Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 76

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 76

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 76: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 76. Alarm ɗin da AA ya saita ne ya…

4,132 words

Alarm ɗin da AA ya saita ne ya tadashi saboda sallar juma'a. A lokacin sha biyu. Wanka kawai ya shiga. Yana fitowa ya shirya cikin wani ɗanyen yadi da yaji ɗinkin manyan yara ya kwanta luff-luff. Fuskarsa ya gyara tare da feshe jikinsa da turarensa masu sanyin ƙamshi kala kusan uku. Ya kawo hula data dace da tsarin adon nasa ya kafa. Matuƙar ƙyau kuwa yayi kamar ka sasheshi ka gudu. Kodan bai cika damuwa da saka manyan kayan bane balle hula oho masa. Wayoyinsa daya kashe ya kunna, ya zubasu a aljihu tare da wallet. Sai kuma ya ɗauka atm ɗinsa ya fiddo wallet ɗin ya saka ciki, duk da kuwa akwai wasu atms ɗin a wallet ɗin, da alama dai yana buƙatar wanda ya dauka ɗin ne a kusa, dan a ajiye yake alamar baya amfani da shi sai da dalili. Kai tsaye sashen Abah ya nufa, cike da takunsa na nutsuwa da rashin son hayaniya. Sai da yay knocking tare da sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shigan. Wani irin murmushi Abah dake kallonsa ya saki, sai kuma ya buɗe masa hannayensa alamar yazo garesa. Murmushi shima AA ɗin yayi, tare da ƙarasawa gaban Abah ya zai zauna a ƙasa ya riƙoshi ya zaunar a gefensa, cike da kulawa da soyayya irin ta ɗa da uba ya bashi runguma ta gefe yana faɗin, “Irin wannan yin fresh haka Autan Oum ɗinsa. Har naji na ƙagu naga tawa ƴar yata koma”. Murmushi sosai AA ya sake yi, dan randa Abah kejin nishaɗi daban ne a rayuwa. Ƙasa-ƙasa yace, “Abah tayi fiye da yanda kake tunanin ganinta, dan na kula maka da amanarka yanda ya kamata”. Dai-dai nan Mamy ta fito riƙe da babbar rigar Abah da hula a hannu, karaf kuma a kunnenta zancen AA. Sai kuma akai sa'a suka haɗa ido da shi. Wani kallo kuwa ta zuba masa mai ma'anoni da dama. Shi kuma sai yay ƙasa da kai yana amsa addu'ar da Abah ke masa da sanya albarka. Gaishe da Aban ya fara yi kafin Mamy ɗin data wani basar da farko kamar bata ganshi ba. A mamakinsa sai ta amsa cike da nuna kulawa har tana tambayar yaya Maanal. Wannan hali na Mamy na girgiza zuciyar AA matuƙa. Kodan shi ALLAH yayisa ba mutum mai iya ɓoye abu bane oho, dan in har ka masa abinda yaji bazai iya shanyewa ba sai ya maka magana, sha yanzu magani yanzu yake, shiyyasa irinsu Sen.. Bukar Kaugama manyan ƙasar ke jin haushinsa. Dan sun so jan ra'ayinsa jikinsu ya nuna wannan ba shigarsa bace su sa'annin mahaifinsa ne, suka fito masa a buɗe game da muƙamin da shugaban ƙasa ya bashi na shugaban matasa, nan ma ya nuna musu shifa wannan muƙami baya a gabansa dan office ɗin ma sai ya gadama yake zuwa. Yana dai bibiyar ayyukan waɗanda ke ƙarƙashinsa daki-daki, amma shi ko sisi daya shafi aikin nan bai taɓa yarda ya shigo hannunsa ba hatta da albashi kuwa. Dan shi ya san kasuwanci duniya ne, duk wanda ya saba da neman na kansa babu ta yanda zai iya shagala da wani aiki na gwamnati koda na wucin gadi ne...........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣7️⃣

