Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 17

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 17

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 17: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 17. .........Yau kam za'a iya cewa…

4,445 words

.........Yau kam za'a iya cewa itace ta riga kowa fara tattara kayan tashi tun lokaci bai gama cika sosai ba. Dan zuciyarta gaba ɗaya a ƙuntace take. Ga ƙirjinta ya mata wani irin nauyi sosai. Tamkar an saita sai ga kiran RK ya shigo mata. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga, sallamarta kawai ya amsa yace ta fito gashi a waje yana sauri ne bazai shigo ciki ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da amsa masa da gata nan. Daga haka taima sauran sallama kamar yanda ta saba ta wuce. “Kai mutuniyarku kamar fa yanayinta ya sake canjawa tunda akace ga budurwar CEO”. Zaharadeen yay maganar yana gumtse dariya. Caraf Yusuf yace, “ALLAH nima na lura da hakan, anya kuwa itama bata faɗa tarko ba? Kasan CEO da farin jini wajen matan kamfanin nan kamar ya musu turaren asiri”. Dariya suka kwashe da shi, Ema dake jin hausar sama-sama dan da Hausa suke gulmar ya ce, “Baku ji labarin ɗazu ba, itama sonshi take shiyyasa take mana wulaƙanci, in dai CEO ne duk zasuyi su gama maitarsu”. Tsaki yakub yayi tare da miƙewa yana faɗin, “ALLAH ya shirye ku, kuna maza amma gulma ta riga ta muku katutu. Haka kawai kuna ma baiwar ALLAH ƙazafin abinda baku da ilimi a kansa.” Caaa suka yo masa da masifa suma, bai kulasu ba yay wucewarsa ya barsu....

★ ★★ ★

“Baby anya kinyi murna da dawowata kuwa?”. RK dake kallon Maanal cikin wani yanayi ya faɗa murya a raunane. Karo na farko ta ɗan dubesa, sai kuma tai murmushi da bata cika yi ba. Shi kansa saida ya lumshe idanu saboda yanda murmushin nata ya wani ratsa masa zuciya. Idanunta ta ɗan janye daga kallonsa ganin yanda yake wani ƙanƙance nasa idanun. “Daga dawowa zaka fara rigimar taka ko”. Ta faɗa ƙasa-ƙasa batare da tunanin zai jita ba. Amma a mamakinta sai taji ya saki ƙaramar dariya da faɗin, “Oh ashe kallon rigimamme ake min ni Rafeeq”. Murmushi kawai ta sake yi batace komai ba. Shima sai ya tada motar suka fice a kamfanin. Sun ɗan yi nisa da tafiyar yanata mata labarin inda yaje. Ita dai bata cewa komai shi kuma bai damu ba. Sai da suna gab da shiga anguwar su Shahidah tace masa, “Yaya jikin Aunty kuwa? Kaƙi dai bani address ɗin naje na dubata”. “Ayya! Amin afuwa gimbiya. Kin san tafiyar nan ce da babu shiri kawai ta kawo tsaikon. Amma idan babu damuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dai ki shirya nazo muje bayan sallar magrib”. Ɗan jimm tai sai kuma ta ce, “Okay ALLAH ya kaimu, zan dai fara sanarma Didi yanda tace”. “Ba damuwa hakan ma yayi”. Ya ƙare maganar dai-dai yana horn a ƙofar gate ɗin. Da sauri maigadi ya wangale ƙofar bayan ya leƙo yaga shine. Sun saba sosai saboda RK akwai sauƙin kai ga ƙyauta, da wannan halayen nasa yake saurin saye zuciyar mutane da yawa. Mutum ne mai sauƙin kai matuƙa, da wahala ka zauna da shi bai shiga ranka a lokaci ɗaya ba. Sai da ya gama dai-daita parking idanun Maanal suka sauka akan motar Yazeed. Motar ta zubama idanu na tsayin sakanni, sai kuma ta buɗe ta fito. Shima RK ɗin fitowar yayi hannunsa ɗauke da ledar da bata san da ita ba, sai lunch box