Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 11

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 11

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 11: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 11. .......Bayan angama sallan komawa haisam yayi part…

4,334 words

.......Bayan angama sallan komawa haisam yayi part d'insa ya shiga wanka,bai jima sosae ba ya fito daga cikin bedroom dinsa ashirye cikin riga da wando marasa nauyi rigan sleeveless hoodie ce army green,irin rigan nan mara hannuwa mai dauke da hula mak'ale a wuya igiyoyinta sun zubo saman kirjinshi sannan gaban rigan anyi wani design din rubutu baki mai walwali, wandon kuwa baki ne 3 quarter ya wuce gwiwarsa ya d'an matse,ba karamin kyau yayi cikin shigan ba,kirarsa ta kakkarfa ta bayyana,baisa hulan rigan ba tana kwance a bayansa sai da ya yi shut down laptop din dake ajiye a falon kafin ya fice ya koma part din hajia,don gaba d'aya yau he's busy working on his laptop dama kuma bai zuwa Gym ranar lahadi,tunda rana hajiya keta kiranshi tana korafin yana gida amman bazai zo suyi hira ba,ya sanar da ita yana wani aikine,tace to ya dawo falonta yayi aikin mana yace mata yafi samun network a part dinsa tayi hakuri da dare zai zo suyi firan.

*** *** **** Tun bayan da ta shige d'akin bata fito ba saida aka kira magriba ta fito yin alwala anan suka had'e da Amadu yana ganinta yace"ke,yaushe ki ka dawo gidan?ba dazun da ki ka dawo daga islamiyya kince man zaki gidan hajia ba?" fatuu dake ta zare idanu tace"ai..ai hajiyan batanan ne shine na dawo" gyada kai yai ya wuce yayi alwalarsa ya nufi masallaci,itama alwalar tayi ta koma daki tayi salla,gaba daya ranta bai mata dadi sai tufka da warwara take zulluminta kada gobe tayi bataje ta bashi hakuri kaman yadda haulat ta bata shawara ba,gashi ita dae harga Allah tsoron zuwa take don batasan abunda zai biyo baya ba,kuma tana ganin mutumin kaman baida kirki,tana ta zaune har aka kira sallan isha'e,anan ta yanke shawarar komawa bashi hakurin bayan ta gama sallan isha din,

tana gama sallan ta shiga yin addu'a tana rok'on Allah da ya taimaketa mutumin yayi hakuri in taje,ta tuba bazata kara ba,tana cikin shafa addu'an ta jiyo sallamar gwaggo ta dawo,gabanta ne ya fadi rass ta shiga tunanin yadda zata fita daga gidan don tasan sai gwaggon ta tambayi abunda zata je yi gidan hajia yanzu,

d'aga labulen dakinta da gwaggo tayi yasata juyawa da sauri tana kallonta da yake akwae wutan Nepa,shigowa ciki gwaggo tayi jikinta sanye da uniform din aiki fatuu dake kallonta tace"Dja66ama bé wargo gwaggo",

"yauwa,ya gidan? "Lafiya lou" ta bata amsa, "ashe bakiji dadi ba?yanzun nan Amadu ke gaya man a kopar gida" fatuu tace"eh amman nasamu sauki sosai,ya bani magani nasha har islamiyya ma naje" jinjina kai gwaggo tayi"kin kuwa ci abinci?" Girgiza mata kai fatuu tayi alamar a'a,ganinta sukuku gashi idanunta kaman tayi kuka yasa gwaggo cewa"kodae wani abun ke damunki?ince ba fitina kika jawo mana ba dae,dama inata mamaki kwana biyu da ba'a kawo man k'ararki ba,fada man gaskia minene fatuu? gabanta ne ya fadi rasss da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tace"a'a gwaggo ba wani abu fa,kawai har yanzu ban dan jin dadi ne"ta karasa gabanta nata faduwa,

Jinjina kai gwaggo tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in"ki tashi ki ci abincin sai ki k'ara shan magani,Allah ya sawaka,ni bari inje in watsa ruwa insamu na kwanta na kwaso gajiya sosai,kizo ki kar6i abincin gama abun biki can cikin jakata da aka ban in zaki ci su cin-cin ne da dublan" daga haka ta fice,sosai gaban fatuu yaci gaba da faduwa jin maganar da gwaggo ta mata,tabbas dole ta tafi taba mutumin nan hakuri tun gobe batayi ba asirinta ya tonu,

