Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 72

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 72

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 72: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 72. Anan Abuja ahalin Ambassador…

4,361 words

Anan Abuja ahalin Ambassador Aliyu Darma cike suke da farin cikin fara azumin da kuma kewar rashin jin AA da Maanal. Ga Mamy dai fargaba ce da damuwa cike fal a zuciyarta. A cikin ƴaƴan nan uku tafi kasancewar a fargabar al'amarin Ajwaad fiye da kowa. Yaro ne mai biyayya, amma kuma yana da taurin kai, sannan yana biyayya ne a gareta a iya abinda ya tabbatar bai saɓa shari'a ba. Ta wani gefe kuma tana tsoron kaidin mace, tare da masifaffiyar soyayyar da yakema yarinyar nan. Ta tabbatar zai iya mancewada wani gargaɗinta can, shiyyasa tafi kowa matsuwa da ƙagauta a jiran kiransa. Amma gashi har tsawon kwanaki biyu shiru kake ji, bayan duk inda Ajwaad yaje a tafiye-tafiyensa yana sauka baya rufa awanni biyar a ƙasar bai kirasu a waya ko video call ba. Amma a wannan karon sai gashi ba haka bane saboda ya tafi da mace. Macen ma yarinyar data tsana fiye da komai a ɗan tsakanin nan saboda ƙarfin abinda take gani a idanun ɗanta game da ita. Dan duk abinda kaga Ajwaad baya jin nauyin sakawa a gaba ya kalla a gaban kowa, baya shayin tattali da nuna kulawa a kansa, baya iya ɓoye feeling na farin ciki a kansa idan yana waje, baya iya riƙe miskilancin sa a kansa a gaban kowa. To lallai wannan abun ya kai ƙololuwar girma da daraja a garesa. Itafa yaron nan ya duba tsabar idonta ya sanar mata a yanzu Maanal nada power ɗin yin komai da dukiyarsa tunda matar sa ce, dan haka bazai iya cewa tabar kamfaninsa yin aiki ba. Tace ya faɗa mata ma'anar *MAWAAD* yaƙi, ita kuma a tsorace take da fassarawa bisa ga yanda zuciyarta ke hasaso mata. Shiyyasa take son ya faɗa da bakinsa, dan in har ya kasance hakane lallai za'a jisu da Ajwaad fiye ma da gidan nan... Shigowa Nuratu tana cin indomie tana magana a waya ya katse ma Mamy tunaninta. Binta tai da kallo dai-dai tana miƙo mata wayar. Ganin yanda tai wani getse-tse a gabanta babu ladabi babu risinawa irin na yaro da babba sai abin ya sosa mata rai. Amma batace komai ba ta amsa, Mamansu Nuratun ce, suka gaisa ta tambayeta ya ibadar azumi da aka fara Mamy ta amsa mata. Cike da siyasa Maman Saheeba ta ce, “Yaya ƴan tafiya an sauka lafiya kuwa?”. Sai da Mamy ta ɗan nisa kafin ta ce, “To zamu iya cewa haka, dan muma bamu jisa ba dai har yanzu bai kira ba”. Ɗan jimm Maman Saheeba tai, sai kuma daga can tace, “Hummm ke ko Aunty ai ya tafi da mace sai abinda muka gani kam. Kefa da kanki kike sanar min yaron nan duk inda zaije baya rufa awanni zai kiraku yace ya sauka. Amma wannan karon kinji shiru ƴar iskar ta hana shi kenan, koda yake keko ai bata yar a ƙasa ba tunda nn