ɗinta daya haɗa ya ɗakko. Ganin inda take kallo shima sai ya kalla wajen, a take fara'ar fuskarsa ta canja, har zai miƙa mata kayan dan baida niyyar shiga ciki amma sai ya fasa. Cike da basarwa yace mata, “Muje”. Kallonsa tayi, sai ya ɗauke kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana amma sai ta fasa, dan ta tabbatar sai ya shiga ɗin tunda yaga Yazeed ɗin na ciki. Ita kam bata san yaya zatai da wannan mutanen ba ƴan rigima. A tare suka shiga falon tana gaba yana biye, Yazeed kuwa na zaune tare da su Barrah kasancewar yau babu islamiyya alhamis ce. Tunda ta shigo shima idonsa kyam a kanta, sai dai yana ganin RK ya tsuke fuska. Jitai kamar ta fasa ihu, amma ta daure dai ta ƙarasa, sannu da zuwa tai masa tare da gaishesa. Shima RK sai ya miƙa masa hannu a ɗage. Shima Yazeed ɗin a ɗagen ya bashi nashin suka gaisa sama-sama. Daga haka RK ya kai zaune yana janye ra'ayin su Haneeff. Shi kuma Yazeed sai ya maida hankali ga Maanal duk da dai yanzu babu fara'ar data shigo ta ɗan gani a fuskarsa. Dama dai can shima ɗin kamar ita ne ba gwanin fara'a bane ba. Magana Yazeed ɗin ke mata ƙasa-ƙasa tana bashi amsa cikin yanayinta na rashin son magana. Yanda RK ya maida hankalinsa akan shirmen su Barrah sai ka ɗauka bai damu dasu ba, sai dai gaba ɗaya kunnesa da hankalinsa na akansu. A haka Shahidah tai sallama ta shigo falon. Wata irin ajiyar zuciya Maanal ta saki acan ƙasan maƙoshi, kamar an saita sai ga Huznah itama ta shigo, sai dai ita tana cin karon da Yazeed tayi wani turus na ɗan firgici, shima ɗin kallonta yake da mamaki. Cikin ɗari-ɗari ta gaida shi gefe kuma tana satar kallon RK da tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke idanunsa ya maida ga Maanal. Amsa mata Yazeed ɗin yay da faɗin, “Ke daga ina haka? Yaushe kika zo Abuja?”. Daburcewa Huznah tayi, dan duk fitsararsu suna tsoron Yazeed kasancewar baya ɗaukar raini dukansu uban kowa yake ci a gidan. Cikin ɗan sarƙewar murya ta buɗe baki zata masa bayani Shahidah ta tari numfashinta. “Ayya yaya Yazeed zumunci tazo yi mana. Jiya ta iso zata mana hutu ne”. Shahidahn ya kalla kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Da wannan Huznah ta samu ta gudu ɗaki cikin sassarfa. Maanal nason shigewa ta ɗan watsa ruwa babu dama, sunzo sun sakata tsakkiya. Haka dole ta haƙura har ALLAH yay balling ta akai kiran sallar magriba sannan suka miƙe dan zuwa massalaci. RK dai ya mata sallama alamar bazai dawo ba. Amma Yazeed baice komai ba, hakan ba nufin shi yana nan kenan. Sanda ta shiga ɗaki baje-baje ta iske Huznah a gado tana waya. Sai ƙyalƙyala dariya takeyi. Komai Maanal batace da ita ba ta wuce bathroom. Daga cikine take ɗan jiyo hirar Huznah ɗin. “Ai ki bari kawai guy ɗin nan ƙarshe ne. Ga ƙyau, ga aji, ga kuɗi ga iya wanka. Kin san ALLAH yau jinai kamar na rungumesa.” Dariya ta ƙyalƙyale da shi alamar ana magana daga can, caraf ta cigaba da faɗin, “Ai gara kam kuyi sauri ku kaini kada naja muku abin kunya a gari, wlhy har gida yasa aka kawoni a wata azababbiyar motarsa. Wa ai gobe ma komawa zanyi dan ya tabbatar da ƙarfina na shigo”.. Kai kawai Maanal ta girgiza da taɓe baki, sai ma ta ɗauke hankalinta daga sauraren zantukan shirmen. Ita dama tasan ba banza ta kawo Huznah Abuja ba, ashe kuwa namiji ta biyo. Kai wannan abun kunya dame yay kama mtsoww!.

