Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 17

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 17

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 17: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 17. "Abun ciwon ne na kawo maka"ta fad'a har lokacin…

4,438 words

"Abun ciwon ne na kawo maka"ta fad'a har lokacin hannuta na rufe da bakinta,he was speechless,cike da mamaki Haisam ke kallonta jin abunda tace wai abun ciwo ne ta kawo masa,cire hannun tayi ganin kallon da yake mata"ba d'azun kace ban kawo maka komae ba,shine yanzu na kawo" tayi maganar tana turo baki,

d'an Murmushin mamaki yayi yana jinjina kai"Open it let me see what's inside", hannu tasa ta bud'e ledan ta d'an turata gabanshi,bin fruit din yayi da kallo,tunani ya shiga yi cikin ransa yana fad'in wani irin yarinya ne wannan,d'agowa yayi ya kalleta"baki san wasa bane,ni wasa nayi maki ai ba ina nufin ki kawo man wani abu ba...."katseshi tayi"ai yakamata dae in kawo d'in tunda dama saboda ni kaji ciwon ko"dan ta6e baki ya yi kawae,in ya biye mata haka zasu yi ta jan maganan"a ina kika samu kudi haka?"ya tambaya yana ci gaba da kallonta, d'an langa6ar da kai tayi tace"Kud'in adashe ne da muke yi nida kawayena yan makarantar bokonmu,to ni ce ke yin tari don ban yarda ba in ba wata kudina ta cinye",

"amman ai ke gashinan sun yi trusting dinki sun baki kuma kin kashe masu, "ai zan biyasu dama d'ari biyar ce kawae ta adashen naira d'arin tawa ce hajiyanka ta bani,itama d'ari biyar d'in dama nida wata za'a ba kwasa yanzu,to rabi nawa ne rabin ne nata"

"Yanzu ina zaki samu rabin ki biyata da kika kashe mata?" yar dariya tayi"zan samu mana ai gwaggo na bani kudin break kuma sai nayi kalaci nike tafiya makarantar kaga sai in tara kudin,kuma hajiyanka ma na bani,ga kawu Amadu ma in nace ya ban wani abu zai ban duk sai in had'a in bata"shiru Haisam yayi yanata kallonta, "ko bazaka sha bane"ta tambaya jikinta a d'an sanyaye,girgiza mata kai yayi"zan sha,amman karki k'ara yin haka,ni wasa nike maki" dan ta6e baki tayi"kenan ni baka son in baka abu?"

"Ina so,amman ba wanda zaki ta6a ma mutane kudi ba,understand?"jinjina mashi kae tayi tace"to ban k'arawa Yaya handsome,da ai abinci ma zan kawo maka kace bazaka ci ba,shiyasa ma na siyo wannan din", "Na koshi ne,da zan ci ai" ya fad'a da d'an murmushi,itama Murmushin take tana kallonshi,

k'okarin mik'ewa ya fara yi"nafa yi wankan" fatuu ta fad'a, d'aga mata kai yayi yana kallonta daga tsaye,ta ci gaba"wllh nayi,ina komawa gida kafin na tafi islamiyyar nayi kawae ban shafa turare bane shiyasa baka ji kamshi ba"ta k'arasa tana d'an sunsuna hijab dinta "miyasa baki sa turaren ba"haisam ya tambaya, "ai bandashi yanzu,dama gwaggo ke siyo man a wurin abokiyar aikinsu irin wanda ake sawa a yar kwalbar nan irin ta fiya fiya,ka santa?" kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"to irinshi,wanda garan rannan ina cikin shafawa ya fad'i ya fashe,amman tace zata siyo man wani"jinjina kae yayi alamar toh,cikin cool voice d'insa yace"yanzu zanje masallaci time yayi" da sauri fatuu tace"to su kankanar fa bazaka sha ba?",

"Zan sha mana,amman yanzu kinga sallah zanje,abunda za'ai ki tafi man dasu part d'in hajiya in nagama zanzo sai in sha,kema sai kiyi sallan ko" kai ta d'aga alamar toh ta mik'e bayan ta d'auki ledan,harta nufi kofa ya tsaidata"Zarah"juyowa tayi ta kalleshi,"wait,am coming"d'aga haka ya juya ya nufi bedroom d'insa,bai jima ba ya dawo,mik'a mata wani had'add'an kwalin turare yayi yace"kiyi amfani da wannan baida karfi sosae,za'a samo maki wasu" zaro idanu waje tayi ganin tana niyyar yin magana ya rigata da fad'in"ba rokona ki kai ba" dariya ta saki tace"ya akai kasan abunda zance Yaya handsome"shima yar dariya yayi"amsa kisa a bag d'inki" kar6a tayi tace"thank you Yaya Handsome" kai ya d'aga kawae daga haka suka nufi hanyar fita tana gaba yana bayanta.

