Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 9

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 9

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 9: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 9. A lokacin da Malan ya shigo ya saka su gaba ya shiga yiwa SHUWWAR…

3,216 words

A lokacin da Malan ya shigo ya saka su gaba ya shiga yiwa SHUWWAR nahisa sai ya kasance suma sun dukar da kawunansu sunna masu jin maganar har cikin bargonsu Sai da ya gama ne ya bada damar a shigo a tafi da ita, a nan ya sake kurawa NAHIDT ido yanai mata kallon da shi da kansa ya san ba kyau a adininsa, aman irin yadda take cijewa tanaa yiwa yar uwarta bankwana ta kasa tashi daga zaunen da take har aka fice da SHUWWAR Fauziya na kofa tana hawaye ita kuma ta kasa tashi daga ita sai shi ya saka shi yin dan Murmushi a sanyaye ya ce" Allah ya basu zaman lafia"

Sai yanzu ta iya dagowa ta kale shi, hawayen cikin idannuwanta na gangarowa, ta saka hannunta da sauri tana sharewa

Murmushi ya sakar mata yana furta" Tashi na maida ke gida "

Mikewa ta yi ta kama hanya bata bi ta kan matarsa da ta shigo yanzu yanzu gidan dan fita ta yi a sace ta tafi ta aikata abinda take gannin shi zai gyarata, domin ita dai ba zata yarda da irin wannan cin kashin ba a rayuwar mijinta !

________________________________

Satinsa uku da dawowa daga garin su SHUWWAR, dawowarsa har zuwa yanzu zama ne yake yi kadan aiki da yawa Abinda ya fara bashi ciwon kai shine karancin masu laifi a garin nan Gari ya riga ya zama capital inda kannanun barayi ne kawai suke bayane na bakin kasuwa, bayansu sai manyan yan hadama dake takatsantsan da takunsu, bayan shi burinsa ya samu waje mai dauke da masu laifi ta yadda zai baza kwonjinsa da horon da ya samu a kasar waje ta dogon karatun da ya yi har ya samu matsayin da yake kai a yanzu

Haka kuma gefe daya mamansa ta jajirce ta murje kan sai ya sake yin wani auren, hakan ya sa ya bada damar samun wata dan ya aura domin shi da kansama a cikin halin rayuwa yake na rashin mace a gefensa

A yau da ya zo gidan nasu ya tardo abinda ya saka shi yarda cewar a duniya idan ka zamto ana yawan ganninka a waje ana iya rainaka sosai, domin yarinyar Fatser yar gidan uwar gidansa ce ta dubi tsabar idannuwansa ta nuna shi take so a gaban mahaifiyarta da mahaifinta inda mahaifinta mamaki ya saka shi tsayar da murmushin da yake yi mata yana kallon mamanta da ta dauki magana tana murmushi tana fadin" Ai ni kam cewa na yi abu ya fi karfina ta samu abanku ta fada masa da kanta ya gani da idannuwansa, Sir ba dare ba rana yarinyar nan maganarta LIEUTENANT GANARAL ne, tun ina daukan abin da wasa har ya zo ya zama gaske a raina domin ta jajirce ta tsaya a kan ra'ayinta, shine dai na ce Yau tunda ya zo bara ta sanar da bukatarta na san ba zata rasa ba"

Mamakin matar tasa ya saka shi kafeta da ido, Ikon Allah, aiki na son rai karara ya bayana a tare da matar tasa, kamar ba ita bace abokin kishinta, abokin ra nuna ana sonsa ana masa meye meye to fa MUHYIDEEN ne, nan har nunawa take zai iya cin gadonsa tana lamari irin na kar a fara yi masu haka din nan, kuma yau itace da fadin irin maganar nan? Bayan ko ga maciji basa yi da mahaifiyar yaron, kishi take yi da ita kiri kiri ?

Fuska ya hade yana kallon y'ar tasa ya ce" Ashe baki da hankali? A nan waye sa'anki a tsakanin ni da Son din? Ashe idannuwanki sun bude haka ne da zaki kawo min raini irin wannan?, Ke yaushe na yi sake da tarbiyar y'ayana da har zaki zo ki dubi idannuwanmu da kafafuwanki a nan ki ce kina son Son?"

Da mamaki hajia ta ce" Aman Elhaj menene damuwar a nan? Inace so halita ne?"

