Kenza eBookz

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy - Chapter 16

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy - Chapter 16

Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 16: Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 16. *INTELLIGENT FANS* Mman Sadeeq Anchau Hajara…

3,370 words

*INTELLIGENT FANS* Mman Sadeeq Anchau Hajara Maman

*ZUMUNTA NOVELLA* Fati al"amin Sadiya muhammed Ummu sudes Nusaiba y gidado Jikar Hajiya Sadiya muhammed Mom sayeed and Noor Aisha Aliyu

*ALIYU GADANGA FANS 3* Halimatu Hauwa"u S Tudu Napeesa Mman Ummeta Mman Useey Khadijat Andijat Innallaha ma"assabirum Halimatu masoyiyata( Neat lady)

_Thank you all For ur Comments and Support...✌💪Allahu ya bar Zumunci Ameen...🙏 SON SO FISABILLAH_😘

*Chapter 20*

""Basu farka ba, sai da wayar Aliyu ta isheshi da karan Neman Dauki kana ya tashi yana ganin mai kiran ya kwashi rawan jiki ya daga wayan yana fadin"Hello Ummah.."Ummah dagachan bangaren tace"Aliyu ga direban nan akofar gidanka yace yana ta knoking Shuru.."Dirowa daga kan gado Aliyu yayi da Sauri yana bude wardrope ya dauko jallabiya ya zura yana fadin"Wlh Ummah bamuji ba.."kai tsaye tace"Toh ka fita waje ka sameshi" daga haka ta yanke kiran.

Sauke wayar yayi yana kallon Azeema dayayi wanda take kokarin tashi zaune tana cije lebe,da sauri ya karisa gareta yana taimakamata tatashi zaune muryanta da alamun barci tace"waye yazo yaya..? hancinta ya lakuce yana fadin"babu kowa Ummah ce ta turo direba da sako,ina zaton breakfast dinmu ne,kamar tasani ko jiya na aikace yarta bazata iya moriya ba yau.".harara ta sakarmai tana bata Fuska Saurin mikewa yayi yana dariya yake fadin"Ko ba haka ba? au naga kina hararata ok baki gajiya ba ko,toh bara nadawo nazo nakara second round yanzu nan kuwa.."Tanajin haka tayi Saurin komawa ta kwanta tana karamin kuka tace"wlh da ciwo bai warke ba Yaya captain.."Tafada tana yarfe hannu kamar lokacin takejin zafi,tara gira yayi yana fadin"Really,Toh nuna min inda keyin zafin?Bata Fuska tayi tana kokarin budemishi kafafunta tana fadin"Allah duba kagani.."ganin yadda yake dariya yana lekawa yasa ta rufe da Sauri tana tura baki baya ta juyamai tana yarfe hannu,baya yaja yana fadin"Bari naje nadawo sai nagani da kyau.."Yafada yana Rufe baki filon kujera ta makamai tana buga kafa,sai kuma ta cije baki tana yarfe hannu saboda zafin daya tsirgamata,waje yayi da gudu yana dariyan Nishadi,Sai daya ya gyara Fuskarsa kana ya fita waje ya tarar da direban gidan kawu da hanzari ya isa gareshi sukayi musabaha kafin ya bude motar ya fito da wani babban kwando,ya mikamai yana fadin"gashi inji Hajiya.."karba yayi yana fadin!"Ok ka gaisheta.."Daga haka sukayi sallama ya juyo dauke da kwando,karaf suka hada ido da Jabir dake jugging aharabar apartment dinshi yana mai dariya shiko Aliyu harda dagamai hannu tare da dankwasamai babban yatsanshi lokaci daya yana dage gira,Da hanzari jabir yabiyoshi da gudu,aiko da hanzari Aliyu ya shige gida ya rufe kofa yana yar dariya,shiko Jabir baki ya rike yana fadin"Kan bala"i dagani sojan chan yasha gara jiya,ji sai wani kyalli yake,tab nima dole ne nazo nayi Auren Tukan gayen nan ya haihu yace ni kaninsa ne.."

