Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 57

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 57

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 57: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 57. _Tofa yau dai Maanal taji ainahin…

4,473 words

_Tofa yau dai Maanal taji ainahin Mamy, mi kuke tunani?🏃🏃🏃_

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣

______________

.......Tsam ta miƙe daga zaunen da take a step ɗin, babu buƙatar ta bada wayar yanzu, dan haka ta fice a sashen. Da alama Haule ma ta shige ta kwanta dan har ta kashe wuta. Maanal taji daɗin samun Oum na wanka, sai kawai ta adana wayar ta kwanta. Koda Oum ta fito likimo tayi kamar mai barci, duk maganar da tayi kuma ta fiske. Hakan yasa Oum ɗin fahimtar tadaiyi barcin. Shirin barci tayi, dan Abah sai kiran wayarta yake. Babu yanda ta iya dole ta kimtsa ta tafi. Saboda ya tabbatar mata yau idan batazo sashensa ba shi zaizo a gaban Maanal ya ɗauketa. Tasan halin kayanta, dan haka ta haƙura kawai tai shiri ta tafi. Sai da tama Maanal addu'a ta shafeta sannan ta rage mata hasken ɗakin ta daidaita mata ac kamar wata ƴar Baby. Aiko tana fita Maanal ta rushe da kuka. Wani irin tausayin Oum mai tsanani na ratsa mata zuciya matuƙa. Tabbas ta taɓa jin Oum ba ita ta haifi su Babban Yaya ba Mamy ce, amma bata taɓa sake tuna hakan ba ko kallon hakan a zuciya balle a zahiri saboda babu wani alamu dazai nuna hakan koda ga Mamyn ne balle Oum data gama sakankancewa. Itafa ganin komai take tamkar almara ko mafarki. Duk yanda taso yin barci hakan ya gagara, dole ta zauna kawai a zaune tana nazartar abubuwa. Daga ƙarshe ta ɗakko wayar nan ta goge recording ɗin da suka saka, yako naɗa da yawa dan harda maganganun Abah da Oum bayan fitar su Mamyn. Batamayi nisa a ji ba ta goge kawai ta ajiye wayar. Mikewa tai ya shiga bayi ta ɗauro alwala tazo ta shiga miƙama UBANGIJI kukanta. Kusan ma dukkan addu'oin ta akan Oum ne....

WASHE GARI yanda su Mamyn sukazo gaida Oum cike da makirci bakuna a washe sai Maanal ta shagala a kallonsu. A ranta tana jinjina lallai maƙiyin ɓoye shine ainahin maƙiyi, dan zai taima rayuwarka illa batare daka sani ba. Balle ace yana a jikinka, tare da kai matsayin masoyi na zahiri. Gara wanda zai zo ya kalleka ya ce maka wane BANA SONKA BANA ƘAUNARKA. Kasan baya ƙaunar taka zaka kiyaye komai tsakaninka da shi. Koda suka nema waya sai ta basu, da Oum tai magana sai tace ai taje kaima su Inte ɗin ta samu sunyi barci shiyyasa ta dawo da ita. A cikin zuciyarta kuwa faɗi take (Oum baki san su wanene waɗan nan mutanen ba. Sunfi duk wani abinda kike kallo a matsayin haɗari haɗari. Amma kada ki damu, ba sunce YAƘIN SUNƘURU bane abun, muje zuwa yanzu ne za'ai wasan na gaskiya. KAREN BANA SHINE ZAI MAGANIN ZOMON BANA. Ni Maanal Habib Giro, na ɗauki ɗammara da alwashin sai waɗan nan mutanen sunyi nadamar sake dawowata RAYUWARSU. idan su aya sukai alwashin gasa miki a hannu ni zan gasa musu ƘARFE ne a tsakiyar kawunansu. Sai sun san ZURU BATA CIN ZURU SAI SAI DAI A HAƊU AI ZURU-ZURU. Ƴaƴa kuma tunda ALLAH ya mallaka niki tofa naki ɗin ne. MUJE ZUWA WASA).

🤣🤣Tofa nace ba. Ƴar mutan Giro fa tace muje zuwa wasa, da alama ainahin MAANAL zata dawo🥱. (Maanal dama in an MUTU ana dawowa😜?)