" Dan Allah malama saurara min hakanan, irin haka ne kuke sakawa y'ayanku tunanin da zai halaka su ku dawo kunna nuna baku san lokacin ba, so? Na yaushe? Kin ga bana son aiki irin na son kai da shirme, idan shi yace yana so fine, idan ita ce zata bilo min da wani hauka ba zan dauka ba, ban haifi yar da ta isa da kanta ba, daga ke har ita ina iya baku mamaki a kan harkae SON!" Ya fada da karfin da ya saka MUHYIDEEN dake kallon TV kamar baya dakin dan rintse idannuwansa domin hayaniyar ta fi damunsa fiye da rainin yarinyar gaskiya

A kausashe ya kuma korar yarinyar da tsawa yana rakata da kallo domin da matsanancin kuka ta fita a falon tana mai jin ciwo a zuciyarta, Me abansu yake nufi? Du wannan kwaliyar , da jiran lokacin nan da ta yi ana nufin a banza ko me? Ama wasa abansu yake, walahi wasa yake yi, bai san ta sha walahaula a kan maganar GANARAL ba? Yadda ta iya tunkararsa yau ai ya ci ace abanta ya shiga mamaki da tsoro a kan neman katangeta da shi!

Mahaifinta a kausashe ya dubi matarsa yana fadin" Haba hajia, da girmanki? Da komai? Na san so halita ne, aman idan baki katse hanzarinta ba me kike so ta zame maki ne? Kin ga yanzu maza basa son tsaurin idon nan, ko daya basa sha'awar irin haka fa, ku kiyaye dan Allah, kece baba a gidan nan bayana, ke ya dace ki ringa tsawatar da duk wani hayaniyar gidana ba ki rinka taya yarana neman fitinata ina zaman lafiyata ba"

Ita kam da ya sani, da shiru ya yi da Neman fahimtar da ita yaren da bata ganewa, domin gaskiya ita abinda y'ayanta ke so ko bata so zata mara masu baya ne, ita kam tana yiwa bukatar yayanta biyaya, to idan bata yi ba me ake so ta yi? Bata bin bayan zaburar da yaro ba gaira babu sabar a hannawa yaro nutsuwa da zaman lafia a banza a wofi

Tana zaunen nan maman MUHYIDEEN ta shigo da salama sakamakon kiranta da SHIEF OF ARMY din ya yi tana gaishe sa matarsa wace kamar jira take ta shigo sai ita ta mike ta fice

Zama ta yi tana kallon yannayin MUHYIDEEN dake kallon TV sannan ta maida hankalinta kan mijinta da ya ce" Kin ce kina da magana a kan maganar auren yaron nan, wacece maganar?"

Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta ce" Maganar a kan tafiya aikinsa da ya kawo yana so a bashi dama ya je garin cen ya yi shekara biyar, Elhaj jiya ina sauraron redio wani abu da aka yi ana fadi sai da raina ya kiya, na san ba shi ya isa ya hanna ta'adanci ba, aman yana bada gudunmuwarsa ba laifi, dan haka na bashi damar ya je garin aman da sharadin auren nan da ya ce yana so a daura masa a nan zai bar matar, ta haka zai zamto ya ringa tafia yana dawowa wajen matarsa yanai mata weekend, sannan idan matar tana kusa da mu ta yiwu wannan auren ya dore in sha Allah"

Tunda ta fara maganar sai yanzu ya dan dago ya kalleta sannan ya yi dan murmushin da sunna gane murmushi ya yi ne idan yannayin kakausan kallonsa ya dan daidaita kamar na mutane sai ko idan sajen fuskarsa ya dan sake hadewa

A hankali SHIEF OF ARMY ya ce" Yanzun ba zaki daina rigima ba? Shekaru fa aka ce ba wata daya ko biyu, soja ne fa, shine zaki raba shi da iyalinsa ki ce a ajiye maki ita a wajenki? To ki yi mata me?"

Kansa ya sake sadawa yana dan kurawa agogon hannunsa ido jin dakin ya dauki shiru, ya tabata mamansa na son saka mijinta ya yarda da maganar nan ne da idannuwanta, domin ta riga ta shanye magana da ido bale idan tanaiwa mijin nata

Muryar SHIEF OF ARMY ne ke fadin" Ba fa zai yiwu ba zakina wani marairaicewa, shi din bakya tausayinsa ne?"

Sake sada kansa ya yi yana son ya furta cewa ba komai, aman kuma baya so ya katse masu magana

Sai kuma ya ji Sir din na fadin" Hasana, Hasana gaskiya kina takura min a kan maganar yarona, kai MUHYIDEEN shin ka amince da maganar nan ne ko baka amince ba? Idan baka amince ba bani da damuwa zata daina ne ta barka ka yi tafiyarka !"

