Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 74

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 74

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 74: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 74. ........Lokacin da suka iso hotel…

4,265 words

........Lokacin da suka iso hotel su AS tuni sun shige, AA ya kalla Maanal dake barci sosai, sai yaji ta bashi tausayi. Ita da ya sani da ragwantar azumi, koda yake yanzu an girma maybe ta daina tunda yaga yau batai raki ba, amma a da duk randa aka kai azumin farko tofa Maanal da kuka take kaishi. Murmushi yayi komai na dawo masa a zuciya kamar film. Baya son takurawa Mr Li, da zasu cigaba da zama a motar ne harta tashi, to yakamata shima a bashi nashi Freedom ɗin yaje ga iyalansa. A hankali AA ya kamata ya kwantar kamar wata ƙwai, kafin ya fita a motar, ta side ɗin da take ya zagaya, ya ɗan duƙo cikin dabara ya kamata tare da juya bayansa ya ɗaurata, a duƙen ya miƙe tana a bayansa har tana gyara kwanci ya miƙe tsaye da ƙyau riƙe da ƙafafunta, ita ko ta sake sarƙe hannayenta a wuyansa ta lafe. Da sauri Mr Li ya tattaro musu kayayyakinsu ya biyosu da shi, a haka ya shiga da ita cikin hotel ɗin, rayuwa ce irin ta ba ruwan wani da wani babu wanda suka zamewa abin kallo, kowa harkar gabansa yake. A haka ya shiga elevator da ita. A bazata ya fito daga elevator ɗin yaci karo da CMO da HOD da alama fita zasuyi, kicin-kicin ya sake yi da fuska, suma duk sai sukai ƙasa da kawuna like bama su ganshi ba. Ko kallonsu baiyi ba balle ya nuna ya ma sansu yay wucewarsa Mr Li biye da shi. Aiko suka juya suna kallonsu cike da mamaki. Eh lallai mace dabance, mace sarauniya ce, mace duniya ce. In ba hakana CEO ne goye da mace, kai lallai babbar magana, al'amarin kamar wani film. Oho AA baima san anai ba, dan yayi gaba kaɗan can ma ya hango CFO tana waya, ɗauke kansa yay dan ta tsaya tsai daga maganar da take kamar wadda ta suma. Shi ko ya saka card ƙofa ta buɗe yay ciki. Mr Li ya saka masa kayan ta ciki yana daga waje ya juya, shi kuma ya saka ƙafa ya rufe ƙofar abinsa sannan ya nufi gadon ya sauke Maanal dake barci bil haƙƙi alamar ta gaji sosai. Takalma ta ya zare mata, ya warware veil ɗin ma ya cire.. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta gyara kwanciya. Tsai ya ɗanyi yana kallonta na kusan minti ɗaya, kafin ya sauke ajiyar numfashi ya sake kai hannu ya fara buɗe botiran rigarta, ya ɓalle fin biyar kamar wadda aka ankarar ta farka, wani kalar cafke masa hannu tayi tana buɗe idanu da ƙyau irin na (lafiya kuwa?) shima sai ya zuba mata nasa a wani kalar kasalance, sai kuma ya shiga jansu ƙasa ya sauke akan hannayen nasu, ita kuma sai tai tunanin jikinta yake kallo ta inda ya buɗe botiran, hannun ta saki da sauri ta kama rigar ta cikuykuye a cikin hannunta ta rufe wajen ruf.... Sai kawai ya samu kansa da sakin wani kalar lalataccen murmushi. Baki ta tura irin na jin haushin dan mi zai mata dariya. Fahimtar hakan sai ya sake sakin murmushin tare da matsar da fuskarsa gab da tata suna busama juna numfashi. “Idan abinda kike tsoron zanyi ai idanuna a cikin naki zanyi ba kina barci ba fa, dan haka karki damu kanki saura ƙiris”. Fuskarsa ta ɗan ture ta juya masa baya, sai ya sake yin murmushi ya leƙa fuskar ta bayanta. Cike da son ƙureta ya ce, “Please ki tayani wanka mana na gaji sosai My EverBloom!”. Gaba ɗaya ji Maanal tai tama daburce ta rasa ina zata saka kanta. Yanda tai ɗin ya matuƙar bashi dariya, tsabar son ya sake ƙureta sai ya riƙota yana faɗin, “Okay! Okay shike nan na haƙura har sai randa aka kawo min ke har ɗakin barcina a lulluɓe like kowace sarauniyar amarya, ki kasance cikin shiri dan babu batun ɗaga ƙafa ranar fa, zan zama kurma ne, sannan makaho na haƙiƙa...” Ita dai tuni ta cusa kanta a tsakiyar ƙafafunta ne tana jin kamar gadon ya rabe biyu kawai ta shige ciki ya maida ya rufe da ita. Shima fahimtar ya gama kaita maƙura ya sashi duƙawa ya sumbaci wuyanta ta gefen kunnenta, wani kalar girgiza jikinta yayi dan har tsakiyar kai taji sumbar nan, sai kawai ya miƙewa yana ƴar dariyan shaƙiyanci yabar wajen. Kaya ya fara cirewa dan wanka shi yafi buƙata fiye da komai a yanzu. Ita dai tana rufe a wajen har sai da ya shige sannan ta koma ta buɗe iya fuskarta tabar jikin kawai a rufe, sai dai ta wani ɓata fuska abin dariya.....

