Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 11

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 11

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 11: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 11. Galala din da ta yi hawayenta bai daina zuba a gurbin idannuwanta ba…

3,332 words

Galala din da ta yi hawayenta bai daina zuba a gurbin idannuwanta ba ya saka shi fadin" kin ga wannan da ya saida maki da kika ce giya, sai da ya maimaita sunnan yana zarro ido yana kallonki, kin san me yasa ya yi haka? Domin da kika zo kin ambaci sunnanta bayan du wanda yake mashayi idan ya zo wajen nan kudinsa kawai yake cakewa mai siyarwar ya san kalar da kudinsa zai siyan masa, yar budurwa baki ga sai da ya yi mamaki ba? Dan ya ga cewar baki saba ba, yau ne zaki fara, shi yasama ya zuba maki kankarar nan dan ya dan rage kaifinta a harshenki, aman ba hakan na nufin kaifin nata zai ragu ba gaskiya domin yau ne zaki fara sha, kuma kin ji na rantse maki idan kika sha wannan giyar gaba dayanta zata kasheki ne, dan babar giya ce mai tsada mai karfi, to ke wai mema akai maki da zafi da zaki fara akidar nan?"

Ita da a hayacinta take, ta tabata wannan bawan Allahn sai ta masa tassss da fitsara, aman a yanzun sai ta samu kanta da rike giyar nan taf a hannunta tana kallonsa ta ce" Ka ga mijina ne ya sakeni, mahaifinsa ne ya ce ban cencenci a hada zuria da ni ba, shine aka sake ni"

Bakinsa ya tabe yana amsar kofin giyar ya ce" Sun yiwa kansu asara ai, a kan ya sake ki ne zaki sha giya? Ko shi kadai ya rage a jinsin maza a duniya? Idan su basa sonki dan wani dalili nasu wani saboda dalilin da suke kinki zai so ki, aman idan kika saka kanki a rayuwa irin ta giya kin san me kika cirarwa kanki? Wahala, yar budurwa kin cirarwa kanki wahala ne, kin ga mu bamu iya abu ba, idan muka fara bamu da hankali, bamu iya yi a kadan kadan ba, zamu yi ta kwabra ne ta yadda zata yi mana ila, kin ga giya anfaninta daya ne tak ko mace biyu shine zata saka fatarki ta yo luwai luwai idan kina shan mai tsada sannan zata saka gashinki ya ringa tohowa sosai idan kina shan mai tsada fa, bayan wannaj dukan wani wulakantarwa na duniya zaki hadu da shi sannan ki je kiyama ki hadu da ubangininki, kin ga tun ina yaro dan shekara goma sha biyar yawo da abokanai na koyi taba giya, maganar da nake maki saboda giya babu abinda ban gani ba na gidan duniya, ni dai ban ajiye nawa ba sai na mahaifiyata da nake gurgura ba dare ba rana, y'ata daya a duniya a makaranta a zageta a cikin kawaye a yi mata gori, ke bara na kadaice maki bani da wata daraja ni na sani dan dole ake cakuluwa da ni..........yanzun ki yanke shawara cikin biyu, Au ki tashi na kaiki gidanku, ko kuma ki fara kashe rayuwarki dan kato ya sake ki"

Ido take kikiftawa tana kallonsa kafin take sake kallon kwalbar da ya ajiye mata a gabanta

Idonta ta rintse da yake ta sarra mata kafin taa mike a hankali tana bude bakinta da kuryarta da ta disashe sosai ta ce" Ka ga banma yi sallah ba kuwa, mu je kawai"

