Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 56
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 56: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 56. A makare yanzu kam ta fito sallar…
3,157 words
A makare yanzu kam ta fito sallar la'asar saboda meeting da sukayi da Director Mustapha gaba ɗayansu Junior Watch Designers na department ɗinsu akan wani ƙaramin project. Kasancewarta ita kaɗai mace sai da ta bari duk suka gama fitowa sannan ta fito daga conference room ɗin. Gudu-gudu sauri-sauri ta isa massallacin, da sauri ta nufi wajen alwala. Kafin ta kammala har an kai raka'a ta farko. Cikin hanzari ta shiga naɗa veil ɗin abayarta da iska ke neman kwashewa. Kamar zatai kuka ta samu da ƙyar dai ya zauna. Juyowar da zatai dan barin wajen ta hango AA dake ƙoƙarin fitowa a mota alamar daga wani waje yake. Yanda ya zuboma wajen ido ya bata tabbacin ya jima yana kallonta. Ɗauke idanunta tai kamar bata ganshi ba tai saurin faɗawa cikin massallacin. Koda aka idar kasancewar bata samu sallar duka ba tana a cikin ƴan karshen fitowa. Kusan duk an wuce kitchen, dan haka ta nufi komawa ciki ita dai kam. Dan har yanzu zuciyarta bata ji zata taɓa cin abincin Companyn ba da ake dafawa. “Sister Maanal”. Muryar AS ta ratsa kunnenta daga bayanta kaɗan. Juyowa tayi, sai dai bata amsa masa ba har ya ƙaraso. Fuskarsa da murmushi ya furta, “Barka da rana, dama boss ne yace a kiraki”. Idanu ta zuba masa sosai. Sai dai fuskarta harta canja. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ganin mutane a wajen, ta jinjina masa kai kawai. Shima bai sake cewa komai ba yay gaba a ransa yana sake jinjina miskilancin ta. Ganin sun nufi hanyar gate kamar zata tsaya sai kuma ta hango motar AA ɗin a can waje gefen titi. Mita take a zuciyarta kiran mi yake mata kuma a waje, itafa idan yace zai cigaba da takurama rayuwarta ALLAH zata fiddo masa kalarta, ya bar ganin tana wannan sauke kan bata son kowa a ma'aikatansa ya fahimci tana da wata alaƙa ta ɓoye ko zahiri ne da shi shiyyasa. Da wannan ƙunƙunin ta ƙaraso. Sai dai ta dogare a waje, yayinda shi kuma yaƙi sauke gilashin motar. Sai da AS ya ɗan masa knocking sannan, a hakan ma bai buɗe kai tsaye ba sai da yaja wasu sakanni. Saukar gilashin ya bata damar ganinsa zaune a mazaunin driver dan gilashin tinted ne. Hannu kawai ya ɗagama AS alamar yaje. Cike da girmamawa ya ce, “Okay sir a dawo lafiya.” daga haka yabar wajen ya koma cikin Company. Shiru ita da shi babu wanda ya tanka, amma shi kallonta yake ta cikin mirror ɗin gefensa. Yanda take ta faman ɓata fuska da motsa lips alamar ƙunƙuni take masa ya sashi lumshe oily ayes ɗinsa yana ɗan sakin miskilin murmushin da iya lips ɗin kawai ya motsa. Karaf kuwa sai a idon Maanal data matso inda yake a kufule. Gimtse fuskar yayi, itama ta sake gimtse tatan tana harararsa. Cike da takaicin murmushi data gani yanayi tabbacin da ita yake tunda kallonta ta kamashi yana yi, “Gani”. “Na ganki ai”. Ya faɗa cikin halin ko'in kula idonsa a kanta. Janye nata idanun tai daga kansa tana jin kamar ta balbalesa da masifa. Amma dai ta daure kodan securitys da zasu iya hangosu. Ita kuma bata buƙatar hakan. Kamar ya karanci abinda take tattaunawa da zuciyar tata ya miƙa hannu ya buɗe murfin side ɗin mai zaman banza tare da faɗin, “Get in”. Sosai yanzu kam ta zuba masa idanu babu ko ɗar, shima ya ko zuba mata nasa cikin tsakkiyar natan. Jitai tsigar jikinta na tashi amma tai jarumtar riƙe kanta da ƙyar. A dake ta ce, “Ni aiki nazo ba yawon banza ba”. “Niko kinga yawon banzan na fito”. Ya bata amsa a daƙile. Kafin ta samu damar bashi amsa ya cigaba da faɗin, “Kina