Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 30

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 30

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 30: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 30. ........Tamkar haɗin baki ta…

4,111 words

........Tamkar haɗin baki ta ɓangarorin biyu su duka sun tasa abinci gaba sun kasa ci. Yanda Ajwaad ke can a gaban Oum yana faman juya ɗan abincin daya zuba a plate anan ma haka ne ga Maanal. Oum dai ta ɗan lallashi Ajwaad, harta amshi spoon ɗin ta shiga bashi da kanta. Sai dai laumarsa batafi huɗu ba yace mata ya ƙoshi a shagwaɓe. Lallaɓashinsa ta shiga yi amma yace shi fa ya ƙoshi kamar ma zaiyi amai yake ji. Babu yanda ta iya dole ta barsa ya miƙe yana goge baki bayan ya saɓi bag ɗin islamiyyarsa. Dan su duka ukun sanye suke cikin uniform. Da kallo yayun nasa suka bisa da Mamy da itama take a falon, sai dai sam hankalinta bama a kansu yake ba. Sai dai babu wanda yayi magana har ya shiga store dake jikin kitchen ya fito, da alama akwai abinda ya ɗakko. Oum kawai ya kalla cikin sanyinsa ya furta, “Oum kimin addu'a sai na dawo”. Fuskarta da murmushi ta ce, “ALLAH ya tsare Autana. ALLAH ya bada ilimi mai albarka. ALLAH ya daidaita tsakani kai da Besty”. Idanunsa masu haske ya ɗan waro waje, sai kuma ya juya da sauri zai fice abinsa. Ai ko Fawzan ya kwashe da dariya. Yayinda Fadeel yay murmushi shi da Oum, Mamy dai kamar ma bata san sunayi ba. Harya saka ƙafarsa ɗaya waje Oum ta kira sunansa. Juyowa yay batare daya amsa ba. “Mamy fa?”. Oum ta faɗa babu wasa a fuskarta. Juyawa yay shima ya kalla Mamyn, sai kuma cikin sanyinsa da magana ƙasa-ƙasa ya furta, “Mamy sai na dawo”. Karan farko ta ɗan juyo ta kallesu su duka, sai kuma ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “ALLAH ya bada sa'a”. Daga haka ta maida hankalinta a kallonta. Murmushi Oum tayi, zuciyarta na sake cika da so da ƙaunar kishiyar tata da takema kallon ƴar uwa. Yayinda Ajwaad ya fice abinsa yana amsawa... Da ƙafa ya fito dan makarantar tasu babu nisa. Hakan yay dai-dai da fitowar su Shahidah Maanal biye da su. Bai tanka musu ba suma basu tanka masa ba. Sai da suka ɗan gota shi sannan ya lura da Maanal dake binsu a baya kamar bata so. Kallon juna sukayi kusan na sakan goma. Sai kuma kowanne ya ɗauke idonsa. Shi ya fara yin gaba like baima ganta ba. Itama sai tai nata gefen, sai dai duk da hakan a jere suke tafiya cikin tazara a tsakkiyarsu ta yanda ba lallai ka yarda tafiyar tasu ɗaya bace. A aji ma koda suka zauna babu wanda ya kula wani. Sai da kusan minti uku sannan ya ciro kwalin drink da babban biscuit ya ajiye gabanta bayan ya buɗe kowanne. Batare da yayi magana ba ya ɗauka Al-qur'ani ya hau bitar karatu. Itama sharesa tayi taƙi ɗauka taci. Sai ma ta ɗakko littafin koyon larabci mai ɗauke da hotuna na zane-zane ta hau zana color. Cikin haushi ya ƙwace littafin ya sake tura mata biscuit ɗin da lemo. “Bana ci”. Ta faɗa a kumbure tana kalmashe ƴan hannayenta a ƙirji ta da juyar da kanta gefe. Cikin haushin shima ya ce, “K kin iyama mutane laifi ki fisu zuciya. ALLAH idan baki ɗauka kin ci ba sai na bar ajin nan.” Tasan zai yi abinda yafi hakan. Dan haka bayan ta gama harare-harare ta ɗauka ta fara ci. Ajiyar zuciya ya saki a hankali yana sake maida hankalinsa ga Alkur'anin. Yanda taci da yawa ya sake tabbatar masa bata ci abinci ba. Yasan wannan halinta ne. In har tana fushi komi za'a bata in dai ba shine ya bataba bazata ci ba. Sauran wanda ta rage ɗin ta miƙa masa, babu musu ya amsa shima ya fara ci, wani ɗan guntu daya gutsira ya rage a hannunsa ta kamo hannun nasa ta saka a baki. Sai ya dungure mata kai. Dariya ta ƙyalkyale da shi. Hakan shima ya saka shi sakin dariyar. Kamar basu ba kuma sai suka warware. Bayan ya gama sukai bitar Alkur'anin tare kafin malami ya shigo musu.....

