Aliyu gadanga complete novel by janafnancy - Chapter 4
Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 4: Aliyu gadanga complete novel by janafnancy Chapter 4. Bayan kowani Sati uku yake zuwa gida,ganin…
2,906 words
Bayan kowani Sati uku yake zuwa gida,ganin Goggo to duk sanda yazo nan yake ganin Azeema tare da ita,duk da yana so ya tambayi wacece,ammh miskilanci da rashin son Raini yasa yake basarwa sai Goggon ne dakanta take shaidamai Diyar marigayiya Fatima ce tabe baki kawai yayi bai wani nuna wani tsausayi ba,ko yaba mganar goggon mahimmanci,itama sanin halinsa ya satakama kanta dashi,Tun ganin Farko da Azeema tayima Aliyu bayan dadewar datayi bata ganshi ba,Allah ya sakamata tsoronshi,saboda ita arayuwarta ta tsani soja,saboda yadda takejin lbrin Rashin tsausayinsu,to Ranar data ga Aliyun ma da kakinsa ne,yazo gidan Goggo fuskarnan babu Annuri kafarsa sanye cikin wannan katon takalmn nasu,wanda in suka taka ka dashi,ko baka mutu ba,sai kayi jnya mai tsawo,lokacin data ganshi ya shigo dakin goggo,itakuma tana sharemata dakin,goggo na ciki,yana dago labule suka hada ido,ai saboda tsoro batasan sadda tayada Abun sharan ba ta kwantsama ihu ba,Wata razananniyar tsawa ya dakamata yana hararanta,saboda ganin yadda take neman Raina mai,wayau shi da gidansu ya shigo ta faramai ihu,tsawan data kara firgitata ta tsorata sai ga fitsari,shar yana zubowa ta kafanta saboda tsoro,dama Azeema akwai dan banzan Tsoro kamar farar kura,Baki yarike yana kallon yadda take shatata fitsari tana kamkame jikinta,aiko karisa shigowa dakin yayi yana kwanto belt dinshi yana fadin"Bush girl yanzu zaki durkusa ki shanye kazantar dakikayi kuwa..."Yake fada yana Shirin kwanto belt Goggo ta fito tana zabgamai harara,kafin tamaida kallonta kan Azeema taga yadda take rawan sanyi saboda tsoro fada Goggo ta hau gadanga dashi kan yazo ya tsorata mata diya korashi tayi,dole ya fice yana tsaki yaso goggo tabari ya lallasa yarnyarnan,banda iskanci da samun waje kamartane zatayima mutane Fitsari a tsaye,shibaima fahimci shiya firgitata ba,to tundaga ranar Azeema take Tsoron Aliyu wanda take kira da YAYA CAPTAIN,bata yarda tadawo gidan ba,sai da yakoma,Baya zuwa gidansu,ammh yana zama wajen sana"ar baba lawal ta kayan gwari,saboda kamar kawu bala,yake kallonsa ko bakomai yaba da gudummuwa arayuwarsa duk da yanzu yadan manyanta.
AZEEZA tunda Allah yasa ta dora ido kan Aliyu,watarana sun dawo daga mkranta suka ganshi wajen babansu,Azeeza saboda kallo sai da takusa fadi,sai da Azeema ta riketa,kallonsa take bata ko kiftawa Azeema ta tambaya waye wanchan na tare da baba? Azeema ta bata amsa da cewa"La baki ganesa ba,Yaya captain ne fa,na gidan Goggo..."Aziza najin haka gabanta yafadi kardai ace dan Shegen nan ne,mara asali,ammh ko gayen yana da kyau,ya hadu,wasa wasa ranar Tunanin Aliyu bai bar Aziza tayi sukuni ba,Tun tana daukan Abun wasa hartazo ta tabbatar da cewa takamu da son Aliyu,gashi ko mgana basu tabayi ba,saboda yana ganin yarinyar yaji lbrinta bata da kunya ko kadan,shiko baya hulda da marasa kunya yanzunan yarinya tanemi rainashi sai yaci ubanta ko agefen kwalan riganshi,shiyasa koda wasa bai taba sakarmata fuska ba tasha ganinshi baknta na rawa tahau gaisheshi shiko sai yagadama ne ma zai amsa da lafiya lau,daga haka ya gimtse fuska,Wani lokacin yake kawai take tana biyema Ramatun intana zaginsa,saboda bataso ta fahimci halin datake ciki. Ramatu kuwa ya tsaneta saboda rashin kirknta baitaba gaisheta ba ko zasu bangaji juna kuwa,shiyasa itama bata kaunarshi,duk inda ta zauna bata da mgana sai nashi dana mahafiyarshi,tasha kawo karansa wajen Goggo tama danta mgana baida tarbiya,sai dai Goggo tabata hakuri tace zatamai mgana,ranar data faramai mgana,cema goggo yayi"in batayi hankali ba duk randa ta shiga gonarshi sai ta zagaya anguwanan tana tsallen kwado.."dakuwa goggo tamai tana fadin"Tunda kasata nima zaka iya sakani kenan"Ko ajikinsa saima cema Goggo dayayi"Shi dai bai ce itaba,so karta sa kanta aciki..