Asiya tasha kuma rainon Fatimah ce. To ALLAH dai ya jishemu alkairi kada a dawo ana ƴan amaye-amaye, tunda ta samu dama yanzu daga ita sai shi ai bazata yarda su raba ɗaki ba, sannan duk yanda zata hillacesa ya bata abinda ta saba samu a titi ai yi zatai”. Wani irin tiririn zafi ne ya turniƙe zuciyar Mamy, muryarta har rawa take dan fushi wajen faɗin, “Aiko dana tabbatar masa nice na ɗauka cikinsa wata tara nai wahalliyar naƙuda kuma. Ni na rasa yanda zan yi da yaron nan Nana, nafi shan wahala a ɗaukar cikinsa fiye da kowa, ki duba yayin haihuwarsa kamar bazan rayu ba jini ya ɓalle min, inaga tunda cikin Ajwaad ya kai wata biyar a jikina na daina barcin kirki har sai da na haifesa. ALLAH kuma ya ƙwalla fin sonshi a rai fiye da sauran amma sam yaron nan baya dubawa.” “Ta ina zai duba kuwa Aunty, gashi nan yanda kika sha wahalar ɗaukar cikin nashi da haihuwa haka kike shan wahalarsa a yanzu, ai ke dai bar hatsabibin yaro kinji. Irinsu ai sune zakka a cikin ƴaƴan da ake cewa. Dan basai yaro na rashin jin shaye-shaye ko makamancin hakan yake zama zakka ba a cikin ƴaƴa. Amma koni taƙadarancin Ajwaad na ban tsoro, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai shegiyar matar nan ta gefenki data ƙara busar masa da zuciya baya kallon kowa sai ita, baya jin maganar kowa sai ita. Ko tafiyar nan bana raba ɗayan biyu itace ta shirya musu ita tunda Yaya ya hana ƴar gwal ɗinta ta tare, kinga in akai haka ai za'a samu abinda ake so. Shima Yayan da yake a ƙarƙashin umarninta yake ya kasa duba gaskiya ya hana. Ai wlhy shi zaki takurawa ya dame su da waya da gargaɗi, idan ma ta kama kwana huɗu su dawo gida”. Sosai maganganun Maman Saheeba ke shigar Mamy, jin abinda tace akan Abah kuma sai ta nisa, muryarta cike da damuwa tace, “Nana maganar Abansu ma a barta, kin dai san halinsa ba'a cika masa gari kamar tuwon gero yake sai yay nauyi. Tsartar jaraba ce da shi, dan halinsa kaf sune a jikin Ajwaad, sauran ƴan uwansa wasu abubuwa kawai suka ɗakko. Amma wlhy Ajwaad bai bar komai na mahaifinsu ba. Da haka cire ma batun shi na sashi a azalzala musu zai harbo jirgina ne da wuri, duk abubuwan dake faruwa badan na kasance mai takatsantsan ba da tuni ba wannan maganar akeyi ba ai. Ki dai bari muyi wani tunanin daban, sannan yanzu dakonsa nake ya kira waya na samu number ɗin komai mai sauƙi ne ai”. Badan Maman Saheeba taso ba ta ce, “Hakane kuma Aunty. Mu barsa to ya kira a samu number ɗib sai musan hanyar kamawar. Bara naje na ɗan kwanta naji azumin farkon kamar zai ɗan yi duka”. Ƙaramar dariya Mamy tayi, tare da faɗin, “Ke dai raguwa ce dai”. A tare yanzu sukai dariyar, Maman Saheeba tai mata sallama suka yanke wayar. Kallonta ta maida ga Nuratu, sai kuma ta ɗauke kanta tana mai girgiza kai kawai. Tunda asuba data tasheta yin sahur tace ita bazatai azumi ba jini yazo mata......

