Ana barin halal original by anty nice - Chapter 17
Ana barin halal original by anty nice Chapter 17: Ana barin halal original by anty nice Chapter 17. Bayan motan muka shiga mu uku, hadiza, zainab da kuma…
3,927 words
Bayan motan muka shiga mu uku, hadiza, zainab da kuma ni, tunda muka shiga na kama bakina nayi shiru, daga hadiza sai M.G suke hira a tsakanin su, daga ni har A.G babu wanda aka ji bakin shi har muka isa gidan amaryah, sun daɗe a waje kafin suka tafi, da niyyan after magrib zasu zo su ɗauke mu. Buɗan kan yayi kyau sosai, amaryah tafito cikin Alƙyabbah fara mai rastin golden, tayi kyau sosai da ita, ango sai wani washe baki yake cike da farin ciki, ana idar da sallan ishaa su Yayah M.G suka zo, wayana naga call ya shigo da baƙon number, har sai da naga zai tsinke tukun na ɗauka, ko a bacci aka tashe ni bazan kasa gane muryam shi ba, "idan kun shiryah muna waje", iya abun da ya faɗa kenan ya katse wayan, murguɗa baki nayi na share shi, don lokacin angwaye sun shigo kenan, haka ƙawaye da angwaye sukai ta hira da tsokanan juna, ni da zainab dai bakin mu shiru, amma hajjah khadijah kam sai zuba ake tayi da sauran friends ɗin amaryah, mudai bamu fito ba sai wurin 8:30, kuma M.G basu sake ƙirana ba kuma basu tafi ba, angwaye ne suka fara ɗaukan ƙawaye, sai lokacin naji wani irin tausayi da kaɗaici ya zo mun, Allah sarki maryam yanzu munyi nesa da junan mu, duk sai naji babu daɗi, muna haɗa ido da ita naga idonta ya cika da wahaye, da dabara nace zanje kitchen na ɗauko ruwa, sai da na fita na ƙira su hadiza a waya, suma cikin dabara suka fito, ummitah da hafsy ma fitowa sukayi, kaman sun san mun ƙaro ko kuma da ma suna da shirin hakan sai naga kowan su a motan shi yazo, babu yadda na iya dole na shige gaban motan A.G, domin muna fitowa naga ya ƙira ummitah da hafsy ya buɗe musu bayan motan shi, sannan ya bar gaban a buɗe ya wani ƙura mun ido, M.G dai yana ta wani sake murmushi a fuskan shi ya buɗewa hadiza gaba, ya buɗewa zainab baya, suna shiga naga ya rufe, dole na wuce gaban motan A.G ɗin na zauna, ko kallon inda nake baiyi ba ya tayar da motan shi, ina jin su hafsy suka gaishe shi amma ni nakasa buɗe baki na gaishe shi, sai ma juya kaina danayi ina kallon waje ta glass ɗin motan, chan na tsinko muryan shi yana tambayan su hafsy, "hafsat me kuke son ci"? Da yake ba mutunci bane ya ishe ta sosai kawai sai naji tace, "tou nidai nida aminaiyata muna ƙauna da kaza, kazar bauchi club, ita kuma Adda suna mutunci da tsiren wurin, don tana son harkan tsire," tana faɗa ummitah na taya ta da, "ae har soya milk Adda tana korawa time to time", ka