ɓatan lokaci, idan kuma kika bari na fito ALLAH da kaina zan ɗaukeki na sakaki”. Tasan zai iya fiye ma da abinda ya faɗa. Wanda ya iya keta mata haddi a cikin gidansu me kuma ya rage. Garama ta shiga tunkan ya kunyata ta a bainar nasi. Sai dai bata shiga kai tsayen ba, sai da ta gama masa ƙunƙuni da hararar motar sannan ta zagaya ta shiga. Ƙin rufe murfin tayi, dan haka ya ranƙwafo tare da kai hannu zai rufo. Hakan ya basu matsanancin kusancin da har take jin kamar zai rungumota ne. Ga ƙamshin turarensa ya wani buɗeta tamkar yanzunne yake fesawa. Samun kanta tai da rawar jiki, sai kuma a zabure takai hannu ta jawo ƙofar ta rufe bam kafin shi yayi. Shiru yay yana kallon ƙofar batare daya janye jikinsa ba. Jin numfashinta kamar yana fisga da ƙarfi, ga sassanyan ƙamshin khumran data saka da wanda tai turaren kayanta na wani saukar masa da kasala. A hankali ya maida idanunsa kanta, ya zubama ƙyaƙyƙyawar cute fuskarta manyan idanunsa. Idanunta a rumtse suke, hakama lips ɗinta sai ɗan motsi yake, ga fuska ta takure kamar zata saki kuka. Idanunsa dake kallon lips ɗin ya janye cikin slow motion yana mai haɗiyar wani busashen yawu daya tokare masa maƙoshi. Kamar wanda aka kwaɗama guduma a ka ya janyo belt ɗin gefenta kawai yaja jikinsa baya ya maƙala ta gefen tsakkiyarsu. Da mugun ƙarfi tako saki numfashinta har sai da ya sake kallonta, sai kuma ya girgiza kansa a hankali yana mai janye idanun tare da lumshesu, sake buɗesu yay a saman titi yana kunna motar. A hankali taji sun fara tafiya, dan haka ta sake sakin sauran numfashin data riƙe tare da buɗe idanunta. Ƙin kallon sashen da yake tai, sai ma ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata idanu take yi. Dan haka kawai yanayin nasu ya tuna mata wani abu. Shiru motar ta ɗauka sai sanyin ac dake ratsasu, dan ko rediyo bai kunna ba. Sai wayarsa da aketa faman kira tana haske da ɗan motsi kawai, bai kuma kula ba kamar ma bai ji ana jera masa kiraye-kirayen ba. Tafiya ba wata mai nisa ba duk da a hankali yake tafiyar suka iso wani katafaren wajen Saloon mai shegen ƙyau. Kallon wajen kawai Maanal take yi, yayinda shi kuma ya samu waje yay parking. Sai da ya kashe motar gaba ɗaya sannan ya juyo yana kallonta. Muryar san nan ƙasa-ƙasa kamar abin dole ya furta, “Muje”. Itama kallonsa tai a karo na farko ta ce, “Ina ɗin?”. “Ina kikaga mun zo?”. Ya faɗa cikin tsatstsareta da kaifafan idanunsa. Fuska ta ɓata sosai, bakinta a sama ta ce, “Ni mizanyi anan wajen? Haka kawai ka ɗakkoni daga wajen aiki ka kawoni nan......” sai kuma ta cigaba da magana cikin ƙunƙunin da baya ji. “Kar dai ki zagen mara kunya kawai”. “Toni ka maida ni inda ka ɗakkoni mana. Na gaya maka ina buƙatar zuwa nan wajen ne. Haka kawai dan neman mutum dai da faɗa.....” “Ai ba sai kina buƙata ba, tunda ni ina buƙata ya wadatar. Ragguwan banza kita yawo da gashi a tsefe kina buɗema mutane suna gani. Oya fita kona ɗaukeki da kaina har ciki wlhy”. Sosai idanunta suka kawo hawaye, dan har yanzu Maanal ba ƙaunar kitso take ba, ta gwammace a wanke a gyara mata kawai. Sai gashi ta marairaice fuska kamar ba ita ke shirin masa tsiwa ba. Idanunsa ya kauda daga kallonta yama buɗe motar ya fita alamar bazai ma saurareta ba. Sake tashi hankalinta yay, tana tunanin fita ta gudu taji an buɗe side ɗin da take. Da sauri ta dubesa, sai ga hawayen da take riƙewar na silmiyowa da gudu. Baki ya taɓe, tare da fara jan hannun jacket suit ɗinsa sama. Hakan na nufin shirin ɗaukar tata yake kenan da gaske. Ai da sauri ta fito tana harararsa da share hawayen dake cigaba da sakko mata. Murmushi yay abinsa cike da mugunta yay ma bayanta