Da kwatance har suka karaso kofar gidansu

Ta jima tana kallon kofar da tunanin Allah ya sa yayarta tana gida

A hankali ta kama kofar ta bude ta zirra kafafuwanta kasa zata fita ta ji yana fadin" Dukan mace ta duniya tana da kima, ko me ta zama a rayuwa kuwa tana da daraja, idan ta hadu da wanda ya san darajarta zata kasance macen da ta fi kowa haskawa a duniya, yar budurwa kar ki manta cewar ko me kika gani na rayuwa ke din halita ce mai daraja,, uwa ce ke, y'a ce ke, kanwa ce ke, yaya ce ke, kin ga abubuwan da yawa , idan ba ke fa Walahi babu rayuwa kwata kwata, kar ki shiga gidanku ki dora kuka , ki je ki godewa Allah, zan dawo gobe in sha Allah"

Tabas ta samu nutsuwa a zuciyarta, tabas koda ace bata dawo normal ba, domin abu ne mai matukar wahala, ita a yanzun ALKALAMIN KADARRARTA ya daina firgitata ya dawo bata tsoro, aman kuma ta ji dama dama a zuciyarta na tunasar da wannan mutumen ya yi mata cewar kai kanta da ta yi gidan giya ba shine mafita a rayuwarta ba

A hankali ta tura ta shiga tana gaishe da baba mai gadi dake morewa da kazar da aka miko masa

Da kallo ya rakata da tarin tambaya a ransa na yannayinta, ko hujab babu a jikinta ba wani mayafi hakan ya sa ya ringa adu'ar Allah ya sa ba sakinta mijinta ya yi ba

A hankali ta kama kofar ta shiga da Salama a bakinta tana waige waige

Yayarta dake zaune tana kwaba lalen da take son kunsawa ta dago da sauri tana sauke dubanta a kanta

Yannayinta ya saka gabanta yankewa ya fadi da karfin gaske har sai da ta zabura tana sakin lallen a kasa tana sake kallon kanwar tata da son mikewa lokaci daya haka kuma bakinta ya kwashi inda inda tana fadin" SHUWWAR, me menene? Ina lulubinki shuwwewwwwwwwwww" maganarta ta katse sakamakon faduwa da ta yi ta dalilin kushin dake ajiye domin idannuwanta sun rufe sam ta kasa ganninsa sai da ta tabeta ya kifar sannan ta ankara

Da sauri SHUWWAR ta idasa isowa tana kamata tana fadin" Subahannalah Aunty Hal anta mash-ghouul?"

Hannunta da ta riketa ta kama tana kallonta ta ce" Na zata ko , ko , na zata ko ya sake ki ne da na ga baki da lulubi bayan matan aure sunna suturta jikinsu ne, kin ga ki ringa saka lulubi dan aure ba abin wasa bane"

Dan murmushi ta yi mai ciwo a hankali ta dora kanta a saman kirjin Nahidt dake yi mata nasiha hakan ya saka Nahidt yin tsiittt lokaci daya kafin a hankali muryarta na rawa ta ce" SHUWWAR me yake faruwa?"

SHUWWAR ta dago tana kallonta , ta maida kanta saman kirjinta a hankali ta ce" Ya sakeni, sai dai shi saki daya ya min, kin ga hakan na nufin ta yiwu idan na kuma yin wani auren zai zaunu"

Wannan karron maimakun zuciyar Shuwwar din ta nemi gazawa ta yar uwarta ce ta nemi gazawa Muryarta a sanyaye ta ce" Shima ya sake ki ne dan an ce ni karuwa ce?"

Ido SHUWWAR ta rintse na kalmar da yayarta ta kirayi kanta a hankali ta girgiza kan nata tana fadin" Aa, bakima shigo cikin maganar ba, kin san me na fahimta.......hasalima ke din kin zamto mahadin Kadarratah ne, aman da ke ko ba ke dole ne rubutacen al'amari zai kasance a kaina, wannan sakin bama dan ke akai min ba, wani soja ne ya saka aka daukomu dan a yi kuraya, a nan dai wa'adin auren nawa ya cika"

