Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 51

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 51

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 51: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 51. Acan massallaci kuwa mutanene…

4,223 words

Acan massallaci kuwa mutanene cikin ɗunbin mamaki. Musamman ma'aikatan Mawaad Company da mafi yawansu suka halarci wannan aure. Tuni musu ya kaure akan batun. Wasu suce Maanal ta kamfani wasu suce ba ita bace ba. A gefe kuma suma kansu su babban Yaya harma da Abah a rikice suke. Ga mutane, dole suka danne dan daga nan an ɗunguma ne ƙaton hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci ga mahalarta wannan ɗaurin aure. Sai dai kuma hankali ya fara komawa akan rashin ganin AA a wajen. Dole aka fara neman layukan wayarsa, amma duk switch off. Hankali tashe Babban Yaya da Uncle Hussain suka koma can gidan dan dubawa. Sunko iso ɗakinsa a garƙame har yanzu. Tun suna bugawa da kiran sunansa har suka fara ƙoƙarin ɓalle ƙofar amma sun kasa. Ga su Abah nata kiransu a waya. Ai kafin kace mi su Aban suma dole sun iso. Nan fa aka taruma ƙofa da ƙyar aka ƙaryata. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kowa ya faɗa ganin AA yashe a ƙasa babu alamar rai a tare da shi sai uban jini dayay masa kaca-kaca, ga alamun zubarsa nan ta baki ta hancinsa. Gaba ɗaya babban Yaya ya ɗagosa jikinsa na rawa, hawaye tuni sun gama wanke masa fuska, da wani irin ƙarfi yake girgiza AA yana kiran sunansa, amma ina gaba ɗaya jikinsa ya gama saki. Babu alamar akwai sauran numfashi a tare da shi. Wani irin baya Abah da jikinsa ke rawa ganin yanda AA ɗin yake yarab yayi, sai da aka taresa dan kaɗan ya hana ya zube ƙasa. Baba Sardauna ne ya samu ƙarfin halin faɗin a ɗaukesa zuwa asibiti. Haka kuwa akayi duk da duk wanda ya kalli AA zaice yama rasu basu fidda rai ba, Uncle Najeeb da Alhaji ƙarami suka kamosa. Daka gansa kaga gawa kawai. A haka suka fita da shi aka saka a mota, suma duk suka shiga aka wuce.....

😭😭😭🥲🥺🤐

___________★

A Kaduna duka amare biyun sunyi ƙyau, sai dai Maanal kwance take zazzaɓi ya mata rijib, tun su Aneesa na ɗaukar abin wasa har suka fuskanci gaske take dan rawar sanyi ma take yi bana wasa ba. Da sauri Najma ta lulluɓeta da ƙaton duvet. Kafin ta fice tai kiran Amaal. Hankalin Amaal ya tashi, amma ta daure cikin hikima tayi kiran Shahidah dan bata son su ɗagama Ammie dake a tsakiyar mutane hankali. Ganin halin da Maanal ɗin ke ciki ba wasan yara bane ba Shahidah ta bada shawarar su sanarma Nene. Aikuwa haka akayi, da taimakon Nene aka bama Maanal magani, sannan ta zauna ta dinga tofa mata addu'oi. Ga ƙawayen Hajiya Basariyya sun cika gidan da kiɗa na hauka dan sifiku suka warware a harabar gidan saboda duk mazan sun wuce Kano sai mata kawai a gidan. A dai-dai wannan lokacin kiran Oum ya shigo wayar Ammie. Kasancewar wayar tana a hannun Amaal sai kawai ta ɗaga. Ko sallamarta Oum bata amsa ba tace, “Ƴar uwata”. Muryarta na rawar kuka. Cikin faɗuwar gaba Amaal tace, “Oum ba Ammie bace nice, wayar tata na hannuna ne ai. Amma Oum mike faruwa kamar fa kina kuka?”. “Dole ne nai kuka Amal dole ne. Yau ALLAH ya tabbatar da Maanal a matsayin matar Ajwaad”. Suɓucewa wayar ta nema yi, sai da ƙyar Amal ta tarota, da wani irin mamaki ta ce, “Oum! Kina nufin Ajwaad aka aurama Maanal?”. Ai da wani kalar sauri kowa dake a ɗakin ya juya yana kallon Amal. Manaal dake kwance tana faman rawar sanyi a bargo tai wani irin yakice duvet ɗin itama ta tashi zaram kamar wadda ke amfani da magic sai gata a gaban Amaal. Wayar kawai ta fige jikinta da muryarta na mazari ta ce, “Oum wace Maanal ɗin? Badai ni ba? Dan ALLAH kada kuyimin haka ni Rafeeq nake so, shi na zaɓa, da shi nake son rayuw.......” Batare data karasa ba kawai ta sulale ƙasa yaraf wayar tai nata waje. Ai da gudu kowa yay kanta ana ƙwala mata kira....

