Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 27

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 27

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 27: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 27. .......Matuƙar mamaki Babban Yaya…

4,372 words

.......Matuƙar mamaki Babban Yaya ya shiga da jin komai daga bakin Oum da RK. Sai satar kallon Shahidah yake da jinjina mamakinsa akan canjawar Maanal. Ta ƙara tsaho duk rashin jin nan da rawar kai babu yanzun. Hakan ba abun mamaki bane ba, musamman idan aka tara yanda abubuwa suka kasance zama a iya ganin fiye da hakan daga Maanal. Nan fa ya tasa Maanal da tambayoyi har ma da Shahidah duk da shi ɗin ba gwanin yawan magana bane ba. Maanal ce mai amsa masan, dan itama Shahidah tana amsa ɗai-ɗai ne. Itafa Family ɗin nan idan ta cire Oum a ciki da Fawzan da Abah da Mamy bata jin sauran a ranta yanzu. Sai ma wani kalar zafinsu da take ji, amma darajar Oum yasa taketa ƙoƙarin dannewa dan Oum ta cancanta. Ana cikin hakan sai ga Fawzan shima ya iso, bayansa matarsa ce Nibras, sai Saheeba matar babban Yaya hannunta riƙe da ƴar budurwar yarinya mai tsananin kama da su Babban yayan. Sai budurwar yarinya ƙyaƙyƙyawa a ƙarshe biye da su hannunta ɗauke da irin box ɗin nan da ake saka kayan abinci. Ambatar sunan Lilly da Shahidah da Fawzan yayi ya saka Saheeba kallon sashen da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna da Shahidahn. A take fara'ar fuskar Saheeba ta ɓace ɓat. Itako Shahidah ta janye nata cike da basarwa tana bama Fawzan amsar maganarsa. Ita dai Nibras bata sansu ba a zahiri. Amma sunayen da aka ambacesu da shi ya sata tsatstsaresu da idanunta, dan ta ɗan san labarin dangantakar tasu da familyn Darma a wajen mahaifiyarta. Sai dai kuma bata da tabbacin waɗan can ɗin ne ko wasu daban. Ita ko budurwar data shigo a ƙarshe gaba ɗaya hankalinta naga AA ne. Dan tuni ma ta kai gaban gadon babu ko kunya ta zauna a kusa da shi. Sai dai hararar daya jefa mata ta sata miƙewa tsaye zambar tana faɗin, “Sorry Yaya”. Komai baice mata ba, ita kuma bata nuna damuwa ba ta ɗan rissina tana gaisheshi da tambayarsa jikin nasa. Sai kuma ta jawo kujera dake can jikin ɗayan gadon dake a ɗakin dan gado biyu ne Naufal na barci a wajen ta zauna kusa da shi sosai. Dai-dai nan Shahidah ta miƙe tana faɗin, “ALLAH ya ƙara lafiya bara mu wuce Maanal ta samu ta huta.” Wani irin ɗagowa budurwar mai suna Nuratu tayi jin sunan Maanal a karo na farko. Sai a yanzu ta kalla Oum kasancewar Maanal ɗin na'a jikin Oum kamar ƴar mage. Tabbas bata san Maanal ba a zahiri itama a wancan lokacin na ƙuruciya dan ita ta rayune ba'a gidansu ba, yayar babansu ce ta riƙeta suna zaune a Lagos. Bayan rasuwar mijinta ne suka dawo Abuja, amma tasan komai na labari tsakanin yarinya mai suna Maanal da Yaya AA ɗinta. Burin ranta, da take fatan ya zama miji a gareta tun a randa ta fara tozali da shi a Lagos. Ƙoƙarin