Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 38
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 38: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 38. Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan…
2,634 words
Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan kawoma Mamy saƙo data manto a wajen mamansa shi kuma yaje gidan ta bashi ya biyo Mamyn dashi ya samu batun ciwon AA ɗin bai sauka ba da har yau ya kaisa ga zuwa asibiti. Shine ya kira matarsa Yaseerah yace tazo itama ta duba shi sai su koma gidan tare. Ita kuma ta kira Huznah ta kuma biya ta ɗakkota a gidan Shahidah kamar yanda mijin nata ya bata umarni. Koda suka shigo kai tsaye sashen Oum suka nufa dan har lokacin itama Mamy na acan dama duka ƴan gidan har su Saheeba da Nibras da Nuratu. Mai aikin Oum Mamy ta saka shigowa da su Abdul ɗin har falon sama na Oum. Duk suna a falo, idan ka cire AA dake can bedroom ɗin Oum da yay barci. Sai Babban Yaya da bai dawo gidan ba tun baro asibiti da yay ɗazun. Nibras da Nuratu na'a falon ƙasa suna girki. Nuratu ce ta fara cewa zata girka ma AA abinci kamar yanda uwarsu da suka kira suna gaya mata abinda ya faru a asibiti ta basu shawarar yi. Sai ita kuma Nibras ta ce itama zatayi dan wani irin tsanar Nuratu take ji tuni batun yanzu ba. Abinda ma ke ɗan sassauta mata ƙinta ganin yanda shi AA ɗin baya wani shiga sabgarta. Itama dai taci kuka bayan dawowar tasu daga koro sun da akayi daga asibiti. A hakan ma ba wani tarihin Maanal ta sani cikakke ba game da alaƙarta da AA, amma ta ɗauki aniyar bugar cikin Fawzan ta sani yau dan tasan irin matakin da zata ɗauka akan Maanal ɗin da dukan ahalinta ma. Dan itafa a yanda take jin AA a ranta ALLAH ko mahaifansa da su Fawzan zata iya kawarwa ta mallakesa ita kaɗai. Su Huznah sun hawo Nibras da Nuratu dake a kitchen basu sani ba. Sai da har su Abdull sun gama gaishe da Abah da Mamy da Oum Abah na tsokanar Abdull sannan suke haurowa da kayan abincin da suka shirya harda mai aikin Oum. Sannu Oum da Mamy ke musu, duk suka amsa tare da tambayar Mamy ina za'a kai masa abincin. D/table Mamy tace su ajiye. Dan haka duk suka ajiye a can ɗin. Juyowar nan da Nuratu zatai tana magana da Abdull sai idanunta ƙuru-ƙuru a cikin na Huznah da tun shigowar Nuratu falon mamaki da ruɗani suka baibayeta. Cikin kuwa ɗan waro ido na nuna mamaki Nuratu ta ce, “Kai wai wa nake gani kamar Huznah?”. Murmushin ƙarfin hali Huznah ɗin tayi, sai kuma ta sinne kai ƙasa wai ita kunyar surukai na wajen ta ce, “Nice Nurry”. Idanu Yaseerah da Abdul-hakeem suka haɗa. Yayinda Mamy ta saki wani murmushin jin daɗin ganin Nuratu da Huznah ma kenan sun san juna. Dan haka sai kawai ta miƙe tana faɗin, “Kunga muje can kafin Maman ɗan nan tace zamu hana mata shi barci”. Dariya Oum tayi dan sanin da ita Mamy take. “Oh abun ma harda ƴar sharri. To shike nan kuje ɗin dai dan kuwa ban san a tada shin”. Mamy ma dariyar ta sake yi. “Ai nasan gaskiya na faɗa”. Shima Abah dariya yaketa musu. Haka Mamy ta fice tare da su Huznah. Nuratu ma tai wuff ta bi bayansu. Suna gama fitowa daga apartment ɗin Oum ɗin caraf Nuratu ta riƙo hannun Huznah dake kusan ƙarshe. Cak Huznah ta tsaya, sai kuma ta juyo tana kallon Nuratu. Murmushi ta sakar mata da faɗin, “Oh oh friend ashe kece? ALLAH duk kin saka mamaki yama rufe ni da ganinki gidan nan kodai gidanku ne?”. Nuratu da zuciyarta keta watsal-watsal a ƙirji ta ce, “Eh gidanmu ne. Amma ba inda aka haifan ba. Gidan da zanyi aure kenan, kuma wanda zan aura ɗin ma kuka zo dubawa. A ina kika san Abdul-hakeem?”. Tsabar yanda zuciyar Huznah tai wata girgiza har taurari ta dinga gani na mata yawo a cikin ido. Cikin rawar baki ta ce, “Waye zaki aura ɗin?”. Cike da gadara da alfahari Nuratu ta bata amsa da, “Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, wato AA Darma”. Ai zabura gefe Huznah tayi tana mai fisge hannunta daga cikin na Nuratu, sai ko gata jikin bango kamar mage ta gamu da kare a kwanar da babu hanyar ɓillewa. Yanda tai ɗin ya saka Nuratu kafeta da ido itama zuciyarta na wantsalawa a karo na biyu. Sai kuma ta matsa gaban Huznah tana faɗin, “K jira-jira wai badai dama Yaya AA kike bibiya ba?. Babbar bala'i wai dama shine kika bamu labari?”. Bata jira amsar Huznah ba tai saurin fara danna wayarta ta latso hoton AA dake cikin wani lallausan farin yadi da yay masa shegen ƙyau ta nuna mata. “Shine wannan?”. Jinjina mata kai Huznah tayi a mutuƙar harmutse. “Kambu are you mad? Wai dama mijin aurena kike bibiya. Ehhhh ahhh lallai kin taro match yarinyar nan. Yau naga baƙar shegiya ubanwa ya aiko ki?”. Tai maganar da nufar Huznah gadan-gadan tana neman kai mata hannu ta shaƙota. Hannun nata Huznahr ta riƙe caraf, a dai-dai nan Fawzan ya iso wajen. “Kai kai kai lafiya?!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba. Dakatawa Nuratu tai daga shirin shaƙe Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce, “Yaya Fawzan wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta raɓu da jikina inata bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ƴar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina haɗa miki jini da majina ta yanda bazaki taɓa sake sha'awar yima kowa ƙwacen saurayi ba dan ........” ta ƙarasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah. Cikin ƙanƙanin lokaci rikici ya harƙume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan faratunnan ƙarin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa bakinta. Ƙara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah ɗin, ita kuma Saheeba ta riƙe Nuratu. Mugun ciwo Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon ƙarnin nan haka suka kasance har sanda huɗu na yatsunta. Jini tuni ya jiƙe wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala. Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana ƙoƙarin sake kai mata wani Abah ya riƙe hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da Fawzan ya mata take yi. Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita kaɗai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci akan AA suke faɗan, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan alaƙar Huznah da zuwa gidan ma. Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ƙaiƙayin baƙin ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari. Cikin ɓacin rai Fawzan ya ce, “Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son aura masa ita tana abu kamar ƴar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka dama ɗazun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to? Mi aka gaya matan akan su Shahidahn”. Cike da mamaki Abah ya ce, “Wace Lilly da Shahidah?”. “Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano”. Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta ɗan rumtse ido. Yayinda Abah ya furta, “Fawzan kasan mi kake faɗa kuwa? Da gaske kake yi?”. “Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta”. Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin ƙirji........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣3️⃣
______________
........A ɓangaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su ƙarasa maganar da suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura saƙon sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata ɗauka ba ta dai daure ta ɗaga ɗin tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da faɗin, “Gani a compound ɗin ku”. Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa ɓoyewa sai da ta furta, “Wasa kake amma?”. Murmushi yayi mai sautin da har taji, “Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga saƙonki”. Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake ƙarfafata akan RK ɗin. Tabbas bata buƙatar yin rayuwar aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da ƴan uwanta bazasu bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal ɗin ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya. Miƙewa kawai tayi ta ɗan gyara hijjab ɗinta na salla da har yanzu bata cire ba, sai ɗan turare data ƙarama jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta ɗauka ruwa a tray da glass cup. A karo na farko ta nufi falon baƙi sannan ta fita compound inda RK yake. Iso tai masa zuwa falon baƙin, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita. Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa daurewa ya furta, “Gaba ɗaya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba”. Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa. “Idan kiɗa ya canja itama rawar canjawa take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan gaɓar serious ne”. “Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance ɗin Maanal. Na kuma ji daɗi da godema ALLAH daya kawo mu wannan gaɓar ɗin.” A hankali ta haɗiye ƴan kwallar data ciko idanunta. “Ɗazun mun fara magana sai dai bamu ƙarasa ba, shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna.” batare da jiran amsarsa ba ta miƙa masa diary ɗin data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro sa daga jakan, sai kuma ya ɗan jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya ɗago ya kalleta. Itama shi take kallo, dan haka ta janye nata idanun. “Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai ɗin koba komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu dukkan tarihin rayuwata data shuɗe a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance ƙalilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tuɓar Oum dan sake samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH in har baka gama karanta shi har ƙarshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna.” daga haka ta miƙe tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa. “Dare ya farayi sai da safe” A karo na farko ya ɗan ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana miƙewar shima. Haka suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta, “Abdul-hakeem”. Sai kuma ya juya yana kallon Maanal. Itama shi ɗin ta kalla, tare da faɗin, “Ka sanshi ne?”. Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman ɓarinta na dama. Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay masa a taƙaice. Kamar RK ɗin zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal. “Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko?”. Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce ɗin ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon Maanal ɗin. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata ƙyaƙyƙyawa da wani skin nata mai ɗaukar hankali da yay ƙaranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching.....
Gaba ɗaya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull ɗin. Dan Yaseerah taso su ɓoye amma Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu, suma suka miƙe suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin kallon ƙurullar da Abdull ɗin ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har ƙasa. Ko bayan wucewarsu da Huznah ta shigo ɗakin Maanal bata kulata ba, tanata ma haɗa ƴan abubuwan da zata wuce da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah ɗin bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe....
_______________★
A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya faɗa sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an samu saɓani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka ɗaukesu a mota wai zasuje wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take. Rasama abin faɗa Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo ɗaya da yay mata ya fahimci hankalinta a matuƙar tashe yake kuma.......
___________★
Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma babansu yaje school ɗinsu ya daidaita komai. Jirgin ƙasa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq ɗin da kansa ya kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal ce tazo ɗaukarsu. Dan ita kaɗai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani ɗin.