___________★

Cikin dauriya da son nuna juriya Huznah ta tashi da azumi, duk da da farko Sageer yace mata idan bazata iya ba ta barshi. Ta dage akan zata iya, jin tace zata iya shima ya sameta yako more da asubar sannan sukai sahur, haushin abinda yay matan ya sata jin sake tsanar cikin. Tana samu ya fita sallar asuba ta saci wayarsa ƙarama ta ɓoye. Koda ya dawo sai ya kwanta a ɗayan ɗakin dan hakan shine samun lafiyarsa. Ba ƙaramin daɗi hakan yayma Huznah ba. Da wannan damar ta saka number Yaseerah cike da fatan samunta, dan bata son kiran ƙannenta wani yaji. Ɗagawa Yaseerah dake cikin ɓacin ran faɗan da suka sha da Abdull akan cikin data samu tayi. Jin Huznah yasata jin mamaki, tace, “Lallai Huznah, shike nan daga yin aure kin manta kowa”. “Humm Yaseerah bazaki gane ba, yanzu ba lokacin kace nace bane tura min numban Mama dan ALLAH”. Da mamaki Yaseerah tace, “Kai kece baki da number ɗin Mama kuma?”. Cikin rawar murya Huznah ta ce, “Ba rasawa nayi ba Yaseerah ƙwace wayata yayi, ni kuma ina son yin waya da wani a cikinsu ko ita ko Ummi, amma na gwada layin Ummi yafi sau a ƙirga bana samu, shiyyasa nake son kiran Mama dan koma minene nasan zata sani”. Sosai al'amarin ya daki zuciyar Yaseerah, amma Huznah ta riga tace mata bata son magana mai tsaho, dan haka ta ce, “Okay bara na tura miki. Amma idan kin gama da Maman dan ALLAH kimin ko flashing ne”. “Ba damuwa”. Kawai Huznah ta faɗa tana yanke wayar. Ko minti ɗaya kuwa ba'a rufa ba sai ga saƙon Yaseerah, jikin Huznah na rawa ta kwashe number a wani littafi ta goge daga massage sannan tai past ɗin wanda tai copy daga massage tai dailing tana shigewa toilet bayan ta murzama ƙofar ɗakin key. Toilet ɗin ma kullesa tayi. Dai-dai nan Maman Yaseerah ta ɗaga kamar a barci take. Kafin ma ta tambayi waye Huznah ta ce, “Mama nice Huznah”. Da sauri Maman Yaseerah ta tashi zaune, ta ce, “Huznah ina kika shige inata neman layinki?”. Kuka Huznah ta sanya mata, kafin ta fara bata labarin komai dake faruwa, tun daga ƙwace wayarta da yayi har zuwa satan tashi da take yi tana kiran Hajiya Basariyya bata samu da maganar ciki daya bayyana jiya. Ba ƙaramar sumar zaune Maman Yaseerah tayi ba, ta ce, “Ciki kuma Huznah yaya akai haka? Sake yarda kikai kika bashi kanki?”. “Mama ya zanyi? Idan ma ban yarda ba ta ƙarfi yake bina wlhy. Wlhy idan naji ko motsinsa ƴan hanjin cikina har kaɗawa suke. Sageer mugune sosai Maama, bar ganinsa shiru-shiru baida kirki da imani”. Ajiyar zuciya Maman Yaseerah ta sauke. Cike da lallashi ta ce, “It's okay! Kukan ya isa haka. Ai idan yasan wata bai san wata ba dan ubansa. Mamanki na katsina ne gidan kawunta.....” Cikin katseta Huznah ta ce, “Na shiga uku Kawu Manu?”. “Shifa! Yayanta ne ya kaita da tsiya-tsiya, amma ki kwantar da hankalinki jiya ta samu wayar yarinyar maƙwafta ta kirani, ta kuma tabbatar min bazata wuce nan da sati ba zata dawo. Kema ki kwantar da hankalinki irin ƴan iskan yaran nan su Sageer ta siyasa ake musu. Ciki dai bazaki haifesa ba dan uban shi, ki cigaba da kwantar masa da kai har ALLAH ya kaimu ya barki zuwa salla zamu san yanda zamuyi da shi, kema kuma kinzo kenan”. Wata wawuyar ajiyar zuciya Huznah ta sauke, ranta fes tace Nagode sosai Mama, ALLAH ya saka miki da alkairi. In sha ALLAHU zan dinga kiranki idan na samu sarari, amma karda ki kira dan zai iya ganewa”. “Babu damuwa in sha ALLAHU”. Daga haka sukai sallama Huznah ta sauke wayar tana murmushi. Gaba ɗaya sai taji kamar an zare mata dukkan damuwar ta ne. Bayin ta buɗe ta fito tana goge kiran da tayi, taje ta cire key ɗin data sakama ƙofar sannan ta koma saman gado ta kwanta.......

