Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 118

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 118

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 118: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 118. ........Cike da tsokana RK ya ce,…

2,398 words

........Cike da tsokana RK ya ce, “Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa”. Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya ɗauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK ɗin yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga AA ɗin, ta yanda zai zama mai haƙuri akan mace, ta yanda zai ƙyautata mata, ta yanda zai shagwaɓata ya riritata, ya sauke haƙƙokinta da ƙyautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ƙara danƙo a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke haƙƙoƙin da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sauƙaƙama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar ƴakin soyayya da farautarta ya ƙare. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ƙara nauyi a sikeli da danƙo fiye da sufagilu. Haƙuri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lanƙwasamu mun miƙe to ya tabbata sai dai mu karye ɓas. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga ƙarshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta miƙe tana murmushi ta kamasa ta miƙar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a danƙashi ga matarsa ya bar Oum ɗinsa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da ƙyar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na taɓa zukatan wannan Family ɗin matuƙa. Ɗagosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta damƙa na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana riƙe hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin ƙarawa kamar yanda Fawzan yayi. Da ƙyar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu faɗa da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka ɓige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA ɗin kansa. Dan haka baici komai ba ya miƙe yay musu sai da safe ya barsu da baƙin cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba ɗaya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan ɗinsa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa haƙƙoƙinsa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke ƙarko da ikon ALLAH. Daga ƙarshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi kaɗai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya ɗagosa yana murmushi ya riƙe masa fuska da hannaye biyu. Cike da raɗa Babban Yaya ya ce, “Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min ƙyawawan yara masu kama da su”. Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai ƙarfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma leƙensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da ƙyar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana miƙewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da raɗa yanda kowa baya ji ya ce, “Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI”. Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce, “Ouch wane muguntane wanan haka Auta?”. Cike da shaƙiyanci AA yace, “Ƙanwarka ta koya min”. Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana faɗin, “Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin ƙanwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh”. Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya ƙwaɓe fuska sannan ya miƙe yace “Muje taɓararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa”. Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake ɓoye ƙarƙashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa riƙe dana AA. Shima AA ɗin sarai yaga Nibras ɗin, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam..