Koda yakoma Azeema ta rarrafa taahiga Tiolet ta sake Shiga Ruwan zafi kafin tayo wanka,koda yashigo ya ganta bakin madubi tana Daura dankwali ta sanya wani less,mai Ruwan kasa,ta daure gashinta da band da hanzari ya karisa yana amsan dan kwalin yake fadin"kawo na daura miki yar kauye kawai.."Sakarmai tayi tana fadin"wa?,kai din ne ka iya Daura dankwali,tab Kaida babu Abunda ka iya sai duka dasa mutane tsallon kwado.."dariya ya sheke da ita yana fadin"Nifa haryanzu Azeemar kaduna bata daina bani mamaki ba,ko za"ayimin karin bayani.."Fari tayimai da ido kafin tace"babu bukatar wani bayani, mamaki kuma kaciga da adanata,saboda kabama Sabbin damar shiga"Ware ido yayi yana kallonta itako bata tsaya wani mgana ba,tajuya tana wani taku ta fice daga bedroom din,Galala yayi yana kallonta kafin ya juya Shima ya fada Tiolet Nishadi yaki sakinshi.

Tana Fitowa daga Kwandon Abincin dama yunwa takeji kichen ta nufa,da hanzari ta dauko Filet da cokali,tadawo ammh tana tafiya tana gwale kafa tana cije baki domin jiya taji maza fa,Sinasir ne da miyar agun sai Ferfesun kan sa,sai ruwan shayi mai hade da Na"aNa"a,Diban Sinasir din tayi guda daya,taci Ferfesun ne taci dayawa sosai Saboda Romonsa,Tana cikin Sude Filet din Aliyu ya Fito cikin Shigar shadda Fara Riga da wando dinki Muhammed,harda hulansa zannah bukar blue saboda aikin na kayan blue ne,yayi kyau sosai saboda yadda yake haskawa ga wani Annuru dayake ta Fitarwa kusa da ita ya zauna yana kallonta,itama Shi take kallo gira ya dage mata yana fadin"yane Yan matan kaduna.."Ijiye Filet din tayi tana mirmishi kafin tace"Samarin bariki kayi kyau.."

Yadda kanshi yayi bisa kafadanta yana lumshe ido kafin yace!Har na kai ki pretty.."Jingina kanta tayi jikin hulansa tana fadin"Sabon suna na samu kuma wai pretty..? Dago da kansa yayi kafin ya sanya hannu ya riko duka hannuwanta yana fadin"yes Azeema yesterday ki sanyani farinciki da babu wanda ya taba sakani Tunda na mallaki hankalin kaina,bansan meyasa ba ammh chanzawarki Azeema tafi komai yimin dadi plz tell waya koya miki duka wannan Abubuwan,domin wlh kina ta zuwarmin da Abubuwan ban mamaki "Mirmishi Azeema ta saki kafin ta kwantomai bisa cinya tana fadin"Naji dadi da na sanya mijina farinciki dama burina kenan Nidai Fatana Allah ya aramin lafiya da tsawon rai nayita Farantamaka har karshen rayuwata.."Tafada idonta na cikowa da kwallah.

Gashin kanta yake wasa dashi yana fadin"Ameen Ameen Thanks for evertin dear Allah yayi miki albaarka.." Da Ameen ta amsa kafin shuru ya biyo baya kowa yana saka Abun da ke ransa,Azeema ko Farinciki ne ya cika jin yadda Yaya captain ya saki jiki da ita yana ta mata godiya,Lafewa tayi ajikinsa tana shakan kamshinsa,daganan sai barci ya sureta,sai da barcin nata yayi nisa kana ya zameta bisa kujera,yaja filet dake kujera ya zuba Sinasir din ya karya bai Fita ba sai ma ya kunna tashar CNN yana kallon labarun,gefe daya yana kallon Fuskar Azeema wacce ke barci agefensa ammh hannunta guda daya yana cikin nashi yana murzashi lokaci bayan lokaci yana sakarmata kiss.