Suna zuwa daidai fence door d'in fita daga part d'in nasa ta juyo da sauri da yake shi a hankali yake tafiyan saboda kafansa mai ciwo,ad'an rude tace"akwae matsala Yaya handsome,in na kae maka wannan fruit d'in part d'in hajiya kuma ta gane abunda ya faru fa ko ka gaya mata ne??"ta kai maganar tana ta zare ido,d'an lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a kafin Calmly yace"don't worry ur self bazata gane ba"jinjina kai tayi harta juya sai kuma ta sake juyowa "Yaya handsome ko ka dafa kaina mutafi naga dakyar kake tafiyan"da'n bude idanu yayi da murmushin da iyakarsa saman lips d'insa yace"sai dae in rankwashi kan" dariya ta kyalkyace da ita ta juya,

A harabar gidan ta tsaya tana yima dawisu wasa can ta d'aga kai ta kalli haisam da ya kusa isa kopan shiga masallaci ta kware murya tace"Yaya Handsome,don Allah kai man Addu'a Allah yasa in zama likita" hannu ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba daga haka ya shige cikin masallacin lokacin ana cikin tada ik'ama,saida ta gama shiriritarta a harabar gidan kafin ta nufi part din Hajiya.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*3️⃣6️⃣*

Lokacin da fatuu ta shiga parlon ba kowa,deep freezer dake a Dining area ta nufa ta bud'e ta saka ledan fruit d'in kafin ta nufi corridor d'in d'akunansu,bedroom d'in hajiya ta fara zuwa ta isketa tana yin salla hakan yasa ta fito ta nufi d'akin Saude itama sallan ta taras da ita tana yi, shiga ciki tayi ta aje jakarta a gefen k'atuwar katifar sauden ta nufi toilet ta d'auro alwala itama tazo ta kabbara sallan,

Juyowa fatuu tayi ta kalli Saude dake zaune tana yin lazimi bayan ta gama sallan tace"ina yini Aunty Saude "fuskarta da fara'a ta amsa" lafiya lou fatima yar gidan hajiya,ya makaranta? "Lafiya lou" ta bata amsa,daga haka ta mike ta fita,bata jima ba ta dawo har lokacin sauden na a zaune,kallonta fatuu tayi bayan ta zauna"Aunty Saude kin daina koya man abincin yan gayu", Yar dariya tayi"ai ba lokaci ne fateema kinga kullum kina zuwa makaranta ga kuma islamiyya ki bari in aka sake yin hutu sai in ci gaba da koya makin ko kuma tunda Azumi ya kusa ma kinga sai mu yi a lokacin don an fi yin abubuwa da yawa"jinjina kai fatuu tayi, Saude ta ci gaba"wai ina kawar nan taki ne kun rabu da zuwa tare",

"wai Haulat,tana nan,sai azumi yazo za ki ganta tana lalla6owa shan A.c"dariya saude tayi, fatun ta sake mik'ewa ta fita bata jima ba ta sake dawowa,ganin tana ta zarya yasa Saude fad'in"Hajiya kike jira ne,kinsan in tayi magriba sai ta yi isha'e take fitowa... "Fatuu ta katseta"a'a ba ita nike jira ba,Yaya hansome ne yace in jira shi anan" ba tare da saude taji sunan da ta kira shi da shi ba tace"ai kuwa shima wani lokacin sai anyi isha'in yake shigowa" d'aga kai fatuu tayi"to bari inje in gaisa da mutumina Aku kafin ya shigo"ba tare da ta jira abunda sauden zata fad'i ba ta juya ta fice,

Hajiya ce ta shigo cikin parlon bayan angama sallan isha,zama tayi akan kujera 2 seater ta d'au remote tana kokarin canja channel Haisam ya shigo da sallama 3 seater ya nufa ya zauna,hajiya ta juyo tana kallonshi da d'an murmushi, shima murmushin ya mayar mata"hope u'r ok sweethrt", "lafiya kalau nike" hajiyar ta bashi amsa tana shirin k'ara yin magana fatuu ta shigo cikin falon da gudu ta kofar baya,juyawa hajiya tayi tana kallonta har ta k'araso ciki a gefen hajiyar ta zauna tana ta dariya"ke kuma yaushe kika shigo?" hajiya ta tamabaya, maimakon ta bata amsa sai cewa tayi"wllh hajiya wancan Akun ya raina ni na kusa in mashi jan bugu"ta k'arasa tana nuna yadda zata buge shin da hannu, hajiya tace"toh,yau kuma miya hada ki da mutumin naki ne?"

