Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 38
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 38: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 38. A hankali ya bi hamatarta da kallo wace ya yi mamakin ganninta sumul…
3,320 words
A hankali ya bi hamatarta da kallo wace ya yi mamakin ganninta sumul kakal ba dis din gashi sannan ba alamun dati a tatare da ita, sumul din wajen abin sha'awa kamar ba hamata ba da kuma kirjinta da ta bankaro dan yin hamarta mai ma'ana ( Maganin bakin kasan hamata, wani lokacin zamu ga mutun ko fari ne hamatarsa tana da dan duhu, idan kuwa yana kwaikwaita kwaikin hamatar tana da baki marar kyau, idan kuma shi din baki ne wahen hamatar yakan fita daban sosai, idan aka taki rashin sa'a mai gidansa ba abinda ke haukata shi irin ya ringa gannin uwar gida na mika ai ba dadi ka ringa daga hannaye hamata na neman saka amai koda bata hamami, maganin wannan da shi da bakin raba rabar kafafuwa, watau cinyoyi wajen dake haduwa shine BICARBONATE, zan hada posting din da hoton nawa Bicarbonate din, zakina yanka lemun tsami ki dan zuba garin bicarbonate kadan sai ki shiga darza a hankali a hankali, ba tashi daya ko yi uku zai cire maki abin nan, idan kikai naci zaki ga kyakyawan result , bashi da effet secondaire in sha Allah)
A hankali ya kawar da idannuwansa a kan hakan yana girgiza kansa ya mike ya koma saman kujerar dake facin din wajen da take zaune ya zauna har sai da ta gama ta diro kafafuwanta kasa tana dan murmushi ta yi zama irin na turi barotao, watau ta wara kafafuwanta ta girka duwawunta ta gantsare kugunta hakan ya bada wata kala ta neman fitina ta dan sake yin murmushi ta shiga ci gaba da aikin tana fadin" bari dai na gama aikin nan kar kilu ta janyo mini bam gani yar marainiya da wahala ake samun masu jin kan marayu a kasar nan"
Kansa ya maido kanta bayan ta karashe maganarta ya zubawa zamanta da aikin dakan da ta fara yi masa ido yana kallonta
Kai ya dan girgiza kasa kasa ya ce" Dakata "
Tana dakan ta dago tana kallonsa hadi da dan dage gira daya ta dan kuga tama fadin" Ka ce?"
Ikon Allah, shi kawai ya tsaya kallo idannuwansa cikin nata, a hankali kuma sai ta fara rage karan dakan harma ta tsayar tana gyada kanta ta ce" Da a layin gidanmu ka taso saudiya ban san yaya zaka kare da ciwon kan hayaniya ba, mu fa a cen idan ba'a tashi da hayaniya ba kowa fara shan jinnin jikinsa yake yi, gaskiya hayaniya ai rayuwa ce, yalabai aman baka taba harba bindiga ba kau?"
Shi kam ta daina bashi mamaki yanzun, ya riga ya san mai iskokai dole za'a samu irin halayan nan a tatare da shi Hakan ya sa bai ba abin damuwa mai yawa ba ya ce" da me kika je kasuwa?"
Dan yin tsai ta yi tana kallonsa , sai kuma ta kalli jikinta ta ce" Au, da hijab din mama ne"
Bakinsa ya tabe ya mike ya juya ya yi tafiyarsa a falon ya koma bangarensa Summa dare suka cika kafin su nemi wajen kwonciya
A lokacin da Mama take ta sinsinar hannayenta tana mai jin farin cikin yau itace zata koyi yadda ake yin turaran wuta ta ce" Kennan mahaifiyarku ke yin na siyarwa?"