A dai-dai lokacin da Maanal ke sulalewa acan a sume anan sashen su Hajiya Basariyya itama ƙaninta ne ya kirata cike da mamaki yake tambayarta yaya haka, yaji ɗaurin aure ya juye akan Sageer ɗan ƙanin Daddy maimakon AA Darma data sanar musu. Shi kuma AA Darma ɗin sunji an aura masa wata wai ita Maanal Habib Giro. Gaba ɗaya Hajiya Basariyya ta saki wayar dake a kunnen nata ta faɗo ƙasa ta tarwatse. Ita kuma tai baya sai gata jaɓar a saman gado ta zube...........✍️

☹️☹️😥😥🥲🤐

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖9️⃣8️⃣

______________

.......Isowar labarin halin da AA ke ciki ya saka komai tsayawa cak ta kowanne ɓangare. Cikin ƙanƙanin lokaci mafi rinjayen manyan family ɗin suna a asibitin. Yayinda tuni RK, Abbu, da wasu likitoci suna a kansa anata ƙoƙarin ganin an ceto rayuwarsa. Sosai Oum ke kuka, kuka mai ban tausayi, dan dole Abah ya dake tashi zuciyar ya kasance da ita. Dama yaranta Babban Yaya da Fawzan suna manne da ita. Abin mamaki a farko Mamy bata asibitin, sai dai ƴan uwanta suka tausheta dan da neman birkicewa tai zata tonama kanta asiri suka janyeta zuwa ɗaki. Sun nuna mata cewar tada hankalinta fa babu abinda zai janyo sai rushewarta a wannan zuri'a, amma idan ta cigaba da dannewa komai ya lafa sai ta ribantu da cikar burinta, saboda tabbas suna zargin akwai abinda ke faruwa tunda har ɗaurin auren yay wannan juyewar, gaba ɗaya kuma laifin sun maidashi ga Oum ne, acewarsu dama itace ta tura RK jikin Maanal ɗin domin hakan ta kasance ita a yaudare ta. To dan haka saita kwantar da hankalinta amarya ta tare a kumayi bikin Nuratu wani satin daga nan sai su san matakin ɗauka. Dan ko zasuyi yawo tsirara suma sai sun bata taimako na kashe wannan aure, acewarsu Nuratu bazatai rayuwa da kishiya ba. Da ƙyar dai suka tausheta ta haƙura suka shirya suka tafi asibiti, sai kuma da suka iso suka tarar da tashin hankali yafi wanda ma suke hasashe. Domin kuwa awanni sai shuɗawa suke babu wani bayani a game da samuwar AA ɗin. Karo na farko da hankalin Mamy ya fara tashi, zuciyarta ta dinga raya mata kadafa ace rasa Ajwaad zatayi. Kai ina bata fatan haka, dan soyayyar da takema yaron daban take akan ta sauran yaran. Sai dai kuma abinda ya ƙona mata zuciya ganin yanda Abah da Babban Yaya da Fawzan keta dama-dama da Oum. Hakama sauran manyan kowa dai hankalinsa nakan Oum, ita aketa tausa da tunatar da ita tai masa addu'a. Dan ita ko kallonta kowa baiba a matsayin wadda tasha wahalar rainon cikin Ajwaad da naƙudarsa, da gaske dai ta tabbata sun ma manta da cewar itace mahaifiyarsa tarihi ya goge hakan....