Koda aka tashi suka fito a jere Shahidah da Amaal kallonsu kawai suka tsaya yi, hakama Fawzan daya fito kallonsu yake yana dariyar shaƙiyanci. Maanal ce kawai ta tura baki gaba, shiko gogan bai kulashi ba yay gaba riƙe da bags ɗinsu. Koda suka iso gida su duka gidan su AA ɗin suka shiga. Tun a ƙofar falo Maanal ke ƙwala kiran Oum. Sai dai Oum na ɗaki bata amsa ba. Haka ta shigo ta nufi hanyar ɗakinta. Sai dai kafin ta shige sukaci karo da Mamy dake fitowa daga kitchen. Dakatawa Maanal ɗin tayi, tare da faɗin, “Mamy ina yini”. Amsa mata Mamyn tayi da kulawa, tare da tambayarta makaranta. Maanal ta ce, “Alhamdullah” tana wucewa ɗakin Oum. Shima Ajwaad dake biye da Maanal ya gaishe da Mamyn, batare data kallesa ba ta amsa kawai tana wucewa abinta. Ɗan Binta yay da kallo, ganin kamar zata juyo sai ya ɗauke kai ya shige ɗakin Oum abinsa. Oum na sallar magriba Maanal baje a gadonta. Ya ajiye bags ɗin nasu yana kallon Maanal ɗin. “Malama sallan fa?”. Ya faɗa yana hararanta. Baki ta tura gaba da faɗin, “Zan huta ne na gaji. An jima ba sai nayi ba”. Harara ya sake zuba mata, batare da yayi magana ba ya wuce toilet ɗin Oum, alwala ya ɗauro ya fito, gadon ya nufa, inda Maanal ta sake bajewa tana lumshe ido alamar barci ma take son yi. Duka hannayensa biyu yasa ya jawo ƙafafunta ƙiyyyy har ƙarshen gadon, ita kuma ta buga ihu tana kai masa duka da faɗin, “Ni ka barni ba nace zanyi ba anjima”. Ko kulata baiyi ba ya direta a tsaye, cike da tsiwa ta dubesa zatai magana ya ce, “ALLAH kika sake magana sai na ɓata miki rai. Wuce alwala konaje na haɗaki da Babban Yaya ko Ammie”. A duniya Maanal na tsoron Babban Yaya da Ammie, dan sune ke cimata ƙaniya a zauna kafiya. Cikin jin haushi ta cire ɗan hijjab ɗinta ta jefa a gadon Oum sannan ta wuce bayi fuuu. Shima ficewarsa yay batare daya sake kulata ba. Koda tayo alwalar kusa da Oum tazo tayi sallar itama...

