Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 42
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 42: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 42. ✨ZAFAFAN DAI ✨
4,360 words
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣0️⃣
______________
.......Fin mintuna uku ya buɗe idanun nasa tare da ajiye carbin sannan ya dubi Maman Yaseerah. “Wato Hajiya babban ƙalubalen shine akwai wadda ke'a zuciyar yaron gaskiya da jimawa. Dan haka yaƙi biyu kawai da zamuyi zai sa ta samu damar aurensa. Na farko shine cire yarinyar daga zuciyarsa gaba ɗaya, ba kuma zamu iya yin hakan ba sai mun san wacece ita. Na biyu zamuyi aiki akan iyayensa, ta yanda ko baya so zasu sakashi dole amsarta. Mu kuma idan ta shiga daga ciki sai muyi aikin karɓa mata zuciyarsa ta yanda bazai sake kallon wata mace ba a duniya sai ita. Kai hatta uwar data haifesa wlhy sai dai tabi bayanta”. Gaba ɗayanzu babu wanda fuskarsa bata washe da murmushi ba. Sai Hajiya Basariyya ce ta ce, “Amma malam taya zamu san wadda ke cikin zuciyar tasa ne to? Sai naga kamar hakan zaiyi wahala”. “Bazaiyi wahala ba Hajiya. Wannan aikin na yarinyarki ne. Ita zata bincika mana ai”. “Karka damu Malam zanyi ƙoƙarin hakan. Sai dai akwai wata yarinya Nuratu da muka haɗu, itama tana sonshi, ban sani ba ko ita ce a zuciyar tashi, dan har ciwon nan itace ta jimin shi”. “Nuratu!”. “Eh malam”. Ɗan jimm yay, sai kuma ya sake ɗaukar carbi ya bata. Amsa ta sake yi ta zaɓa. Kamar dai ɗazun yanzu ma ido ya rufe na wasu mintuna sannan ya buɗe. “Gaskiya ba ita bace. Abinda na gani a kanta mahaifiyarta ke son ta aureshi da wata ta kusa da ita dake a cikin gidan su yaron. Suma kuma suna aiki a kanshi sosai, a yanzu haka ma suna shirin yin mai zafin gaske duk dan itama ya aureta.” “Eh lallai, ashe suma waɗan nan shegun kansu ne. To aiko Malam ai mana maganinsu, dama nace bazan yafe mata ciwon da ta jima Huznah ba. Jiba yanda ta maida min da fuskar yarinya kamar ƴar yarbawa ko goburawa. Ashe itama ba sonta yake ba shegiyar yarinya kawai”. “Karki damu da wannan Hajiya nasu mai sauƙi ne. Yanzu zan haɗa mata abubuwa taje ta cigaba da amfani da su. Nan da kwanaki uku zan kammala aikina nima. Itama sai tai ƙoƙarin samo mana wadda ke'a zuciyar tashi”. Godiya suka shiga jera masa kamar shine mai basu biyan buƙata. Maybe ma basu samun lokacin yima UBANGIJIN dake basun magiya irin haka ba. Gidan su Maman Yaseerah suka koma, dan anan zasu yini zuwa anjima su koma Kaduna......