Sai da su RK suka kwashe awa ɗai-ɗai har bakwai kafin su fara fitowa. Zuwa lokacin har anyi sallar magrib. Amma sai ƙalilan ne suka samun ƙarfin zuwa yinta. Kusan gaba ɗaya akai ca akansu, ALLAH sarki Abbu ga tsufa. Kaida ka gansu kasan su kansu sun jigata. Dan tuni babbar rigar saman kayansu duk sunyi fatali da su shi da RK. Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya bayan yace su sameshi a office. Bayan duk sun zauna a ƙaton haɗaɗɗen Office ɗin nashi cikin nutsuwarsa da Oum suka gado ya ce, “Kowa ya kwantar da hankalinsa tun awa biyu da kasancewar mu da shi aka samesa, bugun zuciyarsa ne yaƙi dai-daita tun ɗazun sai yanzu Alhamdullah. Amma duk da haka yana buƙatar addu'a, yaron nan ya jima a cikin ciwo, zuciyarsa ta kumbura a shirye take da komai ya iya faruwa. Amma Alhmdllh tunda har ankai ga wannan matakin muna fatan iyakar wahalar kenan dan gaskiya ya auna arziƙi. Yanzu za'a canja masa ɗaki domin hutawa, muna saka ran nan da awannin talatin numfashinsa zai dawo a gangar jikinsa in sha ALLAHU”. Sosai kowa ya dinga sakin ajiyar zuciya da jerama UBANGIJI godiya. Harga ALLAH bayanin Abbu ya daki zuciyar Mamy matuƙa. Bayan kamar mintuna biyar aka fito da AA, babu wanda bai ji sabbin hawaye ba, wato ɗan adam ba'a bakin komai yake ba. Wlhy duk iskancin da muke ji a rayuwa da ciwo ƙalilan idan UBANGIJI ya so nuna ba komai bane mu a cikin sakan sai mun bayyana a ba komai ɗin ba. Cikin ƙanƙanin lokaci AA ya canja, kamar ba ɗan gayu ɗan kwalisar nan shugaban Mawaad Company ba ya arrahaman.....

________★

A Kaduna kam ai gidan gaba ɗaya ya hargitse, kafin kace mi dangin Hajiya Basariyya sun cika sashen Ammie. Wani irin harmutsi ne na tashin hankali daban mamaki. Dan faɗi kawai suke sai sun daki Ammie. Yayinda Huznah ke ɗauke da kakkaifar wuƙa tana rantsuwa da UBANGIJI sai ta kashe Maanal. Dole aka rufe Ammie da Maanal har ma da su Amaal a ɗaki. Kafin Nene ta kira Daddy ta tabbatar masa fa akwai matsala ya dawo Kaduna. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa da jin abinda ke faruwa, dole yay kiran CP na Kaduna yace a tura ƴan sanda gidansa. Wannan fa dabara itace ta kawo sassaucin al'amarin. Dan dole kowa ya nutsu kaf dangin Hajiya Basariyya aka korasu sashenta, saboda Daddy ya bada umarnin hakanne kawai bawai a ɗibesu zuwa station ba, sai idan sunyi gardama be. Sai a wannan gaɓar Huznah ta yanke jiki ta faɗi wai ita ta suma. Nan suka rufu a kanta Hajiya Basariyya na kukan idan har ƴarta ta mutu sai ta ɗaure Ammie. Dan sun tabbatar baƙin asiri taima AA Darma dan ya auri karuwar ɗiyarta ragowar wani...