★A ɓangaren Oum kam kewar su Autanta ta isheta, amma kasancewar Najma na rage mata. Dan barcinsu ma su suka sha sai kusan sha ɗaya suka tashi. Sannan ne suka fito falo Najma ta saka musu *SUNNAH TV* sukai zaman kallon tafsir, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fara fita nan cikin anguwar inda malam keyin na mata da safe, na maza da yamma. Sallar azhar ce ta tashe su, bayan sunyi suka ɗan kwanta, kusan ƙarfe uku Najma ta tashi ta fito saboda kiran wayarta da Fawzan yayi cewar ya dawo gida tun azhar, gashi a falon Oum tun ɗazu baiji motsinsu ba. Koda ta fito ta gaisheshi zama tayi suna kallon tafsir, sai hira jefi-jefi da bata shafi komai ba. A haka Babban Yaya ya shigo shima, da'alama kuma ya ɗan jima da dawo gida, dama lokacin azumi basa daɗewa a wajen aiki. AA ne kawai idan bai gadama ba sai gab da shan ruwa zakaga ya shigo. Itama dai Oum fitowa tayi. Tana zama babu jimawa su Inte suna shigo dan tambayar miya kamata a rage na aiki, dan duk azumi gaba ɗaya nan sashen Oum kowa ke zuwa ai aiki, a kuma shirya komai a rumfar bunu dake can compound anan ake buɗa baki ko a tsakiyar gida, ana kammalawa su fice sallar asham anan masallacin kusa da su, inda harda AA a masu jan sallar, dan kuwa babban ɗalibi ne na imam ɗin massalacin. AA akwai ilimin addini, kuma har yanzu akan nema yake bai zauna ba. Kawai dai idan ka gansa a harkar neman kuɗi saika ɗauka bokon kawai aka sani. Amma Alhamdullah anan wajen dukansu Oum batai wasa ba a kansu, kowa kansa cike yake da ilimin addini tunda hatta babban yaya har yanzu bai daina zama gaban malamai ɗaukar karatu ba shiyyasa suke a nushe (KU SAN BOKO BA ILIMIN ADDINI TAMKAR NAMAN KAZA NE A DAFE BA'A WANKE ƘARNI BA🥱) ...

