Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 39
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 39: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 39. Alhamdullah washe gari kuwa sai…
4,318 words
Alhamdullah washe gari kuwa sai ga Nene da yaranta maza magidanta har biyu. Tana ganin Ammie ta gane jinintace. Itama Ammie na ganinta taga kamar mahaifiyarta ce tsaye a gabanta. Nan fa suka rungume juna aka hau koke-koke.. Wannan shine silar haɗuwar Nene da su Ammie. Bayan an sallamesu suka wuce gidanta. Yayinda Maanal data koma sanyi-sanyi bata magana, komai sai dai tabi mutane da ido ta cigaba da shan magani. Duk sati kuma anlkan kaita ganin likita. Ba kowa ke kaitan ba kuma sai Yazeed da baya nuna gajiyawa. Hakama mahaifinsa lokaci-lokaci yana zuwa duba jikin Maanal, dan Ammie dai Alhmdllh nata jikin da sauƙi. Dawowar su gidan Nene bai hana Yazeed da mahaifinsa cigaba da musu hidima ba, musamman ɗawainiyar asibitin Maanal dake fama da jiyya, duk da ba'a kwance take ba daka ganta kasan tana fama da jarabawar ciwo. A haka sukai kusan watanni tara, abubuwa suka fara dai-daita musu. Babban ɗan Nene yace yana son auren Ammie saboda halin matarsa ya ishesa. Amma mi sai rigima ta nema kaurewa. Ana cikin wannan halin ALLAH ya kawo dattijon arziƙi gidan. Wato Alhaji Usman Chalawa mahaifin Yazeed. Yazo domin duba su duk juma'a kamar yanda ya saba. Ganin rikicin dake faruwa babu wani ɓata lokaci ya ce shi yana son Ammie da aure. Dan ya fahimci lallai anzo wata gaɓa dasu Ammie zasu iya fara fuskantar ƙalubale a gidan. Shi kuma haka kawai tausayi bayin ALLAHn ke bashi, kodan shima ya ɗanɗani irin makamaciyar rayuwar a bayane oho. ALLAH sarki Ammie, dan kawai samuwar masalaha ta amincewa da Alhaji Usman Chalawa. Dan bata fatan raba ƙyaƙyƙyawar alaƙar dake tsakanin Nene da surukanta da ƴaƴanta. Sannan tana ma ƴaƴanta fatan ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Ta kuma fahimci anan gidan Nene da wahala a dace da hakan dan a yanzu hakan ma Shahidah da Amaal suyar awara suke anan ƙofar gida dan rufawa kai a siri kasancewar suna kwaɗayin komawa karatunsu. Alhaji Usman Chalawa dai da gasken yake. Dan sati guda kacal da yin wannan magana aka ɗaura aurensa da Ammie. Sati na sake zagayowa ta tare a gidansa. Tarewar data saka suka fahimci ashe ba ƙaramin mai kuɗi bane ba. Ga kuma matansa ƴan balaja'u musamman uwar gidan mahaifiyar Yazeed yaron kirki. Amma sai Ammie ta daure ta jure kodan yaranta su sami ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Sun kuwa samu, dan su duka Alhaji Usman ya maida su makaranta. Har Maanal data ɗan fara samun lafiya kaɗan-kaɗan. Sai dai maimakon ss3 daya kamata ace zata shiga a yanzu sun maida ta ss1. Ruwan addu'a da wadda Ammie ke mata, da jan ta ajiki da ƴan uwanta keyi da wanda Daddy ke mata, da tattalinta da Yazeed yake duk da uwarsa bata so, itama kuma bata saki jikin da shi saboda wani abun kan tuno mata Ajwaad yasa Alhmdllh ta ɗan fara sakin jikinta. Duk da dai nan ɗin ma akwai ƙalubale daga matan gidan da yara, sai dai bai cika damun su ba musamman Maanal da a yanzu ta zama shiru-shiru. Miskila, mara son magana. Idan kaga murmushinta sai Ammie ko ƴan uwanta. Ta tattara hankalinta gaba ɗaya akan karatu da ibada. A