______________

.........Tare da Abah suka fito suka bar Mamy na binsa da harara, sashen Oum suka nufa, can suka samu su Babban Yaya cikin shiri suma. AA yaje ya rungume babban Yaya da shima dai yau yake tsokalarsa. RK da Fawzan kuwa na dariya. Zo kaga idanun Nuratu da Nibras kamar zasu faɗi a jikin AA. Gaba ɗaya sun susuce, a kwana goma kawai yay irin wanan sake zama fresh ɗin. Zukatansu suka shiga wassafa musu ba dole yay ƙyau ba yana more angwancinsa. Wani irin ture tunanin sukai rayukansu a ɓace, tun ɗazun suke a sashen amma basu ga Maanal ba. Wai tana ɗakin Oum tana barci. Jin AA na sashensa kuma baisa sun gajiya ba, dan sun tabbatar bazai iya wucewa massalaci bai zo sashen Oum ba. Aiko sai gashi ya shigo duk ya firgitasu da gayunsa. Tsabar sakawa rai masifa su duka biyun ba wanda azuminsa bai raunana ba saboda yanda suke siffanta wa kansu AA ɗin a zukata. Suko sauran ƴammatan da zukatansu fes suke kowama yayi musu ƙyau a yayun nasu bawai AA ɗin kawai ba. Najma da Fawzan kuwa sun wani kashe ma juna ido cike da shauƙi. Sai ko karaf a kan idon AA. (Kai mi Ya Fawzan ke shiryawa haka?) AA ya ambata a zuciyarsa, sai ya ɗan kalla RK daya fahimci shima hankalinsa akansu Ya Fawzan ɗin yake. Wani signal sukama juna da ido, RK yay dariya yana ma bakinsa zip. “Tab ɗin”. AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi yana miƙewa abinsa batare da kowa ya fahimci inda tab ɗin ɗin tasa ta dosa ba. Fitowa sukai harabar gidan gaba ɗayansu harda samarin yaran nan duk suka shiga motoci. RK da AA da wasu a yaran suna a mota ɗaya. Babban Yaya, Fawzan da Abah da sauran yaran a mota ɗaya. Acan itama Oum ta kaɗa ƴammatan zuwa kowa yay wanka yay salla a shiga kitchen. Jikin babu ƙwari Nuratu da Nibras suka fito a sashen.....

