Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 2
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 2: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 2. Shigowarta sashen nasu da abinda ta…
4,469 words
Shigowarta sashen nasu da abinda ta taras ya wanke mata gaba ɗaya damuwarta. Dan kuwa taci karo da ƴan uwanta biyu da yaransu duka sunzo gidan domin dawowar tata kawai. Ai tuni ta watsar da damuwar RK data Huznah suka rungume juna. Sosai suke matuƙar ƙaunar junansu ta yanda idan ka gansu kai kanka sai sun matuƙar burgeka. “Amma Didi kikace min ke bazaki wani zo tarbata ba”. Dariya wadda ta kira da Didin tayi tana mai dungure mata kai da faɗin, “Naƙi zuwa babarki ta ƙulaceni Auta”. A tare suka kwashe da dariya, dai-dai nan wata dattijuwar mata cikin kwalliya ta fito daga wani lungu mai nuni da hanyar kitchen ne dan hannunta riƙe yake da wani ɗan bowl. Tuni Maanal ta saki yayunta ta nufi matar da sauri ta wani daka tsalle ta rungumeta. Dariya yayunta da yaransu suka sanya. Yayinda matar ke faɗin, “Oh ya ALLAHU jama'a sai yaushe Maanal zata girma ne? Yanzu idan kika karyani fa?”. Cike da shagwaɓa, tare da sake shigewa jikin matar ta ce, “Ni dai bazan taɓa girma ba Ammie. Nayi kewarki fiye da kowa da komai. I really miss you Ammie na”. Ƙaramar dariya Ammien ta saki mai ƙayatarwa, tare da sake rungume ɗiyar tata a jikinta tana mai sumbatar kanta da faɗin, “Nima nayi kewarki sosai Maanal. Congratulations my Auta, yau dai finally an gama boko.” “Kai Ammie dama ana gama boko?”. Ta faɗa cikin dariya mai ƙayatarwa da mutane da yawa basu san tana yi ba. Itama Ammien dai dariyar ta sake yi, sai kuma ta ɗagota tana mai ƙare mata kallo da ƙyau. “Auta duk kin sake rame min, kina lafiya kuwa?”. Kanta ta kwantar a jikin hannun Ammien data riƙe, sai kuma ta amsa da, “Lafiya Lau nake Ammie. Kewarki ce kawai ta hanani sukuni”. “Oh wai kin damu mutane da kewar Ammie kawai. Kina nufin mu bakiyi kewarmu ba ne Auta?”. “To Sarkin kishi, ALLAH Ammie ban taɓa ganin mai kishinki sama da Didi Amal ba. Kijifa dan ALLAH, nayi kewarki itama dole sai nayi kewarta?”. Jefota da filo Amal tayi, da sauri ta kauce tana murmushi. Yayinda Didi Shahidah da Ammie da yaransu ke musu dariya..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣4️⃣
______________
Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________
.......Bayan an natsa da murnar dawowar tata da gaishe-gaishe Ammie tace ta wuce ta gaida mutanen gidan. Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, sai kuma ta shiga roƙon Ammien akan dan ALLAH ta barta taje tai wanka ta canja kayanta tukunna. Ammie zata ƙi su Amal suka tayata roƙonta. Dole ta barta taje ta fara wankan sannan, yayinda su kuma suka cigaba da aikin shirya abinci dan dama girki suke sanda ta shigo. Ɗakin da yake mallakinta ta shiga, an gyarashi tsaf ga ƙamshi mai daɗi na turaren da take matuƙar so na tashi a cikinsa. Sosai ɗakin ya haɗu, sai dai haɗuwar tasa baisa ta taɓa jin daɗin zaman gidan ba. Kawai dai tana zaune ne saboda mahaifiyarta na'a cikin gidan ne. Duk kuma inda Ammie take rayuwa koda a dokar daji ne itama zata zauna ta rayu saboda a duniya bata haɗa komai da soyayyar da takema mahaifiyarta ba. Ita ɗin dabance a zuciyarta. Idan tace daban tana nufin daban a cikin dukan daban. (ALLAH ka gafartama iyayenmu, wanda suke raye ka bamu ikon ƙyautata musu😭🙏). Jacket ɗinta ta fara cirewa, tare da ƙurama rigar ido tana mai sakin murmushi. Finally yau ta gama sarvese, duk da Ammie tace boko ta ƙare, itafa a gareta yanzu ne aka saka ɗanba, sai dai Ammie tayi haƙuri amma sai taga ƙarshen biro in har ana ganinsa. Sanin yaran can zasu iya