Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 20

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 20

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 20: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 20. .......Saurin janye idanun nata tai…

3,486 words

.......Saurin janye idanun nata tai ƙirjinta na wani masifar dokawa. Sai dai ta wani dake a zahiri yayinda fuskarta ke sake komawa ciɗin-ciɗin fiye da yanda tashi take. Boss ne da kansa ba wani ba. Wato AA Darma, da alama shima ya makara fita sallar ne, dan illahirin fuskarsa da hannayensa da ƙafarsa dake sanye da slippers daya saka dan ba takalman da yazo dasu a ƙafarsa bane cover shoes sai nason ruwa suke yi. Elevator na tsayawa itace tai saurin fara ficewa dan harga ALLAH jinta take kamar an matse a cikin rami tsabar yanda ya cika ko'ina da kwarjininsa. Da kallo ya ɗan bita, sai kuma miya tuna oho yay saurin janye idanunsa shima yana fita daga elevator ɗin. Dukansu basu samu raka'ar farko ba. Koda aka idar da sallar mafi yawan ma'aikatan sun wuce kitchen ne kai tsaye, dan ana musu abincin rana a wajen harma dana safe. A manyan dai ba kowa ne ke nufar kitchen ɗin ba sai wanda yaso hakan kasancewar suna da damar sakawa a kawo musu har office. Manaal ma daba gama sanin tsarin tai ba duk da an bata komai a rubuce tun a ranar interview karantawa ne batai ba office ta koma. Hankalinta a rarrabe sai dai tana iya ƙoƙarin ta na ganin ta saita kanta ta buɗe lunch box ɗinta ta fidda abincinta ta hau ci tana cigaba da sarrafa computer ɗinta domin maida aikin zanen da tayi a ciki. A haka a shiririce ta gama shigar da komai kafin ta naɗesa a flash drive ta ajiye. Koda an buƙacesa a wajen meeting da shi zatai amfani. Knocking ƙofar akayi, batare da ta canja daga yanda take ba ta bada iznin shigowa dan ita kaɗaice har yanzu su Yaqub babu wanda ya dawo. Wata budurwa ce da bazasu wuce sa'anni ba. Sanye take da skirt da riga na atamfa sai ɗan mayafi data yana. Cikin girmamawa ta gaishe da Maanal ɗin. Amsa mata tai da kulawa. Hakan sai ya saka yarinyar farin ciki dan yanzu ake gulmar Maanal ɗin a ƙasa cewar dagani zatayi girman kai, sai kuma ita tazo taga ba hakan ba yanzu. “Sunana Mabaruka Rabi'u. Ina ɗaya daga cikin Sales and Marketing Department. HOD ne yace a sanar miki ana buƙatarki a ƙasa idan babu damuwa”. Cikin ɗan sakewar fuska da ba murmushi take ba Maanal ta ce, “Okay sister Mabaruka ba damuwa gani nan tafe”. Murmushi Maburaka ta mata tare da sake ɗan rissinawar girmamawa ta furta, “Na barki lafiya”. Daga haka ta fice a office ɗin. Ajiyar numfashi Maanal ta ɗan sauke, sai kuma ta shiga tattara tarkacen kayan da taci abinci ta maidasu a lunch box ɗin. Ruwa tasha ta ɗan gyara fuskarta sannan ta miƙe ta fice a nutsenta daga ita sai wayarta a hannu. A First floor ta samu kusan dukkan ƙananun ma'aikatan harda waɗanda ba nan ɗinne mazauninsu ba. Sai dai da'alama duk an tattarasu anan ɗinne dan har su Yaqub ma suna a wajen ashe. Duk da cika mata idon da sukai haka ta dake ta gaishe da HOD dake ta faman sakar mata murmushi. Yana ɗaya daga cikin wanda sukai mata interview. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya juya ga ma'aikatan yay sallama. Duk amsawar sukayi duk da kuwa ba dukane musulmai ba a wajen. Ɗan juyowa yay tare da nuna musu Maanal cikin harshen turanci ta ce. “Wannan itace sabuwar _Watch Designer_ ɗin Mawaad Company da aka sake ƙaro mana in sha ALLAHU, zatai muku introducing kanta”. Tafi suka shiga yi gaba ɗayansu. Hakan yasa Maanal ɗan sakin murmushi tana binsu da kallo, sai da suka lafa sannan ta gyara tsaiwarta cike da nitsuwa ta furta, Sunana Maanal Habeeb Giro. Junior Watch Designer kamar yanda aikina HOD ya faɗa. Ina fatan zan samu haɗin kai da yarda daga gareku baki ɗaya”. “In sha ALLAHU!!”. Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ta sakar musu a karo na biyu mai matuƙar taushi. Sai kuma ta haɗe hannayenta waje guda ta sake furta, “Ina mika godiya a gareku da fatan alkairi baki ɗaya. ALLAH ya bamu ƙwarin gwiwar sauke hakkin dake kayinmu baki ɗaya”. Nan ma sun amsa mata da amin. Daga haka HOD ya ɗan ƙara mata bayani akansu. Kafin ya sallamesu kowa ya koma kan nasa aikin. Ita kuma suka nufi elevator tare da shi. Sai faman zuba mata surutu yake ita dai batace komai ba sai ɗan murmushi da take masa na karar haɗuwar farko. Conference room suka nufa kai tsaye daga nan. In da ta sami dukkanin shugabannin da alama su ake jira ma a wajen. Wajen zama duk suka nema, a dai-dai kuma lokacin CEO ya shigo AS ɗinsa biye da shi. Duk miƙewa sukai alamar girmamawa, sai da ya zauna AS ɗinsa ya ajiye masa kayan hannunsa gabansa sannan ya ɗan ɗago ya dubesu. Zaunen suka kai suma a nutse, daga haka room ɗin yay ɗan shiru na kusan mintuna uku kafin ya ajiye tab ɗin hannunsa da yake sarrafawa yay gyaran murya yana kallonsu cike da dakewa da nutsuwarsa. Suma sake nutsuwar sukai da maida hankalinsu garesa. Banda Maanal da tun kallon farko data masa a sanda yake shigowa ta ɗauke kanta bata sake ba. Gaba ɗaya jinta take a takure a wajen dan su biyu ne kawai mata. Sallama yay musu kafin ya sauke dubansa ga tab ɗin gabansa ya fara magana acan ƙasan maƙoshi. “Wannan taro ne daya haɗa ɓangarori guda biyu, wato na shugabanni da kuma ƙirƙira da zane na wannan company. Wato Executive Team da kuma Design and development. Kafin kai tsaye mu fara abinda ya kawo mu akwai sabuwar staff data shigo cikinmu zai ƙyautu ta gabatar da kanta anan”. Ji Maanal tai kamar ta kai masa naushi dan haushi, amma sai ta dake taƙi koda motsi sai da CTO dake gefenta yay mata magana ƙasa-ƙasa. “Sistet Maanal”. Komai batace ba ta miƙe cike da kamewa ta furta, “Sunana Maanal Habeeb Umar Giro. Junior Watch Designer in sha ALLAHU”. Sunyi welcoming nata baki ɗaya tare da mata fatan alkairi. Bayan ta koma ta zauna ya cigaba da faɗin, makasudin shi wannan zaman akan sabon project namu ne in sha ALLAHU. Wasu sun san da shi wasu basu sani ba saboda rashin samun zaman meeting da ba'aiba a wancan satin gaba ɗaya. Akwai Companyn da zamu fitar ma sabon agogo, sun kuma bamu zaɓi kafin mu sake zama dasu. Dan haka Design and development ko kuna da wani sabon design da zaku gabatar mana mu duba?”