Kenza eBookz

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy - Chapter 14

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy - Chapter 14

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 14: Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 14. _*Kyakyawan Shafi lokaci Daya da kyakyawan…

3,303 words

_*Kyakyawan Shafi lokaci Daya da kyakyawan sadaukarwa,eh mana domin Duka Shafin yau na ALIYU GADANGA.,Kacokan Dinsa sadaukarwane ga Daukacin malamai da Shugabannin dake mkrantar primary U.B.E. KOFAR KIBO ZARIA..,Gaisuwan Fatan alherin zuwa gareki ne mai gayyah mai aiki,headmistrees HAJIYA BINTA UMAR ABUBAKAR(Momy)Allah yaja kwana👍😂,Tare da uwar gayyah Assitances,HALIMA IDRIS(Goggo balaraba)😹 Allah dai ya biya,bazan yi toya na manta da albasa ba,jinjinar ban girma zuwa gareka lantarkin zuciyata,kuma malami na,kuma uba yake awajena,lalle na kasance mai sa"a Tunda Allah yahadani da gwarzo kamar ka,UMAR BELLO SADIQ(Uncle me)😘,Soyayyarka gareni sai dai nace A kinda masha Allah,Kulawarka akaina sai da na kirashi da Alhamdulillah Allah nake roko daya iya maka Abunda kagaza,Kafin na wuce zuwa wani ajin yakamata nafara Farawa da gida ne,gaisuwa tare da Fatan alheri gareku MALAMA RUKAYYAH(Maman Suhailat)sai MALAMA AISHA(mmn Fuad)sai MALLAM ABUBAKAR(mallam Ammar),Bazan manta daku ba dole ne nayi jinjinar ban girma gareku iyayan dakina,ANTY HADIZA,tare dake MALAMA AISHA,Bazan manta dake ba kawata abokiyar Cin mushe,😂😛,kuma malamata ba wato ANTY JUWAIRRIYAH,Son so Fisabillillah,kai zan yi Abun kunya ban ambaci uwata ba takaina ba MALAMA ZAINAB(Anty Ummi)tare dake Malama Hafsart,malama jamila,(Namecy),sai malama Harira,Anty hauwa,Malama Asiya dake da malama Hafsart,ban manta dakai ba Mallam Aminu tare da wadanda ban ambataba,gaisuwan Ban girma gareku Allah yabar zaman Tare Ameen..Ku sani ku kara sani JANAFTY AKA SHAKIRA,na Sonku Fisabilillah*_😘😍❤💕💖💞💘🔐

*Chapter 18*

"""Koda garin Allah ya waye,Kafin Anty madina tagama Shirya yara zuwa mkranta Tuni Azeema hartayi wanka,takumayi Turaren Tsugunnonta,takuma sha mganungunanta wanda Anty madina ta nunnuna mata,koda Anty madina ta Shigo Azeema ta cakare,cikin Wata Atamfa mai blue da ja,cikin wanda goggo ta dinkamatane,simple make up ne Afuskarta,ta taje gashinta tayi baya dashi ta saka band ta daure,tsaye take gaban madubi tana cikiniyar Daura dan kwallin Anty madina ta Shigo kallonta tayi tana rike baki kafin tace

"Matar yaya,Allah kinyi kyau kinganki kuwa chanchadi.."Tafada tana dariya Rufe Fuska Azeema tayi kafin tace"Ina kwana Anty madina.."Ta amsa da lafiya kalau matar yaya,yakika tashi..? tafada tana karisawa kusa da ita ta karbi dankwalin tana fadin"Laccan Mu ta farko zata Fara daga Dauran dankwaline,Tunda Shi na tarar kinayi.."Gyada kai Azeema tayi tana kallon yadda ta dankwasa dankwalinta,Kafin ta Dauramata bisa kai,Daurin Maryam babangida tana yi tana mata bayanin yadda zatayi bayan tagama sai tace ta kwance ta daura da kanta,nan da nan kuwa ta aza abinta yayi kyau sosai Tafi Anty madina tayi mata tana fadin!Good matar yaya da alamun, dai zaki Saurin dauke komai,yanzu taho muje mufara dora karatunmu lokaci na kurewa.."Tafada tana jan hannunta zuwa kan gadon,tsakiyar gadon madina ta hau tana fadin"Hayo nan matar yaya..!Hayowa Azeema tayi suka zauna Suna Fuskantar juna bayan Dukkansu sun tankwashe kafafunsu Riko hannunta Madina tayi kafin tafara da cewa.

