Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 161

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 161

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 161: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 161. A sashen Mamy kawai ganin Sille tai a…

3,356 words

A sashen Mamy kawai ganin Sille tai a kanta kawai. Dan tana zaune a falon sama ne ita kaɗai kamar mayya tayi nisa a tunani sosai. Firgigit ta kallesa zuciyarta na harbawa. Sai kuma ta sake zabura tana kallon bayansa da sauri. Cikin ɓacin rai ta ce, “Amma baka da hankali ko? Kai wane irin daƙiƙi ne wai zaka dinga shigo min gida kai tsaye?”. Zama yay kamar bai jita ba, ya ɗauki kwalin jus data ajiye ya cire murfin yasa a baki yasha sosai. Sai kuma ya dire a inda ya ɗauka yana kallonta. “Kin san idan ni daƙiƙi ne a wajenki nayi gadon daƙi ƙancin. Gida kuma na Darma dai dan ke kam bana jin zaki amfanu ma da komai na cikinsa. Koda yake idan kin min yanda nake so maybe ki samu ɗin.” Tsaki mai ƙarfi Mamy tayi da galla masa harara, sai kuma fuuu tai yunƙurin barin masa falon. “Amma kin san ko bayi kika shiga kika tuɓe wlhy sai na biyoki, garama ki dawo muyi magana dan nima banda isashen lokaci”. Cak Mamy ta dakata zuciyarta na wani irin dokawa da ƙarfi saboda kalamansa, ita kam dai ta shiga uku da wannan mutumi. Ta tabbatar zai iya aikata abinda ya faɗan, dan haka ta dawo cike da borin kunya ta ce, “Yau kuma uwar mi kazo da shi”. Sai da Sille yay wata irin dariyar data saka Mamy daburcewa tana kallon ƙasa da faɗin, “Wai baka da hankali ne sai wani ya jika”. “To miye, ba sai kowa yaga babban ɗanki ba.” Mummunan kallo ta watsa masa ta ɗauke kanta. Shima sai ya taɓe baki tare da ɗage kafaɗa ya ce, “Kuɗi nake so”. “Ko kuma uban kuɗi ba”. Mamy ta faɗa a harziƙe. Hankali kwance Sille ya ce, “Dazan samu uban kuɗin ma ai da nayi murna. Dan haka ki bani kuɗi, in ba haka ba kuma zaki sha mamaki. Dama masu gadi sun sanar min Darma na gida”. Kallonsa kawai Mamy ta tsaya yi, zuciyarta na wani irin motsawa. Bata son abinda zai katse mata aikinta da kwanaki tara kacal suka rage mata, gara ta bashi ya tafi ya barta, ita da zata mallaki ninkin abinda yake nata sau ɗari miye na damuwa. Da Abah ya mutu fa dukiyar duk tata ita da ƴaƴanta. Fateema da timilin takaba kawai zata tashi, itama bata raba ɗayan biyu bayan kwanaki tabi bayan Aban tunda ji suke kamar ɗaya zai iya mutuwa idan babu ɗaya. Kinga tata dukiyar itama mallakin ƴayanta zasu zama daɗi kan daɗi kenan. Sai kawai ta saki wani makirin murmushi tare da ɗaukar wayarta. A take ta masa transfer na 50m. Shi kansa Sillen ɗagowa yay yana kallonta da mamaki. Ta ɗage masa gira tana murmushin. “Na baka wannan saboda bana son sake ganin fuskarka a gidana ko inda nake. Idan kuma ka sake zuwa duk abinda nai maka kaine kaja. Shashasha kawai, oya get out of here”. Kallonta sosai Sille keyi, sai kuma ya saki wani makirin murmushi, batare da yace komai ba ya miƙe tsam ya gyara hularsa, sauran lemon ya ɗauka ya shanye ya wurga kwalin gabanta sannan ya fice. Mamy ta raka bayansa da harara tana jan tsaki. A ranta faɗi take (Zanyi maganinka. Bari dai a gama binciko min inda uban naka yake. Duk ma gidan ubanda ya samoka yace maka nina haifeka sai ma baku mamaki kai da shi.” Daga haka tai hanyar bedroom. Tana shiga ta samu ɗayar wayarta na ring. Ƙarasawa tai ta ɗauka da sauri dan tasan wanene zai iya kiran nata. Ilai kuwa shine. Tasa a kunne tana kallon ƙofarta, sai kuma ta nufi closet ta shige bedroom sannan ta ce, “Ina jinka Amo. Yaya akayi?”. Daga can wanda ta kira Amo ya furta, “Hajjaju kayanki sun iso gasu a hannu na. Ya kamata zuwa anjima ki shigo ki amsa. Idan kuma zaki aiko ne tom ina dai jira”. “Woow thanks you Amo. Fitowata bazai yiwu ba weekend ne kowa yana gida, amma zan aiko Haule anjima kada ka damu. Sai dai a basu tsaro iya tsaro Please”. “Baki da matsala hajjaju, sai tazo”. Mamy ta jinjina kai tana yanke kiran gaba ɗaya fuskarta ta gama washewa da farin ciki. Ji take ma kamar ta aiwatar da aikin nata ne ma. A fili ta furta, “Aliyu Darma kenan, baka san wacece Kamila ba. Saboda da kaza ai baya hana a yanka ta. Dolene ka biya bashin soyayyar shekara talatin da wani abu, ka kuma biya bashin wulaƙanci da fifita wata a kaina duk da kasan na fita sonka”. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya........✍️