___________★
Bayan sallar magrib AA ya baro massallaci. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa. Bai sameta a falon ƙasa ba, dan haka ya haye sama. Sai da yay sallama a ƙofar bedroom ɗinta ta amsa da bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune kan abin salla, tunda ya shigo kuma ta zuba masa idanu. Hakan ya sashi tsayawa yay shiru. Wani irin ɓacin rai taji ya tokare mata maƙoshi, a kausashe ta ce, “Ni zan taso kenan”. Komai bai ce ba ya ƙarasa takowa har gabanta ya zauna a saman lallausan carpet ɗin wajen ya tanƙwashe ƙafafu. Kansa a ƙasa ya gaisheta. Kai da ka gansa kasan babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Sai ma shakka da girmamawa irin ta na sama akan na ƙasa. Sai da ta gama shan ƙamshinta cikin kaushin harshe ta furta, “Ajwaad miye matsayina a wajenka?”. Idanunsa ya lumshe a hankali, maƙoshinsa na kaikawon ɓacin rai a cikin wuyansa. Da ƙyar ya iya amsa mata da, “Mahaifiya”. “Ai baka ɗauke ni a mahaifiyar ba. Saboda Fateema ta fini. Inda ka ɗauke ni da ban sharɗanta maka sharaɗi ba harda ALLAH ya isa kaƙi bi. Ya mukai dakai a shekarun bayan akan wannan shegiyar yarinyar ƴar matsiyata?”. Kasa bata amsa yay, sai dai fuskarsa tai masifar rinewa. Mamy ta daka masa tsawa jikinta har yana rawa. “Wlhy zan mareka. Wane alƙawari ka ɗauka min akan Maanal! Da zaɓin matar aurenka?”. Karan farko ya kalleta da rikiɗaɗɗun idanunsa da sukai masifar kaɗewa, sai kuma ya maida kansa ƙasa. Cikin kwantar da murya da girmamawa ya ce, “Mamy ban karya alƙawarinki ba. Kuma ni yarinyar nan babu abinda ke tsakanina da ita yanzu sai ma'aikaciya a company na. Shima kuma aure nace zanyi”. “Karma kayi, nace kadama kayi. Idan aka ɗaura maka auren dasu ka sake su a washe gari. Dan kama karkaɗe kunnenka kaji nan da wata guda za'ayi bikinka da Nuratu da Huznah. Sannan Maanal na baka sati huɗun kacal ka sallameta daga kamfaninka. Idan ba hakaba wlhy wlhy duk abinda na maka kaine kajawosa ciki harda muguwar addu'a. Dan ko mutuwa nayi ban yarda ka cigaba da mu'amala da ita ba. Inko ba haka ba ALLAH ya isa ban yafe maka ba wahalar ɗaukar cikinka da nayi dana naƙudar haihuwarka. Kuma wlhy zan taka har gidan iyayenta a wannan karon naja musu kunne itama kuma Fateeman zanyi fito na fito da ita dan na fahimci itace ta dawo da yarinyar rayuwarka ita munafuka anmimiya. To zan bata mamaki a wannan karon dan ban haifa mata ƴaƴan banza ba balle tace....” “Dan girman ALLAH Mamy kada kiyi haka. Kada kije musu gida. Ni kike da iko a kaina, zan kuma yi miki biyayya. Amma dan ALLAH kada ki ɓata yardar da Oum tai miki, kada ki raunana mata zuciya akan abinda ke da hannunki kika ɗauka kika bata harda shaidu. Hakama Abah bana son yayi nadamar yardar da yay miki. In dai Maanal ce zan barta, bari na har abada na cigaba da mata addu'ar samun wanda ya fini”. “Wannan kuma ya rage naka. Ni dai na gama magana. Kuma ka samesu da maganar Huznah da Nuratu da kanka a cikin satin nan.” Kansa kawai ya iya jinjina mata. Daga haka ta tashi zata kabbara sallarta. Shima sai ya miƙe dan ƙoƙarin tada salla ake a masallaci......
