Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 90
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 90: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 90. .......Mamy na zaune a inda Maman…
4,468 words
.......Mamy na zaune a inda Maman Saheeba ta barta idanunta a lumshe, tun ɗazun so take ta motsa tama ɗauka wayarta ta kirata saboda jinta shiru amma ta kasa. Knocking ƙofar da akai ya sata kallon wajen. Aka ƙara na biyu sai ta bada izinin shigowa. A mamakinta Babban Yaya ne ya shigo bakinsa da sallama. Taɗan zuba masa ido, sai kuma cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma lafiya a daren nan?”. “Lafiya Lau Mamy, Saheeba ce tace kin kirata a waya, na ji shiru kuma shiyasa nai tunanin ko babu lafiya”. A zuciya Mamy tace (Saheeba kuma...?) a zahiri kam rasa ma abin cewa tayi, sai kuma ganin yanda ya zuba mata ido ta ce, “Yanzu Fadeel dan na kira matarka shine ka taso ka biyo ta?”. “Lah Mamy ki fahimta mana, nace najita shiru shiyasa nai tunanin koba lafiya ba. Yanzu fa magana ake ta sha biyu ta wuce. Kinga dole nai tunanin akwai damuwa. Amma tunda lafiya ai Alhamdullah sai da safe”. Daga haka ya juya ya fice abinsa. Da kallo ta bisa kawai abu uku na mata kai-kawo a zuciya masu ɗaci. Na farko miyyasa Saheeban zatai ƙarya cewa itace ta kirata? Sannan ina taje a daren nan to?. Na biyu yanda sam su Fadeel basu damu da ita ba, yanzu ace a yanayin nan daya ganta bazaiyi tunanin bata da lafiya ba, ta inda Ajwaad ya ɗarasu kenan, ko yaya yaga canji daga gareta sai ya gane. Hawaye suka ziraro mata. Tamkar wadda aka bama ƙarfi sai gashi ta yunƙura ta tashi. Dolene taje ta duba Saheeban da Nana ma da taji shiru babu ita babu Ajwaad ɗin. Da ƙyar take tafiya saboda ƙafafunta da suka kumbura suntum, ga ciwon kai gana ƙirji da yake mata kaɗan-kaɗan shima. Shiru tsakar gidan babu kowa, haka ta dinga tafiya cike da ƙarfin hali tana haɗa hanya, tama rasa ina zata dosa, shawarar da zuciyarta ta bata na zuwa sashen Ajwaad tabi, dan gwara ta fara duba Nana tasan halin yaron nan ba ragama ƙanwar tata zaiyi ba. Ta ƙofar kitchen tabi itama, tunda dama tannan ta bama Maman Saheeba shawarar bi. Itama sai da tabi komai na kitchen ɗin da kallo tana taɓe baki, kafin ta shige sai dai falon ƙasan shiru ne babu kowa. Amma fitula a kunne. Kuka-kuka da kiran sunan kamar Nuratu da taji anayi yasata nufar upstairs ɗin da ƙyar dan ƙafafunta sun mata nauyi sosai. Ai kamar jira ake ta gama hawowar kunnuwanta suka jiye mata abinda ya sakata tsayawa cak a firgice. Dai-dai nan kuma su Maman Saheeba suma suka ganta duk sai suka ƙara firgicewa. Jikin Mamy rawa yake sosai, takai hannu ta toshe kunnenta amma abinda take gudun jin tamkar a ƙwaƙwalwarta ake zayyanawa. Idanu a rufe tai wani irin juyawa gaba ɗaya domin komawa a bisa tsautsayi tai tsallaken taka step ɗaya, sai kawai ji kake rikicaaaa manyan mata sun kife. A wani irin mugun tashin hankali Saheeba da Mamanta suka bar Nuratu suka kai kan Mamy da har ta fara mulmulawa tana yin ƙasa. Da shegen gudu suka shiga binta, tana gab da ƙarasa direwa ƙasa gaba ɗaya suka samu nasarar riƙota. Sai dai ina aikin gama ya riga ya gama dan gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska, kuma sam bata numfashi. Anya Saheeba da uwarta sun taɓa shiga irin wannan tashin hankalin kuwa a rayuwarsu. Dan