__________★

Washe gari sai ga Yazeed wai yazo kaita office da kansa. Rasama abin cewa Maanal tayi, tadai cigaba da cusa breakfast ɗin da Shahidah ta tsareta yi saboda shan magani. A haka yazo ya samesu. Ta gama shan maganin tana tattara kayanta sai ga maigadi yazo yana sanar mata ga RK yazo, wai ya kira wayarta switch off. Gaba ɗaya sai Maanal ma ta kasa motsi, idanunta cike da ƙwalla ta kai dubanta ga Shahidah da abin yama fara bata dariya. Dan ita kam Yazeed da RK ɗin yanzu dariya al'amarin nasu ke bata. Kowanne baya iya ɓoye kishinsa akan Maanal. Ta wani gefen kuma tausayi suke bata su duka ukun ma. Inda Yazeed yake Shahidah ta juya, sai ta samu wayam alamar ya fita. “Tofa, shi kuma Ya Yazeed yaushe ya fita”. Da sauri Maanal ta juya inda Yazeed ɗin yake, itama ganin wajen empty sai ta ɗan waro idanunta tare da maida kallonta ga Shahidah. “Didi ina kuma yaje?”. “Wajen abokin takararsa mana. Ai wannan samari naki Maanal na kula kowanne da zafinsa yake. ALLAH dai yasa a rabu lafiya kawai. Kinga muje kawai ni na saukeki da kaina sai a raba rigimar. Ya kamata ma su duka ki hutar dasu zuwa kaiki da ɗakkokin nan dan na fahimci abin yana neman ɗaukar wata hanya ne a tsakaninsu”.

Koda suka fito sun samu rayukan Yazeed da RK ɗin duk a ɓace, kallo ɗaya Maanal tai musu ta wuce ga motar Shahidah tai shigewarta. Sai ita Shahidahn ce ta ƙarasa wajensu. Maanal bata san mi yayar tata ta sanar musu ba, koda ta dawo motar kuma batai mata bayani ba ta tayar suka fice. Haka ta kasance a office babu wani walwala a tare da ita. Dan fuskarta tafi kowacce rana kasancewa a tsuke. Yau ma anyi zama tsakaninta da Marketing and sales manager, sai Head of operation da quality control manager, bayan sun gama meeting akai kiranta da mata tambayoyi akan dai wannan zane nata da company zai fitar. Yau ma da yake bata buƙatar kowa yazo ɗaukarta da wuri ta tashi. Ta fito harabar companyn hankalinta akan agogon hannunta tana kallon lokaci suka kusa cin karo da assistant ɗin CEO. Haƙuri ya shiga bata itama ta bashi. Ta raɓesa zata wuce idonta ya sauka akan AA Darma ɗin dake tsaye shi da wani dattijo suna magana. Yau dai sanye yake cikin farar shadda ƙal datai masa shegen ƙyau da sake fitowarsa a cikakken bahaushensa ɗan arewaci dan harda hula. Da sauri ta kauda kanta tare da ƙara sauri a takunta duk da hakan bai hanata kasancewa a nutsenta ba. Sarai AA Darma ya ganta shima. Amma ya basar ya cigaba da maganarsa da Alhaji Wakili. Alhaji Wakili tamkar uba ne a wajensa, dan kuwa abokine ga mahaifinsu, sai kuma huɗɗar kasuwanci ta haɗasu, dan yanzu haka ma akan wannan project da zasuyi wanda Maanal tai zanen agogon Alhaji Wakili ɗinne ya kawo mutanen....