ƙaramin gwalo, sai kuma ya maida fuskarsa ya gimtse ya rufe murfin data bar masa a buɗe kamar baiyi komai ba. Haka ya tasata gaba cikin wajen tana shartar hawaye. Dai-dai nan Nurry da ƙawarta ke fitowa a kusa da wajen saloon ɗin daya kasance bakery. Cak tai wani irin tsayawa zuciyarta na bugawa da sauri, tuni ta saki ledojin hannunta tana mai bin AA da Maanal dake shigewa cikin saloon ɗin da kallo. Itama dai ƙawar tata AA Darma ɗin take bi da kallo tana haɗiyar yawu, sai da suka gama shigewa ta maido dubanta kan Nurry ɗin da faɗin, “Kanbu Nurry AA ɗinki ne fa da mace? Miya kawosa nan wajen saloon ɗin mata to ma?”. Nurry bata tanka mata ba, sai nufar wajen saloon ɗin da tai a sukwane jikinta har rawa yake tana neman faɗuwa. Ai babu shiri itama ƙawarta ta kwashi ledojin data zubar ɗin tabi bayanta da sassarfa dan gara dai ayi komai akan idonta........✍️
_😂Tofa AA Darma kana cikin alheri yau da alama gaskiya 🥱😆🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣8️⃣
______________
.......Shigowar Nurry dai-dai AA na jama Maanal kujerar zama ita kuma fuskarta rufe da veil ɗinta tana share hawaye. Yayinda matan dake a wajen sun zo ai musu gyara suka musu caaa da idanu. Ma'aikatan kuwa har rige-rigen tambayarsa suke yi abinda za'ayi mata. Fuskarsa babu ɗigon fara'a, bai kuma kalla kowa ba tunda ya shigo ya buɗe baki da ƙyar ya ce, “A duba mata kan idan yayi datti a wanke, sai ai kitso”. Da sauri Maanal ta janye veil ɗin daga fuskarta tana sake ɓarke masa da kukan da kowa kema kallon na shagwaɓa da taɓara. “Ni wlhy bana son kitso, kuma kaina babu wani datti da yayi, koba ranar na wanke ba”. Maganar take da iya gaskiyarta tana kuka tana kallonsa. Dan haka ya wani kalar ɗage mata gira da wara mata shanyayyun idanunsa irin na ki kiyaye ni. Ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji kuma ya furta, “ALLAH idan baki daina min wannan rigimar ba tsaf zan riƙeki na matseki a wanke kan a kumayi kitson ƴan ƙanana ko zamu kwana anan. Dube ki abin kunya kina kukan kitso kamar ba ƴammata ba”. Ai kamar ya tunzurata sai ta sake ɓarke masa da kukan da yafi na farko. Hakan ya saka wasu dariya, wasu ko na mamaki da tunanin ƙaramar ƙanwarsa ce dai halan. Yo irin wannan taɓara haka. Ya shigo yana faman shan ƙamshi da ɗaɗɗaure fuska, amma kalla yanda yake wani kashe murya ƙasa-ƙasa da ko jin abinda yake faɗa ma babu mai yi. Wanda kuwa suka sanshi mamaki suke yi, AA Darma dai shugaban matasa mai Mawaad Company ne haka available. Tab ɗin, ita kuma wacece wannan? Su dai a sannin da sukai masa baida wata ƙanwa mace da suke jini ɗaya wato iyaye ɗaya ai, hasali ma shine Auta a gidansu kamar yanda duniya ta sani. Oho basu dai da mai amsa musu duk wannan. Cike da kwarkwasa wadda zataima Maanal gyaran ta ce, “Ranka ya daɗe za'a ɗan wanke yayi datti”. Mugun harara Maanal ta zuba mata, zatai magana yaja kujerar da aka kawo masa shima ya zauna kusa da ita sosai. Kasa cewa komai tayi sai kallonsa take tana hawayenta. Shima dai kallon nata yake cikin ido sosai yana danne dariya da ƙyar. Kafin ya janye a kasalance yana wani ɗan gyaran murya kamar wanda ke neman rasa kansa. Handku ɗinsa ya ciro fari tas yana tashin ƙamshi ya miƙa mata, cike da kwantar da murya kamar ba shine ke mazurai ba ya ce, “Yi haƙuri to daina kukan, badai nine ba zan rama miki da kaina. Ai ina nan bazan bari su miki da zafi ba, idan ma kina so zan goya ki a bayana mu tafi gida a ƙafa har gida”. “Ni bana so duka, kaina ciwo yake min”. Ta faɗa idonta dake cika da hawaye a cikin nasa. Dole sai shine ya sake janye nasa yanzu ma. Dan data san tasirin da yanayin nata yake masa a cikin