Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 105
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 105: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 105. Tabbas badan halin da take ciki ba,…
3,135 words
Tabbas badan halin da take ciki ba, ga kuma su Oum yasan duk zaman jiran fitowarsu suke, da yau babu abinda zai hanashi yin abinda ransa yaso. Tunda ga abinda ake hanasa gani da ɓoye masa available. Amma ba komai, idan kere na yazo zabo na yawo ai ya tabbatar za'a haɗe wataran. Maanal kam tunda ta fahimci abinda ke faruwa ta shige jikinsa kawai ta rungumesa duk dan hanasa kallar mata jiki. Hawaye kam sun cika mata idanu. Ga jikin nata babu karfi kona sisi. Da ƙyar ta yarda ya saka mata bathroom, ƙasan zuciyarsa kuma yana tunanin shi ya zai yi da kaya suna a ɗakin Oum ne fa. Karo na farko yaji wata kunya mai girma ya baibayesa, kai ya ilahi shine dayin wanka yau a bayin Oum tare da Mace. Rashin makama ya sashi jan towel ya ɗaura ya ɗakkota suka fito, dan ya tabbatar kowa babu a ɗakin. Aiko babu kowan, sai kayansa da ya gani a saman gado an ajiye. Ajiyar zuciya ya sauke, yasan Babban Yaya ko Ya Fawzan ne da wannan aikin. Bai ɓata lokaci ba ya shirya, itama ganin tana rawar sanyi duk da ruwan zafi ya saka musu sai yay saurin duba mata kaya ya saka masa masu kauri. Dai-dai nan akai knocking, sai kawai ya bada izinin shigowa. Oum ce sai RK biye da ita. Kawai sai ga Mamy ma ta shigo. Aiko dai-dai AA na maida hankali ga RK dake masa magana idonsa ya shiga cikin na Mamy, wani mummunan kallo kuwa ta zuba masa mai kaɗa hanji, haka kawai sai abin ma shi ya bashi dariya. Amma dai baiyi ba ya ɗauke idanun nasa tare da kaiwa zaune kusa da Maanal dan RK yace ya zauna ne ya mata komai da kansa. Oum ma na zaune ne ta ɗaura kan Maanal a cinyarta. Komai AA ya mata, RK na nuna masa yanda zai yi. Batare da damuwa ba RK ke faɗin, “Ka saka mata iya drip ɗin nan kawai da zai tsaida aman ta kuma samu ƙwarin jikinta. Dan bai kamata tasha kowanne magani ba ko makamancin hakan saboda kar ai ɓarna har sai zuwa safiya anyi gwajin ciki sannan”. Juyowa AA yay yana kallon RK, shima da yake kallonsa yake sai ya ɗaga masa gira. Ƴar harararsa AA ɗin yayi, shiko ya sanya ƴar dariyar mugunta, ba kuma dan kowa yayita ba sai Mamy, saboda yaga kallon data jefama AA sanda ta shigo. Sannan duk da shi ba likita bane fannin mata yasan babu wani ciki da Maanal keda galabaitar dogon azumin da sukayi ne dana wahalar tafiya, kuma sai ana kai azumin tasha ruwan sanyi maimakon na zafi, ta kuma sha shi da yawa sosai... Tsaf AA ya ɗaura mata ruwan, atake kuwa barci yay awan gaba da ita. RK yace a cire towel ɗin da aka naɗe mata kai da shi a busar mata da shi saboda mura. Daga haka ya fita a ɗakin. Su Abah ne da Babban Yaya da Ya Fawzan da sauran matasan yaran suka fara shigowa suka dubata. Ganin tana barci sai suka fita. Suma matan suka shigo, dai-dai lokacin AA ke amsar hand-dryer a hannun Oum yana faɗin ta barshi yayi sunje suci abinci tunda ta samu barci. Oum bata musa ta bashi, haka ya zauna abinsa batare da tuna akwai Mamy a ɗakin ba, balle matan yayunsa da ƙannensa ya ɗaura kan Maanal a cinyarsa ya fara busar mata da gashin a nutse tamkar ba shi ba. Ai sagade Saheeba da sauran sukai