*** *** *** *** Hajiya zaune a falo tana kallon sabon shirin kwana cas'in na tashar arewa 24, haisam ya shigo da yar sallamar da ba lalle ma in taji ba ya nufi kujera ya zauna yana facing din hajiyar,juyowa tayi ta kalle shi da d'an murmushi"sannu,yau kasha aiki,yini guda mutum na latse-latse,basu hakuri gobe kaje office din" hannu yasa ya shafo forehead dinsa kafin yace"ba aikin office bane" gyada kai tayi sai kuma tace"halan turawan ne,suda basu ganin mutum mai hazaka su kyale,in sunyi hakuri ba tattarawa za kai duka ka koma wurinsu ba"

d'an kwantar da kai yayi baice mata komae ba saima wani lumshe ido da yayi,da sauri ta juya tana kallon t.v jin muryar yawale yana magana,ba karamin cin dariyar acting dinsa take ba yana burgeta,tana ta daria tace"in baya ga ma film,ai ni a zahiri bazan iya d'aukan irin wannan matsayin direba ba,sai kata maimaita mashi magana sannan ya fahimta ina dalili" juyowa tayi tace ma haisam"wai nan direba ne fa ahaka" A hankali haisam ya ware idanunsa kan tv d'in yana kallon abunda hajiyan ke magana akai,dan murmushi yayi ya juya ya dauki wayansa dake aje a hannun kujera yana fadin"in driver dinki ne har marinsa zaki one day", "in naga zai man wasa da rayuwa ba dole na maresa ba,ai wannan kyansa yaron gida ba abu mai mahimmaci kaman tuki ba" shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da latsa wayarsa,ita kuma hajiya taci gaba da kallon su yawale da rayya tana daria,jefi-jefi take waigowa tana ma haisam magana kan shirin don dama haka take bata iya shiru in tana kallo shidai sai dae yayi d'an murmushi ko ya daga mata kai don ba kallon shirin yake ba,so ba abunda yake fahimta.

Hajiya ta sake juyowa tace"akawo maka abinci ko?" Kai ya daga mata alamar eh,ta juya tana kwala ma Saude kira,bayan ta fito ta bata umarnin ta kawo ma haisam abinci tace mata basai ta zubo a warmer ba tunda yanzu zai ci ta amsa da to,ta shige kicin don zubo masa abincin,a tray ta d'auro kayan abincin ta nufo inda haisam d'in yake don ta fahimci indai shi kad'ai zaici abinci baison akai masa saman dining table,saman sofa table ta daura tray din tana gaishe shi ya amsa,tana kokarin zuba masa zo6o cikin cup ya dakatar da ita alamar ta barshi zai zuba da kansa,daga haka tace "aci lpy" sannan ta juya,

cire plate din da aka rufe abincin yayi ya tsaya yana kallon shi wanda spaghetti ce tasha vegetables da busasshen kifi sai kamshi ke tashi,da sauri ya d'ago yana niyyar tsaida Saude dake k'okarin shigewa cikin corridor"hey...." Hajia ta juya da sauri tace"je ki abunki" kafin ta juyo tana dan harararsa"in ma zaka cinye ka cinye don ba abunda za'a rage,wato dazun don kaga can aka bika dashi shine ka tsakura kace azo a dauke ai dama nace zamu hade da daddare ne" haisam dake ta kallonta yana dan cizon lip d'insa na k'asa had'i da dan murmushi yace "did i say anything?" A tsiwace tace"But u'r about to....haka kurum don ka jaman sharri iyayenka su zo su ga ka rame suce hakanan na matsa ka dawo wurina ashe bana baka abinci" Haisam couldn't help it but laugh,sai kace ta daukko wani k'aramin yaro wanda baisan ciwon kansa ba,itama dariyar take taci gaba da kallonta da har yanzu ake shirin da take kallo,shi kuma ya fara cin abincin.