Dan mumushin ya sake yi a hankali ya ce" Aa Aba, na amince da bukatar Mama"

Su dukansu sai suka samu kansu da kura masa ido Sarai tausayin yaron nata ke yawo a sasan jikinta, sai dai idan ta duba ta ga idan ya tafi yana iya zamewa ganninsa ya yi mata wahala sai ta karra yarda da wannan shawarar da ta yankewa kanta

Aa hankali ta furta" Yaushe kake son tafia ne?"

Dago da fuskarsa ya yi yana ji dama ace ya iya nuna murnarsa ta hanyar kurma ihu ya yi rawa? Kai da ya gwada domin da ace mamansa ta san irin taimaka masan da zata yi na barinsa zuwa garin nan da ta jima da barinsa, shi baban abinda yake so ya fara dirarwa wadinan tsagerun da suka yi wasa da hankalinsa, shi MUHYIDEEN MUHAY su dube shi au ce zasu zagaye shi da rainin hankali? Sai ya tura mota an dauko su sau dukansu a duk inda suke sun sake buga game din kafin ya shiga cikin gari hankali kwonce ya ringa buga game dinsa son ransa A dan kagauce ya ce" Yauma sai na je Mama"

Bakin nasa da yace yauma din ta kure da kallo da dan haushi haushi ta ce" To bikin naka fa?"

Da son convaincre dinta ya ce" Mama ba sai ku yi bikin ba, sai ta zauna satin gaba idan na dawo in sha Allah sai mu gaisa"

Yar daria CHIEF OF ARMY yake yi na zumudin yaron nasa ya ce" Ka ga, ba yau yau ba, ka manta sai ka salami na kasa da kai? Ka bari gobe in sha Allah sai ka yiwa garin shigar yama idan muka gama tsaida komai, aure kuwa da kana nan, da baka nan daura shi za'a yi lafiar Allah in sha Allah"

Ita kam yanzun zama da soja ya daina bata mamaki, tana aure da soja, ta haifi soja, sai ya zamto idan sun kwaba kwabarsu take barinsu da halinsu

Zumudin da ya kasa boyuwa a fuskar yaron nata kuwa sai ya hadasa mata farin ciki itama, maganar aurensa kuwa ta fi kowa son ya dauko wata a waje, domin kaf y'ayan mai gidan nata su uku da suka nuna sunna sonsa bata so a yi da dayama, ita ta san wa ta haifa, dan an bashi Y'ar SHIEF OF ARMY ba zai hanna idan kadarar karan zamansu ta biyo ta kanta itama ya maka mata takardar sakinta la'ada waje ba, shi yasa ta bari ya samo ya nuna da kansa shi ya dauko, har mamaki take mahaifin yarinyar da zai saje aure yadda yake zumudi a kan maganar, bayan sake saken MUHYIDEEN bayanane ne ba boyaye ba!

💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣1️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Numfashi ta sauke ta fuskaceshi a nutse ta shiga yi masa nasiha, Nasiha take yi masa a yanzu da take gabansa take cikin rai da lafia, nasiha take masa a duk lokacin da ta samu zama da shi koda na minti daya ne Shekarunta arba'in da hudu a duniya, tun tana da kananun shekaru ta same shi take kuma alfahari da shi, ko a yanzu ta samu haihuwa tana so, zata kuma haihu abinta domin ta tashi da burin samun y'aya masu yawa sai dai Allah ya bata daya ta kuma gode, a sanyaye ta ci gaba da fadin" Kar ka yarda giyar mulkin dake hannunka ta saka ka cin amana, cin mutuncin talaka ko amsar cin hanci dan cutama mai gaskiya, MUHYIDEEN aikinka kar ya baka damar da zaka wulakanta mutun, idan bashi da gaskiya ne ka yi kokarin bin aikinka yadda ya koyar da kai ka hora shi domin wani lokacin da gaskiyarka a kan aikin naka zaka kai kanka ka baro , ka kiyaye haye a kan dan Adam, fuskarsa kake kallo baka san waye shi ba, wanin yana da baiwar da yake iya hadaka da wahala a bisa zannen ALK'ALAMIN K'ADARRARKA, MUHYIDEEN ba kowa ake takawa a zauna lafia ba, wanin Kadararsa ce zata kaishi hannunku ka kasance mai tausasawa, MUHYIDEEN ba kowa akew birgewa a duniya ba, bale ku aikinku kunna tare da majiyansa fiye da masoyansa, wanin zai tsane ku ne dan ra'ayi, wani kuma da dalili, kar ka yi wasa da adu'a, kar ka yi wasa da ambaton Allah, ta haka zaka fi karfin magauta, sannan ka kyautata mu'amalarka ka ji?, Allah ya tsare, ya yi maka albarka ya kare ka, ya karra daukaka ka ya sa ka gama da duniya lafia sannan ya sa aljannah ta zamto makomarka"