_________★

A lokacin da su Maanal suka gama hutawa anan airport Yazeed ne da tashi matar ke isowa tasu ƙasar haihuwar bayan kwashe watanni a ƙetare suna hutawa. Masha ALLAH na faɗa, ganin yanda Yazeed ɗin yay wani kalar yin ƙyau da sabuwar nutsuwa ya yi ƙiba irin ta matasan masu kuɗi. Sai dai fuskar kicin-kicin babu fara'a sam a tare da shi abinka da dama bamai yawan fara'ar bane. A gefensa Nazeefa ce cikin matuƙar gayu ta ƙara wani uban haske da ƙiba itama. Kai daka ganta kasan tana jin daɗi da alama kuma ta harbu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai Aunty Sabuwa, dan haka ita da kanta ta tafi tarbosu Abujan. Nazeefa na hangota ta wani tafi da gudu ta tungumeta tana ihun murna. Hakan ya jawo musu idanun mutane kuwa. Oho ko'a kwalar rigarsu, dan Aunty Sabuwa ma ɗaga Nazeefa tayi tana juyi da ita abinka da siririyar mace, a hakan ma wai jikin ya murje ne. Ƙarasowar Yazeed da abun nasu ya bashi kunya ya sata sakin Nazeefa, sai kawai ji Yazeed yay an wani rungumesa. Tab ɗin, yau fa ake mutuwar tsaye, dan kuwa ita dai Yazeed ɗin yayi. Yayinda Aunty Sabuwa ke faɗin, “Oyoy my Son”. Yazeed na kama da mahaifiyarsa Hajiya Yaya, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya na kama da juna, shiyyasa mutanen dake kallon ikon ALLAH suka ɗauka ita ta haifesa, duk da dai wasu na ɗan wasiwasi na ganin kamar shekarun Aunty Sabuwa bazai kai ta haifi Yazeed ɗin ba. Nazeefa da abin ya sosa mata zuciya ta riƙo Aunty Sabuwa tana faɗin, “Kai Mom harda runguma kuma?”. “To dan ubanki ba ɗana bane shi, ko a lahira ba ance ɗan ɗan uwa kai yake gani ba. Kinga ko a lahira bazaiga Yaya ba ni zai gani”. Baki sosai Nazeefa ta tura gaba, tana kauda kanta. Oho ko'a jikin Aunty Sabuwa, sai ma amsa gaisuwar Yazeed da take yi. A haka suka rankaya zuwa lafiyayyar motar da aka sakama Nazeefa a lefe. Ba shi kawai ba ita kanta Nazeefar sai da tai mamaki. Ta kalli Aunty Sabuwa cikin waro idanu ta ce, “Mom! Wai motata ce ta koma haka? Hawa akeyi ne?”. Cikin rashin damuwa Aunty Sabuwa ta ce, “Eh mana my baby ina ɗan ɗanawa ne kafin ki dawo. Babanki yace idan aka barta a ajiye ba'a hawa saita samu matsala.” sai kuma ta sake rage murya yanda Yazeed bazai ji ba ta cigaba da faɗin, “Sannan banda ke shashasha ce yanda yaron nan ya moreki da ƙyau a hutawar nan taku ai kinsa zai saya miki wadda ta fita. Dan yanzu kinfi ƙarfin hawa wannan. Agolan gidansu fa tsohuwar budurwarsa motan miliyan 90 aka sako mata a lefe da ta miliyan 20+. Ke sai ki zauna kina hawan wannan ta 20m ƙaramar tata ma tafi taki”. Ai wani irin susucewa Nazeefa taji tayi, a zabure ta ce, “Wai kina nufin Maanal Mom?!”. “To inba itaba wa? Ba itace tsohuwar budurwar mijinki ba”. “Kambu Mom shi ɗan gidan KK kura ɗin ne yay mata wannan lefen?”. “Hummm! Ke dai fa labarin mai tsaho ne, amma ina gaya miki likafa taci gaba, kin san uwarta ta iya tsafi, ai a wajen ɗaurin aure komai ya canja, maimakon ɗan kura sai aka bama ɗan tsohon ambassador Aliyu Darma”. “Kuttun uban can kai, AA Darma fa kenan? Koba shine aka gaya muku ya mata fyaɗe ba tana yarinya”. “Shifa kuwa, kedai shiga mota muje ma ƙarasa a gida mijinki na kallonmu”. Tab ɗin gaba ɗaya jikin Nazeefa ya gama sanyi, ji take farin cikinta ya wani gushe a lokaci guda. Kai ina bazai yiwu ace ta ƙwace Yazeed a hannun Maanal ba, sannan Maanal ta aura wanda yafisa. Yo ba Yazeed ba ai ko Daddynsa kansa AA Darma ya fisa kuɗi kamar yanda taji ana faɗa, balle kuma suma babansu Aliyu Darma ɗin ƙurun kansa ne, hakama sauran brothers ɗinsa suma fa akwai kuɗin. Kai family ɗin Darma ma gaba ɗaya sai dai kawai ace wane yafi wane arziƙi saboda iyayensu sun tara musu. Gashi ba wani uban yawa ne da su ba dan a tarihin data bibiya nasu tushe zuri'ar gana ɗaya shi Harɗo Ishaq Darma ɗin ba ɗan asalin ƙasar Nigeria bane, tushensa da ainahin zuri'arsa na wani yanki na sudan ne. Mahaifiyarsa ce ƴar nan Yola ɗin, bata son Mahaifinsa shiyaysa daga haihuwarsa auren ya lalace ta gudo da shi nan. Shi kuma babansa yay fushi yace bazai biyo ta ba har abada ya bar mata ɗan. Dan haka ainahin dukiyar Harɗo Ishaq ta mahaifiyarsa ce daya gada, iyayenta suka bar mata kuma ita kaɗai, shima ya gada a wajenta.. Nazeefa na wannan tunanin suka iso gidansu. Mamaki sosai ya kama Yazeed ganin gidansu Nazeefa suke, shi a ganinsa ai gidansu ya kamata a tafi, sai dai yaji ya kasa magana sam. Lafiyayyan abinci kuwa suka samu an haɗa musu, dan Nazeefa ta gayama uwarta basa azumi saboda tafiya. Shi dai Yazeed hankalinsa duk a rarrabe, kewar mahaifiyarsa yake shima da ƴan uwansa, so yake ya gansu amma anzo nan an masa ɗaurin goro. Haka dai ya daure ya ci abincin sama-sama. Yayinda Nazeefa da Aunty Sabuwa suka kulle a ɗaki bai san abinda suke tattaunawa ba. Yanda suka barsa shi kaɗai ɗin kuma ya sosa masa rai, amma sai yaji ko'a fuska bazai iya nuna ɓacin rai ba. Sun fi minti talatin kuwa kafin su fito suna ƴar dariya, sai lokacin Nazeefa ta zauna taci abincin itama. Sun kammala Yazeed na shirin cewa su tashi suje gida sai ga Babanta. Wato mijin aunty Sabuwa. Ai da wani irin farin ciki ta daka tsalle ta ɗanesa tana ihu. Sai Yazeed yay kasare kawai yana kallon ikon ALLAH. Bayan sun gama murnar su sanan baban nata ya zauna suka gaisa. Babu kunya sai wani faɗi yake wai amarcin ya amshesu sunyi ƙyau abinsu. Kunya kamar ta kashe Yazeed amma bai iya cewa komai ba. Shima baban jan hannun Nazeefa yay suka haye sama, sunfi minti ashirin sannan ta dawo. Nan ma dai ran Yazeed ya sosu, amma ko fushi bai iya nunawa a fuska ga duk da kasancewar sa mutum mai zafi. Suna fitowa ana kiran magrib, aunty Sabuwa tace ko zasu koma sai anyi salla. Kan Yazeed a ƙasa ya ce, “Aunty ayi haƙuri dai mu tafin”. Ido Nazeefa ta ƙyafta mata, dan haka tai shiru. Yanzun ma Aunty Sabuwa ce ta tuƙasu zuwa gida, duk da kuwa shan ruwa ake kuma tace wai tana azumi....

