Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 94

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 94

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 94: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 94. .......Saƙo ya isa ga Mamy…

4,050 words

.......Saƙo ya isa ga Mamy dai-dai da shigar Saheeba sashen tana kuka. Bata kula su Mamanta dake a falo zaune ba ta danna kai cikin bedroom ɗin Mamy, a lokacin ɗayar mai aikinta tana bata ledar da maigadi ya kawo tace saƙone mai delivery ya kawo. Da ɗan mamaki a fuskar Mamy dake kumbure har yanzu ta amsa ledan, dan tasan ita dai bata da wani order a waje gaskiya. Sannan batai da kowa zai aika mata saƙo ba. Ita duk yau ma bazatace tabi takan waya ba. Zata buɗe ledan kenan Saheeba ta faɗo, su Mamanta da suka biyota biye da ita. Cikin tsawa Aunty ta ce, “K lafiya zaki shigowa mutane kina kuka?”. “Daddyn Naufal ne ya rufe ƙofa wai bazan shiga ba na dawo nan sai ya nemeni”. “To saboda mi?”. Maman Saheeba ta faɗa a harzuƙe. Mamy kam kallon Saheeba kawai take kamar ta samu tv da idonta ɗaya da rabi. Ga ciwon kai da zazzaɓi dan ƙafar nan zugi take mata bana wasa ba, ga inda ta ƙone shima yana damunta. Bata son hayaniyar da suke mata a kai, dan haka ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Kira min shi a waya”. Wayar Mamyn Maman Saheeba ta ɗauka, ta lalubo number Babban Yaya ta kira. Amma mi a kashe ma gaba ɗaya. Wayar ta ajiye ta ce, “Ya kashe wayarsa. Bara na aika a kirashi”. Aunty da abubuwan nasu suka fara daina birgeta kallon Saheeba kawai take. Ita fa gaskiya yau badan kar ace sunbar Mamy cikin wani hali ba da yau zata koma Kano. Wannan abun kunyar ya fara isarta. Ta gode ALLAH da bata da ɗiya mace ƴaƴanta biyu duk maza ne. Kasancewar Mamy ta rigasu aure har AA ma ya girma babban ɗanta sosai. Shiyyasa duk cakwakiyar nan ba sanin ainahinta tai ba..... Dawowar Maman Saheeba a fusace ya katse tunanin Aunty. Cikin hargagi Maman Saheeba ta ce, “To yama bar gidan, ance ya zuba yara a mota sun fice.....” Zata cigaba da magana Aunty ta dakatar da ita. “Nana tunda dai dole zai dawo gidan ba sai ayi haƙuri a jirashi ba. Kunga dai ita ba lafiya ne da ita ba wannan hayaniyar ma ba so take ba muje falo.” Badan Maman Saheeba taso ba suka fice. Mamy ta sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai dai taji sun rufe mata ɗakin sannan ta buɗe, wayarta ta ɗauka da hannunta mai lafiya ta gwada kiran Babban Yayan itama. Amma a kashe, sai kawai ta ajiye. Saukar hannunta akan ledar nan ya sata kallon ledar, ita har tama manta da ita. Da hannu ɗayan ta buɗe, ganin an nannaɗe abu kamar box da leda ne yasa ta ajiye ledar ta fara ƙoƙarin warware box ɗin. Kwaline kuwa, koda ta buɗe cikinsa waya ce kawai ƙarama, sai takarda fara. Wayar ta ɗauka ta danna sai taga ta kawo haske. Kamar jira ake ta danna ɗin kira ya shigo. Kasa ɗauka tai har wayar ta tsinke, aka sake kira. Anan dai sai ta daure ta ɗaga, cike da ƙarfin hali tace, “Wanene?”. “Hajjaju! Hajjaju! Kina tsoron ko kidnapper ne shiyyasa kika kasa ɗauka. To kwantar da hankalinki Mrs Aliyu Darma”. Da mamaki Mamy ta ƙara cewa “Waye kai?”