😂😂🏃🏃🏃

____________★ KANO

Tsaye yay kawai yana kallon ƙofar daya gama mummurɗawa ya ji a rufe. A karo na farko ransa ya fara ɓaci da salon iskancin Huznah. Wai mi take nufi da shine halan? Ɗan iska ta ɗauke shi ko mi? Yau kwana ɗai-ɗai har takwas kenan da kasancewarta a gidan, amma tunda baƙi ƴan biki suka tafi da magriba tayi sai ta shige ɗaki ta kulle kanta. Da rana kuwa ita da kowa dake shigowa faran-faran. Hatta shi da rana tsakaninsu normal ne, da farko ya dauka kunya ce da kawaici irin na yaranmu, duk da baiyi zaton samun hakan daga Huznah ba, musamman idan akai dubi da shekarunta da wayewar zamani.. Wani ɗan murmushi yayi a karo na farko, ya sake sakin murmushin a karo na biyu saboda abinda zuciyarsa ta sake hasko masa. Baice komai ba yau ma ya juya ya koma ɗayan ɗakin dan dama bedrooms ɗin biyu ne a gidan sai falo, kitchen, ƙaramin store. Gini ne dai irin na mai rufin asiri ba irin wanda su Hajiya Basariyya suka jima suna fata ba. Yana barin wajen Huznah da duk ke ankare da motsinsa ta ballama ƙofar harara. Cike da tsana ta ce, “Maye, in dai nice mu zuba, wannan jikin kuma ƙwalelenka na AA ne. Dan wlhy sai na sameshi, sai na sabauta rayuwar agolar yarinyar can ta yanda bazata taɓa moruwa ba. Idan Ummi tabar uwarta tana yanda taso a gidanmu ni sai na tabbatar mata KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA. Daga haka ta koma ta kwanta tana cigaba da charting dinta da take yi daman. A dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Zaune ta tashi ganin wanda ke kiran. Sai da ta gyara zama sannan ta ɗaga. Murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Sille ya akayi?”. Daga can wanda ta kira Sille ɗin cikin muryar ƴan daba ya ce, “Normal ne uwar ɗaki. Kawai zance miki Nurry fa babu wani bayani a ƙasa kan bikin nan nata da AA. Dan a majiya mai ƙarfi ance har yanzu bashi da lafiya yana gida yana jiyya sai an kwantar sai an tayar. Babu kuma wani yunƙurin ma za'a sake biki a gidan a wannan satin. Kai ita ma agolar gidan taku tana sashen babarsa bata tare turakarsa ba”. Sosai hankalinta ya tashi da jin har yanzu AA ba lafiya. Cike da mamaki kuma ta ce, “Amma Sille kai bala'i ne, dan ALLAH ya akai ka samo wannan sirri mai girma haka?” “Hahaha uwar ɗaki kenan, karki manta a hannun Nurry kika ƙwaceni, amma bari na baki a buɗe, ina da yarinya a gidan dake aiki ta dalilin Nurry.” “Anya Sille bai kamata na fara tsoronka ba”. Dariya ya ƙyalƙyale da ita jin abinda Huznah ta faɗa. Kafin ya ce, “Haba uwar ɗaki, ai ke ta dabance. Kin ganni nan duk rintsi bana manta alkairi. Sannan amana ɗaya ce”. Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya. Tai masa godiya da tabbatar masa zaiga saƙo ta account ɗinsa daga haka sukai sallama.....