. Bayan Maanal akwai Watch Designers Directors har uku a wajen, sai dai dukansu kowanne nada iya limit ɗin aikinsa ta yanda baya shiga aikin wani. Hakan yasa ɗaya daga cikinsu ɗagowa ya ɗan dubi Boss ɗin. “E to Sir bamu san ko yaya tsarin project ɗin zai kasance ba. Sai musan a cikinmu wazai bada sample” Kansa ya ɗan gyaɗa, sai kuma ya kai dubansa ga Sales and Marketing Manager. Da sauri ya miƙe dan yasan minene ma'anar kallon. Bayani yay a taƙaice, Dan haka sai duk suka maida hankalinsu ga Director Steven. Kansa ta gyaɗa shima tare da maida kallonsa ga Maanal, suma sauran duk sai suka koma kallonta. Yanda suke kallon natane ya bata mamaki, kafin ta nema ƙarin bayani Director Steven ya ce, “Wannan aikinki ne Sister Maanal. Idan kinada wani sample na zane a ƙasa company na buƙatar gani, idan kuma babu zaki iya neman lamanin samarwa”. Gaba ɗaya sai Maanal taji ma kamar zata daburce. Amma ta shiga ambaton ALLAH tare da aro jarumta. Cikin ƴar dakiyar da nutsuwar data azama kanta ta dole ta bata ta jinjina ma Director kanta. Sai kuma ta ɗan kallesu itama ta fara bayani. “Zan iya gabatar da wanda ke a hannuna ɗin idan basuyi ba sai na sake wasu sabbi”. Cikin gamsu duk suka gyaɗa mata kai, kafin boss ya gama shan ƙamshinsa batare daya kalleta ba ya furta, “Zaki iya nunawa”. Bata tanka ba, sai dai ta miƙe hannunta ɗauke da flash drive data naɗe zanen ɗazun da tayi. Amsa Director Steven yayi a matsayinsa na shugaban sashenta, ya nufi ƙaton television dake kusan bango guda a room ɗin yay connecting, atake ɗan tambarin data saka na farko mai ɗauke da zanen agogo mai ƙyau da zanen fuskarta a tsakkiya ya bayyana. Remote ɗin Director Steven ya miƙa mata, dole ta fito daga inda take tsaye ta koma gaban tvn. A nutsenta ta fara danna hoto na biyu ya fito, agogone mai ƙyau da tsari matuƙa duk da kasancewar a zane yake. A take duk suka shiga ambaton, “Woow!! Woow!!” a hankali. Shi dai boss kaimai baice ba, amma fa ya zubama hoton idanu yanda ya kamata, bayani tayi cikakke akan agogon da tsarinsa da nauyinsa. Sai kuma ta koma nuna sassan jikinsa da sunayen data basu da yanda yakama ace ingancinsu ya kasance. Da ƙarshe tai bayanin yanda agogon zai iya buƙatar ingantaccen aiki kafin fitar da shi. Tafa mata suka shigayi tamkar conference room ɗin zai buga shima. Dan har ga ALLAH tayi matuƙar gama birgesu, tayi dukkan bayanin da har sauran ɓangarorin zasu iya yi. Ashekaru kaf ɗinsu babu wanda bai bata fin shekara goma zuwa ashirin ba, dan itace ƙarshen ƙanƙanta da ƙarancin shekaru a cikin nasu, hatta da ɗayar macen zata iya girmar Shahidah ma balle ita. Taji daɗin yanda suka yaba mata duk da shi mai gayya da aikin baice komai ba dai. Sai da duk suka lafa itama ta dawo ta zauna a nata mazauni kafin yay ƴar gyaran murya. “Zamuyi nazari akan wannan ɗin, amma WD Maanal zata iya samar mana da wasu samples kamar uku bayan wannan daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai ku haɗasu a sake tattaunawa”. Duk sun gamsu da hakan. Dan haka ba'a wani sake jan zancen ba taron ya watse. Shine ya fara ficewa a room ɗin AS ɗinsa biye da shi. Duk miƙewa suma sukai hankalinsu akan Maanal suna sake jinjinama ƙoƙarin ta da ƙarfafata. Itako sai wani ɗan karen daɗi take ji kamar ta ciji uwawunta. Ta ƙara ta fita a wajen ta kira Ammie ta bata labari, kai har RK sai yasha labari yau....