tuna inda tasan fuskar Maanal take yi, dan haka ta kafeta da idanu. Ƙirjinta ne yay masifar bugawa lokacin da suka haɗa ido da Maanal dake miƙewa Oum riƙe da ita. Sarai Maanal ta ganeta ita, hakan yasa ta janye idanunta cike da basarwa. Itako Nurry ta kasa janyewa dan ta gane Maanal itama, itace yarinyar da suka haɗu a wajen saloon ranar Sunday ɗin data gabata. Jitai jikinta kawai ya fara rawa, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri saboda tsoron abinda take hasashe, cikin rawar murya da suɓutar baki ta furta, “Wai itace Manaal ɗin da nake jin labari a gidan su Mamy na Kano Aunty Saheeba?”. Ba Saheeba data ambata ba, hatta su Babban yaya sai da suka dubeta, shi kansa AA wani kalar mugun kallo ya zuba mata ita da yayar tata Saheeba duk da matar yayansa ce. Sai kawai jikin Saheeba da Nurry ya kama tsuma. Cikin daburcewa Saheeba da kallon rashin mutuncin da Babban yaya ke jifanta da shi gana AA a gefe ya gama rikitata ta ce, “Wlhy ni ba wani bad abu na sanar mata akanta ba. ALLAH ma ne shaida bani na gaya matan ba. Nuratu ko'a bakina kika ji?”. Ta juya tana kallon Nuratu da zuciyarta ke mazari. Dan ta fahimci itama katoɓarar data nema yi. Sai dai kuma wani irin jin tsanar Maanal ke sake haɗa wutar guguwa a can ƙasan ranta. Kai ta girgiza ma Yayar tan, sai kuma ta ce, “No nima fa ba ina nufin wani bad abu bane ba wlhy ko aka sanar min a kanta. Kawai na faɗa ne ta yanda zan tabbatar da ita ɗin ce bawai dan wani abu ba.” Fawzan ne ya girgiza kansa kawai da katse yanayin ta hanyar faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to. Amma wannan maganar ma baida wani amfani. Ƙanwata muje na saukeku gida ko”. Ya ƙare maganar idonsa akan Shahidah. (Da ada ne catake ita ba ƙanwarsa bace). Suyita musu da jayayya, dan da gaske Fawzan ya girma Shahidah ɗin da kusan shekara uku, kusan ma za'ace AA ne sa'anta. Amma ta girmesa itama da wasu watanni. Alaƙar Shahidahn da babban Yaya yasa suke ƴar jayayyar da Fawzan ɗin sarkin barkwanci da tsokana. Murmushi Shahidah tai masa da faɗin, “A'a mun hutasheka Yaya Fawzan. Da mota ma nazo shiyyasa nace shima Rafeeq ya huta abinsa.” Sai a lokacin RK da komai ke masa kaikawo yay magana. Maanal da tuni tai gaba ya kalla. Dan ita ko kallon Nurry batai ba balle wani dake ɗakin akan maganganun. Hasalima bata nuna tasan anayi ba, tunda tabar jikin Oum tai hanyar ƙofa abinta. Kai kawai ta jinjinama RK da sakar masa ɗan murmushin daya sake tokare maƙoshin AA tai ficewarta. Itama Shahidah sai kawai ta bita tana wani jin sake tsanar wannan family. Biyosu RK yay da sauri, hakama Oum. Dakatar da RK Oum tayi, kafin ta ƙarasa inda Shahidah ke ƙoƙarin buɗe motarta ta riƙo hannunta. Da sauri Shahidah ta juyo, sai kuma ganin Oum ya sakata sakin murmushi. “Lah Oum ko munyi mantuwa ne?”