""Abu na farko kafin mufara dora karatunmu yakamata kifara sanin menene Aure,Aure dai wani Nau"i ne na bauta,gabadayanshi bauta ne na ubangiji,kuma duk Abunda akace Bautane na ubangiji toh sai fa mutum ya dage kuma ya zage damtse,Abubuwa guda biyu da suka kasance ginshikin bauta ma Aure sune LADABI DA BIYAYYAH..Matukar kinaso,kiyi bautar Aure,sai kin kasance,kina da ladabi da biyayyag,kibi mijinki Sau da kafa,yi nayi bari na bari,kiyi amfani da Umarninsa kiyi hani da Abunda yahanki,karki tsallake Umarninsa ko alama,ki kuma bisa don yana gaba dake,tsakaninki dashi tamkar tazaran kasa da Sama ne,Aljannarki,tana karkashin digadigin sane,sai yalamuncemiki zaki Shiga Aljannah,Abubuwa masu muhimmancin dayakamata kisani bayan Ladabi da biyayyah wanda suka kasance ginshikin,ki kasance mai HAKURI.. Hakuri wani babban Tsani ne,Azeema matukar babu hakuri Da juna Da Auren mutane dadama ya mutu acikin Duniyan nan,domin ko harshe da hakori,suna sabawa balle zaman mutum da mutum,Namiji yana son agirmamasa sosai balle ke mijinki yana da son abashi girma bayason Raini ko kadan,kuma yana da isa da takama,toh dole sai kin zama mai hakuri domin zaki dinga ganin yana yi miki komai cikin isa,duk da ya isan ne,domin Shi Shugabane gareki,ki ka sance mai kauda kai,banda yawan korafi kigani kikigani kiji kuma kikiji,Toh in kikayi haka Aurenki zai zauna lafiya kuma zaku Fahimci juna Sosai,abu nagaba danikeson fadamiki,Shine Kisance mace Tagari wacce take maida damuwar mijinta nata,Farincikinshi shima naki ne,ki kasance kina kokarin rike Sirrrinki dana mijinki,domin bayyanar da Sirrinki ga kowa,koda ga goggo ne,ko kakarki ke ko ni kaina,in bawani abu bane wanda yazama dole sai iyaye sun Shiga ba,Shima din ki bari sai dai in Shi yafara furtawa,yin hakan ba karamin karama mace daraja yakeyi ba,kinga duk sanda Namijin yasan baki da Sirri shikenan ya ranmiki Daga ranar zai Fara kokarin Rike Sirrinshi bazai taba bari ki sani ba,Ki sance mai yawan Fara"a ga mijinki Azeema,karki bari ko alama ya zauna cikin Damuwa kiyi amfani da baiwarki ta diya mace ki hillaceshi har ya manta damuwarshi,ki sance mai ba mijinki shawara,ta wajen aiki ne,na game da yan"uwanshi ne,ke nakomai ma,ki zama mace jaruma wacce zata dinga karafafama mijinta gwiwa aharkan komai,kinga in kika cika wadan nan sharudan kin gama cika Sharudan zama MACE TAGARI.."Fatan kina Saurarena da kunnen basira.

