Ana barin halal original by anty nice - Chapter 23
Ana barin halal original by anty nice Chapter 23: Ana barin halal original by anty nice Chapter 23. Addu'a sosai yayah muhammad yayo ana binshi da Ameen,…
4,390 words
Addu'a sosai yayah muhammad yayo ana binshi da Ameen, bayan ya gama Abba yayi gyaran murya tukun yace, "Ayshaa ɗago kanki ki kalle ni", haka na ɗaga kai na kalli Abba, "kinsan meya taru mu yau duka anan"? Girgiza kai nayi duk jikina a sanyaye, ƙura mun ido Abba yayi kaɗan har zuwa wani lokaci, sannan ya buɗe baki yace, "sallama da nasiha, sallama bawai na rabuwa ba, a'a, sallama wacce take da fa'idah, take da daraja take da muhimmanci, amma a ƙasanta mai ciwo," ina jin ya faɗi haka na maida kaina kan ummie danaga gaba ɗaya yanayin ta ya chanja, a hankali na maida kaina kan Abba, "munyi farin ciki da murna da Allh ya nuna mana wannan kyakkyawan rana na gobe da za'a ɗaura miki aure, wanda shine sanadin sallaman da zamuyi dake bawai don mun ƙosa da ke ba, ko gajjiyawa, sai dai yadda haka addinin mu ya umurta da muyi, Ayshaa da ace uba yana aurar da ƴar shi, kuma ya basu wurin zama su zauna a cikin gidan shi, a al'adance, tou wallahi Ayshaa kece irin ƴar da irin uba irina zaiyi, tabbas ke ƴace mafi soyuwa a zuciyata saboda halinki da ɗabi'un ki, ni mahaifinki ina miki albishir da cewa na yafe miki a zaman da nayi dake daga ranan haihuwar ki danayi har zuwa ranan da zaki bar hannuna, har ranan ƙarshen rayuwarki, ke ƴar albarkace wacce ta fito a tsatson ƴar aljannah, kinyi dace da mahaifiya ta gari, wacce ta baki tarbiya na gari, wanda shi nake fata Ayshaa ki nuna a gidan auren ki, ki nuna ke ƴar Nana khadijah ce, ki nuna ke tarbiyar Nana khadijah ce, yadda kika zauna lafiya damu, na roƙe ki ki zauna lafiya da mijinki da ahalin shi, yadda kika mana biyayyah kiyi sama da shi wa mijinki, yadda baki taɓa kawo mun ƙorafin kowa ba a gidan nan, don Allah kada ki kawo mun ƙorafin mijinko, don tabbas zan iya ƙinshi, ko mahaifiyar kice kika kawo mun ƙorafinta wallahi zan ƙita a zuciyata ballantana mijinki, ke ƴace lafiyayyah mai mutunta kowa, ina so ki mutunta ƴan'uwan shi da iyayen shi Ayshaa, don Allah kada akawo mun sukanki, kiyi haƙuri ba haƙurin cutarwa ba, idan akwai abunda ya sha miki gaba, ga mahaifiyar ki da ƴar'uwata Rakiya ki tun karesu da shi, na yadda dasu ɗari bisa ɗari zasu baki shawara, kada ki cinye abu a zuciyarki ya illataki irin yadda ya illata ƴar uwarki", yana zuwa nan ya sunkuyar da kanshi ƙasa, yayi shiru. Nidai dama tunda ya fara nake kuka na ƙasa-ƙasa, amma yana zuwa wurin sai sautin kuka na ya ƙaru, hannu yayah muhammad ya ɗaura akaina yana shafa mun, "Eyyah usumanu kada ka raunana zuka tanmu, wannan rashi na habiba ya ƙone ka muma ya ƙone mu Usmanu, ga tafiyar baiwar Allan nan da yazama na farin ciki amma kullum fargaba nakeji a zuciyata na kewan da zaka shiga usmanu am," ta faɗa tana share hawayenta, ɗago kaina nayi don jin muryan yayah Umar yana, "haba ummie ku da zaku mata nasiha da fatan alkhairi cike da farin ciki shime zaku ɓuge da kuka,? Aunty Rakiya don Allah kuyi haƙuri", ya faɗa yana ƙara basu haƙuri.