suna kallon ikon ALLAH. Zuciyar Nibras kam tamkar zata fashe dan bugun da take yi. Nuratu kuwa ji take kamar ta je ta daɓama Maanal dake barci wuƙa a ƙirji. Suko su Najma abin birgesu yay, Yaya AA sarkin ɗaure fuska da bayama kowa magana ne yau yake busar ma da mace kai. Tab ɗin abin dole ya zama mai ƙayatarwa. Yako zama ɗin, dan sunji sunama kansu addu'ar samun irin hakan daga mazajensu. A haka Oum ta kaɗo kansu duka suka fito domin cin abinci bisa umarnin Abah daya leƙo. Gaba ɗaya Mamy jitake juwa na ɗibarta, dan haka batai zaman cin abincin ba tace zataje ta ɗan watsa ruwa tukunna. Oum zatai magana Abah ya wani riƙe mata hannu ta yanda duk yaran bazasu gani ba. Da mamaki ta kallesa, sai kawai ya wayance ya ce, “Zarah na kodai mun kusa ganin jinin autanki ne?”. Murmushi Oum ɗin tayi, cikin raɗa ta ce, “Haka nake fata Gadanga. Shiyyasa ƙaninka yace baza'a bata komai ba sai anyi gwaji an tabbatar”. Murmushi mai faɗi Abah yayi. Ya sake ɗan matsa mata hannu. Tana ganin Babban Yaya ya juyi zaiyi magana ta zame hannun nata da sauri. Mamy data kasa tafiya tana kallon komai sai hawaye suka wani gangaro mata zuuuu-zuuuu. Wai ita kam yaya zatai da Fateema a rayuwarta ne? Ga kuma wani bala'in da bata taɓa tunanin tsintarsa anan kusa ba saboda yanda tasan Ajwaad na mata biyayya, amma sai gashi yaje ya kwanta da yarinyar nan harda ciki..... Tana shiga bedroom ɗinta ta zube a gado ta fashe da kuka kaikace mutuwa akayi mata, dan wlhy ta jima a rayuwarta bataji abinda ya nema fasa mata ƙirji a lokaci guda ba irin wannan al'amarin. In har Maanal ciki ne da ita, kuma cikin na Ajwaad ai Oum ta gama cinta wasa a wannan gaɓar, ita kuma abinda bazata yarda da shi ba kenan, dan haka ta rantse da ALLAH sai cikin nan ya zama JINI mai gudana a saman tiales ɗin banɗakin Fateema. Da wannan alwashin ta ɗauka waya tai kiran number Maman Saheeba. Tsaf ta zayyane mata komai, ita kanta Maman Saheeba ɗin sai da zuciyata ta sake wani girgizar tashin hankali, dan dama Nuratu ta kirata tana kuka take faɗa mata, sai dai bata fahimci komai ba saboda kukan da Nuratu ɗin ke yi. Ta kuma kira Saheeba bata ɗaga ba, da'alama wayar bata a kusa da ita.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣0️⃣
______________
........Numfashi mai ƙarfi taja, kafin cike da makirci ta ce, “Haba Aunty wannan har wani abin tada hankali ne har kina saka kanki kuka. Yo ALLAH na tuba cikin mi! Cikin ma da ƙila bai wuce kwanaki ba, kinga ko ba buƙatar zubarwa ake ba lalatashi kawai zamuyi cikin sauƙi”. “Nana ta yaya? Yarinyar da bata taɓa cin abincin sashena ba tunda tazo. Ke ni zan ma iya rantse miki ban taɓa zaman minti goma da ita ba”. “Wannan duk ba damuwa bane, ai azumi akeyi, kuma a irin lokacin nan abinci nasan duk a tare kuke yinsa, wannan aikin Saheeba ce zatayi mana shi, bama yanzu ba sai bayan salla. Sannan ya kamata Aunty kima Ajwaad tsiya gaskiya. Munafiki yana sum-sum da kai kamar bazaka saka masa yatsa a baki ya ciza ba amma yasan yay ma mace ciki. Idan wancan na farko yace kuskurene wannan kuma fa? To wlhy sai kin fito masa a mutum sannan, idan ba haka ba ko mun lalata cikin ma a banza tunda ba kunyace da shi ba zai iya sake mata wani a gidan kuna nan sake da baki, wama ya sani ko tun kafin