Wayar na yankewa daga can Sille ya ƙyaƙyace da wata muguwar dariya. Sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Yaro bai san wuta ba kenan sai ya taka. Daga ke har Nurry ɗin kune kuke min aiki bani ke muku ba. Ina amfani da kune kawai na samu kuɗaɗe. Kuna nan kuna jira baku ankara ba sai dai kuga gawar shegen AA ɗin naku kwance a gabanku. Wannan alƙawari na ne, sannan gaba ce ta tsawon shekara takwas ni da shi.. kai yama kamata nasan agolar yarinyar nan ta gidan ku da akace ya aura”. Wayarsa ya sake ɗauka ya shiga tafa saƙo. Babu jimawa akai masa flashing. Kiran number ɗin yay black, kafin ma ta gama ringig ɗin farko an ɗaga. Daga can ƙasa-ƙasa muryar mace ta bayyana. “Baby miya faru ne naga kace na maka flashing idan ni kaɗai ce? Faka-faka kafin wannan ƴar sa idon ta fito wanka”. “Ke nifa yarinyar nan idan tace zata takura miki a gidan nan ALLAH zan aikata barzahu”. “A'a ka rufa min asiri babu ruwan ka da ita. Sannan itama tana da nata amfanin da take mana ai. Yanzu dai miya faru?”. Tsaki yaja mai kauri, kafin ya ce, “Hoton amaryar gidan nan nake so?”. Hankali a ɗan tashe ta ce, “Wai Matar AA”. “In ba ita ba akwai wata amarya ne a gidan?”. A sanyaye ta ce, “A'a. Amma Baby kasan hakan akwai haɗari ko? Taya zan ɗauketa hoto nikam?”. “Kefa wasu lokutan gaja ce wlhy, kuna gida ɗaya baki san yanda zaki shiga jikinta bane?”. “Tab wlhy Baby hakan zai yi wahala. Itafa irin miskilayen mutanen nan ne na gaske. Sannan zan iya ƙirga maka ganinta da nai a gidan nan. Koda yaushe tana ɗaki ko falon sama kuma a sashen Oum take bana Mamy ba”. “K ni hakan bai dameni ba. Kawai hotonta nake buƙata na kuma baki kwana biyu kacal”. Daga haka ya yanke wayar yana huci. Itako daga can sai ta zuba uban tagumi zuciyata na kai-kawo. Sille ya zamewa rayuwarta bala'i, itako miya ja mata shigowa bariki. Ƙiri-ƙiri da uwarta da ubanta a duniya saboda neman duniya su sun kasa tanƙwara rayuwarta ga wani ƙaton banza ɗan daba na juyata yanda yake so kuma dole tabi. Tabbas ta ƙara yarda da kalmar nan ta malam bahaushe dake cewa WANDA BAIYI SHARAR MASSALLACI BA YAYI TA KASUWA. To ita a ganinta ta kasuwar ma ai mai sauƙi ce, TA BARIKI yafi dacewa ace....

__________★

KADUNA

A Kaduna ƙiri-ƙiri Ammie ta hana Daddy sukuni sai rigima take masa akan dawowar su Hajiya Yaya. Shi kuma yayi biris da ita. Da yaga tana neman saka masa rayuwa gaba sai ya shirya yabar mata kasar ma. Wannan abu kuwa ya masifar ƙona mata zuciya. Harda kiran Nene tana kuka. Sai da Nene ta gama saurarenta tsaf sannan ta ce, “Ai ni hakan da yay ya min dai-dai Asiya, tunda nace ki fita a maganar su kin ƙi ko. Su idan sune hakan ta fari dake har fati inaga sai sun shirya bama murna kawai ba. Ba gaban iyayensu suke ba? To ki nutsu idan zaki nutsu kinji na faɗa miki. Kuma nima kada ki sake zuwa min da zancensu. Haka kawai ki dinga ɓatama kanki rai da mijinki akan waɗanda basu ƙi ki faɗi ki mutu ba.... Haka Nene taima Ammie tas sannan ta yanke kiran. Ta kuma tabbatar mata ta kira Daddy ta bashi haƙuri idan ba haka ba zatazo har gidan ta sameta. Wannan faɗa na Nene shine ya kawo ƙarshen rikicin Daddy da Ammie suka shirya ta waya. Sai dai duk da hakan rashin dawowar matan gidan na damunta kodan yaransu dake zuba mata rashin mutunci. Dan ma bata kulasu bata shiga harkar su. Amrah ce kawai babu ruwanta....