haka ta kammala secondary, a Kuma lokacin Ammie ta sake haihuwa ta biyu a gidan Alhaji Usman Chalawa, kamar yanda na farko ya kasance namiji na biyun ma namiji ne, still a kuma lokacin akaima Shahidah da Amaal aure. Kuma dukansu Daddy ne ya zaɓa musu mazan. Bayan bikin Maanal ta fara jami'a itama anan Zariya. Kullum ake kaita a ɗakkota, dan driver na musamman Daddy ya ɗauka mata. Gefe ƴan uwanta na hidima da ita, Ammie da Nene na bata kulawa. Sai dai duk da canjawar komai akwai abubuwa da yawa har yanzu sun kasa canja kansu a gareta. Musamman wasu a cikin ɗabi'un da abaya ba nata ba. Kamar karatun English novels da abaya batayi sai Ajwaad, saka gilashi a ido da makamantansu da yawa da abaya duk ɗabi'un Ajwaad ne. Ammie na lura da ita, sai dai bata taɓa mata magana akan hakan ba, dan tasan sai a hankali Maanal ɗin zata manta komai. Sai kuma yanayin ciwonta ya taka rawar gani sosai na sauƙaƙa tanka matan akan irin hakan kodan gudun abinda zaije ya dawo. Tana shekara ta biyu a jami'a Yazeed ya fito mata da ainahin abinda ke ransa game da ita. Bata wulaƙantashi ba, ba kuma ta amsheshi ba. Ta dai cigaba da girmamashi kamar yanda ta saba. Dan sosai take matuƙar ganin girmansa da kimarsa a cikin idanunta da zuciyarta. Da farko yaso ayi bikin ta cigaba da karatun a gidansa, sai uwarsa ta tada tujarar ƙin yarda. Haka akaita kai ruwa rana dai. A haka cikin amincin UBANGIJI ta kammala karatunta, ta fito da sakamako mai ƙyau, bata wani jima ba ta wuce hidimar ƙasa a Jos, a can ne ta haɗu da Zulaiha da Aneesa da suma hidimar ƙasar ce ta kawosu Jos ɗin ƴan Kaduna ne. Nan fa suka ƙule ƙawance duk da bawani saki jiki take da su ba. Basu fi wata guda ba ta haɗu da RK, sunje sayya wani shago shima yazo, shine ya yarda atm card ɗinsa batare daya sani ba Maanal ta tsinta ta bashi. Wannan itace farkon haɗuwarsu kuma silar tushen alƙar dake a tsakaninsu yanzu. Duk da da farko bata kulashi amma yayta naci batare da nuna gajiyawa ba koda a fuskarsa.......
_________★
MUN DAWO LABARI🚪🏃🏃🏃🏃
Yanzun kam sai muga wane mai rabo ne da Maanal ɗin. AA Darma da a baya ya furta babu soyayya duk da ta'asar daya tafka?. Yazeed daya taka rawar gani a wata gaɓa ta rayuwarsu mai tsanani da wahala shi da mahaifinsa da dukiyarsu da ƙarfinsu da mutuncinsu?. RK daya tsinta dami a kala, ya kuma nuna juriya da haƙuri akan dukkan ja da Maanal ta dinga masa a ƙasa. Ya kuma taka tasa irin rawar shima a yanzu ko muce yake kan takawar. Ga tarihin Maanal da alaƙarta da AA ya sani, zai kasance akan bakansa ko shi zai janye yabar ma AA da Yazeed filin ne?. Da gaske AA ba son Manaal yake ba a wancan lokacin kamar yanda ya faɗa sai yanzun ne ya fara son nata kokuwa akwai wani AJIYA A DUHU ne daya kamata mu sani?.......✍️
_Abin fa da yawa, mudai je zuwa kawai🏃🏃🏃🏃🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣5️⃣
______________
Assalamu alaekum,Yan uwa barka da wannan lokaci, inde Kaya kikeso unigue Wanda bazakigannsu ajikin kowaba se yangayu toh kishiga group din mom safwan Muna turakaya ko Ina cikin amincin Allah Muna seda lace, atampa,shadda,voil,beil,sarka,kayan yara,takalmi ,jaka ,kayan yara, kayan kitchen,Kae mufa komae daruwankane Allah y bamu kasuwa me albarka nagode
Ga inda zamu iya samun mu .
09064820534.
