Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 15
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 15: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 15. Yana zaune agefen yar katifarsa yana cire safar…
4,475 words
Yana zaune agefen yar katifarsa yana cire safar kafarsa ta shigo,aje masa yar kular abincin da cokali asamanta tayi a gabansa tace"gashi nan" tana k'okarin juyawa yace"ruwa fa?"wani kallo tayi masa tana turo baki "kai kawu wai ruwan ma baka iya zuwa kasha in ka gama don kawai ka wahalar dani" harararta yayi cikin d'aure fuska yace"Imi fijirma(ina wasa dake)!zaki kawo man ruwan ko sai na tattaka ki anan,kin iya jin wahalan asa ki yin abu amman baki jin wahalan yawo"tana ta faman turo baki ta koma ta d'ebo masa ruwan ta kawo masa,yar harara ya watsa mata kafin yasa cokali ya fara cin abincin,juyawa tayi zata fita ta hango kwali d'auke da su biscuits dasu sweet aje a jikin bango, d'an juyowa tayi ta saci kallonsa taga hankalinsa na kan abincin da sauri tasa hannu ta rarumo sweet jin karar ta6a kwalin yasa shi dagowa da sauri yace'Fatuu...."da gudu ta fice daga gidan.
________________
Haisam zaune a parlornsa hannunsa ruke da wayarsa yana karatun Al'qurani a hankali ta cikin app d'in Vmuslim,tun bayan da suka dawo shi da Officer direct part din hajiya ya nufa don yin breakfast yasha magungunan da aka bashi,anan ne taga raunin daya ji a kafan,ba k'aramin tashi hankalinta yayi ba taita faman tambayan shi yadda ya samu rauni bacin jiya lafiya lou suka rabu,bai 6oye mata ba ya fad'i mata kwalba ce ya taka amman a part d'in sa yace mata bai fad'i mata ainihin yadda akai ya samu raunin ba,aikam ba k'aramin jimami ta shiga ba mamaki ya cikata na yadda akai akasamu kwalba apart dinsa har ya taka don tasan ko lemun kwalba basu amfani dashi haka dai taita faman jajanta al'amarin,da kanta ta had'o masa breakfast har yunkurin bashi a baki tayi ya hanata yana ta faman dariya,tsare shi tayi sai da ta tabbatar yaci sosae sannan ta 6allo masa magungunan yasha,ci gaba su kai da hira har ya tambayeta miyasa bata je aiki ba,ta sanar mashi cewa tana aikin wani project ne sai ta gama gaba daya sannan zata je,bayan wani lokaci ne hajiyan tayi bak'i hakan yasa haisam din baro part din hajiar,har cewa tayi yaje dakinta ya kwanta yace mata baijin bacci zai koma part d'insa.
A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta tura ta d'an leka ciki,hango shi tayi zaune yaba kopan baya ta yadda duka kafafunsa na asaman kujeran ya mik'ar dasu,k'ira'ar karatun da yake na tashi a hankali, Shiga tayi da yar sallama a bakinta gabanta na d'an faduwa ta nufi can gefen c-table ta durkushe,bai kalleta ba amman yaji shigowar mutum,cigaba yayi da karatunsa ita kuma tana ta kallonshi tana wasa da yatsun hannunta,sai da yakai karshen surar da yake karantawa ya aje wayan a gefensa,tsawon wasu seconds ya d'auka kafin ya juya ya kalleta fuskar nan ad'aure tamkar bai ta6a dariya ba,lokaci guda fatuu tasha jinin jikinta ta shiga motsa baki gabanta na bugawa da karfi da karfi,tana son ta bud'a baki ta gaishe shi amman sam ta kasa saboda ganin yanayin shi,yadau d'an lokaci yana kallonta "Dama ke yar iskace" ya jefo ma fatuu tambaya,a gigice ta zaro idanu tana kallonshi jin abunda yace,girgiza kai ta fara yi a tsananin rud'e tace"A..a...a'a wllh ni ba yar iska bace,na rantse da Allah ban ta6a iskanci da kowa ba kaji na rantse maka...." ta6e baki ta fara yi nan da nan hawaye suka fara zubowa daga idanunta,