Dai-dai Maanal ta fito gate ɗin da nufin samun abun hawa wata taxi ke ƙoƙarin shiga cikin Companyn. Sai dai securitys sun hana mai taxi ɗin shiga, sun tabbatar masa da dole wanda ke ciki sai dai ya fito ya ƙarasa ciki da ƙafarsa. Yanda aka buɗe ƙofar motar a fusace ya ɗan ja hankalin Maanal, a mamakinta sai taga Huznah ce ke fita a motar. Jitai ma gaba ɗaya ta ƙame a wajen ganin yanda Huznah ɗin ke musu masifa da tabbatar musu akanta zasu iya rasa aikinsu. Sukuwa dai securitys ɗin sunce bafa zasu bar mai taxi ya shiga ba dan dokar companyn ce hakan. Ko ma'aikatan wajen indai motar haya suka shigo ƙa'ida anan suke sauka su ƙarasa ciki da ƙafarsu. Ran Huznah ya kai maƙura a ɓaci, kuma dole ta haƙuran ta sallami mai taxi ɗin ta ƙarasa da ƙafar zuwa ciki. Ga ma'aikatan sun fara fitowa sai kallonta ake ana ƙus-ƙus, itako tana wani yauƙi da taku ɗai-ɗai. Maanal dai tuni ta shige taxi ɗin da Huznah ɗin ta fita. Haka ta iso gida al'amarin nata mata kaikawo. Har jitai ta ƙagara Didin ta ta shigo. Zuwa duba Auntyn RK yasata watsar da komai bayan tayi wanka ta shiga kitchen. Da taimakon Linda ta fara haɗa cake da wasu ƴan kalolin snacks da suka shirya zatayi dan dubiyar ita da Shahidah. Suna tsaka da aikin Shahidah ta shigo tare da yara data biya ta ɗakko a makaranta yau da kanta. Dama haka take musu duk juma'a sai dai idan aiki ya mata yawane tabar driver ya ɗakko su kamar yanda ya saba. Joining ɗinsu tayi a kitchen ɗin, anan ne Maanal ke labarta mata batun Huznah. Itama mamaki sosai tayi Shahidahn, sai dai basu iya hasaso abinda ya kai Huznah Maawad company ba, har kuma suka kammala aikin bata dawo gidan ba. Dama ba kowa take sanarma zata fita ba, ko jiya Shahidah bata san da fitar tata ba hakama yau ɗin. Ganin har anyi la'asar RK bai kirata ba bai kuma zo gidan ba ta fara tunanin ko lafiya? Gashi ta riga ta ɗauri niyyar zuwa dubiyar nan yau dai ta huta. Kuma jiya da dare ta sanar masa da anyi la'asar yazo ya kaita dan Didi tace bata yarda sai bayan magrib ɗin nan ba. Jitai kamar ta sharesa, sai kuma dai ta danne zuciyarta ta tura masa gajeren saƙo, daga haka ta koma falo ta zauna dan ta shirya tsaf hakama Barrah da Haneeff da zasu mata rakkiya tsaf suke. Sai kusan huɗu da rabi RK ya iso gidan, yana sanye da shadda shima yanzu ruwan zuma harda hula. A ranta ta ɗan taɓe baki da faɗin (idan anga kuna wankan shaddoji sai juma'a kawai) a fili kam tayi kicin-kicin da fuska daga gaisuwa bata sake kulashi ba, dan shima dai fuskar tashi yau babu walwala. Da alama tun fushin safen ne bai gama sakinsa ba........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖3️⃣4️⃣