Shiru parlon yayi na lokaci mai tsawo, sannan Abba ya dakatar da shirun, "Allah ya jiƙan habiba da rahma, Allah ya raya abunda ta bari da imani" gaba ɗaya aka amsa da "Ameen" banda ni kaɗai da na amsa a cikin zuciyata, "Allah yasa duk abubuwan da nagaya miki kiyi amfani da su Ayshaa, Allah yayiwa sabuwar rayuwar da zaki shiga albarka, Allah ya baki zuriya nagari masu albarka," "Ameen" kowa ya sake amsawa, Hajiya ummah Abba yace ta yi mun nasiha, amma fir ta kasa, "usmanu am me zance wanda baka faɗa ba, har ma abunda ni bazan iya ba duk ka faɗa, fata na dai Allah ya zaunar da ita lafiya yadda mahaifiyarta ta zauna da kowan mu lafiya, ae magana ya ƙare tunda tayi dace da uwa tagari irin khadijah, duk da dai dace da miji nagari adali ne ya zaunar da ita lafiya, don babu irinka a duniyan nan usmanu, mahaifin ka sak kabiyo a halin kirki," ta ƙarasa tana ta share hawaye da jan majina. Ummie Abba ya bada dama ta mun nasiha, amma ummie yau kaman ba ita ba, cewa Aunty Rakiya kawai tayi ta mun, haka kuwa akayi Aunty ce ta mun nasiha da jan kunne sosai akan riƙe sirri, da kiyayan ƙawaye da shawara da su, daga nan Yayah muhammad yayi mun, yayah Ahmad ma ya mun, kowa cike da saka mun albarka, amma aminin hafsy da Abba yace saura shi, gyara zama yayi sosai ya ƙira sunana da ɗan ƙarfi, har sai da na ɗaga kai na dube shi, "Abin ƙaunar kowa da kowa a gidan nan, nidai abun da zan gaya miki shine, HAƘURI! HAƘURI!! HAƘURI!!! BIYAYYAH! BIYAYYAH!! BIYAYYAH!!! TSAFTA! KULA DA GIRKI! IYA MAGANA! SUN DANGIN SHI! wanda duk nayi imani da Allah kin samu training akan su sosai, na ƙarshw duk wanda ya ɗaga iki yatsa ki sanar dani, idan baiyi hankali ba sai na harbe shi, don da a taɓa mun ke, gara a ɗaga garin bauchi da kewaye, atou gara a san da haka", ya ƙarasa kowa yana ƙyalƙyalewa da dariya, ranƙwashi Ummie da ke kusa da shi ta kai mishi tana cewa, "kaji sarkin hankali babban kobo kawai". Dariya shima yakeyi yace, "tou ummie nah idan ba haka nayi ba duk kun raunana mana zuciya, nida nake soja ƙarshe nayi abun kunya na ɓuge da rabza kuka, don ina ganin Abba namijin ƙoƙari yayi bai fashe da kuka ba", duka dariya sukeyi banda ni dana kwantar da kaina akan cinyar yayah muhammad inata share hawaye nah. "aiko zuciya ta sanyaya kaɗan umaru ɗan albarka, ae ni ba ƴan pamilyn mijin nake so ka harbe wa ƙafa ba," sai ta ɗanyi ƙasa da murya tace, "hauwa munfukar gidan nan zaka harbewa ƙafa don ranan har parlor na ta biyo A.G tana kai sukar uwarku, laɓewa nayi a jikin ƙofa da naji alaman shigowarta, amma da yake Aisha tayi kalan sokaye shiru naji bata gaya mun abun da ya faro ba, shiyasa naƙira ƙanina kawun babanku masaka ayita sauƙan qur'ani, duk sharrinta ya koma kanta, ita ta sani munafukar kawai", hajiya umma ta faɗa tana ƙasa da muryah. Abba ne yace "shine ba'a gaya mun ba"? "Tou wani abu zaka iya wanda bakayi shi ba abaya usmanu? Kawai nagama koai tunda na haɗata da Allah, kuma zaiyi maganinta", ta ƙarasa tana hararan Abba da yayi shiru baice komai ba.