Koda Maanal ta koma office zaman wasu sabbin samples na zanen ta fara dan babu wasa batare data kula kowa ba. Garama Yaqub ya mata sannu da zuwa. Tayi nisa a aikin nata akai mudu knocking ƙofa. Batare data ɗago ba ita dai taji sauran na magana da shi. Saurayine kamar su Yaqub da zai iya girmarta ita kam a shekaru, amma kasancewarsu oganninsa cike da girmamawa ya gaishesu. Sai kuma ya maida hankalinsa kan Maanal. Hakanne ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. Duk da tayi mamaki sai ta danne, ta amsa masa da kai. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Sister Maanal kinada visitor”. “Visitor?”. Ta maimaita da mamaki. Sake tabbatar mata da hakan yay ta ha hanyar jinjina kansa. Ta ɗan yi shiru kamar mai nazari tana wasa da pencil akan lips ɗinta sai kuma ta ce, “Okay ina zuwa”. Da girmamawa ya amsa mata da, “Ai kamar ɗan gida yake. Bari na masa iso”. Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Ba'a rufa mintuna biyar ba aka sake knocking ƙofar. Zamanta ta gyara da veil ɗinta, yayinda hankalin su Zaharadeen duk yana akan mai shigowar. Yana buɗe ƙofar ƙamshin turarensa na rige-rigen fara iso mata a hanci, hakan yasa ta ɗan ɗago idanu ta kallesa. Murmushi ya sakar mata yana jingina da ƙofar tare da harɗe ƙafafunsa da hannayensa a ƙirji. Sai kuma ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa ƙirar kamfanin Samsung mai ƙyawu da tsada ya shiga mata hotuna. Hararsa ta ɗan yi tana mai girgiza kanta ta maida ga abinda take yi. Sai da ya gama dan kansa kafin ya kai duƙe ya ɗauki abinda ya ajiye a ƙasa yana ƙarasa shigowa da faɗin, “Oh oh my queen Kinga kuwa yanda kujerar nan tai matuƙar dacewa da ke. Kin gama cika Watch Designer Maanal ɗinki Tawajena. Dan haka ina tayaki murnar shiga sabon Office. Amin afuwa dana kasance a late, tun safe naso nayi hakan uziri yasa ban zauna ba na koma asibiti. Naso tahowa da rana hakan bai yiwu ba kuma dai”. Ita dai kallonsa kawai take yana tsiyaya surutunsa kamar yanda sauran ma ke kallonsa suna murmushi. Hannu ya shiga basu, suna amsa da sauri da kuma girmamawa dan sun san yana da wani babban matsayi da kima a companyn. Dai da ya gama gaisawa da su ya maido hankalinsa kanta yana fiddo cake mai ƙyau daga cikin kwalinsa. Sai kuma ya tsitstsira abu a kansa kamar wata mai shirin hure birthday cake ya kunna masa wuta. Ɗauka yay ya zagaya ta inda take ya ajiye a gabanta sosai bayan ya tattare kayan zanen dake a gabanta ya ɗauke su gefe........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣9️⃣

.........“Bismillanku”. Ya faɗa idonsa akansu Zaharadeen. Sai kuma ya koma ga ƙofa yana faɗin, “Kuma ku shigo”. Mamakine ya kamata ganin ma'aikatansu kusan su goma sun shigo harda AS ɗin Boss. Gaishesu sukai saboda kusan dukansu suna a sama da su. Da kai kawai ta iya amsa musu ita dai saboda al'ajabin RK. Daga haka ta juyo tana masa wani kallon. Ganin yanda ta zuba masa manyan idanun nata masu rikitashi ya wani langaɓe kansa da marairaice fuska yana ɗan duƙowa gab da ita ta yanda ita kaɗaice zata iya jinsa a maganar da zaiyi. “Please ki daina min irin