Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 10

Arman maleek book 1 complete - Chapter 10

Arman maleek book 1 complete Chapter 10: Arman maleek book 1 complete Chapter 10. sun dade sosai suna fira, kafin Rayhana ta an kare da basu dawo da…

4,476 words

sun dade sosai suna fira, kafin Rayhana ta an kare da basu dawo da Sadiyyerh ba, kallon Mijinta tayi tace "Abbu ina Sadiyyerh ban ga shigewarta ciki ba ?", "Sadiyyerh kuma ?", ya fada yana duna bayanshi dan shi yama manta da ita kwata-kwata, "ai ba tare da ita muke ba ko ?", ya fada yana kallon su Zayn, jinjina kanshi yy yana kallon Rayhanar.

"Tun dare fa da suka fita da Yaaah Shehi bata dawo ba, duk mun dauka kuna tare har yanzu", Yaah Shehi ne ya ƙara fitowa cikin wani shirin fitar, kallon Rayhana yy yace "Sadiyyerh fa ?", ya fada yana dan shafa gashin girarshi mai yawa .

kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Rayhana da Ayyana da Yaah Shehi, "Kamar ya Sadiyyerh fa ?, Sadiyyerh ba tare kuka fita ba ,yanzu ka dawo kace ina take, mai kake nufi ?", Ayyana ta faɗa tana kallonshi cikin ruɗu, gyara tsayuwarshi yy yana kallonta, sai dai ya kasa cewa komai , "kamin magana ma, ya zaka yi shiru ?, kar fa kayi musu sakaci da rayuwar Ƴa", ta fada tana kallonshi.

Ciki Ayyana ta yi ta shiga bincika gidan ko tana wani guri, gaba daya gidan ta bincike bata ganta ba, dawowa palon tayi gaba daya fuskarta ta bayyana zallar tashin hankali, "Sadiyyerh fa bata cikin gidan nan", kalmar da ta daki dodon kunnen Yaa Shehu kenan, da sauri ya ware manyan idanunshi da ya lumshe, gaba daya yan cikin palon suka miƙe suma hankalinsu ya fara tashi, gaba daya waya suka fara bubbugawa, Amma Yaah Shehi na zaune kamar butunbutumi bb wani alamu da ya bayyana akan fuskarsa wanda zai nuna maka cewar yana cikin damuwsa ko ya damu da abun da yake faruwa.

Idanun Ayyana da suka yi Jaazir ra watsawa Yaah Shehi, suna haɗa ido yy maza ya dauke idanunshi daga cikin nata, dan yy bala'in jin fargaba da bugun zuciya lokacin da ya kalli cikiin idanunta, "baka damu ba ko ?", ta fada tana kallo shi, bai ce mata komai ba, haka zalika bai kalleta ba, "Wallahi tallahi Maleeq wani abu ya faru da Sadiyyerh sai ka raina kanka, tunda kai taƙamarka Isgilanci da Wulaƙanci tare da rashin nuna damuwa , ace matarka ta Sunnah ka fita da ita amma ba zaka yi tunanin dawowarta ba, har kana ma da kwamciyar hankalin da zaka saki jikinka gar irin wannan lokacin amma bata gida baka san yarda take ba ?, Wlh tirrr da wannan halin naka, in haka Malunta da Sarauta take Tirrr da ita, bb kulawa ?, babu tausayawa ?, bb jin ƙai ?, bb nuna soyayya ?, damuwa bb , sauke haƙƙi ma babu, to me ne ne amfanin Auren tunda dukkan wani haƙƙi nata haka ƙoƙarin saukewa, dole zaka rabu da ita tunda kai baka da Ɗabi'ar Arziki", tana fadar haka ta fice idanunta sun ƙara mugun kaɗawa.

sanyayyan numfashi ya fesar yana mai lumshe idanunshi, tare da cusa yatsun hannunshi cikin kanshi, yana shafawa a hankali, akan fuskarshi ba zaka taɓa hango wani abu mai kama da tashin hankali ba, ko kuma wani alamu mai nuni da cewar akwai wani abu da yake damunsa ba", duk ficewa suka yi daga cikin Palom zuwa waje, kai tsaye gidahen TV .Radio . da Jaridar Saudia suka nufa domin bada sanarwa, cikin abun da bazai wuce 1 hour ba gaba daya Garin Saudia da makwabtansu suka dauki labarin Ɓatar matar Yaah Shehi Arman Maleeq , ko ina ka shiga cikin Social media zancen ake.