__________★

“Mabera! Wai nikam mike damunka kwana biyun nan? Gaba ɗaya baka da sukuni sai tunani da lissafe-lissafe”. Numfashi mai nauyi Daddyn Nazeefa ya sauke, kafin ya juya yana kallon abokin nasa shaƙiƙi da shi da shi suka san juna na haƙiƙa dan kar-tasan-kar ce. “Himm Bakori kenan, kaima ai kasan maganar gizo bata wuce ƙoƙi. A lissafin auren Nazeefa da yaron Alhaji Usman Chalawa wata uku kenan yau cir, kasan dai lokaci yayi da aikina zai fara a kansa ai. Wannan shine lissafe-lissafen da nakeyi. Sai kuma baban naman dana hango yanzu ya shigo a tarko”. “Tofa babban nama kuma? Waye hakan?”. “Ba yanzu zaka sami ba. Sai na gama da Chalawa tukunna. Jiya nayi waya da Nazeefa tace azumi na goma zasu dawo gida. Dan yace mata zasuyi Umra. Dan haka nake shiri, da sun dawo zata fara min nata aikin”. Murmushi Bakori dake kallonsa yayi, a ransa yana mamakin hatsabibancin aminin nasa, ta gefe tausayin yarinyarsa da yake son jefawa a ramin zamba cikin amincinsa yake. Shifa duk iskancinsa ALLAH bazai iya hakan ba. Dan iyalansa nada muhimmanci mai girma a wajensa......

(Humm dan baka san iyalin naka tare kuke raba dai-dai da aminin naka bane Alhaji Bakori🏃🏃🏃🏃) _________★

Alhamdullah jikin AA yay sauƙi sosai, koma muce ya warke sai abinda ba'a rasa ba na tsakanin ruhi da gangar jiki. Kamar yanda yay alƙawarin bama Abah dama ya bashi ɗin. Dan ya tattara al'amarin Manaal ya ajiye gefe kamar ba shine yasha ciwo akan rasata da yaga zai yi ba. Gefe kuma baice komai game da batun ɗaga aurensa da Nuratu sai zuwa bayan salla ba. Sai dai yaƙi yarda su zauna da Mamy duk yanda taso. Da zarar ya fahimci zasu keɓe sai ya zille abinsa. Fahimtar akwai gaɓar da za'azo ya nema mafita ya rasa ya sashi shirin komawa kan aiki. Itama kuma Maanal yace ma Oum ya kamata ta koma kan aikinta, dan shi ba ruwansa idan ta taka doka zai bari kamfani ya hukuntata ne. Hutun kwana goma aka bata, gashi yau suna neman sati biyu. Azumi saura kwanaki bakwai a fara shi kacal. Ita Oum ma tsayawa tai kawai tana kallonsa. Yayinda Maanal tai kamar bata falon ma. Dan tunda ya shigo ta gaida shi ta maida hankalinta ga karatunta, sai shi da Oum ke hirar. Yanzu haka take masa, idan dai ya shigo sashen zata gaida shi, daga wannan gaisuwar ko kallon inda yake bata sake yi komai tsahon zaman da zai yi. Ko kuma tana fahimtar lokacin shigowarsa yayi sai ta koma ɗaki abinta. Wannan abun na cimasa zuciya da ƙona masa rai, amma ya share kamar bai fahimceta ba. Dan ya riga ya sakama ransa daga ita har Aban nata zai iya dasu. Shiyyasa da Oum ta nuna damuwa akan rashi bashi Maanal ɗin zai shiga lallashinta da nuna mata shifa babu komai ta kwantar da hankalinta ta bama Abah dama yay yanda yake so. A ransa kuwa shi kaɗai yasan abubuwan da yake shiryawa.........✍️

_😂Dan Oum mi kake shiryawa? Dan bamu musha mana._

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣

______________

.......A ɓangaren Mamy kam ranta fes akan hakan. Burinta ɗaya yanzu shine Maanal ta dawo sashenta da zama kamar yanda ta zunguri Abah da zancen. Sai dai kamar ya yarda da farko sai kuma taji bai sake maganar ba. Ta ɗan bashi kwana biyu ne ta sake zuwa masa da zancen, dan idan ta cika matsawa zai harbo jirgin ta ne kasancewarsa mutum mai tsarta. Ajwaad kuwa data fahimci kauce-kaucen sa zata tattarashi ne ta watsar, akwai gaɓar data tanada masa ne. Sun gama tsara Nuratu zatazo nan gidan tai azumi. Acewarsu mamanta zata shirya ta tafi umrah sai ace Nuratun tazo nan ta zauna kafin ta dawo. Gefe kuma cike suke da alwashin bayan salla da sati biyu koda tsiya-tsiya sai an ɗaura auren Nuratu da Ajwaad idan ba haka ba kuma suyi maganin Oum... Oho ita bama tasan sunai ba. Duk da bata son haɗin auren Nuratu da Autan nata bata taɓa ji a ranta zatai wani yunƙurin hanawa ba. Fatanta ma ALLAH ya daidaita komai ya canja rayuwar Nuratu ɗin su zauna lafiya da Maanal da shi kansa Ajwaad data san baya son haɗin auren nan. Kai ko Mamy gani take bata so dan haka take nuna mata a zahiri. Da yake zuciyar Oum ɗin a tsarkake take kuma sai bata taɓa bin ƙwaƙwƙwafin Mamy akan komai ba sam...