Haka dai muka tafi muka barsu a parlon shi da su yayah muhammad.
********** Washegari saturday A babban masallacin ƙofar fada aka shaidah ɗaurin auren *AMINU GARBA INUWA (A.G) DA AYSHATU USMAN UMAR (U.U)* sai kuma
*MUKHTAR GARBA (M.G) DA HEEDAYAH GARBA INUWA* Runtse ido A.G yayi a zuciyar shi ya furta. "*ALHAMDULILLAH*" ido suka haɗa da M.G, murmushi yayi mishi, shima M.G ya mayar mishi murmishin idon shi cike da ƙwallah, amma fuskar shi ɗauke da murmushi, lumshe ido yayi ya cigaba da sauraran abun da akeyi, Daddy ne mutum na farko daya miƙa wa A.G hannu suka gaisa, yana congratulating ɗinshi, sannan suka haɗa hannu da M.G, sun kuyowa A.G yayi saitin kunnen M.G yace, "yayah kaman kafin ɗokin wannan rana? Naga har hawayen farin ciki kake shirin zubarwa" M.G bai iya yace mishi komai ba har jama'a suka fara miƙa musu hannu ana taya su murna, daga nan suka wuce inda zasuyi recieption. Alhamdulillah komai ya tafi musu yadda sukayi fata, ana idar da sallan azahar suka shiga gida da abokansu suka gaida Mummy da ƙawayenta, ghotographer ya musu pics sosai, nan A.G ya haɗa rai wai M.G da tashi amaryar shi kuma tashi tana gidan su, haka dai suka gama daga nan suka ɗunguma sai gidan Goggo, nan ma sun haɗu da dangin M.G na fannin goggo da na baban shi da suka shigo, nan ma anyi photona sosai, daga baya suka dingayi da yayunshi da iyalen su, don hattah yayah auwal yazo ƙasan da matan shi da yaran shi, auren autan su mukhtarin goggo.
A gefen mu tun safe nasha wanka da ado da wata super ta mai kyaun gaske, an mun ɗauri mai kyaun gaske, gefe ɗaya kuma an kawo mun sabeer ɗina mun sha gayu sai photona mukeyi, dawowan su yayah daga ɗaurin aure suka mun chaa da tsokana har sai da nayi kuka, yayah muhammad ne ya rarrashe ni ya saka naje na ƙara chanja kaya, shaddah na saka gedzner mai kyau, tasha adon ɗinki sosai, photona mukai tayi wuri dayawa ina rungume da sabeer, duk rauni ya cika mun zuciyata, haka akai ta hoto har da su Abba da familyn shi da suka zo, daga baya Abba ya ƙora kowa na gidan akayi family picture a parlon shi, hannu na ɗauke da sabeer ɗina.
Ana idar da sallan la'asaar akace a fito kai amaryah, don dama an shiryah don Abba yace ana idar da sallah za'a tafi, suna da buɗan kai da hawa.