__________★
“Auta wai ina kika samo mana wannan azababbiyar mota haka ne? Ya subahannallah motar nan ta haɗu ni da Honey sai santi mukeyi fa a waje. Maigadi yace kece kika zo da ita”. Baki Maanal dake kokarin kaiwa zaune a kujerar dining ɗin ta ɗan taɓe, batare data kalla Didin tata ba ta ce, “Daga office ne fa.....” “Aka baki?”. Shahidah ta faɗa cikin katseta. Karan farko Maanal tayi murmushi tare da buɗe kular gabanta. “Kai Didi wazai bani mota kuma. Aikin nawa nai musu. Kawai fa Ajwaad ne baida lafiya yasa na kaishi gida, shine yace nazo da ita zai aiko a ɗauka. Kuma gashi har yanzu shiru”. Idanu sosai Shahidah ta zuba mata kamar mai tuhumarta da su, hakan yasa Maanal faɗin, “Kai Didi wai wannan kallon fa?”. “A ai dole na kalleki Auta, Ajwaad fa. Yaushe har kuka fara shiri haka da shi....?” “Nifa babu wani shiri. Kawai yau kaina ya isheni ne naje kitso, shi kuma ya ganni a wajen zan hau taxi yace sai na shiga ya saukeni a gida. Kawai muna hanya sai cikinsa ya kama ciwo shine ya roƙeni na tuƙa na ƙarasa da shi gidan......” Ita kanta data gama shirya ƙaryar sai taji ta kasa kallon Didin tata. Shahidah da mamakin yau Maanal da kanta ta kai kanta wai kitso ya cikama zuciya sai ta ma kasa magana. Dai-dai nan Uncle Sadeeq ya iso dining ɗin shima. Kujera yaja kusa da matarsa ya zauna. Maanal ta gaisheshi. Ya amsa mata da kulawa yana ɗorawa da faɗin, “Auta wai ƙyautar mota kika ciwo mana ne yau haka a gidan? Irin wannan zazzafar mota haka. Har yanzu fa a kaf Nigeria mutanen dake da motar nan basu da yawa. A Abujan nan ma tafi yawa. Sai Lagos suma. A Abuja kuma AA Darma na cikin wanda suka mallaketa a farko-farko “Ai ta AA ɗin ce”. Cewar Shahidah tana ƙoƙarin zuba masa abinci. “Yauwa koda naji, kai lallai wannan ogan naku kam na ji dake. Anya Yaya Yazeed da Doctor basu samu sabon rival ba?”. “Kai Yaya ”. Maanal ta faɗa kamar zatai kuka. Dariya yayi shima yana ɗaga hannayensa alamar surrender. Sai kuma yay zipping bakinsa. “Okay nayi shiru.” “To kace ba haka kake nufi ba?”. “Nace ba haka nake nufi ba Auta ”. Dariya Shahidah ta sanya musu da faɗin, “Kai kudai shiriritarku bata ƙarewa, kaita biye mata ga abincinka ma zai huce”. “To Honey idan ban biye mata ba wa zan biye mawa. Ƙurama da ƴaƴanta take wasa a dawa ai. Yanzu dai serious AA na ji dake Auta. Zan so gaskiya gobe na ganki a motar nan”. “Assalamu alaikum”. Sallamar mai gadi ta hana Maanal amsama Uncle Sadeeq zancensa. Shine ya amsa tare da bashi iznin shigowa. Sai da ya gaishesu sannan ya miƙama Maanal ledar hannunsa. “Auntyn yara gashi wani ya kawo a baki. Wai daga office ɗinku”. Amsa Manaal tayi, koda ta buɗe sai taga handbag ɗinta ce a ciki, miƙewa tai tana ajiye bag ɗin da faɗin, “Yauwa bara na baka key ɗinsu ka bashi ya ɗauki motar nan”. “Ai ya tafi, yana bani ya juya abinsa ”. Da mamaki Maanal data dakata ta juya tana kallonsa. Sai kuma ta ce, “Ya tafi fa? Ita kuma motar wazai ɗauka?”. “Ai a cikin mota yazo shima fa”. Rasama abin cewa Maanal tayi, sai kawai ta koma ta zauna. Maigadi ya musu sallama ya fita. Abincinsu suka cigaba da ci, sai dai kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman Maanal da Shahidah.....
__________★
“Anya Autana yau wani bai biya maka kujerar Makka a hanyar dawowa office ba?”. Cikin ɗan waro manyan oily ayes ɗinsa ya ɗago yana kallon Oum. Sai kuma ya saka yankakken Apple ɗin daya ɗauka a bowl ɗin gabanta a bakinsa. “Oum ke dai kawai kin fara tsufa ne idanunki basa ganina tar, dole Abah ya zo ya fiddo kuɗin miki wankin ido ko ya ƙaro amarya mai jini a jika”. Dariya tayi da ɗaukar fillo ta ɗan dakesa a kafaɗa, “ALLAH ka maida ni kakarka Auta, kai ba'a ce za'a maka wankin ido ba sai ni. To ina nan har jikokinka sai na gani da waɗan nan idanun. Amarya kuma ƙaryarta sai dai na aljanna”. Yanzun kam dariya ya ɗanyi har jerarrun