Goggo macece mai fada,da shiga Abunda babu ruwanta,indai akan Da'ntane Aliyu,wanda takema kira da GADANGA,Tana da yawan barkwanci da son wasa,shiyasa ya maidata kakarsa,in kaga yadda ake daru tsakanin Gadanga da goggo sai cikinka ya kulle,in yadade baizo ba,tadinga kira tana fadin"Gadanga ko amun yaji ne? saboda kullum da tsiya suke rabuwa,Dakuma yazo ko kwana ba"ayi za"a tsiyace,goggo kenan da Aliyu gadanganta.
Aliyu mutum ne,mai yawan karfin sha"awa shiyasa tunda ya fahimci haka,sai ya rika azumin litini da alhamis,Ammh duk da haka Abu yaci tura sai ya yanke hukuncin fara neman Aure,koda kuwa da yan"matan dake haukan Sonshi ne,yafara neman wata mufida yar kaduna ce,Soyayyarsu batayi nisa ba,suka rabu,sakamakon mahaifinta yace bazai bata shiba,saboda yayi bincike ba"asan asalin sa ba,abun bai dameshi ba ya rabu da ita,bayan ita ya nemi Ummi yar katsina ce Itama itace ke mutuwar sonshi,ita harmgana tayi karfi,su kawu na Shirin zuwa komai ya rushe,bayan ita sai da akayi biyu,duk karatun dayane,Abun ya soma damunshi,duk matsayinshi ace anamai Wulakanci wajen neman Aure ana tozartashi kan baida uba,tun daganan ya watsar da komai ya cigaba da azuminsa kwatsam suka hadu da Ni"imatullahi akaduna wajen Dinner wani abokinsu shima Soja itakuma kawartace ai Tunda ni"ima ta hanga ido,taga Aliyu ta mutu akanshi,sai da tasan yadda tayi kafin tabar kaduna ta kafa gwannatinta.
Ni"imatullahi Ahmed Sidi na iya,diyace ga kwamishar yansanda na jahar gombe,kuma ya'ce daya tilo da iyayanta suka haifa,yar gatace ta karahe,wayayyiyace domin duka digeree dinta harzuwa master dinta ba A Nigeria tayima ba,yar kimanin Shekara ashirin da biyu aduniya,Fara gajera ammh itama babu laifi tana da kyau,Lokaci daya son Aliyu yayimata reshe harda rassa,tun bayabi takanta haryafara saboda yadda take gigitashi da salon soyayyarta,lokaci daya suka afkama juna da soyayyah mai zafi,ba"a dauki wani lokaci ba ya gabatar da kanshi wajen kwamishina zuwan farko duka iyayyan nata sun yaba da zabin diyar tasu ammh sai dai kash,kwamishina na bincikawa sai aka cemasa don makusa Captain Aliyu baida makusa,sai dai makusan guda dayane,rashin takamammen waye mahaifinshi,da kwamishina yaji haka yaso ya butse,ammh sai diyarsu ta nuna,in ba Aliyu ba sai mutuwa,dole aka yarjemai ya turomai magabantashi,kawu bala da mallam lawal sukaje,tun farkon mganar Auren sune jagoran komai har zuwa aka saka ranar Aurensu wata uku,murna wajen Ni"ima ba"a mgana,ta bangaren Aliyu dai laba"asa,donshi babu mai gane yanayinsa.
