Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 13

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 13

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 13: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 13. Hannu ya kai ya dauki remote yayi turning tv…

4,453 words

Hannu ya kai ya dauki remote yayi turning tv on,yana cigaba da shan lemun yana kallo,dawowa tayi tai tsaye gabanshi ba tare da ta d'aukko lemun ba,kallon ta yayi"ina lemun?" hannu ta dan watsa tace "babu" da dan mamaki yace"babu,to duk ina suka tafi?? tace"a'a akwai sauran wasu irin wannan da kake sha ne babu" wani kallo yayi mata mai kaman harara"to wannan shikenan dama aciki kuma baki bukatan shi,ki daukko wani" "giya ce?" yaji ta jefo masa tambaya yana niyyar kai cup din bakinsa,da wani irin expression ya d'ago yana kallonta,sosai gabanta ya fad'i ta shiga ja da baya tafukan hannunta dafe da bakinta furiously yace"zo nan!" sosai ta tsorata da yadda fuskan shi ta canja,a hankali ta fara matsawa dan nesa dashi ta durkushe tana girgiza kai alamar yayi hakuri don ta kasa ma magana,sassauta d'aure fuskan yayi yace"nayi maki kama da mai aikata abunda kika fadi ne...?da sauri ta girgiza masa kai,yace"to miyasa kika tambaye ni? Baki na kerma tace"naga kalan shi wani iri ba irin na lemunan dana sani bane shiyasa nayi tunanin ko itace tunda ni bansan ya take ba,amman don Allah yaya handsome kayi hakuri na tuba" ta d'aga hannuwa,

Sauke ajiyan zuciya yayi ya kwantar da bayanshi jikin kujeran kaman bazai tanka mata ba,gaba daya ya gaji da magana,dama duk duniya a yanzu dai mutum biyu ne ke sa shi magana da yawa,daga Abbas sai hajia,yanzu kuma ga fatuu dama dazun Abbas ya gama nashi,ita abunda yasa ya biye mata dama don akwai abubuwan da yake son sani game da ita don dan kwana biyu da ya santa ya fahimci bata jin magana sosai kuma shi tunda yake bai ta6a cin karo da yarinya irin haka ba,haka yanzu ma da tazo wurinshi sai yaga kaman ba daidai take ba,shiyasa yayi tunanin ko tana da matsalan kwalwa ne,to amman daga baya ya fahimci kaman lafiyarta lau kawai halinta ne hakan.

"Don Allah yaya handsome kayi hakuri kar kayi fushi,wllh bansan irin wannan lemun bane" kwalla ce ta fara gangaro mata a daidai lokacin ya d'ago da kansa yana kallonta itama shi take kallo tana matsar kwalla,gently yace"is okey,amman ki rage yawan surutu mara amfani" da sauri ta d'aga kai alamar toh,alama yayi mata da hannu tazo ta mike a hankali ta tsaya gefensa ya d'aga gwangwanin lemun ya fara magana a nutse"akwai lemu kala kala,wani a roba,wani a can,wani a kwalba,wasu manya wasu k'anana,so ba iya wad'anda kika sani bane lemu kawai,kar ki k'ara ganin wani yana shan wani kalan lemu da baki sani ba kice giya,Understand?" Da sauri ta daga kai,ya ci gaba"abunda yasa nace baki bukatan sa,Energy Drink ne,kuma yana da d'an karfi ne", bude baki tayi da mamaki tace Energy..! Yace"yea,ko baki san miye energy ba?da sauri tace "nasani,is the ability to do work" cike da confidence tayi maganar d'an murmushi yayi,hakan yasa itama tayi "mi kenan yake nufi?, Tace"karfi,karfin yin aiki,shi kake sha kenan shiyasa ka ke da power?" ta fad'a tana nuna damtsen hannunshi dake a murd'e,banza ya mata taci gaba"don dai kace in aka roke ka abu bakayi da nace kabar lemun da zaka bani yanzu sai nima ka samo man iri wannan din,wallahi aiki yawa yake man,inna dawo daga makaranta sam ban hutawa ba kaman gwaggo in tana nan,fatuu yi tankad'e,fatuu dibo ruwa,fatuu fito ki shara,komai ni",