Bayan sallar la'asar badan Mamy taso ba ta tattaro su Saheeba zuwa sashen Oum. Dan cike take da jin zafin Oum ɗin. Oho ita baiwar ALLAH bama ta hankalta da yanayin Mamyn ba, kawai abinda ta kawo a ranta azumi ne dai na farko da kowa sai ya ɗanɗana kafin a saba. Su duka sun kasance a kitchen harda masu aiki. Abah da Babban Yaya da Fawzan sai Naufal suna massallaci daga Asr basu dawo ba sukai zaman jin tafsir. Abinci mai rai da motsi suka shirya ana ƴar hira sama-sama. Wajen biyar na yamma sai ga tawagar ƴan hutu daga Kano sun iso. Abah ne kawai yasan da zuwansu. Tuni fuskar Mamy ta sake tsukewa, yayinda ta Oum ta yalwatu da farin cikin ganin ƴaƴan ƴan uwanta. Domin kuwa samarin yara ne biyar, na Uncle Mahmud biyu, sai na Uncle Modibbo ɗaya da mace budurwa ɗaya, sai ɗaya na Uncle Hussain, ɗaya na Uncle Hassan. Sai sauran ƴammata uku, Autar su Nuwaira, sai biyu da suka kasance jikoki suma ta ɓangaren Abbah mahaifin su Oum. Najma ma dai sosai take a farin ciki. Tuni aka buɗe ɗakunan ƙasa na ɓangaren Oum, samarin zasu zauna nan, su dukasu kusan sa'anni ne dan duk bazasu wuce 20, 21, 22, ba, su kuma ƴammatan wasu sun girmi wasu, akwai sa'annin Najma biyu, biyun kuma bazasu wuce 15 ba. A ɗakin Najma su suka haɗe, duk da Oum tace ya musu kaɗan a sake buɗe wani ɗakin sukace a'a. Samarin kuwa biyu suka rabu. Dan sunce akwai Hashim daya rage shima yana zuwa daga Sokoto ɗan ɗan uwan Oum ne shima dai ta ɓangaren Abbah. Shine wanda su AA suka taɓa zuwa gidansa lokacin da zasu je Giro. ALLAH yaso su Oum da yawa sukai abincin, dan dama Abah nata jaddada musu ayi abinci sosai akwai masu ci. Da suka tambayi su wanene yace sudai su ƙara kawai. Ashe yaran ne a hanya. Gida kam dai Alhmdllh, sai hakan ya sake ragema Oum kewar su Maanal duk da dai sunan manne a zuciyarta a dukkan motsinta. Da taimakon yaran aka shinfiɗa manyan carpet da dama ana tanadarsu ne dan irin wannan lokacin ne kawai. A compound aka baza su, sannan aka shiga fitar da nau'o'in abinci da suka shirya abinka da mutane da yawa. Dandanan wajen yay ƙyau daka kalla kasan a lallai Ramadan ya kama. Yaran sunata ɗauka a waya abinka da ƴan ɗore-ɗoren social media. Da farko Nuratu nata ɗauke-ɗauken kai, sai dai fa tasha jinin jikinta dan ita kanta tasan yaran a goge suke da ilimi sannan gidan iyayensu akwai kuɗi suma, dan sanin kanta ne ALLAH yayma zuri'ar Darma arziƙi tun na tushe daga iyaye. Hakama family ɗin su Oum ta ɓangaren Abbah, K. Kura yana ɗaya daga cikin manyan likitoci a ƙasar Najeriya ga shi kuma ɗan kasuwa, mahaifinsa shima dai ya tara ya bar musu. Abinda ya sosa mata zuciya yanda yaran suka wani watsar da ita amma su kansu a haɗe dan kamar su cinye Najma, haka ma sun janye Anum a cikinsu su adole ga ƴan haɗin kan dangi. Humm tasha jin Saheeba da Mamy suna faɗin haɗin kan Darma Family da masifar son juna da suke da shi, bata tabbatar ba sai a yau ganin ƴan yaran nan yanda suke 5&6 matuƙa. Gasu a nutse babu rawar kai sam a tare da su. A haka su Abah suka shigo bayan sallar magriba, lokacin kowa yaci dabino yasha ruwa sanata yin sallar magrib. Wani irin farin ciki a bayyane kowa ya gani a fuskar Aba, Babban Yaya, Fawzan. Dan tuni yaran sun wani zagayesu. Duk rashin fara'a da yawan magana ta Babban Yaya kamar zai cinye yaran a bayyane dan so. Kai wannan abu na kona ran Mamy, har mamakin irin haɗin kan wannan family take yi..... Abin sha'awa abin birgewa kowa ya nema wajen zama aka fara buɗa baki, maza na nan ɓangaren mata anan ɓangaren abinci a tsakkiya. Kuma duka harda masu aikin gidan ne, harda wanda bama musulman ba duk an jawosu. Wannan itace ainahin ɗabi'ar wannan gida, shiyyasa a cikin masu aikinsu mutum biyu sun taɓa musulunta a bisa jin daɗin wannan yanayin, dan haka suka kyautata rayuwarsu a yanzu haka suna zumunci da su sosai kuma suna zuwa gidan. Bayan an karya da gwargwadon abinda ya sauwaƙa marasa alwala suka tashi suka sabunta, masu ita suka kimtsa aka fice sallar asham anan masallacin dake kusa dasu dan jikin gidan su Hajiya Shuwa yake. Su kansu anan suka iske su Hajiya Shuwa suma sun fito. Massalacin upstairs ne. Ƙasa maza sama mata, kusan ƴan street ɗin duk anan suke salla, musamman da azumi cika yake tab, wani ma sai a lokacin yake tuna wanene makwafcinsa.......✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣9️⃣