marasa mutuncin ko dariya basuyi ba sai wani ɗagawa juna kai suke irin alaman kowa ta faɗi dai-dai, murmushi mai ɗan sauti naji A.G yayi, wanda har sai dana juya na kalle shi, "ku kuma kuna ƙauna da wani abun shan"? Ɗan dariya hafsy tayi tace, "ae muna madaran son coca-cola, wataran har pepsi mukan kora, idan ka ganmu da yogouth tou mutanen mu suna na, dole suke haɗamu da shi, har mun saba sha yanzu". Ni wallahi hafsy da ummitah tsoro suke bani, yarah gaba ɗaya babu kunya a idon su, don wani dariya suka kwashe da shi suna wani godiyan iskan ci lokacin da yace, "yanzu dai a haɗa muku coke,pepsi,yogouth"? Dariya suka kwashe da shi suna godiya muke Babban yayah, kace har gobe zamuyita sha, don idan Allah ya kaimu sai munyi order hajiya shawarmah, sai mu haɗa da yogouth ɗin, yanzu mu karya ƙashin kaza da coke da pepsi na ummitah", murmushi yayi ya miƙa hanyan bauchi club, nidai kaman na fashe da kuka saboda haushin su hafsy, sai wani leƙo kai gaban motan suke kaman wasu sukaye suna ƙara godiya, har muka shiga bauchi club fuskan shi da murmushi, wanda hakan yake ta bani mamaki, amma nasan tsantsan shaƙiyan cin su hafsy ne yake bashi dariya, muna parking naga motan M.G ma yayi parking a gefen mu. Tare suka buɗe motan suka fito, suna fita na juya ina hararan su, da sauri hafsy tace, "wallahi Adda kika ce wani abu recording ɗinki zanyi, yana shigowa na kunna mishi", ta faɗa tana ɗaga wayanta sama tana nuna mun, ita kuma ummitah cike da shaƙiyanci tace, "ae best friend nikan ma har na ɗana, tana kwabsa mana zamu antaya mishi", juyar da kaina kawai nayi na rabu dasu, sai wani dariyan rashin mutunci suke tayi, zuwa chan kaina yana ƙasa naji muryan hafsy tace, "wooww gaskiya gayen nan ƙarshe ne, friend kiga wani taku da yakeyi kaman wani Basaraken zaki, gaskiya matar shi ta more da haɗaɗɗen miji ɗan wanka da aji," ummitah ta amsa mata, "da kuma dace da miji ɗan ƙamshi, saboda Allah hafsisin london bakiji ƙamshin motan shi kaman daɗin zai saka kiyi bacci ba? Nifa na tsorita da gayen nan, don har na fara manta sunan saurayina, meye ma sunan shi friend"? Hafsy na dariya tace, "shege ƙamshi, ƙamshi ya gagara ae, sunan samrayinki, isiyaku zakaran bauchi club", dariya suka ƙyalƙyale da shi wanda har saida suka saka na ɗan dara, don tsiyar su tana da yawa, kuma saida suka saka na ɗan ɗaga kaina ma dubi A.G da yake shirin ƙarasuwa, ashe ya chanja shigan shi ba irin ta ɗazu bane, yanzu wata faran yadi ya saka mai ɗan shara -shara, sai wani lumshe ido yakeyi shi kaɗai yana tahuwa, da sauri na sauƙe kaina ƙasa zuciyata na bugawa da sauri -sauri,gefen shi kuma M.G nashi ne.