kallon nan kina rikita min lissafi na ne”. Harara ta ɗan sakar masa tare da janye idanun gaba ɗaya. Babu yanda ta iya da fitinar RK dole ta hure kamar yanda yake buƙata, dan ya tabbatar mata idan batayi hakan ba babu inda zaije yau. Ganin yaja kujera ya zauna ga mutane ya cika musu office da su ya sata hurewar kawai dan kaɗan kenan daga aikinsa ya zauna ɗin. Cake ne dai duk yanda yayi taci ta gutsira ta bashi a baki ƙi tayi, sai ma tai kicin-kicin da fuska ta yanda dole ya haƙura dan baya son yaga ta haɗe masa ƙyaƙyƙyawar fuskar nan tata damuwa yake shiga. Haka dole da kansa ya gutsira yaci ya miƙama wanda ya gayyato da su Yaqub dake a office ɗin kowa ya yanka yasa a baki. Daga hakan nutsuwa yay sosai yay mata addu'oin fatan alkairi da nasara a wannan aikin, ita harma hakan yaso bata mamaki, yayinda sauran ke amsawa da amin. Bayan ficewar kowa ya wani zabga tagumi yana kallonta. Itako ta sake maida hankalinta ne a aikinta. Sai da taji kallon nasa na neman cutar da ita ta ɗago ta kallesa tare da sakar masa ƴar harara, sai kuma tai masa nuni da su Yaqub da ido. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa da gyara zamansa. Ita kuma ta maida kanta yay ƙoƙarin dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. “Maanal”. Har tsakkiyar kanta taji yanda ya ambaci sunan nata. Kodan ba cika kiranta da sunan yay ba akoda yaushe oho. Sake ɗagowar tayi ta dubesa batare data amsa ba. Bai damuba ya cigaba da faɗin, “Maanal dan ALLAH ki iyakance min wahalar nan mana, na isa aure fa, ga kuma mata a kusa dani miya rage kuma dan ALLAH?”. A hankali yake maganar yanda ita kaɗai ke jinsa, duk da kuwa su Zaharadeen sarakan gulma sun baza kunne amma basa jiyo komai. Lips ɗinta ta ɗan cije zuciyarta na mata nauyi, (miyyasa su basa fahimta ne, miyyasa bazasu gane ba. Ita fa Maanal, wannan Maanal ɗin da suke gani gaba ɗaya a yanzu babu zuciya a ƙirjinta, in dai zuciyace ta soyayya ta ta jima da mutuwa......) “Maanal!!”. Ya sake katse mata tunani, yanzu ma bata amsa ba sai dai ta janye idanunta da suka cika da ƙwalla daga kansa. Aikinta ta cigaba da yi tana ƙoƙarin haɗiye hawayen. Shima sai yay murmushi kawai tare da miƙewa gaba ɗayansa. “Ƙarfe nawa zaki tashi?”. Batare data ɗago ba dan bata son yaga yanayinta ta ce, “Bazan iya cewa ba, saboda ina son kammala aikin nan duka a yau ɗin”. Ɗan jimm yay sai kuma ya jinjina kai da faɗin, “Okay bari na kiraki kawai, ko kuma zuwa six, I will come back kawai”. “Okay thanks”. Ta faɗa a taƙaice. Shima sai ya ɗan murmusa kawai ya juya ya fita abinsa yana ma su Zaharadeen dallama. Fitarsa bai fi da mintuna biyar ba kira ya shigo a wayar gabanta. Koda ta ɗaga sai ta samu AS ɗin Boss ne, wai boss ɗin na son ganinta a office ɗinsa. Idan tace kaɗan ya rage zuciyarta ta wantsalo ta baki kar kuyi mamaki, ta jima shiru da kan wayar a kunnenta bata iya ta ajiye ba. Sai zuwa can ta kife ta da ƙyar ta miƙe cikin ƙarfafa kanta. A dakenta ta isa office ɗin, bayan sun gaisa da AS ya miƙe yana faɗin, “Bismillah”. Komai batace masa ba, yana gaba tana biye da shi har cikin office ɗin. Karo na farko kenan