IBTISAM ta kalleta, sai ta yi murmushi tana dan girgiza kanta ta ce" Na turara dakinmu ne take yi, Abanmu ya hannata siyar da turaran wuta...... "
Nahidt ta yi yar dariya itama tana cewa" Mama ai ko cimar larabawa da take yi na amare idan zasu yi taro ana biyanta baya so, ya fi so ya fita ya nema"
Mama dake hankalce da yannayinsu na sun shiga a yannayi na bege da kuma missing din iyayensu ta furta" Allah ya sa sun huta "
Shuwwa ta kalleta da yannayi na abinda take ji daga zuciyarta ta ce" Bamu ga gawarsu ba fa, sannan bamu ga kabarinsu ba, kabarin da ta nuna mana ba nasu bane, ba nasu bane"
Nahidt ta mintsineta tana girgiza mata kai dan ta ankarar da ita a gaban wa take son fara gardamar tata ta mahaifansu basu rasu ba, ta maida harshenta yaren buzanci ta ce" ki farka a gaban sarakuwarki kike!, Ki daina wannan abin naki, IBTISAM da basu rasu ba kina tunanin akoy abinda zai hanna su neman mu ne?, Da sunna yare kina tunanin kulafurcin soyayar da Abanmu ke mana zai iya zama dukan lokacin nan bai neme mu bane? Sai kin mutu kin je kiyama zaki yarda sun jima da barin duniya ne?, Ya RAB kar ki yi ta fara tunanin mahaukaciya ce ke mana!"
Shuwwa ta lumshe idannuwanta hawayenta suka zuba da yaren larabci ta ce" kina tunanin zan ji kunyar a ce da ni mahaukaciya a kan abinda nake ji a zuciyata ne?, Me yasa zan yarda sun rasu bayan ban ga gawarsu ba?, Har aka kamo mu daga saudiya muna zuwa neman gannin ainahin kabarinsu, ke din da kin yarda sun mutu komai kukan da zan maki zaki yarda ki bini ne? Anmy da abihna basu mutu ba! Idan sun mutu ki maida ni ki nunan kabarin da hankalina zai dauka cewar na iyayena ne, a jikina ban ji ba cewa sunne a kwonce a cikin kasar nan!"
Nahidt zata bata amsa itama rai a bace a sanyaye Mama dake binsu da kallo tana ta hanna kanta zubar hawaye da yaren buzanci cakule da larabci ta ce" Me ya faru da ku?, Me ya faru da ku y'ayana?, Ku fada min dan Allah me kuka gani a rayuwa?"
A tare a firgice suka kallota, A zaunen da take yaren da ta yi da bakinta ba na dan koyo bane, yare ne dake zaune dam a harshenta , tun daga larabcin har buzancin
A hankali Shuwwa ta sada kanta hawayenta suka bale gaba daya a fuskarta Mikewa ta yi tsam ta nufi dakinsu da gudu ta fada saman gado ta fashe da kuka
Nahidt gaba daya ta rikice, ta mike ta koma ta zauna tana kallon Mama zata yi magana Mama ta girgiza mata kai ta ce" Je ki kula da ita, ku yi adu'a kafin ku kwonta, zamu yi maganar da safe in sha Allah"
Wannan maganar ta hanna masu rintsawa gaba dayansu, hakan ya sa tunda Mama ta gama sallar asuba ta zo wajensu ta saka su a gaba kan maganar nan, domin idan su sun samu sun rintsama da kyau, ita ya kwana cikin tunani da mutuwar zuciya
A sanyaye Nahidt dake zaune rike da carbinta tana kallon Shuwwa da Mama ta riko hannunta tana hannata yin kuka ta shiga labartawa Mama rayuwarsu, abinda suka gani na rayuwa, irin tarbiya da soyayar da suka samu a wajen iyayensu, har zuwa ranar rabuwarsu ta karshe da su, da irin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki daga baya, irin neman na kansu da ya zame masu dole ko dan su ci abinci......ta ajiye mata zancen a zuwansu kasar nan ba tare da ta fada mata bayan zancen ba
A hankali ya saki kofar dake bude ya juya ya fice a falon, domin dama ya yo safiya ne sakamakon kiran da akai masa cewar mutumen nan da ya kawo ga dukan alamu yana fama da tabin hankali ne, shi dai ihun da yake yi su tafi, su tafi da matarsa, yanzun sunma ki karra masa wata allurar barcin dan kar ta sake taba kwakwaluwarsa, sunna jiransa ya zo a mikashi likitar mahaukata, shine ya shigo ya gaishe da Mama kafin ya fita ya fada mata marar lafiya gare shi, sai ya tarda bata dakinta, kuma bata kicin, gashi basa zuwa bangaren Chief of army a irin wannan lokacin, sai hankalinsa ya ffara tashi da sauri har zai wuce ya ga dakin yarinyar nan a bude shine ya zo dan dubawa ya tsinci magangannun nan
A hankali yake tuki yana tunani a cikin zuciyarsa ya shiga ayanna'💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 4️⃣2️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Ya shiga ayanna abubuwa a ransa kamar haka' wani lokacin yannayin mutun na fasara irin rayuwar da yake ganni a duniya, Aman baban abun mamakin anya kuwa idan suka samu matsi sosai ba zasu saida hakurinsu da raina ba?, Idan suka gaza yin haka menene hujarsu ta kiyawa?, Idan kuma aka matsa masu har matsin ya kai da suka aikata anya ba'a shiga hakinsu ba? Yan Adam suke fa,...... MUHAY ka shiga a yannayi na sarkakiyar tunani....................'