fararen haƙwaransa na bayyana sosai. Ya kwanto kansa saman kaɗar Oum ɗin yana ƙara saka hannu a bowl ɗin ya ɗauka strowbarry ɗaya. “Tab yagwgwal kenan, Oum zuwa sannan ai inaga sai an haɗaki a tsumma kenan. Inama laifin ƴaƴan dai, ko idan su Naufal sunyi, kai sai dai ma Anum itace mace”. Kunnesa Oum taja tana dariya, shima dariyar yake sai kuma ya dafe hannunta yana ƴar ƙara. “Wayyo first love zaki ciren kunne. Abah kazo dan ALLAH matarka zata cire kunnen jin”. Dariya sosai Oum keyi, ta kuma ƙi sakin masa kunne. A haka RK da babban yaya suka shigo suka samesu. Babban yaya ya zauna kusa da ita shima yana kai hannu cikin bowl ɗin ya ɗauka yanka ɗaya na kankana da faɗin, “Oum dan ALLAH cire kunnen duka”. Sakin ma AA kunne Oum tayi da faɗin, “Oh zuga zugi to anƙi ɗin”. Dariya Babban Yaya da RK sukayi, RK ya ce, “Kaima fa ka sani kunya zaka sha in dai wannan yaron ne da babarsa. Dama shiru ka musu idan ta cire kunnen sai musha dariyar da ƙyau”. “Kuma fa haka ne Uncle R, nima da shishshigin tsiya.” Murmushi AA yay mai faɗi da yima babban yayan gwalo. Aiko ya jawo fillo shima ya kai masa duka. Tarewa Oum tai kafin ya sauka akan AA ɗin. “Wayyo babban yaya so kake yay ciwon jiki. Ga wahalar aiki da ya shawo dama”. Baki buɗe Babban Yaya ya ce, “Yo Oum shi ba namiji bane?”. “Ingarma ma kuwa in dai Autana ne, dan gidan nan yafi kowa ƙarfi”. “Ato faɗa musu shi da ruɓaɓɓen kawun nasa Oum”. AA ya faɗa yana musu gwalo. Filo biyu yanzu kam RK ya ta kwakuso yayo kanshi. Da sauri AA ya wani wantsala bayan kujerar cike da action mai birgewa. RK ya bisa yana faɗin, “Yau sai ka gayan waye ruɓaɓɓen...” Dariya sosai Babban Yaya da Oum ke musu. Dan sai faman zagaye falon suke kamar wasu yara. Kai kamar ba AA ba sarkin miskilanci da kamewa, kamar bashine Mamy ta gama yima tujara ba. Bawan ALLAH ya shanye ya danne dan kar Oum ta fahimci komai. Farin ciki sosai su Oum keji a ransu, dan sun jima basu ga irin wannan yanayin a tattare da Ajwaad ba. Yau kuma sai basu san musabbabin farin cikin nashi ba. Shigowar Abah ta raba wannan faɗa, dan kuwa tara-tara sukai shi da RK Abah ya kama masa shi, aiko RK ya bubbuga masa filon. Sai da Oum tazo ta ƙwace tana faɗin, “Eh lallai yau naga taron dangi, kun tarar min kan yaro”. Tafawa Abah da RK sukayi, ita kuma ta janye hannun AA dake faman tura baki gaba. “Kaga ƙyalesu zasu gani a kwanon abincinsu yanzun nan”. Da sauri Abah ya ce, “A haba ya zaki mana haka.” Gwalo AA yayma Abah da RK, RK ya ta hararesa yana ƙara kawo masa filo Oum tai saurin tarewa. Yayinda Babban Yaya ke kwasar dariya abunsa da faɗin, “Kaga Abah kai da Uncle R kun jama kanku, yau babu ku babu cin girkin Oum a gidan nan”. “Aa baza'ai haka ba, sai mu bata gaƙuri ai Fadeel. Kai har ma ɗan gwal ɗin nata ko Brother?”. Abah ya faɗa yana kallon RK. Shigowar Fawzan ya hana RK bana Abah amsa, duk sai sukai shiru suna kallon Fawzan ɗin da sam babu walwala a tare da shi. Hasali ma bai kula kowa ba ya wuce gaban Oum ya zauna a ƙasan carpet ya ɗora kansa akan ƙafarta. Dan gefe da gefenta AA ne da babban Yaya. A rikice Oum ta shafa kan Fawzan ɗin. Ta ce, “My baby miya faru? Baka da lafiya ne?”..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣1️⃣