Jikin Azeema daya gama yin sanyi tagyada kai tana fadin"Eh ina Sauraranki Anty madina.."gyara zama madina tayi kafin tace"good to kinga duk wannan karatun danayi miki toh matukar baki cika Wadandan Fa"idojin da zan gayamiki ba,toh duk abanza ne,domin kamar kayi wanka ne kayi kwalliyah ka koma kayi ma kanka wanka da Kasa ne,"Kallonta Azeema tayi tana Sauraren mai zata cemata Madina ta cigaba da Fadin"Fa"idojin Sune, *KWALLIYAH,GIRKI,IYA SALON MGANA,SALON KWANCIYA.*Kinga duk wanda kika saki acikin hudun nan Toh ina mai tabbatar miki kin samu nakasu"Zaro ido Azeema tayi madina tace"Yes..Matukar baki iya girki toh yakamata ki daina amsa sunanki na mace,ko baki iya kwalliyah ba,da yadda zaki dau dressing din da zaki dau hankalin megida ba,kema Sunanki Sauna,kana matukar baki iya Salon mgana ba,da yadda zaki Rikita mai gida da salon mgana na jan hankali ba,kema Sunanki sakara,uwa uba baki iya salon kwanciya balle sanin yadda zaki sarrafa maigida ta hanyar rikitashi da salolin kwanciya toh wannan Sunanki Dussa,duk matakan baya,kin gama zubar dasu,don sai wadannan sunyi kyau hasken wadanchan ke bayyana"

gyada kai Azeema tayi kafin tace"Toh Anty kimin bayaninsu daya bayan zan Fi ganewa.."Anty madina tace "Yanzu kuwa matar yaya.bari mufara da kwalliyah, girki wannan sai anjuma zamu Shiga kichen Shi pratical zamuyu kingane.."gyada kai Azeema tayi kafin Anty madina ta Furta..

*KWALLIYAH..* ita kalmar kwalliya ko ahausance sai da aka kawatata kafin Afurta,Ita mace kuma dama asanta yar kawa da kwalliyace,kwalliya kala kalace,akwai wacce akeyin wanka kawai asaka kaya Shikenan,anyi kwalliya toh ni ba ita nake Nufi ba Azeema Firstly Ki lakanci kayan da in kika saka Suna amsanki,riga da Sikat ne,ko kuwa Riga da zani ne? Doguwar rigane? ko kuwa kayan Rumgumar darling ne,ma"ana kananan kaya na zaman Falo,da inda kika karanci Kayan da sukafi fitar miki da Sirrin kyau sai ki lazimci dinka ira irensu,bayan nan kada ki dauka ance kwalliya ki zata wannan kwalliyan ta zamani ne data Fito ta hauka,ki saka Foundation ki zamo aljannah garin gyaran ido ki Rasa gira,No ba ita ba Simple make up,wacce da an kalli mace asan ta san Abunda take,kuma kallon Fuskarta zai sa agane kedin classic ce,ki shafa hodarki sai jambakinki wanda yayi daidai da kalan kayanki Shima kada ki cika,ki laziminci sanya kwalli domin Farin idon mace bai da kyan gani,ki koyi kashe dauri kala kala domin burge mijinki koyi salon Tafiya mai daukan hankali duk zan koya miki wannan,Ki sanya dan kunne da sarka ki sanya awarwaro,da Sauran kawan mata kada kibari mijinki yadinga shakan wari ajinki basai kin zama kwado wajen wanka ba,kiyi koda sau biyu Arana da wankan gaisuwan Safe da waankan barka da dawowa megida,wankan safe ta Kayanmu na hausawane Atamfa ko leshi,ko wht ever dai,da yammah kuwa english wear ne,mai wando ne mai sikat ne,sai dai wanda kika zaba duk dayane ya kasance dai koya kika gilma kamshi ke binki shiyasa duk Rinti duk wuya kada ki Rasa humra ko kiyima Turare yaji sam kada ki Fara Azeema domin kamshin na jan Hankalin Namiji zuwa gareki tare da Kara dankon kauna,sai Abu na gaba