Yan sanda ma sun fara aikinsu na nemanta, bayan gama sun gama bada dukkan wani rahoto suka dawo gida, in da suka bar Yaah Shehi nan suka dawo suka sameshi, ko motsawa bai yi ba, "Anya kuwa kai mutum ne ?, anya kana da zuciya a jikinka ? kai gaba daya baka san damuwa ba ?, bakasan raɗaɗi ba ?, Wlh ka chanja halayenka dan basa sa kyau kwata-kwata ", tana gama fada ta wuce sama.

sosai Yan sanda suka shiga yawon nemanta, amma dakyar suka sameta, a Anguwar da take kusa da tasu, dan ko a ƙafa sai a gangare daga Anguwarsu zuwa chan din. kai tsaye suka nufo gidan da ita, Zayn-maleeq da su Sayyid sun fito zasu fita, suka yi kiciɓis da Yan sanda , Sadiyyerh ya bayansu ,suna tafiya "A ina kuka samota ?", Zayn ya fada cikin karajin murna, da gudu suka fito daga cikin palo , sakamakon muryar Zayn da suka ji cikin munar yana furta cewa "Ina kuka samota", da sauri Ayyana ta rungumeta tana furta "Alhamdulillah. Sadiyyerh ina kika shiga haka ?", ta fada tana kallonta da dukkan farin cikin kan fuskarta "Anguwar da take bayanku", kai tsaye Dan sanda ya basu Amsa, "kai Amma fa mun gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi", ta fada cikin murna, godiya suka shiga musu, Zayn ne ya fiddo kuɗi ya basu ya musu godiya, Jan hannunta Ayyana tayi tana tambayarta, sai dai bb Amsa sai idanunta wanda suka jeme suka koɗe saboda kukan da ta ci take juyawa,lokacin da zasu shigo palo Yaah Shehi ya shigewarshi Abunshi.

"Yanzu Yaron nan dagaske bai damu ba, ya shige ciki ko murna bb ?", Ayyana ta faɗa cike da jin haushn Yaah Shehi, "shiga ciki ki watsa ruwa ", Ayyana ta fada tana sakin hannunta, jujjuya kanta tayi tana cewa "Ayyana bana s......

Kumin Afwa don Allah🙏.

Ya hutun Weekend hope dai kowa yy Enjoy Weekend dinshi Qlau ? [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 20*

Jujjuya kanta tayi hawaye na cika idanunta, miƙewa tayi tana laluɓe ta hau sama, ɗakinta ta bude ta shiga, kan bed ta faɗa ta ci gaba da kukanta, kamshin turarenshi ha Huge Boss ne ya fara cika mata hanci alamar yana very cloth da ita, bata ɗago kanta ba, sannan bata daina kukan da take yi ba.

A hankali ya fara takawa zuwa cikin ɗakin idanunshi na kanta, har ya ƙaraso gurin da take bata ma san ya matso sosai ba, zama yy gefenta, tare da birkitoto ya zamana tana kallom sama daga riginginan da tayi.

tallafo fuskarta yy yana kallonta, kallon fuskarta yake, yana kallon yarda hawaye suke zuba daga cikin idanunta,fisge fuskarta tayi daga riƙon da yy mata, hannunshi ya ƙara kai wa da niyyar taɓata, jajayen idanunta ta bude tare da watsasu akan fuskarta, shi dai bada ban kar ya faɗa ba dai-dai ba da sai yace har wata wuta-wuta ya hango tana ci cikin idanunta, cikin tsanar da ya gani miraran cikin idanunta tace "Kar ka sake hannunka ya taɓa jikina", ta fada tana juya ba, hannunshi ya daura kan kafadarta, janye hannunshi tayi ta wancakalar dashi, miƙewa tayi da niyyar barin ɗakin.