Maman Saheeba bama tasan ta fashe da kuka ba tana kirama kanta ta shiga uku. Saheeba da itama jikinta ke rawa kaf-kaf ta ce, “Mama mun mutu, yanzu yaya zamuyi, wlhy idan bamu fitar da su a sashen nan ba akwai matsala. Kada fa ki manta duk ƴan kano suna a gidan nan. Sannan wlhy Ajwaad baida mutunci komai zai iya yi idan yazo ya gammu da uwarsa kwance a wannan halin, zai ma iya cewa mune muka turota. Mama aurena, dan ALLAH ki taimaka ni bari na tafi wlhy suka ganni anan zasu saka Fadeel ya sakeni, kuma shima nace masa Mamyn ce ta kirani.....” Itama Maman kukan ta fashe da shi, “Yanzu Saheeba sai ki tafi ki barni cikin wannan bala'in? A tunaninki idan ni sun zo sun sameni auren naki zai tsira ne. Ki kamata mu kaita sai mu dawo mu ɗauki Nuratu itama”. “Mama tayaya zamu iya? Ta yaya bayan kin san dai matar nan itama ba laifi ƙatuwa ce. Gwara-gwara ma Nuratun. Mafita ɗaya garemu kawai ki kira Aunty”. “Baki da hankali Aunty kuma?”. “To wlhy itace kaɗai mafitarmu, idan ba haka ba ni dai zan tafi gaskiya. Dan wlhy ina son mijina da ƴaƴana. Bazan so barin gidan nan ba, yo ko kishiya bana fata balle barin gidan kina dai ganin sun haɗa kai an aurama Fawzan ƴarsu shima Fadeel ɗin zasu iya yin haka”. Ran Mama ya ɓaci amma sai ta danne. Da ƙyar ta iya lalubo number Auntyn su, cikin barci ta ɗaga wayar, roƙonta kawai Maman Saheeba ta shiga yi akan tazo sashen Ajwaad ta biyo ta kitchen akwai matsala. “Sashen Ajwaad kuma? Ke kuwa miya kaiki sashen Ajwaad a wannan daren Nana?”. “Bani kaɗai bace ba fa harda Aunty Kamila”. Kamar dai Aunty bazata tanka ba sai kuma ta yanke wayar, ita kanta lokacin da take isowa falon saman abinda ya fara shiga kunnenta duk sai taji ta gigice. Ta ƙoƙarin juyawa Maman Saheeba daketa sheƙama Mamy ruwa taƙi ta farfaɗo ta riƙota. Cikin ɓacin rai Aunty ta zubama Maman Saheeba mari. “Ku daƙiƙan inane zakuzo ma yara sashe a irin wannan lokacin, ƙarfe biyu saura fa. Mike damunku ne? Kun haukace daga ke har Kamila ne”. Duk da Maman Saheeba taji zafin marin nan matuƙa ta ce, “Ni dai dan ALLAH Aunty kiyi haƙuri, ko kamata mu fita da ita karma yaron nan ya fito ya gammu, ko wani a gidan nan ya fahimci muna nan. Nuratu ma tana a sama a sume” Rasama abin cewa Aunty tayi, dan sai lokacin ta iya hango Saheeba dake wajen Nuratu ɗin a yanzu. A fusace ta ce, “Ai gara ma asan kuna nan ɗin, wannan ai jahilci ne da rashin sanin mutuncin kai, ya ALLAH na shiga uku na, wai mi kuke son ku zama ni kam Nana?”. Aunty ta faɗa tana nufar hanya, cike da magiya da roƙo Maman Saheeba ta kamota, Aunty ta watsa mata wani mugun kallo. Da ƙyar dai ta yarda suka kamata suka fita su ukun. Aunty taja ƙofar kitchen ɗin ta rufe. Sun zo kusan tsakkiyar gidan kawai sai sukai ido biyu da Abah. Gaba ɗaya rikicewa sukai, suka saki Mamy a ƙasa babu shiri. Aiko sai gashi ta farfaɗo, taja wani wahalallen numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana kiran, ta shiga uku. “Shiga uku? Ai da sauran lokaci”. Abah ya faɗa yana sakarma Maman Saheeba da Aunty wani murmushi ya juya zai bar wajen. Sarai kuma abinda ya faɗa a kunnen Mamy. Ai ko sai ƙirjinta ya shiga dukan dubu-dubu jikinta na rawa sosai gashi bata gani da ƙyau saboda jini daya ɓata mata fuska. Aunty kuwa cikin sauri ta ce, “Aban Fadeel wlhy ban san komai ba, yanzu suka kirani a waya ina barci ma”. Juyowa Abah yay ya kalleta, sai kuma yayi murmushi kawai ya cigaba da tafiyarsa. Mamy da ke jin kamar zata sake suma muryarta na karkarwa ta ce, “Na shiga uku da gaske shine?”