Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 15

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 15

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 15: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 15. Tunda ta fito ya wani zuba mata idanu…

2,846 words

Tunda ta fito ya wani zuba mata idanu ko ƙyaftawa bayayi kamar yanda ya saba. Bashi kaɗai ba kowa na faɗa a zuciya ko'a fili Maanal ƴar gayu ce gata kuma ƙyaƙyƙyawa. Ko bada kwalliya ta saka kaya ba zakaga sun mata ƙyau. Balle kuma ace tayi kwalliyar ai abin sai wanda ya gani. Gata dai ba fara ba, amma da wahala namiji ya kalleta bai sake mata kallo na biyu ba duk ustazancinsa da kamewa. Badan tafi sauran mata ƙyawu ko wani abu ba, a'a itama kamar kowacce mace take, kuma komai nata irin na kowacce mace ne. Sai dai yanayinta na kamewa da ɗaure fuska kan taka musu birki wajen yimata magana ko fuskantarta kai tsaye. Sam bata da sakewa da mutane, sannan bata da yawan fara'a ko magana sai a inda taso yi ko ga wanda taso yimawa.... Sai da ta tsaya a gabansa ta ɗan yamutse fuskarta da babu walwala sam. Dan bata son kallo sam, ko yaya ake kallonta takan tsargu taji a jikinta, shi kuma taka kallo ɗabi'arsa ce. Yanda take faman yamutse fuskar da sake ɗaureta ya sakashi sakin murmushi da warware hannunsa daya harɗe a ƙirjinsa. Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai nauyi a bakinsa yana sake zuba mata idanun. “Wannan ɗaure fuskar fa? Ko duk laifin rashin cikar lokacin ne?”. Maimakon amsa masa zancen nasa sai kawai ta basar tace masa, “Ina kwana?”. “To lafiya ba ƙalau ba”. Kamar zata sharesa sai kuma ta ɗan kallesa. Fuska ya marairaice mata kamar wani ɗan yaro. Janye idanun nata tai kawai. Shima sai ya saki murmushi. Ƙofar motar ta buɗe mata yana faɗin, “Bismillah”. Komai batace da shi ba ta shiga. Shima ya zagaya nasa ɓangare ya shiga. Motar yayma key suka fice a gidan. Sai da sukai ɗan nisa a tafiya ya kalleta kaɗan ya maida hankalinsa ga titi. “Nace miki ina lafiya amma ba Lau ba, baki tambayeni mike damuna ba?”. Hankalinta na'akan novel ɗinta ta amsa masa da, “Ai banga alamar ciwo a tare da kai ba. Nasan neman maganarka ne”. “Oh oh, ni Rafeeq bin Kasheem. Ni har wani neman maganane da ni kuma?”. “Humm”. Kawai tace a taƙaice. Shima sai ya murmusa yana mai jinjina miskilancin yarinyar nan. Bai sake cemata komai ba sai zuwa can a bazata yaji tana ce da shi “Yaya jikin Aunty?”. Har cikin rai yaji daɗi, dan haka ya amsa mata fuskarsa ƙawace da murmushi. “Jikin Aunty babba Alhamdullah. Duk da dai yau ban leƙata ba sai zuwa anjima. Da ƙyar ma na kuɓuto kaina a asibiti dan na zo na kaikin nan.” “Ai sai da nace ka barni naje kawai”. “Bazan iya hakan ba ai. Shi abu mai daraja killacesa ake. Kaffa-kaffa da shi kuma akeyi. Fatana ma na samu na ɓarar da waccan gwamnatin data tare min ko'ina. Sai kuma nayi sakaci wasu ƴan bani na'iya su shigo neman hanyar min kutse?. Ko baki yarda ba”. “Kaima kasan mi kake nufi”. “Ki rantse kema baki sani ba?”. Shiru ta masa. Dan tama gaji da surutun. Yasa ko fahimtar labarin batayi ma. Sun iso katafaren comyanin *_MAWAAD_* daya tsaru da gini na zamani. Gashi babba sosai ta yanda hasashenta bai taɓa hasaso mata ba. Yanda aka tsara ƙaton harabar wajen da furanni koraye da jajaye harma da wasu kalolin abin ƙayatarwa, ga kwalta lafiyayya shimfiɗe. Hatta ababen hawa na ma'aikata an fakasu ne cikin tsari da birgewa. Bawani hauma-hauma ko hayaniya. Sai securitys dake kula da tsarin shiga da fitar kowa a wajen hatta cikin harabar. Dole ne wajen ya birgeka, dan duk iyayin mutum idan yazo *_MAWAAD COMPANY_* sai tsarinsa ya birgeka..........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣2️⃣