shigowa su fara addabarta yasa taƙarasa zame kayan nata da sauri-sauri ta ciri towol daga Waldrop ɗinta fari tas ta ɗaura. Bayin ta nufa dan tasan duk abinda zata iya buƙata Ammie ta saka mata shi kasancewar ta jima bata gida. Dan watanni biyar kenan bata zo ko weekend ba. Tunma data wuce sarvese sau ɗaya tazo gida, ɓacin ran data gumtsa a zuwan yasa tai alƙawarin ƙin sake zuwa har sai ta kammala. Alhamdullah kuma gashi sai da ta kammala ɗin. Wanka tayi na gaske. Dan sai da ta tabbatar ko'ina na jikinta ya mata yanda take so sannan ta fito tana raɓar ruwa da ƙamshin shower gel ɗin ta mai shegen daɗi daya gauraya da na sabulunta da turaren wanka. Maanal tasan sirrin gyaran jiki da kula da jikin ma. Dan yarinya ce ƴar ƙwalisa akwai son gayu. Damma ba Maanal ɗin da bace data taso da shegen son kwalliya kamar ƴar aljanun. Tana tsaka da shafa mai Amal ta shigo. Cike da tsokana ta ƙaraso gareta tana faɗin, “Uhm kaga ƴar ƙwalisar gidanmu Autar Ammie. Irin wannan ƙamshi haka kamar zaki tashi gari”. Murmushi mai sanyi Maanal ta saki da ɗan girgiza kanta tana ajiye man hannunta data matsa. Wanda ta matsa ɗin ta fara shafawa a fuska tana faɗin, “ALLAH Didi sai kisa a rataye mutum a tsakiyar kasuwa. Daddyn su Safnah na haƙuri dake gaskiya. Yanzu mine abin wani ƙwalisa anan daga shafa mai dai sai wanka. Ni ko fauda bazan shafaba ma”. “A'a wlhy dole ki shafa. Zakije gaida waɗan can ƴan tsirkun ai sai kin cakare. Dama ga ɗan mutuminki yazo garin, dan muna shigowa da shi na fara cin karo a harabar gidan nan ɗazun”. Cak Manaal ta dakata daga shafa man da take zuciyarta na wani irin motsawa da ƙarfi, a take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Sai kuma ta fara haɗiyar numfashi da sauri-sauri. Fahimtar hakan ya saka Amal wayancewa da faɗin, “Amma ban sani ba ko shirin komawa yake a lokacin dan da akwati na gansa ma fa. Fitinanniyar uwarsa a tare da shi ko rakkiya tai masa oho musu”. A hankali Manaal ta saki numfashin data ɗan riƙe a maƙoshinta. Sai kuma ta cigaba da shafa manta da kauda zancen ta hanyar faɗin, “Ina dai fatan kin soyo min fara ta Didi?”. “Harma da su Alewar madara Munaya ta matsa nai miki”. “Oh my sweet daughter ɗina, Shiyasa nake son yarinyar nan. She is my bestie”. “Uhm kudai kuka sani. Ni tashi ki shirya ke ake jira aci abinci. Kin san yau akwai hira duk an haɗu”. Murmushi tayi cike da jin daɗi, dan tafi kowa son irin wannan haɗuwar tasu. Takanji kamar su dawwama a haka tare gaba ɗaya kamar yanda suke da can. A gurguje ta shirya cikin doguwar rigar Abaya milk color da ɗan kwalliyar coffee kaɗan a jiki. Ta saka turarrukanta masu sauƙin ƙarfi. Suna ƙoƙarin fitowa Shahidah ta shigo ɗakin, dariya suka sanya mata dan sun tuna baya. In dai kaga Shahidah tai irin wannan shigowar fuska a ƙwaɓe to abinci aka ajiye zasu fara ci sukuma suka maƙale a ɗaki hira, ita kuma sam bata da jimirin yunwa musamman idan ta dawo daga makaranta ta kwaso rana. Sai ta shigo cikin haushi tana faɗin (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”). Baki suka haɗa wajen furta (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”). Ai ba shiri Shahidah ta sanya dariya da musu daƙƙuwa. Daga haka suka rankaya suka fito inda Ammie ke zaune a tsakkiyar falon da ƴan jikokinta zagaye da ita. Dan a anan aka shirya abincin yanda za'aji daɗin ci fiye da saman table. Manaal na zama yaran duk suka matso kusa da ita kowa na faɗin tare da ita shi dai zai ci. Ganin abin zai zama rigima ta miƙe tana faɗin, “Kunga ku jira ku gani”. Kitchen ta shiga sai gata da babban faranti ta ɗakko, ganin haka Ammie tace, “To ai kawai zuba gaba ɗaya anan Auta sai muci duka baki ɗaya”..