. Banza Auntyn tai mata, dan harga ALLAH murmushin Abah ya matuƙar dakarta. Ita kanta Maman Nana jitai murmushi na girgiza mata zuciya, balle Saheeba da tun cin karo da Aban tai saurin juya baya dan ita ta fara sakin Mamy a ƙasa ma. A karo na biyu Mamy da jini ke rinjaya ta sake sume musu. Aunty da bata fatan bayan Abah wani ya sake zuwa ya gansu kuma, dan gara shi idan tai masa bayani maybe ya fahimceta a zafafe ta ce, “Sai ku kamata muje, kuma wlhy sai dai ku dawo ku ɗauki Nuratu”. A wahale suka kaita sashenta, Haule da motsinsu ya sakata leƙowa ta bisu da kallon mamaki, ganin fa abun mai girma ne zaram ta fito. Gaba ɗaya sunma manta wacece ita sukace ta taimaka musu dan Mamyn ta musu nauyi sosai. Haka ta kama suka haura da ita sama. Suka shimfiɗeta a ƙasa, Aunty sai zagin Maman Saheeba take, ita kuma tanata rantse-rantse Mamy tace ta rakata zatama Ajwaad magana. “Ai kin rakata, kunje kuma kun jiyo abinda kuke buƙatar ji, kun kuma samo sakamakon daya dace daku. Yanzu sai ku jira shima randa yaron zai san su wanene ku marasa hankali kawai tunda ubansa yau ya sani. Kuma sai dai ku koma ku ɗakko Nuratu wlhy bazan koma ba”. Daga haka ta jawo kwalin tissue dake a table ta fara goge ma Mamy jinin daya wanke mata fuska har ya fara jiƙa gaban rigarta. Ashe rauni taji a goshi da haɓarta sai gefen idon dama. Haule ta aika ta kawo mata first ald box tai mata ɗan abinda zata iya ta saka mata audiga da bandage dan a samu jinin ya tsaya kafin dai safiya... Dai-dai nan su Saheeba suka dawo ɗauke da Nuratu, a falo suka ci karo da wata cousin sister ɗinsu Mamy. Motse-motse ya sata fitowa. Da mamaki take duban Maman Saheeba da Saheebar sai Haule data fito da kayan da aka gama gogema Mamy jini. Sai kuma ta kalla wanda suka ɗako da alamu suka nuna kamar bata numfashi. “Subahanallahi. Nuratu kuma? Nana daga ina haka?”. Hawaye Maman Saheeba ta share, tana kaiwa zaune kusa da Nuratu da suka shinfiɗar anan falon, zatai magana caraf Saheeba ta karɓe. “Aunty Mariya yanzu drivern gidansu ya kawota, wai ta matsa ya kawota nan shine ta suma a hanya. To ya kirani a waya da wayarta na fito sai ga Mama itama shine muka shigo da ita”. Matar da yake akwai kwakwazo ta ce, “Innalillahi... Amma miyasa Hajiya Turai zata barta ta fito a wannan tsohon daren? Koda motar gida ce ai akwai haɗari. Haule kawo ruwa”. Da sauri Haule ta wuce kitchen, babu jimawa ta dawo da gorar ruwa masu sanyi a hannu. Saheeba ce ta amsa ta shafama Nuratu. Amma ko gezau, sai da Aunty Mariya nan ta bata shawarar a watsa mata da ƙarfi sannan Saheeba ta zuba da yawa a hannun ta ta watsa mata. Aiko wani irin nannauyan numfashi ta ja mai ƙarfi sai kuma ta sake komawa lagaf. Hankalinsu ne ya ƙara tashi. Saheeba ta ce, “Kodai za'a duba Rafeeq ne”. Da sauri Mamansu dake sharar hawaye ta ce, “ALLAH ya kiyaye, jini Fateema bazai taɓa min yarinya ba wlhy”. Rasama abin faɗa kowa yayi suka sake watsa mata ruwan mai yawa sai gashi ta sake farfaɗowa. Kuka ta fashe da shi tana wani irin zaburowa zata tashi Maman ta maidata, zatai magana nan ma ta rufe mata baki. “Basai kince komai ba dan ALLAH Nuratu, kiyi shiru baki da lafiya”. Kuka ta sake fashe wa da shi mai ƙarfi, wannan kuka ne ya farkar da mutane da yawa duk suka shiga fitowa suma. Nan fa aka zagaye Nuratu. Caraf wata dattijuwar mata ta ce, “Kai yarinyar nan ba lafiya ba tanada iska.” ai jin wannan batu sai su Maman Saheeba suka laƙe, nan fa kowa ya shiga mata tofi, wani ma babu abinda yake karantawa motsa bakin kawai yake yi ya tofa yawu hankalinsa kwance🤣.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣6️⃣