___________★

Gab da ƙarasawa lokacin sahur AA ya farka cikin matsanancin yanayi, wannan abune daya saba fuskanta a rayuwarsa tun a farkon girma, amma baya masa tsamari mai wahala kamar na tsakanin nan, musamman kwanaki biyun nan da kusancinsa da Maanal ya zama dab, suna kwana gado ɗaya, su yini tare cikin farin ciki, ta ɗan saki jiki da shi kuma duk da ba kamar asalin yanda suke a baya ba. Yasan duk yanda Maanal zata kai ga tsanarsa, da jin zafinsa dole ne shaƙuwarsu ta baya ta dinga yin tasiri a gareta da karya lagonta koda lokaci-lokaci ne. Balle kuma yarinya ce ƙarama ita har yanzu, zuciyarta bata gama ƙwarin iya riƙe abu ba irin da tsauri ɗin nan, ya taɓa ji a wani hasashen masana a shekarun ƙuruciya ɗan adam yana da rangwamen tasirantar da damuwa ko ɓacin rai wajen girmama shi a zuciya, ko ɓatama mutum rai kayi ko cutar da shi a shekarun ƙuruciya irin daga 15years na fara fahimtar kai da kai zuwa irin 26 to 7 haka wasu ma har 30 zakaga yana da sauƙin zafafa al'amarin, wani ma cikin ƙanƙanin lokaci yake hucewa abin ya wuce a ransa, wani kuma daka dawo ƙyautata masa ko lallashinsa shike nan ya bar abin koda zai dinga tunawa lokaci-lokaci ransa ya ɓaci. Ko ga rayuwar aure mafi yawan mata a shekarun farkon aure basu cika girmama wasu ƙuntatawa na miji ba, watama mijin ne zai mata laifi idan taga yayi fushi zata bashi haƙuri harma ta durƙusa. Amma da an shiga shekarun hankali 30+ in sha ALLAHU ita zata tafka masa tsiyar ta juya masa ƙeya a gado ta barshi da kallon bayanta ko'a kwalar rigarta. Sannan a lokacin ne zakaji a hira tana ai lamarin rijalu sai su, ko kuma namiji ba ɗan goyo bane ba. Kumafa kafin lokaci idan taji wasu na faɗa haushi ma take ji, watama kaji tana bada amsa da nata dai ɗan goyo ne, koda kuwa yana ƙuntata mata a lokacin. To ba komai ke jawo hakan ba sai rashin girmama abu irin na shekarun ƙuruciya. Ya tabba wannan shike ɗawainiya da Maanal. Dan da'ace tunda suka rabu basu haɗuba sai da ta shiga 30+ na shekaru wlhy da yaga rashin mutunci, kuma ko sama da ƙasa zata haɗe bazata yarda su sake rayuwa ba. Amma yanzu 21+ take da, shiyyasa yake iya raunana zuciyarta da canja mata tunani harta shagalta da shi duk da wancan yanayin bai gogu a zuciyarta ba.........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣3️⃣