Cike da farin ciki suka ci suka ƙoshi, damma Ammie ta hana surutu. Bayan sun kammala babbar yarinyar Didi Shahidah mai suna Barru ta gyara wajen tsaf sauran yaran na tayata. Maanal ya gyara zama da tunanin Ammie ta manta da batun zuwa gaida mutanen gida sai Ammien ta harareta da faɗin, “Oya tashi kije gaida mutane”. Fuska Maanal ta ƙwaɓe sai dai babu yanda zatai dole ta miƙe. Hannun ƴar gaban goshinta Munaya ta kama suka wuce tare. ALLAH badan Ammie ba babu inda zataje. Da sashen Hajiya Yaya ta fara. Hajiya Yaya itace uwargida a wannan gida na Alhaji Usman Chalawa. Tanada yara bakwai tare dashi. Babban shine kaɗai namiji sauran duk mata ne. Macece mai son mulki da ƙyamar talaka. Dan mahaifinta kamar ma shine silar arziƙin mijin nasu shiyyasa take jin komai na gidan ta isa da shi kuma dole a bita har shi kansa mai gidan ma. Sai dai kasancewar shi ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa yasa wani abun bata da power a kansa, dan in ma ta nuna ƙarfa-ƙarfar yakan saurin taka mata birki. Kasancewar ta mace ta farko a gidan part ɗinta yafi na kowa girma da tsaruwa, sai dai hakan ba yana nufin na sauran matan ma bai haɗu bane. A'a a komai dai natan yana sama dana kowa kasancewar ita ta fara tarewa a cikinsa. Sai da Maanal ta dana door bell har sau biyu kafin ta tura ƙofar falon da sallama duk da tasan ba sallai a jita ba kasancewarsa ƙaton gaske ne. Ilai kuwa babu wanda ya amsa mata sallamar duk da kuwa kusan duk yaran na falon harma da ita kanta Hajiya Yayan. Sai dai kasancewar ta danna door bell kafin shigowar yasa duk suka maido hankalinsu ga ƙofar dan son ganin mai shigowar. Suna yin tozali da Maanal wasu a cikinsu suka kauda kawunansu cikin jan tsaki. Yayinda Hajiya yaya ta zubama Manaal ɗin idanu tamkar zata cinyeta da su. Sai Autar Hajiya Yayan da zata iya zama sa'ar Manaal ɗin mai suna Amrah ce tai murmushi tare da miƙewa cike da farin ciki tana faɗin, “Oyoyo mutanen Jos sauka haka babu notis”. Murmushi Manaal ɗin tai mata, yayinda ita kuma ta rungumeta. A dai-dai nan idon Manaal ɗin ya kai ga ƙaton dining table dake gefensu kaɗan. Sosai zuciyarta ta motsa sakamakon saukar ƙwayoyin idanunta akan wanda ke zaune a wajen shima ya zubo ma inda take idanunsa masu kaifi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣5️⃣
______________
Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________
......Da sauri ta kauda idanun nata tamkar bata ganshi ba. Sai ma cikin wayancewa ta ɗago Amrah tana faɗin, “Wai haka kika ƙara lukucewa matar nan?”. Dariya Amarhn tayi da kai mata mintsini a gefen hannunta itama tana faɗin, “Ke dai zauna nan kamar za'a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina”. Murmushi kawai Manaal ɗin tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan hannun Munaya tana mata wasa. Da wannan damar Maanal ta ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa ta kai duƙe duk da kallon wulaƙancin da Hajiya Yaya ke mata da sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa mata sau ɗaya ta ɗauke kanta. Hakan ya ƙona ran Maanal matuƙa amma sai ta daure, fuskarta da ɗan murmushi ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa mata sai ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a dining ya miƙe zai fita a falon yana kai waya kunnensa alamar zaiyi magana. “Ina kuma zakaje Yazeed?”. Uwar ta ƙatse masa hanzari da ƴar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu yay mata nuni da waya zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa. “Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma”. Ɗaya daga cikin ƴammatan ta faɗa fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa Maanal taja hannun Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma wadda tai maganar ta miƙe zumbur tana faɗin, “Ina zuwa bari na muku leƙen asiri. Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a falon nan babu wata waya da zai amsa”. “ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin abincin ma sai wani binta da kallo yake. Kinga muje”. A hasale Hajiya Yaya ta furta, “Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na rabashi da yarinyar nan na kuma haramta masa alaƙa da koda inuwarta ma balle ita. Amma kuje ku ganar min yana ina”. Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar tasu kuma Manaal ke shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta biyu a gidan. Itama dai ɗin ba kanwar lasa bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba. Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri baka isa fahimtar ita ɗin wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran da jama'a da son nuna ita ɗin ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu illa suke farga da ita ɗin wacece. Macijin sari ka noƙe ce ita ta bugawa a jarida. Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da namiji ko ɗaya. Huznah da Maanal ta fara haɗuwa sanda ta dawo itace ƴarta ta farko. Itama ɗin dai family nata akwai kuɗi, dan Yayanta daya riƙeta hamshaƙin mai arziƙi ne. Kuma babban aminin Alhaji Usman Chalawa ne, suna huɗɗar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin dukiyarsu a cuɗe take da juna. Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta ɗaga mata hanci ta ɓangaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa najinsa a wani shege. Komawa su Nanah sukai nasu sashen cikin taɓe bakuna. Dan Manaal na ƙoƙarin shiga sashen Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa. Tun ma kafin su ƙaraso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu tambaya cikin huci dan macece mai ƙiba sosai. Irin ƙibar nan bata wasa ba. Dan ko daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a wajen nan. Zaune duk suka zube cikin takaicin rashin samo abinda za'aci mutuncin Maanal da uwarta yau a gidan. Nanah tace, “Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana”. Cikin ƙwafa da takaicin itama bata samu yanda take so ɗin ba ta ce, “Ya taimaki kansa. Dan wlhy da yau har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani mutanen nan a rayuwata”. “Ai bake kaɗai ba Mamma”. Cewar ƴarta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya mutu kusan shekara uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana ɗaya akai bikinsu da su Shahidah yayun Maanal. Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan ido da jiran ƴaƴan masu hannu da manda irinsu ya hanasu auruwa. Burin kowannensu da ma uwarsu shine suyi auren ƙwarya tabi ƙwarya.. Buɗe shafin zagin su Manaal sukai a falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ɓata fuska dan ita bata son hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata. Babu ruwanta da duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da ƴaƴanta. Ko su duk abinsu bazasu taɓa cewa ga randa Ammien taima wani abu mara daɗi ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?...
A ɓangaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai sashen Hajiya Basariyya da suke kira da Momyn Suhana ya matuƙar haɗuwa. Girmansa kuma ɗaya dana Ammie. Ita dai bata falon sai su Huznah da ƙannenta dake cin dafaffen gyaɗa suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan carpet ɗin tsakkiya ko'a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya batare data musu magana ba sai ga Hajiya Basariyya ɗin ta fito daga kitchen riƙe da kofi tana waya fuskarta da murmushi. “A'a ƴan Jos an dawo kenan?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni ƴarta Huznah bata kawo mata labarin dawowar Maanal ɗin ba tun ɗazun. Juyowa Maanal ɗin tayi fuskarta kadaran kadahan ta ɗan kalla Hajiya Basariyya ɗin da nata fuskan ke ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa, sai dai acan ƙasan zuciyarta wani irin maƙoƙon tsanar Maanal ɗin ne ke mata kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara'a tana nuna ma Maanal ɗin kujera da faɗin, “Haba sai kace wata baƙuwa zauna mana Maanal ga ƴan uwanki nan na bikin cin gyaɗa ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya kammala?”. Kai kawai Maanal ɗin ta jinjina mata kanta a ƙasa, sai dai yanzu da ɗan gajeren murmushi a fuskarta. Ganin bata zauna ɗin ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun Munaya ta ce, “A'a Momy mun gode dama munzo gaisheki ne kawai”. “Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin miƙe gaskiya azo mini hira dai. Suma su Shahidah ki faɗa musu ina godiya sun barni da jira. Tun ɗazun har abinci nasa akayi dasu ga gyaɗa da aka dafa amma shiru kake ji”. “Zan faɗa musu in sha ALLAH Momy”. Maanal ta faɗa cikin muryarta mai zurfi da nutsuwa. Daga haka ta kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama ficewar harda turo ƙofar Huznah taja tsoki da faɗin, “Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu magana mai daɗi. Shegu sunzo sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama faɗin yayansa ne suma na halak. Ko ina suka zama ƴaƴan nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon ƴaƴan nasa ƙilama da cikinsu tazo.” “Hummm”. Kawai Hajiya Basariyya ta faɗa tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah ɗin ba. Hakan ya sake bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma sunfi tsanarta fiye da sauran ƴaƴan Ammien. Duk da kuwa sunƙi jinin Hameed ma da Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba ɗaya dasu. Balle da Daddyn ke tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu ƙasar Amurika yin hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu ne dan hutawa na sati har biyu...