. Fuskar Oum cike da damuwa ta ce, “Ba mantuwa kukai ba Shahidah, haƙuri zan baku. Dan ALLAH kada abinda yarinyar can Nuratu tayi ya dameku. Nasan koda wani abu taji ba wanda kuke tunani bane ba. Dan dukkan abinda ya faru sirrine da iya mu da ku muka sanshi. Ni......” Da sauri Shahidah ta shiga girgiza mata kai, “No Oum dan ALLAH kar kice komai. Mu tsakaninmu dake sai addu'a da fatan alkairi. Kamar yanda tun farko muke miki kallon uwa yayar Ammie haka har gobe wannan matsayin naki bai goge ba a zukatanmu. Bamu taɓa riƙeki a ranmu ba. Kosu wlhy albarkacinki dana Abah da Mamy suke ci har muke jin komai ya wuce kamar bai faru ba. Abinda ya faru ƙaddararmu ce mu duka da ku, babu kuma wanda ya isa ya iya canjata ba gashi komai ya wuce kamar ma bai faru ba” “Na sani Shahidah, amma idan na tuna nakan ji na tsani dukkan kaina wlhy. Kuma ina sha ALLAHU addu'ar da nake tsahon shekaru bazata taɓa tafiya a banza ba. Da izinin UBANGIJI sai Ajwaad ya gyara ɓarnar da yay da kansa. Gaskiya kuma saita bayyana. Abinda duk ke a ɓoye zai fito fili”. Kuka ya sarƙe Oum... Rungumota Shahidah tayi, yayinda Maanal tai saurin shigewa mota hawaye na gudu akan fuskarta. Jikinta sai rawa yake yi. La'ilaha'illa antas-subahanaka inni kuntu minazzalumin ta dinga ambata. Tsohon lokaci har bata san mi Shahidah da Oum suka cigaba da tattaunawa ba Shahidah ta shigo mota. Komai basu cema juna ba sai murmushin da Maanal ta ɗan sakar ma Oum dake mata magana ta ɗaga mata hannu.... Komai dake faruwa a idanun RK ne dake tsaye daga can nesa da su. Shifa gaba ɗaya an ƙarasa kulle masa kai. Yau ya fahimci lallai akwai wani babban al'amari daya shiga tsakanin wannan zumuncin. Sai dai miyyasa kowa ke son ɓoyewa ne? Anya bai kamata ya sani ba? To idan ya sani amfanin mi sanin zai masa. Kawai yana son Maanal hakan ya wadatar da shi. Idan lokacin ya san komai a tarayyarta da Darma Family yayi yasan zata sanar masa duk da ƴan uwansa ne jininsa na kusa kuwa. Koda Oum ta iso inda yake bai tambayeta komai ba. Sai ma murmushi da yay mata yana mai nuna mata hanya alamar suje. Zuba masa idanu Oum tayi sosai, sai kuma a hankali ta furta, “Rafeeq! Da gaske kana son Maanal?”. Idanunsa sosai ya waro a kanta, sai kuma ya narke fuska cike da nuna damuwa ya ce, “Haba Aunty, wane irin tambaya ce wannan mai tarwatsa zuciya. Kema shaida ce ban taɓa kawo wata yarinya gareku da sunan soyayya ba. Miyyasa kuke ganin komai na kamar ba serious ba?”. “Sam ba haka bane ba Rafeeq. Nasan kai mutum mai son wasa ne. Amma ban taɓa kallon al'amuranka a matakin rashin serious ba. Itama tambayar na maka itane kawai.” Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “In sha ALLAHU Aunty zan tabbatar muku da babu wasa akan batuna da Maanal. Dan yanzu haka ma ta bani damar zuwa Kaduna na gana da Daddynta a next week”. Cak Ammie ta tsaya gabanta na faɗuwa. Dan lips ɗinta har ɗan rawa yaso farawa amma tai ƙoƙarin dai-daita kanta da ƙyar. Sai kuma ta sakar masa murmushi kawai da faɗin, “Masha ALLAH, idan mukaje gida zamuyi magana”....