su tafi Chaina ɗin yay wannan ɗin tunda shi dama taƙadari gagararren yaro n.....” “Uhmmm Nana! Please a dinga sassauta irin tsauraran kalaman nan akan yara basu da amfani, duk da Ajwaad nada taurin kai a kaf yaran nan babu wanda nake iya lankwasawa cikin sauƙi irinsa. Su da suka sha daga jikin nawa ma ya fisu min biyayya..” Sosai kalaman Mamy suka daki zuciyar Maman Saheeba, sai ta fahimci lallai dole ta dinga gyara kalamanta tunda har ƴar uwar tata ta fara nuna ranta ya sosu akan zagin Ajwaad da tayi. Cikin ɗan gyaran murya a fili ta ce, “Hakane aunty kuma kiyi haƙuri raina ne ya ɓaci wlhy. Kin san yaran nan da son fusata mutum. Ni dai yanzu abinda kawai nake gani kenan. Mu lallata cikin sannan ki ja masa kunne tunda wancan bai shigesa ba. Shima Fawzan kin masa maganar Amani ɗin kuwa? Wlhy yarinyar nada hankali Aunty, sannan tafi Nibras komai, ƙyan jiki, ilimi, harma da tarbiya. Itama dai uwarta ba wasa ba wajen kuɗi. So nake wlhy mu rikita zuciyar matar nan ai auren rana ɗaya dana Ajwaad da Nuratu..” Fuskar Mamy da murmushi ta ce, “Karki damu zan masa magana shima yau ɗin nan. Dama na bari ne ya nutsu naga kwana biyu yanata kai-kawo na kwangilar nan daya samu. Ki tura min hoton yarinyar ma kada na manta”. Cike da farin ciki Maman Saheeba ta ce, “In sha ALLAHU yanzu kuwa aunty. Harma da no ɗinta”. Daga haka sukai sallama Mamy na sauke ajiyar zuciya. Sai taji ɓacin ran nata ya ragu sosai. Shiyyasa take ƙaunar Nana sosai......
__________★
GIRO
Zaune Gwaggo take ta zabga tagumi abin duniya ya isheta, yau ko abinda zasu ci basu da shi. Tunda Sule ya tattare ƴan sauran kuɗaɗen wajen Sen... Suka koma ƙarƙaf, ga Babu bashi da lafiya sosai. Haka kawai sai ya yanke jiki ya faɗi. Sun ɗan kira mai camix ɗin garin ya dubashi yace ulser ce ke damunsa, sai kuma hawan jini. Nan dai ya ɗan bashi magunguna yay masa ƙarin ruwa. Daga nan ne ma yake ɗan samu ya fita zuwa ƙofar gida. Amma daga ba nan ɗin ba baya iya doguwar tafiya, dan ko azumi ma baya iya yi. Kai zata iya cewa ma itace kawai mai yin azumin a wajen, dama ba'a maganar Haƙila da Sule, Sailu ko ta murje idanunta tace itama ulser gareta mai zafa bazata iya azumi ba. Dan haka da rana sai su dafa abinda ransu keso ita da yaranta suci, ko Babu sai sun gadama ma suke bashi. Itako in aka sha ruwa sai wanda yaga ALLAH yaga Annabi ya sammata kunu a gidan. Shi dama Baba ba magarsa ake ba, sauran matan nashi ma suke cida kansu. Sauran ƴaƴanta kuwa na ma'auri suma taimakon suke nema, tunda dama dai Babu ɗinne taƙamarsu a baya, tunda komai ya suɓuce kuma suma suka shiga halin shiga ukun. Haƙila ce ta shigo wajen tana taunar cingam tana waƙe-waƙe, kanta ɗauke da botikin cin-cin da take yi na sayarwa. Duk da azumi ne haka take fita da shi talla, idan akai magana tace yara take saidawa ai. Ko suma yaran azumin suke. Rashin mutuncin Sule dama ita Haƙilar kanta da uwarsu kesa babu wanda ya iya cigaba da magana. Dan suma mazan gidan yanzu tsoronsu suke ji. Muƙut Gwaggo ta haɗiye yawu tana bin botikin cin-cin ɗin Haƙila da kallo duk da azumin da take. Haƙila ko ko kallonta batai ba ta shige ɗakinsu ta ajiye botikin, babu jimawa ta fito da ɗaurin ƙirji alamar yin wanka, sai ƙunƙuni take a ranta wai Temo... ya bata wahala, shege