Oho su Ammie bama su san anai ba. Dan su nasu hankalin na nan akan Maanal da aka samu ta farfaɗo a bisa taimakon likita da sukai gaggawar kira, abokin Yaya Yazeed kenan. Dole akai mata allurar barci mai ƙarfi domin samun nutsuwarta, Alhmdllh cikin ƙanƙanin lokaci barcin kuwa ya bugeta. Da wannan damar suka samu sukai zaman jimanta al'amarin, dan Ammie tayi matuƙar ƙagara Daddy ya iso, yace ya taho, saboda dole ya baro kano, ALLAH ma ya taimakesa ya samu jirgi. Suna isowa Kaduna yake samun kira daga Kanon akan halin da AA ke ciki, sai kuma hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa. Dole yana isowa yace su Ammie su fara shirin wucewa Kano ɗin. A ɓangaren Hajiya Basariyya ma yace a shirya Huznah dan yau bazata kwanar masa gida ba a gidan mijinta zata kwana, Kanon kenan. Hajiya Basariyya ta birkice zatai masa hauka Yayanta ya wanke mata fuska da mari dan shi dama baya ɗaukar wargi. Ya kuma rantse mata idan ta sake cewa tak sai ya saka Daddy ya saketa. Wannan fa yasa dole ta nutsu, sai kukan baƙin ciki tana jin zuciyarta kamar itama zata fashe ɗin. Tana ji tana gani wasu dangin Daddy duka shirya Huznah dake kuka na fitar hankali. Tana rantsuwar bata son Sageer AA take so, itama ɗin dai Kawu Sani ɗin ne yay mata jan ido dole tai tsit. An gama shirya amarya Huznah tsaf, ashe abokan ango ana gama ɗaurin aure dama sun ɗakko hanyar Kano domin ɗaukar amaryar su. Zancen dinner ɗin da Hajiya Basariyya ta shirya anan Kaduna tasha ruwa kenan. (Sageer dai ya jima yana son Huznah tun tana ƙarama, sai dai Hajiya Basariyya na taka masa birki ganin ubansa bai kai Daddy arziƙi ba. Shi kuma sai kawai ya janye jikinsa ya barta ya cigaba da dabgarsa. Kwatsam sati uku da suka wuce Daddy ya samesa har kano ya zaunar da shi tare da masa tambayar har yanzu yana son Huznah? Sosai ya daburce a lokacin, dan harga ALLAH yana sonta har yanzu, kawai dai ya kama kansa ne dan ya fahimci uwarta da ita kanta sai a hankali. Da ƙyar ya iya jinjinama Daddy kai, aiko a take yace ya bashi ita, yaje kawai ya hau shiri biki nan da sati uku. Amma yana son yay shiru da bakinsa har sai ranar ɗaurin aure. Mamansa da Babansa ma sun sake kwakkwafarsa akan ya kame bakinsa ko a cikin dangi ba'ason kowa ya sani sai ranar. Amma zasuyi shirin biki normal sunan amarya ne kawai bazai fito ba sai ranar. Sauran ƴan uwa ma zai ce musu Daddy ne yakai kuɗin aure da kansa. Lamarin ɓoyewar ya bama Sageer mamaki, sai dai bai iya ya tambaya ba dan baya iya musu da iyayensa. Sannan yana matuƙar ganin girma da kimar Daddy a rayuwa, bazasu manta da halaccinsa ba, shine ya tsaya tsayin daka akan iliminsu da ginuwar iyayensu da dukiyarsa. Ai ko baya son Huznah akace gata zai amsa da hannu bibbiyu. Balle ma yana son abarsa). Sai da aka fara wucewa da amarya Huznah da tawagar dangin Hajiya Basariyya da babu yanda suka iya, dan ƴaƴansu Sani yace kowa ya shirya a wuce da shi akai amarya, wanda bazasu je ba anan cikin Kaduna suke su koma gidajensu biki ya tashi anan gidan Daddy ba'a buƙatar ganin kowa. Hakan kuwa dole sukayi, aka bar Hajiya Basariyya na faman kwasar kuka, sai manya da basu wuce biyar ba aka bar mata akan su ƙarasa haɗa kayan Huznah ɗin kafin gobe a bita da su. Kayan ɗaki dai dama kai tsaye can Daddy ya tura aka shirya a gidan Sageer, na Maanal kuma aka kai Abuja gidan su AA, ita kuma Hajiya Basariyya ta saki baki Abuja na Huznah aka kai, dan ko kaɗan Daddyn bai basu wata ƙofa ta fahimtar komai akan auren ba....

A ɓangaren Ammie tana son ƙarin bayani daga Daddyn itama amma babu fuska, dan ya haɗe gabas da yamma yace su shirya kawai, zasuje can Kanon sai a ƙarasa bikin acan ya tanadar da gidan da zasu zauna. Ita mai biyayya ce akoda yaushe a gareshi, dan haka ta fara shiryawa ita da kaf ƴan uwanta. Wanda zasubi mota suka fara yin gaba. Musamman ƙwai da ƙarkwatar iyalan Nene, tunda dama dai sune dangin kawai, sai abokan arziƙi da ake gaisawa daga haka sukai addu'a suka kama gabansu. Wanda kuma zumuncin yay ƙarfi sosai suka shiga tawagar ƴan wucewa a mota. Ƙarfe biyar Ammie, Shahidah, Amaal, Nene, sai Maanal da aka tada da ƙyar daga barci aka shiryata tana faman layi suka wuce airport dan su jirgi zasu bi, harda shi kansa Daddy ɗin. Wannan abu ya ƙona ran Hajiya Basariyya da sauran danginta. Dan haka suka bata shawara itama ta shirya gobe duk su tafi Kanon gara a ƙarasa komai akan idonta, dan sun fahimci wai Daddy na fifita agolarsa sama da ƴarsa. Haka kuwa akayi, a daren suka fara shirin komai daya dace acewarsu fitar sassafe zasuyi....