Murmushi ya sake yi yace "wannan ai ba wasu aiki bane,and being a girl dole ki koya irin wannan aikin..." tace "to ai sai in mutum aure za'a masa sannan ni kuma fa ba yanzu zanyi ba sai nan da dadewa,ba na fada maka..." da sauri yace "yea,is a child abuse,je ki daukko wani zan kawo maki wannan din" tace "toh,ta juya,ya bita da kallo,kafin ya maida kallon kan t.v. Lemu fanta ta daukko ta dawo ta zauna a inda ta tashi,ta rike lemun tana d'an wasa da robar sai faman murmushi take da ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsananin farin ciki,sai kallon haisam take wanda idanunsa ke kan tv,juyowa yayi suka hada ido kaman jira take ta d'aga lemu daya tace"Allah yaya hansome kana da kirki wllh,kafi kowa na duniyar nan kirki,wai har kudin shanu gomaa ka yafe tabb,nagode thank u so much,God bless you" ta k'arasa maganar tana noke kai,gyara zama yayi ya d'an kwanta yana kallonta, "in kuma kika karya promise din,na dawo nace ban yafe ba sai kice ni mugu ne,nafi kowa rashin kirki a duniya,right? Girgiza masa kai tayi tace"a'a ai wannan ni naja ma kaina kuma,bama fa zan kara ba tunda nasan da nayi zaka sani,ai nagan ma abubuwan da ke fadi maka abu in akayi baka nan" yace "a ina?" Juyawa tayi tana nuna dakin da taje yin fitsari tace"a cikin dakin naga wani abu babba mai uban wayoyi ajiki,kuma ma naga wasu jajayen abubuwa manne a bango,bokayen turawa ne ko?" shiru ya mata,ya lura ta cika tambaya ta rashin kan gado ita kanta ba kan gadon gareta ba,ganin tana ta kallonshi alamar jira take ya bata amsa,ya d'age gira yace"bokayen fulani ne" da farko waro ido tayi waje cike da mamaki,can kuma sai ta gane gatse ne yayi mata don gwaggo ta saba yi mata,hakan yasa ta d'age kafafunta ta tura kanta ciki tana daria gyalenta ya zamo kasa,

Dago kanta tayi a hankali suka had'a ido dashi tana murmushi tace"ashe kaima ka iya irin abun gwaggo"banza ya mata,ganin ta rungume lemun yace"kisha mana" girgiza kai tayi tace"ba yanzu zan sha ba,dashi zanje makaranta gobe in yi break" jinjina kai yayi sai kuma yace"je ki k'aro wani" daga na hannunta tayi tace"ai wannan ya ishe ni" "What about ur friend,bazaki bata ba,ko ba school daya kuke ba?" tace"wai haulatu,ajin mu ma daya kuma seat dinmu daya da ita,tare ma muke yin break din,ai sai mu raba" shiru yayi yana tunanin halinta ne haka bata da had'ama ko kuwa don yace bai son roko shima" je ki daukko mata wani,in nace kiyi abu just do it banson jayayya" da sauri ta mik'e tana cewa"yi hakuri yaya handsome,taje ta daukko coca-cola ta dawo tana daria ta nuna mashi tace"ita haulatu tunda bak'a ce sai in bata wannan ni kuma tunda fara ce sai in sha wannan jan" ta koma ta zauna hadi da rungume roban lemunan,shidai dan murmushi yayi kawai kafin yace"karfe nawa Uncle din naki ke kulle shagon? tace "k'arfe tara da rabi ko goma cikin sanyi amman da zafi kaman yanzu yana kaiwa har sha daya" time ya duba a wayansa yaga 9:50,yace mata "shi zai zo ya tafi dake ne? tace "a'a haka gwaggo tace dai kar na bari ya tashi,amman in ban koma ba har ya tashin zata aiko ya tafi dani" jinjina kai yayi kawae yaci gaba da kallo,can ya mike don ya gaji bacci yake son yi,gashi gobe akwae aiki,ya wuce bedroom dinsa tana ta kallon bayan shi har ya shige,tana ganin ya shige ta kyalkyace da dariyar farinciki,tana tillah robobin lemun hannunta tana cafewa.