Koda suka dawo ɗakin sun sami babban yaya nata zuba faɗa ma Nuratu. Ta inda yake shiga tata nan yake fita ba. Sai shigowar Oum datai masa magana ya tsagaita. Amma duk da haka a fusace yace su wuce su koma gida ba'a buƙatar sake ganinsu a asibitin ma. Haka Saheeba da Nibras da ita Nuratun suka fita ransu a ɓace suma. Sai dai babu damar magana dan tabbas babban yaya da AA basu san wargi ba. Koshi Fawzan dake da yawan barkwanci bawai ya saki kansa bane raini ya shiga tsakaninsa da Matarsa ma balle ita Nuratun. Hatta da ita Saheeba dake matsayin matar babban yayansu da suke matuƙar girmamawa babu raini a tsakaninsu dan matsayin ƙanwa take a wajensa.. Anan suka bar yaran, dan tuni Anum maƙalƙale take da jikin Fawzan dama tun fara faɗan Daddynta. Shi ko Naufal har yanzu yana barci ne.......

____________★

Koda suka iso gida daga Shahidah har Maanal basu sake tada maganar nan ba. Shahidah tayi hakan ne kawai dan gudun tadama Maanal hankali, sai da ta shiga ɗakinta tai kiran Amaal suka tattauna. Sun jima akan wayar suna magana har Maanal ta shigo sannan Shahidah ta yanke kiran dan bata son tasan da Amaal ɗin take waya. Itama Maanal bata damu da sanin dawa Shahidahn ke wayar ba. Sai ma zama da tai a bakin gadon nata. “Har kinyi wankan?”. Kai Maanal ta jinjina mata cike da ƙarfin hali. Sai kuma tai ɗan murmushin san kore damuwar nan ta ƙarfin tsiya sannan ta furta, “Naga mutiniyarki na haɗa kaya fa ko Kaduna zataje ne itama?”. Da mamaki Shahidah ta ce, “Wai Huznah?”. Kai Maanal ta jinjina mata. Ita kuma tace, “Humm to ita dai ta sani, ai garama ta koma ɗin dan nikam wannan gantalin nata na tayar min da hankali musamman a kwanakin nan data san Yazeed baya Abujan. Narasa mi yarinyar nan take yi a garin nan?”. Murmushi kawai Maanal tayi amma taƙi gayama Shahidah gaskiyar abinda ta sani akan Huznah ɗin. Badan bata son ta sani ba sai dan bata son sako al'amarin mutumin (AA🤣) da Huznahr ke bibiya sam a al'amuranta. Sai ma kawai ta basar da zancen ta hanyar faɗin, “Didi nima ina son zuwa Kaduna a weekend ɗin nan”. “Amma Auta kinfa san satin ne bikin Yazeed”. “To minene a ciki Didi. Dan ana bikin yaya Yazeed kuma sai naƙi zuwa Kaduna?.” “Baƙya gudun abinda zai iya zuwa ya dawo”. “In sha ALLAHU babu komai Didi. Kawai ina kewar Ammie ne sosai wlhy. Sannan ina son Rafeeq yaje su gana da Daddy dan na bashi damar hakan”. Da sauri Shahidah ta dubeta. Harshenta har harɗewa yake wajen furta, “Maanal akan mi kike son Rafeeq ya gana da Daddy?”. Ɗan jimm Maanal ɗin tayi tana kokawar saita kanta da danne duk wani yinƙurin raunin da zuciyata ke son bayyanawa akan fuskarta, sai kuma ta saki murmushin karfin hali. Kanta tsaye ta ce, “Na bashi damar neman aurena”. “What!! Neman aurenki fa kika ce Manaal? Rafeeq ɗin? Shifa ɗin ɗaya daga cikin zuri'ar su Ajwaad ne??”. “Tabbas hakane Didi. Shiyyasa ma na bashi wannan damar. Sannan kin manta ne, alaƙar dake tsakanin Oum da Rafeeq tafi ƙarfi fiye da wadda ke tsakani da su. Dan haka na yarda na amince zan auri Rafeeq in sha ALLAHU”. Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin ko waiwayen Shahidah data saki baki da hanci da ido tana kallonta batai ba.........✍️