Atamfah ta holland mai ktau nasaka, sannan aka nannaɗeni da lafayan da Aunty B ta kawo mun wani fari mai ratsin Red ajiki, atamfah ta kuma red ce. Goggo da Aunty rakiya sai Adda ne suka kaini ɗakin ummie, inda take tare da ƴan'uwanta da ƙawayen ta, har ƙasa na durƙusa a gabanta, Bayan an buɗe taron da addu'a Aunty Rakiya tace, "tou matar yayah ga ɗiyata na kawo miki kuyi sallama ki saka mata albarka, ki yafe ta kimata fatan shiga gidanta lafiya", murmushi ummie tayi ta dube ni, a hankali muryanta na rawa tace, "tou ni me Ayshaa ta mun a rayuwan danayi da ita? Albarka na kuma kullum ae yana tare da su", kaina na mayar kan cinyarta na kwantar ina sheshsheƙan kuka, abun mamaki kawai sai aka ga ummie na kuka, "haba Addah ke da zaki rarrashe ta kuma sai ki ɓuge da kuka"? Goggo ta faɗa tana ɗago ni tsaye akan mutafi, hannun ummie na riƙe, ina jin ta itama ta riƙe ni gam-gam, haka dai aka lallaɓa mu muka fice.
Side ɗin hajiya ummah mukaje itama kukan dai tayi tayi tana saka mun albarka, daga nan sai wurin mamah, itama ban kwana na mata tayi ta jero mun addu'a da saka albarka, daga nan aka wuce dani ɗakin mamie, achan najiyo sautin kukan sabeer, sai naji duk zuciyata babu daɗi, haka na daure na tsuguna a gabanta, itama yadda akayiwa su ummie haka aka gaya mata, hannunta ta saka ta riƙo duka hannaye na ta riƙe su gam acikin hannayenta, addu'a take mun da fatan alkhairi, amma gaba ɗaya jina nake kaman na zabga ihu, saboda wani irin matse mun hannaye da tayi da ƙarfin gaske, wanda har sai da naji hannayen mu suna fitar da zufa nida ita, saboda babu space ɗin da iska zai shiga, adda'a tayi ta ja, daga baya kuma ta miƙar dani ta rungume tana muyafi juna, hannu Aunty Adda ta saka ta ɗago ni a jikinta muka fita, hannu na kai sai tin hanci na nashaƙi wani warin da naji yana mun kaman na jan miski, ni tun asalina bana son warin shi, sai naji kaman miski kaman kuma wani ƙarni-ƙarni yake mun, muna shiga parlon Abba na goge hannun a jikin cottons ɗiɓ parlon da dabara, amma dai har jikin lafayyah na ina jin yana warin abun. Muna shiga naje na durƙusa a gaban Abba, kuka nakeyi sukuma sunata mun addu'a da nasiha, a ƙarshe Abba yace muwuce kada mu ɓata musu lokaci, kafaɗu na ya riƙo na miƙe tsaye, hannun shi ya saka ya riƙoni muka wuce har waje, motan da aka kawo na ɗaukan amarya Abba ya umurci su goggo da wasu a family su shiga, motan shi ya saka yayah muhammad ya matso mishi kusa da mu, baya ya buɗe ya saka ni, sannan shima ya shiga, ya umurci Aunty Rakiya ta shige gaban nashi motan.
Duk ƴan kai amarya ya saka suka wuce, muka bi su abaya, ashe kafin mu isa yasaka yayah Ahmad ya taho tare da A.G, masu rakiya dukka side ɗina suka wuce, mu kuma muna isa A.G suka fito a parlon shi suka tarye mu shida yayah Ahmad.