. “Ni ba ɓoyayye bane, musamman a gareki, BABBAN ƊANKI ne da kika manta tsohon shekaru. Amma yau ya dawo ya tuna miki da kansa, da hakkinsa na ɗa dake a kanki. Maimakon na baki wahalar tunani ɗan fara duba ɗayan saƙon”. Ajiye wayar Mamy tayi, zuciyarta na ɗan tsinkewa, ta ɗauka takardar da aka naɗe abu a ciki ta shiga kiciniyar buɗewa abinka da mai hannu ɗaya. Da taga zata sha wahala sai ta yage ta kawai da baki. Hotuna ne suka faɗo har guda biyar. Na farko ta ɗauka kamar mai jin tsoro. Hoton Maanal ne, bata wuce 14-years ba a jiki. Gefenta da ɗan sauran jikin mutum kaɗan an yage sa da alama ba ita kaɗai ce a hoton ba. Kai tsaye kuma Mamy ta gane Ajwaad ne a wajan. Ajiyewa tai batare data fahimci komai ba da farko, sai kuma kamar wadda aka haskoma wani abu a brain tai saurin sake ɗaukar hoton ta juya bayansa. Ai wani irin waro idannunta tayi, sai kuma cikin rawar jiki ta ajiye ta ɗauka na biyu, hoton Jariri ne sabuwar haihuwa a cikin zanin atamfa batik ta da, babu kaya a jikin yaron, daga gani kasan sabuwar haihuwa ne da ko awanni bai yi da haihuwa ba aka ɗauki hoto. Yanzu kam zuciyar Mamy ce ta motsa sosai a cikin ƙirjinta. Ta ƙurama zanin ido zuciyarta na tsitstsinkewa, sai kuma ta kai dubanta ga date ɗin da aka ɗaɗara a jikin hoton tamkar da gayya. A wannan gaɓar jitai tamkar zuciyar tata ma ce ta zubo cikin bakinta, jikinta kam rawa yake sosai, wayar ta ɗauka ta danna kiran Number, bugu ɗaya kuwa a ka ɗaga mata. “Wanene kai?”. Ta faɗa cikin hakki da sarƙewar numfashi. Wata shegiyar dariya Sille yayi daga can, cike da iskanci ya ce, “Ya da ruɗewa haka Mrs Darma, ko har kin gama kallon hotunan ne duka? Idan baki gama ba ƙarasa tukunna”. Ƙit ya yanke kiran. Idan Mamy tace bata jin kamar zuciyarta zata fashe a yanzu ƙarya take, cikin rawar hannu dana zuciya ta ɗauki hoto na uku, yaro ɗan shekara bakwai da babban mutum a gefensa da suke matsannciyar kama. A yanzu kam jikin Mamy tari ne ya sarƙe Mamy mai ƙarfi, ta kalla ƙofa da sauri tana danne bakinta domin hana tarin kanta na wani irin bubbugawa kamar ana dukan ƙarfe da ƙarfe. Lips ɗinta na rawa-rawa ga hawaye na gudu ta furta. “Ju..j... Junaid”. Hoton ya suɓuce a hannunta ya faɗi, tamkar mai tsoron taɓa wuta ta ɗauka na ƙarshe. Matashin saurayi ɗan shekaru kusan ashirin da biyar ne a jikin hoton, tabbas ta taɓa sanin fuskar, amma ta manta a ina ne, kuma yaushe ne??... Dai-dai nan kira ya shigo wayar. Jitai tana tsoron ɗaga ma kiran a yanzu harya tsinke aka sake kira na biyu. Zuciyarta dake bata shawarar ta ɗaga taji wanene shi? A ina ya samo wannan hotunan taci ƙarfinta. Ɗaukar tayi sai dai ta kasa magana. Daga can Sille dake jiyo fitar numfashin Mamy a sarƙe cike da shaƙiyanci ya ce, “Nasan kin gama kallon hotunan nan duka zuwa yanzu Mrs Darma? Nasan kuma kin gane wasu a ciki, musamman Surukarki, Tsohon zumanki, da Jaririn nan”. Sosai jikin Mamy ke ƙara ƙarfin rawa, har tana buge ƙafarta mai ciwo, azabar data ratsata ta sata sakin ƴar ƙara saboda ƙafarta. Daga can Sille dake iya jiyota ya ce, “Relax Mrs Darma, karki ruɗar da kanki. Dan ban baki hotunan dan ki ruɗe ɗin ba. Na tabbatar dukansu suna tare da alamar da zaki tunasu. Idan kuma baki tuna ɗin ba zan baki lokaci ki tuna su daga nan har zuwa 1 week sannan ki banbanta su da tunanin miya alaƙantasu a waje guda, bayan kowanne kinyi AJIYA A DUHU ne a mabanbanta GURBI. Na barki lafiya Mrs Darma”. Ƙittt wayar ta yanke. Ba ƙaramar zabura Mamy tai ba domin son dakatar da shi, amma ina ya kashe, hannunta na rawa tai ƙoƙarin sake kiransa wayar amma switch off. Yunƙurawa tai zata tashi ruɗani ya mantar da ita halin da take a ciki azaba ta ratsata. Ai tuni ta saki wayar tana sakin wata azababbiyar ƙara. Wuff Haule ta shigo ɗakin kamar wadda take jiranta dama. Koda yake jiran nata take a ƙofa kam. Itace ta riƙeta dan ƙoƙarin faɗowa a gado take. Cikin dabara kuma tana tattare hotunan nan ta kwashe da hannu ɗaya, sai da ta kwantar da Mamyn sannan ta duƙa ta ɗauka wayar dake a ƙasa dan idon Mamy a rufe suke sai zufa take. Wayar da hotunan Haule ta tura ƙasan gadon Mamy bada nisa ba sannan ta miƙe tana faɗin, “Hajiya bari a kira su Aunty”. Kafin ma Mamy tai magana Haule ta fice da sauri.....