........A motar ma gaba ɗaya sai ya maida hankalinsa akan tuƙi da surutun su Barrah ya shareta, itama dai hankalin nata naga duba wasu novels da Aneesa ta tura mata sunayen su. Tafiyar tasu ba wata mai nisa bace suka iso. Gidane daya amsa suna gida, dan ko'a cikin garin Abujar kasan mai shi yaci ya ƙoshi. Sai da security ɗin ƙofar yazo har inda suke yaga waye sannan ya danna remote ɗin hannunsa gate ɗin fari tas ya zuge kansa. Godiya RK ya masa tare da shigewa cikin katafaren gidan daya yalwatu da shuke-shuke masu matuƙar ƙayatarwa da bama zuciya nutsuwa. Kafin yau Maanal na jinjina girma da tsaruwar gidan Daddy, hakama gidan Didinta Shahidah gidane mai ƙyau da ƙawa. Sai dai gidan nan ya matuƙar disashe mata waɗan can da take tunanin babu kamarsu. Hatta da parking space a tsare yake anan. Tunda suka fito su kansu yaran ke bin ko'ina da kallo baki a buɗe, Haneeff dai daya kasa haƙuri matsowa yay kusa da Maanal cikin raɗa ya ce, “Mie-mie! Uncle R house ya haɗu kamar ba'a Nigeria ba”. Kasa cema yaron komai tayi, sai hannunsa daya riƙo nata ta ɗan matsa kaɗan. Dai-dai nan RK dake tattaro kayan tsarabar da bai san ko minene ba ya juyo garesu. Ƙaramin murmushi ya mata ganin yanda take binsa da kallo, batare da yace komai ba ya nuna mata hanya alamar suje, tare da kama hannun Barrah. Ɗauke kanta tayi kamar bata fahimta ba, sai ya sake sakin murmushi yay gaba, dan wannan yana ɗaya daga cikin halayenta dake matuƙar birgesa. A gidan sassa ne har kusan shida. Kuma kowanne da tsarinsa, sannan tsakaninsa da ɗan uwansa akwai ƴar tazara ta yanda baka isa sanin mi nacan keyi ba, ko shi yasan mi kakeyi a naka part ɗin. Part na tsakkiya a hannun dama suka nufa, RK ya danna bell tare da ɗan juyowa ya kalla Maanal. “Ni dai kar aje ana fushi dani a gaban Aunty na”. Yay maganar yana kashe mata ido ɗaya. Harararsa ta ɗan yi kawai, tare da ɗauke kanta. Shi kuma sai ya sake sakin murmushi. Zaiyi magana aka buɗe ƙofar. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce sa'ar Maanal ba, cike da girmamawa ta ɗan rissina tanama RK ɗin sannu da zuwa. Duk da jikinta fes yake cikin tsafta a kallo ɗaya zaka fahimci mai aiki ce, sai dai masu aikin ma irin wanda ke samun kular nan dan babu wani nakasu a tare da ita. Kayan hannun RK ɗin ta amsa, yayinda shi kuma cikin dakewa kamar bashi ba yake tambayarta “Aunty fa!?”. “Tana upstairs....” Kansa kawai ya jinjina mata, batare da yace komai ba suka ƙarasa shiga cikin falon da yasha black & golden color na kujeru da labulale, sai wani irin ƙamshin turaren wuta ke tashi mai ratsa zuciya. Ga sanyin ac mai kashe jiki. Gaba ɗaya jikin Maanal sai ya ƙara sanyi. Bata sake tsinkewa da al'amarin ba sai da ya danna wani maɓalli ƙofar glass ɗin dake kamar bango guda ta zuge kanta suka shigo wani falon, nan kam komai golden yellow & white ne, shima dai babu kowa sai ƙamshi dake tashi, wayar da yake dannawa ya kai kunnesa, ba'a wani jima ba aka ɗaga. “Aunt mun iso”. Ya faɗa cike da girmamawa. Maanal dai data zama kamar wata gunkiya bata san amsar da aka bashi ba taga ya juyo ya kalleta da murmushi, sai kuma ya