______________
.......Hannunsa ya ɗaura akan nata dake shafa kansa, muryarsa cike da rauni ya ce, “Oum Nibras ce, wai ni takema gorin haihuwa yau, ni ɗin nan ni, ni dake da ƴaƴa har biyu a gidan nan, ga Naufal ga Anum”. Sai hawaye suka fara gangaro masa. Shi dama haka yake yana da rauni sosai. Babban Yaya da AA sun fisa ƙarfin zuciya. RK ne ya kai duƙe gabansa, sai kuma a hankali ya jawosa jikinsa ya rungumesa. Haka shima AA a hankali ya zamo daga kujerar ya zauna a kusa da su yakai hannunsa saman bayan Fawzan ɗin. Tuni idanunsa sun juye, fara'ar fuskarsa ta ɓace ɓat. Haka shima Babban Yaya sakkowa yay ƙasan ya zauna, su ukun duk sai suka sakashi a tsakkiya. Oum da tuni hawaye sun cika mata ido har sun fara sauka ta janye dubanta daga kallonsu ta maida kan Abah dake tsaye kawai shiru yana kallonsu shima. Tabbas babbar damuwarta a duniya yanzu shine ganin zuri'ar Fawzan data Ajwaad. Rashin samuwar ƴaƴa daga Fawzan har yanzu na tayar mata da hankali, tana cikin damuwa. Dan haka take tsaye kansa da addu'a sosai da sadaka. Haka shima AA akan aure...... Wani kalar miƙewa da AA yayi a fusace ya sakasu zabura su duka. Tamkar wani sojan da allurar ɗaukar fansar yaƙi ta tsikara ya nufi ƙofa, dama ransa fal yake da damuwar Mamy, yanata dannewa ne kawai dan kar Oum ta gane. Ai babu shiri Abah yay saurin shan gabansa. “Ajwaad! Ina zakaje?”. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi maƙoshinsa na wani irin masifar kai-kawo a wuyansa da sauri-sauri. Sai kuma ya buɗesu akan Abah, cikin zafin rai ya ce, “Ita wacece da zata dinga wulaƙantashi? Kodan taga tayi na farko ba'a ɗauka mataki ba shine ta sake maimaitawa yau, idan haihuwar iyawace miyyasa tata uwar ta haifeta ita kaɗai! Sai na koya mata hankali yau a gidan nan”. Murmushi sosai Abah yayi, sai kuma a hankali ya riƙo hannun AA ɗin daya sake yunƙurawa zai wuce. Maidosa yay jikinsa ya rungumesa kawai, tare da ɗora hannunsa a saman bayansa ya shiga shafawa. Sai kuma ya riƙo hannun Oum dake tsaye a gefensu tana hawaye, jikinsa ya matsota sosai itama ya rungumeta ta gefe. Dai-dai nan Mamy ta shigo falon da sallama, bayanta Nibras ce ke kuka sosai kamar wadda akace uwarta ta mutu. Zabura AA yayi daga jikin Abah, sai da ƙyar ya sake dannesa. Cikin wani irin raɗaɗin da yake jin zuciyarsa ya ce, “Abah ka barni, ka barni na koyama wannan wawuyar iya magana wa miji tunda inda ta fito ba'a koyar da ita ba......” “Ya isa! Ya isa! Haba Autan Oum ɗinsa. Please cool down kaji my sweetheart.” Abah ya faɗa cike da lallashi yana cigaba da shafa bayan AA da matsesa a jikinsa da har rawa yake saboda masifa. Shifa dama idan yay fushi sai addu'a. Sosai Nibras taji hankalinta ya sake tashi, kukanta ya ƙara ƙarfi, AA ɗinta yana fishi da ita, ina bazata iya ba, da tasan abinda zai je ya dawo kenan da bata faɗama Fawzan ɗin abinda ta faɗa ba. Dan ita fushin AA yafi ɗaga mata hankali akan na Fawzan ɗin. A hankali ta fito daga bayan Mamy da itama take kallon AA ɗin zuciyarta na sake girmama al'amarin sa. Ga wani ƙududun ganin duk yaran anan tare da Oum. Wannan zaman hirar daren da suke zuwa wajenta yana ƙona mata rai, ita wani lokacin ma daga gaisuwar safe ba sake ganinsu take ba sai wata safiyar, amma ita Oum in har suka dawo aiki wani lokacin ma sai sun fara zuwa sashenta kafin su wuce wajen matansu. Da sunyi isha'i kuma nan suke sake tahowa wani lokacin ma anan ake haɗuwa dinnar dole. Eh dole mana, dan ita dai ba'a san ranta bane ba, a hakama dan matansu nata ne duk yanda Oum ɗin taso jan ra'ayin Saheeban da Nibras basa sakin jiki da ita. Garama Nibras saboda AA yafi zama sashen Oum ɗin tana nacin zuwa ta zauna... Durƙusawar Nibras gaban AA da Abah yaja suka zauna ya maido Mamy a hanyyacinta. Babu wanda bai zubama Nibras ido ba na mamaki, itako shaiɗanci na soyayyar da takema AA ya rufe idonta bama ta fahimci shirmen da take shirin sake tafkawa ba. Muryarta na rawar kuka ta ce, “Yaya AA dan ALLAH kayi haƙuri kada kayi fushi da ni. Wlhy sharrin shaiɗan ne ya sani faɗa masa hakan kuma nayi nadama.....” “Baki da hankali ma, nima zaki bama haƙuri ba wanda kikama laifinba ashe!!”