Kuce min ina uwargida ran gida Hajiya Yaya. Ai tana sashenta ita da ƴaƴanta da su Aunty Sabuwa na kwasar dariya. Dan su tun farkon faɗan daɗi yay musu. Acewarsu ai Hajiya Basariyyar ce dai-dai da Ammie. Zuwan ƴan sanda a gidan ne ya su nutsuwar dole suka cigaba da gulmar daga ciki. Koda Daddy ya dawo kuma Hajiya Yayar tazo domin bugar cikinsa sai yay mata banza, dan dama haushinta yake ji akan tura Yazeed honeymoon ɗin dole da tayi. Itama ganin yanda yay matan sai tai zuciya wai ya dizgata saboda bata da muhimmanci a garesa. Bai kulata ba taja ƴan matan ƙafafunta ta koma sashenta cikin ƴan uwanta suka sake buɗe babin zagin Ammie da Hajiya Basariyya ɗin ma. Koda za'a wuce da Huznah babu wanda yay niyyar bi a cikinsu, sai kuma Daddy yasa aka tattaro masa kaf ƴaƴan yace su shirya su bi masu tafiya Kanon. Babu yanda suka iya suna tura baki da ƙunƙuni dole sukai shirin tafiyar. Ganin haka sai Aunty Sabuwa ta zuge Hajiya Yaya akan ai ta shirya kawai suma subi ayari dan ayi komai akan idonsu. Dan Jaraba da masifa Hajiya Yaya fa bata jurar doguwar tafiyar mota saboda ƙiba amma haka ta shirya ɗin suka wuce batare da ko sanin Daddy ɗin ba......

__________★

Su dai su Ammie kasancewar tafiya ce ta jirgi sun isa cikin mintuna ne, dama kuma sai biyar na yamma suka wuce. Sunbi taxi ɗin cikin airport zuwa anguwar da Daddy ya tanadar musu gida. Da gani gidane sabo amma komai a kwai a cikinsa. Wannan ba abun mamaki bane dan sana'ar Daddyn kenan sayen gidaje da sayarwa. Maanal dai dana barci take ko'a hanya. Dole suna shiga aka nema mata wajen kwanciya ta kwanta. Su kuma suka fara ƙoƙarin gabatar da sallar magriba. Shima Daddy ta fita massallaci. Bayan an idar da sallar ne ya dawo yace suyi shirin zuwa asibiti, amma da nufin za'a bar Amaal saboda yara da kuma Maanal. Dan masu tahowa a mota ma na gab da shigowa cikin Kano. Wanda suka taho da Huznah ma su har sun iso, dan ita kai tsaye gidan nata mijin aka isa da ita ita da ƴan rakkiyarta... Su Ammie sun iso asibiti dai-dai gama jawabin Abbu, su Oum na ƙoƙarin shiga massallacin asibitin dake da ɓangaren mata dana maza domin gabatar da salla. Dan asibitin mallaki ne ga Abbu, shine wanda ya fara ginawa bayan dawowarsu Nigeria. Kafin aima RK nashi a Abuja kamar yanda ya buƙata. Suka kuma sake yin reshe a wasu sassan jihohin a yanzu haka domin dai taimakon al'umma...........✍️