______________
.........Ganin hankalinsu ya raja'a akan Nuratu Haule ta zame jikinta ta fita. Ƙasan bene ta maƙale tai kiran Sille. Bugu biyu ya ɗauka, yanda taji muryarsa kuma ya tabbatar mata da wata macen yake tare. Kishi ne ya turnuƙeta, amma tasan ko giyar wake tasha bata isa yin magana ba, kaɗan daga aikinsa yasa taje har gida yay mata dukan tsiya. Sai kawai ta fara masa bayani cikin rawar murya.. “Dear ya kamata ka baro Lagos ɗin nan tunda ka gama aikin daya kaika ka dawo Abuja, dan abubuwa nata faruwa. Kaga dai anci biki an gama yau ango ya shiga ɗaki ga Nuratu can taje ta jiyoma kanta abinda ya dame ta. Hakama Hajiya Kamila kaca-kaca suka shigo da ita cikin jini, ban sani ba ko itama daga sashen AA ɗin ne oho. Dan Mamar Saheeba da Saheebar sun kima ƙarya. “Naji”. Ya faɗa a taƙaice yana wani shiii da baki na iskanci ya yanke wayar. Duƙewa Haule tai a wajan ta sanya kuka......
__________★
Iskar sanyin asuba ce ta farfaɗo da AA, dan yana kaiwa border shima ya sume. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa wani irin nauyi na masifa. Bishi-bishi ya ke kallon Maanal, sai kuma a hankali ta fito masa a cikin ido. Gabansa ne ya faɗi, ya zabura duk da bashi da wani ƙarfi ya matsa daga jikinta. Hannu ya kai ya kunna lamp ɗin dake side drawer, kafin ya kai yatsarsa sai tin hancinta amma babu numfashi, zuciyarsa ta shiga tsitstsinkewa da rarrabewa, gefen wuyanta ya maida ya taɓa jijiyar wajan, nan ma babu motsi. Ji yay kamar shima zai ƙara sumewa. Sai ya ɗora kunensa a saitin zuciyarta... Bugun da tashi zuciyar take ai tamkar zata faso ƙirjinta ta fito a yanzu. A karo na farko ya yunƙura zai tashi, amma hakan ya gagara saboda wani irin ɗaurewa tamau da cikinsa yay masa. Ga jiri yana ji ga ciwon kai mai tsannanin gaske da bai taɓa fuskanta a rayuwarsa ba. Kan ya dafe da hannu ɗaya, ɗayan na riƙe da cikinsa. Ba irin ciwon cikin jiya bane ba, yanzu ji yake tamkar an ajiye masa dutse ne. Sai da yaja fin minti biyu kafin ya sake yinƙurawa cike da ƙarfin hali da jarumta. Aiko ji yay kamar ya fasa ihu dan azaba, amma ina bazai iya zama yana kallon Maanal a haka ba. Da ƙyar ya miƙe a galabaice ya nufi bayi, ruwa masu zafi ya daidaita ya sakarma kansa na shower. Yafi mintuna biyar a haka sannan yay wanka yay na tsarki cikin ƙarfin hali ya fito yana dafe da cikin nasa, dan ko iya miƙewa da ƙyau baya yi ma. Ga idanunsa kamar zasu faɗo idan ya buɗe saboda ciwon kai. Bashi da kaya a ɗakin, sai dai in wanda ya cire zai maida. Ba kuma zai iya haka ba. Haka ya daure ya fita cikin haɗa hanya ya koma ɗakinsa, jallabiya kawai ya ɗakko ya dawo. Yana ƙoƙarin zama dan ya ɗago Maanal duk da shi yasan da wahala ya iya hakan saboda cikinsa yaga wayarsa na haske. Kamar zai share sai kuma ya tuna Rafeeq yace zai kirashi da asuba. Da ƙyar ya iya kai hannu ya ɗauka, Rafeeq ɗin ne kuwa. Ɗagawa yay batare da yay magana ba, daga can RK ya ce, “Ajwaad!”