Koda aka idar da sallar shi da Fawzan suka dawo, direct ɗakin Oum suka shigo, sun samu Maanal a saman jikinta kwance tana mata surutu. Fawzan ya gaida Oum, shima Ajwaad haka. Amsawa tai fuskarta da murmushi tana kallon Ajwaad, sai kuma ta kalla Fawzan suka saki murmushi. Ajwaad ɗin na kallonsu, amma bai tanka ba ya zauna kusa da Oum ɗin shima yana ɗakko bag ɗin Maanal na islamiyya. Sai da ya gama fiddo books ɗin duka sannan ya kalla Maanal dake ta surutu wa Oum. “Parrot tashi kiyi aikin islamiyya idan anyi isha'i mayi na boko”. Cikin ɓata fuska alamar fushi take da shi har yanzu, “Tace ni kayi min barci naje ji”. “Ko mutuwa ko?”. Ya faɗa cike da gatse. Tashi Maanal tai zaune idanunta cike da ƙwalla tana kallonsa. Sai kuma ta kalla Oum da faɗin, “Oum kin gansa ko, so yake ma na mutu ya huta ban girma naga ya zama kamar Daddy da Baabu ba”. Da ƙyar Oum ta danne dariyarta, “A'a in sha ALLAHU Auta bazaki mutu ba sai kinga girman Auta ya zama kamar Daddy da Baabu. Yo ina dalili Auta gaskiya ka bari. Ƙuruciya tare tsufa tare in sha ALLAHU”. Dariya Fawzan ya sanya da faɗin, “Wato Oum soyayyar nan fa na tafiya da ni.....” Harararsa Ajwaad yayi, sai kuma ya rufe books ɗin zai tashi Oum tai saurin kama hannunsa ta maida shi ta zaunar tana gumtse dariya. Sai kuma taima Maanal nuni data matsa suyi karatun. Ƙarfin dariya Fawzan ya ƙara tare da miƙewa ya fice yana faɗin, “In dai nine ma nayi nan. Bara dai naje mu daidaita da Amaal nima kozan samu Besty na”. Filo Oum ta ɗauka ta jefa masa. Ai ko ya ƙarasa fita a guje. Shi dai Ajwaad bai kulashi ba. Sai aikin da suka fara shi da Maanal na islamiyya. Basu tashi ba kuma sai da aka kira magrib. Ana idarwa ya dawo suka ƙarasa suka fara na boko kuma anan falo. Dan Oum sam bata barinsu su biyu a ɗaki, shiyyasa ma aka saka camara a ɗakinsu duk da ba'a taɓa kama ko ɗayansu da wani halin rashin tarbiyya ba gaskiya.... Da ƙyar Maanal ta bari suka kammala homework ɗin nan. Abinci ma tace ta ƙoshi sai da Oum ta lallaɓata ta bata tea. Ai ko tana gamawa ta ɓingire a jikinta ta hau barci. Sai da barcin yay nisa Ajwaad yazo ya ɗauketa ya kai ɗakin Oum ya kwantar, dan yasan ta gaji ɗin kam, kuma yanda tayi barcin nan duk bala'in dama za'ayi ayi bazata yarda tayi wanka ba. Dama haka take, kusan rayuwarta raba dai-dai ce a tsakanin nan gidan su Ajwaad da can gidansu. Dan ko kayanta a rarrabe suke saboda ko'ina a gidajen biyu tana zama. Wani lokacin sai tai sati bata leƙa gidansu ba sai kewarta ta ishi Baabu ne ya aiko a kirata sannan. Idan kuma ƴan arziƙin na kanta kullum sai taje ta gaida Ammie da Baabu ɗin. Idan kuma aljanun nata suka koma can gidansu kullum zata zo ta gaida Oum ne......