Fitar Haule dai-dai da shigowar AA da Fawzan sashen. Dan kiran da Oum tai masa ya sashi dole ya baro sashensu. Su Shahidah na shigowa sashen shi kuma yana sakkowa daga upstairs. Cike da gulma suka zuba masa ido, sai da yay gab da gama sakkowar suka fuske kowanne na mamaki a zuciyarsa, dan kaga AA a fuska zaka rantse bazai iya kallon mace ba saboda jin kai. Amma munafukin yama ƴar ƙanwarsu walmakalifatu yanzu ya fito yana wani basarwa. Aunty Sakina kawai ya gaisar, itama dai Amaal dake gimtse dariya ta gaishesa. Ciki-ciki ya amsa zai wuce dan ya fahimci munafuncin dake a fuskokin su musamman Shahidah da Amaal Shahidah ta ce, “Oh ni bazaka gaisheni ba”. Harara ya zuba mata, cike da baƙar magana ya ce, “Sai kin ƙara girma”. Dariya Aunty Sakina ke musu, hakama Amaal ƙasa-ƙasa take tata. Shahidah tai ƙwafa ta ce, “Haka kace ko, zako kasan na girma yau kuwa, dan da Auta zan wuce har sai kazo ka durƙusa ka gaisheni”. Kallonta yay kamar zai yi magana sai kuma yay shiru, a duniya babu wanda ya saka shi gaba kamar mutane uku, Yaya Fawzan, Shahidah, Rafeeq. Ficewa yay batare da yace mata komai ba, sai kuma ya saki murmushi yana cizar lips dan bai ƙyaleta ba, saboda Aunty Sakina da yake jin nauyi kawai ya zaɓi yin shirun yanzu, amma taci bashi. Sashen Oum ya nufa gaisheta ya samu ƴan kano basu tafi ba suma ya zauna suka gaisa shine Oum ke sanar masa Mamy babu lafiya. Ya fito da nufin zuwa duba Mamyn suka haɗu da Yaya Fawzan. Zai fara aikin tsokanarsa shima yaja hannunsa yana faɗin, “Fara rakani na duba Mamy mu dawo zan iya da kai kaima”. Dariya Fauzan yayi, bai musa ba suka nufi sashen Mamyn. Shine suna shigowa suka samu Haule na sanar ma su Aunty halin da Mamyn ke ciki. Ba ƙaramin tashi hankalin AA ya shiga ba da ganin halin da Mamy ke ciki ba. Nan fa ya shiga tambayar Fawzan accident sukai. Babu wani alamar ruɗewa irin ta AA ɗin a tare da Fawzan ya ce, “Aa sunce ta faɗo ne daga stairscase jiya da dare......” nan dai yay masa bayanin komai.........✍️85