______________

........A ɓangaren ƴan chaina kam a yau su kuma zasu ɗauki nasu azumin. Dan kammala yin sahur ɗin Maanal da AA kenan. Yanda ta takura masa da batun kiran ƴan Nigeria ganin da sauran lokacin kammala sahur ma balle ai batun sallar asubahi yay zaman kiransu video call dan yasan a yanzu darene an dawo sallar asham acan. Hakanne kuwa, dan shigowar su Oum ɗin kenan sun sake zama anan compound masu ƙara abinci na shiri masu hira nayi saƙo ya shigoma babban Yaya a waya. Murmushi yayi tare da miƙama Fawzan dake kusa da shi waya. Fawzan na gama karantawa ya wani kwashe da dariya. Duk kallonsa kowa yayi, baima jira kowa ya tambayesa ba ya miƙe yana faɗin, “Oum ki shirya autanki zai kira video call yanzu”. Aiko tuni fuskar Oum ta washe da sabuwar fara'a, yayinda Mamy tai saurin duban Fawzan. Suko yaran suka shiga ɗoki zasu ga Yaya AA. Dan tunda suka iso suke tambayar yana ina. AA nada farin jiki ga yaran family ɗin, dan duk da bai sakar musu fuska indai suka ce suna buƙatar abu ko bashi suka tambaya ba in dai yaji zai yi musu abin yace wancan ya barsa. Sannan in dai sukai irin wannan zuwa hutun zakaga yana musu saye-saye na abubuwa daban-daban. Ranar salla ko zai sa a kaisu duk inda suke so koma shi ya kaisu. Nuratu kam jikinta har rawa yake, dan tunda Babban Yaya yaje ya ɗakko laptop a sashensa ya dawo compound ɗin ji take kamar taje ta fisge system ɗin daga hannunsa ta hana kowa ganin AA sai ita kawai. Sai dai babu wannan damar. Ita kanta Mamy abinda take rayawa a tata zuciyar itama kenan. Cike da girmamawa Babban Yaya yazo ya ajiye laptop ɗin a gaban Abah, Mamy da Oum na gefe-da-gefensa daman alamar sun gama shiryawa. Kasa haƙuri da yaran sukai duk sai sukazo suka zagayesu ta baya. Su dai su Saheeba basu motsa ba, amma hankalinsu na wajen, musamman Nibras da Nuratu ji suke kamar su fisge laptop ɗin. Tar-tar AA ya bayyana a screen ɗin, hakama su Abah sun bayyana masa fes shima. Wani irin bugawa ƙirjin Mamy yayi, dan haka kawai sai zuciyarta ta kissima mata ganin AA ɗin na wani walƙiyar mutumin daya sha angwanci. Abah da Oum kam murmushin da AA ɗin ya ɗan sakin musu suka mayar masa. Cikin nutsuwar nan tasa da rashin hayaniya ya furta, “Assalamu alaikum. Abah, Oum, Mamy barkanku da shan ruwa”. A tare Abah da Oum suka amsa masa, sai kuma ya shiga gaishesu, dai-dai nan Maanal dake cin abinci a gefensa ta matso jin ya ambaci sunan su Abah ɗin. Dan ita da farko a tunaninta ma aiki zai yi. Ganin su Oum da tayi sai tai saurin komawa baya dan abin yazo mata a bazata. Dariya Abah da Oum suka sanya, shima AA dai murmushi yayi, kafin ya furta, “Tun jiya fa take rigima a kiraku a kiraku, ni kuma ban samu zama ba saboda ɗan fita da mukayi shopping”. Sosai murmushin Abah ya sake faɗaɗa, cike da tsokana yace, “Haba Babyn Oum mune kuma ake ɓoye mawa, common zo na ganki”. Sosai kunya ta ƙara rufe Maanal, ta matso kusa da AA kanta a ƙasa, shiko yaƙi ya ɗan gyara ta samu ta zauna yanda ba sai ta raɓu da jikinsa ba. A haka ta gaishesu tare da yi musu barka da shan ruwa. Oum ta ce, “Naga takaina ni Fateema, Baby wannan boye-boyen fuskar na miye?”