_________★

A kwana a tashi asarar mai rai. Yau ga su Maanal da yin graduation na gama primary. Zokaga rawar kai wajan mutuniyar. Balle da taji Oum ta shirya musu party ita da Bestyn nata. Duk da dai shi ya nuna baya so, amma Oum tace babu fashi sai tayi tunda Maanal naso. Babu yanda ya iya dole shima ya sakko aka hau shirye-shirye. Ammie kanta ba son fatin take ba, dan tasan hanyar kashe kuɗi kawai Oum ta ƙirƙiro ma kanta. Dan koda ta sanarma Babu ma kai tsaye yace shifa gaskiya bai da kuɗi. Cikin sanyin murya ta ce, “Aunty ce fa dama ta shirya musu bawai kuɗi zaka bayar ba. Naga ya kamata ka sani ne shiyyasa”. “Oh to ALLAH ya taimaka. Dan nima ina da nawa uzirin ne ma shiyyasa. Tunda hutun nan mai tsayine ina son muje gida gaskiya. Gwaggo nata magana akan hakan”. Wani irin faɗuwa gaban Ammie yayi, a take zufa ta shiga tsatstsafoma goshinta. Ganin ya juyo yana kallonta saboda jin tayi shiru tai saurin gyara yanayinta tayi ɗan murmushin yaƙe. “Kai amma nasan yaran nan zasuyi murna sosai. Musamman ma Maanal da tunda aka baro garin ba'a koma da ita ba shekara kusan shida.......” “Oh ke baki murna kenan?”. “A'a haba yazance bana murna ni da garinmu. Baka fahimceni bane ba dai”. Komai bai sake cewa ba sai shigewa toilet ma da yayi dan dama shirin wanka yake yi. Jagwab Ammie takai zaune zuciyarta na wani irin farfashewa a ƙirjinta. Gaba ɗaya jikinta rawa yake. Tabbas ta cancanci tai kewar tushenta, sai dai rasa wani giɓi da babban ƙalubalen data baro yasa mata jin tsoro da rashin son zuwa garin. Sai dai tasan ko giyar wake tasha bata isa bijirewa umarnin mijin nata ba kuma ɗan uwanta. Jin motsin zai fito yasa ta miƙe da sauri ta fita a ɗakin, tana mai ƙoƙarin danne komai..........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣8️⃣

______________

.........Babu bai sake bi takan bikin su Maanal ba, yama maida hankali a shirya musu tafiya gida. Yayinda Ammie taketa ƙarfin halin yin nata shirye-shiryen itama batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ƙayatar. Anci ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta ɓingire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a ɗakinta. Ɗaukarta tai cak ta maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta. Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye ɗakin Oum Abah ya shigo. Yakai zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce, “A'a anan surukar taki tai barci?”. Dariya Oum tayi tare da faɗin, “Kaji Aban su da wata magana suruka kuma?”. Murmushin sa ya sake faɗaɗawa shima da faɗin, “Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban mamaki. Zan so wannan abotar tasu ƙarshenta ya kasance hakan”. “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har cikin raina nake jin matuƙar ƙaunar yarinyar nan wlhy”. “Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumuɗi ba nifa da a yanzu zan ɗaura musu aure kawai”. Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace, “Ayi haƙuri dai a barsu sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren fiye da ita”. “Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a ɗazun Baban nasu ke sanar min zasuje gida hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai.” “Kai masha ALLAH, ai ni har ƙoƙarin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara”. “Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu na ƴan sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji. Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara girma”. “Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano dan tana jin daɗin zaman garin......” Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa. “Lafiya Autana?”. Oum ta faɗa tana kallonsa. Fuska ya ɗan yamutse kamar zai saki kuka ya ce, “Oum kaina ke ciwo. Kuma ina jin yunwa”. “Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba?”. Kansa ya ɗaga mata alamar “eh”. Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya....