Sanye cikin jallabiya mai gajeren hannu ash color ya fito,komawa yayi inda ya tashi ya zauna yana kallon yadda take wasa da robobin lemun,dagowa tayi suka hada ido tayi dan murmushi a hankali tace"Yaya handsome" shiru yayi kaman mai tunanin wani abu kafin yace"ba sunana haka ba" sakin baki tayi da mamaki tace"amman ai haka naga ansa a jikin riganka" yace"yeah,but wannan rubutu ne kawai", "ya sunanka to?"ta tambaya, d'an k'ankance idanunsa yayi yace"Haitham" cike da mamaki ta rika maimaita duka sunan,haisam da handsome can tace"ai to duk d'aya ne ko wancan da turanci wannan da hausa ko"d'age gira yayi yace"koh? Jinjina kai tayi"eh mana,kuma ni nama fi iya fadin handsome din kuma ai shi ya dace da kai,baka san mi yake nufi bane?" ta fad'a tana daria,dan murmushin gefe kawai yayi baice komai ba,daman saida yayi tunanin zata iya cewa sunan daya ne.

Kallon time ya k'ara yi a wayansa lokaci guda ya mike yana fadin"it's already late,tashi na raka ki" toh tace ta fara kokarin mikewa hannuwanta rungume da lemunan,ta wuce gaba yabi bayanta daidai bakin kofan fita ta juyo da murmushi tace"in ringa zuwa ina gaida ka?"daga mata kai yayi alamar eh,daga haka suka fice.

Unguwar shiru ga duhu saboda an dauke wuta,gidaje kad'an ne gaban su ke dauke da hasken wutar generator da suka kunna wasu kuma solar saidai gaban gidan hajiyan yafi ko ina haske saboda fitulun jikin gidan da suke akunne gaba daya,ko alluran mutum ta fad'i a wurin zai iya ganinta,gaban shagon Amadu ma akwai hasken kwai mai caji ga wasu mutane biyu a tsaye suna siyayya,suna kaiwa daidai rabin bangon gidan hajiyan yaja ya tsaya agaban fence itama tsayawar tayi tana kallonshi hannu yasa ya shafi forehead dinshi gently yace"Good nyt" murmushi tayi itama tace"to good night yaya handsome" jinjina mata kai ya yi daga haka ta wuce.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story._

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*2️⃣9️⃣*

Haisam na ganin ta kai k'arshen katangar ya juya ya nufi gida don yaga akwai mutane gaban kiosk din. Tana gab da isa shagon Amadu taja ta tsaya tana tunanin wani abu sai kawai ta juyo ta nufi lungun dake tsakanin gidajen su da gidan hajia,daidai haisam na niyyar shigewa kwanar gate kaman ance ya juya yaga tasha kwana saboda hasken da ya haska lungun da tabi,tunani yayi a ranshi ina kuma yarinyar zata da daren nan,juyowa yayi ya tsaya yana kallon hanyar data bi,a hankali ya fara tafiya ya koma hanyar daya baro,daidai lokacin da ya kai karshen bangon ya juya yana kallon lungun lokacin ta karya kwanar dama ta shige ya daina ganinta,tsaye yayi yana ta kallon inda tabi yana cigaba da tunani,can ya ayyana kilan aikenta akai bata je ba sai yanzu,"ai kuma cewa tayi ta tambayi zata zo gidan hajiya don ta baka hakuri",wani bangare na zuciyarshi ya ayyana mashi can dai ya d'an ta6e baki hadi da d'age kafad'a daga haka ya juya ya koma gida.