______________

........Tunaninsa ya katse saboda wani irin murɗewa da cikinsa ya ƙarayi. Sosai ya dunƙule waje guda yana mai ambaton sunan ALLAH. Wannan yanayin ne ke sashi riƙe kansa da tsiya-tsiya daga taɓata tako wace irin siga, dan ya tabbatar a ƙarshe wahala zai sha, ko kuma ya aikata abinda shi da kansa zai dawo yana ƙalubalantar kansa. Duk fitinarsa bazai iya ƙin biyayya ga iyayensa ba, wlhy koda ace zai cutu ya gwammace hakan. Ya tabbatar Abah bazai hanashi matarsa dan cutarwa ba, idan har zai iya juriya da haƙuri na shekaru, na ƴan kwanki ne zai nuna gazawa.... Dai-dai nan tunaninsa ya sake tsayawa, sakamakon kaɗawar alarm. A hankali Maanal ta fara motsawa, sai kuma ta shiga buɗe ido bakinta da addu'ar tashi a barci. Yau ma a kai da ƙafan suka kwanta, ta kuma jera filos a tsakkiya, dan bayan ta farka a barcin daya figeta saboda matsananciyar kunyar da ya sakata a ciki sai taga AA a gefenta har yayi barci, da alama kuma yayi wankan, tashi tai itama saɗaf-saɗaf zuwa bayi tayi wankan ta canja kaya, ta sake dawowa a hankali ta kwanta bayan ta jera filos ɗin, barci kuwa yay awon gaba da ita dan har yanzu jinsa take sosai. Tana ƙoƙarin tashi zaune idonta ya sauka akan AA daya juya mata baya, amma yanda ya ɗan dunƙule jikinsa kamar ranar sai gabanta ya faɗi, a ranta rayawa take kar dai baida lafiya?. Babu mai bata amsa, bata son kuma yin magana, sai kawai tai ƙoƙarin sauka, bayi ta nufa tana ɗan waiwayensa, harta shiga bai motsa ba. Duk abinda take AA na jinta amma ya daure har sai da ta shiga bayi sannan ya tashi zaune cike da jarumta da juriya. Abin tausayi idanunsa sun wani kaɗe, jijiyiyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Yana zaune a haka cikin ambaton UBANGIJI Maanal ta fito, ganinsa zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya, shima ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya janye idanun dan wani irin ji yay kamar an dakar masa kai da hama sakamakon saukar idanunsa akanta. Wani irin ƙyau kayan barcin data saka sukai mata, duk da bawani sun matseta bane kasancewarsu masu santsi sun kwanta mata a jiki luf. Tana zama ya miƙe, batare daya sake kallonta ba ya wuce bayi dan baya so taga halin da yake a ciki. Yafi mintuna goma a bayin sannan ya fito, Maanal bata yarda ta kallesa ba sam, duk da bata kawo a ranta ma wanka zai yi ba. Shima yaji daɗin ƙin kallon nasa da batai ba, jallabiya ya ɗauka ya koma ta bayanta ya saka ya zame bathrobe ɗin. Sai da ya ɗauka maganinsa ya sha yana addu'a a ransa ALLAH ya taimakesa ya samu natsuwa sannan ya juya a karo na farko ya mata magana... Kallonsa ta ɗanyi itama, dan yanda taji muryarsa kamar mai mura sai da zuciyarta ta tsarga. “Baka da lafiya ne?”. “Mi kika gani?”. Kanta ta girgiza masa kawai, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Ba komai”. Shima numfashin ya ɗan furzar, cikin son kauda yanayin yace tazo suyi sahur barci yake ji, gashi fitar wuri zasu yau. Komai bata sake cemasa ba tazo ta zauna. Daga ita har shi basu wani ci abin kirki ba, dan kowa da abinda ya damesa. Shine ya fara tashi yaje bayi ya sake yin brush yayo alwala. A mamakinta maimakon kwanciyar da yace zai yi sai taga yayi salla raka'a biyu ya ɗauka Alkur'aninta ya fara karatu, gashi sai wani sauke ajiyar zuciya yake a jajjare. Itama dai gyara wajen tayi taje tai brush ɗin tayo alwalan....