Muna shiga A.G ya rusuna yana nunawa Abba wurin zama, kujeran da Abba ya zauna ya manna ni a gefen shi na zauna, shi kuma yana rungume dani a kafaɗan shi, daga nan duk su Aunty dasu yayah suka nemi wuri suka zauna, shiru parlon ya ɗauka bayan an gama gaisuwa, ƙurawa A.G ido Abba yayi har zuwa wani lokaci mai tsawo, har sai da A.G yayi kaman ya koma ƙasa ya zauna, saboda ƙasa zai zauna Abba ya hanashi ya saka shi dole ya zauna kusa da Yayah Ahmad, duk sai A.G yaji kallon ya na tayar mishi hankali, har sai da Abba ya gama kallon shi na wani lokaci mai tsawo tukun yayi gƴaran murya yace,
"Aminu"! Ɗago da kai A.G yayi a nutse ya amsawa Abba da "na'am ranka ya daɗe"! Ya maida kanshi ƙasa yana ƙara risinawa, ido Abba ya maida kan Yayah Ahmad yace "buɗe mana wurin da addu'a", addu'a sosai yayi daya gama, Abbah yayi gyaran murya yace "A.G ga Ayshaa ƴata da ka nemi aurenta akan ka ganta ta maka kana sonta, ka zaɓeta akan ta zame maka uwar ƴaƴanka abokiyar rayuwarka right"? A.G ya ɗaga kai ya amsa da ehh, "a'a ka buɗe bakinka ka amsa mun" Abba yace mishi, "hakane Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma," A.G ya faɗa. "good, nakawo maka Ayshaa da hannu na ba saƙo ba, na kawota na danƙa amananta a hannun ka Aminu, na kawo ta na baka amanan ƴata mafi soyuwa a zuciyata, ƴata da idan an taɓa tou tabbas an taɓa zuciya da rayuwar usman" Abba ya faɗa yana nuna kanshi da hannun shi, hakan yasaka dukkan su suka sunkuyar da kansu ƙasa suna jijjiga mishi kai. "Ayshaa amana ce a wurinka Aminu, haka kaima amana ne a wurinta, kuma na jaddada mata ban yadda ba ban ƴafe ba idan tayi wasa da amananka da yake kanta, ban yadda ba ta ƙunsa ma baƙin ciki, ban yadda ta ɓata maka ba sai a bisa kuskure, haka kaima, Nakawo maka Aysha ne da sharaɗin ban baka aurenta don ka wulaƙanta mun ita ba yadda dayawa maza sukeyiwa matayen su a yanzu, ban yadda ka dakar mun ƴa ba, ban yadda ka kashe mun ita da baƙin ciki ba, idan Ayshaa tayi kuskure ka hukunta ta yadda addini ya tsara, amma dis time around duk wanda na bashi auren ƴata ya tozarta tou wallahi zanyi mishi hukunci daidai da abinda yayi, idan mutum yaji ƴata ya gajji da ita, tun wuri ya ɗauko ta a mutunce yadda nakawo mishi ita ya kawo mun abata,babu duka babu zagi". Sannan ya tausasa muryan shi ya cigaba, "Aysha ta samu tarbiyan da nayi imani da Allah ko bayan ranmu bazata bamu kunya ba, haka kaima nake kyautata maka kyakkyawan zaton na bawa ƴata miji nagari ɗan manyan mutane, na roƙe ku ka haɗa kanku ku zauna lafiya, daga nan Abba ya dinga haɗamu yana mana nasiha mai ratsa zuciya daga ƙarshe Aunty ma tayi mana, inda take gayawa A.G, bawai Abba bai yadda da tarbiyan shi bane ya kawo ni har yaja mishi kunne, a'a yayi hakane saboda karin magana da hausawa suke cewa, *IDAN MACIJI YA SAREKA.......* idan kaga tsumma dole ka kiyaye, saran da Aliyu yayi mishi ne yake firgice da shi, nan A.G ya nuna shi hakan ma yayi mishi, kuma ya ƙara jin aranshi Diamond mai tsananin daraja da tsada ya ɗauko, kuma yayi alƙawari da ƙarfin shi da lafiyar shi da komai nashi zai kare Ayshaa, insha Allah sai kowa yace gara da akayi.