*IYA SALON MAGANA.* Kefasan akwai dayawa matan da basu iya mgana da miji ba,wata in tana mgana da mijinta kamar tana mgana da wani kaninta ko tsaranta ba karya harshe ba Tautausawa ba girmamawa bawani karkwasa balle wani Shagwaba a"a sai dai kawai damkam dinkin kamar wata Sauna ko sakarya yakamata mata su gane harshenki yazamanto kala kala ne,ma"ana harshen da zakiyi mgana da mijinki dabam,wanda zaki amfani dashi wajen mgana da kawarki dabam,wanda zakiyi da makotanki dabam,kai kowa kinsan yadda zaki karya harshe ki iya salon mgana dashi Sai kiga kin zama mace mai aji da kima a idon Jama"a,mganar yadda zaki karya harshe wajen Miji Shine First look at me Azeema kamar ace kene Abban Hidaya muna zaune haka kamar zanyi mai wata mgana mai muhimmanci abu na Farko sai na Fara jan Hankalinsa zuwa gareni,bayan na kuramai ido na langwabe wuya gefe daya na marairaice To indai yaga kinsamai ido haka zai bar dukkan Abunda yake ya tambayeki"Noor meya faru ne?Zaki Fara rigimarki ko? ke kuma dagajin haka sai ki shagwabe Fuskarki da muryanki kice"Abban hidaya ya mganarmu Ta Ranar naji haryanzu bakace komai ba.."Ki karishe kinamai Fari da ido,toh lokaci daya zaki ga ya Rude yana tambayanki wata mgana,ke kuma sai ki kalailayeshi bisa jikinsa,domin yin nesa da Jikin miji na rage Shakuwa Shawarata gareki Jikin yaya captain yazama wajen zamanki matukar yana gida ta hakane body contact dinku zai Shaku da juna,kuma shi Namiji yanason adinga mannemai ana lafemai bisa jiki,kin Fahimta..? ajiyar Zuciya Azeema ta Sauke kafin tace"Na gane Anty madina.."ta gyda kai tana fadin"Naji dadin jin hakan yanzu bari muje gaba lokaci na Tafiya,Abu na karshe kuma wanda yafi muhimmanci Shine

*SALON KWANCIYA..* Zaro ido Azeema tayi Da Sauri tana Rufe baki da hannu hararan wasa Madina ta mata Tana Fadin"Stop joking Azeema Abu ne mai muhimmaci infact ma Shine ginshikin Aure,so u better listening very carefully don zai miki amfani ki cire kunya domin dama rayuwar aure sai ka cire dukkan wata kunya kake iya mace mai aji da Kima a idon mijinta.."Saurin gyada kai Azeema tayi,kafin Anty madina ta dora da cewa