da sauri ya riƙe waist dinta, wata kalar juyowa tayi, zai yi mgm ta ɗaga mishi hannu, ido rufe ta fara cewa "bana son ka ƙara taɓani , kaje chan karuwar da ka ajiye ka ringa taɓata Mtswww", ta fada tana juyawa, wani irin fisgota yy, yana kallon cikin idanunta.

da sauri ta dauke idanunta , ta fice daga cikin ɗakin, kai tsaye ɗakin Ayyana ta nufa, jij karar takowarshi zuwa cikin ɗakin yasa ta rufe tare da sanya key, jikin ƙofar ta tsays tana wani irin kuka sosai, numfashinta har sarkewa yake.

Haka aka ringa yi tsakanin Yaah Shehi da Sadiyyerh , da yazo guri take tash, yanzu bata sonshi bata son ganinshi, tun bb wanda ya fuskanci hakan har kowa ya riga ya gane, amma kuma bb wanda yy musu magana, a cewarsu in ta ishesu sun faɗa. Gently ya shigo Palon yana samye da Alƙyabba Baƙa irin ta manyan Mallumma, kanshi na sanye da hirami da makawuya, idanunshi liƙe da wani siririn glasses irin na Mallumma, yana tafiya a hankali kafarshi sanye da Cover shoes , yana tafiya yana baza kamshin turaren Huge boss mai masifar kamshi da sanyaya zuciya.

da Sallama a bakinshi ya shigo palon, a zaune ya tarar da Umma Jakadiya, Ayyana, Zayn-Maleeq, Sayyid-Maleeq, Abdul-Maleeq, Anty Rayhana, Yaah Muhammad , Yarsu Amnah , Amaturrahman, Amatul-Azeez , Sadiyyerh, gaba dayansu suna cikin palon suna hira , yana shigowa Sadiyyerh da rake sanye da wata Abaya Blue black , gashin kanta da yake gyare wanda Ayyana ce ta gyara mata shi, ta sanya mishi hula ,Tsumewa tayi , tayi shiru tana kaɗa kafafunta.

tana ɗaga idanubta suka yi ido biyu sai ta dauke kanta, a hankali ya shiga takawa zuwa inda take, zama yy yana tattare Alƙyabbar jikinshi, yana zama ita kuma ta miƙe tare da yin sama, gaba daya binta da kallon suka yi, banda Yaah Shehin da yasan dama hakan ce zata faru, izuwa yanzu kowa ya fara ganin laifin Sadiyyerh kuma, sun san yanzu Yaah Shehi Sulhu yake nema tsakaninsu, amma taƙi , kuma daɓa ba tun yau suka san taurin kanta da kaffiyarta ba, bata da saurin fushi, amma tana da wahalar saukowa gata da muguwar ƙafiya da riƙo .

zaka iya mata abu ka manta amma ita bazata manta ba, sai tace *in maye ya ci ya manta, Uwar Ɗa bata manta ba*, sai dai kafin suga irin wannan fushin nata ana dadewa, dan ko tana fushi da kowa bata yi da Yaah Shehi, kuma da yazo yace mata abar wannan fushin da faɗa shi kenan ta barshi, amma gashi yau ita take yi dashi.

bb wanda yace da ita ko shi komai, yana kallonta ta ƙasan ido har ta haye sama .

ruf ya rufe idanunshi , hannunshi na kan gemunshi a hankali yake dan jaa kamar mai cire wani abu, haka yake zaune gurin daya, Ayyana ma da ke fushi take da shi sai ta tashi tayi tafiyarta, Yah Muhammad ne ya matso kusa da Yaah Shehi, cikin yin ƙasa da murya yace "Shalelen wai mai kawa Kanwata da Ayyana ?, naga muna fira suna ganinka suka shige ciki", ya fada yana kallonshi, shiru yy baice komai ba, "Matsalata da kai faɗin rai ", ya fada yana harararshi.

bayan gama jin duk abubuwan da suke faɗa ya miƙewarsa, tare da hayewa sama.