Buɗe motan yayi ya shigo, juyawa yayi kaɗan baya yana duban su hafsy da suka wani nutsu kaman gaske, murmushi yayi yace musu, "yanzu insha Allahu zasu kawo, sai kuma shawarman account ɗin waye za'a tura so dat goben sai kuyi ordern,", da sauri ummitah tace "zubasu kawai a acct ɗin Adda, don duk ƙawancen mun nan da kake gani akan almanu sai mu munafurci junan mu, bawa Adda kawai don ita mai amana ce, zata mana order gobe, inda chanji ma bazata ha'ince mu ba zata raba mana", tana faɗa hafsy na gyaɗa mishi kai, "eh yayah A.G hankaɗa su wurin Adda, don mu akwai ɗan sauran nutsuwa a tare da mu, ƙarshe idan ma ɗayar mu kasa sai ta ha'inci ƴar'uwarta duk ta saka rechage card ko data, don ba kan gado bane wataran damu". Abun mamaki wallahi dariya A.G ya ƙyalƙyale da shi, sakarun suma suka shiga taya shi, nidai kaman na buɗe window na falfala da mugun gudu don kunya, tsabar wayo ne fah yasaka suka gaya mishi haka, wato *AUNTY NICE* na daɗe banga tsageru irin suba, kuma hattah yayah ishaq da yayah umar basu barsu ba, yanzu zasu haɗe su zaga su, halin sune yazo ɗaya shiyasa suke abota, kuma ko ƙaryah ɗaya tayi bazaki taɓa jin ɗayan ta ƙaryata ɗayar ba, sai dai itama ta tayata, gasu da shegen wayon tsiya, don ɗaya tana faɗan abu ɗaya take gane ina aka dosa, shidai A.G gaba ɗaya nishaɗi yake da shi a lokacin, muna haka har ma'aikatan suka kawo saƙon, bayan motan duk aka zuba musu, sannan A.G ya tayar da motan yana cewa, "wannan leda ɗaya kajin kune sai aka san muku tsiren kaɗan, don kada kuyiwa su Adda wayo ku cinye nasu, ɗayan ledan kuma na ummin mune, nasu Adda kuma yana hannun jama'an ta, tare dana hajiya ummah, kuɗin ku kuma zan zuba a acct ɗin Addan mu, haka yayi"? Ƙyalƙyala dariya sukayi lokaci ɗaya, hafsy na wani gyaran muryah tace, " yayan mu insha Allahu na maka alƙawari yau zan raba dare na tayaka da addu'an Allah ya baka mata ta gari wanda bazata hana mu zuwa gidan kaba, wacce zata barka kana mana abun duniya, kaga yayah muhammad da yayah Ahmad ae tsantsar addu'an da nake musu ne idan sun haɗani da abun duniya Allah ya amsa, kaga ae matan su nagari ne? Tou amma duk basu kai wannan aminiyata ɗin ba, don yayah umar yana kyautata mun, shiyasa nafi dagewa da roƙa mishi ta gari, kuma cikin ikon Allah sai ya samu Ummitah, ae ummitah mutum ce har da ƙari, matsalarta sai an dage ta bar yayah umar ya tara na kanshi, saboda bakinta baya hutawa da ciye-ciye, tou kaima ka shiga sahun addu'a na," dariya ummita ta sake ƙyalƙyalewa da shi tana duban hafsy tace, "Allahummah Ameen ƙawata, ae duk zamu saka shi cikin addu'a, amma nikan sai daga gobe idan Allah ya kaimu, don gaskiya yau kam naci naman nan bacci zanyi don na gajji, amma gobe kam idan Allah ya kaimu, zan maka addu'a Allah ya baka nutsattsiyar mace irim Addan mu, don yanayin ku ɗaya wallahi, akwai nutsuwa akwai alheri ". Ta faɗa tan turo kanta gaban motan, ni dai narasa dalilim da ya saka na haɗa hanya da su, don ni har wani jiri -jiri nakeji tsabar haushin su, a haka muka ƙarasu cikin gidan mu, inda A.G yake ce musu, "nagode da niyyan ku, ae ko bakuyi ba nagode, kuma Allah ya amsa bakin ku ya bani Addan na ku", ya faɗa yana ɗan maida idon shi kaɗan gefe na, shashun kuma haɗa baki sukayi suna wani ihun murna, ummitah nacewa, "wallahu kun dace, nifa ɗazu har mafarkin ido biyu nafara dana ganku, nace lallai za'a haifo yara ƴan gaske anan, wayaga kyau na dukan kyau, nutsuwa Na dukan nutsuwa, Allah dai ya tabbatar da alkairi, Allah yasa ka dace da samun zuciyata", murmushi yayi yana wani mun kallo da ya saka duk jikina fara rawa, ƴan tsiyar kuma