Ga kuma link na group ɗin mu.
https://chat.whatsapp.com/CuYcnxM1Z7VCYL5tqnyuL7
_____________
.........Daddy shine ya lallaɓa Maanal da su Shahidah fitowa wajen baƙin Giro. Gwaggo kakarsu, sai Babu mahaifinsu, sai Malam Aƙilu ƙani ga Baba Haruna. Wanda bayan barowar su Ammie Giro ya aure gwaggo. Zama kawai su Maanal sukai batare da sun kalla kowa ba balle gaishesu. Sai da Daddy yay musu magana sannan suka gaishesu ciki-ciki, dan Maanal ma kam bakin kawai ta motsa. Baabu ne kawai ya amsa cike da zumuɗi idanunsa cike da ƙwalla yana kallon ƴaƴan nasa, farin cikin rayuwarsa. Ita kanta Ammie ɗin satar kallonta yake. Zuciyarsa na matuƙar rawa da ganin ɗunbin canjawar da tayi. Canjawar da a yanzu idan yace ya taɓa aurenta wani sai ya gallara masa maruka kafin ya ƙaryatashi. Dan shi duk ya rame ya lalace tsufa ya taso masa saboda ciwo. Ga zaman ƙauye da canjin rayuwa tamkar bai taɓa zama aji ba a rayuwarsa, ga fitinar yara guda biyu da ALLAH ya bashi tare da Sailu amaryarsa. Ɗansa namiji shalele ya zama fitinanne a garin Giro da kewaye, sai mace dake bimasa itama dai marabarta kaɗan da namijin.. Daddy ne ya katse shirun da gyaran murya. Kafin ya ɗaura da sallama. Duk suka amsa. Cigaba yay da faɗin, “Alhamdullahi da kasancewar mu anan, kafin komai zan fara da nasiha a garemu baki ɗaya musamman akan ku yarana. Ina roƙon ku kuyi haƙuri da koma minene zukatanku suke tunawa da suka faru a baya. Ba'a fushi da iyaye, ba kuma a ƙin su sai idan akan abinda zai zama saɓon ALLAH ne. Koma minene ya faru ya rigada ya farun ya wuce. To a barsa a ya wuce ɗin a tari gaba. Yau ga mahaifinku sunzo garemu da muhimmiyar magana kamar yanda suka faɗa, sai dai dama bamu kai ga tattaunata ba ALLAH ya kawo ku. Dama a nawa shirin shine na buƙaci ganinku a gobe idan ALLAH ya kaimu, sai kuma komai ya sauƙaƙa.” Sake maida hankalinsa yay ga su Babu, fuskarsa da murmushi ya cigaba da faɗin, “Inaga tunda ALLAH ya sauƙaƙa gasu sunzo kafin ma mu nemesu ya kamata mu tattauna ko”. “Hakane”. Cewar Kawu Aƙilu yana gyara zama. Sai kuma cikin dakiyar murya ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda ka faɗa abinda ya faru ya riga ya wuce hakane Alhaji, dan haka maganar tuna baya da anyi kaza ko anyi kaza babu zancen maimaita shi ko tada shi. Dama munzo nan ne akan batun ita Maanal, wanda yake neman aurenta yaje garemu a satin daya gabata kuma mun bashi. Saboda dalilan ganin shi ɗin mutumin kirki ne da muke da tabbacin zai riƙeta da mutunci kamar yanda muka samu sauran ƴan uwanta a mutuncinsu.......” Cikin mamaki da ruɗani Ammie da Nene da su Maanal duk suka kallesa. Yayinda Daddy ya kasa jurewa shima dan shi zatonsa haƙuri suka zo basu da neman yafiyar su Ammien akan abinda suka aikata musu a baya, ashe wata fitinar ce suka zo da ita kuma. “Me neman aurenta kuma? Wanene shi haka da mu anan bamu sanshi ba?”. Cewar Daddy da mamaki. Wani irin ɗaure fuska gwaggo tayi, Babu zai yi magana ta hararesa. Cike da isa ta ce, “Sunansa Alhaji Bukar. Sanata ne babba a ƙasar nan, kuma mun bashi, munzo nan ne ma saboda mu tabbatar muku mun bashin sannan mu wuce da ita can Giro dan nan da sati biyu za'ayi biki kamar yanda ya buƙata”. Tuni zufa ta gama wanke Daddy, ya dai daure da ƙyar ya maida dubansa ga Maanal da take ma su gwaggo wani irin shegen kallo, sai dai uffan batace ba. “Manaal” Daddy ya kirayi sunanta a hankali. Juyawa tai tana amsa masa. “Waye kuma Alhaji Bukar?”