Juyar da kanshi yayi gefe sam ba abunda yaso fada ba kenan, it was just an unfortunate slip of the tongue,shi kanshi yaji nauyin abunda yace d'in,kuka sosae take yi tasa hannu tana murzar idanunta sai faman rantse rantse take na ita ba yar iska bace, "Tashi ki tafi" haisam daya juyo yana kallonta yace har lokacin fuskarshi a d'aure,kallonshi tayi tana niyyar magana ya daka mata tsawa"just leave!" da sauri jiki na kerma ta yunkura zata mike gocewa tayi ta bigi c-table d'in dake gefenta sosai ta bugu har sai da haisam ya d'an yamutsa baki,kopar fita ta nufa tanayi tana waiwayenshi tana kuka a tunaninta ko zaice ta tsaya amman bai ko juyo ba balle ya kalleta har ta fita, bakin kopar ta tsaya kaman bazata tafi ba sai shesshekar kuka take yi, A hankali ta fara tattaka stairs din balcony"yanzu shikenan kin 6ata masa rai zai fasa yafewar da yayi hajiya da gwaggo duk zasu sani kuma sannan gwaggon zata san ke ce wadda su Gaye suka kusa yima fyade a kangon su....."zuciyarta ce take raya mata hakan,cikin tsananin rudewa ta juya ta koma jikin kopan kama handle d'in tayi ta dan tura ta kad'an ba tare da ta lek'a kanta ba ta fara magana"Don girman Allah yaya handsome kayi hakuri don darajar Annabi,in kana kaunar maman ka hajiya,wallahi tallahi ni ba yar iska bace kowa ya sani a unguwar nan,wllh ko Bello na gidansu Umar makwabcin mu kwanaki da ya rike man hannu sai da na daddage na falle shi da mari kuma ko haulatu zaka tambaya zata fad'i ma hakan,ko gwaggota ma tasan anyi hakan don har cewa tayi na kyauta dana mare shin" dakatawa tayi taci gaba da kuka tana shessheka,
Duk maganganun nan da take haisam din na jin ta,don tun bayan da ta fita yake zaune still,bai motsa ba ko wayarsa ma bai d'auka ba,gaba daya tun bayan da fatuu tazo wurin shi he felt distubed,shi mutum ne da baison hayaniya,ji yake gaba daya ya takura, Tsam ya mike ya nufi hanyar fita,fatuu najin an kama kopan za'a bude taja baya da sauri sai faman zare ido take,tsaye yayi a bakin kopan bayan ya bud'e yana kallonta ya goya hannayenshi a kirji,itama shi take kallo da kumburarrun idanu fuskarta tayi jage jage da hawaye ganin yana ta kallonta baice komai ba kuma har lokacin fuskarshi a tamke take yasa ta sunnar da kai k'asa had'i da sa gefen gyalenta tana goge hawayen fuskarta hakan kuma yasa gyalen sa6ulowa daga saman kanta,jin shiru bai yi magana ba yasa ta d'an saci kallonshi ta kasan ido suka hada idanu hakan yasa ta d'ago ta marairece fuska ta fara motsa baki kaman zata yi magana amman ta kasa cewa komae saboda kafetan da yayi da ido,
Sauke Ajiyar zuciya yayi calmly yace"ki tafi kawae,in don laifin da kika yi man ne na fasa glass I hv forgiven u already,so karki damu bazan tada maganan ba,kije ki ci gaba da yin rayuwan ki the way you want" yana gama maganar ya juya zai koma cikin parlorn da sauri tace"to don Allah kar kayi fushi dani..."juyowa yayi ya d'an kalleta,ta langa6ar da kai taci gaba"Don Allah,wallahi ni ba yar iska bace,kawai zuwa nayi in fad'i ma gaye ka yafe man shida yace bazaka ta6a yafewa ba shine..."bata k'arasa ba ya juya ya shige, Matsowa tayi jikin kopan wadda bata idasa rufewa ba,ta kama handle din ta ci gaba"Don Allah kayi hakuri kar kayi fushi dani,wllh ko gwaggota da haulat in naga sun yi fushi da ni banjin dad'i" Haisam dake a zaune tun bayan da ya shige yana jinta sai faman ta6a kopan take tana yin yar k'ara,hannun daman shi yasa ya dafe forehead d'insa,wannan shi ake kira da karfen kafa😂.