sai wani smilling suke suna ƙara turo kawunan su gaban motan, ni da ma M.G ne ya kwashe su da nafi samun sauƙi, yana tsayar da motan na kai hannu zan buɗe sai naji ta lock, juyowa nayi na kalle shi, "yayah xaki fita bayan baki amsa musu addu'an su ba?" "wallahi kam yayah, kuma ma banga ta baka acct ɗin nata ba hehehehh", hafsƴ ta faɗa tana wani dariyan iskanci, kallo na yayi yace bani acct ɗin kafin ki fita," sannan ya buɗewa su hafsy ƙofan yana ƙara musu godiya, sai wanidariyan daɗi suke yi suna mishi godiya, sannan ummitah ta ɗan leƙo ta glass tace mun, "Adda nikan zan ƙira mama nagaya mata anan zan kwana, kuma a side ɗin ummie zamu kwana don kada mu takurako hajiya ummah ta takura mu, don tana ganin mu da ledan nan zata ɓoye nata ta saka ido a namu, gara muje wurin ummie, ita sai ma taci ta rage mana mu ƙara da safe, zamu ƙiraki zuwa anjima muji yayah labarin alert mai kukan tarararat", tana gama faɗin haka sukayi ciki da sauri suna dariya. Tsaki nayi ban shiryah ba, hakan ya saka naji A.G ya wani ɗan tuntsire da dariya, a hankali yace, "kai yaran nan sun sakani nishaɗi, ballantana ma da suka haska mun ashe Adda tana son tsire mai ɗan ƙarago, ashe bazan sha wahalan wani sayan kaza ba" ya faɗa yana duban fuskana, turo baki nayi gaba, wanda sai lokacin bakina ya buɗe nace, "kai fa baka san kalan ƙaryan su ba fah? Maƙaryata ne na gasken-gaske, kuma wallahi wayo suka maka don ka saya musu nama da shawarma, haka sukeyi wa su yayah Ahmad, nidai babu ruwana", na faɗa ina maida fuskana kanshi da naji dai yau sai dariya yakeyi, "wayace miki ban fahimci wayon su ba, ae abun da yaringa sakani nishaɗi kenan har kika ga ina dariya, bakiji wayon da suka mun ba na maganan shawarman su na gobe"? Ya faɗa yana ƙara sautin dariyan shin, nima ɗan murmushi najyi kaɗan nace, "sun ɗauka ba'a gane sune ae, ni tsoro suke bani ma wallahi, harta masu son su basu ƙyale su ba", dariya ya ɗan sakeyi kaɗan yace, "nidai sun sakani nishaɗi, kin san mai wayo wani lokacin ɓuya yake a bayan wayon shi, bakiji sunce a tura miki kuɗin acct ɗinki ba, kinsan meye dalilin su"? Dariyan naji ya ɗan zo mun, son nasan shima ya fahimce su. Nima dariyan naji ya zo mun, sai na ɗan dakata da sauraren Ayshaa na ɗan dara, itama dakatawa tayi tana darawa, domin tuna lokacin da abun ya faru, gashi yanzu duk anzama iyaye.
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba, har na gajji da jiran naji me zai ce amma sai naga yayi shiru, duka hannayen shi yana kan stearing motan, idon shi na kallon gaban motan, "bari na bar ki kishigs gida, saboda bai dace na tsayar da ke a mota ba, insha Allah gobe zan shigo idan kina free, don jibi zamu wuce Abuja", juyowa yayi yana kallona, ko jira yake yaji mai zance? Ni kuma sai nayi shiru ban ce uffan ba, ƙoƙarin buɗe ƙofan nakeyi sai najiyo muryan shi yana cewa, "3weeks zanyi na koma, sai bayan six month zan gama insha Allahu, tsarabanki gobe zan shigo miki da shi insha Allahu," Buɗe motan nayi na fito waje, hannu na riƙe da handbag ɗina, fuska a ɗan ɗaure nace, "sai da safe mungode," banjira jin mai zaice ba nayi gaba zuwa side ɗin ummie nah don na mata saida safe, ina shiga na samu babu kowa a parlor, ɗakin ummie na wuce, ta fito daga toilet alaman alwala ta ɗauro, gaban mirron ta na ƙarasa inda naga ledan namanta akai, kallona tayi tace, "hafsy tace mun yayan ku A.G ne ya saya mana ko?" ɗaga kai na mata alaman hakane batare da nace uffan ba, "tou angode Allah ya musu albarka" a zuciyana na amsa sannan na mata saida safe, ko ta kan su hafsy ban bi ba, don nasan ina zuwa zasu ɓata mun lokaci.