........Zama AA yay kusa da Mamyn ya share mata hawayen da yaga suna silalo mata, ga jikinta na rawa. A mamakin kowa sai ta buɗe idanunta tana kallonsa, sai kuma ta sake runtse idanun dan abinda ta jiyo jiya ne ke rige-rigen dawo mata a cikin kunne saboda kallon fuskarsa da tayi. Cikin rawar lips muryar na fita da ƙyar zuciyarta na ƙuna ta ce, “Ajwaad ku kaini asibiti ƙirjina”. ALLAH sarki rayuwa, ɗa mai jinƙai daban yake komai wahalar da kake bashi a rayuwa. Mamy bata gama rufe baki ba AA harya miƙe, layin RK ya fara ƙoƙarin nema. Babu jimawa kuwa ya ɗaga, zai fara tsokanarsa shima AA ɗin ya katsesa da faɗin, “Rafeeq kana ina ne?”. Ɗan jim RK yay daga can, sai kuma ya nisa ya ce, “Ina asibiti. Miya faru?”. “Ambulance! Ka turo Ambulance yanzu ta ɗauki Mamy.” Murmushi RK yay mai sanyi, a ransa yay hamdala dan dama abinda yake jira kenan tun ɗazun, daurewa kawai yake yi amma hankalinsa gaba ɗaya nakan halin da Mamy ɗin ke ciki. Sai dai yasan bazai samu abinda yake fata ba sai AA yaje yaga halin da take a ciki saboda wasu dalilansa. Cikin abinda baifi mintinan ashirin ba Ambulance ɗin ta iso, zuwa lokacin harsu Oum na'a sashen dan abun kamar wani magic jikin Mamy ɗin ya rikice alamar jininta ya haura sama ko gani idannunta basa yi. Su Abah sun fita tun ɗazun, hakama Babban Yaya bai dawo ba. AA da Yaya Fawzan da kansu suka sakko da Mamy ƙasa, sannan aka sakata a abin ɗaukar mara lafiya aka fita da ita. ALLAH sarki Oum baiwar ALLAH, itace ta shiga kusa da Mamy ɗin. Su kuma su AA suka shiga motar Fawzan. Saheeba ma ta ɗauka su Mamansu suka bisu....

_________★

Su Maanal basu san mike faruwa ba. Tana can da ƴan uwanta dan ba ƙaramin farin ciki tayi da ganin yayun nata ba, duk da yanda suke tsokanarta musamman Amaal ita dai tanata ɓoye fuska, har suka gaji suka barta, sun baje mata kayan daɗin da suka kawo mata kowa na wani tattalinta. Sai Ammie da suka kira ta video call suka sha hira. Maanal na kuka Ammie nayi saboda farin cikin yanda abubuwa suka canja, baiwar ALLAH ji take kamar tai tsuntsuwa tazo Abujan ma. Albarka da addu'a babu irin wadda bata jerama AA ba yau harma da Maanal. Sunyi hirarsu cike da farin ciki da shaƙuwa. Maanal nata zubama Ammie shagwaɓa wai tana son ta tazo Kaduna idan ta warke sai ta dawo. Ammie dake murmushi ta ce, “A'a Auta kiyi zamanki a ɗakinki kinji, ko sashen Aunty ban yarda ki koma ba balle Kaduna. Kefa yanzu kin girma, kiyi zamanki gidan aurenki kima mijinki hidima. ALLAH yay muku albarka ya baku zuri'a mai albarka kinji. In sha ALLAHU zanzo bikin Fawzan ai nan da sati uku”. Murmushi Manaal tai mai sanyi, cike da shagwaɓa ta ce, “Amma Ammie a wajena zaki kwana ko?”. Dan kawai Ammie ta kwantar mata da hankali sai tace eh. Aiko hakan yama Maanal ɗin daɗi sosai. Bayan sunyi sallama da Ammie suka koma hira a tsakaninsu, hirar da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne akan batun fyaɗen nan, Amaal ta sanya Maanal gaba da sabuwar tsokana. Tun tana ƙyaleta harta fara ramawa, suka fara tsiyar tasu ta sako-da-sako. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa Giro da babbar salla. Dan Maanal ta rantse sai taje ta maidama Gwaggo da kaf mutanen gidansu murtani babu fashi. Yanda tayi ɗin ya tabbatar ma su Amaal ƙanwarsu ta dawo ainahin Maanal ta shekarun baya data mutu. Aiko ɗari bisa ɗari suka bata goyon baya akan wannan ƙudirin nata, sun kuma roƙi Aunty Sakina kada ta gayama Ammie dan sai sun dawo zasu sanar mata karma ta hana su. Ta tabbatar musu bazata faɗa ba, kuma tana goyon bayan zuwan nasu itama.... Sai da sukai Magrib sukai ƙoƙarin tafiya, a lokacin ne Hajiya Shuwa ta shigo yima Maanal gashi take sanar musu ai an tafi da Mamy asibiti jikinta ya rikice. Mamaki ya kama Maanal dan sai lokacin ma ita take sanin Mamyn bata da lafiya gaba ɗaya...