furta, “Okay gamu nan”. Yana yanke wayar. “Sorry muje tana sama”. Ya sake faɗa idanunsa akan Maanal ɗin. Kanta kawai ta jinjina masa batare da tace komai ba. Sai dai tana mamakin ta ina kuma zasu bi zuwa saman dan bataga hanya ba sam anan. Amma a mamakinta sai ya nufi wata ƙofa da su, anan ne taga ƙafar benen da shima aka ƙawata matuƙa, dan hatta a ƙasansa ma wasu kujeru ne guda biyu aka tsara da gani wajen zaiyi daɗin hutawa. Haka dai suka haura upstairs ɗin Maanal na sake jinjina jin daɗin da masu hannu da shuni keyi a ƙasar nan. Dole su manta da talaka, dole talaka yasha wahala dan bataga ta yanda za'a iya tunawa da rayuwarsa ba anan. A sama ma wani tsararren falon suka samu, wanda aka ƙawata da ash color na kujeru dama labulalen, nan ɗin ma dai ƙamshin turaren ne yay musu sallama da sanyin ac kaɗan, sai kuma nutsatstsiyar muryar dattijuwar dake musu lale marhabun cike da ƙasaita. Kasancewar RK ya rufe Maanal yasa bata ganin dattijuwar itama bata ganinta, sai dai muryar ta wani irin dakar mata ƙirji. “Rafeeq ƙaniyarka, dalla gyara ka wani rufe min ƙanwar tawa bana ganinta”. Dariya RK yayi tare da matsawa gefe yana faɗin, “Oh Aunt ni yau baki son ganina kenan?”. Baki ta buɗe zata bashi amsa amma sai ta gagara hakan, sakamakon saukar idanunta akan Maanal da ita nata idanun ke kallon ƙasa, dan RK ɗin na matsawa daga rufetan da yay ta rissinar da idanunta saboda yanda bugun zuciyarta ke ƙara ƙarfi. Ga wani irin yanayi mai wahalar fassara dake ratsata. Hakama zuciyarta ta mata nauyi matuƙa a cikin ƙirjinta..... Gaisuwar Barrah da Haneeff ce ta katse dattijuwar daga kallon Maanal, ta saki ajiyar zuciya da sakin murmushi tana miƙama yaran hannu da faɗin, “Ƙanwata kinga ƙaraso mana, Bismillah zo gareni”. Sake motsawa zuciyar Maanal tayi a karo na babu adadi, dan Muryar nan tana mata wani irin amsa kuwwa ne da maimaita kanta a matsayin wata murya da amonta ya faru ya kuma shuɗe a duniyarta ta baya. Amma sai ta dake, cikin yanayinta na nutsuwa ta cigaba da taka lallausan carpet ɗin dake tsakkiyar kujerun zuwa inda dattijuwar take zaune, dan tana zaune ne daga ƙasa abinta duk da tima-timan kujerun dake falon. Cak Maanal ta tsaya yayinda take gab da kaiwa inda dattijuwar take, bakomai ya sakata tsayawar ba sai murya ta biyu data daki tsakiyar kunnenta tayi amsa kuwwa a cikin kanta. Sam batai zaton akwai wani bayan dattijuwar a cikin falon ba duk da taji wani ƙamshi bayan na turaren da aka saka a gidan da wanda ta tabbatar dattijuwar keyi. Sai da RK ke faɗin, “Wai dama da gaske kake daga massallaci gida zakayo ashe?”. “Kaje nemana ne?”