kusa kufcema AA ya danne da ƙyar, sai kuma ta kalleshi itama kamar wata yayarsa ta ce, “Kai ma ka kalleta ko?”. Kansa ya girgiza mata yana sake rungumota. “Ai har abada babu wata surar jikin mace da zata sake birge Ajwaad balle ta zame masa abin kallo in sha ALLAHU Besty. Kiyi haƙuri Besty mubar maganar nan wlhy ko tunawa bana son yi dan ƙona ni take matuƙa, ina jin nauyi da kunyar Yaya Fawzan da ke kanki da yarana, shiyasa har yanzu ji nake ban gamsu da abinda nai mata ba ma”. Karon farko Maanal tayi murmushi tana shafa ƙirjinsa cike da kulawa. Sai kuma ta tausasa murya ta koma lallashinsa. Sun jima a bayin kafin su fito, haka ya taimaka mata tai shirin barci shima yayi, basa jin yunwa dan sun ci abinci a jirgi gab da zasu sauka. Dai-dai nan bell tai ƙara, yasan su twins aka kawo dan haka yaje ya amso su hannun Abah, sai coffee da Abah yay musu order shima suma su Babban Yaya sun amshi nasu. Sukaima juna sai da safe ya koma nasu shima ya shigo. Bayan sunsha coffee ɗin Maanal tayi feeding su twins kwanciya kawai sukayi duk da AA na cikin yanayin buƙata haka ya daure....
__________★
Satinsu ɗaya kenan a Chaina, Alhamdullah jikin Maanal kuma yayi sauƙi sosai, dan anan ma ta sake ganin likita sun tabbatar musu komai kuma normal. Shi AA ma ranar baya nan sunyi tafiya da abokinsa prof.. wani program. Oum da dama tafe take da kayan gyaranta sai tayi amfani da wannan damar ta shiga gyara Maanal ta jiki data ciki. Dan danan ta ƙara murjewa da gogewa dama ramar nan da tayi duk ta ciko abinta, sai wani glowing take kuwa Masha ALLAH. Ameerah da Najma suka sakata gaba, wai da alama Yaya AA na dawowa ba sauƙi za'a sake samo twins. Tun tana ƙyalesu harta fara ramawa itama. Kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki da ƙaunar juna ta haƙiƙa. Su twins sam basu da taka maiman wajen zama. Barci kawai ke kaisu wajen Maanal. Kwanan su AA takwas suka suka dawo. Kallo ɗaya da Maanal tai masa ta fahimci babu sauƙi, dan bai ɓoye mata ba ya fito fili ya nuna mata yana cikin wani hali. Murmushi kawai tayi batace komai ba, sai da ta taimaka masa yaci ya ƙoshi ta jashi bayi yin wanka. Anan ne fa ya kasa jurewa aka fara sakin layi, ƙarshe dai babu arziƙi aka kammala wankan aka fito. Daga nan ne fa labarin ya canja. Haba ai yayi haƙuri, kusan wata biyu. Yako tabbatar mata yayi haƙurin, dan taji a jikinta har sai da ta koma masa kuka da magiya. Amma ina sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya koma lallashi da ban haƙuri, itako tana zuba masa shagwaɓa. Tun daga ranar aka buɗe sabon shafin amarci. Kullum suna sake mannema juna, kowa ƙoƙarin ƙyautatama ɗan uwansa yake. Kamfani kuwa suna tafi da komai yanda ya dace daga nan tamkar suna a gida Nigeria. Ga yaransu sunyi ƙyau sosai kamanin iyayensu na sake fitowa a tare da su. Haka suma su Babban Yaya komai Alhamdullah, daga ɓangaren aiki har samun soyayya wajen matayensu, dan daga Ameerah har Najmah suna iya ƙoƙarin su suma na faranta musu. Ga ciki suna fama amma basa nuna gajiyawa da kulawa. Tsakaninsu da Oum da Abah tamkar iyaye ne da ƴaƴa ba surukai ba da iyayen miji. Duk abinda basu fahimta ba haka Oum ke zama ta koya musu yanda zasu gane. Kamar yanda suke kiran iyayensu da ƴan uwansu haka suke kiran Mamy suna gaisheta da Aunty, tun Mamyn bata sakewa har dai ta sake ɗin. A haka suka shiga watan haihuwa, dan tsakaninsu babu wani nisa sosai. Gaba ɗaya sai kulawarsu ta koma ƙarƙashin Oum da Maanal. Mazansu da ƴan uwa na binsu