11pm ya shigo cikin gidan hannunshi riƙe da wasu manya-manyan Ledoji masu dauke da Tambarin *Al-Ihsan Fashion Design* . A hankali yake taka steps din benan har ya isa sama, kai tsaye bedroom din Sadiyyerh ya nufa, a hankali ya fara kwankwasawa, daga ciki yaji sautin maganarta tana cewa "Waye ?", chan ciki yace "Uhmmm",wani dogon tsuka ta jaa kafin ta ƙara gyara kwanciyarta. ba kaɗan ba Yaah Shehi yaji zafin wannan tsuka da ta mishi dan har cikin ransa yaji, yasan dan tasan ya tsani wannan tsukar shi yasa tayi, yanzu duk wani abin da tasan baya so shi take ƙoƙarin aikatawa, saɓanin da da duk abun da baya so bata yi.

Har ya juya suja haɗu da Umma Jakadiya, murmushi ta sakar mishi, a hankali ya dan loma bakinshi, yana kallon ledar hannunshi, "gashi!" ya miƙa mata yana barin gurin, numfashi ta sauke tana jaddada zuciyar Sadiyyerh, koma mai ya mata yanzu ai ya isa ace ta huce sa boda yarda yake bin kanta, amma taki, "Yarinyar nan nason yin Amfani da damar da Allah ya bata", ta fada tana nufar cikin ɗakin,bugawa ta shiga yi, amma babu amsa, daga chan ciki , cikin tsuka Sadiyyerh tace "wai waye ?", ta faɗa cikin faɗa-faɗa "Uwarki ce sai ki buɗe ki bugeni", ta fada cikin kufuluwa dan yanzu ta fara bata haushi da irin Iskancin da take yi.

Da sauri ta bude tana jaa baya, tare da yin ƙasa da kanta, a hankali ta furta "Sannu Ummuna !", kallonta tayi daga sama har ƙasa kafin tace "ai ke za'awa sannu. nace kece mai Sannu Sadiyyerh, ke yanzu wannan halin naki ashe har yau baki daina ba ?, Wlh ki ci gaba da dukkan abun da kike, kina ganin Mijinki Salihi Bawan Allah, amma kina gasa mishi aya a hannu, wlh kar kiyi fatan ganin ranar da zai goge ya fara rama abun da kike masa, dan yanzu zamaninan da muke, irin Yaah Shehi wlh tsada suke da wuya samunsu ko an tona, amma ke kina wasa da Damar da Allah ya Ara miki,duk kuwa da kinsan cewar *SO DAYA TAK DAMA TAKE ZUWAR WA MUTUM A RAYUWARSA* .

na lura kin rasa wanda zai faɗa miki gaskiya shi yasa kullum haukarki da Yarintarki suke ƙara jaanki , ki daina ganin yana yage miki baki yana sakar miki jiki ,Wlh daga ranar da ya gano cin kashin da kike mishi ba zaki kara jin dadin zama dashi ba, gwara ki zauna kiwa kan ki karatun ta natsu", ta fada tana wulla mata kayan da ta shigo dashi a hannunta.

Shiru tayi tana bin bayan Umma Jakadiya da kallo, sai taji kamar ta haƙura tabar konai sai taji bazata iya ba, tayi Alƙwarin gaskiya bazata ci gaba da zama dashi ba in kuwa ta zauba to sai dai su ci gaba da zaman da suke yanzu , dan bazata kara bari ko hannunta ya taɓa ba, dudduba kayan da Umma ta kawo mata ta shiga yi, duk da Express ne ɗinkin Amna ya yi kyau sosai, an mata su kamar na Amarya.

Guraren 1am Anty Rayhana tazo ta sameta zaune tana latsa waya, kallonta tayi tace "Anty!", "ba wata Anty sai gaskiya in da ni Antynki ce ai da kin yi abun da na sanyaki", shiru tayi bata ce komai ba.