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖9️⃣9️⃣

______________

........Sosai Oum taji daɗin ganin Ammie, hakama su Babban Yaya dama su Baba Sardauna isowar su Ammien akan lokaci batare da sun fifita shagalin biki ba ya faranta musu rai matuƙa. Sun kuma sake jinjina martabawar Daddy. Ammie dama ƴa ce ga wannan family na Darma, dan duk an santa musamman ma su iyaye da ta ɗauka matsayin iyaye a sanda tana rayuwa tare da Oum. Cikin girmamawa ta dinga gaishesu da yima AA addu'ar fatan samun lafiya. Suma sunta amsawa cike da dattakonsu da mamakin ganin yanda ta canja kamar ba ita ba. Dan shi Baba Sardauna ma kasa haƙuri yayi sai da ya mata ɗan ƙorafi na gudarsu da tayi. Haƙuri kawai ta bada ita dai, dan tasan zaman kace nace da kare kanta kamar raini ne take musu. Hakama Shahidah sai da su Babban suka tsokaneta cikin ƙarfin hali. Itama dai murmushin kawai take saki kanta a ƙasa... Nene ce ta bama Oum labarin halin da Maanal ke ciki. Dan tunda suka iso taketa faman tambaya. Kowa yay mata addu'ar samun lafiya itama amma banda Mamy da ahalinta. Dan su fa farko ma yi sukai kamar basuga su Ammien ba sai kuma mi suka gani oho musu suka ware dai aka gaisa. Bayan sallar isha'i su Ammien sukai musu sallama da addu'a ga AA tunda ba'a bar kowa ya ganshi ba gaskiya. Suma kuma su Oum ɗin gida ma zasu wuce Fawzan da RK da Uncle Hussain kawai za'a bari. Har mota sukai musu rakkiya, bayan sun wuce suma su Oum ɗin suka wuce...

Su Ammie sun samu ƴan tahowa a mota sun iso. Dama da abincinsu nacan Kaduna duk suka taho, dan haka sai aka samu sauƙi babu wata damuwar abinci ko ruwa balle lemuka. Sai a wannan lokacin Daddy ya samu zama da su Nene da Ammie, dan suma su Yaya Nuhu sun iso, dama suna a Kanon su ai tun daurin aure tunda Daddy ne kawai da Yaya Sani suka wuce ɗazun. Dalla-dalla Daddy yay musu bayani da tabbatar musu dama can tun kawo kuɗin aure da akayi bada sunan RK akai ba, da sunan AA su Abbu suka kai kuɗi Kaduna. Kuma sun tabbatar masa RK ne da kansa ya sakasu yin hakan, amma sun roƙesa akan dan ALLAH kada kowa yasan hakan har sai ran ɗaurin aure. Suka kuma bashi haƙuri akan al'amarin AA da Huznah bamai yiwuwa bane, dan da'a haɗa auren shi AA ɗin ya cutar da ita gara a aura masa Maanal ɗin kawai kamar yanda kowa yasan hankalinsa akanta yake. Dalilin ƙin bijirewarsa ne kawai basu sani ba kuma sun gagara ganowa. Da kuma suka binciki miyyasa shi RK ya haƙura ya sadaukar masa, sai yace musu wataran zai faɗa, yanzu dai shi buƙatarsa duk rintsi AA ya samu auren Maanal ne kawai. Shi kuma ya basu zaɓin koma wacece zai amsa da hannu biyu kuma zai riƙe amana in sha ALLAHU. Wannan zance shine ya girgiza Daddy, yaji zuciyarsa ta karaya sosai game da son haɗa Yazeed da Maanal daya dage a baya. Bayan wucewarsu kuma washe gari ya zaunar da Yazeed yay masa nasiha sosai sannan ya gaya masa gaskiya akan yabama AA Maanal dan shine yafi cancanta. Abinda ya shiga tsakaninsu a barshi kawai a matsayin ƙaddara da babu makawa sai ta faru su basu isa hanawa ba. Yazeed mai biyayya ne a garesa, dan haka ko jayayya baiyi masa ba. Daga ƙarshe ya bama Ammie da Nene akan ɓoye musu da sukayi tun farko shi da yaran Nenen. Murmushi kawai Ammie tayi, sai Nene ce keta faman sanya albarka da tabbatarma Daddy cewar baiyi laifin komai ba. Hakan ma da yay shine dai-dai. Dan ɓoye aure alkairi ne kodan gudun maƙiya da mahassada. Yanzu ba gashi anyi komai cikin kwanciyar hankali ba babu wani tsugunne-tsugunne. Amma da ace an bayyana ai ba'asan irin ƙurar da zata tashi ba sam. Hakan kuwa hankalin kowa kwance. Shi kuma Ajwaad ALLAH ya bashi lafiya da ita kanta ma Maanal ɗin. Itama Huznah suka sanya ma nata auren albarka sosai tare da roƙar Daddyn a lallaɓata dan ALLAH harta haƙura. Dan an mata laifi sosai. Murmushi kawai Daddy yayi. Ya kuma basu labarin yanda ya ƙulla shima auren na Huznah bayan wucewar ƴan Kano da yay nazari. Ya kuma shawarci Yazeed suka yanke hukuncin hakan dan a samu masalaha, itama a taimaketa da zaman gidan tana kara tsofewa.....