___________★

Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumuɗi banda Maanal da tace idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun cigaba da shirinsu kawai. A ɓangaren Ajwaad ɗin ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu. Har ya samu Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da batun. Amma sai ya kwaɓesa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar zuwa Adamawa suga gida... Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da badaƙala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashirɓan kamar zata shiɗe. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya shige ɗaki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga ƙarshe da zazzaɓi ya yini ranar. Har washe gari sai da aka sanya masa ƙarin ruwa. A ɓangaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama ƙarshe zazzaɓi ya rufeta. Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka ɗan tsaya aka dubata. Washe gari suka ɗauki hanyar Suru da shima keda ɗan nisa daga nan cikin birnin Kebbi ɗin. Dan a ranar ɗin ma basu isa ba sai da zuhur.. Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ƙato bane can sosai. Ba kuma ƙarami bane ba. Suna da wutar lantarki sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan. Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a ƙasar da ake damawa da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka ɗauka, nan kam basu isa ba sai yamma sosai. Giro dai ƙaramin garine, amma ƙauyene mai ƙyau da ƙayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumuɗi musamman ganin harda baƙin fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin. Tun daga waje zaka san gidan ƙaton gaske ne. Dan ƙofa ce wangamemiya ƙwarai da gaske. Sai ƙatuwar bishiyar ceɗiya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta kaɗan massalaci ne da ɗakuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a sanyaye Ammie ta fito fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da ɗan wayonta. Tuni yaran sun fara kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. Ɗakuna ne guda biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke buɗe wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan buzu yanata rubutu a wani ƙatoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman ƙafarta zuciyarta na mata ɗan sanyi, ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu... “Barka da hutawa Baffah”. Ammie ta faɗa a hankali kanta a duƙe dai-dai tana shiga cikin ɗakin. Sai lokacin tsohon ya ɗago ya ɗan kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta, “Lale da mutanen garin dabo”. Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo riƙe da hannun Maanal data dogare a ƙofa. Sai da suka kai zaune tsohon ya sake faɗin, “Ashe zaka cika alƙawari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani kafin na koma ga ALLAH?”. Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta, “Ai min afuwa Baba, ai min afuwa”. Murmushi tsohon yay mai faɗin gaske. Sai kuma ya miƙama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana maƙe kafaɗa alamar bazata je ba. Turata Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce, “Wuce kije mana ban son raini”. Duk da tsohon bajin abinda Babu ya faɗa yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a ɗarare. Bai ƙiba ya kama hannunta ya zaunar a gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta, “Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwaɗayin ku ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne”. “ALLAH ya huci zuciyarku Baba”. Babu ya sake faɗa da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta ɗora da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk suka shiga gaishesa. Hannu duka ya miƙa musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk ya taɓa kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal na ɗan inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye ƴar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya naɗa akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar alewa dake cike da wata ƙwarya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan..... Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai ƙaton gaske ne da sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ƙarƙashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da aƙalla sun kai kusan ashirin. Yara ne sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake tsaitsaye wasu ma daga su sai karin ƙirji. A hakan kuma ƙalilanne a matan gidan, waɗan nan wanda bazasu iya haƙuri bane saboda zumuɗin son ganin Ammie da yaranta. Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na raɓe jikin Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na ƙoƙarin gaishesu da kalmar “Ina yini”. Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ƴar shekara biyu. Yanzu ko gashi tana ƴar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar.. Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne ɗakin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene aka dan katange da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Gwaggo mahaifiyar Babu ɗaya nata. Sai ɗayan na kishiyarta da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ƙara mata baƙin jini a gidan da ma wajen surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani ɗan dutse daga ƙofarta tana alwala. Sau ɗaya ta ɗago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa da fara'a yana faɗin, “Barkanki da wannan lokaci Gwaggona”. Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana faɗin, “Sannu Gwaggo! Mun sameku lafiya?”. Maimakon ta amsa su su duka a daƙile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi. “Babana kasha hanya”. Murmushin ƙarfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya ɗan sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa ya maida mata da murmushin yana faɗin, “Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma ina da alwala”. Kanta kawai ta jinjina masa. Ya miƙe yana kallon su Shahidah dake rakuɓe suna kallon Ammie dake duƙe kanta a ƙasa har yanzu. “Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana”. Jikinsu a sanyaye suka ɗaga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu daɗi. Yasan dole sai haƙuri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani. Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na damunsa matuƙa. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin ƙiyayyace wannan mai zafi........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣9️⃣

______________

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR GOLDEN COLLECTIONS TA TANADAR MUKU KAYAN ADO N FITA KUNYA KAMAR SU ATAMFA,LACES ABAYA SHOES AND BAGS DA KAYAN DECORATIONS D FURNITURES A FARASHI ME SAUKI

__________

Readers Also Read