Lebenta ta dantse tana son hanna kanta kuka, aman sai da abin ya gagareta ta fashe da kuka tana rike SHUWWAR a jijinta ta ce" Shin mun fi kowa aikata laifi ne da muke fuskantar irin wannan hukuncin a wajen al'uma, menene laifinmu? Me muka yi da zafi haka?, SHUWWAR I'm sorry, I'm sorry dear"

SHUWWAR ta karra kwontar da kanta a sanyaye ta ce" Haka nawa ALKALAMIN KADARRAR yake, Aunty ina tunanin bani da rabon yin aure a duniya"

Wanu kukan NAHIDT ta fashe da shi wanda ya fitar da Zahra'u dake kicin tana soya masu zabuwa da sauri tana fadin" Kamar kuka nake ji NAHIDT"

Jikinta ne ya yi wani irin mutuwa tunda ta ga SHUWWAR rungume a jikin NAHIDT din

Tunda Shuwwar ke koke kokenta idan an saketa bata taba jin tana zubar da hawaye irin na yau ba, A yau itama da kanta ciwon sakin Shuwwar din ne yaa ringa sukanta a kirjinta har ta kasa tsayuwa a kan kafafuwanta ta karasa da sauri tana dukawa a kusa da su ta rungume su gaba dayansu a jikinta

Kukansu suka sha su su uku NAHIDT dake kuka tana fadin" Shikenan dan bamu da kowa sai a ringa wulakantamu?, Shi yasa ban sakawa kaina soyayar na yi aure a zuciyata, domin na rigaya na sani cewar babu wanda zai iya jin kaina, babu wanda zai aureni ya zauna da ji domin Allah, ya zamana dan iskama ta kirki yake so mai fitacen usuli, kowa idan ya tashi ta kirki yake so ido rufe, mu kuma da muka kasance a haka ba sai mu karre a haka ba?, Aman SHUWWAR bata cencenci haka ba, Shuwwar ya cencenci ta samu gida ta zauna da mijinta, bata takawa kowa ba, bata kashewa kowa ba, idan takamar mazajen dake sakinta dan ina fita ina harkar badala ina samun naa abincina ne daga yau na daina, walahi na daina, su aureta su kilace min ita dan Allah ba dan halina ba"

A sanyaye SHUWWAR ta sake riketa a jikinta tana fadin" Da ace zasu dube mu bayan mun tuba su dauke mu ba dan su ringa goranta mana ba, su kula da mu domun Allah, aman kin ga Aunty, ko sun aure mun dan su wulakantamu ne, kina gani fa irin soyayar da yake nuna min aman ana kaini ko kallo ban ishe shi ba, yakan shiga ya fita aman banda dakina"

NAHIDT tana kallonta ta ce" kina nufin har yau da ya sake ki babu abinda ya shiga tsakaninki da shi?"

A hankali SHUWWAR ta sada kanta tana jin nauyin irin maganar nan ainun

Fauziya da ta kasance mai sanyin cikinsu aman yau itace da fadin" Dama tun usil bai mana ba, bakya gannin kama yake da munafukai? Fin karfinmu kika yi, a yanzu da ya kasance bai taba ki ba Alhmdulilah, matsiyaci algungumi kuma walahi sai mun kwaso kayanmu harda akwatunnanki!"

Ita kam so take ta kwonta ta huta dan kanta ciwo yake yi mata, dan haka ta nemi da su sama mata wajen kwonciya so take ta kwonta

A wannan daren ta samu soyaya a wajen yan uwanta taamkar zasu maida ita cikin cikinsu, domin a shinfida daya suka kwana gaba dayansu har akai kiran sallar asubah

Abin mamaki su dukansu kiran sallar ne ya tashe su suka kuma gabatar da sallarsu a kan lokaci, a nan Fauziya ta shiga kwashe shinfidar da sukai a falo suka kwana tana mayarwa ciki sannan ta shiga gyagyara gidan itaa kuma SHUWWAR ta koma dakinta ta kwonta dan barcin ba wani isarta ya yi ba