Yau ta kasance lahadi, dan haka Oum ta samu Abah da batun komawar Maanal aiki gobe idan ALLAH ya kaimu. A cewarta da zaman nan gara ta koma aikin sai ta samu nutsuwa sosai. Da farko Abah shiru yayi, dan sai ya dinga hango ai zuwa office ɗin zai saka Ajwaad yaga ya samu wata dama akan Maanal ɗin ne. Shiru ya ɗanyi na wasu sakanni, sai kuma cikin jinjina kai ya ce, “Okay zan yi tunani akan hakan”. Miƙewa Oum tayi tana masa sallama, dan har yanzu basu koma dai-dai da Abah ɗin ba. Ta dai daina fushin da take yi da shi. Da kallo kawai ya bita yana murmushi da girgiza kansa. A ransa yace (Fatete na rigima kenan) da murmushin Oum ɗin Mamy dake da shi yau ta shigo ta samesa. Koda yake tun ma bikin su AA ɗin Oum tace ta bar mata Abah ɗin har sai Maanal ta tare. Hakan ba sabon abu bane ga Oum. Dan haka kawai idan ta bushi iska sai tace ta barma Mamy Abahn na sati biyu koma na sama da hakan. Wani lokacin Abahn ne ma ke gajiya ya balbaleta da masifa yace shi bai yarda ba kamar dai yanda ya sakata kwana a gunsa dole randa yayar Mamy ta kwana a gidan. Sosai ran Mamy ya sosu da murmushin nasa, wanda tasan akan Oum ɗin ne tunda sun haɗu a waje. Tarasa ya zata raba wannan shaƙuwa da soyayyar, duk da haihuwar da tayi, da kwantar da kai tana musu bauta su duka biyun har yanzu Oum ta fita matsayi da girman iko a wajen Aliyu. Sam baya iya ɓoye ƙaunar da yake mata koda a gabanta ne ita Kamila. Baya shakkar yabon Oum ko sanya mata albarka ko yin kwatance da ayyukan alkairinta. Hira goma zaka zauna da shi zai ambata maka sunan Fateema so takwas ne kansa tsaye. Cikin takaici ta haɗiye ɓacin ranta ganin ya juyo gareta, a hankali ta maye fuskarta da sassanyan murmushi cike da makirci take tambayar fitar Oum ɗin wai taga ranta a ɓace. Ikon ALLAH sai Abah ɗin yay nauyin baki yau, dan murmushi kawai ya mata baice komai ba. A ƙasan ransa kuwa hankalinsa na'a kan Oum ɗin ne, buƙatarta yake a jikinsa ƙwarai da gaske, yana kewar sassanyan ƙamshinta da kulawarta a garesa. Badan wai Mamyn bata masa ba ita, kawai dai yana jin na Fateema a garesa special ne. ALLAH shine kaɗai yasan irin son da yake ma Fateema da ƙauna a rayuwarsa, shiyyasa yake kallon al'amarin Ajwaad da Maanal tamkar nashi da Fateema ne. Dan soyayyar yaran gaba ɗayanta tamkar gado ne daga tasu soyayyar, abinda kawai ya banbanta shine shi da Fateema jini ɗaya ne... Haushin ganin ya tafi zurfin tunanin nasa wanda Mamy tai imanin akan Oum ne yasa ta miƙe ta wuce bedroom ɗinsa. Dan tana fara ganin irin wannan signing ɗin a garesa a duk lokacin da Oum ta bar mata shi take fahimtar ya gundura da ita hankalinsa nakan matarsa. Tasha zargin kodai Oum tana musu hakan ne dama dan wani tarko nata ko shiri, amma idan ta nutsa a bincike sai ta gano sam ba hakan bane ba.. Abah ya jima kafin ya dawo daga duniyar tunanin nashi, sai sannan kuma ya farga babu Mamy. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya ɗauka wayarsa ya tashi ya fita domin kiran ɗan uwansa suyi shawara akan batun Oum ɗin na komawar Maanal aiki. Wato Uncle Mahmud.....