Da Azeeza taji lbrin Auren da Aliyu zaiyi sai da ta kwanta asibiti saboda firgici da damuwa,Duk iyayanta suka damu,kamar Azeema taji lbri,duk irin diban albarkan da Azizar take mata bata damu,tanajin yar"uwan nata har ranta sabanin ita Azizar datake zaune da Azeemar don bata da yarda zatayi ne,ammah har aranta take jin ta tsaneta batasan dalili ba,kodon hudubar mahaifiyarta akanta ne,ohoabunda kawai tasani bata ma kaunar ganin Azeema cikin Farinciki tafiso ita da uwarta suyi farinciki,itakuma ta dauwama cikin kunci,ayanzu haka shekarun Azeema 20 ayayinda Azeeza take da 15 ammh dayake tana da girman jiki,in akace shekarunta kenan wasu ma basu yarda,dauka suke ita ke gaba da Azeemar.
Ganin gabatowar Biki yasa Aliyu yafara gyaran gidansu,kusan dai Aliyu bawani mai kudi bane,Baya da burin tara arziki,ko yau adinga lbrinsa,amtsayin shi wanine,shidai burinshi ya taimaki kasarsa da lafiyansa da kwazonsa,kodon watarana in ya mutu atuna dashi,yana da Rufin asiri daidai gwargwado,Saboda baidawani dawainiya akansa,goggo ce haryanzu kawu baidaina hidima dasu ba,hatta shi Aliyu,son duk kudadansa,suna kammalle abanki ne,gidan nasu dama dan madaidaicine mai yalwar dan tsakar gida gefe wajen zubda ruwa,sai Famfo,daganan yammah akwai wani daki,ciki daya,nan ne dakin Aliyun,sai daga gabas dakuna guda biyu,daya goggo naciki,daya kuma tana ijiye kayan Abinci da sauran karikice,yana tashi gyaran ya bude dakunan goggo ya hadesu waje daya yayi mata babban falo da Dakuna barci guda biyu da tailot yazubamata kayan more rayuwa sai daga waje yayi musu katon madafin girki,sai barayinsa,dayake buge dakin,yayi ya hade musu Falo da two bedroom da kichen da Bayi,saboda nan zasu fara zama kafin su wuce kaduna,Tsakar gidan ma yasa aka kankare,aka saka interlock,Daga wajen kuma aka fitar da garejin mota,saboda motarsa,baya ma zuwa da ita gomben,saboda ba wajen adanata,yafi hawa motar haya Abunshi,don shifa Babu ruwansa bai dauki Duniya da zafi ba,akayi fenti mai kyau da kayatarwa daga wajenma an gyarashi sosai,tundaga nesa kana hangoshi yana daukan ido..
Tunda biki ya matso yan bani na iya suka damu kwamishina da tsegumin Aliyu,har mgana takai ga kaninshi wanda zai bada Auren Ni"ima,tun kafin Daurin Aure yaso adakatar da mganar,ammh kwamishina yaki yarda saboda yadda mahaifiyar Ni"imar da rike wuta,saboda sanin yadda diyarsu ke mugun Son Aliyu,Ni"ima kuwa tayi rawan kafa,kamar mene,duk da danginta sukaje mata jere,suka dawo suna raina inda Aliyun zai ijeta,harda uwarsa,uwa uba harda anguwan suka raina,sunce ta yaku bayi ce,ma"ana ghetto area ce,Da fari Ni"ima tayima Aliyu mgana,ammh sai ya numata shidin bawani bane,in zata zauna dashi ahaka,Final,in kuma tanaganin tafi karfin nan,To door iz open babu lalle ba dole,shi bazai dau wannan Rainin ba,don baicemata shi wani ne,ba,Shi kawai Sojan Nigeria ne,mai bama kasarsa gudummmuwa.,Dole Ni"ima tai ta bama Aliyu hakuri,domin zaga zaga yayimata,dakyar tashawo kanshi,ya hakura,tasan halinshi sarai baida wasa,shiyasa take kafkafa dashi kada ta balloma kanta Ruwa.