WASHE GARI

Zuwa washe gari duka ɓangarorin uku sai muce Alhamdullah. Idan ka cire AA dake kwance a gadon asibiti har yanzu bai farka ba. Amma dai ana saran daidaituwar al'amura da yawa a tare da shi. Maanal ma ta tashi jikinta da sauƙi, sai rashin ƙarfi da rashin walwalar fuska. Dan ko abinci sai da Nene ta zaunar da ita ta bata da kanta a baki cike da kulawa, tana kuma mata nasiha cikin hikima. Zuwa tashin hantsi Daddy da Ammie da manyan gaba ɗaya suka je asibiti suka duba jikin AA, har yanzu dai ba'a bari a shiga inda yake. Dan sun tarar da su Oum duk a waje, suma kuma basu jima da zuwa ba, tare kuma suka baro asibitin da su, saboda manyan family ɗin na Darma sun yanke a cigaba da bikin kawai, dinner ce da aka shirya gaba ɗaya sai walima, sai suka soke dinner ɗin za'ai walima kawai. A jiya ya kamata a kawo amare ayi dinner da daddare da safe ai walima da buɗar kai kowa ya ɗauki matarsa. Da kuma abin ya juye sai ya zam yau za'a kawo amaren ayi walimar zuwa gobe kowa ya kama gabansa. Wannan yasa shi kansa AA ɗin farkawarsa kawai ake jira dan za'a wuce da shi can KK HOSPITAL na Abuja ne. Idan kuma an samu yanda ake so ma falillahil hamdu.....

________★

A ɓangaren su Hajiya Basariyya kam dole ta sauka a gidan ƴan uwarta, su kuma can dangi suna gidan amarya wasu kuma a gidan iyayen angon musamman dangin su Daddyn, ita kuma dangin Hajiya Basariyya ɗin aka barsu a gidan Huznah amarya da har safiyar yau kuka ya gagara tsaya mata. A hakan ma dan Maman Yaseerah na tsaye a kanta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta auren nan sai sun kashesa ta auri AA ta fidda Maanal. Dan haka ita da wata ƙanwar Hajiya Basariyyan itama hatsabibiyar kanta sune zagaye da Huznah ɗin suna ta ɗorata akan mugayen abubuwa da zata dinga tafkawa mijin dama iyayensa duk da kuwa ƙanin ubantane uban nasa uwa ɗaya uba ɗaya. Itako tsaf take ɗauke komai harma tana ƙara nata a cikin zuciya. Oho sudai dangin Daddy ko'a kwalar rigarsu, shahalin bikinsu sukeyi cike da farin ciki, Hajiya Yaya kuwa ta shige cikinsu tayi kane-kane danta ƙona ran Hajiya Basariyya, dan su basu san su Ammie suma suna nan Kanon ba sam, tunda sai da suka taho sannan Daddy ya taho da su Ammie, kuma sunji ance ango babu lafiya a tunaninsu ai biki ya tsaya tunda anata kai waketa kaya, shiyyasa taga gwara ta maida hankali tayi maganin Hajiya Basariyyar kafin ta koma kan Ammie, duk da ma dai case ɗinta da Ammien yanzu kaɗanne ALLAH ya raba ɗanta da ƙarfen kafa, sai dai hassadar wanda yarinyar ta samu a matsayin miji ne ya kasa wuce musu a ƙahon zuciya daga ita har ƙanwarta Sabuwa... Duk abinda Hajiya yayan keyi yana komawa kunnen Hajiya Basariyya, tayi niyyar shiryawa kuma itama ta koma can cikin dangin mijin nasu da ƙyar ƴan uwanta suka dinga tausarta akan tabar komai a gama bikin lafiya idan suka koma gida ayita. Amma yanzu kam ta shanye kodan su san ta yanda zasu raba wannan aure na Huznah.....

________★

Readers Also Read