"In Akace Salon kwanciya ba Ana nufin komai bane illah yadda zaki iya Salo salo tare da hikimar Sarrafa mai gida A Shimfida,Na farko bawai ki zama wata dussa ba,kina kwnce duk inda miji ya juyaki ki juya kamar wata bichan No ki zama kece kike jan Ragamar Abu kezaki dinga sarrafashi Ta salo kala,kala wanda zai gane yes yana tare da cikakkiyar mace wacce ta san Kanta,ki sance wacce zaki jiyar da mijinki dadi takowani Fanni,ki sanyashi yayi miki kuka harda koke koke,ki sakarmai jiki,shima ya sakar miki kada kiji kunya ki saki jikinki ki Tsotse mijinki daga sama har kasa,shima haka kuskuren da mata yakeyi Shine sai ga mace wai sunyi Fada da miji sai kiga ya nemeta Shimfida,wai Saboda yabata miki rai sai kiga mace tayima namiji sharaf yayi yadda yagama dama dake,bawani Taimako,toh hakan kuskure ne,wlh yana kawo tsana koda bata miki rai yayi,in kika tsage kika farantamai wlh tallahi da kanshi zai gane yayi Kuskure har yabaki hakuri,Azeema sai kin dage sai kuma kin zage damtse,domin Duk cikarki mace matukar baki gyara chan headquater ba duk abanza,kinga magungunar dana baki kina amfan dashi,duk dakaina na hada kayan Ni"imar mata ne,Kayan Gona ne,sai su aya dasu dabino,sai su kanunfari da Sauran itatacenmu,kada ki bari Fruit yadinga Wuceki duk Rana,ki lazimci Shansu akoda yaushe,domin Babu Abunda yakaisu kawoma mace Ni"ima kamar Shi,ga madara ga zuma koda baki dashi siya madararki ta sajet kullum na Hamsin ki dinga kalata da zuma duk safiya ki dinga sha kigani wlh sai kin bani labari,ammh yanzu mata sun Haukace da mganin mata kamar ibada,Abun haushi ma sai wani lalacewa Daya Fito yanzu sai kaji ance wai kashin tantabarama mganin mata ne kasiddan,ke kuma don kina wawiya Tantabara ta Fitar da cuta ke kuma ki siya,ki dinga Turawa kamar wata zararriya wlh mata mu Farka da wannan Siya siya dakikeyi da sana"a kikama da kudin daya fiye miki wlh domin yanzu kishinki Abun hannunki dakuma yadda kika dauki Aurenki,matukar Baki da sauran Abubuwan nan,koda mganin dubu dari zaki sha wlh kullum Asauna zai dinga kallonki,babu wani cigaba sai ci baya daga Karshe sai kifara Tunanin kila an samiki hannu ne,toh in zaku Farka tuni ku Farka kikama Allah da manzansa ko kya rabauta Ranar gobe kiyama..."Jinjina kai Azeema tayi tana Fadin"Tabbas mganarki haka take Anty madina kuma nayi miki alqawarin insha Allahu bazan baki kunya ba.."Damke hannunta madina tayi tana fadin"Yauwa matar yaya Naji dadin jin haka,yanzu mike muje Falo na koyamiki salon tafiya masu jan Hankalin maigida So nake ki rikitamin yayan Nawa fa.."Tafada tana Dariya da Hanzari suka mike atare suka rankaya zuwa babban Falon Gidan,wanda Tuni mai aikin ta tsaftaceshi,takoma kichen tana wanke wanke kwanuka.

Anty madina ta dage sai koyama Azeema salon Tafiya take,da yadda zata dinga mgana cikin jan aji da shagwaba,bata barta ba sai da ta tabbatar da ta iya kuma ta kwatanta kana ta kyaleta,daganan taje ta kwanta itama tace taje ta kwanta sai zuwa anjuma su Dora daga inda suka tsaya.