A ɗaki na samu su zainab sun baza nama a plet kowa tana figan nata, gefe ɗaya kuma sun ajiye mun nawa a leda, hiran su suke tayi na sha'anin bikin da muka gama, nidai abunda yake damuna ya dameni, nayi mamakin M.G daya na sauƙe su ya wuce abunshi, don ina ganin ko cikin gate ɗin gidan bai shigo ba, daga waje ya ajiye su, ni bai isa ya mun shariya ba, don ko wallahi wurinta yazo, Allah ya bashi sa'a, haka na ci naman ba wai don ina jin daɗin shi ba, gaba ɗaya na rasa me yake damuna ne kawai, haka muna gamawa kowa tayi shirin kwanciya.
Washe gari duk shaƙiyancin su hafsy ban kula su ba, don ina ankare da su agaban ummie suke zabga rashin mutuncin su suna dariya, har suka saka hankalin ummi dawowa kanmu, alama kuma kaman ta fara zargin wani abu ne daga yana yin dariyan su, 50k ya tura musu na shawarma, kuma yadda ya bayar haka na saka musu 25k ma kowa, ganin hakan ne suka fara tiƙa dariya kaman wasu tumakai, nidai ban kula su ba na juya na bar ɗakin.
Hadiza ne da ta fito daga side ɗin su habiba take ce mana yau kam sun haɗu har sun gaisa, nan habiban take ɗan tsakura mata abunda yake faruwa, wai haka kawai Aliyu zai burkice mata yace shi bai taɓa son ta ba, kuma shi ni yake so amma don su cuce shi suka aura mishi ita, shi bai san ma yayah akayi ya rabo da ni ya koma mata ba, daga nan kuma idan ta tanka akan ae abunda yayi Ayshaa shi yayita, ae duk ɗaya ne yayi haƙuri itace ƙaddaran shi, ae kuwa nan zai kama dukan ta yana ƙiranta da mummunan ƙaddara dai, tana gayawa hadiza tana kuka, akan ita wallahi mamie ne ta matsa akan maganan, ita dai tasan yana burgeta amma ita ma batasan yayah akayi wannan al'amari ya faru ba, tayi -tayi ta kaucewa abun amma ta kasa, kuma mamie tace zata tsine mata idan ta bari abun ya fasu, hadiza tana gaya mana cike da tausayin habiba, "hmm kunsan babu abun da mushirikiyar uwarta bazata yi ba, yanzu haka ma ita ta maida hankalin habiba kai, gashi asirin ya karye aure baije ko ina ba, sai tsaraban ciki", zainab ta faɗa tana ya mutsa fuska.
Bayan sallan azahar zainab ta wuce unguwar su, hadiza kuma tace sai gobe da safe insha Allahu.