A bayane mijinta ke amsawa yana cike da mangarin soyayar da take nunawa yaronta cikin hikima, a bayane ya furta" Uwa kennan, mutun baya tsufa da muradin uwa a gefensa, Allah ya jikan mahaifanmu"

Da amen suka sake amsawa su dukansu ukun sannan ya mike yana masu salama ya fita a falon

A lokacin da ya karaso kusa da motarsa ya ga yarinyar nan da ta gama baza rashin kunyarta a kansa a zaune a saman daya daga cikin motocin gidan ga Bodyguard dinta a gefe yana tsaye ita kuma ta harde hannayenta tana kallon waje daya

Da hannunsa ya yiwa Bodyguard din nata alamun yana iya ajiye hannunsa sannan ya bude motar ya shiga ya tada A razane ta kallo wajen motar tana sauke dubanta a kan fuskarsa Da sauri ta sada kanta sakamakon wani kakausan kallo da ya maka mata wanda sai da ta ji hanjin cikinta ya kule waje daya Ba ita ta dago kanta ba sai da ya bar wajen da motarsa sannan ta dago tana bin sawun motar da kallo duda farin sawu ne a saman Wajen A hankali ta furta" Kasancewarka bamban da sauran maza ya sa nake so ka zamo mallakina LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN"

__________________________________

*Bayan sati daya da kwana hudu*

Turaran wutar dake ajiye ta kunna bayan ta gama moping din falon , hakan ya sa dakin daukan kamshi na musaman wanda ya sakata sauke ajiyar zuciya duda irin yadda zuciyar tataa ke cinkushe da matsalar da take fuskanta tunda ta yi auren nan

Bata san shigowarsa ba, bata ji shigowarsa ba, hasalima sai da ta juyo ta ganshi a tsaye a jikin garu ya kafeta da kallon da ba zata iya fasarashi kai tsaye cewar kallon harare ne duba da ita ya dace ta harare shi ba shi ya dace ya harareta ba

"SHUWWAR ashe dama kin taba yin aure?" Ya fada a kausashe yana sake kureta da kallo hakan ya sa gabanta kwonci kwonci ya fadi

A hankali ta idasa zuwa wajen kujera ta zauna tana sake fuskantarsa ba tare da ta furta masa kalma daya ba

Karasowa ya yi yana zama yana kallonta a birkice ya ce" Magana fa nake yi maki, ashe dama ba budurwa na dauka ba!?"

SHUWWAR ta dube shi tana hadiye bacin ranta ta ce" Kana nufin baka san na taba yin aure ba ka aureni? Ko kana nufin wannan dalilin ne ya sa runda aka kawoni gidan nan yau sati biyu aka yadani sai dai na hangoka tare da matar mahaifinka ka zo ka wuce?"

" Wannan itace amsar da zaki bani bayan ina matsayin mijinki na tuhumeki da magana mai mahinmanci wada aka fada min tun ranar da aka kawo ki ta dakeni ta hanna ni zuwa dakinki dan ciwon da nake ji a zuciyata aka kuma fada min fitar da yayarki take yi ba komau bane sai yawon bariki na zo maku da tambayar dan ki gaskata min aman shune zaki nemi yi min amsa ta rashin tarbiya?" Ya fada da fada fada hakan ya sakata kikifta ido tana kallonsa

Watau tunda aka kawota gidan nan aka nuna mata dakinta rabonta da wani abun mutunci ya hadata da mutanen gidan Wanu gani gani suke yi mata a bayane kuma sukan yada mata magangannun da ta ajiye haka aa matsayin dama tana iya fuskantar irin haka ko yayane, ta share kowa ta ringa farin cikin gannin ta waye a gidan miji itama A hankali awani dake shigewa ya saka ta fara damuwa da rashin gannin mijin nata a bangarenta Ba dan ta saba ko ta matsu da wani abu ya shiga tsakaninta da SUDAIS ba, ko daya , hasalima ita ba taba yi ta yi ba sannan bata cikin jinsin yan matan dake kwalafa ransu da abin nan , kai tanama iya cewa ita halitarta ba ta d'a namiji bace sam, aman kuma sai ta ringa jin ya dace ace mijin nata ya zo inda take ko dan ya ji yaya ta kwana yaya ta tashi

Readers Also Read