"ni dai yanzu Anty muje amin lalle na, san kinsan gobe Sallah kuma tun yau zamu fara aiki", ta fada tana jaan hannunta, miƙewa tayi suka fito palo, nan suka tarar da su Zayn, "Zayn ko zaka siya mana Baƙin Lalle da jaa a Super market din nan ?", ta fada tana kallonshi, "ina ma da Jaan da nazo dashi", "to siyon baƙin", ta fada tana zama gefe.

"Amma fa kin san Yaah Shehi baya son Baƙin nan ko ?", Anty Rayhana ta faɗa tana kallonta, "ni badan shi zan yi ba ai", dariya ta dan yi tare da cewa "to dan wa ?" , "ni dan kaina zan", ficewa yy domin siyo mata.

Chan bai fi minti biyu da fitw ba ya dawo, kallonshi Sadiyyerh tayi tace "ina lallen ?", yana kallon wayarshi yace "Yaah Shehi ne yace , in na sake na siyo sai ya saɓa min", tsuka taja tare da cewa "ni ban san mai yasa yake son takurawa Rayuwata ba haaaba", ta fada cikin mugun takaicin da ya luluɓeta. "Tun da yace kar a siyo nima bazan zanashi ba, yanzu dai dauko min Jaan a cikin Jakata a ɗaki ki kawomin A kwaɓa Lallan", ta fada tana gyara zamanta,ba tare da musu ba Sadiyyerh ta miƙe ta shige ciki, bata jima ba ta dawo hannunta dauke da wata babbar leda .

miƙawa Anty Rayhana Ledar tayi, "ɗibo min ruwan zafi", bb musu ta kara wucewa kitchen bata jima ba ta dawo da cup mai dauke sa ruwan zafi sai turiri yake, miƙawa Anty Rayhana tayi, ta zauna a gabanta, tana mai daura fararan ƙafafunta da suke tass kan wani babban pillow .

Anty Rayhana da kanta ta kwaɓa musu lallan , bayan ta gama ta fara zanawa Sadiyyerh Flowers masu kyau sosai, a hannunta , suna yi suna fira, amma Sadiyyerh tayi gum da baki ta sa boda haushin da take ji, ta kuma kuɗurta sai tayi baƙin, ko wani guri ne sai taje an mata sa boda ta ƙuntatawa Rayuwar Yaah Shehi in ya gani tunda shi baya so .

sai da aka gama zama mata a hannunta, kamar Anty Rayhana tasan mai take tunani ta fara zana mata Jaan ma a bayan hannunta, kamar zata tsalla ihu kallonta tayi tana shagwaɓe fuska, dariya tayi ba tare da tace mata komai ba.

bayan an gama na hannun ta fara mata na ƙafa, bayan an gama aka sanya mata leda , tana zaune nan Anty Rayhana ta tafi gurin su Ayyana suna aikin Sallah, ita kuwa suna palo, gajiya tayi da shirun da bakintw yy kawai sai ta biyewa su Zayn suka ci gaba da firarsu, har sai da lallanta ya kama sosai ta cire, Maa sha Allah, lallan ba ƙaramin kyau ya mata ba, ta fito sosai, miƙewa tayi ta shiga kitchen bayan ta wanke, "Kaiiiii haka lallan nan ya yi kyau, gaskiya nasan Yau Yaaah Shehi har kyauta zai min in ya gani," cewar Anty Rayhana cikin tsokana, turo bakinta tayi tana ci gaba da aikinta, "baki ce komai ba ?", "Allah Anty zaki san har ya goge bai ganshi ba tom ", ta fada rana wani cin magani.

dariya kawai Anty Rayhana tayi va tare da tace komai ba, Ayyana ce tace "Rayhana gobe ki kitse mata kan nan nata pls , ya yi tozozo da yawa","Tom Ayyana", ta fada tana yanka flower din da take yanka cin cin.