_🥱🥱Nifa a wata gaɓar rasa abincewa nake 😆._

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣2️⃣

______________

.........Wani irin kalar zubewa Shahidah tayi a saman gadonta kamar wadda aka kwashema dukkan ƙarfi da zuciya a lokaci ɗaya. Kalaman Maanal na mata wani irin kai-kawo dai-dai da bugawar zuciyarta. Sai kuma kamar wadda aka zabura ta lalubo wayarta. Kira ta sake dannama Amaal. Aiko bugu ɗaya ta ɗaga dan dama tun ɗazun nemanta take itama amma ta gagara samunta.... “What! Rafeeq fa? Maanal kuwa nada hankali? Kota manta alaƙar dake tsakanin Rafeeq da Ajwaad ne?”. “Nima na faɗa mata hakan wlhy Amaal. Amma ta nuna min ai alƙar dake tsakanin Oum da Rafeeq tafi ƙarfi akan wadda ke tsakanin Rafeeq da su Ajwaad. Ni wlhy nama rasa wane tunani zanyi. Dan tabbas akwai ƙura babba. Anzo gaɓar fa da dole Ammie tasan halin da ake ciki kin san dai Auta da taurin kai da kafiyar tsiya”. “Amma kin san zamusha faɗa akan ɓoye matan da mukai. Sannan na faɗa miki jiya naje gidan na samu Daddy na shirin zuwa Kebbi domin ganawa da waɗan can mutanen na Giro. Na tabbatar kuma yau ɗin nan sun tafi ma shiyyasa nake ta nemanki tun safe. Yanzu haka can gidan zanje dan Hameed ya kirani ya sanar min Ammie na ciwon kai yau gaba ɗaya a kwance ta yini kuma yaga Daddy ya fita daga wajenta da safe kamar a fusace. Kinga ko ya tabbata akan zuwa Giro ɗin ne maybe ta nuna bata so ko”. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Amaal komai zai iya faruwa kam. Wannan wace irin gaɓa ce mai rikitarwa da tada hankali. Aiko muma bamuga ta zama ba dole na ɗauka hutu Kona kwana huɗu ne muzo Kadunan gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga nan kawai har biki”. “To gaskiya hakan ne ya kamata kawai ku taho. Bara naje naga halin da Ammien ke ciki”. Jiki a sanyaye Shahidah ta amsa ta da to kawai suka yanke kiran.

Bata leƙa Maanal ba sai bayan sallar magriba, ta sameta tana karatun Alkur'ani. Zama tai dan haka Maanal tana kaiwa inda ya kamata ta tsaya ta dakata. Duban Shahidah tayi da da faɗin, “Didi kina son wani abu ne?”. “A'a Auta, ina Huznah take?”. Sai da Maanal ta ɗan taɓe baki sannan tace, “Naga Yaseerah ta kiranta yanzun nan ta saka hijjab ɗina ta fita a rikice. Ban san mita gaya mata ba amma da alama Yaseerahn na wajen gidan nan ma dan naji tana cemata gata nan zuwa ba sai ta shigo ba”. Kai kawai Shahidahn ta girgiza da faɗin, “To ALLAH ya ƙyauta. Dama zance miki ne inaga gobe in sha ALLAHU zamu wuce kadunan gaba ɗaya”. “Didi aikinki fa? Wani abu ya faru ne?”. “Babu damuwa zanma Abban Barrah magana ya nema min hutu na kwana huɗu tunda oga na abokinsa ne. Kinga idan biki ya tashi sai mu taho gaba ɗaya kawai”. Magana Maanal taso yi, sai kuma ta ce, “Okay ALLAH ya kaimu to”......

_____________★

A ɓangaren AA kam shima bayan wucewar su Maanal ya matsa aka sallamesa. RK yaso ƙin yin hakan amma ina. Ganin yana neman birkice musu Oum tace yasa a sallame san kawai. Sun iso gida Mamy da Abah na shirin zuwa asibitin dubashi. Dan shi Abah yau yaje gidan gwamnati tunda safe sakamakon kiran daya samu daga mataimakin shugaban ƙasa. Ita kuma Mamy ta fita dan ko kai AA ɗin asibiti bata san anyi ba sai da ta dawo ko sashenta bata shiga ba taci karo da Abah ya fito zaije asibitin. Shine yace ta juya suje dan yasan halinta zata iya ƙin zuwa saboda kawaici. Bata ce masa komai ba suka nufi motarta data ajiye yanzu, dai-dai nan kuma sai ga ƴan asibitin ma. Sai kawai suka runguɗa zuwa sashen Oum dan AA yace shi can zaije baya son sashensa. Can ɗin kuwa aka nufa da shi har ɗakin Oum. Anan suka zagaye sa cike da kulawa da tsantsar soyayyar da kowa ke masa a gidan....