A banagaren Mama kuwa sosai ta basu dama sukai kukansu son ransu kafin ta sake yi masu wata tambayar da ta saka su wannan karron kallon kallo tare da kasa furta mata koda A ne
Murmushi ta yi tana sake fuskantarsu a sanyaye ta ce" Ta yiwu ku ji tsoron idasa min labarinku, sai dai ban san dalilin da zai saka ku kasa idasa min shi ba, ta yiwu kunna tsoron kar na ji yaya kuka rayu bayan an cutar da ku an zo an fasa maku labarin cewa iyayenku sun rasu, iyayen nan naku da suka yi maku gata na rayuwa tsaftataciya, da dan mahaifinku za'a bi daga karatu sai barci, mahaifiyarku ke kokari da zarar ya gusa sai ta fitar da ku koyi aiki, ta dage ta koya maku dukan wata wahala da zaku iya jurewa, hakan ba yanna nufin bata tara maku ba, haka mahaifinku nemansa a kanku, an zo an kwashe komai da nufin za'a ajiye maku, sannan an nuna maku a yanzu fa ya zama wajibi ku fito ku garwaya da kowa, al'uma masu mabambantan halaya ku shiga gari gari ya ganku ku ga gari, ku saka kaffafuwanku wajen da baku taba zuwa ba, dan zalinci a rai biyun nan kacal wanda a yanzu da kuka warware kuka zama yan mata ana iya daukanki a ciyar da ki dan abincin lomomi kalilan ba da yawa ba, sai aka zabi cutarwar ta hanyar nuna maku dole ku biya hayar da kuke, ku kuma biya abincin da zaku ci, rayuwa kuma ai dole sai da cin tuwo koda babu muhali, Babu wani a kusa da zai kwaba ko ya yi fada dan a gyara, babu wata soyaya tsaftataciya da zata saka zuciya aminta harma ta samu laushin halaya, a sake ake a bakin titi babu wanda zai iya duba da soyaya irin ta musulunci ya taimaka?, To kuwa da kuke tare gar zuwa yanzu mo me kuka ganni na rayuwa ni sai dai na taya ku kukan hakan da kuma gyaran hakan, da kuke zaune a tare ni ba mahaukaciya bace ba kuma mai take ganninta bace, na tabata kun sha gwagwarmayar rayuwa a tsakanin mutanenmu masu son kansu da mugun nufinsu, masu rayuwa da son ransu da kidan ganga irin na shedan a zukatansu, daidaiku suke ganni su bari, an zo an rabu da mahaifinkama an karya masa kara a ido bale babu idannuwansa, babu na mama bale na yaya? Ina so ne tunda na fara na dire abin a ma'aunin da ya dace, menene karashen labarin da *ALK'ALAMIN KADARRARKU* ya zanna maku, IBTISAM me ya faru da ku bayan wannan?"