Zayyano irin Abubuwa dasuka faru wannan Ranar toh tabbas zan gama littafin nan ban gamashi ,Bayan Azeema tatashi daga barci suka dasa hira ita da yaya captain cike da kwarewa da kuma wayewa,ita kuma Azeema tana kwance kan jikinsa tana bashi amsa cikin yanga da yauki lokaci bayan lokaci kuma ta sakarmai kukan zafi ita kafafunta ciwo suke,shiko yana ta biye mata yana Faman lallashinta,sai zuwa yammah kana yasamu kiran Kawu akan yazo gobe su Goggo zasu koma gombe,Wanka ya sake zai Fita ai Azeema tasaka kukan Shagwaba sai ya tafi da ita,toh ganin ita kadai ne agidan bata saba ba,yasa yace ta Shirya su tafi da hanzari ko ta Shirya suka Fito tana kallen kallen cikin barikin ta tsorata yadda take ganin Sojoji na wucewa da gudu kamar wani Abu,na faruwa Makalesa tayi tana makyarkyata shiko yana ta mata dariya,ammh karin ya yarda zaije da ita sai da tayi mishi alqawarin daidaita Tafiyarta duk da karfin hali take,ammh saboda tana son zuwa haka ta cije tana hade kafanta,ammh duk da hakan da mutum ya lura dakyau zai gane somethings is happen.

Su Ummah sunyi mamakin ganin Azeema,ammh sai basu yi mamaki ba ganin yadda suka rabu jiya,basu dade da zuwa ba direban kawu ya kwashi su goggo da Baba Ade,da kayan arziki niki niki sai wanda yagani,duk da kawu yayi yayi goggo ta kara ko Kwana biyu ammh taki yarda dole ya kyaleta,Su goggo na wucewa suma basu dade ba suka wuce bayan doguwar Nasihar da kawu yayi musu daganan basu wuce gida ba,Restaurant yakaisu suka ci abinci dazasu koma gida Ya Shiga yahuza Suya ya siyo musu kaza da madarar hollandian,masu sanyi,basu koma cikin bariki sai dare lokacin ana kiran issha"i Ledan kayan ya bata ya wuce masallaci itakuma ta Shiga gidan,da zai dawo tare da Jabir suka Shigo,lokacin hartayi wanka ta sauya kaya cikin wani material baki da kwalliyan ja,jin Shigowarsu yasa ta sako babban mayafi ta fito falo suka gaisa da jabir yana ta mata Tsiya yana fadin"Matar Soja a bariki."mirmishi kawai take tana sadda kai.

Jabir bai dade ba,ya yi musu sallama ya koma gidansa,kazan Aliyu ya fito musu dashi sukaji suka koshi,domin Shi yayi ta durama Azeema abaki yakuma bata madarar,tasha yau ma kafin su kwanta sai da yaso maimata Abun jiya ammh Azeema tasakamai kuka da magiya da zafi sanin Raunin dataji jiya ne yasa ya sausautamata ammh fa sai da ya samu yar Natsuwa daga jikinta koda yashiga wanka Azeema gefe takoma tana Share kwallah Nipple dinta sunyi jawur saboda tsotsa bakinta ko haryana wani tsantsi saboda yadda yake shan lasa,yana Fitowa itama wanka ta fada Ammah sai da takara Shiga Ruwan zafi domin Anty madina tafadamata Shizai Taimaketa duk Ranar da Yaya captain yayi Disvargin dinta.

_________________

_Masauratar garin Agadez_

"""Da gudu Wata mota 607 kirar Piagion,baka ta shigo cikin babban kofar masarautar inda ainihin sashen matan maimartaba suke Dogaran dake waje suka Rumtuma da gudu zuwa ga motar suka mata dafifi daya daga cikinsu ne,ya bude murfin motan yana fadin"Barka da dawowa Yarima dan sarki jikan Sarki yarima mai jiran gado. "gabadayansu suka amsa sai da yabata lokaci kafin ya saka kafafunsa zuwa waje,kafar nasa sanye da wani katon takalmi booth ne baki masu igoyoyi duk ya daure su,Kafar Nasa farace sosai,takamarsa ne yasa bai Fito kai tsaye ba sai daya bata lokaci sai gashi ya fito masha Allahu daga sama har kasa na karemai kallo sanye yake da riga da wando masu Ruwan kasa baground dinsu sai ratsin green,kansa sanye da hula Shima irin kayan jikinsa kugunsa tamke da wani katon bell baki,daga gefen kafadansa Sai ga wani dan Anini daya nuna sunanshi Baro baro kamar haka.