.........“Ya kikaga companyn?”. RK ya katse mata tunaninta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tare da juyowa ta ɗan kallesa. Ganin shima ita ɗin yake kallo sai ta ɗauke kanta kawai. Cikin ɗan yamutse fuska ta ce, “Balaifi komansu da tsari gaskiya. Sai dai ina fatan ba ƙawar gini bace kawai”. Dariya ya ɗan yi a taƙaice. Ya ce, “Maanal bari na baki a buɗe, Mawaad Company ko kamfanin Rolex bazasu nuna masa yatsa ba a ɓangaren agogo. Basa ɗaukar ma'aikaci sai wanda yasan abinda yake yi. Sannan babu zancen sai ɗan wane ko sanayya, akwai turawa ma'aikata anan tun daga Chinese harma da Europe da sauran ƙasashen baƙaƙen fata. Komansu da ƙa'ida da doka yake tafiya. Kayansu ba kayan yara bane, manyan sarakuna da attajirai ke iya sayen kayansu a kowacce kusurwa ta duniya, tunda kikaga turawan nan da larabawa na tururuwar amfani da agogunan Mawaad ai ba sai na cigaba da cewa komai ba. Barama dai na daina cewa komai, ke da kanki zakizo kina bani labari watarana in sha ALLAHU. Abinda nake so dake dai ki nutsu wajen interview nan. Dan harda boss ɗin companyn da kansa za ai miki ita, ina nufin CEO na companyn. Duk da dai nasan banda matsala dake in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a da nasara idan alkairi ne. Muje na rakaki har ciki. Zan jiraki har ki kammala sai muje ki duba Aunty babba ko?”. “A'a ka koma wajen aikinka kawai ba damuwa. Idan na gama zan koma da kaina. Tunda bamu san yanda abin zai kasance ba. Duba Aunty kuma basai ka kaini ba zanje da kaina ne”. “Hummm” ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi. Daga haka suka fito a tare. Idan ka gansu dolene su birgeka matuƙa. Dan sun dace da juna. A jere suke tafiya cikin tsari da nutsuwa. Dan shima RK dai-daita tafiyar tasa yay data Maanal duk da kasancewarta mai sanyin tafiya da tsantsar nutsuwar iya taku. Sam bata da hauma-hauma ko garaje a tafiya ita. Sun tsaya a haɗaɗɗiyar ƙofar wajen data kasance ta zallar gilashi, koda yake bama ƙofarba shi kansa ginin akwai gilashi sosai a cikinsa shiyyasa ya zauna da ƙyau kaikace ba'a Nigeria kake ba a wata Chaina ce can dan sune mayu. Sai dai kuma a cikin Abuja wannan ba komai bane kasancewar akwai gine-gine na ƙawa da ƙasaita da sukafi Mawaad Company komai ma. Duk da sanin da securitys ɗin ƙofar sukaima RK sai da ya saka I'd card ɗin aikinsa akan wani computer sannan ƙofar ta buɗe masa da kanta. Ya gaisa da securitys ɗin idanunsa akan Maanal datai kicin-kicin da fuska. Juyawa yay ya musu ɗan taƙaitaccen bayani a kanta. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai... (Eh lallai ashe kallo na daga ciki) cewar Maanal a zuciya. Dan kuwa tabbas Companyn nan ya ginu da iya nasa tsarin da ƙawa. Sun fara iske reseption, anan suka tsaya suka saka sunansu sukai signing kamar yanda tsarin Companyn yake ga baƙo ga ma'aikaci, kafin ma'aikatan dake a floor na farko, zamu iya cewa wani department ne anan na sashen Companyn, duk sun duƙufa aiki, yayinda wasu ke faman kai kawo da uzirin gabansu daya shafi aiki. Tunda suka shigo wasu ke kallonsu, wasu na zungurar wanda basu gani ba, yayinda wasu ke ƙuskus, wanda ke ɗan kusa da su kuma na gaishesu. RK kaɗai ke amsawa, Maanal kan ɗan jinjina kanta kawai itadai tana mai kallon komai. Daga haka suka isa ga elevator, shi ya danna ta buɗe, ya mata nunin ta fara shiga sannan shima ya shiga. Shine ya sake daddana number floor ɗin da zasuje sannan ya matso kusa da ita yana magana a hankali. “Kin fara ganin yanda tsarin yake ba?”