gashi ba wani kuɗin kirki yake bata ba. Duk yanda zai gurjeta baya iya wuce dubu biyar yace ta bishi bashi. Kullum kuma aikin kenan, ita kuma tana zuwa ta bashi kanta ne kawai saboda yana mata yanda take so. Temo... Dai inyamuri ne irin masu shiga ƙauyukan nan su buɗe shago, sunansa Temoty ne. Mutanen Giro ke kiransa Temo.... Temo shine ya fara keta budurcin Haƙila saboda shegen kwaɗayinta, tun tana shan wahala harta goge, dan gaba ɗaya har zuwa yanzu shekarun haƙila basu wuce goma sha ba. Kai ko ƙirjin ma yanzu ne yake bayyana a jikinta sosai, ƙwailayen ma bata gama cika cif-cif ba amma idonta ya buɗe. Dan yanzu har cikin Suru samarine da ita kala-kala. Abin tausayi ga rayuwar yarinyar nan indai ta fita a gida to yini take daga ɗakin wancan saurayi zuwa wancan kango ko gajiya batayi, ba kuma komai ya sata zama karyar maza ba sai shan magunguna kamar ba yarinya ba. Sarai Sailu ta jima da sanin Haƙila nabin maza, amma kuɗaɗen da take kawo mata da ɗan shayi da burodin baba kalla da indomie da tsire yasa ta kasa yin magana. Kai bama ita ba matan gidan kansu sun sani, tsoron Sailu ya hana su cewa uffan... Gwaggo na ganin Haƙila ta shige bayi ta miƙe da sauri ta afka ɗakin. Cin-cin ɗin ta ɗebo a cikin zani ta fito, jikinta na ɓari ta afka ɗakinta ta ɓoye. Ta goge hannunta da man cin-cin ɗin ya ɓata ta dawo ƙofar ɗakin ta sake zama kamar batai komai ba. Babu jimawa kuwa Haƙila ta fito ta sake wuce Gwaggo. Tana ko shiga ɗakin su sai gata ta fito kamar an jehota. Zaram Gwaggo ta miƙe abinka da mara gaskiya, gashi data ɗauka cin-cin ta manta ta rufe botikin. Wani irin cin kwallar Gwaggo Haƙila tayi cikin ƙaraji kamar sa'arta tace, “To tsohuwar banza bani kuɗina, munafuka ɓarauniya”. Muryar Gwaggo har rawa take, “Kudinki kuma haƙila, ni na ɗauka miki kuɗi ne?”. “Wlhy zan iya sharara miki mari anan gurin kema kin sani, idan baki ɗauka min kuɗi ba ai kin ɗauka min kayan kuɗi ƙaramar ɓarauniya dako satar baki iyaba ma. Ban kuɗin cin-cin ɗina inba haka ba wlhy na saki zanen nan anan nai tsirara mu daku.....” “Haƙila! Haƙila! Uwar tawa kika shaƙema wuya haka kina jifanta da sunan ɓarauniya?”. Babu ne dake shigowa yay maganar. Baki sosai Haƙila ta gatsina, cike da tsiwa da rashin girmama iyaye tace, “Yo Babanmu ita taja, daga fa shigata wanka ta afka ɗakin Innarmu ta ɗiba min cin-cin, itama ba haka take kiranmu ɓarayi ba, bayan kuma a wajenta muka gaji satar tsohuwar alakwankwan kawai”. Wani irin runtse idanu Babu yayi ƙirjinsa na masa zafi. Cikin rawar murya ya ce, “To kiyi haƙuri ki saketa. Gwaggo miyasa kika taɓa mata kaya?”. Kuka Gwaggo ta fashe da shi itama. Dan harga ALLAH taji shaƙar nan ta Haƙila. “Yanzu Habibu ka yarda da maganar ƴarka kenan na ɗauka mata cin-cin ɗin?”. “To Gwaggo ni mizance. Kinga fa ranar sai da nai miki nasiha akan al'amarin Sule da Haƙila a gidan nan, na nuna miki ki daina shiga sabgarsu su ba kamar su Shahidah bane da kike iya tankwarawa. Uwarsu kuma ba kamar Asiya bace da zatai miki kawaici ta kauda ido. Kika min alƙawarin dainawa gashi tun ba'aje ko'ina ba kunayi.” “To wai dama kai baba kana tunanin wannan kilakakkiyar tsohuwar zata kama kanta ne a cikinmu. Mu dan ALLAH ma ka daina mata wata nasiha ka barmu da ita mu gurji ruɓaɓɓen bakinta