A daidai gaban kofan kwangon ginin data 6uya ranar juma'a lokacin data fasa ma haisam glass ta tsaya,tura kanta tayi tana lek'en ciki wanda yake dund'um ba haske,lokaci guda ta shige ciki ko tsoro bata jiba,ta nufi wata kofa, Zaune suke su ukku saman windunan wani babban d'aki,da gani falo ne aka fitar,suna ta busa hayaki sunyi mankas da wiwi(Allah ka shiryi al'ummar Annabi,Amin),jin motsin mutum ya shigo yasa daya daga cikinsu fad'in"kwalawa yasin...."da karfi yayi maganar duk suka dire na karshen na niyyar direwa da karfi fatuu tace "kai Gaye nice fa" jin hakan yasa shi tsayawa ya juyo yana k'are mata kallo cikin duhu,fiddo wayarsa yayi ya kunna fitila ya haska inda take tsaye,cike da mamaki da kuma fargaba cikin muryarsa ta wanda ya bugu da wiwi yace"Aljana!,kece ko kuwa Aljanar gasken ce" turo baki tayi tace"ni fa ka daina ce man Aljana banso" jin hakan ya tabbatar mashi da itace,juyawa yayi jikin windown yace"Goga,6aure ku dawo ba kwalawa bane" daga haka ya juyo ya nufo fatuu yana fad'in"ke Aljana miya kawo ki fadarmu da daren nan?", "ba kaine kace mutumin nan ko d'an gidanmu bane bazai yafe abunda nayi masa ba,to yace ya yafe kuma ko gwaggotah bazata sani ba" ta k'arasa tana murmura idanu, Gaye yace"wai mi kike magana akai kiman gwari-gwari don ni ba fahimtarki nike sosai ba na riga na dau caji kingane ko" yana maganar ya kasa tsayar da kanshi awuri guda,bude murya tayi tace"wannan mutumin dana fasa ma glass din mota wanda kace kudin gilashin yakai miliyan kuma inba'a biyashi ba gidan yari za'a kaini..." yace "eahh hakane,to minene?", "to yace ya yafe,yanzun nan daga wurinshi nike,naje na bashi hakuri kaga ma har lemunan roba ya bani" ta d'aga lemunan tana nuna masa,waro idanu yayi yana kallon robobin ta hasken fitilan daya kunna ya fara karanta sunansu a wawware"Co,co ca,co-la,da fannntah...", "Wai Gaye yane,mike faruwa ne anan wurin naga ana d'aga lemu ko kawo mana akai mu k'ara ne?" Goga ne yayi maganar wanda tuni suka diro ciki shida dayan suka zauna inda suke da suka ci gaba da bushe-bushensu,Gaye ya waiga yace"baabah ina yarinyar nan wanda muka hadu d'azun da safe na baka labarin ta rotsa ma wani mutum gilashi harma na nuna maka gidansu mutumin?" Goga yace"eah baabah na ganeta wata yar fara mai kumatun nan ko,mi ya faru da ita ne?",

"kaganta nan tazo wai abun mamaki mutumin nan yace ya yafe mata,yanzun nan ta dawo daga wurinshi kaga harda lemunan gora ya bata,shine tazo ta fada man" wata yar iskar dariya gogan yayi yace"yo kai baabah wannan ai ba wani abun mamaki bane,taje ta basa gurasa ba dole ya yafe ba" Gaye ya juyo yana kallon fatuu fuskarsa dauke da yar dariya yace"shegiya Aljanna yar k'arama dake kinsan takan abun,ashe gurasa kika gutsira masa,ahh dole ya yafe kam" cikin rashin fahimtar zancensu da sauri tace"ni wllh ba wata gurasar dana kai masa,yo ni ina naga wata gurasa,dama a bokonmu ake saidawa to kuma yau bama ranar zuwa bace..."