. AA ya faɗa a matuƙar hargitse yana yunƙurowa kamar zai falle fuskarta da mari. Da sauri Oum ta riƙo hannunsa cikin nata. Sai kuma ta kalla Nibras data rumtse ido a tunaninta marinta AA zaiyi. Cikin taushin murya da yakana ta kirayi sunanta. “Nibras!”. Idanunta ta buɗe a hankali, sai kuma ta kalla Oum ɗin. Hannu takai ta share hawayen dake cigaba da gangaro mata sannan ta ce, “Na'am”. “Zonan”. Babu musu ta matsa jikin Oum dan mafita take nema kawai da AA zai huce. Fushin nasa sukar rihinta yake yi. “Nibras gaskiya Auta ya gaya miki bashi kikama laifi ba ɗan uwansa kikamawa. Dan haka Fawzan zaki bama haƙuri. Sannan ina jan hankalinki da tausasa harshenki ga miji a yayin magana koda cikin fushi ne, ita kuma haihuwar nan mu yarda ALLAH shike badata, komai kuma nada lokacinsa. Kefa shaida ce kunje kunga likitoci ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma ana tabbatar da ku dukanku lafiya lau kuke, lokacine kawai baiyi ba. Nibras Baba shekara goma sha huɗu Umma bata gaɓa ko ɓatan wata a gidansa ba, amma ko mu dake a gabansu bamu taɓa jin eheem ga kowanne su akan hakan ba. Har ALLAH ya iyakance yau gasu twins a raye harda nasu yaran. Kuma lokaci ne ALLAH zai kawo kinji. Muna muku addu'a a dukkan motsinmu kinji ko”. Da sauri Nibras ta ɗaga kanta tana satar kallon AA dake a gefen Oum ɗin. Kafin ta matsa kusa da Fawzan da RK da Babban yaya suka saka tsakkiya. Hannayenta duk biyu ta haɗe waje guda muryarta na rawa ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri Jaan, sharrin shaiɗan ne dana zuciya. Amma in sha ALLAHU bazan sake ba na tuba.” ALLAH sarki Fawzan sarkin haƙuri, sai ya sakar mata murmushi, muryarsa a sanyaye ya ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya wuce.....” Bai ƙarasa ba AA ya miƙe fuuu ya fice a falon. Da kallo duk suka bi shi, musamman Nibras dake jin zuciyarta na kumfa a cikin ƙirjinta. Ji take kamar ta bishi da gudu ta rungumesa. RK ne ya katse yanayin da faɗin, “Aunty dafa autanki ne babban Yaya a gidan nan da kowa yaga takansa. Dan discipline Master za'ayi na gaske”. Dariya Abah da Fawzan da Oum suka sanya, Babban Yaya yayi murmushi. Mamy kam wani shegen kallo ta watsama RK a kaikaice. Yayinda Nibras kanta ke a ƙasa kwai. Cikin nutsuwa da dattko Abah ya shiga musu nasiha Oum na taya shi, yayinda Mamy ta miƙe batare data tofa komai ba tunda ta shigo. Kallonta Oum tai fuska cike da murmushi. “Madam ya baki mana addu'a ba zaki tafi”. Murmushi Mamyn ta saki kaɗan, “Oh baku gode bama dana taro muku ƴar taku dake shirin fita a gidan. ALLAH ya kiyaye gaba ni nayi nan mu kwana lafiya”. Murmushi Abah da Oum suke yi, wata ƙaunarta na sake ratsasu. Hakama RK da su Fawzan, duk murmushin suke yi. Nan dai suka ƙara musu nasiha har RK da Babban Yaya musamman Nibras. Ta nuna nadamarta sosai, duk da ita hankalinta sam ba'a kansu yake ba yana ga AA daya fita a fusace. Ta san yau ko barci da wahala ta iya yi mai daɗi, sam bata son ganinsa a damuwa, balle kuma ace itace ta ɓata masa ran ai al'amarin yayi girma da yawa gaskiya......