. AA dake kishingiɗe a saman lallausan carpet ɗin kusa gab da dattijuwar dan filo ne kawai ya raba tsakaninsu gabansa wasu document ne barbaje, sai dai a hannunsa shi novel ne yake karantawa, a maimakon shaddar ɗazun yanzu kam ƙananun kaya ne baƙaƙe a jikinsa. Amsar da RK ya bashi yana nuna Maanal da faɗin, “No naje ɗaukar Maanal ne kawai dai” ya sashi wani kallar ɗago idanunsa ya sauke a kan Maanal ɗin data kasa gaba ta kasa baya. Dai-dai nan itama Dattijuwar da hankalin ta ke akan su Barrah ta ɗago tana maimaita sunan. “MAANAL!” Sai kuma ta miƙe zaram. “Rafeeq da gaske Maanal ɗina ce kamar yanda zuciyata ta ayyana min yanzu-yanzu ko suna ne yazo ɗaya, to amma akwai kamanni mafa” ta kai ƙarshen maganar tana ƙarasowa inda Maanal take. Lallausan hannunta mai ɗauke da zabba masu ƙyau da ɗaukar idanu, tare da bangles takai kan haɓar Maanal data lumshe idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago. Sosai take raba idanunta akan fuskar Maanal ɗin, sai kuma ta juyo ta kalla RK da shima ya miƙe cike da mamaki, janyewa tai ta maida ga AA da ya maida idanunsa ga book ɗin hannunsa sai dai tuni abinda yake karantawar ya suɓuce masa. “Auta gane min nan, wlhy Maanal ce ko? Ko Auta Manaal ɗina ne dai ba wata ba. Ajwaad taso, taso dan ALLAH ka tayani gani ko idanun nawane dai ba Baby ba bace....” Da wani irin ƙarfi AA ya rumtse idanunsa batare daya ɗago ɗin ba, ko motsima baiyi ba daga yanda yake. Sai RK ne ya ƙaraso wajen cikin sassarfa yana faɗin, “Aunt da gaske kin san Maanal ɗina? Maanal Please! Da gaske kema kin san Aunty na?”. Duk ya ruɗe da farin ciki shi kam. Cikin rawar muryar kuka Maanal da tausayin yanda dattijuwar ta rikice ya sake mamayeta, a hankali ta shige jikinta tana faɗin, “Oum nice, Maanal ɗinki ce Oum. Dama baki manta dani ba, dama zan sake ganinki? Ashe muna da rabon sake haɗuwa kafin na koma ga ALLAH”. Wani irin kuka mai ban tausayi ya suɓuce mata, sai dai hakan bai hana muryarta fita cikin nutsuwa da sanyi ba. Sanyin dake bayyana tasirinsa a jikin AA, duk yanda yake sake kamewa da dakewa abin na neman fito da kansa. Dan Barrah da kukan Auntyn tasu ya sakasu yin narai-narai da idanu suma zasuyi kukan ta matsa gab da shi tana faɗin, “Uncle kaga Mie-mie na kuka ita da Grandma”. Amma ina baiji yarinyar ba, sai da ta ɗan girgiza shi sannan firgigit ya buɗe idanunsa da suka kaɗa matuƙa tare da ɗagosu ya sauke akan yarinyar. Dai-dai kuma Barrah ta miƙe ta nufi inda Maanal take ta rungume mata ƙafafu tana kiran sunanta. Ɗago Maanal Oum tai daga jikinta itama tana share nata hawayen ga murmushi yaƙi barin fuskarta. Hannayenta duka biyu tasa tana sharema Manaal hawayenta da suka gagara tsayawa, dan gaba ɗaya ma ta kasa cewa komai saboda ita kaɗai tasan irin kalar farin cikin da take ciki. Juyawa tai ga RK da ke kallonsu cikin ruɗani, murmushi ta sakar masa shima. “Rafeeq ALLAH yay maka albarka kaji, yau kam kayi mun babbar ƙyauta daka kawo min ɗiyata har gida.....” “Aunty duk kin ruɗar dani wlhy, wai kin santa ne daman?”. “Sosai kuwa Rafeeq, zan iya cemaka kusan nice na raini Maanal ma”. “What!? Raino fa?”