★★★

Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan kawoma Mamy saƙo data manto a wajen mamansa shi kuma yaje gidan ta bashi ya biyo Mamyn dashi ya samu batun ciwon AA ɗin bai sauka ba da har yau ya kaisa ga zuwa asibiti. Shine ya kira matarsa Yaseerah yace tazo itama ta duba shi sai su koma gidan tare. Ita kuma ta kira Huznah ta kuma biya ta ɗakkota a gidan Shahidah kamar yanda mijin nata ya bata umarni. Koda suka shigo kai tsaye sashen Oum suka nufa dan har lokacin itama Mamy na acan dama duka ƴan gidan har su Saheeba da Nibras da Nuratu. Mai aikin Oum Mamy ta saka shigowa da su Abdul ɗin har falon sama na Oum. Duk suna a falo, idan ka cire AA dake can bedroom ɗin Oum da yay barci. Sai Babban Yaya da bai dawo gidan ba tun baro asibiti da yay ɗazun. Nibras da Nuratu na'a falon ƙasa suna girki. Nuratu ce ta fara cewa zata girka ma AA abinci kamar yanda uwarsu da suka kira suna gaya mata abinda ya faru a asibiti ta basu shawarar yi. Sai ita kuma Nibras ta ce itama zatayi dan wani irin tsanar Nuratu take ji tuni batun yanzu ba. Abinda ma ke ɗan sassauta mata ƙinta ganin yanda shi AA ɗin baya wani shiga sabgarta. Itama dai taci kuka bayan dawowar tasu daga koro sun da akayi daga asibiti. A hakan ma ba wani tarihin Maanal ta sani cikakke ba game da alaƙarta da AA, amma ta ɗauki aniyar bugar cikin Fawzan ta sani yau dan tasan irin matakin da zata ɗauka akan Maanal ɗin da dukan ahalinta ma. Dan itafa a yanda take jin AA a ranta ALLAH ko mahaifansa da su Fawzan zata iya kawarwa ta mallakesa ita kaɗai. Su Huznah sun hawo Nibras da Nuratu dake a kitchen basu sani ba. Sai da har su Abdull sun gama gaishe da Abah da Mamy da Oum Abah na tsokanar Abdull sannan suke haurowa da kayan abincin da suka shirya harda mai aikin Oum. Sannu Oum da Mamy ke musu, duk suka amsa tare da tambayar Mamy ina za'a kai masa abincin. D/table Mamy tace su ajiye. Dan haka duk suka ajiye a can ɗin. Juyowar nan da Nuratu zatai tana magana da Abdull sai idanunta ƙuru-ƙuru a cikin na Huznah da tun shigowar Nuratu falon mamaki da ruɗani suka baibayeta. Cikin kuwa ɗan waro ido na nuna mamaki Nuratu ta ce, “Kai wai wa nake gani kamar Huznah?”. Murmushin ƙarfin hali Huznah ɗin tayi, sai kuma ta sinne kai ƙasa wai ita kunyar surukai na wajen ta ce, “Nice Nurry”. Idanu Yaseerah da Abdul-hakeem suka haɗa. Yayinda Mamy ta saki wani murmushin jin daɗin ganin Nuratu da Huznah ma kenan sun san juna. Dan haka sai kawai ta miƙe tana faɗin, “Kunga muje can kafin Maman ɗan nan tace zamu hana mata shi barci”. Dariya Oum tayi dan sanin da ita Mamy take. “Oh abun ma harda ƴar sharri. To shike nan kuje ɗin dai dan kuwa ban san a tada shin”. Mamy ma dariyar ta sake yi. “Ai nasan gaskiya na faɗa”. Shima Abah dariya yaketa musu. Haka Mamy ta fice tare da su Huznah. Nuratu ma tai wuff ta bi bayansu. Suna gama fitowa daga apartment ɗin Oum ɗin caraf Nuratu ta riƙo hannun Huznah dake kusan ƙarshe. Cak Huznah ta tsaya, sai kuma ta juyo tana kallon Nuratu. Murmushi ta sakar mata da faɗin, “Oh oh friend ashe kece? ALLAH duk kin saka mamaki yama rufe ni da ganinki gidan nan kodai gidanku ne?”. Nuratu da zuciyarta keta watsal-watsal a ƙirji ta ce, “Eh gidanmu ne. Amma ba inda aka haifan ba. Gidan da zanyi aure kenan, kuma wanda zan aura ɗin ma kuka zo dubawa. A ina kika san Abdul-hakeem?”. Tsabar yanda zuciyar Huznah tai wata girgiza har taurari ta dinga gani na mata yawo a cikin ido. Cikin rawar baki ta ce, “Waye zaki aura ɗin?”