Ammie na kitchen da Sakina da su Waleed suna ƙarasa aikin abincin buɗa baki Hameed da yaje kaima su maigadi abinci ya shigo da ɗan gudu yana faɗin, “Ammie Yayanmu ya dawo”. Kallon yaron kawai Ammie ta tsaya yi, sai kuma zuwa can ta ce, “Yazeed!”. Kai Hameed ya jinjina mata kuwa tare da faɗin, “Aunty Sabuwa ce ta kawosu a mota, gasu can suna buɗe sashen Yayan, su Aunty Basira sun fito sai kuma suka tsaya basu je wajensu ba suna kallonsu daga nesa”. Murmushi Ammie tayi. Sakina kuwa data kasa shiru, “Tofa ikon ALLAH, ita surukar ce taje ta tarbosu kenan? A dole kam yara su tsaya duk da uwarsu bata nan ai ince sashenta zasu fara sauka”. Ammie ce ta ce, “Ai maybe kuma daga can wajen Yayan suke tunda kika gansu da Sabuwa ɗin.” Sakina dai da kamar bata gamsu ba ta ce, “To ƙila hakane Aunty”. Daga haka suka fito a kitchen ɗin domin zuwa yin sallar magrib tunda kowa yaci dabino yasha ruwa.............✍️