Tashi Abba yayi tsaye ya ɗagoni muka tsaya, nidai ban da kuka babu abinda nakeyi, domin nasan Allah ya mun komai na rayuwa, ya bani gata na iyaye nagari, ƴan'uwa nagari , dangi nagari, kuma duk maso ƙaunata, gashi yanzu ya bani miji Nagari, mijin marainiya mai ƙaunata, Abunda zan nema kawai Allah ya zaunar dani da shi lafiya ya bamu zuriya ta gari, hannu Abba ya miƙawa A.G, da sauri ya ƙaraso gaban Abba amma yakasa bada hannun shi, har sai da Abba ya rungumu shi, hannuna ya cire a nashi ya ɗaura akan na A.G, ae kuwa da hanzari ya riƙeni sosai, "Aunty nice nidai aduniya ban taɓa jin wani halittah na ɗa namiji daya taɓa riƙe hannu na bayan Abba dasu yayye na, gashi dai ɗabi'ace ta yayuna su rungumo mu, especially ma ni, Abba ma idan munje gaishe shi sau dayawa hannun shi yake miƙowa mu gaisa, amma ko yayah ishaq bamu taɓa riƙe hannun shi ba saboda kiyaye wa, amma nidai ban taɓa jin hannu mai laushi ba irin na A.G, har tsoro naji a zuciyata nace, hala taurin nawa hannun zaiji, saboda laushim da hannun shi yake da shi banyi tsammanin akwai maza irin haka ba a duniya", Nidai murmushi nayi ina bin hajiya Aysha da ido, matse hannuna yayi cikin nashi, ina jin yadda hannun shin yake rawa, a haka Abba ya sake jaddada mishi amanan da ya bashi, sannan ya umurce shi daya sada ni da ɗakin shi, ina jin Abba yana zame hannun shi ajikina na zabura zan chafko shi, amma sai naji A.G yasaka dukka hannayen shi ya riƙe ni, ae kuwa da sauri na ƙara fashewa da kuka murya a sama nace, "Abba na kada ka tafi ka barni," amma sai abba ya dafa kaina ya ƙara saka mana albarka yayi hanya fiya daga parlon, aeko da ƙarfi na ɗaga murya nace, "Abba sisto ka zaka bari da wani"? Tsayawa Abba yayi chak a bakin kofan, ganin haka Aunty Rakiya ta ƙarasa ita da yayah Ahmad suka riƙe shi suka fice a parlon batare da ya juyo kaina ba, maida kallona nayi kan yayah muhammad da zaibi bayan su nace, "besty kada ku tafi ku barni tsoro nakeji", shima ɗan murmusawa yayi kaɗan bai kai chan ciki ba ya juya yayi waje batare da yace uffan ba, da sauri na maida kaina kan A.G, bakina har wani ɗan ɓari yakeyi nace, A.G nikan kabar ni na biso, tsoro nakeji", Hmmm A.G duniya ne, kawai Jawo ni yayi ya buɗe ƙofan ɗakin shi ya shige dani, muna shiga kuwa ya rungumeni tsaf a jikinshi bai bani amsa ba tanbayan da nake ta mishi na ina zai kaini ne? Kuka na fashe dashi kawai mai ƙarfi, idan banyi ƙarya ba yakai sama da mintuna Goma muna a haka, har sai da aka ƙwanƙwasa ƙofan tukun naji muryan shi ƙasa -ƙasa yana tambayan waye? "Hudah ce yayah", ajiyan zuciya ya sauƙe, bai kuma ɓalle jikin shi da nawa ba yace, "meye ne kuma Hudah"? "Mummy tace amaryar ka kaita za'a shiryata saboda buɗan kai, su Yayah M.G duk sun shiryah", tou kawai ya amsa mata da shi ta juya ta fice. Ina jin shi yayi tsaki yace "duk fitar M.G ne wallahi da wasu bidi'a, an ɗaura aure an kawo amaryah kuma meya saura ne nikan? Basai a haƙura da bidi'an da baida wani dalili ba? Hala Ƴan rakiyan kawo amaryan ma Abba ya kafa su sun tafi".
