Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 36

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 36

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 36: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 36. .........“Subahanalillahi Naufal ya…

2,241 words

.........“Subahanalillahi Naufal ya akai haka?”. Oum ta faɗa tana kallon Naufal first born ɗin babban Yaya kenan da a safiyar yau suka dawo daga Kano shi da sauran ƙannensa biyu ƴammata. Kafin Naufal da yay ƙwalƙwal da idanu alamar zai yi kuka ya bata amsa ta maida dubanta ga AA da yay tsaye a ƙofar duk ya tare ko'ina babu ma ta yanda zata iya shigowa. Sake leƙo fuskarsa tayi daga bayan san da take sai kuma ta kalla direction ɗin daya zubama idanun. Kallon cikin ido suka zubama juna shi da Maanal.. sai dai kafin ta iya yin wani yunƙuri RK da tuni ya baro inda yake yazo ya kama Naufal ya ɗaga gudun kar ya taka fasashshen plate ɗin daya tarwatse shi kaɗai ya katseta da faɗin, “Alhamdullahi ai babu ma abinda ya zube kamar plates ɗin ne suka suɓuto kawai daga basket ɗin, inaga tuntuɓe yayi ne”. “Ai kasan Naufal da wautan tsiya. Tun da naga ya figo basket ɗin da gudu nasan komai zai iya faruwa. Baka dai ji ciwo ba ko?”. Tai maganar tana kallon Naufal ɗin dai. Kansa ya ɗaga mata cike da shagwaɓa ya ce, “Oum Uncle ne fa ya kusa sawa mu faɗi”. Yanda yay maganar yana kallon AA yasa duk suka kallesa suma. Taɓa AA Oum tayi, dan gani tai ma kamar baya motsi, sai dai kuma tana taɓa shin ya juyo ya kalleta, hannunsa ta kama cikin nata ta rumtse da ƙyau, sai kuma ta juya ga Naufal da RK kema dariya da faɗin, “Ko kuma kai ka kusa sakawa ku faɗin ba. Aunty ai banyi zaton yanzu zaku ma taho ba. “Rafeeq ai bana wasa da Baby na sam. Balle kace yau za'a sallameta shiyyasa nace in sha ALLAHU da wuri zanzo. Sai kuma Auta da nake son yaga likita yau shima”. Karo na farko RK ya dubi AA sosai. Ganin yanda idanunsa sukai masifar kaɗewa ya ce, “Ya Salam badai kan nasa bane har yanzu?”. “Shine kuwa wlhy yaƙi sauka, jiya haka ya kwana a wahale”. Ta bashi amsa tana jan hannun AA ɗin zuwa gaban gadon da Maanal take. A kwance take yanzu ta juyama ƙofa baya, hakan yasa Oum zama a bakin gadon kusa da ita. Shi kuma yay tsaya kawai daga gefen Oum yana kallon ƙofa dan yaƙi sake kallon Maanal. Kujera RK ya tura masa cike da kulawa ya ce, “Zauna anan bara na duba Doctor Rasheed ɗin muga. Ai da kun sanar min da gida yazo ya samesan”. “Yayi ƙoƙari ne ai Rafeeq, kwana biyun nan yanata zaryar zuwa gidan, kuma dama yace idan bai sauka ba yau asibiti ya kamata yazo ya duba shi da ƙyau shiyyasa”. Jajantawa RK ɗin ya sake yi kafin ya juya ya fita yana jaddadawa AA ya zauna. Sai dai ko kallonsa yaƙiyi balle ya zauna ɗin. Yana daga tsayensa duk da hajijiyar da yake ji na jujjuya masa kai. Oum kuwa data riƙo hannun Maanal a hankali ta shiga kiran sunanta. Hakan yasa cikin dauriya da jarumta Maanal da tuni ta goge hawayenta tas ta juyo ɗin. Suna haɗa ido da Oum ta sakar mata murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta shige jikinta cike da shagwaɓa ta ce, “Oum ni nayi fushi sai yanzu”. “Oh oh my baby kada kiyi fushi kinji, ayima Oum afuwa yaya jikin naki?”. “Naji sauƙi Oum. Yaya Rafeeq ma yace zasu sallameni yau”. “To Alhamdullah ALLAH ya ƙara afuwa. Tun jiya naso zuwa shima sai Auta ya kwanta shiyyasa” “Hy Aunty”. Naufal ya faɗa yana ɗagama Maanal hannu fuskarsa da murmushi. Murmushin itama Maanal ɗin tai masa. Sai kuma ta ɗaga masa hannun itama ta ce, “Hy Handsome”. Farin ciki ne ya kama Naufal jin an kirasa Handsome, dama Uncle AA ne kawai ke kiransa da sunan. Gaban gadon ya ƙaraso sosai. Ya ce, “Nagode Aunty da kika kirani Handsome. Kun zama biyu kenan ke da Uncle.” yay mata nuni da AA. Batare data kalli AA ɗin ba taima Naufal murmushi kawai. Gaisheta yaron yay da tambayarta yaya jiki, ta amsa masa da kulawa tana zaunar da shi kusa da ita. Sai kuma ta kalla Oum tana faɗin, “Yana kama da babban Yaya sosai”. Dariya Oum tayi a karo na farko, idonta akan Naufal ta ce, “Kodai Auta. Dan komai na Naufal Auta ne sak, duk da dai dama suna kama da Fadeel ne shima ɗin, amma Fadeel ai fari ne, shiko Naufal irin fatanku gareshi ke da Auta”. Maimakon Maanal ta amsa zancen sai ta basar ta hanyar shagwaɓe fuska ta ce, “Oum mi kika dafo min?”. Dai-dai Oum zata bata amsa RK ya shigo. Idonsa a kansu sai kuma ya kalla AA, da kulawa ya ƙarasa garesa yana faɗin, “Wai baka zauna ba. Ko duk ƙulafucin Oum ɗin kaka ne kazo ka tsaya mata a kai kamar zaka koma ciki kai da ɗayar Autar tata. Common malam zauna kada ka faɗi”. Yanda baiyi magana ba tunda ya shigo yanzun ma bai tanka ba, sai dai ya zauna ɗin dan shima yasan in ba hakan yay ba tabbas gab yaje da zubewa a ƙasa, sam kuma baya son cigaba da tada hankalin Oum, dan kwana biyun nan da baida lafiyar nan har rama tayi, ga shi itama tana fama da kanta.....