Hummm mi kuke tunanin Mamy ta saka an kawo mata ne?🙆

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣6️⃣

______________

.......AA kam kai tsaye gidan Daddy ta nufa, inda suka ɓoye Yazeed. Dan tun a washe garin da aka kamashi shi da Nazeefa aka taho da shi Abuja. Ita kuma tana can a kadunar wani gida, an ajiye tsohuwar dake kula da ita. Ba yau AA ya fara zuwa gidan ba, ba shi kaɗai ba hatta Abah da su Babban Yaya suna zuwa. Dan sosai aka dage akan Yazeed kuma alhamdullahi ana samun abinda ake so yanda ya kamata. Dan ya dawo hayyacinsa yanda ya kamata sai dai abinda ba'a rasa ba dan harkar sihiri wuya gareta. Daddy dake kallon AA da murmushi ya ce, “Son ka ƙaraso?”. Shima AA yana murmushin ya ce, “Eh Daddy, ina kwana”. “Lafiya Lau Alhamdullah. Ya ƙoƙarin ku? ALLAH ya saka da alkairi ya bada ladan zuminci. Ai naga mutuminka jiki ya ƙara sauki sosai gashi har muna hira kuma naga ana kula da ibada”. Murmushi AA yayi kawai, sai ya ɗan kalla Yazeed. Hannu Yazeed ya bashi suka gaisa. Ya tambayesa ya ciwon kan?”. Dan tunda aka dage da addu'oin sai ciwon kai ya gallabi Yazeed ɗin. Ya ce, “Alhamdullah ya iyalin”. A taƙaice AA yace, “Alhmdllh”. Dai-dai nan akai kiran wayarsa. Ya cirota a aljihu yana dubawa. Sai kuma ya kalla Daddy cike da girmamawa ya ce, “Inaga ya ƙaraso”. “Okay to bari nace maigadi ya shigo da shi”. Daddy ya faɗa yana ɗaukar waya yay kira. Babu jimawa kuwa sai ga baƙo da maigadi sun shigo... Wajen zama Daddy ya nuna masa, bayan an gaisa ya dubi AA cike da girmamawa ya ce, “Oga aimin afuwa huldup ne ya ɗan riƙeni a maraba, nayi zaton bazan kai haka ba a kaffi ɗin nan wlhy”. “Karka damu, yanzu ya ake ciki?”. Laptop ɗinsa ya zaro daga jakka yana faɗin, “Alhamdullah munyi nasarar samo yaron a jiya kamar yanda na sanar maka. Sai dai da ƙyar ma muka samu ya iya tuna sakashi akai yayi register ɗin shima kusan shekara biyar data wuce. Sauƙin da muka samu kuma anan cikin kasuwar su abin ya faru, wanda kuma yay masa register ɗin har yanzu yana a kasuwar. Yaso ƙin bamu haɗin kai shima sai da Faisal ya nuna masa I'd card ɗin aikinsa sannan ya tsorata. Sai mukai amfani da bayanan shi register ɗin yaron aka duba duk wanda ya sai layi a wannan ranar. Alhamdullahi mun