. “Daddy ban sanshi ba nikam, bana kuma buƙatar saninsa. Sai dai ina roƙonka cike da girmamawa ka faɗama waɗan nan mutanen su bar mana gida su koma inda suka fito. Idan ba hakaba wlhy wlhy wlhy sai na kawo musu human right.” sai kuma ta miƙe a hankali tana duban gwaggo da wani irin ƙasƙantaccen kallo. “Ke kuma idan kina buƙatar mutuncin furfurar kanki kiyi gaggawa tarkata komatsanki ku kama gabanku. Ashe kina da baki ko ido da kwallin kwaso waɗan nan ƙazaman ƙafafun naki zuwa garemu? Kin manta mu ba jininki bane? Kin manta a yawon tazubar uwarmu ta samo mu? Kin manta bazaku haɗa zuri'arku da lallatacciya mai ɗauke da cikin shege ba? Kin manta... Kin manta.... Da yawa. To karki yarda ki bari na tuna miki, dan tunawar na nufin shiga ukun ki, tun kina iya banbance su waye a gabanki ki koma inda kuka fito. Inba haka ba kuwa.....” ta saki wani murmushin da jinjina kanta tai wicewarta da karkaɗa ma gwaggo yatsa na tabbatarwa. Harga ALLAH gwaggo ta matuƙar tsorata da yanayin Maanal. Eh tasan dama yarinyar tun tana ƙaramarta fitsararriya ce, amma bata san rashin kunyar tata har ya kai haka ba. Da ƙyar ta iya ƙarfafa zuciyarta ta maida dubanta akan Ammie. “Asiya ni ƴarki kema wannan ɗibar albarkar a gabanki kina jinta”. Murmushi sosai Ammie tayi, kafin a karo na farko ta sanya idanunta a cikin na gwaggo. “Mi kuke son nace da ita Talle....” “Talle?! Asiya ni kike kira da Talle?”. Gwaggo ta faɗa a zabure tana katse Ammie. Murmushin Ammien ta sake sakin mata, sai kuma ta ɗan laɓe baki, “Shi nasan sunanki, tunda shi na tashi nasan ana faɗa miki. Tabbas kamar yanda Maanal ta faɗa kuyi gaggawar barin gidan nan tunda mutuncinku, dan wlhy bazan hanata ɗaukar dukkan matakin datai niyya ba ita da ƴan uwanta. Tun farko ma da nasan abinda ya kawoku gidan nan kenan da bazaku ko zauna ba balle shigowa nan. Amma kunci arziƙin mahaifina ya fito ne daga ku, hakama mijin aurena daya ce na saurarenku, dan shi tuwo dai tuwo ne ba'a canja masa suna. Amma waɗan nan yaran baku da wani hurumi akansu, dan da bakinki kin tabbatar ma da duniya ba jinin ɗanki bane ba. Shima kuma ya tabbatar da hakan, idan duk kun manta maza kuje ku sake sabon tunani dan tuna hakan zai matuƙar taimaka muku. Idan kuma na sake ganin ƙafar ɗayanku a cikin gidan mijina na rantse da ALLAH sai kunyi dana sani da nadamar sani na. Yarinyata kuma nada mijin aure, kai koda bata da shi gara na jerata naita kallo matsayin kayan adon ɗaki da ace kune kuka zaɓa mata mijin aure........” “Asia!”. Daddy ya kirayi sunanta a hankali yana mai riƙo hannunta, ƙoƙarin fisgewa Ammie tayi idanunta na cikowa da hawaye, dan gaba ɗaya neman birkice musu take yi kamar ba Ammie Sarkin haƙuri ba, dole ya miƙe tare da jawota jikinsa kawai ya rungume. Murmushi Nene da ko a bata furta ba ta saki, hakama Shahidah da Amaal sai suka miƙe suna wata ƴar dariyar shaƙiyanci. Dan su kam ai ba sai sun ce komai ba, Auta ta gama komai ita da Ammie. Babu kam rawa jikinsa ya fara yi, da sauri ya duƙar da