A hankali ya zame hannun daga kan goshin ya juya ya kalli kopan"Come in" ya fad'a da wata irin dishasshiyar murya,turo kanta tayi jin kaman yayi magana sai dai batasan miya ce ba"kira na kayi"ta tambaya ta inda ta sak'o kan,a hankali ya cira kai ya kalleta,yadda tayi yaso ya bashi dariya amman ya share ya d'an daga kanshi alamar eh,aikuwa da sauri ta idasa shigowa ta nufi inda ta tashi dazun ta durkushe gaba daya gyalen ma ya dawo a hannu daga ita sai Uniform riga da wando ga gashinta yayi wani tumm a d'aure,
Shiru sukai na wani lokaci shi yanata kallonta ita kuma sai faman murzar idanu take da gyalen hannunta,a hankali ta saci kallonsa ganin ita yake kallo yasa ta dakata da abunda take yi itama taci gaba da kallonshi tana kyakkyafta idanu hadi da motsa baki, hannu yasa yana shafa beard dinsa cikin cool voice yace"ga ki kaman zaki wayo ashe baki da shi" kya6e fuska tayi tace"wllh ina da wayo fa" d'an ta6e baki ya yi"da kina dashi ai bazaki je can wurin ba at dat time,da banje in a right time ba baki san mi zai faru da ke ba....", "Nasani,fyade zasu yi man"ta fad'a tana sussunar da kai,still yayi sai dai sam baiyi mamakin jin haka daga bakinta ba,don yarinyar da bata kaita bama yanzu zata san kalmar fyade koda bata san ainihin abunda yake nufi ba saboda yadda ake fadakarwa game da aikatashi a kafafen sadarwa irinsu tv,radio da sauransu,gashi a jiya tace yima yarinya k'arama kamarta aure is a child abuse,yana ganin tasan miye ne auren shiyasa har ta fad'i hakan don inba haka ba ai a garinsu ya tabbatar ana ma yaran da basu kaita bama aure, ci gaba da magana tayi"ai shima a makaranta anyi mana bayani akanshi kuma an fad'a mana abubuwan da zamu yi don mu kare kanmu,ance in wani da bamu sani ba ya kira mu yace zai aike mu wani gida da bamu sani ba to kar muje,ko ya kira mu a wani wuri kaman kango yace zai bamu wani abu nan ma kar muje,ko kuma mu ga wani yana ta6a mana jiki to mu hana shi in bai bari ba muje gida mu fad'i ma iyayenmu,shiyasa da Bello na gidansu umar ya kama man hannu na felle shi da mari" ta kai maganar tana gwada yadda ta mare shin har sai da Haisam ya dan juya fuska,
Juyowa yayi yace"to ai ba gwaninta kikai ba tunda jiya da kafafunki ki ka kai kanki inda za'a cutar da ke" da sauri tace"ni fa wllh kawai zuwa nayi in fad'a ma gaye cewa ka yafe d'in,shida yace wai bazaka ta6a yafewa ba,shine fa abokansa suka ce wai k'arya nike hada cewa wai kai kanin babanane ko mamata da zaka yafe man hakanan wai zuwa nayi ka da....." da sauri ya d'aga mata hannu"shikenan,since they've been arrested duk wannan bayanin zasuyi acan ne ba sai kin maimaita man ba", Jinjina kai tayi tace"za kau suyi bayani mai dalili,duk sai sun yabawa aya zakinta tunda su yan iska ne,amman kasan mi yaya handsome?"Girgiza mata kai yayi alamar a'a tace"wllh shi fa Gaye ba ruwanshi baiso ayi man abun ba,har cema su yayi su kyale ni inyi tafiyata don Allah,don abunda zasu yi man babban laifine hukuncin sa d'aurin rai da rai,amman wannan banzan abokin nashi gago ne ko gogo oho ni ban iya sunan ba,ya ki ya kyale ni wai suma sai na basu abunda na baka,har rantsuwa nayi masu ba abunda kai man don Allah ka yafe man kace kawae in daina rashin ji,amman katoton banzan yaki yarda..."d'an dakatawa tayi tana maida numfashi kafin taci gaba"harfa cewa yayi wai rabon da ya samu irin wannan daman tun akan wata ko hajara,kenan kaga dama sun saba yima yaran mutane fyade ko?"
Haisam da yayi still yana saurarenta tamkar ya kunna radio,ya dan ta6e baki kafin yace"whatever dai zasu yi bayani acan,ke ma in kika je sai kiyi masu duk wannan bayanin" wata zabura tayi ta kwalalo idanu"ni kuma!to ni mi zanje yi police station?nifa ba laifin da nayi Allah,kuma abunda yasa naje wurin gayen da dare saboda banyi tunanin zai cutar dani ba saboda shi wllh ko hannuna bai ta6a rukewa ba,kawae dai in ya ganni yana tsokana na yana ce man wai Aljana", D'an kankance idanu yayi yace"aikam dole zaki je can...." tun kafin ya k'arasa ta fara kokarin rage tsawonta har idanunta sun kawo ruwa alamar zata fara kuka,d'agowa yayi yana mata nuni da hannu yace"No,yi zamanki zaki je ne don akwae bayanai da suke so daga gare ki,yadda incident d'in ya faru,dat's all" komawa tayi ta zauna had'i da yin dan murmushi lokacin kuma kwallan da ta taru ta zubo sharrr,haisam dake kallonta ya dan girgiza kai calmly yace "kuka bai maki wuya ko" tsayawa tayi da goge kwallan da take da gyalen tace"wllh hankalina ne ya tashi,nayi zaton nima kulle ni za'ai,amman kaine zaka kai ni can din?" d'aga mata kai yayi alamar eh,tace"A motar mai fasassan gilashin?" banza ya mata yana mata kallo mai kaman harara,da sauri tace"au na manta kuna da su da yawa,to amman fa gwaggota da hajiyanka basu san abunda ya faru ba,kar kuma su zo su sani,dama yau da na dawo daga makaranta na iske Ladidi mai waina tana ba gwaggo labarin anzo an kama Gaye wai jiya wani mutum ya gansu suna k'okarin yima wata fyade,baka gan yadda hankalin Gwaggota ya tashi ba fa" ta k'arasa had'i da rike ha6a, "Don't worry bazasu sani ba,amman akwae abunda zan fad'i maki yanzu shima yana cikin sharadinmu na glass indai baki kiyaye ba you know what would happen" kasak'e tayi tana kallon shi,d'agowa yayi daga jikin kujeran ya d'an duk'u hadi da linke hannuwansa asaman cinyoyinsa,ganin hakan yasa itama ta goyo hannayenta saman kirjinta ta yi masa kuri da idanu,
On a serious note ya fara magana"I don't want u to repeat same mistake u made yesternight" da sauri tace"ba zan k'ara ba Allah kuwa" tayi maganar tana girgiza kai,Haisam ya ci gaba"kowa da kike gani zai iya cutar da ke,including your own blood brother..." zaro ido fatuu tayi tasa hannu ta rufe bakinta alamar mamaki,haisam yace"yeah.."cire hannun tayi tace"to amman ai ni yayana fa ba anan yake ba yana can garinmu sai dai kawu Amadu harshi kenan zai iya cutar dani din?" nodding kai yayi kafin yace"baki ji nace ko d'an uwanki na jini ba" shiru ta d'an yi alamar tunani can tace"kenan yanzu da kawu Amadu ya kara rike man hannu in gaya ma gwaggo?" girgiza kai ya yi"ba irin wannan ba,ai shi d'an uwanki ne zai iya rike ki..." shiru yayi don bai san taya zai mata bayani ba,fatuu dake ta kallonshi ganin yayi shiru tace"ko kana nufin ta6a cikin jiki?" kai kawae ya d'aga mata,da alama ta kashe bakinshi,jinjina kai tayi alamar ta fahimta can ta d'ago tace"HAR KAI.......?"