____________★

A Kaduna kam shirin kai lefe ake gidan su amarya. Shi ango ma baya nan yana Lagos kwana takwas kenan. Kaya ne na garari aka shirya na kuma fariyya. Jiya yini guda masu shiryasu na aikin nan. Akwatina set ashirin daa huɗu cif, kaloli daban-daban. Kuma kowane set zaka samu kusan akwati biyar ko uku harda masu goma sha biyu. Ga galleliyar mota new model a 2023 sabuwa dal a ledarta. Hajiya Basariyya dai tana nane dasu a gabanta ake komai duk da zuciyarta a ƙuntace take, amma yafi yarda data danne ayi komai akan idonta, Ammie ko yanda ba'a gayyaceta ba bata saka kanta a sabgar ba daga ita har Sakina da har yanzu take a gidan. A yau ɗin ma sai suka ƙirƙiri zuwa gyaran jiki abinsu. Duk bidirin shirin kayan da akai basa nan. Aiko Hajiya Yaya da ƴaƴanta suka samu na zaginsu wai Ammie tana hassada ne saboda ba ɗiyarta bace ba. Koda suka dawo gidan haka suka cigaba da habaice-habaicen su Ammie tayi kamar ma bata jisu ba... Washe gari tun sassafe gidan ya fara tara dangin Hajiya Yaya. Sai wasu a dangin Daddy dake ɗan ɗasawa da Hajiya Yayan. Yanda gidan ya cika saika ɗauka bikin ne ma ya fara. Har lokacin kuma babu wanda ya zo ya cema Ammie tazo ga lefe kota shirya zuwa kai lefe, ita kuma tayi biris da kowa bata saka kanta ba. Bayan sallar azhar suka cika motoci goma cif sai ta amarya dake tsakkiya da toyota hilux da aka zuba kayan lefen a ciki. Haka suka tafi a jere gwanin sha'awa, duk inda suka gitta sai an tanka kuwa. Dama haka suke so, gari ya ɗauka ko'ina ayi zancen wannan aure. To ALLAH ya cika burinsu dan kuwa an fara, sakamakon ƙannen Yazeed kaf da wasu a dangi tun jiya sun gama watsa wannan lefe a kafafen yanar gizo tako ina.. A can gidan Aunty Sabuwa ma gida cike yake tanƙam da ƙawayenta ƴan duniya da dangin mijinta. Anyi abinci kala-kala domin tarbar baƙi duk da kuwa aurene na dangin juna. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba anguwar ta gama rikicewa, dan kuwa kiɗa suka saki sosai da dj ɗinsu da suka tanada. Kafin a ɗan sarara a shiga buɗe kaya, masu video nayi, masu hotuna nayi, masu guɗa nayi harda ƙawayen amarya. Dan babu kunya hatta amaryar ma tana a gidan abinta sai washare baki take da jin kanta sama ƙololuwa, dan tasan ita kam ta wuce tsara sai dai ta taya ƴan baya da addu'a kuma, amma 2025 kam tata ce... Tukuyci na miliyan ashirin aka bama ƴan kawo lefe suma da tarin kayayyakin snacks da akai packaging, sai drinks da ruwa katon-katon, dambun kaji, danbun jan nama, soyayyu da gasassun raguna a ƙyafe guda biyar. Lallai wannan al'amari ya kai duniya tasan da shi. Dan kuwa ba garin Kaduna kawai ba duniya ce ta ɗauka sakamakon yanda komai ke yawo daki-daki a media tako ina. Dan hatta tarbar da suka samu da shagalin da akai a gidan Aunty Sabuwa shima anata ɗorawa. Hakama tukuyci da kayan alatun da aka maƙare musu motar da ta kawo kaya shima dai duk an ɗora. Hakan ya sakama jama'a kwaɗayi da shirin son ganin yanda wannan shagalin biki zai kasance na ƙwarya tabi ƙwarya. Wanda kuma suka san ainahin waye uban amaryar dan bai kai ko kwatar dukiyar uban ango Alhaji Usman Chalawa ba nata mamakin hidimar da su ma su Aunty sabuwar sukayi. To kowa dai na son yaga yanda za'a kwashe kam, dan in dai har kawo lefe kawai duk akama waɗan nan hidimomin ai taron biki kam dole ko mu ƴan kallo mu kasance a cikin shirin shan kallon (😂 lolz)....