Tunda ta amso abincin ta dawo d'aki ta kasa cin wani na kirki yan lomomi ne tayi taji duk ya fita ranta ba kuma don bata jin yunwar ba,sai don hankalinta daba a kwance ba,tunaninta yadda zata fita yanzu ba tare da gwaggo ta hanata ba don dole fa taje taba mutumin nan hakuri da daren nan,tsam ta mik'e hannunta dauke da plate din abincin ta maida kicin ta rufe a tsakar gida tayi tsaye tana zullumin zuwa tambayar gwaggon daga baya dai ta nufi d'akin gabanta nata faduwa,d'aga labulan d'akin tayi ta shiga da yar sallama gwaggo da har ta kwanta amman bata yi bacci ba ta d'ago da kanta tana k'okarin kunna fitilan wayanta "fatuu,djam? ta tambayeta,Matsawa tayi kusa da gadon tana kallon gwaggon tace"d..dama gidan hajia zanje" cike da mamaki gwaggo tace"gidan hajiya da daren nan,me zaki je yi?", "Un..dama jiya ne dana je tace in koma yau zata bani sako,to dana dawo islamiyyar safe ban lafiya sai d'azun dana dawo ta yamma naje sai na iske bata nan ta fita ita da t.k amman Aunty Saude tace man in koma in ta dawo don kafin ta fitan saida ta aikota tazo ta kira ni ta iske ban dawo daga islamiyyar ba" ta k'arasa maganar sai faman zare ido take gabanta naci gaba da bugawa da k'arfi,ba don ba haske sosai ad'akin ba da tuni gwaggo ta gane k'arya take shirga mata don har yar zufa tayi,

sanin dama hajiyar na aikowa kiran fatuu wani lokacin yasa gwaggo cewa"to miyasa tun dazun baki je kinga ko ta dawon ba,kika bari dare yayi har haka tara fa ta kusa inma bata yi ba..." da sauri ta katseta "ai ina niyyar dana gama sallah in koma sai kuma kika dawo" gwaggon tace"to ki maza kije ki dawo karfa ki zauna har Amadu ya tashi" cike da farin ciki tace"ah bazan zauna bama" daga haka ta fice ta nufi hanyar fita ko hijab bata yi tunanin taje tasa ba iya d'an bakin gyalenta na gado ne a saman kanta ga kan yayi wani tum saboda gashinta dake a kwance ba kitso yayin da jikinta ke sanye da riga da skirt na material da alama tana son sa riga da skirt,gidan hajiya ta nufa duk da fargabar da take ji hakan bai hanata tunkarar gidan ba don tasha alwashin a daren nan sai taba mutumin nan hakuri.

Sauran kad'an haisam ya k'arasa cinye abincin wayarsa ta hau yin wata kara alamar notification,sanin karar ko ta miye yasa da dan sauri yakai hannu kan hannun kujerar yadau wayan yana dubawa lokaci guda yanayinsa ya canza da wani irin expression mai kaman mamaki kaman bacin rai yake kallon videon fatuu dake sand'a tana tunkarar falonsa,lokaci guda ya furta"Again...! jin haka yasa hajiya juyowa tana kallonsa "ince dai lafiya ko?"ta tambaya,"Yea,nothing" ya bata amsa yana k'okarin mik'ewa don ya yanke a ransa sai yaje yaji mike kawo ta part dinsa,ganin yana kokarin tashi Hajia tace"wai mike faruwa,gashi nan yanayin fuskar ka ya canja kuma ka ki ka sanar dani" d'an murmushi yayi"nace ba komae Sweethrt,just wani sako ne na tura shine aka sanar dani bai shiga ba zanje nai resending" ya fadi mata hakanne don ta kwantar da hankalinta, tace"to baka sha zo6on ba", "kar ki damu zan sha lemu inna koma can" dan 6ata rai tayi ta fara korafi "shikenan baza'a bar mutum ya huta ba,yini guda mutum nata faman latse,latse haba" yar daria yayi yace"to dama mai nema ina yaga hutu sweethrt" yana gab da fita daga falon tace"zaka dawo muyi hira ko? d'aga mata hannu yayi yana juya shi alamar a'a yace"ki ci gaba da kallon ki saida safe tomorrow is Monday and early to bed early to rise.." daga haka ya fice hajiya na fadin"Allah ya tashe mu lpy toh".