. Ƙasa magana AA yayi, sai da ƙyar ya ce, “Uhmm”. “Babu dai wata matsala ko?”. Nan ma ya daɗe kafin ya iya furta, “Akwai, bata numfashi sam. Nima kaina da cikina na ciw....” Ya kasa ƙarasawa saboda kansa dake kamar ana bugawa da wani ƙarfe. “Wannan sakamakon dama shi nake tsoratar maka tun jiya. Yanzu dai bara muyi salla gani nan zuwa gidan”. “Uhmm”. Kawai yace ya kife wayar batare daya yanke kiran ba, sai RK ɗinne ya yanke daga can. Duk yanda yake tunanin taimakawa Maanal bazai iya ba, ga salla ana ƙoƙarin shiga. Kuma har cikin ransa bazai iya kiran kowa ba. Dama ace cikin ƴan uwanta akwai wani ko Amaal zai iya sawa tazo ta taimaka mata. Baya son wasa da salla, dan haka ya tashi ya gabatar da ita a zaune. Yana zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe sai dai bai rufesu ba duka yana ɗan kallon Maanal kiran RK ya sake shigowa wayar. Hannu kawai ya kai ya ɗauka, yana ɗagawa RK ya ce, “Zaka iya buɗe ƙofar?”. “Ko sakkowa bazan iya ba”. “Okay ina zuwa, bari na samo keys wajen Aunty. Ka ɗan daure kaɗan saka mata kaya masu kauri, dan zamu shigo ne koda Aunty haka”. “No! Rafeeq kar kai min haka Please ”. “Dole ne ayi hakan Ajwaad, dole ne laifin da kowa ke kallonka da shi na tsawon shekaru ya shafe a yau....” Kafin AA ɗin ya sake magana ma RK ya yanke wayar. Idanunsa ya lumshe tare da cije lips da ƙarfi. Fahimtar babu wani isasshen lokaci ya sashi mikewa cike da ƙarfin hali, closet ɗinta ya nufa, ya samo riga mai kauri sai dai ba wadda zata dameta ba ya fito. Sai da ya ɗan zauna kansa ya lafa kafin ya iya saka mata rigar da ƙyar, ya tattare gashinta dake a baje ya tufke waje guda. Bargon ya sake ja ya rufa mata ya maida hannunsa a goshinsa ya dafe kansa yana kallonta da idanunsa da suka canja launi gaba ɗaya....
★Kai tsaye RK sashen Oum ya nufa. Ƙofar a buɗe take, dan haka ya shiga kawai. Babu kowa a falon ƙasan amma yana jiyo motsin su Mah-mah dake a bedrooms ɗin. Ɗan jimmm yay na tunanin wazai samu, sai Umma ta faɗo masa, tunda koba komai a yanzu tamkar itace uwa a family ɗin kasancewarta matar Baba Sardauna dake matsayin uba. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran layinta. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗauka, gaisheta yay, a ɗan rikice ta amsa tana tambayarsa lafiya dai ko kira da asuba yace ba komai gashi a falo ne... Baima gama sauke wayar ba ƙofar bedroom ɗin tsakkiya ta buɗe. Umma ta fito sanye da zabgegen hijjabi idonta akan RK. Yanda take sauri kamar hijjabin zai taɗeta ta faɗi ya sashi saurin tararta yana faɗin, “Umma relax ba wani abu bane ba fa”. “Ka tayar min da hankali Rafeeq mike faruwa?”. Hannunta ya riƙo ya ce, “Kwantar da hankalinki. Nace babu komai fa. Dama su Ajwaad ne ke buƙatar taimako, dan akwai matsala. Yanzu haka ma nace ya buɗan ƙofa ga doctor nan zata zo amma bazai iya sakkowa daga sama ba dan shima bashi da lafiya. Ita kuma ta suma”. Yanda RK yay maganar kansa a ƙasa yasa Umma tsohuwar arziƙi ta fahimci komai, sai dai kuma zuciyarta ta shiga wasiwasi. Amma batace komai ba tace kawai “Muje”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma yace, “Bara na amsa key wajen Aunty ya kulle ne”. Zama Umma tayi, shi kuma ya haura sama. Kai tsaye bedroom ɗin Oum yay knocking, Hajiya Basariyya tazo ta buɗe. Ganin shine sai tai wani shock. “Rafeeq lafiya kuwa?”