_To labari ya waiwayo gidan su Ammie😄🏃🏃🏃_

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣8️⃣

______________

........Maanal bata tashi ba sai da Oum ta tasheta ganin 2 na neman wuce wa. Daka ganta kasan sosai take jin azumin nan, duk ta yi laƙwam har wata ƴar rama tayi, to dama can Maanal raguwa ce akan azumi, kawai dai kura ce tai lafiya aka fara dauriya irin na mu mun girman nan. Wanka tayi tai salla, wasu skirt da riga masu taushi da rashin nauyi ta saka. Skirt ɗin ya buɗe sosai. Haka ma rigar bata wani kamata ba amma sun mata ƙyau. Cike da rashin ƙarfi ta sakko falon ƙasan, ƴammatan yaran duk suna zaune harda Nurry da tuni ta dawo hakama Nibras duk sun ci kwalliya abunsu kamar ba masu azumi ba. A dai-dai nan su AA suka shigo. Shine a gaba shi da Muhseen dake bashi labarin makarantar su, baya cewa komai yana dai sauraren yaron kawai. Su babban Yaya biye da shi, sai yaran RK da Fawzan a ƙarshe. Duka yaran hannuwansu da ledodin fruits, sai suka nufi kitchen suna ajiyewa. Shi ko AA da idanunsa suka fara sauka akan Maanal dake ƙoƙarin kaiwa zaune a kasalance inda take ya nufa ko kunyar ƙannensa har ma da ƴaƴa dake fallon bai jiba, balle tasu Nuratu da baima san dasu ba, gasu Babban Yaya kuma a bayansa da Abah. Zama yay a hannun kujerar da takai zaune bayan ta janye idonta a cikin nashi tana amsa maganar da su Meena ke mata. A ƙasan maƙoshi sosai ya furta, “Kina lafiya?”. Kanta ta jinjina masa fuskarta a marairaice. Shi ko yana kallonta da fararen idanunsa da ke kamar an watsa mai a cikinsu saboda yanda suke wani irin ƙyalli mai ɗaukar ido sosai gasu farare tas. Sai kuma ya kai yatsunsa biyu a goshinta alamar son tantance zafin jikinta. “Lilly ba lafiya ne?”. Babban Yaya ya faɗa idonsa a kansu. Da sauri Maanal ta ture hannun AA dake shirin kaiwa wuyanta cike da jin kunya ta kalla babban Yayan. Sai kuma taga ashe ma harda Abah, ai saita ƙara daburcewa ma harta so bama su Aban dariya. Dan tuni ta zamo ƙasa ta fara gaishesu. “Kinga tashi-tashi ƴar gidan Abanta, zauna abinki kinji. Fatan dai kun dawo lafiya, ɗan gidan Oum ko harararki baiyi ba tunda yaga bana kusa.” Murmushi sosai Maanal tayi ta ɗan kalla AA suka haɗa ido, sai ta maida kanta ta risinar tana girgizama Abah alamar eh. Yace, “To Masha ALLAH ɗan Oum ka fita ko ba sabulu.” dariya duk akai a falon banda Nurry da Nibras da kishi ya kume. Maanal ta gaida babban Yaya shima, sannan ta juya tana gaida su Yaya Fawzan da RK. Babban Yaya ne ya tambaye ta amma dai bata azumi ko, dan AA yace shi yanayi. Amsa ta bashi da tanayi itama, sai duk tausayinta ya kamasu. Abah ya shiga yima AA faɗan miyyasa ya barta ta ɗakko azumi tunda yasan awannin zasuyi tsaho. Cike da tausasasawa AA ya ce, “Abah ba laifina bane fa, kasanta tana da rigima”. Baki Maanal ta tura gaba kaɗan da faɗin, “Kaima kana da ita ai”. Dariya duk akayi, banda AA daya ɗan murmusa kaɗan yana wani kallonta ƙasan ido. Babban Yaya da Abah ma dai murmushin kawai sukayi. Hakama Oum dake fitowa. Miƙewa Nuratu tayi idannunta cike da hawaye, dan bata jin har yanzu AA yako kalleta. Oum ta tsaidata da faɗin, “A'a Nuratu ina zuwa? Ai ku wuce muje kitchen lokaci naja kada a makara yau. Muneer