Da sauri ya nufi part dinsa don baison ta fice kafin ya isa,

A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta turata kad'an sannan ta turo kanta tana leken cikin falon,a iya hangenta bata hango mutum ciki ba sai computer da ta gani ajiye saman table hakan yasa tayi tunanin ko ya shiga cikin d'aki ne,fiddo kanta tayi waje ta shiga tunanin ko har yayi bacci ne,to yanzu ya zata yi ita?wata zuciyar tace anya kuwa yayi bacci,ai da ya rufe kopa,can kuma tace k'ilan kuma bai rufe kopa tunda akwae jami'an tsaro a bakin gate.....a daidai lokacin haisam ya shigo cikin part din har ya iso bakin balcony din bata ji motsinsa ba,k'ara tura kopan tayi tana sake lek'en cikin falon taga ko ya fito,cike da mamaki haisam ke kallon bayanta yama rasa tunanin da zai yi akanta babban abunda ya d'aure mashi kai shine mike kawo ta part d'insa?miye hadinshi da ita,sannan yama akai tasan inda yake,fuska a matukar d'aure tamkar bai ta6a daria ba ya tattaka stairs din ya haye"Excuse me!"yace mata, a firgice fatuu ta juyo don sam bata ji motsin shi a bayanta ba balle tasan dashi a wurin,a tsananin tsorace take kallonsa ganin ya daure fuska tamau,wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi lokaci guda ta fara ja da baya,atunaninshi rugawa zata yi kaman yadda tayi dazun hakan yasa a kausashe yace"kina guduwa zan sa aje har gidanku a kamo ki,gida mai kiosk right?" hannu fatuu ta shiga yarfawa jin abunda yace,kenan da gaske ne duk abunda Gaye ya fada mata,don dama yace mutumin ya tambayeshi kwatancen gidansu,lokaci guda ta rude ta kid'ime ta shiga fadin"innalillahi....nashiga ukkuna"tana ta faman yarfa hannu kamar wadda wuta ta kona.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*Paid Book*

*2️⃣6️⃣*

kama handle din kopan yayi ya tura kafin ya juyo fuskan nan ba wasa ko kadan yace"biyo ni! a hankali ta fara jan k'afafunta kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki tabi shi ciki kaman yadda ya bata umarni,haisam na shiga ya wuce saman kujera wurin da ya zauna d'azun da Abbas yazo,ita kuwa fatuu tana shigowa wani ni'imtaccen sanyi had'i da daddad'an kamshi suka kai mata karo,zaro idanu tayi baki bud'e ta shiga bin ko'ina na falon da kallo,ba komai yafi dauke mata hankali ba face chandalier(fitilan sama) yadda take d'auke da sarkoki masu kyau,tunda take bata ta6a ganin irin fitilan a zahiri ba sai acikin film din yan kasashen waje,ita bata ma ta6a tunanin akwae irinta a Nigeria ba,gaba d'aya ta saki baki tana ta kallonta har gyalenta ya zamo ya tsaya kan tudun gashinta dake fake,

Ganin bata k'araso cikin falon ba kuma yaji lokacin da ta shigo yasa haisam waigawa ya kalleta,tsayawa yayi yana kallon ikon Allah kaman ba itace ke kerma ba,bai ce mata komai ba ya juya yai powering laptop up ya jingina da kujera ya jira tagama booting kafin ya fara daddanata kuma har lokacin fatuu bata daina kalle kallen da ta ke ba,ganin bata da niyyar shigowa ga dare nayi shi kuma yana son yaji abunda ke kawota part din nasa yasa shi daukan wayarsa ya d'an bubbuga gefenta a saman c-table,aikuwa firgit fatuu tayi ya juya ya dan kalleta ya had'e giran sama da ta kasa,hakan yasa da sauri ta nufo cikin falon can gaban red armchairs ta wuce tana isa gefensu kawai ta zube saman gwiwowinta tayi kneel down,

baice mata komai ba yaci gaba da operating laptop d'in hakan yasa ta samu daman cigaba da kallon fitilar da alama ba k'aramin daukan hankalinta tayi ba,a hankali ya d'ago idanunsa ya dan kalleta sai kuma ya mik'e ya nufi bedroom dinsa tabi bayansa da kallo har ya shige kafin ta maida kallonta kan fitilar dai,

bai dau lokaci ba ya fito hannunsa dauke da wani k'aramin kwali,daidai bakin corridor ya tsaya ya kai hannu ya latsa wani switch lokaci guda hasken fitilar da fatuu ke kallo ya dauke,sai kuma ya k'ara latsa wani lokaci guda hasken wasu fitilun ya gauraye gidajen dasu T.V suke ko wane gida na pop cast din na d'auke da fitila hakan ba k'aramin kawata wurin yayi ba,ai kuma sai ta maida kallon nan wurin har wani dan dukar da kai take,ita mamakinta daga ina hasken ke fitowa don ba'a ganin fitilun sai dai hasken kawai,komawa yayi ya zauna ya fara kokarin bude kwalin da ya fito dashi hakan yasa fatuu ta maido hankalinta kanshi tana so taga minene a ciki,screen glass ne ya fiddo wanda yake sawa in zaiyi aiki da dare don yai protecting idanunsa daga illar hasken screen,binshi da kallo fatuu tayi lokacin da yasa glass din don ba karamin kyau yayi masa ba tamkar fashioned glass haka yake,kasa d'auke idanuwanta tayi sai kallonshi take tun daga saman kanshi har kasan kafafunsa cikin ranta tana ta mamakin yadda akai hajiya ta haifi mai kama da yan kasan waje ita da take bak'a kuma ba wani kyau ne da ita sosae ba,shikam ji kyau kaman shi yayi kansa ta ayyana a ranta,ga dogon hanci ba kaman na hajiyan ba d'an mai fadi dashi,ji yayi a jikinsa tana kallonsa hakan yasa ya yi mata kallon kasan ido suka had'a idanu,da sauri ta sadda kanta kasa don sai taga kaman harararta yayi,tana ta wasa da yatsun hannunta gabanta na cigaba da faduwa.

"mi kike zuwa yi apartment dina? Ta ji ya jefo mata tambaya, Da sauri ta d'ago ta kalle shi tana faman zare ido,ci gaba yayi da magana ba tare da ya kalleta ba"ina sauraranki,ki gaya man abunda ke kawo ki nan don dazun ma naga kinzo" gabanta ne ya cigaba da bugu da sauri da sauri,sai faman motsa baki take ta rasa ma ta ina zata fara,mi zata ce mashi,d'agowa yayi furiously yace"am i not talking to human being? ganin yadda yayi maganar yasa da sauri ta fara magana cikin in'ina tace"d...da...dama..." sam ta kasa magana saboda kafeta da yayi da ido sai faman kerma hannuwanta ke yi,ya fahimci ta tsorata dashi hakan yasa yadan sassauta daure fuskan da yayi yai lowering voice d'inshi yace"uhun dama what?" "dama zuwa nayi na baka hakuri don Allah kayi hakuri ka yafe man laifin da nayi maka,na tuba Allah bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana dan ta6e baki alamar zata fara kuka sai kace k'aramar yarinya lokaci guda hawaye ya fara sauka daga idanuwanta tasa gefen gyalenta tana gogewa, "wonder shall never end.." abunda haisam ya fada cikin ransa kenan,shi mamakinsa wai hakuri tazo bashi,shi da tunda tayi masa laifin yama manta da ita,to miyasa zata zo bashi hakuri?ya jefa ma kansa tambaya lokaci guda kuma ya tabbatar ma da kanshi dole akwae dalilin yin haka,wannan bayin kanta bane don bai tunanin tana da cikakken hankalin dama zata gane tayi laifi har ta bada hakuri,amman koma miye dalilin he will find out now.

Tsayawa yayi yana kallonta kaman mai nazarin wani abun sai kuma ya janye idonsa yaci gaba da abunda yake yi ita kuma sai faman murzar ido take ita ala dole kuka take kaman yadda haulat tace tayi,"wani laifi ne ma kika man? ya jefo mata tambaya ba tare da ya kalleta ba,da sauri ta d'ago tana kallonshi kaman ba itace mai murzar idanu ba,mamaki ne ya cikata aranta tace"kenan ma ya manta abunda nayi masa,dama banzo b...." ya katse da cewa"sai na maimaita maki ne? da sauri tace "a'a,d..dama nice wadda ta rotsa maka gilashin mota,amman na tuba bazan k'ara ba"tayi raurau da idanu alamun zata yi kuka tana ta6e baki,