. Yanzu ko AA dariya yayi kaɗan, hakan yasa Maanal mintsininsa ta yanda su Oum bazasu gani ba. Fuska ya ɓata yana kallon Oum, “Oum kinga ta mintsine ni ba, na rama kuma Abanta yace na masa ba daidai ba”. Cikin dariya Oum ta ce, “Gaskiyarka Auta. Aba kama ƴarka magana ta kiyaye mu”. Murmushi Abah yayi, ransa fes, Mamy dai wani kalar kallo take ma AA da shi kaɗan yasan ma'anarsa, dan haka ma ya ɗan rage kallon sashen da take. Hira Abah ya dinga jan Maanal da ita, tun tana sinne kai harta ware tana basu labarin Chaina shi da Oum. Yanda take yi ɗin sosai farin ciki ya mamaye zuciyar Oum da Abah, yayinda AA ya zama ɗan kallo kawai gashi tana a jikinsa batare data farga ba. Tsaguwar da ƴan hutunsu sukai yasa suka haƙura aka miƙama ƴammatan dake kusa da Oum. Wani irin waro idanu Maanal tayi na mamakin ganin Najma, Meeno, Maimoon, Jiddo, da Lailah, sauran ƙananun bata ganesu ba. Yanda ta zano sunan kowa babu mantawa ya sakasu a farin ciki sosai. Shi kansa AA sai yaji daɗi, dan son ƴan uwansu a cikin jininsu yake. A dake AA da yaga ko takansa basu bi ba ya ce, “Baku iya gaisuwa ba ko? Auntynku kaɗai kuka sani”. Ai a tare suka shiga faɗin, “A'a Yaya kayi haƙuri!” sai kuma suka shiga gaishe shi da girmamawa. Ɗan mintsininsa Maanal tayi ƙasa-ƙasa tace, “Jealousy”. Kaɗan ya murmusa yana wani kallonta a ƙasan ido. Tasan saboda yaran ya wani kame, sai taji ya bata dariya. Dan AA akwai tsare girma. Daƙyar suka miƙama samarin suma, a mamakin AA suma duk Manal ta ganesu, dan babu wanda bata kira sunansa ba, tafa yi mugun sanin ƴan family ɗin Darma ɗin nan dan haihuwarta ne kawai ba'ai a cikinsu ba. Suma da ƙyar suka iya daina ma AA surutu dan sunata roƙonsa su dawo suna missing ɗinsa, sannan kowa yana lissafa masa abinda za'a saye masa. Lokacin da laptop ɗin takai gaban Nuratu, Nibras da Saheeba sai da sukai wani ɗan shock. Gashi hakan yayi dai-dai da AA ya ɗan duƙo a jikin Maanal yana mata magana a kunne, ita kuma ta irin juyawa da saurin nan ta saka yatsarta a saman lips ɗinsa alamar yay shiru. Shi kuma batare daya lura an ajiye laptop ɗin a gaban wasu ba dan ita tama juya baya tunda shi take fuskanta ya kama hannun nata ya tura yatsar nata a cikin bakinsa kai kace wani lollipop ya samu. Da sauri ta fisge hannun tana wata ƴar dariya da kai masa mintsini shi kuma yana murmushi da ƙoƙarin riƙe hannun nata zai maida a bakin. A bazata tana ƙoƙarin ƙwacewa da juyowa a lokaci guda saboda tsoron kar wani ya gansu idonta ya sauka a kansu duk kamar sunyi sumar zaune. Ba shiri ta ankarar da shi ta hanyar faɗin, “Besty su aunty fa”. Sai lokacin ALLAH ya bashi ikon ganin nasu, maimakon ya saketa sai ya basar kawai yama sake mannata da ƙirijinsa hannun nata dai da take son ƙwacewa bai sakin ba ya dai haƙura da sakawa a bakin. Dole ta haƙura dan tasan ba sakin zai ba. A haka ta shiga gaishesu, Saheeba ce kawai ta iya amsawa da ƙyar, Nuratu kam a bazata sai hawaye, dan numfashinta har ja yake kamar zai fice a ƙirjinta, sai ma ta miƙe tabar wajen kowa ya bita da kallo musamman sauran da basu san abinda ke faruwa ba, Nibras kam hannunta sai rawa yake tana ƙoƙarin riƙesa da ɗayan. A dake AA ya amsa gaisuwar Saheeba. Sai itama Nibras ɗin ta shiga gaisheshi muryarta na ƙoƙarin ƙwacewa tana riƙota da ƙyar. Maimakon ya amsawa Nibras gaisuwar a wani irin daƙile ya furta, “Ita matata laifi ta miki kika ƙi amsa tata gaisuwar?”. Kanta ta girgiza da dauri. Cikin zaro ido Maanal ta juya tana kallonsa tare da ɗamƙe rigarsa, irin (miye haka kake yi ɗin nan) shiko yaƙi kallonta. Dole ta juya tana amsa gaisuwar da Nibras take mata fuskarta da murmushi dan harga ALLAH bata ji daɗin abinda AA ɗin yay ba. Dai-dai nan Yaya Fawzan yazo ya ɗauke laptop ɗin daga gabansu. Ya wani ware idanu da faɗin, “Inye kaga amarya da ango”. Ai ba shiri Maanal da maganar ta sata jin kunya tai saurin duƙewa, ƙoƙarin kamota AA yayi ta zille tama tashi gaba ɗaya. Tana jiyo dariyar Fawzan cike da shaƙiyanci. A gado ta naɗe bata sake zuwa wajen ba balle gaida Yaya F. dan tasan halinsa na tsokana, yanzu haka ma tana jiyo yanda ya saka AA a gaba shi kuma ya kasa bashi amsa.....