Nidai da sauri nace, "wallahi suna nan, ina jin muryan su ma" shiru yayi baice uffan ba, kuma bai sake ni na tafi ba. A tsorace na sake cewa, "mummy tace mu shiryah da wuri fa", still dai bai kulani ba, shidai ya manna kanshi shi a saman kafaɗa ne, chan naji shi kaman mai barci yace, "ko na ƙira Abba ne nagaya mishi suna nan basu tafi ba, don nasan yanzu zai umurcesu su tafi, mummy kuma babu matsalah Daddy ya isheta ta ƙyale mu da maganan bidi'an nan". da sauri na har da fashewa da wani sabon kukan nace, "wallahi nayi burin bikina ya zama akwai buɗan kai da hawa, udan ba'ayi ba za'a mun dariya, kuma bazan taɓa daina damuwan rashin yin ba", aiko ina faɗin haka da sauri ya juyo dani ina kallon shi, dukkan hannun shi zube akafaɗa na, tsoro naji yadda naga udon shi a lumshe kaman bazai iya ganina ba, a raunane ya buɗe baki yace, "zan shirya muje, zanyi abun da kike so, ai naji ance ba haramun bane ma, amma don Allah ana gamawa su tafi kinji beauty", da sauri nake ɗaga mishi kaina alaman naji, nan kuwa ni kaɗai nasan wani irin masifaffen tsoron da nake ji a ƙasan zuciyata, har ƙofan da zai fitar da ni daga sashen Shi ya rakani, yana riƙe da dukkan hannaye na ya ƙira Hudah, tana zuwa yace ta wuce dani side ɗina na shiryah, da sauri kuwa ta amsa mishi, dukka hannayenta ta saka ta riƙoni muka fice, a parlor na muka samu su Aunty Rakiya da sauran ƴan'uwa, nan ta riƙe ni muka wuce ɗakina, inda aka fara mun shirin fita wurin buɗan kai da za'ayi a haraban gidan su A.G. Wurin buɗan kan ya cika maƙil da ƴan'uwa da abokanan arziki, gefen mu M.G ne zaune da amaryar shi, sun sha ankon blue shaddah shida A.G, haka wurin ɗaurin aure sunyi ankon white shaddah, gefen shi Heedayah ce zaune fuska a rufe, nima gefen A.G aka zaunar dani, M.G ne yafara buɗe fuskan amaryar shi, bayan ya liƙa mata kuɗi ya koma ya zauna, sannan A.G ya tashi ya biɗe nawa fuskan, ina jin shi yana liƙa mun kuɗi yana ɗan taka ƙafana a hankali, haka na share shi dai ban motsa ba.
ƴan uwana da nashi suna ta aikin liƙa mana kuɗi, gefe ɗaya ma ƴan'uwan M.G suna ta liƙa musu, Yayah Ahmad ne ya shigo shida wani aboki, M.G suka fara liƙawa, sannan suka dawo kanmu, liƙa ma A.G yayi, amma daya dawo kaina key ɗin mota ya ɗaura mun a tafin hannu na, aiko gaba ɗaya fili ya ɗauki tafi, har sai da A.G ya miƙe tsaye ya rungume yayah Ahmad, M.G ma tashi yayi ya rumgumeshi fuskan su duka cike da farin ciki, hannu A.G ya miƙo kan cinya na ya ɗage key ɗin, aljihun shi ya saka, gaskiya buɗan kan ya ƙawatar, ko dan motan da nasamu abun ya mun daɗi sosai.
Daga nan motoci ne suka ɗauke mu zuwa kallon hawa da zasuyi, shima hawan babu laifi yayi kyau sosai, ni dai dayake bai dame ni ba ko kaɗan, so ba wani burgeni sosai abun yayi ba, A.G nah yayi kyau da shigan da yayi, a ido na ma kaman yafi kowani namiji a wirin kyau.