jiki data tausaya masa. Cikin ɗan ƙara samun kansa da shaƙewar murya ya saka mata handky ɗin cikin hannunta yana faɗin, “Ciwon kai ba, zan saya miki magani. Faɗa min mi kike son kici naje na sayo miki yanzu”. Kafaɗa ta maƙe alamar bata son komai. Amma sai ya shiga lallashinta kamar ba AA Darma ba. Gaba ɗaya sun manta kansu a yanzu da matsayinsu komai ya rikiɗe musu zuwa baya, bayan data shuɗe musu da ɗunbin tarihin tunawa suyi kuka da dariya idan ya kama duk a lokaci ɗaya. Ƙoƙarin miƙewa yay siyo mata cake da tace tana so. Caraf cikin ma'aitan wata tace, “Sir basai kaje da kanka ba bara a amso mata nan kusa da mu”. Tsabar neman ɗuwawun zama ko kuɗin bata amsa ba balle jiran amsarsa tai ƙoƙarin ficewa. Amma sai Maanal da takaici ya cika ta dakatar da ita da faɗin, “Ni naka nake so”. Dariya taso bashi amma ya danne da ƙyar baiyi ba. Batare da yace komai ba ya miƙe ya fita. Ita kuma ta harari ma'aikaciyar. A yayin fitar tasa ne ya ɗan kusa buge Nurry da tun ɗazun tai sumar tsaye saboda mamakisa daya gama cika mata zuciya da ruhi ganin yanda yake abu kamar bashi ba. Kai itafa sai taga ma kamar a mafarki take. Kai in ko mafarki ne wannan mafarki ya mata muni da yawa, ALLAH dai ya farkar da ita ta daina gannin wannan tashin hankali. Gulmar AA ɗin da wasu mata keyi a kusa da inda take tsaye dan har ya fice shi batare daya ma lura da ita ba ya sata fahimtar fa ba mafarkin bane gaske ne. Sai taji zuciyarta na neman tarwatsewa. Karan farko ta motsa jikinta kamar mara laka ta fice itama tabi bayansa. Tasan halinsa sarai baya ɗaukar raini ko rawar kai, dan haka ta tsaya har ya fito daga cikin bakery ɗin hannunsa ɗauke da ledoji guda biyu. Yanzun ma sam hankalinsa bai kai gare ta ba, dan haka cikin kwantar da murya ta ce, “Assalamu alaikum Yaya AA”. Cak ya tsaya daga tafiyar da yake yi, sai kuma kamar mai ciwon wuya gently ya dubeta, irin duban nan na sau ɗaya ya ɗauke kansa yana shanye dukkan sassaucin fuskarsa. Da sauri ta matso inda yake sosai. Muryarta har rawa take wajen gaisheshi. Sau ɗaya ya amsa mata, har yayi kamar zai wuce sai kuma a daƙile yaɗan sake dubanta. “Mikike yi anan?”. Wani irin sanyi taji a ranta da ƴar kulawar tasa. Saita samu kanta da sake kwantar da murya cike da yanga ta ce, “Munzo sayen snacks ne a bakery ɗin nan”. “Okay”. Ya faɗa yana wucewarsa. Binsa tai da kallo kamar mayya, hawaye na ciko mata idanu. Ƙawarta da itama jikin nata ke a sanyaye ta ƙaraso gareta. Batace mata komai ba ta share hawayenta sai kuma ta miƙa mata hannu ta amshi bag ɗinta. Wayarta ta ciro ta shiga laluben number yayarta. Bugu ɗaya kuwa Saheeba ta ɗauka. Sai kawai ta sakar mata kuka. A ruɗe Saheeba ta shiga jera mata tambayoyi. Da ƙyar cikin garsheƙar kuka Nuratu ta sanar mata komai. Sai dai maimakon taji Saheeba ta amsa mata sai taji muryar Mamy, ashe lokacin suna tare ne Saheeban na'a sashenta. Cikin ɓacin rai Mamy ta ce, “Ki bisa wajen Saloon ɗin ki ɗauka min hotonsa shi da yarinyar”. “Amma Mamy zai gane nice na ɗauka na tura muku, kuma ALLAH sai ya hukuntani”. “Okay kinfi tsoronsa kenan akan umarni na ko Nuratu?”. “Ba haka bane Mamy. Dan ALLAH kiyi haƙuri”. Ƙwafa Mamyn tayi, tare da yanke kiran kawai. Hakan yasa Nurry sauke ajiyar zuciya. Ko giya tasha ai bazatayi gangancin aikata abinda Mamyn tace tayi ba. Yaya AA fa, tab ɗin wlhy dandaƙar ɗan akuya zai mata har gaban uwarta ba damuwarsa bace. Dama dai ace bai ganta bane da zata iya ta ɗauka ɗin. Amma ya ganta ta gansa har sunyi magana ai ko zata cika duniya da rantsuwa yasan itace ta aikata. Haka ta samu kanta da zama a cikin mota ita da ƙawar tata suna dakon jiran fitowarsu.....