Ana sallan ishaa wuraren 8:00 sai ga ƙiran A.G, ina ɗauka naji yace , "ina waje", raina ne naji duk ya ɓaci, babu yadda na iya na fito parlor na gayawa hajiya ummah A.G yazo yana waje, bakinta kaman zai tsage tsabar fara'a tace naje na shigo da shi mana, haka na fita babu ko ɗan powder a fuskana, na daiyi wanka bayan magrib saboda bana sallah, dogon rigan material na saka, amma dai ina ƙamshi na gaske, gyalen material ɗin kawai na yafa na fita, yana tsaye a jikin motan hannun shi riƙe da wayan shi yana dannawa, ina isowa turaren shi mai suna *BVLGARI* yana tashi a jikin shi, designer ne mai ƙamshin gaske, yana sanye da blue jean, da red ɗin polo, yayi wani haske yayi kyau a idon masu ganin kyaun shi, sallama na mishi murya chan ƙasa -ƙasa, ban yadda mun haɗa ido ba lokacin da ya kallo ni, shiru yayi baice mun komai ba, naga muna ta ɓata lokaci a tsaye, sai na daure na ɗago kaina nace, "mu shiga parlon ummah" bai ce uffan ba sai ido da ya zuba mun, juyawa nayi na nufi hanyan parlon, ina jin shi ya rufe motan ya biyo baya na, a parlon muka samu hajiya ummah zaune ta ƙurawa T.V ido kaman gaske tana ganewa, don kuwa labarai ne ake yi a channel ɗin CNN, zama yayi yana gaisheta cike da sakewa a fuskan shi, itama da fara'arta take amsawa, sannan ta tambaye shi "ina M.G?" murmushi a fuskan shi yace, "M.G yaje neman aure, ya tafi hira", ya bata amsa yana ɗaukan remote ya rage vulome ɗin da madam ummah ta wani ƙure, dariya tayi na jin daɗi, "kaii kai kai abu yayi kyau, a gari yake neman auren kenan"? Ta tambaye shi, "ƙanwata autar mu yake nema, sunan ta Heedayah". "kace ƴar gida za'ayi kenan? A ashe muktari yayi maka wayo, shi kam a gida ya samo, kaima ae yakamata ka nemo, sai a haɗa ku tare asha biki, don abun zai fi armashi", murmushi yayi ya ɗago kai ya dubeni, sanan yace, "ke baki iya kawo wa baƙo ruwa ba ko? Haka za'aje gidan ki"? Turo baki nayi na miƙe nayi hanyar kitchen ɗin, ina jin hajiya ummah nacewa, ae banida wayo ne ko kaɗan, wannan mijinta ae zai sha fama, sai dai Allah ya bata nagari kuma ɗan gida. Maida kallon shi yayi kan hajiya ummah yace, "hajiya ae ni yakamata kibawa ita, kinga nima nasamo ƴar gida irin na M.G, sai ayi tuwona mai na ko", ya faɗa yana bina da kallo fitowa na daga kitchen, hararan shi nayi ina mamakin wayon mutumin nan, wato so yake ya ɗaureni kenan ko?. Cike da murna hajiya ummah tace, "idan nice wallahi na baka, kuma nayi imani daga iyayenta har yayunta babu mai hanaka, kai dai gata nan sai ka nemi haɗin kanta, mudai fatan mu ɗa addu'an mu Allah ya haɗa kanku, Allah yasa ace gara da akayi, bari na baku wuri kuɗan zanta, Allah yayi albarka abu yayi kyau", haka ta miƙe tayi ɗaki tana bani sallahun idan mungama na kashe mata T.V kada ya zuƙe kuɗin Usmanun ta. Murmushi yayi yadawo da kallon shi kaina bayan ta ƙarasa shigewa ɗakinta.