★Matuƙar sanyi jikin Auntyn su Mamy yayi da ganin yanda RK ke tsaye akan al'amarin Mamyn tunda suka iso asibitin, dan cikin ƙanƙanin lokaci likitocin da zasu dubata sun rufu a kanta. Sai taita kallon Maman Saheeba da tace bata yarda a kira Rafeeq ya duba Nuratu ba tun a jiyan. Itama kuma Mamyn da akace a kira Rafeeq ya dubata da safe catai bata yarda ba. Ta maida kallonta kan Oum datai shiru damuwa kwance a fuskarta, AA da Fawzan sun sakata a tsakkiya suna lallashi. Sai Auntyn taji kamar ta fara jin kunyar kanta. Anya kuwa babu gyara akan al'amarin su na ƙin baiwar ALLAHn nan Hajiya Fateema. Koba komai fa itace sanadin shigiwar ƴar uwar tasu a wannan daular. To wai miyema aibunta da suke zaginta? Ƴar uwarsu fa ce da kanta ta ɗauka yaran ta bata..... Wannan tunani shine danƙare a zuciyarta har RK ya fito yana sanar musu karaya ce fa a ƙafar Mamy, sannan akwai ƙonewa a jikinta... A tare Oum da Ya Fawzan sukace, “Karaya da ƙonewa kuma?”. Sai suka juya suna kallon su Maman Saheeba alamar tambaya. AA kam yama gagara cewa komai. Cikin ƙarfin hali Oum ta ce, “Aunty amma bakuce mana da ƙuma ba ai, batun karaya nasan maybe wancan likitan ne bai san aikinsa ba”. Cikin ƙarfin hali Aunty ta ce, “Wlhy bamu san da ƙunar ba muma Oum Fawzan (da haka take kiran Oum kafin Mamy ta nuna bata so). Amma tabbas tea ya zuba mata a jiki babu kuma wanda yay tunanin zai ƙonata, ita kuma batayi magana ba”. RK ne ya ce, “Ai shi ruwan zafi ba'a rainashi gaskiya. Yanzu dai an kira wanda zai yi ɗorin karayar kun san mu anan asibitin muna aiki da ɗorin karayar gargajiya ne saboda mai yi mana aiki na wannan fanin yasan aikinsa. Zamu jirashi dan yana a suleja ne. Amma gaskiya likitan can da kuka kira ya dubata bai san komai ba, kuma da ƙafar nan takai wasu kwanaki a haka komai zai iya faruwa. Dan haka ina baku shawara ku kiyaye, kusan da waɗanne irin likitoci zakuyi mu'amula musaman wanda kuke iya kira gida su muku aiki.” Daga haka ya juya ya fita ransa a ɓace. Ita kanta Oum ranta ya ɓaci, dan tun ɗazu dama yanda sukai ɓoye-ɓoyen halin da Mamyn ke a ciki yanata mata kai-kawo a zuciya. A ganinta mizaisa suyi hakan? In dama ƙaramin ciwo ne sai ace. Shi kansa Abah ta fahimci ransa a ɓace yake. Ture tunanin tayi daga ranta gaba ɗaya ta ƙyautata musu zato kawai da yardar ma zuciyarta abinda suka faɗa a ɗazun. (Wannan shine babbar halayyar Oum dake saka mata kwanciyar hankali akan zamanta da kowa, take kuma iya hakuri da dukkan jarabawarta. Tana da ƙoƙarin ƙyautatama mutum zato. Ko abu akai mata a gabanta mara ƙyau kai tsaye bazata saka jin zafin mutum a ranta ba, sai taita kawo uzirin maybe kaza ne, ko kaza yasa yay haka. Sai kaga zuciyarta ta samu salama da kwanciyar hankali. Mu gwada kasancewa haka zamu sha mamaki wlhy koda akan mazajen aurenmu ne ma🙏😀). Waya ta ciro ta kira Abah ta sanar masa komai. Yace mata suna masallaci idan sun idar da salla zasu zo. Daga haka ya yanke kiran. Mamaki ya kamata jin babu wata damuwa a cikin muryarsa. Amma sai ta ture tunanin kawai. Ta kalla su Fawzan tace suje suyi salla suma....