Kamar yanda ya faɗa da wuri suka fita yau, sai dai fa sam baya a cikin walwala. Companyn jiya suka koma, shi baima shiga ba, a mota suka barshi yace mata zaije wani waje ne. Kai kawai ta jinjina masa da masa addu'a dan ta fahimci yau ƴan miskilan ne a ka. Alhamdullah yau ma sun samu ilimi sosai dan komai an musu ne a bayyane practical. A rai Maanal na jinjina mutanen nan da halayyarsu, sam babu mugunta a tare dasu. Baƙar fata ne zai iya abu ya koya maka cikin sauƙi harda wasu sirrika nashi tab ɗin. Duk da ta fahimci AA nada babbar alaƙa da companyn ne amma ta jinjinama halaccinsu. Dan ta fahimci hakkane a lokacin da idannunta ya sauka a hotunan dake manne a wani office da suka shiga na mutane goma harda hoton AA. Al'amarin nata mata kai-kawo a rai amma ta rasa yanda zata tambaya. Yau sunfi jiya daɗewa anan, suna fitowa kuma masauki aka maida su. Ita kaɗai Mr Li ya ɗakko, koda ta tambayesa AA sai ya sanar mata suna meeting ne. Bata tambayesa meeting ɗin mi ba kawai tai shiru. Har ɗakinsu yay mata rakkiya da kayayyakin da bata san na miye ba. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya tare da cire kaya tayo wanka ta fito tai sallar azhar da taga lokacinta yayi. Sosai take jin kewar su Ammie, dan haka ta jawo wayarta data koma bata da amfani, dan in tace ma tayi magana dasu ta net bata da data. Haƙura tai ta kwanta kawai, sai ko barci mai nauyi yayi awan gaba da ita. Bata farka ba sai la'asar, tana mamakin yanda lokaci ke gudu anan, abu kamar ba azumi akeba. ALLAH musulman ƙasar nan suna cin ɓagas. Tayi Asr ta zauna taita karatun Alkur'ani. Wajen shida saura akai knocking ƙofa, tashi tai da tunanin ko AA ne. Amma koda ta buɗe sai taga Mr Li. Gaisheta yay tare da sanar mata ta shirya zasu fita. Ɗan jimm tai, sai kuma ta tambayesa AA ya sani. Amsa ya bata da ai shine ma yace azo a ɗaukesu su duka. Ajiyar zuciya ta sauke, ta koma ciki ta hau kimtsawa. Abaya ta saka mai laushi da ƙyau fara tas, ta ɗan gyara fiskarta ta ɗauka handbag ta fito. Tana isowa motarsu Yaqub na wucewa, Mr Li ya buɗe mata itama ta shiga yaja suka fice a hotel ɗin. Tafiyar ba wata mai nisa bace sosai suka iso wani waje mai ƙyau. Ko ina tarwai da haske tamkar rana. Tana fitowa a mota idannunta suka sauka akan AA dake tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan riƙe da waya yana latsawa, shigarsa ce dai ta safe sai dai yanzu akwai coat a sama, har yanzu fuskarsa babu walwala. Koda ya ɗago idanunsa yana kallonta sai taji wani iri dan idanunsa har yanzu basu washe ba. Takowa yay cike da ƙasaitarsa da nutsuwa zuwa gabanta, dan ta tsaya cak ne tana kallonsa. Dab da ita yaja ya tsaya, kallonta kuma yake ƙurr.. Nata idanun ta risinar tare da faɗin, “Ina yini”. Maimakon amsawa a ƙasan maƙoshi yace mata, “How are you?”