kansa ƙasa hawaye na cika masa ido. Yayinda gwaggo ta gama macewa a zaune ita da Kawu Aƙilu. Oho ko'a jikin Daddy, dama yayi hakan ne da gayya duk da sai da ya yaƙi kansa matuƙa saboda kunyar Nene. Kusan minti ɗaya tana a jikinsa kafin ya cirota a hankali ya zaunar da ita shima ya zauna a kusa da ita. Kallon su gwaggo yay babu ko kunyarsu ta sisi. “Ina fatan basai mun cigaba da wata jayayya ba. Amma ni zan baku haƙuri, in sha ALLAHU kuma zamu zo gareku domin auren ita Maanal, dan kamar yanda mahaifiyarta ta sanar muku tana da mijin aurenta a hannu.” Wani irin miƙewa Kawu Aƙilu yay a fusace yana kallon Daddy, “Alhaji munzo nan ne domin mutuntaka. Dan haka kada ka zubar da wannan darajar, kar kuma ka biyema sheɗaniyar can Asiya dan zamu iya yin komai a wannan karon kan yaran nan”. Murmushi kawai Ammie tayi, hakama Daddy. Sai Nene ce a wannan karon ta furta, “To kudai yi a hankali”. Harararta Kawu Aƙilu yayi, hakama gwaggo. Babu kam da har yanzu kansa ke'a ƙasa sai ya share hawaye. Cikin sanyin murya ya ce, “Gwaggo dama na ce muku abinda ake shirin yi kuskure ne, sannan mutumin nan wlhy bai dace da Maanal ba. Kada kuɗi su rufe muku idanu ku.....” “Rufe min baki shashasha kawai sallamamme, anƙi a bari ɗin, mu da su kuma mu zuba ɗan halak ka fasa. Dalla tashi mu wuce”. Komai Babu bai sake cewa ba ya miƙe. Haka suka fice yana waiwayen Ammie data ɗauke kanta gefe......
_______★
“Amma mutanen suna da ƙarfin hali gaskiya. Tab ɗi jan”. Murmushi Daddy yayi da kallon Nene da tai maganar, sai kuma ya kauda cike da girmamawa ya ce, “Bayin kansu bane Nene kuɗi ne ke angiza su, amma in sha ALLAHU zan bincika wanene shi wannan Alhaji Bukar ɗin da suke faɗa. Karku wani damu da su in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Ina ganin kuma kawai a haɗe auren nan na Maanal itama shine kawai masalaha. In ba hakaba zasu iya zagayewa su ɗaura mata aure da mutum nan fa”. “Eh kaima kazo da magana mai muhimmanci, amma suma sun san basu isa yin hakan ba....” “Idan har aka ɗaurama Maanal aure dan saboda su ma ai munji tsoron su kenan. Ka barsu suyi duk abinda suke tunanin zasu iya. Danni ma so nake suyi ɗin domin allura ta tono garma. Dan haka ina roƙonka Daddyn Hameed komai ayisa kamar yanda aka tsara tun farko. Yanda aka shirya bikin nan da farin ciki bana son a ɓata ma Yazeed shi dan ALLAH”. Ɗan jimmm Daddy yay yana kallonta. Sai kuma can ya saki ajiyar zuciya da jinjina kansa. “Shike nan na fahimceki. ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”. A tare suka amsa da amine...
Bayan fitar Daddy Nene ta kalla Ammie. “Asiya miyyasa kikace masa haka. Kamar bazai ji daɗi ba, zai kuma ga da gaske baƙya son wannan haɗin ne”. “Nene sam ba so bane bana yi, bana son a ɓatama Yazeed farin cikinsa. Hakama Mahaifiyarsa ina son a bata damar masa auren gata kamar yanda ta shirya. Wlhy ban taɓa baƙin ciki ko fatan kasancewar Maanal matar Yazeed ba. Shi ɗin mutumin kirki ne. Amma ina fargabar ta tsinta kanta a irin rayuwar dana tsinta kaina a shekarun baya. Wadda gashi nan har yanzu tana bibiyata. Yanzu ashe Nene har mutanen nan nada ido da kwallin zuwa su nuna suna da alaƙa da yaran nan?....” hawaye suka shiga zarya a fuskarta.....