********************

""Kokafin Sati daya tacika Tuni Azeema Tazama yar gari,in ka ganta bazaka iya ganeta farat daya ba,tayi haske tayi kiba fatarta ta goge sosai,ga iya daukan dressing ga Tafiyar Daukan Hankali salo salo Natafiya da Da Namiji ba wanda Azeema bata sani ba,salon kwanciya kuwa ta haddace kaloli sunfi kala ashirin wanda Anty madina ta zage Ta nuna mata su pratical Tagani kuma ta kwatanta mata,Hakika Azeema ta karu da Anty madina ta bangarori dama,ta bangaren iya girkin zamani,snaks,ne da Abincimu na gargajiya ba wanda Azeema bata iya ba,ga Shi ta koyi iya zama da kowa yanzu ga iya karya harshe kamar wata uwar mata,domin yanzu Tuni mganarta yakoma shagawaba shagwaba saboda yadda ta haddatu,bangaren gyaran jiki kuwa har dilka Anty madina tayi, mata,magungunarta kuwa tun kafin satin su cika Azeema tasan ta zama mace domin kowani gaba na jiknta yanzu yana bukatar motsawar da Namiji ne,ga Ni"ima da Allah ya zuba mata wuni take chanza pants😂saboda yoyo,ita kanta Madina tayi mamakin Saurin daukewar da Azeema tayi komai cikin lokaci kadan,Shiyasa Aranar data cika sati Anty madina takaita wani shagon kwalliyan mata aka yi mata gyaran kai da kunshi mai kyau da daukan Hankali,zanen Fulawa hannu da kafa,ja da baki,nan da nan Azeema ta dawo taraurauwa, Satin na cika Ummah ta kira Madina tace tadawo da ita yau goggo tace su mikata dakin Mijinta,madina bata Haufi kan Azeema ba domin tasan bazata ta bata kunya ba,tuni ta hadamata kayanta cikin manyan akwatuna guda uku wanda Ta siyamata,Tuni bose ta kawo Dinkunan data dinkamata,tare da kananun kayan data siyamata hade da kayan kwalliyanta da duk Abunda zata bukata,Ita kuma Azeemar Ta Shirya cikin wata Atamfa milk da zanen ja ajikinta dinkin Riga da Sikat,wadanda suka kamata sukayi mata cas dasu hip dinta da boobs dinta duka sun bayyana ta cikin kayan,ta Daure gashinta da band dinta bayan ta kafe kanta da Daurin zara buhari,fuskarta da make ammh simple one ne,kafarta sanye da takalmi half cover ja,haka jakarta sai mayafinta ma ja ne,tayafoshi bisa kanta wanda kallo daya zakamata kasancewa eh lalle wannan Azeemar ba itace Azeemar nan ta gombe ba,wannan Azeemar Kaduna ce,domin wayewa tare da wani kissa da kisisina na mata Tuni Azeema tayi haddanshi,ko yadda take takunta kadai ya isa masu karatu ku gane cewa Azeema fa tayi Shiri sosai kan zama da yaya captain,Karfe Hudu direba ya kwashe su,ita da Anty madina da yara Harda mai aikinta gidan gabadaya suka tafi,kusan tare suka Isa gidan su da Anty mardiya wacce tazo itama amika Azeemar gidan yaya captain da ita.

Ita kanta Anty mardiyan bata iya gane Azeema ba ,sai da Anty madina Ta sanar da ita,rike baki tayi tana mamakin wannan al"amari lokaci daya ta Tahau jinjinama Madinar saboda Namijin Kokarin datayi akan Azeemar,atare suka shiga babban Falon gidan inda suka tarar da Ummah da Baba ade sai goggo suna zaune suna hira,Suka Shigo madina da mardiya sune kan gaba,sai Azeema dake bayansu tana rike dasu hidaya dakuma ya"yan Anty mardiya,Ummah tatashi tana faman Tarban ya"yanta cikin Farinciki,har Azeema Tashigo ta gaishesu ba wanda ya Shaidata Itako ganin haka sai ta koma gefe tana Wasa dasu hidaya Ummah ce ta kalli Azeema tana fadin"Madina hala wannan Kanwar megidanki ne.."kallon juna sukayi su duga ukun kafin Madina da mardiya su kwashe da dariya goggo ce ta katsesu da fadin"Wai ni ina diyatace banganta ba..? Dariya madina ta saka tabama Mardiya hannu suka kashe,kafin mardiya tace"gaskiya na jinjinama madina,yanzu ko dukkanku ba wanda ya gane Azeema? galala suke kallonta kafin Goggo tace"ina Azeemar..? Azeema dake gefe ta daga hannu tace"Gani fa anan goggo Tundazu nake kallonki ammh sai naga kamar baki gane ni ba.."Tafada tana yar dariya.