. “Alhamdullah”.. Ta faɗa itama a taƙaice. Bai sake cewa komai ba yay gaba, binsa a baya tayi, sai kuma ya dai-daita tafiyarsu suka shiga a jere. Wani keɓantaccen waje suka shiga, an gyara wajen sosai anyi shimfiɗu an jera abinci da alama na buɗa bakinsu ne. Kallonta yay a karo na biyu sai kuma ya matso dab da ita ya kama haɓarta yana kallon ƙyaƙyawar fuskarta, ƙasa tayi da nata idanun. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, cike da kulawa ya furta, “Mike damun ki? Duk kinyi sukuku ko azumin ne?”. Kanta ta ɗan girgiza masa alamar a'a, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗinta murya cike da sanyi ta ce, “Barci bai isheni ba”. Sake riƙe fuskarta yay sosai yanzu kam da hannu biyu, shima a maƙoshi ya ce, “Sorry my Babie. Ba zamu jimaba ai, muna yin salla sai na maidaki ki kwanta okay”. Kanta ta jinjina masa fuskarta na wani shagwaɓewa. Yanda tai ɗin sai ya sashi sauke ajiyar zuciya, cike da tsokana sai dai fuskarsa babu wani alamar wasa ya ce, “Karfa a dinga fakar idona ana karya azumin nan”. Karan farko Maanal ta waro idannunta sosai a kansa kamar yanda yara keyi idan abun ya basu mamaki, da ɗan karsashi ta ce, “Lah nice kuma zan karya azumi? Nafa girma”. Shima idanun ya ɗan waro waje kamar yanda tayi, sai kuma cikin raɗa ya furta, “Lah na manta ashe half ɗin Ajwaad ta girma ta zama ammatansa yanzu. Na fara shirin zama ango kenan?”. Kifa kanta tai a ƙirjinsa dan maganar ta bata kunya, musamman a yanda ya furta yana wani ƙanƙance idanu. Shima sai ya murmusa zuciyarsa cike da shauƙi. Fin minti ɗaya suna a haka kafin ya ɗagota tare da furta, “Kina da alwala ne?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Shima sai bai sake cewa komai ba ya nufi wajen da kayan abincin suke ya ɗakko goran ruwa da ɗan bowl dake cike da dabino ya dawo wajan. Handbag ɗinta ya amsa ya ajiye a table ɗin kusa da su, sannan yay mata nuni da kujerar gaban table ɗin. Babu musu ta kai zaune, shima ya zauna a wadda take facing nata. Ruwan ya ɗauka ya kuskure baki itama ya bata, ya ɗauka dabino ya gutsira rabi ya kai rabin bakinta. “Wai ansha ruwa ne?”. “A'a zamu karya namu ne”. Ya faɗa cikin yanayin tsokana yana tsareta da idanunsa masu laushi. Sai baƙar maganar ta bata dariya. A cikin maƙoshi tayi murmushi sannan ta riƙe hannunsa suka saka dabinon a bakinta tare, itama ɗauka tayi ta kai bakinsa. “Fara ci”. Ya faɗa a sauƙaƙe. Kanta ta ɗan girgiza, “Kai ne babba ai”. Har cikin ransa yaji daɗin abinda ta faɗa, dan haka ya murmusa kaɗan yana kamo hannun nata shima ya gutsira rabin dabinon, cike da kulawa yace, “ALLAH yaya miki albarka! Barka da shan ruwa”. A saman lips ta amsa da amin tana ɗan murmushi da saka sauran dabinon a bakinta. Irin wannan yanayin kan karya mata zuciya matuƙa, takan ji abin da girma ta yanda har zuciyarta ke raunana taji anya zata iya aiwatar da shawarar su Didi a kansa. Sai dai wani gefe na zuciyarta kan kwaɓeta da gargaɗarta da tuna mata rayuwar da suka tsinta kansu a ciki bayan faruwar komai sai yaji ina.........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣4️⃣