*LIEUTENANT UMAR ABDULNASEER TAMBARI BUZU..* Kenan wanda ya kasance sojan kasa ne dayake aiki akarkashin Sojojin kasar Niger a yankin Niamey,dogon Namiji ne mai dauke da kyau da zati,Baya naja da Sauri saboda yadda naga yana kama da Aliyu gadanga sai kace wasu yan biyu saboda yadda komai nasu yazama iri daya ban tsorata ba sai daya fara taku da yanayin isarsa da takamansa komai irin na Captain Aliyu ne,dogarawan dake durkushe kasa suna zubamai kirari yadagama hannu kafin ya Shiga babbar kofar da zata sadashi da sashin Mahaifiyarsa wato GIMBIYA FASILATU.

Tunkafin ya karisa sakon isowar tilon Yaron sarkin ya cika Masarautar Duk da baifara isa Fada ba,ammh har jakadiya takaima sarki rahoton dawowar baban dan Nasa kuma magajinsa wato yarima Umar,ita kanta Gimbiya Fasilatun Tuni wata amintattaciyar baiwarta ta Shigo ta labarta mata bata ma kai ga Ficewa ba sai ga Yarima Umar din ya Shigo cikin Babban Falon na mahaifiyarsa wanda yaji kayan alatun more rayuwa,tana zaune bisa wani Tuntu na gidan Saurata gefenta wasu kunyangu ne,sunata faman mata Fifita da wani katon Faifai mai wani gashi gashi ajikinsa,yana Shigowa suka mike da hanzari kafin su sake zubewa suna fadin"Brka da zuwa yarima dan Sarki jikan sarki kuma sarki agobenmu in Allah ya yarda..!Suka hada baki Suna fada.

Fuskars babu Fara"a ko kadan ya daga musu hannu,jikinsu na rawa suka mike suka fice,dakin ya rage daga Shi sai mahaifiyarsa cikin wani taku ya isa kusa da ita yazauna kasa kusa da kafafunta yana fadin"Barka da hutawa Ranki shi dade.."ta dago tana kallonsa kafin ta sanya hannu ta dauko Tuffa cikin wani Faranti ta saka abaki ta gutsira kafin ta sanyamai baki Shima ya gutsira maidawa tayi ta ijiye tana fadin"Brka da zuwa yarima Umarun Faruq yarima mai jiran gado.."Tafada tana mai mirmishi tabe baki yayi yana Tauna Tuffan bai yi mgana ba sai da yagama hadiyewa Tukunnah yace"Nifa Ranka shidade bani son kina sanyawa ana min kirari da yarima mai jiran gado,sam ni mulki baya gabana Nafi kaunar aikina fiye da komai.."Yafada yana bata Rai.

Mirmish tamai mai kayatarwa kafin tace"Naka wasa Umar,ka manta duk sanda kayimin wannan mganar nasha fadamaka tun Wuri ma ka sanya son mulki aranka domin watan watarana kaine zaka mulkemu a wannan Masautarta ta *TAMBARI BUZU.* Saboda Maimartaba bai da wani da Namiji sai kai,sauran kannenka duka mata ne Umar,kuma ko ba mutuwa ba akwai Tsufa kuma dole masauratar nan na bukatar Adalin Sarki kamar mahaifinka kuma bakowa bane face kai.." ido ya tsuramata harta gama mganarta ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Uhm...,Mommy kenan ni duk ba wannan ba wata tafiya ce ke gabanmu next month in Allah yakaimu duk da bansa rai dani aciki ba sai gashi Sunana ya fito.