. Maimakon amsa masa da baki sai ta ce masa, “Uhmm”. Kawai, dai-dai nan suka iso inda suke son zuwa. Sai da ta gama buɗewa suka fito. Sun samu matashiyar budurwa ɗauke da files a hannu zata shiga elevator ɗin. Tana ganin RK ta saki ɗan murmushi da faɗin, “A'a ashe shiyyasa yau garin kamar da hadari, ashe babban baƙo ne damu a Mawaad”. Murmushi yay mata da amsa mata da, “Kedai masheranciya ce Labibah. Ykk ya aikin?”. “Babu wani sharri sai gaskiya. Aiki gashi nan muna ciki. Nikuma ina lafiya”. “To Masha ALLAH. Iji dai boss na nan?”. “Humm zaune kuwa. Kasan baya wasa ai sai da dalili ko zai leƙa office ɗin gwamnati. Yanzu naga ya dawo dan ya shigo da safe sai kuma ya fita.” “Okay, to bari mu ƙarasa”. “Babu damuwa. Sis.. barka tunda shi ya kasa gabatar min dake”. Karan farko Maanal data ɗauke kai daga garesu ta ɗan juyo ta kalleta. Hannu ta bata kawai alamar suyi musabaha batare da tace komai ba. Sai shine ya ce, “Labibah bazaki taɓa canjawa ba. Da kinyi haƙuri ai zanzo da ita har office ɗinki ne idan na gama da boss”. “Ato shike nan babu damuwa kuje. Nima zanje office ɗin CMO ne”. “Okay tom ba damuwa sai mun fito”. Daga haka ta saki hannun Maanal ta shige elevator ɗin su kuma suka wuce. Office ɗin Assistant ɗinsa shine farko kafin na boss dake ciki. Ya tarbesu da girmamawa alamar akwai sanayya tsakaninsa da RK ɗin sosai. Dan RK ɗin yata tsokanarsa kafin yace masa bari ya sanarma boss ɗin zuwansu. Ita dai Maanal hankalinta ma nakan ɗan bin Office ɗin da kallo. Komai tsaf kuma ƙal babu wani tarkace ko hayaniya. Baifi mintuna huɗu ba ya fito yana sanarma RK oga yace ya shiga shi kaɗai. Murmushi kawai RK yay da ɗan girgiza kansa. Kafin ya matsa inda Maanal take zaune dan shi dama yana daga tsaye ne. “Kinga ina zuwa. Minti biyar kawai”. Kanta ta jinjina masa batare da nuna damuwar da yay tsoro ko ɓacin rai daga fuskarta ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta ciro novel ɗinta daga bag ta cigaba da karatunta. Shima Assistant ɗin barin Office ɗin yay da alama akwai inda zaije. Kusan mintina huɗu sai gashi ya dawo. Mazauninsa ya koma ya zauna bayan ya ajiyema Maanal ruwa da lemo. Baice mata komai ba itama batama kulashi ba balle kallon abinda ta ajiye. Tana nan a zaune fin mintuna goma sannan RK ya fito. Zama yay a kusa da ita yana bata haƙurin daɗewarsa. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Ba komai”. Ta maita hankalinta ga book ɗinta. Shima dai wayarsa aka kira, dan haka ya miƙe ya fita aka sake barinta ita da Assistant. Suna nan a haka wani ɗan abu dake desk ɗinsa yay ƙara, miƙewa taga yayi ya nufi hanyar officer ɗin ogan kamar yanda suka faɗa. Bai wani jima ba ya dawo, cikin mutuntawa yace mata ta taso suje. Littafinta ta saka a bag ta miƙe batare da tace dashi komai ba. Ta wani elevator ba wanda suka shigo ita da RK ba suka shiga da Assistant ɗin, cikin sakanni ya saukesu inda suka nufa, koda suka fito nan ma sai taga offices ne a wajen. Sun shiga wani waje da alama ta nuna conference room ne, sai dai bai ƙarasa da ita can ciki ba ya nuna mata wajen zaman daga nan ta inda aka shirya kamar masauƙin baƙi. Tana zama wata ta kawo kofin coffee ta ajiye mata da drink. Atare suka bar wajen ita da Assistant ɗin sai ita kaɗai kenan. Babu abinda ta taɓa ta sake ciro novel ɗinta ta cigaba da karatu......