"ni yanzu mai zan yi ?, naga Anty na yanka cin cin", ta fada tana kallon Umma Jakadiya, "Samosa dasauran aikin gobe ke zakiyi komai ", numfashi ta fesar, kafin ta fara haɗa flower din Somaso sai da ta gama , kafin ta ɗibo namanta a Fridge da wankeshi sosai, ta sanyashi a tukunya ta daura a gas, magi ta dan zuba, kafin ta koma kan carrot din da ra fiddo, wankewa tayi , ta fara yanyankashi ƙanana sosai, lokacin da ta gama , naman ya tafarfasa, tsameshi tayi ta mayar da carrot din shima ta dan dafashi sama sama.

lokacin da zata fama tafasashi ta gama daka namanta, kwashewa tayi ta ajiye a gefe, Fran fam ta daura kan gas ta zuba mai ba wani mai yawa ba sosai, Albasa ta dan zuba, sai da manta yy zafi kafin ta fara zuba namanta. bayan ta gama ta zuba Carrot , magi da kayan kamshi ta zuzzuba , bayan ta gama soyashi sama-sama........... [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 21*

Bayan ta gama soyashi sama-sama ta kwashe ,Fran ta kara daurawa, ta matsa da kwaɓaɓɓan Fulawa dinta, brush masu taushi guda biyu ta samu daya ta sanyashi cikin bowl din da ta zuba mai, dayan kuma cikim robar fulawa.

na man ta dauka ta shashafa a cikin Fran din, bayan yy zafi ta dauki na cikin fulawar ta fara shasshafawa, yana dan fara soyuwa take daukewa tasa wani, ficewa duk suka yi , sakamakon gama aiyukansu da suka yi.

After 1 hourAnty Rayhana ta shigo, riƙe baki tayi tana kallon yarda take , "wannan ai baza kiyi sauri ba ke daya gashi da yawa, bari na taya ki", ta fada tana kunna dayan side din Cooker din, Fran ta daura ta fara tayata suna yi suna fira har suka gama.

yayyankaww suka fara , Anty Rayhana tana zuzzuba kayam haɗin tana liƙewa da kwaɓaɓɓiyar fulawa, tana yi Sadiyyerh na soyawa,sai gashi sharp-sharp cikin 2 hours suka gama, tattara komai suka yi suka adana.

"Sauran aikin fa ?", ajiyar zuciya ta sauke tana share zufar fuskarta tace "Ayya Anty wlh na bala'in gajiya ki bari in kika gama min kitson muka yi Sallah tum da lokaci yy sai na ƙarasa ", kallonta tayi kafin tace "kin san dai Yaah Shehi sai ya ci Abin ci zai fita ko ?", taɓe bakinta tayi, kafin tace "uhmmmm ban sani ba sai yanzu ", ta fada tana taɓe baki.

dukan kafadarta tayi tana dariya tace "zama ko sani ai yar Jakar Uba",A tare suka fice daga cikin Kitchen din.

kowa Bedroom dinshi ya nufa, Wanka Sadiyyerh ta fara yi dan har wani zufa-zufa take ji, Alwala ta dauro ta fito, ledar kayan da Yaah Shehi ya kawo mata ta jawo dubawa ta shiga yi, yatsina fuskata tayi, lokacin da ta fiddo wani black lass mai ratsin Ash da red , ɗinki Abuja Bubu da yy masifar fitowa da lass din an yi planting back din tun daga mazaunai har ƙasa, ɗinkin yy mata kyau ss.

fito dashi tayi, zip din rigar ta bude "Allahumma lakalhamdu anta kasautani hi, as'aluka min khairihi wa khairi ma suni alahu. wa a'uzubika min sharrihi wa sharrima suni a lahu" , ta furta ya yin da take saka kayan a jikinta, cif suka zauna cikim jikinta, tayi wani irin kyau, kanta ta gyara ta sanya dan kwallin a kanta ba tare da ta daura ba .

kalolin turaruka ta fesawa jikinta, wanda ita kanta ta gamsu da kamshin da jikinta yake yi ɗari bisa ɗari, plat shoe ta sanya , kai tsayevwaje tayi abunta.

tana fita waje wani kamshi ya daki hancinta, idanunta ta daga da sauri lokacin da taji saukar haɓɓarshi akan kafadarta, "wa'iyazubillah " ta furta a hankali tana lumshe idonta.