Zuwa ƙarfe 10:00pm na dare dukkan jama'a sun watse, kowa ya kama gaban shi an gajji da ganin gidan amaren, haka ƙawaye da dangi duk sun tafi gida, daga ni sai hadiza da zainab, sai hafsy da Aunty j da suke jiran yayah Ahmad yazo ya ɗauke su, sun ƙara gyara gidan sun saka turaren wuta, ko ina ƙamshi mai daɗine yake fita, nima daidai lokacin na fito a wanka, Aunty j tana tayani kintsawa sai ga yayah ya ƙirata akan su fito yana waje, batayi saurin fita ba sai dana shiryah acikin wata doguwar rigar atamfah mai kyaun gaske, ta gyara mun fuska da ɗan light make-up, ta yafa min gyale ya rufe mun fuska bayan ta fesa mun turare duka jikina, ina jin su duka suka fita suka barni ni kaɗai, nidai ban iya nace musu komai ba sai hawaye na da nake sharewa, ga wani irin fargaba da nakeji yana cika zuciyata, bayan wasu ƴan lokuta masu ɗan tsawo sai naji an buɗe ƙofan ɗakin baki cie da sallama, A.G ni ya shigo ina jin shi ya mayar da ƙofan a hankali ya rufe, ya ɗan daɗe kaɗan abakin ƙofan, daga baya kuma sai naji takun tafiyan shi yana shigowa cikin ɗakin, duk wani sautin takun shi haka nake jin sautin bugun zuciyata, kafin ya ƙaraso na haɗa wani uban zufa kaman nayi gudun ceton rai.
Zama yayi a bakin gadon ya ƙura mun ido, chan kuma ya saka hannun shi ya yaye lulluɓin kan, runtse idona nayi naƙi kallonshi, ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan ƙarfi kaɗan, sannan ya sunkuyo da kanshi saitin fuskana ya sumbaci goshina, "*MARABA DA KYAKKYAWAR SALIHAR MATANA, MARABA DA RAYUWAR A.G, MARABA DA HASKEN ZUCIYA DA GIDAN A.G, MARABA DA ƊAWISUN A.G*" ya ƙarasa faɗa yana haɗa fuskanshi da nawa, nidai har lokacin ido na duk suna kulle, sai hawaye ne kawai suke bin kumatuna, harshen shi ya saka ya fara lashe hawayen, hakan da yayi ya sakani fashewa da kuka, shiru yayi ya dakata da abun da yakeyi, muryah a hargitse yace, "Eeshan A.G meyake faruwa? Kukan kewan su ummie ne ko kuma na farin cikin kasancewa da A.G? Idan na kewa ne nima na koma gefe nayi tagumi na kewan mummy nah, idan na farin cikine don Allah ki jirani muyi tare".
Ido na duka na buɗesu akan shi, wai kukan farin cikin ganina a gidan shi? Lallai ma, shi bai san kewan ƴan'uwana da iyaye na nakeyi ba ko? Rufe idona na sakeyi na ƙara sautin kukan, rungumoni yayi jikin shi sosai ya na lallashi na, da kyar dai ya samu nayi shiru, daga nan ya kamo hannu na muka fita zuwa parlor.
Kan kujera ya zaunar dani ya kunna mun T.V, sannan ya dawo gefe na ya zauna hannun shi riƙe da nawa yace, "kiyi kallo zanje nayi wanka na dawo, zaki bani labarin abunda kika kallah, ko zaki rakani nayi wankan"? Juyar da kaina gefe ɗaya nayi na ƙi kallon shi, murmishi yayi ya miƙe ya wuce side ɗin shi, yakai kusan 45mns kafin ya dawo parlon cikin wasu white kayan bacci, three quater ne da riga armless, sai wani ƙamshi a hankali da yake tashi a jikin shi, kitchen ya wuce ya ɗauko ledan da ya bansan lokacin da ya kai kitchen ba, a saman tray ya ɗauro da filet da cups, ƙamshin kajin ne ya cika parlon wanda jin hakan yasaka ni wani mummunan faɗuwar gaba, wanda har sai da naji alaman kaman fitsari ya ɗan biyo jikina, ɗan gyara zama nayi ina mamakin tsoron da nakeji mai sakani mummunan faɗuwar gaba irin haka, duk yadda yayi naci naman nan kasawa nayi, daya takurani ma kuka nasaka mishi, haka ya haƙura yaci naman yasha jus ɗin shi, daga nan ya tattare su ya wuce ya kai kitchen.