Sai bayan sallar isha'i mai ɗori yazo, lokacin suma su Abah na asibitin harma da Babban Yaya. Su Hajiya Majdiya da su Umma ma sun iso asibitin jin shiru su Oum basu dawo ba. Ƙafar Mamy tayi tsami sosai, ta yanda ana taɓa ƙafar sai da ta saki wani ihun da har reseption sai da aka ji. Ashe ma karaya har biyu ce ba ɗaya ba. Dole sai da su AA suka shiga aka riƙeta, a haka ma RK yaji tausayinta an mata wata allurar kashe zafi. Sumarta biyu dan azaba. Su kansu su AA ƴan riƙeta sunyi sharkaf da zufa duk da acn dake a ɗakin. Shima hannun an gyara mata, shi kam targaɗe ne. Matuƙar tausayi dole ta baka. Allurar barci aika mata bayan sun farfaɗo da ita. Ganin ba wani abu ake buƙata ba RK yace zasu iya tafiya gida tunda anyi gyaran. Dan allurar da sukai mata ta awa goma sha biyar ce, ita da farkawa sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Auntyn su Mamy kawai aka baro a asibitin, sanda suka iso gida sha biyu saura. Kowa sashensa ya nufa, Saheeba tabi Babban Yaya, wani kallo daya watsa mata bama tasan ta tsaya cak ba. Dama mamarta ce tace ta bishin. Aiko bataga fuska ba dole ta wuce sashen Mamyn duk da hararar da maman tata ke mata.....

_______★

Tun bayan fitar Hajiya Shuwa hankalin Maanal a tashe yake, ta kira wayar Oum ba'a ɗaga ba. Ta kira ta AA shima haka. Ta kira Yaya Fawzan shima bai ɗaga ba sai taji matuƙar damuwa da tunanin ko dai wani abu ne ya samu Mamyn. Dan yanda Hajiya Shuwa da su Didinta suka bata labarin halin da Mamyn ke ciki abin ya tsaya mata a rai. Tun tana kallon agogo da cigaba da kiran AA harta sare, a haka ta lallaɓa ta fito falo, ta window ta leƙa compound babu kowa sai hasken fitulu, motocin gidan ma duk an fita da su sai huɗu kawai dake a lulluɓe, sai maigadi na gyangyaɗi gidan shiru sosai. Har zata saki labulen idonta ya sauka akan Nibras dake tsaye a barandar sashensu ta upstairs. Idanu ta zuba mata sai taga gaba ɗaya hankalinta na'a sashensu ne. Tsaki Maanal taja da faɗin, “Wawuya”. Ta bar wajen. Sai kawai ta sakko ma falon ƙasa cike da dauriya, a hakan ma da sauƙi dan tana jin daɗin gashin nan na Hajiya Shuwa. Anan ta kwanta cikin kujera, tun tana kallon agogo har barci ya saceta... Tunda AA ya shigo idanunsa suka sauka a kanta. Zuba mata su yay shiru yana kallonta na tsawon lokaci. Sai kuma ta bashi tausayi. Ƙarasowa yay inda take. A nutse ya saka hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta. Sama ya haura da ita yana tafiya a hankali dan kar ta tashi. Har ko ya kwantar da ita a gadon ɗakinsa bata farka ɗin ba, duvet yaja ya lulluɓa mata tare da duƙowa ya sumbaci lips ɗinta da goshinta sannan ya wuce closet ɗinsa yana cire kaya. Sosai yake jin damuwa akan halin da Mamy ke ciki, haka ya samu yay wanka yayo alwala. Shafa'i da wutri yay ƙoƙarin yi, yana idarwa kiran Oum ke shigo masa. Ɗagawa yay, Oum tace ga abinci nan zata saka a kawo musu hankalin kowa a tashe an manta ko Maanal ba'a kawoma abinci ba........✍️ 86