"Sadiyyatouh!", ya furta mata cikin kunnuwanta, ƙiris ya hana ta fasa ihu sa boda yarda tsiƙar jikinta yy wani mugun tashi , idanunta ne suka fara kawo ruwa , yunƙirin kwacewar ma da take kwana biyu yau bata yi ba, numfashi ya fara saukewa, yana manna lips dinshi da wuyanta a hankali ya furta "wai rigimar mene haka ?", ya fada yana lumshe idanunshi , " ni ka sake ni", ta fada tana ƙoƙarin fisgewa, kara mannata da jikinshi yy yana shaƙar kamshi turaren jikinta da yake sanyaya mishi zuciya, jikinta yy wani mugun sanyi.

"uhmmm ni bazan sake ki ba", hawayen idanunta na zuba ta sanya hannu zata zame mishi hannunshi da yake kan jikinta, riƙe hannunta yy yana kallon lallanta da yy mishi wani irin kyau, hsnnun ya ƙara a bakinshi tare da bashi wata sumba mai kyau.

" ni ka sake ni, kar ka ƙara taɓani bana sonka , bana kaunarka mayaudari kawai", ta fada hawaye sharrrr na zubo mata, wani abu mai kama da mashi yaji ya soki ranshi, "bana sonka , na tsaneka!", ita ce maganar da ta ƙara dawowa dashi hayyacinshi bayan jin waccan maganar tata.

janyewa yy daga jikinta ya nufi hanyar sauka ƙasa, Haɓɓar Alƙyabbar jikinshi ta riƙe tana cewa ", nace maka ka sake ni Maleeq!", ta fada cikin wata kaurarriyar murya.

bai kulata ba ya ƙara nufar hanyar fita, cikin yar tsawa tace "Wlh sai ka rabu dani maha'inci", ta fada tana ƙoƙarin juyawa, wata fisga yy mata, wadda sai da kashinta yy ƙara, idanunshi da suka rine ya watsasu kan fuskarta, har wani ruwa-ruwa idanunshi yake tarawa , sa boda ɗacin maganar da tayi mishi.

Sosai ta firgita da irin kallon da yake mata, da yanayij yarda idanunshi suka sauya kala har ma da irin riƙon da yy mata.

bai iya ce mata komai ba, ya saketa ya wuce abunshi, da gudu ta faɗa bedroom dinta tana kuka sosai, bed ta fada, tana kuka , Addu'o'in samawa kai sauƙin ta shiga jerawa , amma bata jin komai har wata suya take jin kirjinta na mata, duk wani juyi da zata yi kan bed din kallon Yaah Shehi take rungume da wata , hannunshi kan cikinta "Yaaah Subhanallahi!", taya ma zata iya mantawa da hakan, da kamar wuya.

Zallar ɓacin ran da yake ciki ne ya hanashi ma zama cikin gidan gaba daya, garden ya nufa, yana tafiya a hankali.

tunda ya fara jin sanyayyiyar iskar cikin garden din sai hankalinshi ya fara kwanciya, bama kamar daddadan kamshin da yake fita daga furannin da suke gurin, numfashe idanunshi yy a hankali yana fesar da sanyayiyar iska mai cike da kamshin mouth freshener a hankali ya furta "Yaah Rab!", ya furta yana mai daura hannunshi akan sumar wuyanshi da tayi luf a bayanshi, ƙarasawa yy gurin wasu fararan kujeru masu kyau da suke gefe daya, ta gefen yana dauke da wasu ƙorayen filawowi da farare , kusa dasu kuna ga wani abu jan da yake zubo da rywa gwanin kyau.