Wata mahaukaciyar dariya gaba dayansu suka kwashe da ita harda gaye,ganin haka yasa fatuu ta d'an tsorata ta juya zata tafi,caraf taji gaye ya ruk'o hannunta,da sauri ta juya tana kallonshi cikin fushi tace"kai Gaye miye haka da Allah sake man hannu ni in tafi gida" kai tabar wiwin dake hannunshi yayi wurin bakinta yace"haba Aljana ya zaki kawo mana ziyara har fadarmu kitafi ba tare da kin ta6a komai ba,kinsan mu akwai karamci,kidan busa kema" da karfi ta buge hannunshi cike da masifa tace"Allah ya tsari kakata Dije,Allah ya kyauta in sha wannan abun,ni ba yar iska bace..." jin hakan yasa Goga da 6aure durowa daga saman windunan da suke zaune suka nufosu a kausashe goga ke fadin"kee,to su waye yan iskan kenan,ai kece ma babbar yar iskar da daren nan fa kika je wurin wani k'ato ya gama dak'una ki,shine don kin raina mu kin d'auke mu masu kawunan kifi zaki wani zo kice wani ya yafe maki hakanan,k'anin gyatumarki ne shi ko na gyatumin ki iyehh??" shuru tayi tana kallon shi ganin yadda yake maganar yasa taji tsoronsu ya kamata gashi sunyi mata rumfa,da sauri ta juya zata fice Goga yasa kafa ya tad'iyota ta yo baya ta fad'i kasa da6ar ass dinta ya daki wani dutsi,da karfi ta saki wata razananniyar kara tace"Wayyo Allah gwaggo!!"

Haisam na komawa falon ya kashe laptop din ya kaita saman desk ya ajiye kafin ya dawo ya dauki cup da can din lemun daya sha ya jefa cikin wastebin din parlon shi kuma cup din ya nufi fridge dashi saida ya dauraye shi a wani d'an madaidaicin basin dake makale a bango gefen fridge din kafin ya maida shi ciki,yaje ya kashe kayan kallo ya rage hasken fitilun wurin baifi guda biyu ya bari a kunne ba,daga haka ya nufi Bedroom hannunshi ruk'e da wayarsa,yana shiga ya jefata saman gado ya wuce cikin laudary,toilet ya shiga yayi brush daga haka ya fito,yaso ya watsa ruwa duk da yayi after ishaa sai dai ya gaji so yake kawai yaji sa a kwance,yadda yake ba tare da yasa sleeping dress ba ya haye gado,saida yayi addu'ar kwanciya kafin ya mika hannunshi yai switching fitilan dakin off daga haka ya kwanta ya lumshe idanunsa alamar bacci.

*** *** ***

Duk'awa Goga yayi inda take zaune tana ta murza wurin da dutsen ya cakar mata yace"kina nufin tafiya zaki batare da muma kin d'an sammana ba,haba ke kuwa,ai ance yaba kyauta tukuici,da gaye bai sanar dake gilashin nada tsada ba ai bazakiyi tunanin kije ki rokesa ya yafe maki ba ta hanyan basa abun dadi" yunkurin mikewa ta fara yi duk da radadin da take ji,hannu yasa ya dannata ta koma kafin yasa duka hannuwansa yana k'okarin kwantar da ita,lokaci guda fatuu ta gane abunda yake kokarin yi mata da sauri ta shiga kiciniyar mikewa tana fadin"ni ka kyaleni,wllh ba abunda naje yayi man saboda Allah ya yafe man,cewa yayi in daina rashin jin magana..." ganin abunda goga ke yi yasa Gaye da sauri ya duk'a gabansa"baabah mi kake kokarin yi haka ne,don Allah rabu da ita ta tafi,zai iya yuwuwa ya yafe mata hakanan kasan suna da kudi sosai fa,miliyan ba wata tsiya bace a wurinsu kyautarta ma sai suba mutum" harara Goga ya dalla ma Gaye yace"koma dai miye yasin bazan ga samu inga rashi ba,abu har gida dama na jima ban k'ara samun irin damar nan ba tunkan yarinyar nan hajara", juyawa yayi yace ma dayan"kai 6aure zo ka kama man in daure shegen bakin nan nata inba haka ba zata tona mana asiri ne" jin haka yasa fatuu kwara baki tace"Wayyo na shiga ukkuna,a taimaken...bata karasa ba ya buge bakin da karfi,a fusace ya juya yace ma Gaye"dallah kai kuma ka rike man kafafunnan nata" baki na rawa yace"don Allah Goga ka kyale yarinyar nan,abun da fa kake shirin yi ba k'aramin laifi bane wllh,hukuncinsa fa daurin rai ne,kana jin yadda kullum ake sanarwa,kuma kaga ta san mu, ba kamar ni har gidan iyayena ta sani wllh asirinmu tonuwa zaiyi baabah" tsawa ya daka mashi yace"to ni wawa ne da zan bari ta tona mana asiri,dallah zo kaji yanda zamuyi" matsawa Gaye yayi gab da shi,alamu yayi masa na ya kawo kunnansa,ya rad'a masa wata magana,a firgice Gaye ya d'ago yana kallon Goga ta hasken fitilan wayansa dake rike a hannunshi,lokaci guda ya shiga girgiza masa kai alamar a'a,ganin haka yasa fatuu k'ara rudewa duk da bata san miya fada masa ba,kara k'arfin wurga kafan da take tayi saboda Goga da 6aure sun riketa gam,ga gefen bakinta ya fashe saboda bugun da yakai mata........,

A hankali ya bud'e idanunsa cikin duhu yana kallon ceiling,duk yadda yaso ya kwanta don yayi bacci ya kasa baccin,abunda yafi d'aure mashi kai tunanin ina yarinyar taje da ya tsaya masa a rai,bai ga dalilin da hakan zaisa ya zama restless ba,juyawa yayi ya koma yana facing window yayi shiru yana tariyo hiran da sukai da ita cikin ransa kaman maison gano wani abu...., "_*_uhm nasan gaye sai yayi mamaki sosai idan yaji ka yafe man,shida yace wai ko dan gidanmu ne kai bazaka yafe man ba,dole sai an biya ka,ko kuma akaini gidan yari,aiko sai na fada masa to ka yafen inna ganshi,nasan yanzu haka suna can kangon da suka saba zuwa yin shaye-shayensu,Allah dai ya shirye suu...._" tuno wannan maganar ta fatuu yasa shi tashi zaune da d'an sauri hannu ya kai ya kunna fitila haske ya gauraye d'akin ya jingina bayansa ajikin headboard,a fili yace"kar dae yarinyan can wurin wannan Drug abuser din taje da daren nan don ta fad'a masa I forgive her..."da sauri ya saukko da kafafunsa ya dau wayarsa ya nufi kofar fita a korido ya tsaya ya sanya wasu slippers a kafarsa daga haka ya fice.

Tsawa Goga ya kwatsa ma Gaye"dallah ka rike man kafafunta,in kai baza kai ba mu zamu yi,kasan kuma ba fita zakai ba,gara ma ka bamu hadin kai kawai muyi yadda na fada maka" ba yadda gaye ya iya dole yabi umarnin goga don shine babbansu ko kayan harkar ma shike kawo masu su siya wani lokacin ma kyauta yake basu don shi mutumin manyan mutane ne,d'an bangar siyasa ne na kirki. Rike kafafuwan fatuu ya fara kokarin yi ta han6arar dashi tana girgiza masa kai,a fusace Goga yace"dalla ka riketa da kyau shegen karfi ne da ita kaman doki" tasowa yayi ya kama kafafun da kyar ya danne su,Goga ya kalli 6aure yace"ina wannan hankacin naka cire sholin ciki ka daure mata baki" ya amsa da toh shikuma goga ya rike ta gam dama duk yafi su girma,bayan ya d'aure bakin,goga yace mashi ya zagayo ya fiddo nashi a cikin aljihun shi ya daure mata hannuwa,6aure ya sake amsawa da toh yayi yadda yabashi umarni,wata yar iskar daria goga yayi yace"yauwa komai ya zama ready,6aure zo ka rike hannuwan don tana iya kwancewa" rike hannuwan 6aure yayi shi kuma ya mike tsaye.....,

Tsaye Haisam yayi cikin center din yana haska gidajen wurin da fitilan wayansa,kokari yake ya gano ko akwai kango a wurin,sai dai a iya haske-hasken da yake baiga wani kango ba yawancin uncompleted buildings din dake layin duk arufe suke da kofofi wasu Gate,dan k'ara gaba yayi yana ci gaba da haskawa har yazo kusan karshen layin baiga kango ba hakan yasa ya fara tunanin ko he was wrong about d girl..."

Daidai saitin kafafun fatuu Goga yazo ya fara kokarin cire belt din tsohon jeans din jikinshi,duk da rirriketan da sukai bai hana ta girgixa kai ba tana dan motsa kafafunta kad'an saboda danne su da Gaye yayi,ga wani gurnani da take,ganin goga na k'okarin cire wandonsa yasa ta k'ara karfin gurnanin da take yi......

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*3️⃣0️⃣*

Juyawa haisam yayi da niyyar barin layin gurnanin da fatuu ke yi ya sauka cikin kunnuwansa abun ka da dare gari yayi tsit da sauri ya juya baya trying to locate inda abun ke fitowa,yana d'an kara taku ya ga kofan shiga wurin wanda take bude ba kofa daidai lokacinne kuma fatuu ta kara k'arfin gurnanin,da sauri ya kutsa kai without second thought ya nufi inda yake jin abun na fitowa, ".....dallah Gaye ka riketa da kyau,wai ya zaka bari k'aramar yarinya tafi karfinka ne,na gaya maka idan kai bazaka yi ba mu wllh sai munyi......." Wannan maganar ta Goga ita tayi ma Haisam jagora zuwa dakin da suke,yana isa bakin kofan d'akin ya haske su da fitilan wayansa da take da haske sosai lokacin goga na niyyar afka ma fatuu,ai suna ganin an haskesu su duka suka nufi windunan wurin da gudu zasu dire,cikin zafin nama haisam ya bisu yana k'okarin kamo goga wanda ke gudu saman wandonsa rik'e da hannunsa,cakk haisam ya tsaya sakamakon wani rad'adi daya ji tun daga kasan kafarsa har tsakiyan kansa,a hankali ya maido kafansa ta dama baya ya haska kafan hagunsa don a jikinta ne yake jin rad'ad'in,kwalba ce ya taka ta hudo ta k'asan takalminshi ta shige cikin kafan sosai,a hankali ya duk'a yasa hannunsa na dama yana kokarin cire kwalbar,sai dai ba karamin yanka tayi masa ba radadi yake ji sosae,runtse idanunsa ya yi yasa hannu ya cije lip dinsa na k'asa da k'arfi ya fisgo ta,har saida yayi dan sound a hankali"ahhh..." saboda azabar da yaji,aikuwa nan da nan jini ya fara zubowa kaman yana jira...

Ita kam fatuu tana ganin duk sun ruga ta fara kiciniyar kwance hannuwanta cikin sa'a d'aurin ya saki ta samu ta fiddo hannuwanta a gigice ta mike ko tsayawa kwance bakinta bata yi ba ta nufi hanyar fita cikin rashin sani saboda kidimewa da tayi ta kaima bango karo a tunaninta nan ne kofar fita,taga-taga tayi tayo baya gabadaya zata fad'i,ganin haka yasa Haisam da ke haskata tun lokacin data mik'e tarbota cikin zafin nama don ba k'aramin buguwa tayi ba,ba kamar goshinta ji kake wani K'UMM!, Sosai ya rungumeta ganin tana ta son kwacewa ta gudu a hankali ya dan duk'a yakai bakinsa saitin kunnanta wanda kanta ke saman cikinshi cikin calm and cool voice yace "is okey,u are safe now" lokaci guda ta gane voice dinshi hakan yasa ta lafe ajikinsa ta kankameshi sosae jikinta sai faman rawa yake da gani ta razana sosae,yayin da shi kuma azaba da radadi keta damunsa a tafin kafarsa haka ya daure ya kai hannu ya kwance hanki din dake rufe da bakinta ya jefar cike da kyankyami don k'auri kawae yake,