Ai gabadaya goggo da Baba Ade da Ummah Suka saki baki Suna bin Azeema da kallo,madina ta mike tana fadin"Azeema tashi ki juya musu su kara ganinki da kyau.."cikin kunya Azeema ta mike tana juyawa,ai bata gama ba Ummah ta mike ta Rumgumeta Tana fadin"Job weldon makka da madina wlh kin yi aiki mai kyau Allah ya biyaki.."goggo ko fadi take"Azeema tace tadawo haka? lalle yanzu bani da shakka akanki diyata,Madina Allah yayi miki albarka kin cece aure Allah yayima Rayuwa albarka."Haka Baba ade keta kwararama Madina da Ummah addu"a Ummah ce ta mike tace"ya kamata muyi harama kafin dare yayi ko? Madina tace"Ummah Ni da nace nida mardiya mufarayin gaba saboda gyare gyare da goge Tunda dai mace bata taba zama agidan ba,dole gidan yana bukatar gyara,in mun kammallah sai mu kiraku awaya sai ku taho da Azeemar.."Jinjina kai Ummah tayi kafin tace"Eh kuma fa kinyi mgana,to ku hanzarta sai mu mu taho daga baya.."Jin Haka yasa Madina da mardiya suka mike kowacce Ta dauki jakarta,tare da yar aikin Madina suka tafi yara kuma suka makalema Azeema sai ummah tace abarsu,direba ya kwashesu tare da akwatunan Azeema da Sauran kayanta,Koda suka isa barikin Sojojin dake babban get basu barsu sun Shiga ba,sai da madina ta kira yaya captain tace gasu abakin barrak dinsu,an hanasu Shiga,cikin lokaci Captain ya yi musu waya sai gasu madina abakin apartment din Aliyu nan suka tarar da Aliyun da jabir suna tsaye,dukkansu sanye da Fararen kaya riga da wando masu tambarin Army daga gani suna wani Training ne,da hanzari Aliyu ya isa garesu sukuma suka firfito suna gaisheshi ya amsa yana tambayansu ya yaransu,bai tsaya wani mgana ba,ya mika musu makullin gidan yana fadin"Ga key din nan,already koda kuka kirani muna kan wani aiki ne.."karba Madina Tayi cikin girmamawa,wucewa yayi Shiko Jabir ya tsaya yana gaisawa dasu yana mamakin mai ya kawosu,nan take Shaidamishi Azeema ce zata tare anan barikin,baki Jabir ya saki yana mamakin Aliyu don ko alama bai taba Fadamai ba,koda ya tambayeshi mai su Madina zasu zo suyi cewa yayi bai sani ba,Shi yakarasu har kofar gidan kafin ya juyo yabi bayan Aliyu da gudu har ya cimmai yana fadin"Sannu uban yan Sirri ko nace bakin munafiki boyen mai ake mana,toh naji Ashe zaka samu wajen hutu ne ba lbri.? ko kallonsa Aliyu bai ba harma ya cire rai da zai yi mgana sai chan yaji yace!eh taya zan gayamaka Tunda kai yaro ne,haryanzu baka girma ba,ka bari in ka kara kwari mayi wannan mganar.."baki jabir yakama yana fadin"kutumar ubanchan Ammh fa ka raina min wayau,kalli Mazantakana dakyau yasin tafi taka kwari da juriyan wahala.."Kallonsa Aliyu yayi kafin yace"Allah ko,kenan ka jaraba ka gani,"Eh na jaraba mana,.."yar dariya Aliyu yayi kafin yace"eh lalle ka lalace kenan kana Shigo da wata ciki kenan da daddare...? kallonsa Jabir yayi yana fadin"ina kenan..? ciki gidan ka mana,kana jarabawa...? baya Jabir yaja yana Fadin"Allah ya isa da sharrin daka kullamin,ni ko Rumgume mace bantabayi ba."kai tsaye Aliyu yace!"Toh kagani haryanzu da Sauranka yaro,Kabari ka girma ma tattauna mganar.."daga haka ya wuce yabarshi nan yana Duramai zagi harda Allah ya isanshi Abun yamai zafi,duk kwanan karfin halin dayakeyi ammh gayen chan yacemai yaro Tabdijam dole ya mike tsaye.

Readers Also Read