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching love story._
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*3️⃣3️⃣*
".....Har kai in kayi man hakan in fad'i ma hajiyanka ko gwaggotah?" komawa yayi ya jingina da kujeran yasa hannu ya rike gemunsa da bakinsa, kallonta kawai yake,fatuu ta wuce duk yadda yake tunani,tai mashi zuru da idanu da alama amsa take jira,ganin haka yasa ya daga mata kai alamar eh,can kuma ya cire hannunsa daga bakin gently yace"But i will never do dat..." da sauri ta katseshi"dama nasan kai baza ka cutar dani ba,kai mutumin kirki ne ai" shi dai kallonta kawae yake kaman yana nazarin wani abu.
"Kin ta6a yin ciwo aka kai ki asibiti?" ya jefa mata tambaya,
tace "A ina?can garinmu ko nan" yace"ko ina" dan langa6ar da kai tayi"acan garinmu ba'a ta6a kaini asibiti ba in ma ban lafiya jik'a man magani ake in sha ko asaman a abinci,kuma ma ni ina dad'ewa banyi ciwo ba fa,yauwa na tuna kaka na yana sawa ana man turaren magani,ba na fad'a maka yace wai shedanu ne su kai man fitsari aka ba,to fa yana nufin wai aljanu gareni"
"da gaske kina da su?" haisam ya tambaya,girgiza kai tayi tace"nidai wllh bani da wasu Aljanu amman sai aita cewa su gare ni ko a makarantar bokonmu ma kowa kallon mai aljanu yake yiman tun daga wata rana da displine master ya bugan man kai na fad'i ina bori shikenan akace aljanu gare ni kuma wllh ina sane nayi borin,to fa haka nan ya tsaneni ko laifi mukai mu da yawa ko bai bugi kowa ba sai ya buge ni,ni kuma shiyasa nayi masa bori dama kuma banson a bugan man kai ai kai ma kasan baida dadi ko?" daga mata kai yayi alamar eh,
ta ci gaba"amman kasan mi,tun daga lokacin wasu malamai suka daina buguna ma ajiki sai a hannu su duk atunaninsu aljanun gare ni harda sauran yan makarantar ma tsoro na ake,sai su rika cewa wai k'arfin da ke gareni ba nawa bane na aljanun ne" ta k'arasa maganar tana ta dariya,shima d'an murmushi yayi sai kuma yace"to ita grandma d'in taki bata fad'a maki ko da gaske kina dasu ba?" gyara zama tayi tace"ai ita dama bata cewa inada su,ko da na fad'a mata abunda ake cewa a makarantar cewa tayi k'aryane in rabu dasu,amman kuma tana cewa zata kaini asibiti wai a binciki kwakwalwata wai banda cikakken hankali,ba kaman in na siyo mata rigima"ta k'arasa maganar tana tikar dariya had'i da sussunar da kai k'asa,shi dae kallonta kawai yake,
"ko kaima kana ganin banda cikakken hankalin ne?" fatuu ta jefo mashi tambaya,girgiza mata kai kawai yayi alamar a'a tace"nifa wllh zafin marin da kayi man ne yasa na jefan maka gilashi kuma nayi zaton in ya fashe kawai za'a walde shi ne kaman yadda ake walde kofa,ashe shi wai sai dai a canja,Allah yaso ni mai kudi kuma mai kirki na jefan mawa ai da kuwa an kai ni asibitin mahaukata mai dalili na gidan yari"ta k'arasa tana dariya hadi da jinjina kai,shi dai d'an ta6e baki yayi baice mata komae ba, jin kafarsa mai ciwo ta sage masa yasa ya d'agata yana k'okarin d'aura ta saman kujerar,ganin haka yasa fatuu cije baki tana yin d'an sauti"shiiii.." juyowa yayi ya kalleta bayan ya d'aura kafan da sauri tace"sannu,da zafi ko?"yar harara ya wurga mata ba tare da yace komae ba ganin haka yasa ta sake cewa"kayi hakuri Yaya handsome,kaji ciwo ta dalili na" ta k'arasa maganar tana turo baki hadi da langa6ar da kai,
d'an daure fuska yayi"ban yin hakurin,kin zaunar dani a gida ban je aiki ba ke gashi kin je school" yar dariya ta yi tace"nama san wasa kake ai,kai da nayi ma asarar million amman ka yafe balle wannan" cike da mamaki yace"kenan ita asarar kudin yafi wannan?" tace"eh mana,million fa kudi ne da yawa",
"to kuma in k'afan ya lalace fa saboda ciwon?" tace"da million ai za'a iya yi mata magani har ma arage canji" jinjina kai kawai yayi yana kallonta underneath his breath ya furta"this's serious!", wayarsa ce ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka yana duba mai kiran Henry shine sunan da ya gani,d'aga kiran yayi kafin ya kara a kunne cikin harshen turanci ya fara magana daga ji wanda yake wayar dashi bature ne don slang english yake yi,ita kuwa fatuu k'ura masa idanu tayi kaman mujiya baki bude,yana cikin yin wayar yayi dariya har hakoransa suka bayyana a lokacin kuma wani abu yaja hankalinta a fuskar tashi,k'ara kura masa idanu tayi cike da mamaki ta ke bin fuskarsa da kallo har d'an kwantar da kanta take yi tana lek'o d'ayan 6arin fuskarshi,duk abunda take yana lura da ita ta wutsiyar idonsa,juyowa yayi ya kalleta bayan ya gama wayan fuskarshi ad'an d'aure tana ganin haka da sauri ta kama kanta tace"naga kana da irin abuna anan amman a dayan 6arin ban ganshi ba"tayi maganar tana nuna masa dimples d'inta bayan ta yake baki tana dariyar yak'e wai don yaga dimples din",
still yayi yana kallonta kafin yace"d'ayan kike nema kenan?" d'aga masa kai tayi alamar eh,ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace"to babu" da sauri tace"kenan kai guda d'aya kayi gado?", d'age gira yayi"meaning?" "ina nufin wurin mamanka ko babanka ka gaje shi,kasan fa in mutum guda d'aya gareshi to cikin iyayenshi guda ke dashi,kaga ita hajiya nasan bata da shi,to kenan a wurin babanka ka gada" jinjina kai yayi yace"ko?" tace"eh mana" can kuma ta rik'e baki da sauri "kai,to ai nima babana bai dashi wllh gashi kuma biyu gare ni,to ya akai hakan ta faru?" ta jefa mashi tambaya,watsa hannuwa yayi yace"how do i know" d'an tunani ta yi kafin tace"nifa dama wata kawata ce itama tana dasu ta fad'i man hakan,amma yanzu na ma gane yadda take nufi,in cikin iyayen mutum guda d'aya na dashi duka biyun to sai mutum ya gaji duka shima,in kuma cikin iyayen d'aya nada guda d'aya to sai mutum ya gaji guda d'aya shima kaman kai kenan" tana maganar tana d'aga hannu kaman malama na bayani,