Rai ɓace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya faru ba babu wanda ya tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga nan suka gaisa da shi ya bama Hameed da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. Ƙanensu kenan guda biyu. Yarane matasa da zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar su Maanal ɗin. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa sosai kasancewarsa farin mutum tas.. Suna cikin hira da ƙannen nasu ne babu zato akai knocking ƙofar falon. Kafin wani yay magana a cikinsu mai knocking ɗin har ya shigo. A take Maanal ta shanye fara'ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko nace faɗa irin na sako duk da kuwa ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta rufe gashinta da ƙyau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da ɗan murmushi hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama ƙarema Maanal kallo a kai-akaice. Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana ɗan murmushi ya ƙaraso. Cike da girmamawar da yake bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama, kafin ta ɗora da faɗin, “Baka wuce Abujan ba kenan?”. “Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe zai dawo. Nima kawai sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman jiransa ina kuma da abinda zan ɗanyi anan ɗin”. “To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan al'amuranku”. “Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai”. Ya faɗa cike da jin daɗi yana maida hankalinsa kan Maanal dake ƙoƙarin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, “Ke ƴar hidimar ƙasa yaushe kika dawo?”........✍️
Hummm yanzu fa aka fara shimfiɗar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga kuma RK. Ga Maanal da bama musan alƙiblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan ne? Ya dai kamata a haska mana mu gani ko zamu tayasu lalube🏃🏃🏃🏃🏃.
Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa biyar da zasu zo muku da sabon salo na musamman in sha ALLAHU. Kowanne da salonsa da kuma takunsa. Mi kuke jira, ai sai kawai kuzo ayi tafiyar nan daku karku bari sai wasu sun baku labari.😘😘😘👌
A fa dun inda ZAFAFAN suke ZAFAFAN ne🫣😘😘👍🏻
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣6️⃣
ALBISHIRINKU 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
Idan kinada burin samun babban jari🤝 ko siyan wata babbar kadara irinsu gida mota ko gold fili ko Gona ko canja kayan daki ko kinada yanmata kinaso kisaimusu kayan aure ko canja rayuwarki daga tunanin yauda kullum xuwa lissafin dollars 💰daga Kwance 💃 Uhmmm garzayo kiyi rijista da 52U kiyi aiki kisha mamaki acikin shekarar nan rayuwarki xata canja ta dalilin yin rijista da $21 kacal😱
Yar uwa kisani cewa a kullum muna fuskantar tashin hankali idan akace mana darajar dala tatashi😫 Kullum naira da muke kashewa darajarta Kara faduwa takeyi😩
Tsadar rayuwa kowa yanxu fama yake da wnn tashin kayan😰 Mezai Hana kuxo mu runtuma muyi harkar dollars din kawai sbd yazamana ko ina muna nan 🤗
52U harkar dollars ce Mai sauki ga samu 52U alkhairi ce rijista kawai xakayi da $21/35k bayan haka baasaka kudi a 52U kuma 52U babu level level kawai rijista ne akeyi da kudi ba platforms bane ❌ Networking ne💯 Yanxu mu yan 52U idan akace mana dala tatashi murna mukeyi ba bakincikiba sbd inkanada dala kacanjashi naira ninkuwa yakeyi💃