........Maanal ɗin ya kalla, sai kuma cikin taushin muryarsa dake fita ƙasa-ƙasan nan ya ce, “Oum tama yi barci ita, kawai a barshi nima na ƙoshi zan sha shayi dare ya riga yayi”. “Auta kasan bana son zama da yunwa ko, itama zata iya farkawa anjima ta nema abincin”. “Oum ALLAH bana jin yunwa, itama kuma inta farka sai ta sha tea ɗin kiyi haƙuri”. “Shike nan ALLAH ya tashemu lafiya”. Sallamar yay mata shima ya ajiye wayar yana miƙewa. Shima baibi takan tea ɗin ba ya nema wajen kwanciya dan barci ne a idonsa sosai. Sai dai me yana kwanciyar ya saka Maanal a jikinsa sai yaji kuma yanayinsa na sauyawa. Sosai yake jin buƙatarta, amma ya danne da tsiya-tsiya kodan bayanin da RK ya masa akan dole ya kauda idonsa akanta harta warke. Sannan shi a kanran kansa tausayi take bashi sosai. Dan yasan jiyan nan bai mata da wasa ba sam. Da ƙyar ya samu yay barci, gabannin asuba kuma ya sake farkawa a yanayin matsuwa sosai, sai kawai ya shiga bayi ya shashsheƙa ma kansa ruwa yayo alwala yazo ya hau nafilfili da karatun Alkur'ani. Hakanne ya bashi ƴar nutsuwa har lokacin salla yayi. Sai da ya tada Maanal ya taimaka mata tayo alwala sannan ya fita salla.....

_________★

1 WEEK LATER

Alhamdullahi satin AA guda ke nan cur da angwancewa. Ba ƙaramin dauriya yay da juriya ba na kauda kai akan Maanal ba. Idan ka cire ɗan sumbatarta iya lips hatta kissing ɗinta dainawa yay, dan tunda yay hakan a washe gari bayan ya dawo sallar asuba ya ƙare da ciwon ciki bai sake kwantatawa ba. Sauƙinsa ma ciwon Mamy da zaryar zuwa dubata asibiti tana cimasa lokaci. Idan kuma ya dawo gida sai ya hau aikin office. Hakan bai damu Maanal ba dan itama harga ALLAH tana son ko zai nema wani abu kuma daga gareta to ya kasance ta warke tas kamar yanda kullum Hajiya Shuwa ke gargaɗinta, dan ta kula shauƙin soyayya na ɗawainiya da yaran. To Alhamdullah gashin da take mata ya taka rawar gani sosai ga kuma jikinta baya riƙe ciwo a cikin kwana huɗu ma zaren ɗinkin ya gama fita tas a jikinta. Sannan bata jin zafin komai sai ma wata nutsuwa ta musamman. Zuwa yau da take cika sati kam ras take jinta, kamar yanda doctor da tazo ta duba ta ma ta tabbatar ta warke sarai, dama tun shekaran jiya Hajiya Shuwa tace ta ga warke ɗin. Amma tai gum da bakinta. Zuwa yanzu kam dai su kaɗai ne a gidan nasu. Sai Auntyn su Mamy dake jiyyarta ita da Maman Saheeba dan an sallamota yau kwana biyu kenan zata ƙarasa jiyya a gida, badan ma jininta da yaƙi sauka ba su RK nata fama da kwana uku zatai su sallameta a asibitin, anyi-anyi ta faɗi mike damunta taƙi. Da ƙyar dai da lallashin da AA ke mata da kulawa aka samu jinin nata ya dai-dai shine aka sallamosu. Fuskarta ta saɓe raunikan sun warke, hakama hannunta har an kwance ƙafarce kawai dai da ɗaurin karaya, itama nan da kwana biyu ake saka ran kwancewa saboda bata da ƙan jiki. Maganar hotunan nan kuwa da sun zo mata a rai sai ta turesu da tsiya-tsiya. Kai da ka ganta kasan abin duniya ya isheta. Amma sai kowa ke ɗauka ciwon ne, itako ita tasan tashin hankalinta.

Readers Also Read