Gyara zama yayi yace"what if duka iyayen na dasu kuma guda biyu kowa,ya kenan za'ai? dage idanu tayi sama alamar tana nazarin tambayar tashi can ta kalleshi tace"sai mutum ya gaji guda hudu kenan" jinjina kai haisam yayi cike da son jin yadda hakan zata faru yace"ta ya ya?" yatsun hannuwanta manunai tasa ta nuna saitin da dimples d'inta suke tace"kaga nan biyu,sai kuma asamansu ko ak'asan su wasu biyun su fito" shiru haisam yayi yana imagining yadda dimples hudu zasu fito ma mutum a fuska,can yace"ke kin ta6a ganin mai su haka?" shiru tayi tana zare idanu can ta fashe da dariya tace"wllh ban ta6a gani ba,kam yo mutum ma ai kaman Aljani zai koma" dariya shima haisam din yayi har fararen hak'oransa suka bayyana, yace"kawae kin zauna kina shirya man k'arya... " da sauri ta katse shi tana turo baki "wayyo Yaya Handsome wllh bafa k'arya nike ba,baka ji nace wata kawata ce ta fad'i man hakan ba,kaga ita ce ke yin karyar ba ni ba ko",
Sigh yayi ya shafi gefen fuskarshi,ita kuma sai sussunar da kai take alamar taji kunya,d'an Murmushi yayi yace"is okey na fahimta ba k'arya kikai ba" da sauri ta kalleshi tayi yar dariya,shima har lokacin da Murmushi a fuskar tashi "What's ur name?" ya tambayeta,tace"Fatuu,baka ji jiya ina fad'a ba a labarin dana baka",dage gira yayi yace"I mean your real name"
"Fateema"ta bashi amsa,
jinjina kai yayi kawae,shiru sukae na wani d'an lokaci,tana ta wasa da yatsun hannunta, remote haisam ya dauka yai turning tv on,da sauri fatuu ta juya jin sautin tv din, ganin yadda take ta d'age kai tana yin kallon don a k'asa ta ke zaune haisam yace"Zarah..." shuru bata waigo ba da alama bata ji shi ba,d'an daga murya yayi ya kara kiran nata aikuwa da sauri ta waiwayo tace"ni kake kira da Zarah?"
"yeah,ko ba sunan ki bane?" dariya tayi tace"sunana ne,Fateema zahra,amman fa ba wanda ke kira na da haka" tayi maganar tana jaddada mashi da kai,hannu yasa ya shafi beard d'insa kafin yace"nima sunan da kike kirana dashi ba wanda ke ceman haka" kyalkyacewa tayi da dariya tace"ka rama kenan" bai ce mata komae ba, "ka kira ni to" fatun ta fad'a,
yace"just to say u can have a seat,naga kina ta d'age kai zai iya maki ciwo" jin haka yasa ta mik'e tana d'an yake baki"wllh fa harma naji kaman ya fara zafi,to a ina zan zauna wannan ko wanccan" ta nuna d'ayan 6arin kujerar da yake zaune da kuma armchairs d'in dake a d'ayan bangaren "duk inda ya maki" ya bata amsa,yar dariya tayi tace"to bari in zauna can gefen kujeran nan naga kafi zama asamanta nasan tafi dadi ne ko?" dan ta6e baki yayi fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi"in kin zauna zaki ji" tace "to"daga haka ta nufi dayan 6arin L-shape d'in ta zauna ta daidaita zamanta sosae kafin ta juyo tana dariya tace"taushi wllh"d'an Murmushi yayi yasa hannunsa na dama ya shafi forehead dinsa,ita kuma ta juya taci gaba da kallon,