Nidai ban yadda na ɗago da kaina na kalle shi ba, amma a jikina naji shi yana kallona, chan kuma naji muryan shi, "naso M.G mutaho tare ae, amma yaƙi, wai shima zai gyara zaman shi ne a wurin yarinyar nan, gashi ni sai naga kinƙi sakewa da ni", ɗago kai nayi na kalle shi, a zuciyana nace kaji mun mutumin nan, wai M.G yaƙi rako shi, wato hiran ma M.G ne zai mishi, tou zaman auren fah? Ƙara ɗaure fuskana nayi, don so kawai nakeyi naji yace zai tafi, amma mutumin ki kam sai ya gyara zama, "ina su hadiza da zainab, ko suna ɗakine?" ɗago kai nayi na kalle shi a fakaice, sannan nace, "zainab ta tafi gida ɗazu, hadiza kuma sai gobe insha Allahu, tana ciki tana waya ne", na faɗa da ƙyar kaman an mun dole, shiru ya sakeyi daga nan baice komai ba, amma kuma idon shi yana kaina, nidai wasa kawai nake da gyale na, ina ji kaman nace mishi sai da safe, haba me za'ayi da mutum shiru, ni shiru shima shiru ae abun baiyi ba, gaskiya M.G bai kyauta mun ba, bayan nagama sakawa raina shi zaice yana sona, amma sai naji wani daban, kuma tsaban banida muhimmanci a fuskan shi nace kada ya nemi sister A.G shine yayi kunnen uwar shegu yaje ya nema, nima daga yau na cire shi a raina, bazan sake tunanin shi bama, nima zan dage da addu'a Allah ya fito mun da wanda nake so, don wannan kam sallaman shi zanyi, ɗago da kai nayi ina kallon shi jin yana mun sallama akan zai tafi gida, da jin daɗi na amsa mishi da "nagode sai da safe" na faɗa ina miƙewa, ganin shima ya miƙe tsaye zai fita, har jikin mota na rakashi, tsayawa yayi kaɗan yana kallona, "me zancewa mummy"? Ɗago kai nayi da hanzari don jin abunda ya ke faɗi, "ka gaisheta" na samu bakina da faɗi, murmushi yayi mai ɗan sauti sannan yace, "inji waye zance mata"? hararan shi nayi a fakaice ina mutsul -mutsul da baki, kafin nace wani abu sai naga an buɗe gate, zuciyata ne naji ya yanke lokaci ɗaya, domin motan Abba ne ya shigo, daga ni har A.G bin motan mukayi da kallo har sukayi parking, ganin haka A.G ya dubeni da murmushi a fuskanshi, "bari ni naje na gaida surukina yasan ni waye yanzu a wurin shi, ki jirani" ya faɗa yana karasawa inda Abba yake fitowa daga motan, kaman an dasani a wurin kuma nakasa tafiya, ina ganin Abba ya miƙa mishi hannu fuska cike da fara'a, amma A.G yaƙi miƙa nashi ya duƙa yana gaida Abba, kafaɗan shi Abba ya ɗan buga yana amsa gaisuwan shi, idon Abba kuma akaina da nake tsaye jikin motan A.G, ganin haka ya saka na ƙarasa inda suke tsayen, hannu Abba ya miƙo mun na ƙarasa jikinshi, "sisto yayah akayi? Ina sauran ƴan'uwankin?" na'amsa mishi da suna ciki, sannan yace ya muka bar A.G a waje bamu shiga ciki da shi ba, ina ganin A.G yana wani sauƙe smilling, sannan yace, "Abba ta shigar da ni parlon hajiya ae, yanzu na fito ne zan kuma gida, saboda Daddy ya shigo gari ina so mu gaisa da shi", cike da farin ciki sukayi sallama da Abba nah, nidai duk a hargitse nake jin kaina, Abba na wucewa na mishi sallama, shidai murmushi yakeyi ya wuce motan shi.
********** Washe gari da wuri hadiza ta kama hanyan Tafawa ɓalewa, sai naji duk gidan babu daɗi, ga ummitah ma ta tafi gidansu tun jiya, hafsy kuma tayi gidan Aunty Rakiya, haka na wuni tare da ummie nah, da la'asaar na shiga side ɗin Mamah don mu gaisa, abun mamaki ina fitowa sai muka haɗu da habiba da raliya zasu fita, daga gani kuma habiba babu lafiya ne, don duk fuskanta ya wani hau, wani zuciyan yace na tsaya mu gaisa, wani zuciyan kuma yace kedai wuce babu ruwanki, ina kallon ta muna haɗa ido tayi mun murmushi, nima sai na maida mata na wuce, duk sai naji ta bani tausayi, gaskiya Aliyu bai kyauta mata ba, da ƙaramin shekarunta ya maida ta bazawara.