______________★
“Sir! An tabbatar min yau bata shigo aiki ba kwata-kwata”. AS ne da furucin cike da girmamawa. Fin minti ɗaya kafin AA ya ɗago idanunsa daga rubutun da yake yi, akan AS ya zubasu. Hakan yasa AS saurin rissinar da nashi ƙasa. Shima janyewar yayi ya maida ga rubutun da yake yi. Kafin da ƙyar ya furta, “Tayi wani reporting ne akan rashin zuwan nata?”. “Gaskiya bana jin hakan, amma zan sake bincikawa.” Komai baice ba. Hakan ya saka AS fita sum-suma ransa fal mamakin boss ɗin nasa yau. Anya kuwa babu wata alaƙa tsakaninsa da yarinyar nan? Koda yake ɗan uwansa ne ya kawota companyn ai, maybe ƴar uwarsu ce. Da wannan tunanin ya kai a kujerarsa. Sannan ya jawo phone ya shiga neman shugaban department ɗin su Maanal.
A ɓangaren AA kam tunda AS ɗinsa ya fita sai ya samu kansa da kasa cigaba da fa aikin nasa, zuciyarsa ce ke ta faman kai-kawo. Karfa yarinyar nan da gaske take tabar aiki? Kai ina bata isa ba. (To wane ƙarfi gareka akan hakan?) Wani sashe na zuciyarsa ya ayyana. Fuska ya yamutse, sai kuma ya saki siririn tsaki yana kai hannunsa saman goshinsa ya murza. Fin mintuna biyu sannan ya miƙe. Jikin ƙaton window ɗin office ɗin nasa ya nufa, ya zubama waje ido na fin mintuna biyar. Sai kuma ya kalla agogon hannunsa mai shegen ƙyau. Wajen zamansa ya koma, ya ɗauka wayarsa dake fes-fes kamar ba'a amfani da ita yau da kullum ya shiga sarrafawa. Koda yay kiran number ɗin da yake buƙata sai ya ajiyeta ya ɗauka Bluetooth ɗinsa ya manna a kunnen... “Assalamu alaikum Son”. Daga can RK yay sallama. Cikin taɓe baki AA ya amsa masa, sai kuma ciki-ciki ya ce, “Ka nema ɗanka tun dare bai maka ba”. Dariya RK ya sanya da faɗin, “Sai dai ƙari dan na riga na samu gaka nan. Lafiya kake mun kiran tsakar rana?”. Ɗan jimm AA yay, sai kuma ya sake tsuke fuska kamar yana gaban RK ɗinne kafin ya furta, “Miya hana yarinyar nan zuwa aiki yau?”. “Yarinya kuma? Wace kenan?”. Kamar AA bazai amsa ba, sai kuma dai a daƙile ya ce, “Wadda ka kawo”. “Oh Maanal wai? Am sorry laifina ne wlhy, naso shigowa na nema mata alfarma sai aikin gaggawa ya sameni, taje Kaduna ne Mamanta babu lafiya. Amma yanzu nan munyi waya ta tabbatar min jikin da sauƙi ma. Gobe ma zasu dawo”.. Ɓoyayyar ajiyar zuciya AA ya saki, a fili kam sai ya hau faɗa. Wai dan mi ita bazata zo da kanta ta sanar ba. Ai ita suka ɗauka aiki ba shi ba. Miye-miye ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ko tanka masa RK bai sake yi ba ya yanke wayarsa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣6️⃣
______________
........Wannan yanke waya ya sake ƙona ran AA matuƙa. Dama RK ɗin bai san yanda yake jin zafinsa bane. Aiko sai ya sake cika yay fam. Ƙarshe ya kira Oum da ƙorafi, sai masifa yake yi ita har ma ta kasa fahimtar faɗan. Sai da yay mai isarsa cike da kulawa ta ce, “Auta ɗauka ruwa kasha. Ka kuma ja numfashinka sau uku. Idan a zaune kake ka kwanta kai shiru na kamar mintuna biyar kaji ɗan albarka”. Karan farko ya saki ajiyar zuciya. Sai kuma ya kashe wayar ya ɗauka ruwan yasha kamar yanda tace. Ya kuma ja numfashin da fesarwa sannan ya koma rukunin kujerun office ɗin ya kwanta a 3 sitter ya lumshe idanunsa. Fin mintina ashirin yana a wajen sai da akai kiran sallar zuhur sannan ya miƙe.....