D'agowa haisam yayi ya had'e hannuwanshi ya daura ha6arshi a sama yana kallonta hakan yasa ta sunnar da kai ya lura bata son had'a ido dashi ajiyar zuciya ya sauke yace "miyasa kika zo bani hakuri?" da sauri ta sake d'agowa tana kallonshi sai faman zare ido take sam bata so ta sanar dashi yadda sukai da Gaye don kada yace ashe ba don Allah tazo bashi hakurin ba sai don taji gilashin nada tsada kaman yadda haulat ma ta gargadeta,lokaci guda ta fara tunanin karyar da zata fada masa...kaman haisam yasan abunda take tunani yace"mark u!ba'a man k'arya,da zaran kika fad'a man karya yanzun nan zan gane karya ki ke and I hate people who're telling lie kinga laifinki zai kara yawa kenan" wani irin kuka cikin fatuu yayi ta had'iye miyau da kyar, shikenan ba daman tayi masa karya don ta yarda sosai da abunda yace ta k'ura ma computer din gabanshi ido tana tunanin ko tanan yake ganewa in an masa karyar don taga wasu abubuwa jone ta gefenta.

"baki ji mi na tambaye ki bane?bana son maimaita magana" fuska a d'aure yayi maganar hakan yasa fatuu gyara kneeling dinta ta fara motsa baki cike da fargaba tace"d..daman Gaye ne yace wai...wai gilashin motan nada tsada sosae,wai bazaka ta6a yafewa ba sai an biya ka,duk da ni naga kana da kalan masu kirki,am..amma shi yace wai in ba'a biya kaba gidan yari za'a kaini...."ta kwashe duk yadda sukai da gaye ta sanar masa tana ta d'age baki tana langa6ar da kai ita irin yaji tausayinta d'innan", Sigh haisam yayi cikin ransa yace "exactly my thought,cire hannuwansa yayi daga k'asan ha6arsa ya maida kallonshi kan laptop din gabansa "wanene Gaye? Kaman jira take da sauri tace"wani mara jin magana ne anan unguwar d'an shaye-shaye yace wai yaga sanda na jefi gilashin motan ka kuma wai shi ka tambaya kwatancen gidanmu" d'an guntun murmushin gefe yayi jin abunda tace ga kuma k'aryar da gayen yayi masa don ya gane wanda take magana akai,kallon k'asan ido yayi mata"kice mai irin halinki kawai" da sauri tace"ai ni bana shaye-shaye kuma ma ni yanzu na shiryu na bar rashin ji daman shaidanu ne suka yiman fitsari a kai haka kaka na ke cewa" ta k'arasa tana ta6e baki alamar zata cigaba da kuka,

Danna wani key haisam yayi da karfi da alamar dot yayi kafin ya d'ago sosai yana kallonta on a serious note yace "While,duk abunda guy din ya fada maki gaskia ne,bcos i see no reason just don na raba ku fada zaki man asara irin wannan,dama abunda yasa ban dau mataki tun ranar ba lawyer na bai gari don bani son ai wasting time dina shiyasa ban reporting wurin police ba,gara muje court kawai a biyani hakkina,but luckily enough ya dawo yau so gobe zamu tafi can don already yasa anyi filing case din" ai ba fatuu ba ni kaina saida gabana ya buga don ba alamar wasa a fuskarsa yayi maganar,ita kam fatuu tsananin tashin hankali ta shiga,kuka na kirki ta fara tana masa magiya,

fad'i take"Don Allah,don soyayyar ka da manzon Allah,don hasken goshin manzon Allah kayi hakuri,in kana son ga kabarinka gana manzon Allah,in kana so ka gaisa da manzon Allah(S.A.W) yaya handsome kayi hakuri ka yafe man na tuba Allah bazan k'ara ba...." cike da mamaki haisam ke kallonta ganin yarda duk ta tashi hankalinta tana masa wani rokon da shi tunda yake bai ta6a jin kalarsa ba ga wani suna da ta kira shi dashi wai handsome,jingina bayansa yayi da kujeran yasa hannu daya ya rike ha6arsa had'i da bakinsa yaci gaba da kallonta kaman mai nazarin wani abu,ita kuwa har lokacin kuka take ga majina dake ta zubo mata sai faman sa gefen gyalenta take tana gogewa,hakan da take yasa haisam jin kyankyami don ya tsani majina bama ita kadai ba sam baison abun k'azanta,tsam ya mik'e daga inda yake ya nufi fridge dinsa don tun d'azun yake jin kishi saboda da yaci abinci baisha ruwa ba,ya bude ya d'auko lemun gwangwani tare da wani glass tumbler mai kyau ya rufe fridge din ya dawo cikin falon ya aje su a gefen laptop din sannan ya sake juyawa ya nufi wurin tv cikin wani gida ya dauko silver tissue box mai shegen kyau sai kyalli yake ya dawo ya zauna dashi a hannunsa ita dai fatuu sai binsa take da ido tana murzar idanunta da gyale tana cigaba da yin shesshekar kuka ga wata ajiyar zuciya mai k'arfi da take yi,