Fin tsahon mintuna talatin tana a wajen babu wanda ya sake zuwa, har ranta ya ɗan fara sosuwa sai ga wasu mutane uku sunzo sun gittata sun shiga conference room ɗin, tsakanin inda suka bin da inda take akwai ƴar tazara, shiyyasa bata wani shaida kowa ba. Bayan shigewarsu fin mintuna biyar wasu biyu suka sake wucewa, kasancewar bata ɗago ba a yanzu sai da suka gama shigewa taji motsin rufe ƙofa. Ƴan mintuna kaɗan Assistant ya zo wajenta yace ta shiga. Kanta kawai ta jinjina masa tare da maida book ɗinta a bag ta miƙe. A ranta tana mamakin wannan abu kamar wulaƙanci, ana tattalin ɗaukar ma'aikaci da alama su nan yanga sukeyi. Da wannan tunanin ta tura glass door ɗin a hankali ta shiga da sallamar da bata tunanin zasuma iya jinta saboda yanda ta yi ta ciki-ciki, dan wani irin bugawa ziciyarta ke mata da sauri-sauri da batasan dalili ba, amma haka ta danne tana ƙarama zuciyar tata ƙarfi. Sai dai kuma da alama sun ji sallamar tata ɗin, dan wasu a cikinsu sun amsa. Taji hakan ne a bayyane dan ba kallonsu take ba su duka. Sai da ɗaya a cikinsu ya furta, “Bismillah zaki iya zama”. Sannan ta ɗan ɗago ta kallesu tana mai jinjina kanta zuciyar tata dai na cigaba da bugu. Mutane ukun dake fuskantar inda zata zauna kawai ta iya ma kallo cikin sakan biyu. Wanda ke zaune kuma a kujerar dake gefen inda take bata ko kallesu ba. Sai kujerar dake tabbatar da oga kan zauna yayin meeting shima bata wani dubesa ba. Shima kuma kansa a duƙufe yake yana duba wani magazine kamar ma bai san da zaman kowa ba a wajen. Kujera ɗaya taja ta zauna zuciyarta na mamakin ai mutane biyar kawai taga sun shigo, ya akai taga kusan takwas anan?, rashin mai bata amsa ya sata shiga gaidasu. Amsa mata duk sukayi, sai dai bata jin shi wancan ya amsa ɗin. Shiru kamar na mintuna biyu kafin ɗaya a cikinsu ya fara mata tambaya. Babu ko ɗar a tare da ita ta amsa masa. Kansa ya jinjina sosai dukansu suna mamakin ta. Wanda ke tsakkiyar sa shima ya sake jeho mata tasa tambayar. Nan ma ta sake amsawa babu ko wani ɗar. Dukansu kam sai da suka sake dubanta wannan karon saboda jarumtarta da kaifin basira da suke kallo a bayyane, sai dai abinda basu sani ba dannewa kawai takeyi, dan tana cikin wani hali da ita kanta ta gagara bashi fassara. Gashi a masu mata interview ba wai baƙaƙenmu bane balle ma ace hausawa. Hausawa biyu ne ma kawai a cikinsu sai CEO ɗin da har yanzu bataga fuskarsa ba. Amma dai hannunsa dake saƙale da wani shegen Designer agogo da zoben dake neman harmutsa tunaninta na azurfa ya nuna bakin fata ne duk da kallon fisha tai masa kawai. Na ukunne da baice komai ba tun ɗazun a yanzu cikin turancinsa mai fita da harshen Chinese ya furta “Woow, You are amazing young lady”. Sai kuma ya shiga tafa mata. Suma sauran tafa matan suka farayi suna mai kallon boss ɗin nasu da har yanzu bai tanka ba baima maida hankalinsa a kansu ba yanata duba magazine ɗinsa hankali kwance. Ganin dai bashi da niyyar kulasu suka haƙura suka daina. Sun bata takarda da kayan aiki tai zanen agogo a take anan, zanen da yay mugun basu mamaki da ƙaryatar dasu. Daga haka File suka tura mata da mata bayanin zata cike tai singing a take anan. Bata musa ba taja file ɗin gabanta. Ta ɗan dudduba abinda ke cikinsa kafin ta shiga gudanar da dukkan abinda suka buƙata zuciyarta na mata wani irin sanyi ƙalau dan kuwa dai sun tabbatar mata da ɗaukarta aiki ne. Acan ƙasan ranta kuwa tana mamakin nasu tsarin. Daga interview a take a wajen kuma babu batun kaje ka jira sai a tabbatar maka da an ɗaukeka aiki. Haka dai ta gama cike komai tana zancen zucinta ta basu. Bayan sun dudduba suka miƙama ogan nasu da sai a yanzu ya ajiye magazine ɗin ya fara duba file ɗin. A karo na farko oga kwata-kwata da yay kamar bashi nan a wajen ya ɗago kansa bayan kammala duba komai na file ɗin, cikin wani irin dakewar murya ya jeho mata tasa tambayar data tilastata kallonsa. A yanzu ba bugun zuciya kawai taji ba, zuciyar tatace gaba ɗaya zata iya cewa ta tarwatse a dalilin kallon ido cikin ido da sukaima juna. Suma, ɗaukewar numfashi, ko gushewar hankali ko tsatstsagewar zuciya batasan yanda zata kira yanayin data tsinta kanta a wannan lokacin ba ma.........✍️

_Tofa jama'a mi kuma ke shirin faruwa anan?. CEO na Mawaad Company da Maanal? Kumuje zuwa wasan na ainahi ma yanzun ne zai fara a duka ɓangarorin😆 in sha ALLAHU 😉👌_.

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣3️⃣

Readers Also Read