Ranar Daurin aure kiran da Kanin kwamishina yayimai kenan kan su bazasu bada diyarsu,ga wanda baida cikakken Asali ba,Sai yaga Dangin Maihaifinsa,tukunnah inko basu,to sai dai yayi hakuri bazasu basu diyarsu ba,Kwamishina baida yadda zaiyi dashi,dole ya bashi goyon baya,wannan Shine musabbabin Abunda yafaru awajen Daurin Aure,da yadda Daurin Auren yakoma kan AZEEMA, da duk Abubuwan da suka biyo baya...
*Karshen Asalin Tushe*
*Yanzu muka Shiga gabar,ku biyoni don ji yazata kaya gadai gwarzo nan Captain Aliyu Abdulnaseer Tambari buzu,dakuma zaratan matan Azeema,Azeeza,da Ni"imatullah..*
#Comment,share and Vote..# #Janafty...# *ALIYU GADANGA..!* _(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12* _Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘 Ladingo yar Mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*NOT EDITED*💥
*Chapter 6*
Jabir ya dade dakin Goggo suna hira sai wajen 10:00pm na dare,Goggo taga Aliyu baida niyyar bude kofar shashensa,fitowa tayi da kanta ta isa har kofar shashen tahau bugawa tana fadin"Gadanga kazo,ka bude kofarnan.."kazo ka bude nace ko?goggo take fada cikin fada.
Yana kwance akan Daya daga cikin kujerun Falo,inda Allah ya taimakeshi lokaci da"akazo za"a yima Ni"ima jeren kayanta,hanawa yayi,saboda bazama zasuyi anan dinba,cemusu yayi kada su damu,ko gidanshi na cikin barikin akwai komai,so no need su wahalar da kansu,dayake dama already ya rigaya daya gyara barayinsa nasa bayan ya kawatashi dakayan alatun more rayuwa.
Yanajin Buga kofan Goggo,da maganart,ammh yayi mata banza,yana kwance dagashi sai boxers kadai,babu ko riga ajiknsa,gashin kirjinsa yayi kwance luf dashi,Idanunsa suna lumshe ne,ammah ba barci yake ba,Damuwa tareda bakinciki ke mukurkusan shi,shi yanzu bama ta Ni"ima yakeyi ba,ta makomar rayuwarshi yakeyi,"Waye Mahaifinsa?inda gaske Goggo takeyi shi ba shege bane,to ina mahaifinsa da Danginsa suke? Tambayar da haryau bai samu mai amsamai ba.
Goggo jin Shuru ya sata matsa jikin tagan kofan tana fadin"wlh ko kazo ka budemin,ko in kira gardawa suzo su balle kofan,na shigo har cikin naci maka mutumci,tunda kan mace,gadanga zaka dinga min kyaluwa ina mgana.."Tafada tana kwafa,Ajiyar zuciya ya sauke kan ya mike jikinsa asanyaye,bude lumsassun idanunsa yayi,bansan sadda na Furta subhannallah ba,saboda yadda idanunsa,suka chanza launi,sunkoma red sosai,Jikinsa babu kwari yazo ya murza key din kofar ta bude,bai bi takan Goggo da jabir dake tsaye ba,ya juya yakoma cikin falon yazauna kan kujera,yana kauda kansa,Shigowa dakin Goggo tayi tana fadin"Gadanga..Gadanga..Gadanga.."Saunawa na kiraka.."