Zama yy gefe, yana mai lumshe idanunshi da kyau, yanzu tunanin Yarinyar ya faɗo mishi a rai, shi ya dan manta ma da ita kwana biyu, ko yaje Asibitin baya zuwa gurinta, gashi lokacin aikinta na ta tahowa, jaaan gashin gemunshi yy, yana son motsa bakinshi ya bude, dakyae bakin ya bude a hankali cike da natsuwa yace "Astagfiroullah!", ya furta yana dan haɗe kafafunshi, muryan Zayn ce tasa ya dan ware idanunshi a hankali, sai da ya dam kalleshi kafin ya kara lumshe idanunshi ba tare da yace mai Uffan ba.

gurin ƙafafunshi Zayn ya zauna a ƙasa, a hankali ya dauki hannun Yaah Shehi ya daura akan sumar kanshi mai yawa, wadda ta kusan tarar da ta Yaah Shehi a yawa, "Hammana", ya furta a hankali, jij kiran da yy mishi ne ya tabbatar mishi da cewar akwai abun da yake so daga gareshi, shafa kanshi yy ba tare da yace komai ba, hakan kuma shine ya bawa Zayn damar yin mgn , "me ne ya samu Sister na sameta tana kuka ", ya fada a hankali, ba tare da Yaah Shehi ya hude ido ba, ba kuma tare da sanin cewar zai bashi Amsa ba yace "Rigima!'", yana fada ya tsuke bakinshi ba tare da yy mgn ba.

Shiru dukkansu suka yi, Zayn ya wani ƙara naba'a yy shiru yana sauraran kukan tsuntsayem da yale gurin wanda yake fitar da sauto mai dadi.

Kitso sosai Anty Rayhana ta yaryarawa Sadiyyerh na gani na fada yy kyau sosai, gashin nan ya sauka har gadon baya, girgizata daga gyangyaɗin da take Anty Rayhana tayi, zabura tayi tana kallonta , dariya de ta kwace mata tana nunata, "gaskiya ke kura ce, yanzu daga ɗan taɓa ki shine kika yi wannan Uwar zaburar ", ta fada tana dariya, cuno baki tayi bata ce da ita komai ba.

miƙewa duk suka yi daga gurin, Kai tsaye Sadiyyerh ta koma kitchen domin ƙarasa aikin da ya Rage mata, bata an ƙare ba taji alamun mutum a bayanta, da sauri ta juyo, tana juyowa ta faɗo kan jikinshi, ƙara ta fara ƙoƙarin kwallawa dan ba ƙaramin tsoro taji ba, gashi bata san cewar shi bane, da sauri ya jijjigata yaba kallon cikin idanunta, numfashi ta sauke tana zazzare idanunta a hankali ta zame daga jikinshi ta juya.

kanta da dan kwalinta ya zame yake kallo, "Alhamdulillah!", ya furta ba tare da ya bari ta ji mai ya furta ba, ƙara juyowa tayi da mug din coffee , jaaa baya tayi da sauri dan ra dauka ya fice tuni garin jaa da bayan da zata yi by mistake mug din ya kwaɓe daga hannunta, gaba daya ta wanke ƙafafunta dashi, "Allahumna Ajirni fiii Maseebati", ta furta tana sulalewa ƙasa, jikin Yaah Shehi har rawa yake gurin ƙarasawa gareta, da sauri ya ɗagota yana kallon ƙafar da lokaci daya tayi jaaajir .....

~BAN HAKURI DA CAPITAL LETTER .DON ALLAH KUMIN UZURI WLH HIDIMA TA SHA KIN KAII YANZU HAKA GAGANIYA HAKE DAKYAR NA SAMU NAYI, GASHI KUMA BB YAWA, PLS KUMIN UZURI KU YAFENI IN SHA ALLAH MUN KUSA KOMAWA, MUNA YI KAMAR DA~

LOVE YOU SO MUCH FAN'S🥰🫶 [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.22*

Dafa Kafadarshi tayi da hannu bi-biyu ta dafe tare da daura fuskarta kan kirji shi ta murza hancinta a jikinshu, cikin muryar raɗaɗi azaba tace "Washhhhhhh Yaah Shehi, Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!", ta furta lokaci daya zufa na wanke mata jikinta, da sauri ya ƙara rike yana kallon yarda take ƙoƙarin zameww daga jikinshi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull