Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 27
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 27: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 27. Shuwwar ta dakata tana cire safar hannunta da ta saka take faman aiki…
3,259 words
Shuwwar ta dakata tana cire safar hannunta da ta saka take faman aiki a kusa da tukwane ta dauki tissu ta share dan gumin da ta tarra tana kallon kicin din da tunanin wai ina hanyar da iska ke dan fita ko shigowa ta dubi auntynta ta ce" Mah, wahala ce fa muke yi, domin a tsamtsamce yake da abinda zai kai bakinsa"
Da dan mamaki take kallonta ta ce" A tsamtsamce kika ce?, Yaya aka yi kika sani?"
Shuwwa ta watsa hannayenta tana kallon yamboll din da NAHIDT ta sakata dakawa dan fitina ta ce" domin jiyama na yi girki a gidan nan, kuma bai taba komai ba, daidai da liptona dinsa sai da ya tarda ni dakina ya sakani sha sannan ya tafi da shi, na tabata ritsani ya yi dan ya ga idan zan iya sha ne ko me........, Ina tsoron ko yana tare da tsoron cin abincin kowa a rayuwarsa "
Nahidt ta dan kura mata ido na dan lokaci sai kuma ta saka yar dariya tana fadin" Kin san me ya fado min a rai? Marin da kika sha a lokacin da kika ajiye abincin Rislane ya zo taba maki nono kika kiya uwarsa ji take abincin ne kika ki ci ta wanka maki mari, kai a ranar kin daku shuwwa"
Shuwarma ta saka yar dariya tana zarro idannuwanta ta nunota da hannunta ta ce" Kema ai kin dakun kin manta da kika cewa uwar jaka kema ta wanka maki mari? Aman mun masu tsiya kai da bamu bato saudiya ba sanadiyar kayar da uwar nan da muka yi da sai an yanke mana kai a tsakiyar gari dan a kiyaye gaba"
Yar dariyar raha suka yi tuna ranar da sukai gudun ceton rai, Daga bisani Nahidt ta dubeta da kyau ta ce" ribar aikatau din da muka yi menene Shuwwa?"
Shuwwar dake zaune saman yar karamar kujera ta dan sake kura mata ido tana kallonta aman ta ki ta ce da ita komai, hakan ya sa ta sake sakin murmushi ta ce" Ribarsa shine, naci wa farin cikin uban gidanmu, girkawa ba tare da tunanin za'a taba ko dan tsakure ba, girki da soyayar abinda muke dafawa...........Shuwwa karasa min mana?"
Shuwwar ta lumshe idannuwanta tana tuna rayuwarsu a sanyaye ta ce" naci da maimaici a kan lokaci, tsafta da kwanoni masu fuzgar maganadisun kwalon idannu, kula, hankalta da yannayin wanda ya ajiyemu, shi abu mai daraja shi yake janyowa kansa daraja ne"
Dan murmushi Nahidt ta yi a sanyaye ta ce" Ba lallene ace dan ya ki ci ko dan ya saka ki sha yana tare da tsatsamcin cin abinci, ta yiwu damuwarsa ta tsafta ce, ta yiwu a matsayinsa na baba ba lallene kai tsaye ya aminta da girkin macen da ta shigo da niyar zaman aure da shi ba, dole yana da bukatar yarda da ita, yana da bukatar gane hannunta, idan har ya sha Lipton dinki na jiya zan iya ce maki yana da kyautata zato a gareki, ko kuma akoy abinda ya tabatar masa cewa har yanzu baki fara kauce hanyar da zaki nemi ransa ba, Shuwwa yaya aurenku ya kasance? Kai tsaye fa aka sarka ku, me yasa aka maku irin sarkawar nan? Wanda ya sarka din shine barazana wa nutsuwar d'ansa? Ko kuma ke din nan kece barazana wa tunaninsa?"
Shuwwa dake mayar da safunnan hannayenta ta juya wajen aikinta a hankali ta ce" Nama fi zargin cewa kamar nice barazana wa nutsuwarasa, domin na kula da kallo irin na kiyaye , irin na gociya, ko nace irin na tsatsani da mutun din nan da yake min da zarar na matse masa waje Tabas , na shi tunani a kan sake saken matayensa, sai na ji ina so na san a kan wani dalili yake sakinsu shi kuma? Ba wai dan ni na zauna da shi ba, lalallaa nakan yi sha'awar talafawa mutun , bale shi din nan kin san kama da me yake min?"
NAHIDT ta girgiza kai tana kallonta
SHUWWA ta ce" kama yake min da dan jariri irin lukutayen nan mararsa hakurin nan......, Oh my god idan ya harzuka wollah hanyar da zan shige nake nema"
Nahidt ta kilkile da dariya tana nunota da yatsa ta ce" Nice kat, du iskancinki SHUWWA na ga an riko damatsunnanki sai na koma na rufe daki na shiga tayaki da adu'ar kar ya karya ki, kai aman Shuwwa mijinta duniya ne, kin ga damatsunnan kuwa?"
SHUWWAR ta yatsina baki ta ki ta baya amsa domin ita abinda Nahidt ke fadi din ta gama ganota dan ta saka mata ra'ayin mutumen nan ne, so take ta sakata ta kamu da soyayar mutumen da shi da kansa ba wani son kansa yake yi ba?, Yaya zasu kwasheta kennan? Ta katashe rayuwarta a birkice ko?
Nahidt ta shiga ciro manyan kuloli tana son zaban wa'inda zasu zuba abincin tana fadin" Ki iyakance kowace yar aiki da kama maki girki, wannan aikin bai kai rabin wanda kike yi kika saba yi ba, kar ki dorawa kanki cewar sai kin yi abinci kala uku, biyu, ko hudu, ki gyara takardar girkinki ki ringa yin daya kwakwaran da idan aka ci an san an ci girki mai dandano, ki sani ko LIEUTENANT GANARAL ne shi, yana so ya ringa gannin ana tatala masa, namiji na so ya ga an san ciwonsa, ba kawai da ya bude a kwashe a zubar ba, na fi ganewa ki ringa yin kalolin juss kina shake frij dinki da su , da dan abin marmari su cak ne, su biscui ne, su soye soyenmu na mata ne masu dandano kina ajiye as idan an gama cin mai nauyi a dan yi kallin TV ana dan lalube lalube ana dan tsakura, harkar zata fi tafiya daidai!"
SHUWWA ta dafe kanta ta juyo tana kallonta, a hankali ta furta" Ba sauki a lamuranki NAHIDT sai na Allah"
Da haka suka yi aikace aikacensu, sunna yi Shuwwar na leka yan falo, tana gamsuwa da aikinsu, sunna gamawa ta salame su ta koma wajen yar uwarta suka yi komai suka gama
Babu yadda SHUWWAR bata yi ba kan Nahidt ta bita dakinta su shirya ta ce ba da ita ba, ta mata rakiyar amarya daga shi idan ta ganta a dakinta to fa haihuwa ta yi, Wannan takaicin ta shaka ta yi tafiyarta ciki ba tare da ta tankata ba domin ta kula so take su raba hali ne Kafin ta je nata dakin sai da ta fara shiga nasa ta sake tatare gajeran wandonsa tana fadin" sangarta bata da kyau, kai ba zakana boye dan ciki ba salon a dauka ka nuna kamar an ganka a zirrr ne? To Allah ya taroka soja!"
A nutse ta yi wankanta, da su shiga ruwan dumi da zama, da su anfani da ruwan wanka, da komai da komai sannan ta fito ta shiga mulke jikinta da hadin humurarta mai mai a ciki wada suka hada suka raba gida uku su uku A nutse ta ciro bra da pant a cikin saitin kayan mijinta na biyu tana kallon su domin shi dan kasuwa ne dake odern kaya waje yan kasuwa na siya a wajensa, hakan ya sa ya ringa lodo mata yan kasa da kasa masu daraja da kyau da tsari, Dan murmushi ta yi tana ciro doguwar gown a cikin akwatin dogayen rigunanta mai ruwan ash da duwatsu a gaban Dora su ta yi saman turaren wutar da ta zuba ta ci gaba da gyaran jikinta zuwa gashin kanta Sai da ta gama sannan ta shirya ta dauki san kwalin da yar siririyar agogonta ta daura a hannunta ta nufi waje a nutse ta sauko kasa a lokacin karfe takwas na dare ne hakan ya sa tana idasa saukowa ta shiga neman Nahidt, aman bata ganta ba
Ta juya da niyar nufar dakinta aka bude falon aka shigo Shirun da ya dauki wajen bayan ta rintse idannuwanta gammm tana tuna yadda suka rabu dazun sannan tana jin kamar kallonta ake yi ya sakata juyowa a hankali gabanta na dan dokawa sukai ido hudu da junna
A tsaye yake kikam ya cire hular dake kansa, sansanyan kanshin falon da tsaftarsa sun kara haifar masa da lumshe idannuwa a kan yinwar da ta ciyo shi wadda ya dawo da ita daga office ga kuma gajiya Yawun bakinta ta hadiye da kyar tana cire idannuwanta a kansa a kasan zuciyarta tana fadin' idan kika yarda kika ringa guduwa da zarar kin ganshi kin shiga uku, zaku kula saka ne ta yadda zai zamto tautau da kuda ke da shi, ke maza je ta gabansa nuna masa kema fa jaruma ce!'
Kirjinta na dokawa da komai ta ringa taka kafafuwanta masu dauke da jan lalle ta wuce da sando tana dauke numfashi ta nufi wajen diner Ta tabata bashi da kunyar kallo ita kuma tana son isar masa da wani sako ta haka, hakan ya sa a hankali ta bude kular abincin da suka dafa a sanyaye ta ciro cokali ta saka cikin abincin dake wasar wasar ta juya alamun cakudewa take yi sannan ta dauki guda ta dan juyo irin idan kana son yiwa yaro rowar nan ta ciro harshenta mai laushi da color din jarirai ta lashe lebenta na sama kadan ta karashe da cije na kasan gefe guda, sannan ta kanne ido daya tana kallon gefe kadan aman face dinta gaba daya a barinsa take wace ta tabata in dai yana tsayen har yanzu to fa ita yake kallo ko dan ya samu na cin zalin! A hankali ta saka yambos din a bakinta ta datsa ta gutsura ta lumshe idannuwanta daga cikin makogwaronta ta shiga dan gurnanin fadin" Ummmmmmmmmmmmmmm,awnnnnnnnnn,ayneeeeeeeeeeeeee so, so , so dadiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiihhhhhhhhhhhhhhhhhhhhu i swear😌😌😌😌😌😌"
Idannuwansa ya cire da sauri daga kanta ya juya ya shiga haurawa da uku uku yana wani irin saurin da ya sakata bin bayansa da kallo
Ajiyar Zuciya ce ta kwace mata a hankali ta ajiye ta sha ruwa ta rufe ta juya ta nufi dakin yayarta jikinta tamkar an zare mata lakah
Dakin ta kama ta murda ta shige, tana shiga ta hangota saman salaya tana jan carbi, saman makeken bed dinta kuwa wayarta sai harke take da alama kiranta ake yi
Wajen wayar ta nufa tana karra karewa dakin kallo da mamakin tsaruwarsa da dankareren bed din dake cikinsa
Wayar ta dauko tana dubawa Gannin Aban shuwwa ya sakata dan yin tsam kafin ta daga ta koma saman kujerar dake kusa da Nahidt din ta amsa salamarsa a nutse ta furta" Abana barka da dare"
Da sauri NAHIDT ta ringa idasa jan carbinta ta daga hannu bata yo roko ba ta ce" Allaah ka gyara komai Alalh fatiha" ta taso da sauri ta zauna kusa da Shuwwar tana kallon wayar
A nutse ya ce" Y'ar gidan Aba ,ina yayar taki take ne?"
Nahidt ta mata nunin cewa ta ce bata nan Shuwwar ta tabe baki ta ce" Abana ta ce na ce bata nan"
Nahidt ta zarro ido tana kallonta, shi kuma ya yi dan murmushi yana fadin" Yanzu Nahi abinda kika yi hankali ne ko aikin da ba na hankali bane tarewa a gidan kanwarki?"
Nahidt ta tabe baki a sanyaye ta ce" Ai dama na san haka zaka ce, shi yasa da na zo na tambayi mijin wai idan na kwana a nan za'a ce na yi aikin hauka ne?, Sai yace min wannan shirmen hausawa ne harma ya bani takardar da ko dare na yi ni yar gida ce ba bakuwa ba, Alhmdulilah da kanwata a gari ba zan ringa rabe rabe ba, ko ka ake na je gidan Malan mai matar so?"
Malan ya yi shiru a hankali ya ce" Amshi wayar " Wayar ta kalla ta kalli Shuwwar, ta amsa ta mike hakan ya sa Shuwwar dirowa tana zuwa ta karra kunnenta tana sauraro
A hankali ya ce" Kin amsa?"
Ta tabe baki ta ce" eh na amsa"
"NAHIDT, tsakani da Allah da annabi yanzun menene a cikin nan na bacin ran da zai saka ki yi tafiyarki mu yi ta nema? Yayanki gayanan bai koma gidansa ba shi da matarsa har yanzun so suke su ji daga gareki domin ya je barikin an hannashi shiga ai basu sanshi ba, Nahidt menene a ciki dan Furera ta amshi wayata? Kema kin san ba zan kyaleta ba bayan magangannun da ta fada ai ba kyau "
Nahidt ta yatsina bakinta ta ce" Ka ga dai kawai idan dan ka ce wannan ne ka kashe, meye zaka ce mata da ya wuce ka lalasheta an kira mata miji tsakiyar dare ko? Wai nice karuwa? Malan na taba nuna maka hali ne fisabililahi ?"
Kallonsa ya kai kan Hamza dake zaune yana sauraro, tsam ya mike ya fice a dakin hakan ya saka Hamza yin murmushi yana girgiza kansa kasa kasa ya furta" Allah na gode maka, Allah ka yafewa marainiyarka"
Malan na fita ya ce" Ke, idan kina magana ki daina irin wannan da ni na fada maki, kuma da kika ce haka ni da na san lafiyarki kalau ai ba zan daga ba, ai ba adalci bane da ace y'ata ce ta kireni tsakiyar dare sai na daga kaina tsaye ,aman ke kin san mata da shirme da hade hade ko? Ta ga damar ta yi mana wata fasarar daban ko? NAHIDT to yaya kike so na yi akoy fa haki a ciki wanda Allah ke iya kamani da shi a bayane ke kin sani ko?"
Nahidt ta ce" kar ka damu , ka yi hakuri ni bama zan kuma kiranka ba"
Malan ya yi dan tsai a hankali ya ce" Ni ai zan kireki kulun kulun "
NAHIDT ta ce" Bana so Muhamad, bana so dan Allah"
Malan ya ce" Nahidt ni ina so, kuma babu yadda na iya sai na yi, dan Allah Nahidt na tambayeki mana?
Nahidt ta gyada kanta bata ce komai ba domin jikinta gaba daya ya mutu murus ne sai Shuwwar ce ta ce" Um"
Ya ce" Dan Allah da kika fito daga gidan yayan ina kika je? Daga cen kika je ina?"
Nahidt ta bude idannuwanta ta sauke a kan fuskar Shuwwar da itama ita take kallo, a sanyaye ta ce" Daga cen gidan Shuwwa na zo Muhammad"
Ajiyar zuciyar da harta Shuwwar sai da ta ji ce ya sauke a sanyaye ya furta" Allah ya miki albarka, ya karra kiyayeki da ke da kuluhin musulmi"
Kasa amsawa ta yi, domin ta gane samun relief dinsa na jin bata je yawon banza bane, gaba daya sai ta ji gwuiwoyinta sun mata nauyi, hakan ya sa ta lumshe idannuwanta tana sauraronsa a hankali ya ce" Ki dawo kusa da ni "
SHUWWAR ta zarro Idannuwanta tana kallon yayar tata, sannan ta maida dubanta wajen wayar da sauri ta saka hannunta ta katse kiran kafin ta fasa ihun da ya zo mata tana kallin Nahidt ta ce" Tun yaushe, tun yaushe aka fara irin haka da ubana ake son munafurtata, a fasara min tun yaushe ?"