Lalabawa NAHIDT ta yi ta dauko wayarta ta koma saman kujera ta mikar da kaffafuwanta ta dan ringesa ta shiga jerin sunna mai farawa da A

A hankali take yin kasa har ta zo daidai sunnan da aka saka ABAN IBTI

Sunnan ta ringa kallo tana ta tunanin abinda ya dace ta makawa wannan bawan Allahn da a nan ta fada, a tsaye ta fada, a zaune ta fada ta hanna shi daurawa IBTISAM auren nan aman sai da ya aikata

Rubutawa ta fara rai bace kamar haka" Asalamu alaikum, ba zan tambayeka ka tashi lafia baa tunda bani da matsala da haka, Liman an sakota a karro na hudu ba tare da takamaiman dalilin da ya wuce ana gudun auren irinmu, wai ina da tambaya, dama musulman haka suke ne? Ko dan mai jin kan musulmai mai adalci ya shude zamani sai tarihinsa muka tarar? Allah ya tsinewa masu halaya irin na wasu daga cikin musulman, na fada na karra Aban IBTI! Ka sani ba zaka kuma daura mata kowa a matsayin miji ba, abinda ta samu na ciwon zuciya ya isa haka!"

Tana turawa ta kashe wayarta ta gyara kwonciyarta itama domin yau ba gyaranta bane na Fauziya ne yin safe

_____________________________________

Cikin barcinta ta ringa jin magana sama sama hakan ya sakata farkawa a dan tsorace tana diro santa santalan fararan kafafuwanta kasa hadi da kai dubanta saman agogon dakin nata

Idannuwanta ta dan fitar na mamakin gannin lokacin da ta dauka tana barci haka kuma ta sake kai dubanta wajen kofar sakamakon jin muryar namiji yana daria , sai muryar NAHIDT da ta Fauziya

Takalminta na wanka ta janyo dan abin dake kusa da gadonta ta cire kafa ciki mai laushi mai gashishika ta saka kafafuwanta ciki sannan ta mike a hankali tana cire doguwar rigar da ta kwana da ita dan wahala ta fitar gaba daya

Farin pant ne a jikinta, irin fari kal din nan sai jigidar dake jikin kugunta mai ruwan fari daa ratsin blue kwatankwacin sararin samaniya da hasken ruwan teku Jigidar a jikinta take irin ta yi daf a jikin kugunta sai biyu da suka sauko saman fafadan duwawunta wa'inda ga dukan alamu tsarinsu ne ya zo a haka domin daya na bin daya ne sukai sannan a daune suke dasss a jikin nata

Santala santalan cinyoyinta da basa dauke da gargasa sakamakon anfani da ALAWA ta fitar da gashin jiki da suke yi dan gyaran jikinsu, Tsananin kula da fatarta da take yi kuma ya saka har daukaan ido cinyoyin nata suke da bayanta da shafafen cikinta

A hankali ta duka ta cire sarkar kafarta yar siririya ta azurfa wace ta siyeta daga saudiya ta hanyar wata dake cen aka sako mata a cikin kayan gwonjo da wani Elhaji ke siyarwa da aka kawo aka bata

Nan ta ajiye sarkar ta bude sif dinta tana duba wajen da take da tabacin ba zata rasa tawul ba Ai kam ta samu wankaku a jere a kilace hakan ya sa ta dauki daya mai ruwan blu ta daura a kirjinta sannan ta ja pant dinta ta cire ta nufi bayi da shi a hannunta dan wanke shi

Ta dan jima a ciki domin sai da ta gama dukan uzurinta ta dauro alwallah ta fito tana tsane ruwan gashin kanta sakamakon wanke shi da ta yi

Sasaukar sutura ta saka tana daukan abin cire datin kunne da kumb ta fito dan jin muryar nan na karra fitowa a falonsu

Turus ta yi sakamakon mutumen da ta gani zaune a saman kujerra dare dare abinsa tamkar wanda ya zo gidansu

Da mamaki take sake kallonsa da yan uwanta daje zaune sunna ta maida zance sunna dariya

A birkice ta sake dubansa ta ce"

I'm sorry🥰🥰🥰, yau du ban zauna ba litinin🥰🥰🥰💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣3️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Tana kallonsa da expression na mamakin ganninsa a irin wannan lokacin a cikin falonsu haka ta ce" You?"