da baya iya shiru jarababbiya kawai. Kuma wlhy sai kin biyan kuɗin cin-cin ɗina ko kuma yanzu na kira Hure dilalliya tasai tsohon gadon ɗakinki a kuɗina”... “Ai bama sai kin kira Hure ba ni kaina muyi ciniki ƙanwata dama na gaji da kwana ƙasa cinnaku namin walmakalifatu.” “To shike nan ma Yaya Sule”. Haƙila ta faɗa tana sakin wuyar rigar Gwaggo. Ƙarasowa Sule yay ciki batare da ko kallon Babu yayi ba, dan shi bama ya magana da Babu saboda ya masa faɗa gaba yake da shi. Gwaggo da Babu na tsaye kamar gumaka su Sule suka shiga ɗakin Gwaggo. Gadon ƙarfenta ƙarami suka ɓallo, bayan sun zazzage mata katifar rimi dake kai da ƴan tsummokaranta. A gabanta, a gaban Babu sukai cinikin gado Sule ya bama Haƙila kuɗi yace ta tayasa su kafa gadon a ɗakinsa dake tsakanin na Gwaggo da na uwarsu. “An gama babban yaya, amma tsaya abama Baba la'adar ganin ido mana”. Haƙila ta faɗa tana matsawa kusa da Baba ta saka masa ɗari biyu a aljihu, tako zo kim-kim suka kama gado zuwa ɗakin Sule suka haƙa. Katifarsa da taima gadon yawa dan ta 6by6 ce daya sato a wani gida haka suka ɗorata a gadon. Ya haye ya wani baje yana sauke numfashi. Itama Haƙila hawa tayi tana faɗin, “Yaya bara na ɗana nima”. Dariya ya sanya da faɗin, “Ƴar son banza, ai ni wannan satar cin-cin tamun rana. Wai ina babarmu?”. Baki haƙila ta taɓe, “Kaima ka sani tana can biye-biyen ƙauyuka wajen malamanta neman asiri”. “Ko kuma masu danneta ba”. Dariya Haƙila ta sanya, cike da shaƙiyanci tace, “To kaga laifinta ne, Baba ya riga ya ruɓe dole taje inda zata samu ƙarfi. Nidai tsorona kawai karta kwaso mana ciki wani susu can. Amma bari nasan maganinta, maganin hana ɗaukar ciki zan dinga jefa mata a ruwa bata sani ba”. Dariya sosai Sule ke kwasa. Kai bakace hirar uwarsu mahaifiya suke yi ba..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣1️⃣
______________
.........A waje kam jiri ne ya nema kwasar Gwaggo, sai da Babu dake hawaye ya kamata ya zaunar sannan. Zama yay shima kansa a ƙasa yana kuka yace, “Gwaggo kinga sakamakon ko? Ni nasan hakkin Asiya bazai barmu mu zauna lafiya ba, hakkin ƴaƴana bazai barmu mu zauna lafiya ba. Baba Umar ya min komai na gatan rayuwa shi da Mama Lubabatu. Amma suka tafi suka barni da ƴarsu ɗaya jal na gagara riƙe amanarta, na cinye dukiyarta, na wulaƙantata, na ƙuntata rayuwarta, haka nake hanata hakkinta saboda karuwaina, nazo a ƙarshe ma nace ƴaƴan da muka haifa ta hanyar sunna ba nawa bane ba. Gwaggo duk kece kika ɗorani akan hakan, kika takura sai na auri Sailuba wai dan tayi maganin Asiya. Yau gashi ba maganin Asiya Saulu keyi ba maganinki da ni take yi ita da ƴayanta. Jiba yanda na koma, kamar ban taɓa sanin a daga ilimi ba, kamar ban taɓa rayuwa a birni ba, kamar ban taɓa yin aiki ba wai aikin ma na ƴan sanda harda matsayin dpo. Gwaggo hakkin Asiya bazai barmu ba. Jiba inda muka samu Asiya, jiba ƙyaƙyawar rayuwar da take ciki, ƙaton gida, tana auren babban mutum, ta ƙara komawa yarinya kamar ba ita ta haifi su Shahidah ba, ƴaƴa mazan da kike mata gori taje ta haifesu acan. Ni ga nawa nan ya zame min ƙadangaren bakin tulu. Nayi nadama Gwaggo, nayi ALLAH wadai da halina”.. Kuka ya sarƙeshi, itama Gwaggon kuka take sosai kamar numfashinta zai bar gangar jikinta......
__________★