Shuwwa da a da take da karfin gwuiwar fadawa koma waye abinda ya faru da su da irin aure auren da suka yi a rayuwa sai a yanzu , a yanzu yanzu tsoron hakan ya darsu a cikin zuciyarta, ba komai ya hadasa maya haka ba kuwa sai gannin yau gata da ranta a gaban wata halita a duniya da ta saurareta, ta ji komai dala dala nata, harma ta yarfa da furucinta cewa bata yarda iyayenta sun rasu ba, sai take tsoron kar ta ji karashen labarin rayuwarsu da suka yi kafin haduwarsu da ita ya saka ta tsane su harma ta kore su, hakan ya sa take ta kallon bakin Nahidt da ta sake rike mata hannu ta ringa bayanawa matar nan irin gwagwarmayar da ta gani ta rayuwa, wace take dafe da ita , su fada ruwa su fada wuta su fito su kankami junna, su yi kuka su yi dariya , irin yadda maza sukai wasan kura da rayuwarsu rayuwa irin ta rabe rabe ko su ce dauki ajiye, aure aure da koke koke da wawurar auren da zarar ya gabato, fadanta da sojan da bata san wanenen shi ba haka shima, sakin da ta samu a ofishinsa har zuwa juyawar igiyar aurenta daga wuyan yayanta ya koma kansa, bayanuwar mutanen da aka ce wai dangi suke a gare su wa'inda kwata kwata suka kasa dauka da mahinmanci kai suka kasa saka soyayarsu a zukatansu harma suke neman yin nesa da su ido rufe domin su din baki ne a rayuwarsu kuma boyayun sirika ne a nasu sirikan har zuwa irin rayuwar da suke yi da SOJA GIDAN Baban gidan CHIEF OF ARMY, da zuwa shigowarsu jirgi da shi da saukarsu a garin nan
Idannuwanta cike da hawaye fuskarta shabe da shi tana kallon fuskar datijuwar dake hawaye tana kallonsu ta ce" Wannan shine labarinku, wannan shine takun salon rubutun *ALK'ALAMIN KADARMU* , mu namu ALK'ALAMIN kadarrar baya wasa Mamah, baya sasauci Mamah, ko kuma shi haka ne sasaucinsa a ganninsa a garemu? Gashi kuma mun sake bayanar da mikin dake rayuwarmu a nan Mamah, wa ya sani ko zaki kyamacemu? Allah dai shi muka rika, mu Marayu ne"
Da muryar kuka IBTISAM ta ce" Mu ba marayu bane Mamah, ta yaya za'a kyamacemu dan iyayenmu sun matsa?, Na kasa yarda da haka mama, ta yiwu ni kuma mahaukaciya ce Ba'a sani ba, dan Allah a fahimtar da ni cewa idan an mutu mutuwa batai bakin fentin da take kawo kanta da kanta ba mama, mutuwa fa ko a cikin rami ya rufta da kai da kanta take shelar kanta Mama, ita makociyarmu ita kadai ta jiyo labarin har ta fadawa kowa kuma kowa ya leka bai ga komai ba, karshema kudancewa ta yi ta tashi daga wajen da muke ta koma wata anguwar da take da mukami a cen.........shin menene a nanade a cikin kudin tarihinmu ne ?"
A hankali ta matso ta yadda zata iya kasancewa tsakaninsu haka
A hankali ta kamo hannayensu dake cikin na junna tana kallonsu sunna kallonta
Dan murmushi ta yi tana girgiza kanta ta ce" Alhmdulilah ala kulli hallin"
"Zaku iya maimaita kalmar godiya ga Allah subahanahi wata Allah kuwa?" Ta sake fada tana kallonsu
A hankali suke gyafa kawunnansu A sanyaye ta sake furta" Alhmdulilah"
Summa da daidaya sai suke fada sunna kuma yin shiru da bakunnansu
A sanyaye ta ce" IBTISAM kin ga nima ban yarda cewar sun rasu ba"
Da sauri NAHIDT ta kalleta a raunace ta ce" Mama haba Mama"
Mama ta yi gagawar cewa" Haba Nahidt, to ai ba sabo bane, ba laifi bane, ba haramun bane, abinda nake ji ne na fada , kuma ina mai tabatar maki tun daga cen kasan zuciyata nake jin cewa basu rasu ba"
Tsatsareta suka sake yi da ido har Shuwwa ta ji idannuwanta na zafi a hankali ta ce" Mama kema baki yarda ba ko?"
