Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 198

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 198

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 198: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 198. ........Sosai Oum ta tsaya akan masu…

2,856 words

........Sosai Oum ta tsaya akan masu jego sukai jego mai ƙyau da kulawa. Bawani batun wanka ko gargajiya amma komai Alhamdullah. Ga yara sunata ƙyau abinsu kamar ka lashe. Bayan sunan ne AA da Yaya Fawzan suka je Nigeria. Satinsu ɗaya suka dawo, sai dai sun biya ta saudia sun ɗakko Naufal da suka samu hutu. A zuwa sun nan sosai zuciyar Mamy ta karaya, dan ta gama yarda dai ƴaƴanta ba nata bane ba na Fateema ne. Mijin ma nata ne. Duk da nadama ta mamayeta ta gagara ɗaga baki ta nema gafarar kowa har yanzu. Sai aikin kuka, su dai su AA sunta lallashinta da mata nasiha iya iyawa. Sannan suna mata dukkan gatan daya dace akan komai tsaye suke a kanta. Kai bama su ba ko Baba Sardauna da su RK hidima sukema Mamy sosai, kawai dai sunan bata a gidan Darma ne yanzu. Sai nakasan ƙafa data ido data zuciya dake zagaye da ita. Idan akai dubi ta wani fannin kuma data gangar jiki saboda HIV. Amma da yake tana shan magani bama zaka gane ba. Zuwan Naufal yama kowa daɗi, yaro ya ƙara girma ya fara zama ɗan saurayi, kamaninsa da su AA ya fito tsaff kamar sunyi kaki. Abin mamaki ko tambayar Saheeba baiyi ba. Sai ma farin cikin ganin su Oum da sabbin ƙanne har huɗu daya samu. Duk motsi sa kuwa yana manne da yaran nan. Yay hutunsa ya gama Abah da Oum suka maida shi Saudia, suma sun ɗan huta na sati uku sukai umrah suka wuce Nigeria dan Baba Sardauna baya jin daɗi. Sun duba shi aka gaggaisa da ƴan uwa da abokan arziƙi, har gidan Mamy Oum taje. Taji daɗin kuma ganin yanda Mamyn take cikin kulawa mai tsafta da nagarta. Suka sha hira Mamy na faman kukan zuci. A yanzu ma ALLAH bai bata damar roƙon Oum gafara ba. Girman kai da taurin zuciya na hana bakinta buɗewa akan hakan. Satin su Oum biyu a Nigeria suka koma abinsu....