Kai tsaye ta takalleshi kafin tace"Wata Tafiya kenan? gyara zama yayi yana fadin"Gwanntin kasar Nageria ita ta kawo ziyara zuwa ga gwannatin kasarmu kuma azuwan datayi ne ta nemi hadin gwiwa da gwannatinmu domin Subata wasu daga cikin dakarun Sojojinta guda dari zuwa Nageria domin hadin gwiwar yakar yan boko haram da masu garkuwa da mutane,hadin gwiwan ta hada da cameeron da chadi,da Niger da kuma Nigeria,shine acikin wadanda za"a Tura harda bacth dinmu aciki kuma nine Shugaban tawagarmu.."Washe baki Gimbiya Fasilatu tayi tana fadin"Masha Allah wannan ai Abun alfahari ne,Allah yabada sa"a Allah yasa acimma buri,yanzu kaje kayi wanka kaci abinci ka huta nasan zuwa lokacin maimartaba ya bar fada yana Shashensa zan aika jakadiya tamaka iso sai kaje ku tattauna saboda yau bani keda Turaka ba gimbiya Razeenah ce"Gyada mata kai kawai yayi kafin ya mike ya fice yana mamakin yadda Mommysa tayi Farincikin da wannan Tafiyar wanda Shiko ko alama tafiyar bata kwantamai ba.

*Intelligent writer's Asso.* *Janafty Aka Shakira*💇 *2019..* *ALIYU GADANGA..!* _(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12* _Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_Sadaukarwa ga FIKIRAR MARUBUTA..,kamar irinsu,HassanAtk,and Hussain80k mai warin baki😹😛,Sai ke my abokiyar Hassada Mrs Sardauna,Ina kike kawata Hassana Dan labarabawa,Walidition,Diyata Ladingo,Sisinah Aisha Alto,my mryam obam Rabi"atu Sbs,Sahibata Hafsart Hafnan,...Da duk jama"ar dake gidan Fikirar marubuta kusani ku kara sani Janafty na muku Son kauna mara iyaka,Ina kuke yan Group din KHADIJA CANDY NOVELS..Ina gaisuwa Salwess,Da duka sauran masu Sharhi dake cikin group din,sai ALIYU GADANGA FANS1..ina kike My Esha,dake mman Muneebata,Aisha Adris,Fatima garba,Mman Ummu(Nemecyna),Kuma yan ALIYU GADANGA FANS2,Ina kai gaisuwa Allah yabar zumunci da duka Sauran group din dasuke Sharhi kan wannan buk din,Ina godiya Sosai Allah yabar Zumunci BOHOT BOHOT LOVE_

*NOT EDITED*💥

*Chapter 21*

""Bai isa Shashen mai martaba ba sai zuwa dare bayan an idar da sallar Issha"i lokacin angama hidimar Fada Sarki ya Shiga cikin gida wajen iyalansa,Lokacin da Umar ya tarar dashi yana kishingide cikin kayatattacen Falonsa wanda yaji kayan alatun more rayuwa,Tuffa ne ahannunsa yana Ci,gefe daya kuma yana duba wani littafin Iziya,jikinsa Sanye da riga da wando,irin na gidan Sarautu,Yana ganin Umar yatashi daga kishingiden yana mikamai hannu Karisawa yayi yana mai mikamai hannun yana fadin"Barka da hutawa Ranka yadade...".

Kusa dashi ya zaunar dashi yana dafa kafadansa yace"Yauwa Umar Sanda,ya aiyukan,nasamu lbrin dawowarka Tundazu toh lokaci muna fada kasan Sha"anin mulki sai da taka Tsantsan,nima dabakazo ba,yanzu nake Shirin zuwa shashen naka.."mirmishi Umar ya saki yana kallon Fuskar mahaifinsa mafi soyuwa gareshi,kafin yace"Eh Abbah Tun dazu na Shigo nima Ban leka Fada ba,saboda gajiya ammh kasan kowani hali nake ciki Dole nazo har shashenka na isheka.."girgiza kafadansa yayi yana fadin"Hakan na dakyau,ya wajen aikin naka Fata dai komai lafiya.