jeka sanarma Maman Naufal da Mamy suma dasu Haule”. Amsawa Muneer yay yana miƙewa, su kuma ƴammatan suka shiga tashi suna nufar kitchen. Miƙewa Maanal itama tai shirin yi AA ya maidata ya zaunar batare da kowa ya lura ba, sai kuma ma dai-dai hakan Oum ta ce, “Baby banda ke kekam zauna ki huta”. A marairaice Maanal ta ce, “Oum zan iya, zammafi ganin saurin lokacin fa”. “A'a bazakiyi komai ba, sai dai ki zauna kina tayamu hira”. Da sauri tace eh ta yarda. Tashi tai tabi Oum, sai AA ya koma ya zauna inda ta tashi ɗin yana amsa wayarsa da ake kira. Yanda kitchen ɗin ya cika kowa na ƙoƙarin fara aikin da aka basa sai abin ya burge Maanal. Tana matuƙar ƙaunar rayuwa family house musamman mai haɗin kai da ƙaunar juna irin haka. Sai taji tana ma Mamy addu'ar shiriya da nata halin, dan tabbas da itace babba a matsayin Oum lallai gidan nan da tuni ya tarwatse, irinsu Mamy basa iya haɗa kan iyali koda nasu kaɗai ne. Shigowar Mamyn ta katse mata tunani, cike da girmamawa ta gaisheta, amma sai Mamyn ta amsa sama-sama cike da gatse kuma ta furta, “Sai yanzu ake ganinki ƴan chaina”.. Gaban Maanal ne ya faɗi, tai saurin kallon sashen da Oum take sai taga hankalinta sam baya anan. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, dan duk wanda yaji a yanda Mamy tai maganar ALLAH sai ya tsargu, saboda kalamai ne a kaikaice amma masu tsauri. Cikin son kare kai ganin murmushin da Saheeba tayi Maanal ta ce, “Ayya Mamy yanzu nake shirin tafiya sashen ki sai Oum tace a kiraku”. Wani kalar tsaii Mamy tayi tana kallon Maanal ɗin, ita ko tayi fuska abinta tama maida hankali kan Batool da Maimoon dake zaman gyara fruits ta shiga nuna musu yanda zasu yanka kankana a sharp mai ƙyau. Suna a haka akai kiran la'asar, Oum da Mamy suka fita salla, sai Oum tace suma su rabu biyu idan sun dawo sai wasu suje. Maanal da taga ba aikin komai take ba sai itama ta miƙe kawai. Lokacin suma mazan sun fice sallar, daga can zasu zauna jin tafsir ne. Kowa yana dawowa daga salla aiki ya ɗora, zuwa shida an fara fidda komai waje, Maanal dai tuni ta dawo falo dan ƙamshin abincin sai suka fara hawa mata kai, ga ƙarfin jikinta ya sake raunana matuƙa har tana neman fara galabaita dauriyace kawai dan karta tayarma kowa hankali yasa ta dake. Amma duk wanda ya kalla idonta da yay zuru-zuru zai fahimci ƙarfinta ya fara ƙarewa. Aiko da ƙyar ta iya tashi tai alwala kamar kowa duk suka koma waje inda aka shirya abincin da wajen salla. Tana daga kwance aka kira salla, kowa ya fara ƙoƙarin cin dabino ita ruwa ta ɗauka mai sanyi sosai ta shiga sha. Saida ta shanye roba ɗaya tas, ta sake ɗaukar wata ta ɗora, ta sha rabi Najma ta amshe tana faɗin, “Easy mana Aunty Maanal”. Komawa tai ta kwanta tana lumshe idanun da sauke numfashi. Ta jima a haka kafin tai dauriyar tashi yin sallar itama, tana idarwa ta sake komawa ta kwanta. A haka su AA suka shigo suka sameta. Sosai hankalinsa a kanta yake, dan shi kansa a jigace yake balle ita, amma ganin Oum na ƙoƙarin kamata ta tashi ta jinginata a jikinta sai ya sauke ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Kaɗan taci abincin tace ta ƙoshi, Oum zata cigaba da lallashinta Abah yace ta barta haka kawai. Kwance