Mama ta gyada kanta tana sakin hannunta ta dafe gaban goshinta tana fadin" Kin ga, su sun rayu da ku ba tare da sun fada maku garinsu ba, Menene dalili? Kasata mai dadin riko a zuciyya?, Ko daga rami ka fito watau aka ce cen ne asalinka zaka ga ko ka tare a karshen kasashen duniya lokaci zuwa lokaci kana sako maganar garin haihuwarka kana begenta harma ka ringa fadin abubuwan da kuke da shi masu daraja a garinku, aman ace iyayenku basu da shaukin zanta haka a tare da ku kadai da Allah ya basu? Wannan shine tabatuwar labarin mahaifiyarku , na yarda cewa Hamza yyayanku ne kuma danginku ne suka wakilci daurin auren IBTISAM, sai dai labarin mahaifinku ne na kasa kamo zaren maganar, shi kuma wanene shi?, Shin shine mahaifin Hamza ko kuma shi din wani ne daban mai tatare da boyayan Al'amari?, Abinda na sani shine zuciyata ta kasa aminta cewar sun rasu, ban sansu ba, ban taba ganninsu ba, ban san me ke tafe da rayuwarsu ba, aman ina ji ban yarda da sun bar duniya ba........."
Ajiyar zuciya take ta saukewa ta dora da fadin" Ni dai mutun ce kamar kowa, ban isa na iya cire maku damuwarku ba, aman kun san me? Zamu tashi tare mu je saudiya da ku, zamu je wajen da kuka zauna da iyayenku shekaru masu yawa baya, zamu sake bincikawa sannan mu sake bibiyar hakan, Daga nan zamu amshi dama wajen ikon kasar mu je mu duba kaburburan su, zamu roki Allah idan sunne ya saka mana salama da dangana a zukatanmu, zamu yi iya yinmu, idan har amsar ta zo daya ce cewar babu su, zamu zo mu zauna mu fahimci junna, domin a rayuwarku komai ya yi min banda al'amuranku na furucin bakinku, da wasu abubuwan, a matsayina na wace zan rikeku tamkar uwa a wajenku zan fada maku gaskiya cewar dole zamu kasance masu laushi, matan da suka amsa sunnayensu mata, a farawa daga yau, daga yanzu yanzu yanzu zan fara da baku kadan daga cikin sirikana, ba gudu ba ja da baya kuma sai kun yi domin ni mamanku ce!"
Gaba dayansu har wani tsigar jikinsu ke tashi, dama bayan Malan akoy wasu mutanen da suke rike da dabi'un mutane masu daraja na gidan duniya?, Basu kara yarda da lamarin na gaskiya bane sai da ta gama barawa masu aikinta salahun dukan abubuwan da take so su kular mata yau sannan ta aiki Lami zuwa bakin hanya ta siyo mata manyan Po na hawa biyu, sannan ta ja su makeken dakinta mai dauke da falo da dakunna biyu a cikinsa bayan falonta ta shige daka da su ta fara ciro kayayakin da gaba dayansu sai da mamaki ya fara kashe su kafin su maida hankalinsu kanta domin wani zama da Shuwwa ta yi a kasa ta baje kafafuwa ta sakata mikewa ta sakata ssake zamanta ta halin nuna mata cewar mace yarinya ko baba, ya dace ta kiyaye zama irin na wara kafafuwa, ta iya zama na hade kafafuwanta ko a ina zata zauna, wannan din zai hanna mata saurin kamuwa da iskar gaba
Kayayakin da ta fara fitarwa sunne SASAKEN BAURE, Kananfari, Cristaux de menth, ta raba masu aiki kan daya ta dora dahuwar sasaken bauren nan, daya kuma ta zo ta daka kananfari, sannan ta ciro abin cire akaifa da kayan gyara ta baje masu a nan kafin ta koma falo dan amso Po din ( bayanin yadda ake anfani da su a page na gaba in sha Allah)
___________________________________
Daga wajen da suke tsaitsaye sunna kallon kokowar da ake dima tsakanin Lieutenant Ganaral da wannan bakon marar lafiyar abin na daga masu hankali, sunna so su shiga aman umarnin da ya bada cewar a barsu ya saka kowa ke tsaye jinninsa a akaifa yanna kallon abinda yake faruwa