. “Ƙwarai ma kuwa. Haihuwar Maanal ne kawai ba'ayi a gabana ba. Kunga bismillah kumuje mu zauna”. RK dai da ƙyar ya kai zaune, sai dai idanunsa akan Oum da Maanal kamar mai tsoron su ɓace masa. Waya Oum ta ɗauka tare da bada umarnin a kawo ruwa. Babu jimawa kuwa sai ga yarinyar nan data buɗe musu ƙofa ɗauke da tray wata da bazata wuce sha huɗu ba biye da ita. Cike da ladabi da girmamawa suka ajiye kayan a saman Centre table, sai kuma suka shiga gaishe da su RK. A dai-dai nan Oum dake riƙe da hannun Maanal kamar mai gudun a ƙwace mata ke tambayarta, “Ina ƴar uwata Maanal? Ina su Shahidah da Abban ku?”. “Oum Ammie na nan lafiya Lau, hakama su Didi, wannan ma yaran Didi Shahidah ne”. “Masha ALLAH! Masha ALLAH! Yanzu yaran Shahidah ne wannan? Kai jama'a ALLAH mai alkairi. Kuzo nan kuyi haƙuri ganin ƴata ya ɗauke min hankali”. Tai maganar tana kamo su Haneeff da sukai ƙwale-kwale saboda kukan Maanal ɗin. Cikin ɗari-ɗari bakamar ɗazu da farko ba suka ƙaraso wajen Oum ɗin, sai da Maanal ta kallesu da sakar musu ɗan murmushi ta ce, “Itama Grandma ce ku gaisheta ku faɗa mata sunayenku”. Karo na farko yaran suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka shiga gaishe da Oum ɗin. Barrah ta faɗa mata sunanta, da sauri Oum ta kalla Maanal. Murmushi Maanal ɗin tai mata da jinjina kanta. “Eh Oum sunanki aka saka mata, Ammie ce taso sakawa tun akan su Waleed, sai kuma suka kasance maza. Shine Didi na haihuwa aka saka”. Wani irin rungume Barrah Ammie tayi a jikinta, ƙauna matuƙar ƙaunar Ammie na ratsa ƙashinta da ɓargo. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “ALLAH sarki ƴar uwata. Ashe Asiya bata manta da ni ba”. Murmushi mai ciwo da ƙuna Maanal ta saki batare data iya cewa komai ba. Sai wasa take da yatsunta kawai. Oum ta juya ga AA tana faɗin, “Auta kaji fa ashe Asiya bata manta dani ba. Sunana aka sakama ɗiyar Shahidah”. Karo na farko ya saki wani irin murmushi mai ban mamaki, irin mai maƙalewa a gefen bakin nan da sai kana kallon mutum kake sanin yayi, sai kuma ya yunƙura a hankali ya riƙo hannun Barrah, matsota yay jikinsa kawai ya rungumeta. A mamakin kowa dake falon sai ji sukai ya furta, “I love you so much tunda kikaci sunan Oum na, ALLAH ya albarkaci rayuwarki”. “Uncle ni banda ni?”. Haneeff ya faɗa babu zato. Dariya Oum da RK da masu aikin nan sukayi, yayinda Maanal tai ɗan murmushi da girgiza kanta. Shi kam AA idanunsa ya buɗe sosai a kan yaron, sai kuma shima ya sakar masa murmushin da miƙa masa hannu ya riƙosa, cikin maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Kaima ALLAH yay maka albarka”. Cike da farin ciki Haneeff ya amsa masa. Shima RK da Oum duk suka amsa............✍️

🤔Nayi tambaya ko nayi shiru wai???.. kai Bara dai na haɗiye kayana🥱. Idan kuma akwai mai irin tunani na mu haɗu a comment 🏃🏃🏃🏃🏃

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖3️⃣5️⃣

Readers Also Read