Humm wannan Nibras ALLAH ya taroki dai to🏃😥. Wai da irinsu a gaske🤔 ko sai a novels 🥱🥺😌.
__________★
“Kai malam wai fushin ne har yanzu dai?”. RK ya faɗa idonsa akan AA dake zaune a bakin gadonsa da waya a hannu yana sarrafawa. Daga wanka RK ɗin ya fito daga cikin bayinsa, dan yau anan ɗin zai kwana. Tunda suka baro sashen Oum shi da babban yaya yayo nan. A inda AA ɗin yake har yanzu anan ya samesa, yayi wanka ya canja kaya zuwa kayan barci. Tun daga amsa sallama bai sake kula RK ɗin ba shima kuma bai bi takansa ba ya ajiye dai basket ɗin da Oum ta haɗo musu abinci ya wuce toilet. Shine yayo wanka ya fito. A inda yabar AA ɗin ya sake samunsa, shine ya jefa masa wannan tambaya ta “Kai malam wai fushin ne har yanzu dai?”. Dai-dai yana zama a bakin gadon yana goge fuskarsa da ƙaramin towel. Karan farko AA ya ɗago ya kallesa, sai kuma yay guntun tsaki yana ajiye wayar. Shiru na wasu mintuna kafin ya ce, “Bazaka gane ba wlhy na tsani yarinyar nan. Ni banga mi Ya Fawzan ya gani a jikinta ba har yake zaune da ita. Gaba ɗayanta a zubinta ma shashasha ce” “To miji da matar sa ai ba'ace miya gani a jikinta ba. Kawai dai ita na kula tanada matsala ne. Ince ko cikakken 5 months ba'ai da yin irin wannan case ɗin tsakaninsu ba. Boko da ƙarancin ilimin addini ya mata yawa ne kawai, ga gata data samu a gidansu mara amfani. Yo mara amfani mana tinda babu cikakken tarbiyyar ɗiyan malam bahaushe a tare da ita dam, gefe kuma nake gani akwai sharrin ƙawaye kamar dake zugota”. “Oh, shine kuma duk zata tattaro haukarta tana saukewa a kansa. Ni ban san mike damun ya Fawzan ba sam, bana son wannan sanyin halin nasa. In dai zai ware rana ɗaya yaci mata uwa ai da ta dawo hankalinta. Kawai ka zauna yarinya ƙarama ƴar cikinka na raina maka wayo, da auren wuri yay daya haifeta ai”. Dariya RK yay da ɗan dukan kafaɗar AA ɗin, “Common Oum's boy hakan fa normal ne ga ma'aurata. Bari dai kayi auren malam zama ka ɗauki fiye da hakan. Mace kuma ko jika kayi da ita a ɗakin aure ai dai-dai kuke tunda ta gama ƙure maka girma”. Harrarsa AA ɗin yay. “Oh irinsa zaka zama kaima kenan?”. Cikin dariya RK ya ce, “Idan ta kama mizai hana. Balle ma nasan ni tawa mai hankali ce zata dinga lallaɓani bazata bari ta ganni cikin fushi ba. Kai ni yanzu ma fa zuwa nai muyi magana da Aunty da Yaya akan batun nawa wannan kuma rikicin ya shiga tsakkiya. Magana ta ALLAH aure nake so, idan har anyi azumin nan dani a tuzuru bana son nayi babbar salla a gwauro”. Sosai AA ya taɓe baki, sai kuma ya koma ya kwanta yana ɗaukar wayarsa, cikin halin ko in kula ya ce, “Ka samu matar kenan?”........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣2️⃣
______________