data shigo office ɗin. Ƙaton gaske ne, ya kuma ƙayatu da abubuwan more rayuwa matuƙa gaya. Tamkar ba office ba komai dake a cikinsa fari ne ƙal, hatta da kujerar zamansa da desk kai komai da komai. Sai kuma Mable's ɗin da aka shimfiɗa a ƙasan ya kasance baƙi wulik tamkar wata ajiyayyar kwalba. Ƙamshi kam ba'a magana, ga ac kamar an ƙuresa da gayya. A cikin sakanni da basu wuce biyar ba taima office ɗin wannan kallon. Yana zaune a mazauninsa hankalinsa gaba ɗaya nakan computer ɗin gabansa, yayinda hannunsa ke danna keyboard dinta, na haggu kuma riƙe da document. Yanzu kam ya cire rigar saman suit ɗin nasa sai ta cikin kawai. Duk da shigowar tasu bai ɗago ba balle ya nuna yasan da su. Cike da girmamawa AS da ya ɗan matsa kusan gaban desk ɗin sosai ya ɗan rissina tare da faɗin, “Sir gata tazo”. Sai da ya ɗan ja sakan kusan biyu kafin ya ɗago mayan fararen idanunsa da ke nuna matuƙar gajiya da aiki ya sauke akan AS ɗin nasa. Sai kuma yay luu da idanun ya ɗaukesu daga kansa ya maida ga computer ɗin tare da ɗan kai hannu ya gyara gilashinsa. A can ƙasan maƙoshi ya furta, “Zaka iya tafiya”. Sake rissinawar girmamawa AS yay ya juya ya nufi ƙofa. Sai da yazo saitin da Maanal ke tsaye tayi kicin-kicin da fuska matuƙa a hankali ya furta, “Sister Maanal bismillah ki ƙarasa”. Daga haka ya fice. Yitai kamar bazata ƙarasa ɗin ba, dan ta ɓata fin minti ɗaya kafin ta ɗaga ƙafarta da ƙyar. Koda tazo inda yake maimakon ta zauna sai tai tsaye abinta. Shima yi yay tamkar ya manta da ita sai aikinsa yake kawai hankali kwance. Sunja fin mintuna uku a haka kafin ya ɗago kansa a hankali ya wani zuba mata idanu, sai kuma ya sake ɗaure fuska fiye da yanda ta shigo ta samesa. Cikin ƙausasa harshensa, da tsaurara kalamansa ya furta, “Ba'a baki tsare-tsare da dokin wannan companyn bane?”. A yanda yay maganar yasa ta ɗago nata idanun ta kallesa. Kallon ido cikin ido suka zubama juna, fin miti ɗaya kafin ta janye nata, sai kuma ta canja yanayinta, cikin yanayin girmamawa irin na oga dana ƙasa ta furta, “Am sorry Sir, an bani tun ranar farko da nazo”. Kamar wanda yaji haushin yanda tayi ɗin sai ya wani cije lips tare da ɗauke kansa a lokaci guda. Buɗe-buɗen document ɗin gabansa ya fara yi, sai da ya sake jan minti ɗaya a hakan, sannan ya cigaba da magana batare da ya kalleta ba. “Wannan Companyn ba lambu soyayya bane ko club. Idan buƙatar ganinki yake ko zuwa gareki ai yasan inda kike. Karya sake zuwa min nan da shirme in ba haka ba zan ɗauki mataki a kanku ku duka zaki tafiya”. Tafasa zuciyar Maanal take, tafasa irin mai yunƙurowar nan daga ƙirji zuwa maƙoshi har ka dinga jin turirin a cikin bakinka. Karo na biyu ta ɗago ta dubesa kamar zatayi magana sai kuma ta haɗiye, shiru ta sake yi tana daidaita kanta. Zuwa wasu sakanni kanta a duƙe da girmamawa ta ce, “Kayi haƙuri sir, in sha ALLAH zamu kiyaye. Na barka lafiya”. Daga haka ta juya ta fita abinta. Wani irin wurgi yay da file ɗin hannunsa tare da dukan desk da ƙarfin masifa, sannan yay baya ya kwantar da jikinsa gaba ɗaya a kujerar yana furzar da huci masu masifar zafi...

Readers Also Read