da addu'ar sauka lafiya. Alhamdullahi Ameerah ce ta fara haihuwa ɗiya mace. Zo kaga murna wajen a halin Darma dana Hajiya Shuwa da dangin babanta na Katsina. Dan danan hoton yarinya mai kama da babanta ya baje ko ina. Kowa farin ciki yake da annashuwa. Anama Baby addu'a anama mai jego. Anama su Oum barka. Lokacin da Mamy taga hoton Baby harda hawayenta. Ita Aunty ma wlhy yanzu tausayi ƴar uwar tata ke bata. Sati ɗaya da haihuwa aka sakama yarinya sunan Oum, sunan Anum ke nan, sai dai ita suna mata laƙani da Zarah. Duk da ba ƙasarsu ba AA yace sai sunyi shagali. Haka kuwa akayi, suka haɗa ɗan walimar cin abincin dare suka gayyaci abokan arziƙi na ƙasa da baƙin haure irinsu. Akaci akasha aka ɗan rausaya. Ƴan Nigeriya sai videos sukaita gani kawai da sanya albarka. Maijego tayi ƙyau har ta gaji, hakama Baby da ƙawayen maijego su Maanal, su twins yayu da sukai ɓul-ɓul abinsu dan har sun fara koyon zama ma sun sha ƙyau. Sati uku tsakanin haihuwar Ameerah data Najma, itama ta sulluɓo yar budurwa mai kama da Yaya Fawzan. Yara dai duk sun rantse gidansu zasu ɗakko. Ya suhanallah wannan haihuwa ta musamman ce a zuri'ar Darma baki ɗaya. Danda nan itama hoton Baby ya fara yawo, finally Yaya Fawzan yaga jininsa a duniya. Ga yarinya ƙatuwa Masha ALLAH. Mutane sun so azo Nigeria a yi suna, sai dai yanzu ma haƙuri su Oum suka basu, dan su fa da gaske so suke su bama Nigeria iska sosai da sosai. Nan ma AA bai haƙura ba yace sai fa sunyi bikin suna. Haka kuwa sukayi shi tamkar na haihuwar Ameerah. Yarinya ta ci suna Khadijah. Nan ma anci an sha an yi wadaƙa sai dai mu babu damar cin banza wannan karon an barmu a Nigeria 🤭🥱. To ALLAH ya sanya albarka bazamu fasa addu'a ba ai.........✍️
215
........Sosai Oum ta tsaya akan masu jego sukai jego mai ƙyau da kulawa. Bawani batun wanka ko gargajiya amma komai Alhamdullah. Ga yara sunata ƙyau abinsu kamar ka lashe. Bayan sunan ne AA da Yaya Fawzan suka je Nigeria. Satinsu ɗaya suka dawo, sai dai sun biya ta saudia sun ɗakko Naufal da suka samu hutu. A zuwa sun nan sosai zuciyar Mamy ta karaya, dan ta gama yarda dai ƴaƴanta ba nata bane ba na Fateema ne. Mijin ma nata ne. Duk da nadama ta mamayeta ta gagara ɗaga baki ta nema gafarar kowa har yanzu. Sai aikin kuka, su dai su AA sunta lallashinta da mata nasiha iya iyawa. Sannan suna mata dukkan gatan daya dace akan komai tsaye suke a kanta. Kai bama su ba ko Baba Sardauna da su RK hidima sukema Mamy sosai, kawai dai sunan bata a gidan Darma ne yanzu. Sai nakasan ƙafa data ido data zuciya dake zagaye da ita. Idan akai dubi ta wani fannin kuma data gangar jiki saboda HIV. Amma da yake tana shan magani bama zaka gane ba. Zuwan Naufal yama kowa daɗi, yaro ya ƙara girma ya fara zama ɗan saurayi, kamaninsa da su AA ya fito tsaff kamar sunyi kaki. Abin mamaki ko tambayar Saheeba baiyi ba. Sai ma farin cikin ganin su Oum da sabbin ƙanne har huɗu daya samu. Duk motsi sa kuwa yana manne da yaran nan. Yay hutunsa ya gama Abah da Oum suka maida shi Saudia, suma sun ɗan huta na sati uku sukai umrah suka wuce Nigeria dan Baba Sardauna baya jin daɗi. Sun duba shi aka gaggaisa da ƴan uwa da abokan arziƙi, har gidan Mamy Oum taje. Taji daɗin kuma ganin yanda Mamyn take cikin kulawa mai tsafta da nagarta. Suka sha hira Mamy na faman kukan zuci. A yanzu ma ALLAH bai bata damar roƙon Oum gafara ba. Girman kai da taurin zuciya na hana bakinta buɗewa akan hakan. Satin su Oum biyu a Nigeria suka koma abinsu....
________★