. “Lafiya lau Aunty, zan amsa key ɗin sashen Ajwaad ne”. “Key! Wani abu ya faru ne?”. Kafin ya bata amsa Oum tazo wajen jin an ambaci sunan AA. Ganin Rafeeq kuma sai ya sake rikita ta. Ta ce, “Majdiya bashi hanya ya shigo”. Shiga RK yayi, Oum da duk take a rikice tace, “Rafeeq miya faru da su Ajwaad ɗin ake neman key?”. “Babu abinda ya faru Aunty ku kwantar da hankalinku. Ya kulle ƙofar ne kuma bazai iya sakkowa ya buɗe ba. Shi da Maanal ɗin kuma duk suna buƙatar taimako”. Daga Hajiya Majdiya har Oum shiru sukai suna kallon RK cike da nazari, sai kuma suka kalla juna. Oum ce tai ƙarfin halin faɗin, “Bara na ɗauka maka”. Hajiya Majdiya kuwa sai ta jeho masa tambaya. “Rafeeq mike damun su?”. Kafin ya bata amsa nan ma Oum ta dawo, key ɗin ta miƙa masa. Sai kawai ya juya ya fice dan ana kiran wayarsa ya kuma san doctor ce. Yana gama sakkowa Umma dake falo na jiransa ta miƙe, a tare suka fito, Umma ta nufi sashen AA shi kuma ya nufi motar Doctor dan ya faɗama maigadi daman ya buɗe mata. Tana hangosa itama ta fito. Mace ce babba dan zata iya kaiwa ma sa'ar su Oum, ya gaidata da girmamawa sannan suma suka nufi sashen AA ɗin da har Umma ta buɗe ta shige. A falo suka samu Umma tsaye, Doctor Ruƙayya ta gaida Umma cike da girmamawa, itama ta amsa da kulawa tana mata godiyar tasota da akai da sassafe haka. Dan gari ya fara haske zuwa yanzu. Wayar AA RK ya sake kira, yana ɗagawa ya ce, “Gani tare da Umma da Doctor. Ka koma wani ɗakin zan sameka su sai su dubata”. “Uhmm”. AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi. Har ya yunƙura zai miƙe sai kuma ya ɗan matsa ya sumbaci goshin Maanal da lips ɗinta. Murya a shaƙe ya furta, “I'm sorry Bestie. Please for give me. You bloomed in my childhood, and you rule in my forever, my sweet Everbloom. ALLAH yay miki albarka. Yay miki sakamako da mukullin aljanna, ya shayar dake farin ciki na har abada fiye da wanda kika shayar da ni a daren jiya. ALLAH ya hanani ikon munana miki har abada”. Ya sake sumbatar lips nata a hankali sannan ya miƙe da ƙyar. Fita yay yana waiwayenta, shi kaɗai yasan irin nauyin da yake ji zuciyarsa ta masa. Sosai yake jin haushin kansa. Ɗakinsa ya buɗe ya shiga, dai-dai nan su RK ke haurowa, sun kuma ji ƙarar rufe ƙofar da yayi. Sai duk suka fahimci shine, dan haka RK ya nufi can yana nuna musu ɗakin kusa dana AA ɗin. “Inaga tana nan Umma ku shiga. Bara na ganshi shima”. Can ɗin suka shiga, shi kuma yay knocking ɗakin AA, fin sakan biyar kafin ya tura ya shiga. Wutar ɗakin da AA bai kunna ba ya kunna. Can ya hangosa a saman gado ya dunƙule waje ɗaya. Can ɗin ya ƙarasa, batare da yay magana ba ya zauna a kusa da shi. Hannunsa ya ɗauke a hankali daga saman cikinsa daya riƙe, ya maye gurbinsa da nashi ya ɗan danna wajen. Ai da ƙarfi AA ya wani cije lips yana sake matse idanunsa dan azaba. “I'm sorry”. RK ya faɗa a hankali. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaƙi buɗe ido ya kallesa. RK ya ɗan girgiza kai da sake faɗin, “Kanka na ciwo. Kuma da alama akwai zazzaɓi tare da kai”. Shi dai AA bai ce komai ba, shima RK bai damu ba. Sai ma wayarsa daya zaro a aljihu ya shiga kiran wayar Oum. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. A taƙaice ya ce, “Please Aunty zamu samu ruwan lemon tsami da lipton?”. Cikin sanyin murya mai nuna damuwa Oum ta ce, “Za'a samu Rafeeq yaya jikin nasu?”. “Alhamdullah da sauƙi karfa ki damu. A ɗan haɗa da shayi mai kauri sosai cikin yaran nan wani ya kawo min”.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣7️⃣