Ajiyar Zuciya Umar ya sauke kafin yace"Lafiya ba lafiya ba Abbah..."kallonsa yayi idanunsa sanye da Wani Farin medicated glass mai karama Mutum karfin gani,kafin yace"Lafiya meyafaru Umar zaki.."?Kada kai yayi yana Fadin"Wlh Abbah mganar hadin gwiwar nan ne Kasar Nageria ta nemi gwannatin kasarmu data hada hannu Suyi tare,Toh acikin Sojojin, daza"a Tura Nigeria Abbah harda tawagarmu kuma nine shugaban Tawagar.."Kallonsa yake har ya dire dan mirmishi yayi mai kafin ya maida kansa gefe yana kallon wani waje Mamaki yakama Umar a ladabce,yace"lafiya Abbah ko acikin mganata akwai Abunda yabata maka rai ne?.."girgiza kai kawai maimartaba yayi kafin ya saka hannu ya zare gilashin dake idonsa kafin yace.

"Ko daya Bata batamin rai ba,saima Tuno min da wani gibi dana kasa cikewa,karka damu Umar Allah natare dakai kuma addu"ar iyaye na bibiyanka,insha Allahu zakuje lafiya ku dawo cikin Nasara.."kai tsaye Umar yace"Ammh Abbah ka taba zuwa Nageria ne,wai ina Nufin koda yawan Ran gadin gidan Sarauta ne?" Kallonsa yake kur kafin ya kauda kai yayi Shuru sai zuwa chan yace"Na taba Rayuwa A Nageria bama zuwa ba Umar.."Da mamaki Umar ke kallon mai martaba kafin ya washe baki yace"Toh Abbah wani yanki ka zauna..? Yanayin Fuskarsa sai ta chanza Jikinsa yayi sanyi yayi Shuru baiyi mgana ba,ganin haka yasa Umar Saurin cewa"Afuwan Ranka ya dade bansan Tambayata zata bata maka rai ba Allah huci Zuciyarka.."bai yi mgana ba sai ma mikewa dayayi yazura takalminsa irin na gidan Sarauta hanyar wani kofa ya nufa sai da yakai kofar dakin kafin ya harde duka hannuwansa ta baya ya waigo yana fadin"Baka Batamin ba Umar,tambayarkace ban da amsarta domin nikaina Bansan awani yanki na rayu ba balle har na dora da wani Abun,Abu daya na sani inaji ajikina cewa ada achan baya nayi Rayuwa da wasu mutane,wanda Ahalin yanzu suke bukata,ammh kuma Allah ya boyemin Abun,addu"a zaka taya mahaifinka Allah ya bayyanar da Duhu yazama haske.."Yana gama fadar haka ya Shige kofar da hanzari.

Duk da Umar bai gane ina mahaifinsa ya dosa ba,ammh yasani koma miye shi Toh Tabbas,yana da matukar amfani sai yasamu kanshi da addu"ar Allah ya bayyana koma miyeshi,bai wani jima ba ya tashi dauke da Tuffa guda daya ahannunshi,yana Shirin Ficewa sai ga gimbiya Razeenah cikin alkyabbanta zata Shigo sukaci karo,baya yaja yadan rankwafa yana fadin"Barka da Fitowa Ummah.."Mirmishi ta saki tana fadin"Yauwa Umarur Faruqu saukan yaushe ba lbri,dazu kannenka keta zencenka.."kai ya sosa yana fadin!Dazu ne Ummah,agajiye nadawo Shiyasa ban Shigo ba,Zan Shiga da Safe mu gaisa da kiddo's dina.."Gaba tayi tana fadin!Ayyah..Yakamata.."Ficewa yayi yana fadin"Afito lafiya Ummah.."Ta amsa Da Allah ya sa Umar.