Ko dagowa baiyi ba,yace cikin husky voice dinsa"Wai ni Goggo don Allah menayi miki ne?kamata fa yayi ki tsausayamin na rasa,love of my life,ammh kinzo sai fada kikemin.."Yafada yana wani kyabe fuska kamar zai yi kuka,Jikin goggo ne yayi sanyi ta karisa gareshi tana fadin"Yo ai kaine gadanga wani lokacin da ban haushi,ai ni na dauka bazaka wani damu ba,duba da yadda mahaifinta ya tozartaku gaban dubban jama"a,wlh indai kana da zuciya bai kamata kaji dacin Abun ba.."tafada tana zama kusa dashi kansa ya dauka ya kwanta bisa cinyarta yana fadin"koma miye,goggo i Love her,duk da Abunda mahaifinta yayi i knowa Ni"ima tana cikin wani hali yanzu cuz she luv me goggo i swear she can do without me.."Yafada yana damke hannun goggon
Dungure masa kai tayi da dayan hannunta tana fadin"Wai ban hanaka min mgana da wannan yaren Nasaran ba,sai na fara cin kaniyarka tukunnah ko"Tafada tana yar dariya,bai tankata ba ganin haka yasa ta hausha shafa kanshi tana fadin"karka damu kanka Kaji,Allah yabaka mace tagari saliha,na tabbatarmaka Azeema zata zemamaka sanyin idaniya nan gaba,mganar mahaifinka kuwa mucigaba da addu"an gadanga inda rabon sake haduwa,Allah zai hada,ammh ina ji ajikina,Abdulnaseer bai mutu ba yana nan Araye,Ammh inda yakene,ban sani ba,Allah shiya barma kansa sani.."Tafada idonta na cikowa da hawaye,mikewa Aliyu yayi yana kallon goggo kan ya saka hannu ya shafa fuskarta yana fadin"To goggo,in bai mutu ba,yana ina,? ko yan"uwanshi ba wanda zaki tuna,ko yataba fadamiki.."Shuru goggo tayi kan ta sauke ajiyar tana fadin"Gaskiya baitaba fadamin ba,sai dai yana yawan Ambatan Agadez domin yacema mallam ko abaya daga yankin ya fito,ammh kasan Agadaz ba karamin gari bane,kuma shekaru sunja,gaskiya mawuyanci Abune,agano wanda ya sanshi sakamakon babu wata shaida da zata bayyana hakan,..,"Tafada muryanta asanyaye."
mirmishin karfin hali yayi yana kallon jabir dake tsaye yana kallonsu cike da tsausayi,kauda kai yayi yana cije lips dinshi ganin haka goggo ta dafa kanshi tana fadin"Aahhh..Haba Aliyu gadanga kusar yaki,Soja mazan fama,ko filin daka asan takunka,makiya da Abokan gabama tsoronka suke,kaga Saurayi na mamanshi uhmm,kaga Ango Azeema ka.."Saurin mikewa yayi yana dariyan Dole jabir ya tayashi,hanyar bedroom dinsa yanufa yana fadin"Sai da safe Goggo,plz go and sleep,nasan kin gaji dayawa.."ya fada yana fadawa bedroom din ransa bace,babu Abunda yabatamai rai sai kiransa da Angon Azeema da goggo tayi,saboda bacin rai kamar ya kunduma zagi,ammh sai ya tuna goggo ce,ita baikamata azageta ba,uwace,uwa kuma tanada matukar muhimmanci,balle tashi data kasance na mussaman ne.
Goggo batai gaddama ba,ta mike tana ma jabir sai da safe,tasan ko banza ya sauko daga muguwar bakar zuciyar da yahau,barayinta takoma tana yan wakewakenta ko ajikinta,domin ita wannan Aure yayimata daidai,sai alokacin ma ta tuna da Azeemar wanda tun da rana tace mata zata gida,tayi wanka ta dawo ammh Shuru bata dawo ba,bata damu ba sanin halin Azeema da rashin son mutane da hayaniya yanzu haka Rashin sakewan yasata kin dawowa,alwala goggo tayi tazo ta kabbarta sallar,bayan ta sallame issha"i tayi shafa"i da Wuturi,bayan nan ta dukufa rokama Aliyu fatan nasarar rayuwa kafin ta gangaro,kan Allah yayima Aurensu da Azeema albaarka tadau tsawon lokaci tana addu'o'i kafin ta kwanta,zuciyarta fess.
Aliyu yana Shiga bedroom dinshi yafada wanka,ya dade aciki bayan ya Dauro alwala ya fito,yana daure da tawul akwankwansonsa,daya kuma yana kansa,yana tsane ruwa da jabir ya cikaro wanda yayi dare dare bisa lafiyayye gadon dayasha wani ubansu bedsheet,kallo daya yayimai ya kauda kai Aransa yana fadin"Dan iska,ba don Tsohon dan Sandan nan,yayimin cikas ba,ai da yanzu nine bisa gado na ina biyan ladan kudina.."Yafada yana wani Runtse ido,kamar yana Kallon Tanadin dayayima yau din.