★A ɓangaren Oum kam, wayar RK ta kira. Bayan sun gaisa ta tambayesa mike faruwa shi da Autan ta. Kansa kawai ya girgiza bai ɓoye mata komai ba ya sanar mata. Sannan ya ɗora da faɗin, “Karki wani damu da shi, kin san masifa bata masa wahala yanzu. Saboda aikin kamfaninsa sai taƙi zuwa taga mahaifiyarta.” Murmushi kawai Oum tai da faɗin, “ALLAH ya ƙyauta. Barni da shi idan ya dawo zamuyi magana. Kaima kuma ALLAH ka daina fusata min yaro”. Ƴar dariya yay daga can shima. “Ya daina dai fusata kanshi Aunty Babba. Ko kuma ki masa aure koya rage wannan zafin ran mara amfani. Ni bara naje inada theater ne yanzu”. Koda ya ajiye wayar sai ya saki murmushi. A fili ya furta, “Ajwaad kenan, ai kayi sakaci, in dai nine babu gudu babu ja da baya akan Maanal. Komai rintsi sai na mallaketa dan ina sonta. Sanin ainahin alaƙarku a yanzu bazai sa na janye ba tunda da bakinka ka furta ba sonta kake ba ba wani ya matseka ba. In sha ALLAHU a ƙarhen watan nan za'aje nema min aurenta sai dai koma mizai faru ya faru”. Ya ƙare zancen da murmushi....
Eh lallai Uncle RK namu ka shirya kenan😂👍. Ina bayanka walle🏃🏃🏃
_______________★
“Ammie mufa munce miki muna nan har biki”. “Ban yarda ba, kowacce ta koma ɗakin mijinta ranar juma'a sai ku dawo. Ko kun manta duk kuna aiki? Kuma kun san zamanku a gidan nan bazai haifar da ɗa mai ido ba. Musamman Maanal. Idan kuma so kuke ku ɗaga min hankali itama a birkitata to”. Da sauri Shahidah ta ce, “A'a kiyi haƙuri Ammie, zamu tafin anjima in sha ALLAHU”.
Badan su Shahidah sun so ba suka shiryo a ranar suka dawo Abuja. Dan sam Ammie taƙi yarda su sake tattauna batun su gwaggo. Da sun ɗakko maganar sai ta zame. Gashi ma daga ƙarshe ta korosu. Kuma har so sukai suyi mata maganar su Oum. Amma yaya zasuyi, farin cikinta shine nasu. Washe gari dole su duka sukai shirin komawa kan ayyukansu. Duk da dai da farko Maanal ta turza akan rashin komawa wajen nata aikin. Sai da Shahidah ta buɗe mata wuta da tabbatar mata zata haɗata da Ammie sannan ta shirya rai a ɓace. Shahidahn ce ta sauketa sannan ta nufi nata wajen aikin. Shigowar Maanal ɗin dai-dai da fitowar AA daga mota hannunsa akan kunne ya manna waya alamar magana yake. A kanta ya fara sauke idanunsa dake cikin gilashi, cak ya samu kansa da tsayawa, yayinda ita kuma datai kamar bata ganshi ba tai wucewarta. Idanu ya lumshe a hankali tare da buɗewa a lokaci guda. Sai kawai ya miƙama AS wayarsa dan sam ba fahimtar mi'ake cewama daga can ɗin yake ba....
A reseption suka sameta tsaye ita da Yaqub suna signing. Nan ɗin ma tamkar bata gansa ba ta wani irin ɗauke ido tana sakarma Yaqub wani shegen murmushi daya sanya zuciyar AA ɗin neman kamawa da wuta. Dan Yaqub ɗin na gaishesa ma ko kulashi baiyi ba ya wuce fuu. Hakama sauran mutane da wasu a ma'aikatan dake wajen domin yin signing ɗin bai kula gaisuwar kowa ba. AS na biye da shi da drivern sa dake ɗauke da basket alamar abinci ne a ciki. Ƙus-ƙus ma'aikatan suka fara na shigowar boss a fusace yau. Maanal dai batace uffan ba, batama nuna tasan mike faruwa ba. Koda suka bar wajen Yaqub ya maimaita maganar shima bata kulashi ba. Sai dai me suna zama sai ga waya wai ana nemanta a office ɗin CEO. Jitai kamar tace bazataje ba, amma dai ta dake ta miƙe tana sanarma Yaqub da zasuyi wani aiki tare cewar tana zuwa. Da kallo su Zaharadeen suka bita bakunansu cike da gulma. Dama tun shigowarsu ita da Yaqub ɗin suke binsu da kallon gulma. Ita kuma bata basu fuska ba bayan gaisuwa tai zamanta bata ko kula tambayar da suke mata na rashin zuwa aiki jiya ba da sukai...