Juyowa fatuu tayi bayan wani d'an lokaci ta yamutsa baki, "yaya handsome wai baka da Arewa24 ne,nifa wllh wannan bangane abunda suke cewa" haisam dake daddana wayarsa ba tare da ya kalleta ba yace"ba kina fahimtar turanci ba" tace"ai nifa irin namu na nan nike dan ganewa ba irin wannan suri surin ba" ta k'arasa maganar tana turo baki,sai lokacin ya d'ago ya kalleta"to ai duk abu d'aya ne.." ta katse shi"to ai nasu gudu yake ban ganewa kai naji ka iya d'azun kana yi,ni sam ban iya ba,in dai akwae Arewan ka maida man" nodding kai yayi yace"baza'a rasa ba sai dai bansan a ina yake ba,let me search" searching Arewan ya fara "kenan kai baka kallon Arewan?"fatuu ta jefo masa tambaya,kai kawai ya d'aga mata alamar eh,tace"tabb kai yan turancin kenan kawai kake kalla shiyasa ka iya kaima,zaka koya man?" nan ma kai ya d'aga mata alamar eh,"to yaushe zaka fara koya mun?" sai lokaci yayi magana ba tare da ya kalleta ba yace"ba yanzu ba,sai ansamu enough time yanzu ina busy" jinjina kai tayi tace"zan jira kuwa,haulat ta bani dani in na iya har malaman makarantarmu ma sai na nuna masu su basu iya turanci ba...." da saura ta juya ta kalli tv jin ana magana da hausa lokaci guda ta washe baki tace"yauwa ga inda muka fi wayo nan...." juyowa ta sake yi a kalli haisam rai adan 6ace tace"wllh su Arewar nan sai suyi ta maimaita film" d'ago kai yayi ya kalli tv din sai kuma ya maida kan akan wayar da alama wani abu yake da ita, "Don Allah yaya handsome ka maida Tauraruwa ko Hijira suma duk hausa ake yi" ba tare da ya dago ba yasa hannu ya dauki remote din ya mik'o mata,bin shi tayi da ido ba tare da ta taso ba,hakan yasa ya dago yace"ki zo ki amsa mana" tashi tayi ta nufesa tsayawa tsaye tayi a gabansa bayan ta kar6i remote d'in tace"nifa ban san ya ake yi ba,bamu da dish agidanmu" dagowa yayi da d'an mamaki ya kalleta,to in basu dasu ya akai duk tasan channels din da ta fadi mashi yanzu,kaman tasan mi yake tunani tace"dama a makwabtanmu nike zuwa yin kallo,mu yar tv garemu da vedio to daga baya aka saida vedion aka siyo DVD muna kallon cassette,kuma sai tv din ta lalace aka kaita gyara bayan ta gyaru munci gaba da kallo kuma wai rannan sai aka maido wuta da karfi ta sake lalacewa da aka kai gyara sai aka ce ai ta kone ne,tun daga lokacin ne bamu da kayan kallo,ita kuma banzar Naja'atun da nike zuwa gidansu kallon rannan muka yi fad'a har na falleta da mari shine tayi man gori tace karna k'ara zuwa gidansu kallo,ni kuma sai na daina zuwa don banson inje ayi man wulakanci don ba kyalewa zanyi ba ko innarsu ce tayi man sai na rama ehe,ai dai arziki na Allah ne suma ba finmu sukai ya basu ba" ta k'arasa ranta a 6ace ta kumbura baki da alama abun yayi mata ciwo,ganin haisam din yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace"ina nufin fa ada lokacin da banjin magana shine ba zan kyalen ba,ni yanzu bama ruwana dasu,anan gidan nike yin kallo in na zo wurin hajiya,kuma kai naga abun naka ba irin nata bane shiyasa bansan ya zanyi amfani da shi ba",
Sigh haisam yayi Calmly yace"kome ta maki laifin ki ne miyasa zaki mare ta,ke komae aka yi maki sai bugu" ya k'arasa maganar ya dan 6ata fuska,ganin haka yasa fatuu marairaicewa tana nannok'e kai muryarta kaman zata yi kuka tace"to ai ita ta ja ni fa,raina man wayo tayi ni kuma naji bazan iya hakuri ba,kai ma rannan dana yi maka ba daidai ba ai mari na kayi ko amaimakon kayi hakuri",