______________

.......Miƙa mata ruwa da yay ne ya katse mata tunaninta, sai ta sauke ɓoyayyan nunfashi kawai ta amsa. Sun sha ruwa sannan ya miƙe yana faɗin, “Muje yin salla suna jiranmu”. A mamakin Maanal ta wata hanyar daban suka fito, sai taga masallaci madaidaici a wajen. A ranta tace wai ina yake samo irin wajajen nan? Dama akwai musulmai a Chaina kamar haka. A ƙarshen bango taga CFO, dan haka ta nufi inda take, ba'a kiran salla a massalacin, sannan ba'a salla da mic. Sai suka bata tausayi, amma koma miye UBANGIJIN da suke ibadar dan shi mai ji ne da ganine a kowane irin yanayi. Basu da yawa sosai, kusan ma zatace sune suka cika massalacin. Sunyi sallar magrib sannan suka fito. Wajen nan da AA ya fara kaita suka koma. Ganin yanda CFO keta shareta cikin kame kai itama sai ta watsar da ita, an gaggaisa da yima juna barka da shan ruwa suka zazauna. AA na kusa da ita, da kuma kansa ya zuba musu abinci ita da shi, ita dai duk sai ta jita a takure, shima ɗin bada wani sakewa yake cin abincin ba. Suko su AS kwasar girki suke hankali kwance duk da suna jin nauyin AA ɗin. Ita da shine suka fara tashi, dan haka sai ya jata kawai suka fito a wajen. Waje suka samu suka zauna, ya ɗan tsareta da idanu. “Mike damunki? Ko har yanzu barci ne?”. Kanta ta girgiza masa, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ina jin kewar su Ammie, tunda muka zo banyi waya da su ba. Ko barka da shan ruwa ban musu ba”. Nauyinta yaji akan hakan. Dan shima ya fahimci bai kyauta ba, shi ya kira iyayensa sun gaisa amma ita bai kira nata ba. Duk da har ga ALLAH yayi niyyar yin hakan shafa'a yayi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I'm sorry”. Batace komai ba shima sai yay shiru. Cikar lokaci sallah ya sakasu tashi. Sunyi isha'i da asham. Koda suka fito anan suka bar su AS, shi da ita suka wuce, wani gidan abinci mai shegen ƙyau suka isa, ganin an saka halal ya sata sauke ajiyar zuciya. Abinci aka shirya musu na gani na faɗa, anan kam cike da kulawa ya rinjaye ta sukaci suka ƙoshi. Basu koma hotel nasu ba sai kusan ɗaya na dare. Shi kam a gajiye yake fiye da ita, dan haka yana kwanciya sai barci. Dama haka yake so shiyyasa yaba kansa wahala da zirga-zirga ko zai samu raguwar kusancin zamansu a tare idan sun dawo makwanci. Saboda shi kaɗai yasan abinda yake fuskanta a jikinsa da wannan zaman waje ɗayan nasu. Ya kuma fara fahimtar gangar jikinsa so take taƙi bashi haɗin kai bisa shirinsa......

_________★

9-Ramadhan.

A yau ɗaukacin musulmai suka kai azumi na tara-tara a wasu ƙasashe, wasu kuma na ƙoƙarin ƙarisa kaiwa irinsu Maanal dake a Chaina. Yau gaba ɗaya a busy suke, dan sunata shirin komawa ƙasarsu ta haihuwa. Babu abinda Maanal zatace da UBANGIJI sai godiya a kwanakin nan, domin kuwa ta ƙaru da abubuwa masu yawan gaske. Irin siyayyar da AA yayi mata har tsoro abin ya bata, wai iyaka ma wanda ta gani kenan. Dan bata sani ba ma ya tura wasu kayan Nigeria kusan kwana uku kenan. Duk da daɗi da Chaina tai mata hakan bai hanata jin ɗokin komawarsu gida ba. Dan tayi kewar kowa da Kowa. Duk da zuwa yanzu hatta su Ammie duk tana waya da su...

Readers Also Read