bayan wani dan lokaci ganin ta daina kermar ya janyeta a hankali gefe guda ya haska mata tasa takalmanta ya duka ya d'aukko gyalenta dake agefensa ya d'an yarfe shi sannan ya mika mata,ta amsa ta yafa shi saman kanta wanda tuni gashinta ya warware yayi kaman fanka don tana da cikar gashi sosai,a hankali yace"mu tafi"yayi maganar yana haska mata hanya,da kyar ya daga kafansa ya fara tafiya duk da zafin da take masa haka ya daure ya rik'a takata a hankali jini naci gaba da zubowa saboda taka tan da yake, Tana gaba yana bin ta a baya yana haska mata hanya har suka iso bakin kofan fita daga ginin gidan,yana k'okarin sa kafanshi a hankali ya fita yaga ta juyo da sauri zata koma ciki tsayawa yayi yana kallonta ganin haka yasa da sauri tace"lemunana zan daukko" ji yayi kaman ya fizgota ya wawwanka mata mari saboda haushi da ta bashi,tsawa ya kwatsa mata yace"C'mon leave this place...!bakinki ne lemun" da sauri ta juya taci gaba da tafia sumi-sumi. Tana zuwa k'arshen lungun gidan Hajiya ta juya zata karya kwanar gidansu Haisam dake can bayanta saboda a hankali yake tafiyan ya dan d'aga murya yace"muje gidan hajia" ba musu ta juya ta nufi gidan,ta riga shi isa hakan yasa tayi tsaye a bakin kofan parlonsa,bayan d'an lokaci ya k'araso tana ganin ya shigo part din ta tura kopan falon da sauri ta shige,tsayawa yayi bakin tap din da ake ba flowers ruwa ya wanke kafan da takalmin wanda gaba daya kalansa ta koma ja saboda jinin da kafansa keta fitarwa har lokacin,abunka da dan madara,tana shiga ta nufi can gaban armchairs inda tayi kneel down d'azun ta durkushe,

Shigowa yayi bai ko kalli inda take ba a hankali ya nufi kujera ba tare daya cire takalman kafansa ba ya zauna,hannu ya kai ya dauki tissue box ya 6allo mai d'an yawa ya ninninkata kafin ya tura kasan foot dinsa dake zubar da jini,bayan yayi hakan ya mike ya nufi hanyar bedroom d'insa yana dan jan kafan a hankali,binsa da kallo fatuu tayi ta d'an yamutsa baki alamar tausayi,sai da ya shige sannan ta juyo,fitowa yayi hannunshi rike da dan first aid box na karfe ya tsaya ya kunna fitilan sama don ba haske sosai kafin ya nufo cikin parlon,komawa yayi inda ya tashi ya zauna,ita dai fatuu sai binshi da ido take, d'age kafan yayi saman table ya bude akwatin ya fiddo d'an scissors ya fara yanke bakin wound din da kwalbar taji masa,ganin haka yasa fatuu cije hakora tayi wani d'an sauti"shuuu! Sai lokacin yayi mata kallon kasan ido hakan yasa da sauri ta sunkuyar da kanta,dressing din ciwon yayi ya nad'e saitin ciwon da bandage, Bayan ya gama ya d'ago ya kalleta itama kallon shi take,alamu yayi mata da kanshi tazo da sauri ta mike ta matsa gab dashi ta duka cotton ya ciro ya dangwali spirit ya mika mata yace"goge nan" ya fad'a yana nuna mata gefen bakinsa,hannu na rawa ta kar6i audugan ta fara goge inda ya nuna mata sai dai sam ta kasa goge jinin dake a wurin wanda har ya fara bushewa,wata cotton din ya ciro ya dan duk'u yayi mata alamu da hannu ta matso da kanta,goge mata jinin yayi kafin yace"kije wancan room din da kika je d'azun ki wanke face dinki ki ciccire abubuwan dake a kanki ki kulleshi"yadda yayi maganar kaman an masa dole,

Readers Also Read