Nahidt ta lumshe idannuwanta hawayen dake ciki suka samu damar zuba a hankali ta rungume jikin Shuwwa muryarta na rawa ta ce" Shuwwa?"
Shuwwar ta lumshe nata idannuwan itama tana sauraronta Nahidt ta ce" Shuwwa babu abinda kike tunani, babu ko daya shuwa, wulakanci ne irin na Abanki shuwa, so yake ya idasa kasara min dukan wani kuzarina Shuwwa bayan ya san shi bai nuna haka ba, hasalima ba zaya iya ba, shuwwa na shiga uku na cuci rayuwata....." Ta fashe da kukan da ya saka shuwwa lumshe idannuwanta tana dan taping din bayanta a hankali ta jata kusan gado ta zaunar da ita Kasa ta Duka saman kafafuwanta ta dora kanta a saman cinyarta tana lumshe idannuwanta ta ce" Astagfrullah wa atubu ilaik, Astgfrullah wa atubu alaiki"...........
Nahidt ta lumshe idannuwanta tana dora hannunta saman na Shuwwar din bata iya cea komai ba
A hankaki Shuwwar ta ce" Kin yi laifi, Domin ba zan ce maki mema kika yi ba bayan kin aikata laifi mai muni a wajen ubangijinki, sasaucina daya ne kina son gyarawa, kuma Allah kuwa gafurun rahim ne ai , Nahidt ki so shi idan kina son Abana, ki so abinki Nahidt, Abana mutun ne mai daraja, mau mutunci Nahidt ke kin san uban marayu ne, a kalaman Abana na gane yana cikin halin muradinki yana shayin furta maki, Nahidt ki karra matse masa lamba har ya fada da kansa sannan ya wahalta kafin ya samu....."
"Shuwwa matansa?, Anguwarsa?, Mutanen dake zagaye da shi? " Nahidt ta fada muryarta na rawa rawa
Shuwwa ta ce" Mu hada su da Allah, wanda yai mana gori shi da Allah, wanda ya zagemu dan kadararmu shi da Allah, wanda kuma ya ce a fili zai yi fito na fito wannanma dan ka kare kanka ai ba laifi, bana tunanin Furera zata kayar maki da gaba, aunty kuwa dama inaga yanzun ta gane hanya Nahidt"
Nahidt ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallon yadda kiran ke ta karra shigowa, tana so ta je da gudu ta daga ko dan ta ji muryarsa sai dai ba zata daga din ba, ba zata daga ba ko daya zata yi hakurin kamar yadda Shuwwa ta ce, itama ta jure a ja abanta bale ita?
Wayar tafi da gidanka dake kuka ya saka Shuwwar mikewa da mamakin wa ke kira dakin NAHIDT ?
Dagawa taa yi ta yi shiru bata ce komai ba
Sai da ya ja numfashi kadan cen kasa ya ce" wa zai yi servg dina?"
SHUWWA ta zarro ido tana ciro abin a kunnenta, sai kuma ta maida da sauri jin kamar ya sake daukan wata maganar A hade ya kuma fadin" Nd Nahidht ta fito fr eat"
Daga haka ya katse kiran da ya sa Shuwwa yin mutuwar tsaye
Kai ta girgiza ta ce" Na rantse tarko ne, kai, walahi tarko ne babu inda zamu tafi"
Nahidt ta tsatsareta da ido tanai maya kallon tuhuma ta ce"💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 2️⃣9️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*Alhmdulilah mun watse taro lafiya, na gode sosai da adu'o'inku*
Da kallon tuhuma ta ce" Me kikai masa ne Shuwwa?"
Ido ta dan zarro ta ce" Me kuwa zan yi masa aunty?, Kin ga ni babu abinda na yi masa kawai dai na san shi din mugu ne kuma na san idan muka fita falon cen babu abinda ba zai faru da mu ba"