. Cike da gadara da alfahari Nuratu ta bata amsa da, “Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, wato AA Darma”. Ai zabura gefe Huznah tayi tana mai fisge hannunta daga cikin na Nuratu, sai ko gata jikin bango kamar mage ta gamu da kare a kwanar da babu hanyar ɓillewa. Yanda tai ɗin ya saka Nuratu kafeta da ido itama zuciyarta na wantsalawa a karo na biyu. Sai kuma ta matsa gaban Huznah tana faɗin, “K jira-jira wai badai dama Yaya AA kike bibiya ba?. Babbar bala'i wai dama shine kika bamu labari?”. Bata jira amsar Huznah ba tai saurin fara danna wayarta ta latso hoton AA dake cikin wani lallausan farin yadi da yay masa shegen ƙyau ta nuna mata. “Shine wannan?”. Jinjina mata kai Huznah tayi a mutuƙar harmutse. “Kambu are you mad? Wai dama mijin aurena kike bibiya. Ehhhh ahhh lallai kin taro match yarinyar nan. Yau naga baƙar shegiya ubanwa ya aiko ki?”. Tai maganar da nufar Huznah gadan-gadan tana neman kai mata hannu ta shaƙota. Hannun nata Huznahr ta riƙe caraf, a dai-dai nan Fawzan ya iso wajen. “Kai kai kai lafiya?!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba. Dakatawa Nuratu tai daga shirin shaƙe Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce, “Yaya Fawzan wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta raɓu da jikina inata bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ƴar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina haɗa miki jini da majina ta yanda bazaki taɓa sake sha'awar yima kowa ƙwacen saurayi ba dan ........” ta ƙarasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah. Cikin ƙanƙanin lokaci rikici ya harƙume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan faratunnan ƙarin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa bakinta. Ƙara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah ɗin, ita kuma Saheeba ta riƙe Nuratu. Mugun ciwo Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon ƙarnin nan haka suka kasance har sanda huɗu na yatsunta. Jini tuni ya jiƙe wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala. Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana ƙoƙarin sake kai mata wani Abah ya riƙe hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da Fawzan ya mata take yi. Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita kaɗai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci akan AA suke faɗan, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan alaƙar Huznah da zuwa gidan ma. Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ƙaiƙayin baƙin ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari. Cikin ɓacin rai Fawzan ya ce, “Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son aura masa ita tana abu kamar ƴar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka dama ɗazun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to? Mi aka gaya matan akan su Shahidahn”. Cike da mamaki Abah ya ce, “Wace Lilly da Shahidah?”. “Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano”. Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta ɗan rumtse ido. Yayinda Abah ya furta, “Fawzan kasan mi kake faɗa kuwa? Da gaske kake yi?”. “Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta”. Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin ƙirji........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣3️⃣

______________

Readers Also Read