samu kafin mutumin ya saka yaron wannan aikin shima yayi register a wajen kamar dai yanda yaron ya faɗa mana da farko. Yanzu dai ga hotonsa da sunan da yay register ɗin”. Yau maganar yana miƙama AA laptop ɗin cikin girmamawa. Amsa yay yana dubawa, cikin mamaki ya ɗago ya kalla Daddy, ganin shi yake kallo shima sai ya miƙa masa laptop ɗin. Amsa Daddy yay yana kallo shima cike da mamaki ya ce, “Mabera!”. “Daddy da gaske shine ɗin kenan?”. “Tabbas shine Ajwaad, duk da hoton yayi kusa kuma bai fita sosai ba wannan Mabera ne. Ga sunan ma, Junaid Abba Mabera. Kawai ya fara saka sunan uba ne a farko kafin nashi”. Kamar an bugama Yazeed guduma a kai ya dafe kan nasa saboda jin sunan Baban Nazeefa da aka kira, sai kuma ya shiga ambaton sunan ALLAH. Atare duk sukai kansa suna tambayar lafiya. Ina ya kasa magana, sai jujjuya kai yake, AA da kamar ya harbo jirginsa a nutse yaje kan dining ya ɗakko gorar ruwa na addu'oin Yazeed ɗin ya kawo, bashi yay yana faɗin, “Yazeed kasan Junaid Abba Mabera ɗin ne?”. Ƙara Yazeed ya sake saki. AA ya sake maimaita sunan yana ɗibar ruwan a hannunsa ya zubama Yazeed saman kai. Ai sai ya fasa ƙara gaba ɗaya. Ganin haka sai Faisal da Daddy suma suka cigaba da kiran sunan Mabera. Kawai sai Yazeed ɗin ya yanke jiki ya faɗi a sume. Daddy zai tada hankalinsa AA ya ce, “Daddy ka kwantar da hankalinka. In sha ALLAHU ina kyautata zaton lokacin nasara ne. Da alama an goge masa sunan a memory ɗinsa ne shiyyasa ya kasa tunawa gaba ɗaya, ƙila kuma jin sunan shine makarin sihirin shiyyasa”. “Tabbas oga haka ne, dan nima irin haka ta taɓa faruwa da Yayana kuma kamar dai na yallaɓai ɗin nan da kake gani.” Sosai su Daddy suka jinjina al'amarin, kafin aka zubama Yazeed ruwan addu'ar sai gashi ya farfaɗo. Cikin ikon ALLAH kuma yana buɗe baki sai ya fara da addu'a. Addu'ar Daddy ya tayasa suka ƙarasa, AA ya kamashi ya zauna da ƙyau. Sai ya dinga binsu da kallo. Zuwa can yace, “Daddy zan sha ruwa”. Ruwan AA ya miƙa masa, ya amsa yashanye tas yana sauke ajiyar numfashi. Sai kuma yabi gidan da kallo yana faɗin, “Daddy ina ne nan kuma? Miya faru?”. Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, dan ya fahimci yanzu ne Yazeed ɗin yay asalin dawowa a hayyacinsa.......

________★

Tunda Sille ya baro gidan Mamy yake ta faman kai-kawo, dan tabbas bai yarda da matar nan ba. Dolene akwai abinda take shiryawa. Yanda ya fahimci tasan darajar kuɗi bazata bashi har 30m a lokaci guda ba. Sannan wannan yawan kuɗin na nufin ta tara abinda yafi haka kenan. Wanda zai yi ƙyautar 30m a lokaci guda bayan ya bada 20 a baya ai lallai yaci ya tada kai musamman ga mace irinta da bata aiki bata kuma sana'ar komai. Yanzu ya sake fahimta da yardar maganar Baa ɗinsa. Lallai Darma Family nada kuɗi. Waya ya ɗauka yay kiran, bugu ɗaya aka ɗaga. A ƙage ya ce, “Baa! Akwai ƙura fa”. “Ƙura kuma Son, ta guguwa kota ƴan dambe?”. “Ta guguwar dai......” Tsaf ya zayyane masa komai. Shima Mabera shiru yay tsahon lokaci cike da nazari, zuwa can yace, “Tabbas akwai abinda take shiryawa. Kamila raino na ce, sannan nasan abinda zata iya tun bata gama sanin kanta ba. Shaiɗaniya ce, da wannan innocent face ɗin taya zata iya juya Nigeria ta koma dajin sambisa. Abinda za'ayi ka kira yarinyar nan da take aiki a gidan ta sanya mana ido a dukkan motsinta. Ko ka kira Hajiya Turai”. “Okay Baa! Sai dai yarinyar, Turai bata gari tayi tafiya”. Ya yanke kiran, komawa yay kiran Haule. Sai dai bata ɗaga ba, amma ta tura masa text cewar tana zuwa. Hakan na nufin nata kusa da Kamila, dan haka ya barta yay zaman jira. Baifi mintuna biyar ba sai ga kiran Haule ya shigo. Muryarta har rawa take ta ce, “Baby kayi haƙuri, ina gaban Hajiya shiyyasa”. “Mi kike mata?”. “Tace na shirya zata aikeni wani waje. Amma sai six na yamma dan tana son na dawo dai-dai an shiga sallar magriba”. Jimm yayi na sakanni. Kafin ya ce, “Ta gaya miki wajen aikar?”. “A'a gaskiya”. “Okay later duk yanda ake ciki ki kirani”. Daga haka ya yanke. Haule tai shiru tana kallon wayar. Mamaki na kamata jin yanda yanzu yake amsa mata magana a sauƙaƙe. Ɗazun nan fa har dukanta yay a gidansa dan kawai tace masa tana period. Shiyyasa ma ta saka riga kai dogon hannu, dan jikinta duk sayin belt ɗinsa ne daya zaneta da shi. Ga zazzaɓi tana ji dan ba dukan wasa yay mata ba harda kamun kunne. Tana son Sille sosai, shiyyasa take iya jure wahalhalun da yake bata da azaba kala-kala da wulaƙanci. Burinta a ƙarshen duk wannan azabobin suyi aure. Wlhy zata jure komai ko a yaya yake dan sonshi take yi da gaske....

_________★

KADUNA

Tun wucewar su Sageer kalamansa ne keta maimaita kansu a kunnen Huznah. Ta kasa samun sukuni gaba ɗaya. Bata san zata iya yin kewarsa ba sai da tazo kwanciya. Sai ta jita tamkar marainiya. Gashi tunda ya kirata yace sun sauka bai sake kira ba. Ita kuma yana tsoron ta kira shi Ummi taji. Haka ta daure da ƙyar barci ya ɗauketa gabannin asuba. Washe gari Hajiya Basariyya da sassafe ta bar gidan zuwa Zaria. Maimakon zuwa gidan su Najma kai tsaye a wani waje suka haɗu da Maman Yaseerah. Ganin yanda ran Maman Yaseerah ke a ɓace Hajiya Basariyya ta ce, Lafiya kuwa naga ranki a ɓace fiye ma da nawa?”. “Humm Basariyya kenan, gara ke kina da mafita akan Huznah, duk da case ɗinmu akwai banbanci, ke haihuwa ce baki so tayi da Sageer, ni kuma haihuwa nake son Yaseerah tayi da Abdullahi.” “A'a to minene ba gashi zata haihun ba?”. “Wace haihuwar kuma bayan jiya ta haihu ɗa babu rai, kina cikin wannan tashin hankalin ne shiyyasa ban kira ki ba. Ga Alhaji ya hanani zuwa dubata ya tura ƙanwarsa da Majdiya yanzu haka suna hanya”. “Eh lallai babbar magana. Wai mike faruwa damu ne haka? Wlhy ko ganin Huznah bana sonyi tsakanin jiya zuwa yau”. “Taya zaki so ganinta abin nan fa da ciwo. Duk zamanki gidan Kawu Manu ne ya kawo matsalar nan, amma da tuni mun ɓarar da shegen cikin ai. Yanzu dai yaya ake ciki”. “Hummm nayi magana da Dr Reyama jiya tace a haka ma za'a iya cire cikin, sai dai ta saka kuɗi masu yawa. Ni kuma wlhy a yanzu banda wannan kuɗin, dan dudu kuɗin account ɗina 300k ne. Suma wanda Yaya ya bani ne na tura miki 200k kinje wajen malamin can dake aiki akan dawowar kayan nan na hannun Yazeed. Shiyyasa nazo ki ara kin 200k na cika dana hannuna su zama 500k ɗin data buƙata. In sha ALLAHU komai na daidaita zan dawo miki da su”. Shiru Maman Yaseerah tayi fuskanta na canjawa, sai kuma ta nisa. “Shike nan zan baki, amma kina lissafawa ko ya zama 500k kenan harda 300k da aka bama wancan mutumin na bayan tsauni”. “Na sani bananta ba Aminiya”. “Yayi zan sa miki a account. Ni bari na koma dan ina cikin damuwa”. “To ba damuwa. Nima dai idan aka kammala aikin nan na Huznah zanje Abujan na gano Yaseerah ɗin.” “Okay”. Kawai Maman Yaseerah tace tai ficewarta. Sai abin ya tsayama Hajiya Basariyya a rai. Amma batace komai ba ta fito ta shiga mota ta kama hanyar Kaduna. Dan bama taso kowa ya farga da rashinta a gidan har ƴaƴanta...........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣7️⃣

______________

.........Koda Hajiya Basariyya ta koma gida batace da Huznah komai ba. Hasalima ko gaisheta tayi sama-sama take amsawa. Sosai Huznah ta shiga damuwa, har wata ƴar ramar dole tayi. Baiwar ALLAH sai dai kaga tayi tagumi shiru ko ƴan uwan nata ma ta kasa sakin jiki da su. Duk abinda ke faruwa babu wanda ya sani. Duk da dai Huznahr na ƙoƙarin shiga gaida Daddy a sashensa. Yanda yaga ta ɗan rame sai abin ya bashi mamaki, gashi bata da walwala. Sai yake tunanin ko kewar mijinta ne. Bai dai ce komai ba ya barma cikinsa. Amma ita Ammie haka kawai tasha jinin jikinta da yanayin Huznah ɗin. Sai ta fara jan yarinyar jikinta dan akwai tausayi, tana fama da ciki kuma ana sakata a damuwa. Hakan sai ya saka Huznah ɗin fara saki jiki da Ammie, har in tana son abu sai ta faki ido taje sashen tace Ammie ta bata ko Aunty Sakeena. Wani lokacin ta zauna taci anan, kota ɓoye ta tafi da shi......

________★

Bayanin komai Daddy yay ma Yazeed. Aiko sai kuka yake da hawaye shaɓe-shaɓe yana roƙon Daddy ya yafe masa. Ya ringa yima AA kuma godiya. AA ya nuna masa babu komai, akan Ammie komai zai iya yi dan tamkar mahaifiya take a wajensa. Kawai dai yana bashi shawara ya ƙara dagewa da addu'a a kwanakin nan, dan zasu fara bibiyar Mabera. Dan haka za'a koma da shi Kaduna kuma zai cigaba da acting like har yanzu yana a cikin wancan halin. Yanzu idan sunje Kaduna ɗin ma za'a maida shi gidan da Nazeefa take sai a fiddosu tare ta yanda zata ɗauka a gida ɗayan suke daman. Ɗari bisa ɗari Daddy da Yazeed sun gamsu da shawarar AA ɗin. Dan tabbatas Mabera shegene al'amarinsa sai da bada ƙafa. Tunda har ya iya irin wannan ƙullin a jikin Yazeed ɗin to komai fa zai iya yi. Sun sake tattaunawa sosai da tsara abubuwa masu yawa kafin AA ɗin yay musu sallama ya tafi. Suma zuwa yamma zasu wuce. Amma shi Daddy zai tafi a mota yanzu, shi kika Yazeed yabi tarain ɗin dare....

________★

Kusan lokaci ɗaya su Maanal da AA suka shigo gidan. Sun raka Oum ne yin jajen haihuwa gidan su Abdull, daga can suka wuce asibiti suka duba Yaseerah dake tare da su Hajiya Majdiya. Sai suka shiga wajen Nuwaira data tarkato ta biyosu dan RK yayi tafiya yau da safe zuwa Jos. Kuma zai yi kwana biyu dan sai ana jibi salla ma zai dawo... Duk da Maanal taji daɗin fitar hankalinta a rarrabe yake akan lamarin mutumin can data gani ɗazun ya shiga sashen Mamy. Tata saka ido taga an kira Nuratu ko wajenta yazo amma bata ga hakan ba har suka fito, dan hada ma Nuratun suke tare. Saheeba dai ana can ana rawar ƙafar haɗama Babban Yaya abinci yau yace tayi girki. Shiyyasa ma taƙi ta bisu.. AA ya iso kusa da Oum yana kama hannunta da mata sannu. Murmushi tai masa da faɗin, “Sannunmu Auta. Kaima sai yanzu kake shigowa?”. Sai da ya kalla Maanal da ke kallonsa a kaikaice sannan ya ce, “Ki bari kawai Oum uziri ne ya riƙeni sosai. Amma kukan kun daɗe halan yawo suka sakaki kukaitayi?”. Sai da suka fara tafiya yana rike da Oum ɗin take bashi amsa da, “Babu laifi mun ɗanyi yawon kam. Dan munje gidan Hajiya Batoola ma, kafin muje asibitin. Kasan Majdiya ta maƙalemu da surutu ta hanamu fitowa shine kuma muka leƙa Nuwaira ashe ma tana shirin tahowa nan ne. Sai kuma muka biya yaran nan suka sayo kayan kwaɗayi”. “Eh lallai kunsha yawo kam, ɗazun da safe muke magana da Uncle R ɗin yace uzirin gaggawa ya taso masa zuwa Jos zata taho nan na aika driver ya ɗakkota baya son tai driving saboda jikinta. Tunda ta biyoku ai shike nan.” Dai-dai nan Mamy ke fitowa daga sashenta ita da wata mata. Ta zuba ma AA da Oum ɗin ido, sai kuma ta janye cikin takaici zuciyarta na mata nauyi da zafi matuƙa a cikin ƙirji. Oho su bama su ganta ba, dan har sun shige su Maanal biye da su, sarai Maanal taga Mamy, hakama Najma da Nuratu, amma duk sai suka watsar da ita suka shige. Ameerah da hankalinta bai kai ba tana waya ma ta shige, dan harga ALLAH ita kam bataga Mamyn ba sam...

Readers Also Read