____________★
“Daddy wannan shine bayanin dana samu a kansa. Sunansa Bukar Bala Ɓatagarawa. Senator ne kuma.” Murmushi mai faɗi Daddy yayi tare da gyara zaman wayar tasa yana kallon Yazeed dake masa bayanin dan video call suke yi. Kafin ya iya cewa komai Yazeed ya ce, “Daddy wai miya haɗaka da shi ne kake masa irin wannan binciken?”. Kai tsaye Daddy ya ce, “Maanal yake so”. Cikin matuƙar mamaki da razani Yazeed ya ce, “Maanal kuma Daddy”. “Ƙwarai da gaske, dan har yaje ya samu iyayenta acan Giro sun gama magana......” Tsaf Daddy ya zayyane masa komai. A take yanayin Yazeed ɗin ta canja, idanunsa suka kaɗa jazur. Cikin tsananin damuwa ya ce, “Daddy wannan nake gudu dama tun farko. Yanzu shike nan na rasata? Wannan fasiƙin mutumin zasu bata saboda zalunci?”. “Baka rasata ba Yazeed, sam baka rasata ba. In har ina raye in sha ALLAHU bazaka rasa Maanal ba. Ka kwantar da hankalinka kai dai kabar komai a hannuna. Yanzu yaushe zaka dawo? Kwana biyar fa ya rage ɗaurin auren nan amma babu ango babu alamarsa”. Sai da Yazeed ya haɗiye yawu mai ɗaci sannan a sanyaye ya ce, “Daddy zan taho zuwa alhamis insha ALLAHU. Kayan dana maka bayani nake son naga saukarsu akan idona. Kuma sunce sai Wednesday zasu iso. Shiyyasa na bari alhamis sai na dawo”. “Bazai yiwu ba Yazeed. Ka taho Wednesday ɗin kawai. Kada mutanen nan suga rashin damuwarka akan ƴarsu tayi yawa. Ita ɗin ƴar uwarka ce kada ka wulaƙantata kodan Baba da Inna dan ALLAH. Ka kwantar da hankalinka ka ƙyautata mata sai ALLAH ya mallaka maka abinda kake so cikin sauƙi. Maganar Alhaji Bukar kuwa kada ma ta dameka, dan bazatai wani tasiri ba da izinin UBANGIJI.” “In sha ALLAH zanyi duk yanda kace Daddy. Bara naje akwai meeting da zamu shiga dama”. “Okay babu damuwa sai na jika, ALLAH yay maka albarka. Ya azurtaka da zuri'a masu albarka da zasu maka biyayya kamar yanda kake mana”. “Amin Daddy na gode”. Kai kawai Daddy ya jinjina tare da yanke wayar. Sai kuma ya maida dubansa ga Ammie da tun fara wayar tasa ta shigo, har zata juya ta koma ya hanata ta hanyar dakatar da ita da hannu. Dole ta dawo ta zauna. Akan kunnenta sukai duk zantukansu, sai taji zuciyarta ta raunana da tausayin Yazeed ɗin. Yaron kirki mai natsuwa da sanin mutuncin iyayensa.. har ga ALLAH tana son Maanal ta auresa, sai dai tana tsoratar mata wahala da ƙiyayyar uwar miji dan itama ta ɗanɗana a baya tasan ciwon da hakan ke da shi......
____________★