____________________

_Gombe_

Su goggo sun sauka gida lafiya,goggo akafara Saukewa kafin awuce da Baba Ade gidanta cike da kayan arzikinta ta sanadin Azeema domin kawu sai da yabata 20k dakyar ma ta amsa,sai kayan Abinci wanda yabasu ita da goggo harda na mallam lawal,wanda dama akidane Duk wata in zaiyima goggo sako,toh harda nashi aciki yamaida Abun Nauyi ne wanda ya rataya awuyanshi don ko komai Mallam Lawal nada matukar Tasiri ga rayuwar kanwarshi Suwaiba da Aliyu,balle yanzu da Aliyu ke Auren diyarsa.

Sai washegari goggo ta Shiga gidansu Azeema ta kaima mallam lawal sakon kudinshi da kayan Abincin Da kawu yabada abashi,haka yaketa zubamata godiya kamar yayimata kuka,domin kudin sunzo akan gabane,kasuwa taja baya gashi babu kudi ahannunsa,toh ga budi daga Allah,Nan yake tambayar Azeema aiko goggo ta tankwashe kafa tana bashi lbrin Azeema na kaduna in ma yaganta bazai ganeta ba,Yaji dadi Sosai yayita musu addu"an zaman lafiya,inna Ramatu kuwa dakyar ta iya bude baki ta amsa gaisuwan Goggo itako ko ajikinta bata damu ba,Tadade suna hira da mallam lawal kafin tayimai sallama zata tafi dago kan dazatayi taci karo da Azeeza Inna Ramatu ta rikota zasu bayi,Goggo ta tsorata da ganin yadda Azeeza ta dawo,saboda yadda ta rame duk kibar nan dakuka sani bata,tayi baki tarame fuskarta tayi wani iri,Bakinta duk ya bushe,dakyar take Tafiya,har suka Shiga bayin,Goggo na binsu da kallo sai da suka Shigene kana goggo ta maida kallonta kan Mallam lawal tana Fadin

"Mallam lawal,nace meya samu Azeeza ne,naga duk ta kare..? kada kai yayi kafin yace!Wlh bansani ba Suwaiba tun Ranar da kuka tafi ta kwanta ciwo,daga zazzabi shikenan jiki yaki dadi,toh Rashin kudi ne yasa Ita uwar tata bata kaita asibiti ba,ammh Tunda yanzu sun samu gobe sai Su Shirya su Tafi.."Gyada kai goggo tayi kafin tace"ikon Allah,anya ko Tana cin Abinci.."?Girgiza kai Mallam lawal yayi kafin yace!gaskiya bata wani ci,koni sai na mata jan ido take iya ci kadan,bata da aiki sai kuka nayi Tambayan Duniyarnan tafadamun meke damunta taki mgana,ta tambayi mahaifiyarta itama tacemin bata sani ba.."kada kai kawai Goggo tayi tana fadin!Allah Shi kyauta..Allah kuma yayayemata Abunda ke damunta.."Da Amin ya amsa,kafin Shima yamike har waje ya rakata yanata mata godiya.

Koda Su Azeeza suka Fito daga bayi basu samu goggo ba,waje Inna Ramatu ta zaunar da Azeeza inda Mallam lawal ya tashi,Kasa zama tayi saboda bata da karfin jiki,komawa tayi takwanta tana tari,inna na mata sannu,dagowa tayi tana fadin"Inna Da Azeemar aka dawo..?"tafada cikin alamun ciwo,Tsaki Inna taja kafin tace"Mtsewww..Bansani mara zuciya koda ita akadawo ubanki zatayi miki,duk uban wulakancin dasukayi miki,aiko yacu ki kama kanki,shiko shegen yaron nan mara asali,wlh ko bayan Ran Azeema ban amince ki aure shi ba.."tafada cikin kakkausan murya kafin ta wucewarta madafi tana ta fada tana zagin Azeezar hade da Azeemar lokaci daya tana kuma tsinema goggo don tace ita tazo anguwansu ta haifan musu dan Shege yazamantomata bala"i.

Readers Also Read