Kure shin da ta yi da ido ya saka shi sakar mata lalausan murmushi yana fadin" Morning princess"

Juyowa NAHIDT dake cire safa ta yi tana fadin" Oh my baby ta farka? Zo zo zo nan"

SHUWWAR ta kasa daga koda kafarta daya ce bale ta je din da suke fadi har sai da Fauziya ta fito da plat mai dauke da dankalin turawa a soye da ta soyawa mutumen ta karaso tana ajiyewa ta ce" Shuwwa kin farka? Zo ki karya mutuniyar ta gasa maki"

SHUWWAR dake kallonsu da mamaki ta ce" Dama kun san wannan mutumen ne?......" Ta juya tana kallonsa ta ce" Dama ka san yayuna ne?"

NAHIDT ta ce" ke wani irin dama ya sanmu? Dazu ne mun fito zamu je gidan su Sudais muka same shi a kofar gida, yake cewa jiya shi ya kawo ki, ya ce yana son ganninki dan jiya ya barki hankalinki tashe, na takaice maki dai ai da shi muka je gidan su SUDAIS , baki ga abinda Sudais ya so yi mana ba da ya ga Hamza, kiri kiri ya so kirta mana rashin mutunci bayan ya bamu akwatunnan da wata mata ke ta fadin a kan me zai bamu akwatunna ai bata ci akwatunna ba , ko sadakinsa ya ci mu maida masa in ji ita matar, shi kuma ya ce kennan dama jira muke ya sake ki shine muka zo masa da wanda ya mayr gurbinsa ya nuna masa shi wani ne a kasar nan? Dadin abin babu Wanda bai san waye Hamza giya ba, kin ga shirmen d'an adan ko? Sai ya fake da guzuma ya harbi karsana, shi a nan a tunaninsa wulakanta Hamza ya yi da laifin n da Hamzan ke aikatawa a yanzu, dan Adam kan mance laifin wani na yanzu na iya zamaa naka na gaba, shi kuma ka ga ya daina komai ya shiryu tamkar ba shi ba, wa ya ga SUDAIS na tatular giya????????????"

Fauziya ce kawai da ita NAHIDT din suka sheke da dariya banda SHUWWAR dake tsaye a labarin da suka bayar bata ga daya da zai iya sakata dariya ba, uwa uba a barcin safen nan da ta yi har suka je suka aiwatar da aikin nan banda ita suka amso mata hakkinta banda ita?, To shi kuma wannan din waye shi ne? Ba taimako bane? Ai ya yi ya gama me kuma ya zo yi nan?"

Hamza na kallonta ya ce" yar budurwa zo nan ki zauna mana"

Wajen da ya nuna ta bi da kallo, sannan ta sake binsa da kallo

Tsayuwarta ta gyara ta budi baki zata yi magana Baba Mai gadi ya yi salama A nutse ya ce" Hajia Man Liman ne ke salama"

Sai da gaban Nahidt ya fadi, domin ta tabata zuwan nan da Liman zai yi harda tafiyarta tata ta ita kanta, tana kallon wajen da baba yake ta ce" Baba ce nai masa bama nan"

Fauziya ta kalleta tana fadin" Aa baba muna nan"

Ita da kanta Shuwwar sai ta rasa shin tana so Abanta ya shigo yanzu kuwa ko bata shirya fuskantarsa ba?

Shi dai Baba komawa ya yi ya sanar da Malan cewar sunna ciki yana iya shiga

Readers Also Read