______________★

Sosai kasancewar su Oum a asibitin ya ɗan ragema Maanal nauyin da zuciyarta tayi. Dan ma hankalin Oum ɗin ya rabu biyu saboda AA. Dan shi ma bayan Doctor ya dubashi sosai sun ɗan kwantar da shi amma yace na yini ɗayan ne kawai. A wannan yanayin Shahidah ta iso asibitin ta samesu. Tayi farin cikin ganin Oum sosai. Kasancewar an hana kowa zama a ɗakin da AA yake dan suna son ya samu barci sosai duk sai suka tare anan ɗakin Maanal ɗin. Sai bayan sallar azhar da AA ya farka Oum ta nufi can. A lokacin ita kuma Maanal ta samu sallama. Koda suka gama tattare kaya zuwa mota Shahidah tasa Maanal gaba tai domin duba AA. Bata so hakan ba, sai dai bazata iya musu da Didinta ɗin ba. Musamman daya kasance RK na tare da su ne. RK ne ya fara shiga bayan yayi knocking an bashi izinin shiga. Sai Maanal, Shahidah a ƙarshe. Oum na zaune a kujera, shi kuma AA na kan gadon ya jingina da filo Oum zata fara bashi abinci a baki, sai faman ɓata fuska yake alamar baya son cin abincin ko kuma duk ciwon ne oho masa. Plate ɗin abincin Oum ta ajiye tana kamo hannun Maanal da faɗin, “Masha ALLAHU ƴan matana anyi sallamar dai?”. Kai Maanal ɗin ta jinjina mata a ɗan shagwaɓe. Ita kuma tayi murmushi da faɗin, “To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne.” Amin RK da Shahidah suka amsa da shi, kafin Shahidah ta maida hankalinta ga AA daketa kallonta. Duk da yasan dama zai iya ganin nata, amma sosai mamakinsa ya bayyana amma ya gagara iya cewa komai. Wannan ba komai bane daga halayensa, dan haka Shahidah bata damu ba, sai dai zafinsa da suke ji tun na shekarun baya akan ƴar uwarsu taji yana taso mata. Komai dawo mata yake kamar yanzu ne yake faruwa. Da ƙyar ta iya dannewa ta tambayesa jikinsa. Karan farko yay ɗan murmusa, irin guntun murmushin nan mai tabbatar da ƙunar zuciya. Tabbas yaga tsanarsa a bayyane akan fuskar Shahidah, hakan na nufi har yanzu suma basu mance komai ba, basu mance abinda ya faru ba suna riƙe da shi a ransu fiye ma da Maanal. Baiga laifinsu ba, dan ko shine hakan zai yi, amma inama zasu fahimcesa kamar yanda Oum ta fahimcesa bayan ya zauna da it..... Maganar RK ce ta katse masa tunaninsa, ya ɗan kallesa sai kuma ya janye idanunsa yana jinjina masa kai. Baya son sakama ransa tsanar ɗan uwansa kodan daraja da kimar Oum, amma tabbas zafinsa yake ji, kishinsa yake ji mai tsanani akan Maanal. Ta yanda ya gwammaci ya dinga masa shiru akan abubuwa da dama fiye da yin magana. Sai yanzu Maanal da tunda tai masa kallo ɗaya bata ƙara ba ta furta, “Ya jiki?”. Daga haka tai shiru. Shima sai bai amsa ba, ya dai ɗago idanunsa ya kalleta kawai. Yana ƙoƙarin janyewa akai knocking ƙofar. Shahidah ce ta amsa sannan ta bada izinin shigowa. A hankali aka turo ƙofar, yana sanye cikin lallausan farin yadi da yay masa matuƙar ƙyawu, sosai kamanninsa da AA ke a bayyane, ta fuska da ɗabi'u. Sai a shekaru ne kawai suka banbanta da hasken fata. Ɗan ja yay ya tsaya turus yana kallon Shahidah da itama take kallonsa, sai kuma tai saurin kauda idonta. Shima janyewa yay ya maida ga Oum, sai kuma ya sake waresu akan Maanal da itama take kallonsa. Cikin kasa daurewa ya ce, “Oum kinga mi nake gani?”. Murmushi sosai Oum ta saki mai ciwo, sai kuma ta jinjina kanta da faɗin, “Na sani Fadeel. Shahidah ce da Lillyn ka”. “Wai da gaske ne kenan?”. Yanzu kam har sai da hakwaran Oum suka bayyana a waje, sai kuma hawaye suka ciko mata idanunta. Da ƙyar dai ta iya dannewa ta sake bashi amsa........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣1️⃣

______________

Readers Also Read