Gaban Derressing mirrior din dake Dakin ya isa yana kokarin bude wani lotion na kamfanin OLIVE yana shafawa kallonsa Jabir yayi kafin yace"Hy Dude wai duk wannan Shariyan namiye ne? bafa ni bane kwamishina Ahmed Sidi na iya ba,balle ka huce akaina,kuma Dude wlh Seriously Azeemar dakake kumburi don Ka aureta,yasin tafi Ni"imar taka komai,kai infact ma itace matar Rufin asirinka,don ta rufamaka lokacin da Uban Ni"ima ya tona maka,so Ni banga Abunda damuwa in kayi duba da komai MUKADDARI NE.."yafada yana yar dariya,wani kallo Aliyu ya wurgamai ta madubi baice komai ba,ganin haka Jabir yakara cewa"am wlh Dude ta hadakomai dakake bukata wajen mace,i know kaima aikana ganin yarinya,so quiet da ita,gaskiya kana da sa"a Dude.."Wani Takaichi ya kulle Aliyu baisan sadda ya waigo yana fadin"Nagode Shehi jabiru da Tunatarwa,buh juz give me 5 minutes,.."yafada yana jan Side drower din dake gefen gado,ya fiddo da wani Memo da pen,ya yagi daya ya dora zai fara rubutu Jabir ya kallesa yace"Mezakayi..."ko kallonsa baiyi ba,yace"Sakinta zanyi...!kwalalo Ido jabir yayi kan yace"what are u mad.."?ka saketa,kai Dan iska ne..? yafada yana kama baki,wani dirty look Aliyu ya sakarmai kafin yace"yap,yo ai naga kafini bukatarta,Tunda har ka iya kwatanta tana Abun bukata na more rayuwa gata She iz quit ko?sai na sakar maka ita,tun kafin kafara tunanin binta da Aurena akanta.."yafada yana wani hade rai.
Tsaki jabir yaja kan yace"Buraouban ka,banza kawai sakarta manq,wazai hanaka.."yafada yana ballamai harara,dariyan yake Aliyu yayi kan yace"Kai ne Babban Da'n iska,in ba Da'n iska ba,gaban mijin mace ka hau suffanta ta,ai kai ne banza,ajawo gara kawai.."yafada yana wurgamai takardan da pen din afuska yana fadin"Take ur eyes away from my Wife,i Swear zan iya kashe mutum in yakara suffata Iyalina..yafada cikin kakkuasan murya,yana wani buga kafa
Zabura jabir yayi ya duro daga gadon yana fadin"Me kake takama dashi?Kaki? Kai mallam kamar yadda alluran ke yawo ajikinka,haka take yawo ajikina,ko zamu gwada,billahil lazi sai na barar maka da hakoran gaba,karyan zama Shege kake.."yafada yana hararansa fuskarsa ahade,baya Aliyu yaja yana fadin"Ubanka zanji u already know me ko"?yafada yana wucewa jikin wardrope dakin, yana kokarin budewa,da harara jabir ya rakasa yana fadin"wlh an ma Cuci marainiyar Allah,An hadata da Da"n iskan Soja kawai,ai daka tsaya kaga yadda zan sauyama kammanin.."Dariya Aliyu yayi yana fadin"Sai kaje kafadamusu su kwance auren su auramaka tunda kai ba Da'n iska bane,tunda na lura u are jealous,.'ko kallonsa Jabir baiyi ba ya fada Tiolet,yana kunkuni yana fadin zai zane Aliyu da daddaren nan,shiko yana jinsa yamasa banza,sai ma jallabiyansa daya zura ya Shimfida darduma Ya Tada salla,shiko jabir koda ya fito shima Daure da alwal,shima sallar ya tada,kowa yana nashi ko wajen kwanciya sai da suka buga,harda Ture ture agado kamar wasu yara,dat how Captain Aliyu and captain jabir Art when they are together,kuma basu iya rabuwa da juna,ko cikin bariki suna tare,ammh kuma kowanne yanajin kansa awani Shege ne...
********
"Ni"ima kuwa cikin mawuyacin hali aka kaita Asibiti,likitoci suka amsheta da gaggawa zuwa emargency Sun ci bakar wahala kafin su daidaita numfashinta,domin jninta yayi bala"in hawa,ga zuciyarta ta buga sakamakon wani Abu dataji wanda yayi matukar razanata,kuma zuciyarta ta Firgita da Abun,yanzu koma miye,ayi kokarin ganin An magancemata matukar ana son Rayuwarta ta Daidaita.