______________
.........Yana ajiye wayar ya tashi ya fara buɗe kit ɗin daya shigo da shi, wanda Doctor ce tazo masa da shi dan daya kirata ya sanar mata dukkan abinda yake buƙata. Drip ya fito da shi da allurai kusan kala uku, sai syringe guda biyu da kan allura. Allurai yayi a cikin ruwan AA na kallonsa ta ƙasan ido, sai dai zaka iya ɗauka barci ma yake. Amma azaba ce keta nuƙurƙusarsa. Ga sanyi yana ji har cikin cikinsa. Ga ciwon kai da zazzaɓi. Tsaf RK ya gama haɗa komai, ya miƙe yana hanging ruwan a jikin hanger daya ɗakko a closet ɗin AA ɗin akai knocking. Sai da ya ƙarasa sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. A mamakinsa sai yaga Oum ce da kanta. Sai kawai ya matsa mata ta shiga, cikin sauri AA yaja filo ya saka a wajen tare duvet ya rufe jikinsa da bai gama dai-daita ba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci hakan kodan jallabiyar jikinsa mai ɗan santsi ce. Dariya RK ya danne kawai ya kauda kansa, wato shi aka raina sai ba'a rufe ba. Kayan hannun Oum daya amsa ya ajiye, ita kuma ta zauna kusa da AA tana kai hannunta saman kansa da duk jijiyiyin sukai raɗa-raɗa. Muryarta a sanyaye sosai ta ce, “Sannu kaji Auta?”. Tab ɗin, ai ji AA yay kamar ya nutse dan kunya. A karo na farko na rayuwarsa ya kasa buɗe idanu ya kalli Oum. Itama ta fahimci yanayin nasa amma sai ta shareshi. Hannunta ya riƙe cikin nashi, idanun nasa still a rufe murya can ciki ya ce, “Oum ina kwana”. “Lafiya lau! Ya jikin naka?”. Kasa amsawa yayi, RK dai yay murmushi. Ruwan lemon tsami da lipton ɗin ya zuba masa a kofi yana faɗin, “Tashi kasha wannan sai ka sha tea ɗin musa drip ɗin”. Ƙasa motsawa AA yay sai da RK ya taimaka masa, da jikin gadon ya jingina shi, sai lokacin ya ɗan buɗe idonsa dake jajur ya ɗan kallesa, RK ya ɗage masa gira ɗaya. Harararsa AA yay ya amshi kofin kawai. RK yay dariya da faɗin, “Ka dai ji da shi, kana halin ciwo kana masifa da idanu”. Murmushi Oum tai da faɗin, “ALLAH Rafeeq kai ke ja Auta na ƙin yin uba dakai, dan uban banza ne anan”. “Aunty dama ai baƙya ƙi goya masa baya ba, amma wannan yaron da kike gani baida kunya, ba komai zan daina masa dariya”. Harararsa AA ya sake yi. RK ya kwashe da dariya ya ce, “Ka cigaba da hararata zan barka da ciwonka ne”. Shi dai bai sake kulashi ba. Ya gama shan ruwan lemon tsamin ya miƙa masa kofin, tea ya sake miƙo masa. Amma sai ya girgiza kansa alamar bazai sha ba. “Aiko dole kasha wlhy, kuma yanzu nan dan so nake ya saka ka amai. Hakan ne kawai zai bamu abinda muke so a tare da kai”. Lallashin AA Oum ta shiga yi, saboda ita ya daure ya sha fin rabi, aiko kamar yanda RK ya faɗa sai amai ya fara taso masa, da sauri ya kamashi suka wuce bayi. Sosai yayi sa har kamar zai amayar da Kayan cikinsa. RK ya taimaka masa ya wanke fuskarsa da bakinsa suka fito. Sannu Oum keta jera masa cikin damuwa. Shi ko ya wani riƙe mata hannu kamar yaron da bai son gusawa daga jikin mamansa. A haka aka ɗaura ruwan bayan ya masa allurai biyu a hannun ya kumayi biyu a cikin ruwan... Kamar jira barci yay awan gaba da shi cikin sakanni......