Wani irin daddaɗan ƙamshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba ɗaya falon ya ɗauki wani irin ƙyau mai ƙayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba ƙaramin daɗi ƙamshin gidan yay musu ba. AA zai zauna Yaya Fawzan ya ce, “A'a ango tashi kaje kazo mana da amarya muna nan”. Ɗan jimmm AA yayi, sai kuma ya miƙe dan harga ALLAH soyay daga iya nan suyi sallama su koma shi kaɗai yaje ga matarsa. Amma bazai iya ba yana jin nauyin Yaya Fawzan ɗinsa. Tsayawa yay a ƙofar ɗakin ya zubama handle ɗin ido na sakanni, dan Amaal ta tura masa text cewar Maanal ɗin na nan ƙasa. Sai kuma ya sauke numfashi a hankali sannan ya murɗa handle ɗin kamar baya so ya tura kai ciki da sallama ƙasa-ƙasa. Zuwa yanzu Maanal na kwance ne dan ta gaji da zaman, ga tsoro na shigarta haka kawai, ta kira Didi Amaal tace su dawo dan ALLAH tsoro take ji, shine tace mata ta daure na ɗan lokaci ne gasu AA ɗin nan shigowa. Tun tana kallon ƙofa harta zame ta kwanta idanunta a lumshe ta faɗa tunanin duniya da nazarce-nazarcen ruguntsumin cikinta. A wannan yanayin taji an buɗe ƙofa, kafin ma ta nema ba'asin wanene sassanyan ƙamshin turarensa ya shigo mata hanci duk da yanda nata ke tashi da wanda aka sanya ma ɗakin ma. Luff tayi kamar mai barci tana ƙoƙarin saisaita numfashinta har ta fahimci isowarsa inda take ya tsaya cak. Shiru bata buɗe idanun ba, yana daga tsaye shi kuma ya zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yake gani kaɗan raunanan idanunsa. Kallon fin minti guda sannan ya wani fusrzar da iska mai nauyi sakamakon saukar idanunsa akan ƙugunta daya wani bada shep ta hanyar fidda lafaffen cikinta zuwa cikar ƙirji dana ƙugun dan lafayar mai kwantawa ce a jiki. Sannu a hankali kamar wanda baya so ya duƙo yana kai hannu ya yaye fuskarta da ƙyau, cike da raɗa ganin taƙi buɗe idanun ya furta, “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki Madam pretender”. Baki Manaal ta ɗan cuna a karo na farko, amma still taƙi buɗe idannunta. A karo na farko yay murmushi kaɗan, sai kuma tunawa da ana jiransu yasa shi sake furzar da numfashin ya ce, “I'm sorry drama queen. Ajiye shagwaɓan muje wajen su Yaya Fawzan mu dawo duk sai ki tattaro kiyi min harta shekara 8 da suka wuce da nayi missing duk zan ɗauka a yau ɗin nan koda ina faɗuwa ina tashi ne”. Shiru nan ma tayi, sai dai ta buɗe idannunta a hankali ta sauke a kansa, suka ɗan zubama juna ido, sai kuma ta janye nata tana tashi zaunen a nutse. Taimaka mata yay batare daya janye nasa idanun ba ya miƙar da ita, sai kawai ya sanyata a jikinsa ya rungume. “Alhamdullahi! Alhamdullahi! Alhamdullahi!” ya jera har suka uku a jere yana sauke ajiyar zuciya. Cikin raɗa ya sake faɗin, “Ya rabba nagode maka daka nuna min wannan rana, kai ne ka bani ita tun tana ƙarama, ka jarabceni da kuɓucewarta a gaɓar dana gama sakankancewa, ka dawo min da ita a lokacin dana gama sallamawa na rasata, ka bani ita a randa na gama yarda tawa rayuwar ta ƙare kenan gaba ɗaya. Yau gashi ka shigo da ita a cikin gaba ɗaya duniyata a gaɓar da nake cikin matsanancin zumuɗi, ƙagare, farin cikin kasancewar tamu. ALLAH kai mata albarka, ya rabbi ka tausasa min ita ta zame min mar'atussaliha. Ya rabbi ka ƙarfafa min ita ta zama uwar ƴaƴana jajurtacciya, ya rabbi kai mata rahama mara yanke wa, ka tsare min ita daga kowanne irin sharri na fili dana ɓoye, ka baibaiyeta da alkairinka da rahamarka, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Khadijah, kasa ta zama mai koyi da Nana Ai'sha. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Hafsah. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Saudah, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Zainab. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Faɗima. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Asiya, ƙasa ta zama mai koyi da ɗabi'un salihan mata bayin ALLAH duka da sauran matan MANZON ALLAH daban ambato ba da jaruman mata da sukai ma addini hidima tako wace fuskar alkairi. Ya rabbi kasa tai koyi da ƙyawawan halaye, haƙuri, juriya, jarumtar Oumna. Ya rabbi ka zama shaida, ita ɗin ta musamman ce a gareni, irin musamman ɗin da baki bazai iya ma furta wa ba.....” Tsam-tsam Maanal ta sake rungumeshi hawaye na sauka mata. Fin minti uku suna faman sauke ajiyar zuciya sannan ya janyeta da ƙyar ya share mata hawayen ya gyara mata lulluɓin lifaya ɗin ya kama hannunta a jikin nashi yaja suka fice. A haka suka fito daga bedroom ɗin kamar makaho da ɗan jagora har cikin falon. Sai a lokacin Maanal ta fahimci basu kaɗai bane ba. Zaunar da ita yay sannan shima ya zauna kusa da ita. Cike da girmamawa yace ma Yaya Fawzan “Gata”. Murmushi yaya Fawzan yayi mai faɗi, sai kuma ya kalla Maanal ɗin yace, “Lilly!”. Jin muryar Yaya Fawzan yasa Maanal amsa masa da “Na'am Yaya F”. “ALLAH yay miki albarka. ALLAH yay miki albarka! ALLAH yay miki albarka!. Nagode ma UBANGIJI daya kaimu wannan rana cike da lafiya da tsohon rai. Dan gaskiya dana mutu banga wannan ranar ba dole ne ma na dinga muku fatalwa banga ƙarshen movie ɗin ba”. Murmushi su RK suka shiga yi, Yaya Fawzan ya cigaba da yiwa Maanal da AA nasiha da addu'a yanda ya kamata. Kafin su RK su amsa kowa yay tashi a taƙaice. Daga haka suka miƙe bayan RK yazo gaban AA ɗin ya ajiye wani haɗaɗɗen basket da akai ma wani irin ado da flowers a sama aka kuma rufesa da net. Shine da Nuwaira suka haɗashi, Sai kuɗi da suma akai ma wani irin nannaɗar ado a wata flower ɗin daban, daloli su kuma wai na sayen baki. Daga haka sukai sallama suka fice. AA ya ɗan rakosu wajen sashen. Sai Yaya Fawzan ya maidashi ciki yana faɗin, “Koma ciki mun yafe bama son rakiyar, dan nasan ma badan ALLAH zakayi ba Auta, maybe ma jikake kamar ka koromu waje kawai. Dariya sauran suka sanya sosai. RK ya matso saitin kunnen AA ya raɗa masa, “Adai bi min daughter a hankali yarinya ce dan ALLAH. Dan wannan fitinar dake cikin idanunka ma ta isa firgitata”. Harararsa AA yayi, RK ya bar wajen yana dariya. Sai kawai yaji an riƙo masa hannu. Dariyar ya tsayar tare da juyowa. Ganin AA ne ya riƙosan ga wani irin kallo da yake masa sai shima ya zuba masa nasa idanun. Tsohon mintuna biyu suna kallon junan, su sauran da basu san mike faruwa ba sunyi gaba abinsu dan komawa sashen baƙi su samu su kwanta suma su huta, gobe kuma in sha ALLAHU Kano tai ɗiba. Da wani irin hankali AA ya shiga jawo RK baya sannu-sannu harya dawo gabansa gab, cak ya tsayar da shi akan ƙafafunsa suna kallon juna cikin ido. Sai kuma kawai AA ya wani kalar jawo RK ya rungume. A tare suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi, RK yay murmushi yana ɗagowa bayan ya ɗan bubbuga bayan sa. Magana AA ya buɗe baki zai yi, amma RK ya hana hakan ta hanyar yimasa zipping a baki yace, “Shiiii karkace komai, oya good night my son. Dan ALLAH karka ɓaro min aiki da safe kaga dai na gaji nima mamanka zan ɗauka mubar gidan nan ta ɗan min tausa”. Daga haka ya barsa anan tsaye. AA ya bisa da kallo harya ɓacema ganinsa, a hankali ya furta, “I love you Uncle. Kai ɗin na daban ne a gareni ƙololuwa”. Sai kuma ya ɗan murmusa tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda sannan ya murɗa ƙofar ya koma ciki, key ya sake murzawa daga cikin ya kulle........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣1️⃣

______________

Readers Also Read