Maanal takai har sai da aka fara shirin fita salla ta ɗan ƙarfafa kanta, Oum taso ta zauna gida ta huta amma tace zata iya. Haka suka fice hankalin AA a rarrabe. Ana idar da sallar isha'i dole Maanal ta haƙura, dan jiri ma take gani, ga abincin da taci sai juya mata yake kamar zata amayoshi. Ana idar da wutri itace farkon miƙewa. Oum ta bita da kallo, sai kuma ta miƙe ganin kamar Maanal ɗin na layi. Alhamdullah Maimoon na kusa da ita da sauri ta riƙeta. Cikin rawar murya Maanal ta ce, “Maimoon muje gida amai nake ji”. Babu musu Maimoon ta riƙota sukayo gaba. Sune farkon shigowa gidan. Sai Oum da tun fitowarsu ta biyosu, sai akai sa'a RK da AA sun fito suma suke tambayar Oum ɗin lafiya dan ganinta a ruɗe. Sama-sama ta ce, “Baby! Ina ga bata jin daɗi”. Kowa yasan wa take cema Baby, dan haka suka rufa mata baya, AA da kansa shima ke ciwo jiyake kamar ya rufe idanu ya gansa a gaban Maanal. Aiko shigowarsu gidan dai-dai da fara aman Maanal. Dan da wani irin ƙarfi ta fisge jikinta ana Maimoon tai wajen fanfo da akema flowers barruwa jikinta sai rawa yake ta fara aman. Su duka can sukayi kanta, yayinda Maimoon data bita ta riga su isa tana riƙe da ita. Ina AA na zuwa baima san ya janye Maimoon ba ya riƙo Maanal a jikinsa. Ganin yanda take yunƙuri sai kawai ya rungumeta ta cigaba da yi a jikinsa. Aman ma duk ruwa ne tunda ba wani abincin kirki taci ba. A wannan halin su Mamy suka shigo suka samesu. Dukansu sai sukai mutuwar tsaye ganin yanda AA ke rungume da Maanal tana amai a jikinsa. Zuciyar Mamy na rawa tace, “Ciki? Ciki Ajwaad yay ma yarinyar nan?”. Wannan furuci nata ƙasa-ƙasa karaf sai a kunnen Nuratu, a wani irin rikice ta ce, “Ciki kuma? Na shiga uku na”. A bayyane tayi tata maganar ita, dan haka ta shiga kunnen kowa harda Abah dasu Oum. Hatta AA ɗin ma yaji, amma da yake hankalinsa na kan Maanal ne bai kula ba. Nibras kam jitai kamar zata sume a wajen. Ajwaad ɗinta ne yama wata ciki! Kai ita kam ai itace ta shiga uku ba Nuratu ba. Saheeba ce ta kama hannun Nuratu ta damƙe domin maidota hankalinta.... Maanal dai data gama yin lagab idannunta na lumshewa ta kwantar da kanta a ƙirjin AA dake rungume da ita. Bawan ALLAH idanunsa sun kaɗa sosai damuwa ta bayyana matuƙa a fuskarsa. Kan nata ya dafe da hannunsa yana shafawa, sai kuma a hankali cike da raɗa dan babu wanda zaice a wajen yaji mi yake faɗa ya ce, “Sannu. Kin gama?”. Luuuu Maanal ɗin ta buɗe idannunta ta ɗan kallesa, sai kuma ta maida ta lumshe a hankali. Abah ne ya matso inda suken cike da kulawa yana mata sannu, sai kuma yace, “Ajwaad ɗagata a damshin ruwan nan kuje ciki ka gyara mata jiki kaima ka gyara naka sai Rafeeq ya duba ta?”. Kai kawai AA ɗin ya jinjina. Sai kuma ya miƙe ɗauke da ita camak abinka da dogon mutum da ya wadatu da ƙarfin jiki. Duk da kallo suka bishi, su Maimoon kuma suka shiga gyara wajen. Kansa tsaye sashen Oum ya nufa da ita, Oum na bayansu hakama Abah, can ɗin kuma kowa ya nufa dan Maanal ta basu tausayi, sai RK ne ya shiga mota yana faɗin bara yaje ya ɗakko kayan aiki. Ya Fawzan ne ya bisa domin masa rakkiya........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣9️⃣

______________

Readers Also Read