d'ago kanta tayi suka hada ido yayi mata alamar tazo da hannunshi,mikewa tayi ta nufi inda yake a gefen center table din ta durkushe idanunta sunyi jawur har sun fara kumburi,miko mata d'an akwatin yayi tasa hannu biyu ta amsa tana kare mai kallo don ta rasa mi zata yi dashi duk da tissue din ta leko,ganin haka yasa ya d'an duku ya kar6i abun ya jawo tissue din ya 6allo mata kana ya mika mata ya aje box din a saman c-table ya koma ya jingina yana cigaba da kallonta ahankali ta kai tissue din hancinta tana sunsunawa saboda wani sanyin kamshi da take kaman daga sama taji yace"abunda na baki ki da ita kenan?"cikin sauri ta fara goge fuskar tata sai murzar fuskar take still kallonta yake a hankali ta saci kallonsa suka had'a ido hakan yasa a hankali ta cire tissue daga fuskarta ta rike a hannu gyara kneel down din tayi taci gaba da rok'onsa,

cikin marairaicewa tace"don Allah yaya handsome kayi hakuri,kwarankwatsi kaji na rantse bazan k'ara ba,don Allah yadda Allah ya rufa maka asiri kake a aljannar duniya kada kasa akai ni gidan yari,ka barni inci gaba da kwana ad'an gidanmu ina cin abincin gwaggota,don wllh ko munje kotun bani da kudin da zan biya ka Allah kuwa" tana maganar tana d'an jujjuya kai lokaci guda wasu hawayen suka gangaro,

Shi abunda yafi daure mashi kai yadda yarinyar ta tashi hankalinta akan maganar biyan kudin,koda su talakawa ne bai yi tunanin zata tashi hankalinta har haka ba,nan take ya fara tunanin ko ana maltreating yarinyar ne,cike da son gano hak'ikanin gaskia cikin cool voice yace"ai bake zaki biya ba,dama duk in yaro ya nemo rigima ai parents dinshi ne a ciki in abun biya ne su zasu biya ke ai nasan bazaki iya biyana ba" kaman jira take ya gama maganan ta kar6e"ai ni a wurin kakata nike kuma bata da kudi talaka ce ita"takai maganar tana sauke ajiyan zuciya, "Amman ai guy din nan yace tana aikin asibiti kuma nasan ana samun kudi a aikin..."da sauri fatuu ta saka salati"Innalillahi... Wallahi gaye bai tsoron Allah,na rantse karya ya fad'a maka",

yace"kenan bata aikin? tace "A'a ai kai ba'a yima karya, tana yi amman fa attender ce a asibitin,kasan miye attender din? ta tambayeshi,a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, "masu fa share-share da goge-goge har jinin haihuwa su ke gogewa" ganin ya d'an yamutsa fuska yasa da sauri tace"ai sai sun sa safar hannu suke yin aikin kuma in sun gama suna wanke hannuwansu,kuma ma ita gwaggon tsafta gareta kullum da ta dawo aiki take yin wanka kuma ta wanke kayan aikin" d'an yamutsa baki yayi yace"kyauta take aikin ne" tace"a'a ana bata albashi amman basu da yawa abinci take siya mana bama su isa mu rinka cin shinkafa kullum sai an had'a da tuwo",

"Ina Dad dinki?ya tambayeta,tace" ba a garin nan yake ba yana Yola acan jimeta anan kauyenmu yake sunan shi rugar baffa ard'o", "ku fulani ne kenan? daga masa kai tayi alamar eh,yace"kuna da shanu?" batare da ta kawo komai a ranta ba ta k'ara daga masa kai alamar eh,dan guntun murmushi yayi" shikenan sai abani shanun madadin kudin gilashin,ni kuma nan yan kud'adena da nike saving sai in bada a gyara man glass din,tunda na fahimci cash bazasu samu ba"

Readers Also Read