________★

Rayuwa mai daɗi da nagarta ta cigaba da wanzuwa a cikin zuri'ar Aliyu Abubakar Darma. Hankalinsu ya kwanta matuƙa yanzu. Ga yara sunyi ɓulɓul da su su twins na gudunsu da magana ras. Zarah da Khadee ma na fara koyon tafiya. Yara masha ALLAH kamar ka lashe dan ƙyau da kulawa. Su dukansu basa ma banbance iyayensu saboda haɗin kai da iyayen ke da shi. Kowa ya yarda shi uba ne, kowacce ta yarda ita uwa ce. Yanda zata kula da wanda ta haifa, haka zata kula da wanda bata haifa ba. Mafi yawan lokaci ma a wajen Oum suke kwana. Suna da shekara ɗaya a Chaina Maanal, Ameerah, Najmah suka zo Nigeria halartar bikin yaran gidan su Ammie da zagaya dangi. Kowa ya gansu sai ambaton masha ALLAH. Yaransu kamar a cinye dan so. An sha biki daya amsa sunansa biki, dan kuwa Daddy yara takwas ya aurar a rana ɗaya. Hajiya Basariyya tazo abin tausayi, ta haihu tuni yaron ma ko isashiyar lafiya bai da shi sikila ne. Gaba ɗaya sai ta tsangwami kanta, ta kuma gigita da ganin irin daular duniyar da su Ammie ke ciki yanzu. Da itama bataima kanta mugunta ba da harda ita anan fa. Amma gashi nan masu aikin gidan ma sun fita fasali da ƙyawun kallo. Da taga Maanal kuwa ai sai ta ƙara sakin baki. Yarinyar ta girke abinta ta zama cikakkiyar mace komai yaji, ga ƙyau ga gayu ya ranta abin sha'awa masha ALLAH. Ko wajen events Hajiya Basariyya bata iya zuwa saboda kunya. A hakan ma Huznah ta mata ɗinkuna masu tsada, amma kayan daban jikinta daban koda ta saka. Duk sanda idonta ya sauka akan Daddy sai tayi kuka dan tausayin kanta. Sai ma taga kamar an ƙara masa wani ƙyau da ƙuruciya shi da matan nashi. Haka dai akasha biki amare aka kaisu gari daban-daban, Khadijah kawai aka kawo Abuja gidan Yaya Yazeed. An kammala biki da kwana biyu ALLAH yay ma Gwaggo rasuwa. Dama su Maanal nada planing ɗin zuwa Giron sai kuma ga dalili. Haka suka shirya suka tafi ita, Amaal, Shaheeda da Ammie sai Nene, dan Aunty Sakina mijinta ya hana itama da yake tana aure yanzu anan cikin Abuja. Duka harda yara suka tafi. Sun ko samu tarba ta girmamawa, haka akai zaman uku da su, Gwaggo dai ansha jiyya sosai, dan ita duk da tana shan maganin HIV ɗin abin ya haɗa mata da tsufa shiyasa ta jigatu. Babu dai Alhamdullah, sai Sailu ce dai duk ta rame tayi baƙi, kodan abin ya mata yawa ne ga baƙin cikin Haƙilah da ɗanta, dan ta haihu namiji yaro kama da ubansa Temo sak. Kaida ka ganshi kaga ɗan ƙabilu, ga cin masifa kamar jaki. Bai fi shekara ɗaya da rabi ba amma cizon ƴaƴan mutane da yagushi ba'a magana. Idan akai magana Haƙila ta tsige mutum tas. Yawonta kuwa babu abinda ta fasa sai tai kwana uku bata gida, haka take barma Sailu ɗan kuma dole ta kula da shi, idan ta dawo kuma tai ta mata tujara kamar ba uwarta ba. Shi dai Sule ALLAH ya taimakesa, yana cikin Sokoto yanzu haka yana karatunsa na addini dana boko. Idan ka ganshi kamar ba shi ba, ya nutsu sosai masha ALLAH. Hakan yama su Maanal daɗi suma, sun kuma tabbatar masa yana kammala wannan makarantar Saudia zasu nema masa gurbin karatu. Aiko yayta murna da farin ciki. Haƙila kuwa da sukai ma faɗa ganin tana neman musu rashin kunya sai suka ƙyaleta suka ma fita sabgarta har akai uku suka baro garin. Suka bar Babu da kuka da kewar ƴan jikokinsa. Har yanzu zuciyarsa ta kasa sabawa da rashin Ammie, a kowane motsinsa cikin tuna rayuwarsu ta baya yake da nadamar kuskurensa. A wannan karon ma haka yayta neman gafararsu har su Maanal. Suna dawowa Abuja da kwana biyu su Maanal suka fara shirin komawa Chaina, dan mazajensu fa sun dame su. Najmah na Kano, dan haka Ameerah da Maanal suka shirya suka sameta acan suma. Sun zagaye ahalin Darma har Yola wajen Gwaggo Khadijah. Har gidan Huznah suka je itama akai zuminci. Maanal taji daɗin ganin yanda rayuwar Huznah ta canja, dan sun sake gida ma yanzu ga ƴan yaranta uku gwanin sha'awa. Daga ƙarshe suka yada zango a gidan Mamy. Mamy taji sun zo ƙasar, amma bata san suna Kano ba. Yau tunda ta tashi bata jin daɗi, ga Aunty ta fita biki a dangin mijinta. Sai ita kaɗai a gidan sai mai aikinsu. Tana tsakar gida tana shan iska Ahmad da Muhammad suka shiga gidan da gudu, Najma na kiransu amma ina basu dakata ba. Suma Zarah da Khadee na ganin yayinsu sun yi ciki sai suka bisu da nasu gudun. Gaban Mamy sosai ya faɗi, ta dinga bin yaran da kallo dan Muhammad dake gaba na shigowa kawai ya fara zagayeta Ahmad na binsa suna dariya, su Zarah ma sukabi layi. Zuciyar Mamy na bugawa tana musu magana amma basu kulata ba sunata dariya da gujegujen su. A haka su Maanal sukai sallama suka shigo. Sai da kan Mamy ya nema fashewa. Ganin wasu cikakkun mata ƴan gayu ƴan ƙwalisa da kallo ɗaya zakai musu kasan nera ta zauna a jiki da suturarsu. Ga wani ƙamshi na girma ya cika tsakar gidan. Sai da Ameerah tama yaran tsawa suka tsaya cak sannan Mamy ta dawo hayyacinta. A nutse suka ƙarasa shigowa fuskokinsu da murmushi suna mata sannu. Fahimtar kamar bata ganesu bane yasa Najmah faɗin, “Mamy Maanal ce da Ameerah da Najma. Sai jikokinki”. Gaba ɗaya sai lips ɗin Mamy suka fara rawa, idonta ya cika da ƙwalla. Da ƙyar tai musu jagora zuwa cikin gidan. Sunata kallon ko'ina su dai. Bayan sun shiga sun zauna mai aiki ta kawo musu ruwa. Cikin girmamawa suka gaida Mamy, ita ko tana amsawa da rawar murya. Maanal ta harari yaran da suka tsaya suna kallon Mamy kamar sun sami magiji. “Wai baku iya gaisuwa bane ba yaran nan”. Da sauri Muhammad ya kama kunensa ya ce, “Sorry Mie-mie”. Ganin haka shima Ahmad ya kama nasa kunnen, hakama su Zarah, suka haɗa baki suka ce “Sorry Mie-mie” bakuna a taɓe abinka da ƴan madara🥱. Maanal ta ce, “Oya naji a gaida Mamy”. A tare yaran suka matsa inda take cike da ladabi bakinsu a haɗe sukace, “Mamy good afternoon”. Yawu mai kauri Mamy ta haɗiye. Tana murmushin yaƙe ta ce, “Kuna lafiya?”. Kansu suka ɗaga mata dan suna jin hausarsu tsaff. Ganin tayi shiru Ahmad ya ce, “Baki ce ya Grandpa da Grandma, da Daddy's ɗinmu ba?”. Mamaki ya kama Mamy, ga shi su duka huɗu sun wani tsareta da idanunsu sak irin na Aliyu da Fateema da su AA. Sai kunya ta kama su Maanal. Najmah ta ce, “Ta tambaya a zuciya, oya azo a zauna”. Mamy zatai magana sai ga Aunty, yanda Aunty ta nuna farin cikin ganinsu ta kuma shiga kiran sunan yaran ɗaya bayan ɗaya da buɗe musu hannaye alamar suzo sai sukafi sakin jiki da ita. Da gudunsu kuwa sukaje suka shige jikinta suna dariya kamar sun santa. Dan su basu da wahalar sabo, in dai zaka jasu a jiki yanzu zasu sallama. Sai abin kuma ya dami Mamy taji kunya sosai. Sai bin yaran take da kallo dake nane da Aunty, itako sai nannan take da su kamar zata cinye. Basu sake kula Mamy ba kuwa. Ana haka sai ga AA ya kira video call. Yaran suka shiga ɗoki suna kiran Abie-Abie. Shi ko sai murmushi yake musu cike da kulawa da soyayyarsu. Labarin abinda Aunty tai musu suka shiga bashi, su Zarah bakin bai gama nuna ba sai murmushi suke saka shi.........✍️216

..........Haka dai ya biye musu sai da kowa ya gama bashi nashi labarin su duka huɗun sannan ya gaisa da su Aunty, godiya yay mata sosai, itako tana harararsa da daƙuwa. Wai dan mi zai mata godiya ita da jikokinta. Mamy ma ta amsa suka gaisa. Yanda batai masa maganar yaran ba shima bai mata ba. Haka yaran suka ƙara amsa suka koma gefe sun hana iyayen. Dama haka suke musu, wataran har gori suke musu idan sukai magana. Musamman Ahmad ya iya faɗin “Ai Daddy's ɗinmu ne dai”. Suko suce ikon ALLAH ai mu daga sama muka faɗo. Haka AA ya biye ma yaran nan sunata shiririta har Babban Yaya da Yaya Fawzan suma suka samesa suka ɗora, da ƙyar suka yarda sukai musu sallama Khadee harda kukanta sai da Maanal ta goyata aka samu lafiya. Yaran nada shaƙuwa sosai da iyayensu bata wasa ba. Koda su kaɗai suka taso suke gani sai kakanni su oho. Anan gidan suka kwana, washe gari suka shirya komawa Abuja Manaal bata jin daɗin jikinta. Aunty ta haɗa musu shatara ta arziƙi. Mamy kam sai kukan zuciya. Amma ta buɗe baki ta nema gafararsu suma ta gagara. Haka suka koma Abuja. Kwannasu biyar da dawowa suka fara shirin wucewa. Maanal ta ziyarci Mawaad Company har sau kusan uku. Ta duba komai yana tafiya dai-dai yanda ya dace. CFO dai ta ajiye aiki tuni. Su Zaharadeen sai wani bata girma suke. Yaqub daya kara samun girma a yanzu yana matakin Designer director shima har gidansa taje sukai zuminci da matarsa mai kirki, haka taita girmama Maanal taima Khadee da Zarah kitso dan dasu taje....

★★ Randa suka dawo Chaina mazan nasu ne da kansu suka je tarbosu. Ba kunya suka rungume su sannan suka koma kan yaransu. Sun iso gida Oum ta shirya musu beta dan yanzu sun canja wajen zama. Suna a gidan dake ɗaukar family ne gaba ɗaya. Sun sami Naufal yazo hutu, sai dai sunyi ƴar tafiya shi da Abah sai dare suka dawo. Tuni yara suka tare wajen Oum da Abah da Naufal. Su AA suka sami filin sharafin baje soyayya dan sunyi kewa. Maanal ma dai dauriya kawai take dan bata jin daɗi. Sun dawo da sati ɗaya jikin nata ya takura mata AA ya ɗauketa suka je asibiti. Gwajin farko aka gane ciki ne. Zo kaga murna wajen Abah, Oum, Babban Yaya, Yaya Fawzan da uban gayya AA. Haka Ameerah da Najma ma. Kowa addu'a sauka lafiya yake mata. Wannan karon dai kam laulayi take sosai tun a farkon cikin, sai da ya shiga wata na huɗu ta samu lafiya da ƙarfin jiki. Haka suka cigaba da rainon cikin nan kowa na bata kulawar data dace. Gefe AA na kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a zuciya. A haka ALLAH ya kaita watan haihuwa, wannan karon ma aka ciro mata baby girl mai kama da iyayenta. Hotunan baby ya cika wayoyin dangi, washe gari RK da Nuwaira suka isa Chaina da yaransu biyu suma kyawawa. Sosai su Oum suka farin ciki da zuwansu, nan fa suka haɗu aka sha shagalin haihuwar Baby. Bakin AA ya kasa rufuwa dan farin ciki. Ranar suna yarinya taci suna Ruƙayya, zasuma ce mata Urwa. Wannan karan kam RK ya shirya walimar da akaci aka sha aka gagije. Bayan suna maijego ta cigaba da jegonta kafin a koma filin daga. Suma su Ameerah suka fara nasu laulayin kuma. Ai a wannan gaɓar Mamy tama rasa nacewa, UBANGIJI ya tabbatar mata shine maiyi da tsarawa bayinsa rayuwa. Ga dai masu cikama ƴaƴanta burinsu nan da ƴaƴaye. Wani lokacin a ɓoye take saka hoton yaran su shida reras da iyayensu uku da Oum da Abah sai su Maanal taita hawaye. Tayi mai isarta ta goge dan ko Aunty bata bari ta gane duk da aunty tana ƙyaletane kawai amma ta gane komai. Amma tunda tana ɓoyewa sai take barinta a hakan kawai...

★★ Urwa nada shekara ɗaya da rabi, yaran Ameerah da Najma da suka haima duk maza suma Abubakar, da Umar nada watanni bakwai-bakwai jikin Mamy ya rikice. Babu ɓata lokaci su Oum gaba ɗayansu har Abah suka nufo Nigeria. Kai tsaye Kano suka sauka, maimakon gida kuma asibiti suka wuce inda take kwance. ALLAH mai girma da ɗaukaka sun shiga ɗakin da take kawai ta zuba musu ido tana hawaye. Magana take son yi amma babu baki dan kwana uku kenan maganarta ta dakata. Haka taita kallonsu da idonta ɗaya tana hawaye. Su Naufal na zagaye da ita su takwas cas sai iyayensu a bayansu, Oum Abah da su Maanal na gefensu. Sai Aunty da yaranta suma. Ta kafe Abah da ido na tsawon lokaci sannan ta koma kan Oum, ta juya idanun ta sauke akan su Maanal ɗaya bayan ɗaya sannan ta maida kan su AA, tai ɗan murmushi ta maida kan su Naufal. Fin mintuna biyar tana kallon yaran sai tari, sai aman jini, abu kamar wasa dan danan aka nemo likita. Su kuma akace su fito. Cikin abinda bai wuce awa guda ba ALLAH yay mata rasuwa. Sai likita fitowa yay jiki a sanyaye... Hawaye sosai Oum da su Maanal da Aunty keyi. Abah ya duƙar da kai kawai yay shiru, haka ma su Babban yaya idanunsu duk sun kaɗe hawaye na cika su. Sosai tausayin mahaifiyarsu ya kamasu na rashin neman gafarar mutane da batai ba. Duk da sunyi iya ƙoƙarinsu na ganin tayi hakan amma ALLAH bai bata iko ba. Haka aka ɗauki gawarta, zasu wuce gidanta da ita Baba Sardauna yace a kawota gidansa. Hakan ya saka su Babban Yaya jin daɗi, a gidan Baba Sardauna akai mata wanka aka shiryata, sannan aka sallaceta aka miƙata makwancinta na gaskiya. Ahalin Darma sun nuna dattako da kara sosai. Dan har na nesa sai da suka dawo har ma wanda basa ƙasar ƴaƴa da iyaye. Hakama su Ammie, su Hajiya Shuwa da ƴan uwa da abokan arziki duk sunzo. Tsohon shugaban ƙasa mai sauka ma yaje da tawagarsa. Manyan mutane darajar ƴaƴanta da tsohon mijinta sun taka rawar gani. Haka akai addu'ar uku gidan baba Sardauna cike. Ko abinci ba ƙaramin aiki yayi a gidan nan ba sai godiyar UBANGIJI. Dan rasuwa yanzu ta zama tamkar biki musamman idan kana da gata. Bayan addu'ar bakwai suna shirin wucewa aka sake wata rasuwar. Babu ya rasu a Giro. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, sosai su Maanal sukaji rasuwar nan suma. Haka aka ɗunguma akai Giro kuma. Ba'a biznesa ba sai da suka isa. Harda su AA da su Babban Yaya, su baba Sardauna duk aka sallaceshi aka kaishi gidansa na gaskiya. Nan ma kwana su uku sai da akai uku sannan suka wuce aka bar su Maanal kawai da su Ammie, Amaal, Shahidah. Sai da akai bakwai har ma suka ƙara kwana uku akai sannan sukai shirin barowa. Koda aka raba gonakin gadon daya bari haka suka ɗauka suka bama Sailuba su da Sule dake kuka matuƙa kamar ransu zai fita. Haƙila kam tayi gaba babu wanda yasan inda take. Wasu suce tana Lagos, wasu suce tana Tafa, ALLAH dai kaɗai yasan tana ina sai ita. Su Maanal sun taho sun bar ƴan Giro da kewa. Dan sun san yanzu kam ganinsu zai musu wahala ai. Tunda dama dan mahaifinsu suke zaryar zuwa. Yanzu ko babu shi sai ta ALLAH kuma. Sun dawo Abuja juma'a su Maanal suka koma Chaina Lahadi........✍️217

..........Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun canja, su AA sun dawo Nigeria gaba ɗaya, sai dai sun sake gida dan Abah da su kansu basa son tuna komai daya faru a waccan. Sabuwar rayuwa, sabon family, sabon muhalli.

Readers Also Read