____________★

Kuka bana wasa ba Nurry tasha da jin batun ɗaga bikinta dana AA har sai zuwa bayan salla. Wani irin tsanar Oum da Maanal ta ƙara faɗi da kauri a zuciyarta. Nanfa ta shiga ɗaukarma kanta alwashi kala-kala na gasama Oum da Maanal aya a tafin hannunsu. Dan ta tabbatar kamar yanda taji iyayenta na faɗa makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma... Hakan ya ɗan sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta ɗan saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama ƙawayenta da abokan arziƙinta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya.....

___________★

WASHE GARI.

Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal ɗin ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA ɗin baima saka ran komawar Maanal ɗin yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a ɗakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ƙofar bedroom ɗin sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga ɗakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na haƙuri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. Ɗan nesa da shi ta zauna, sai kuma ta ɗan zamo a kujerar kaɗan cike da neman magana ta ce, “Yaya Aliy ina kwana” (haka take kiransa lokacin ƙuruciya). Hararta yay da faɗin, “A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran ɗanki zaki ce dani wani yayan gulma”. Ƙaramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce, “Kun tashi lafiya?”. “Alhamdullahi”. Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faɗin, “Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaɗin driver zai dinga kaita ba ɗanki ba. Dan bana son wata alaƙa ta haɗasu. Ki kuma gargaɗesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ƙara yawan kwanakin suspension ɗin”. Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs ɗin yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal”. Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office ɗin....

Oum ma bayan tafiyar Abah ɗaki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje ɗayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faɗi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla ƴan company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita ɗin matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?..... “Ko baki son komawa ne Baby?”. Oum ya katse mata tunani. Ƙasa tai da kan nata tana ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin ƴan kamfani ne”. Dariya sosai Oum ta sanya da faɗin, “Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki riƙe girmanki, ki ƙara ƙwazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka”. Cikin jinjina kai Maanal ta ce, “Amin”... Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haɗa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal ɗin ta koyi yanayin fitar tashi tunda na ɗan lokaci ne zasu koma fita a taren..

Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matuƙar ƙyau da haska chocolate color skin ɗinta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan ƙamshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da ɗan lips-gloss kaɗan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye ƙaramar handbag ɗinta saman table ɗin dining ɗin itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen ƙamshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matuƙar ƙyau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta ɗan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara ƙoƙarin zuba abincin a ranta tana ƙunƙunin (wayace ya sake airin kayanta) “Auta har an fito?”. Oum ta faɗa dai-dai isowar AA dining ɗin. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai ɗan bata side hug. Sai kuma a ƙasa-ƙasa ya furta, “Barka da safiya my everything”. Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da, “Ka tashi lafiya ya ƙarfin jikin?”. “Alhamdullahi Oumna, ai ɗanki ya warke sarai in sha ALLAHU ”. “Masha ALLAH haka muke fata ai Auta”. A hankali Maanal data ƙi sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuɗi da maradin hakan ta ce, “Ina kwana”. Batare daya kalleta ba shima ya ce, “Lafiya”. Daga haka ya kalla Oum a ɗan shagwaɓe ya ce, “Oum yunwa zata cinye hanji na”. Ƙaramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal ɗin dai-dai ta ɗago ta hararesa. Dan itace ke faɗar haka idan tana jin yunwa. Gira ɗaya ya ɗage mata irin (Ni ɗin kike harara?) sai ta sake murguɗa masa baki sannan ta ɗauke kanta. Ita dai Oum wurin tai ƙoƙarin bar musu tana faɗin, “Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne”. Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta ɗauke idanun nata. Tsohon minti ɗaya kafin tace, “Me zaka ci?”. Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta ɗago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya ɗago lumsassun nasa ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips ɗinta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce, “Nace mi kake so?”. Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips ɗin nasa ƙasa-ƙasa ya furta, “Ke!”...........✍️

_Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba😌😣, shine nace bara na tambayeku🫣🏃🏃🏃🏃🏃🏃._

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣

______________

Readers Also Read