Zamansa a kusa da ita bayan ya kammala wayar ya sakata ɗagowa ta kallesa, gira ɗaya ya ɗan ɗage mata yana wani ƙanƙance idanu. Idannunta ta kawar, tana ɗan tura baki gaba. Murmushi ya ɗanyi tare da ɗan taɓe baki, sai kuma cikin taushin sauti ya ce, “Kinga Besty zo kiji wata magana”. Shiru kamar bazata tashi ba, sai kuma ta yunƙura a hankali zata zauna. Kamota yay ya kwantar a jikinsa, sai taji tsigar jikinta na tashi, ga wata kunya mai kassara jiki. Agogo ta kalla, gudun karsu shiga lokacin gama sahur. Tsaf ya lura da yanayin nata, sai yay ɗan murmushi a zuciyarsa. A fili ya furta, “Kwantar da hankalinki, awa kusan ɗaya ce damu gaba”. Hannu tasa ta rufe fuskarta kawai. Shi ya san tun Maanal na yarinya ta musamman ce, hakan yasa ɗabi'unta da yawa suke sakashi kallon mata da yawa a basu iya komai ba. Ganin yanda ta rufe ido ya sashi kai yatsarsa manuniya a kansu ya fara sosa mata samansu. Dole ta buɗe idanun a hankali, suna shiga cikin nashi tai ƙoƙarin janye wa amma sai ya hana hakan. Kaɗan yaja mata hanci tare da faɗin, “Yarinyar nan ke da kunyar nan taki ko......” Kauda fuskarta tai tana murmushi. Shima sai ya ɗan murmusa hannunsa riƙe da fuskrta cikin raɗa ya furta, “Na tambayeki wani abu?”. Kanta ta jinjina masa kawai. “Mi doctor yace miki jiya a asibiti?”. Ai da gudu tai ƙoƙarin tashi a jikinsa amma ya riƙeta, magana tai ƙoƙarin yi kamar zatai kuka yace, “Relax! Tunda baƙya son na sani. Amma kin yarda ni na faɗa miki wata magana?”. Shiru kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta jinjina kai. Hannunta da take matsewa waje guda ya kamo cikin nashi, cike da lallashi da son kwantarta mata da hankali ya cigaba da magana da sanyin murya da tausasa lafazi. “Besty! Ina son ki kwantar da hankalinki tsakanina dake. Nasan akwai abubuwa da yawa da kike buƙatar ji daga gareni amma ban faɗa ba, nima akwai wanda nake buƙatar son ji daga gareki amma ban tambaya ba. Lokaci nake jira, akwai gaɓar da zamu zo wannan matakin ne in sha ALLAHU. Abu na biyu nasan a baya bamu taɓa kallon kammu a wannan matsayin ba, ko nace daga ɓangarenki, dan ni dai a gareni wannan shine burin rayuwata na farko daya fara ginuwa tun ma ban fahimci wanene ni ba.....” Karo na farko Maanal ta kallesa, wani irin lumshe mata idanu yayi ya sake buɗewa. “Kada kiyi mamaki, kada kuma ki tambaya, kada ki damu da son sani game da jin hakan domin ba yanzu ba. Abinda nake so daga gareki a yanzu kawai haɗin kai, kwantar da hankali, ki kwantar da hankalinki dani, bazan taɓa aikata wani abu a gareki ba bada yardarki ba Maanal! Duk yanda zan tsinta kaina a matsuwa ta buƙatar jiki kota rayuwa ki sani ke kinfi hakan muhimmancin da bazan fifitasu a kanki ba. Domin su na wuccin gadi ne, zasu iya samuwa su wuce sai wani lokaci a buƙace su, ke kuma ta har abada ce, akoda yaushe kece kaɗai Ajwaad, kece kaɗai nake iya buɗema zuciyata, ke ce kaɗai nake iya buɗema damuwa ta, kece ƙawa! Kece ƙanwa! Kece aboki! Kece aminiya! Kece abokiyar dariya! Kece abokiyar magana! Kece abokiyar kuka! Kece abokiyar karatu! Kece abokiyar sirri! Ko duk kin manta? Kin manta haka saboda nisa da ratar da ƙaddara ta bamu ne? Kin mance haka saboda jarabawa da UBANGIJINMU yay mana dan yaga ƙarfin imaninmu? Kin manta saboda a yanzu tunaninki na baki komawarki mace matancin naki ne kawai zan iya buƙata? Noo Manaal! Noooo! Wannan Ajwaad ɗin na nan a naki tun na waccan rayuwar, bakuma zai taɓa canjawa daga hakan ba domin a matsayin da dama na gina kenan tun fil azal. Ki sani tubalin ginin da kayan ginin an samar da su ne daga himmar aiki mai ƙarfafa ƙwanji tun daga ƙarƙashin zuciya da bigire na fitowar TSIRRAI daga HUKUNCIN UBANGIJI. Wallahil azim inda zaki ce Ajwaad bazan taɓa baka kaina ba mu rayu a haka yanda muke ni mai riƙe miki wannan ALƘAWARIN ne dan ba wannan nake kallo ake ɗin ba, ke! Ke! Ɗin nake kallo a matsayin Ke! Kawai Maanal.....”✍️

Hummmmmmm

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣0️⃣

______________

Readers Also Read