"wai daga nace Aku mai fitsari a tsaye shine yace man fatuu mai kashin kwance" hajiya tace"ah laifinki ne don mi zaki ce masa mai fitsarin tsaye a ina kika ga yana fitsari a tsaye"turo baki tayi"to ai ni wasa nike masa ko" hajiya tace"ai shima wasan yake maki nasan,ina Dije ko tana wurin aikin?", "Eh tana can tana faman share-share da goge goge" hannu hajiya tasa ta d'an bugi kafad'arta"ja'ira aikin nata kike ma tsiya,ai da share sharen take biya maku buk'atunku ko,ita dije yanzu ai saidae ma tasa ayi don babba ce ita,ta jima tana aikin gashi har ta iya allura ciwo ma in bai tsanani ba tana fad'in maganin da za'a ba mutum.... " fatuu ta katseta"har k'arin ruwa ma tana sa ma mutane"hajiya ta jinjina kai"to kin gani,ai dije akwae kwazo",

Juyawa tayi ta kalli haisam dake danna wayarsa ya d'an kishingida hadi da mikar da kafafunsa saman kujeran sai kuma ta saci kallon hajiyan ganin ta maida hankalinta kan tv yasa ta mik'e taje gabanshi a hankali kaman mai rad'a tace"in kawo maka fruit d'in?" ba tare da ya kalleta ba ya d'aga mata kai alamar eh,juyawa tayi ta nufi hanyar kitchen,sai da ta bud'e freezer ta fiddo ledan kafin ta shige cikin kicin din,a saman plate mai dan fad'i ta jero mashi bayan ta cire bawon su ta yayyanka amman bata yanka Apple d'in ba,yadda ta jera su sunyi gwanin sha'awa.

Gefen kujeran da haisam yake ta aje kafin ta juya ta kinkimo sofa table hakanne yajawo hankalin hajiya kanta ta bita da ido ganin abunda take,gaban Haisam ta aje table d'in ta daukko plate din fruit din ta d'aura,fuskarta d'auke da d'an murmushi bayan ta mik'e tace"Yaya handsome gashi nan"sai lokacin ya juyo ya kalli fruit din kafin ya d'aga kai ya kalleta shima murmushin yayi ahankali yace"thanks", hajiya da ta saki baki tana kallonsu tace"ina aka samu fruit ko Tk ya dawo ne?shi naba sakon ya taho dasu d'azun da nace Saude ta had'a man fruit salad take sanar dani sun k'are",

juyowa fatuu tayi ta dawo wurin hajiyan ta zauna"ba shi bane wannan na Yaya handsome ne", "toh yaya handsome kuma?" hajiya ta tambaya,kai fatuu ta daga mata alamar eh,juyawa tayi ta kalli haisam wanda gabadaya hankalinshi na akan wayansa da alama chatting yake sai faman Murmushi yake tace"kai ka zo da ftuit dinne?" Kafin ya bata amsa fatuu ta amshe"ni na kawo masa abun ciwo ne,baki ga bai lpy ba" da mamaki hajiya ta kalleta"ke kika kawo masa?" jinjina mata kae fatuu tayi alamar eh sai kyakkyafta idanu take hajiya tace"daman kinsan Haisam ne?", "Eh mana baki ji har sunanshi na fad'i ba" dan ta6e baki hajiya tayi sai kuma tace"amman baki ta6a ceman kin sanshi ba,shi dae nasan magana bata dame shi ba daman ba lalle ya fad'a man ya sanki ba..." da sauri fatuu ta tari numfashinta"to nima ai ina da sirri ko" bud'e idanu hajiya tayi cike da mamakin maganar fatuu tace"ah lalle kam ni shaida ce,amman yaushe kika san ya samu raunin ne?naga jiya da dare ya hadu da tsautsayin" wuki wuki da idanu fatuu tayi ganin kaman hajiyan nason ganota,turo baki tayi tace"kai hajiya bafa kyau zurfafa bincike nasan kin sani,nace maki na sanshi baki ji ma yaya nike ce masa ba,ai d'azun bayan na dawo boko nazo shine naga bai lafiya to ban shigo nan ba saboda lokacin islamiyya yayi shine fa na tafi" jinjina kae hajiyan tayi alamar gamsuwa,

Kallon Haisam tayi ganin hankalinshi na akan waya bai shan fruit din tace"Yaya handsome kasha mana" ta6e baki hajiya tayi"uhmm karma ki wahalar da bakinki...." maido idanunta tayi kan hajiya"bai shan fruit ne?"ta tambayaa, "Yana sha amman shi fa komae sai an matsa masa yake ci kaman wani k'aramin yaro,kwata-kwata baison cin abinci ina ga dae tsukakkun yan hanji ne dashi" zaro ido fatuu tayi ta juya ta kalleshi har lokacin idonsa na kan wayar tamkar bai jin abunda ma suke cewa,hajiya taci gaba"kinga dae yadda yake k'ato tubarkallah, kamata yayi ace yana cin abinci hannu baka hannu kwarya,amman sam baison cin abinci k'irar tasa duk bogi ce ta k'arfe ce,yanzu fa inda zai sha fruit dinnan to wllh kina iya ganin ba lalle ya k'ara cin wani abu ba da daren nan,k'ilan sai dae ko tea da biscuit ko snacks,yafa iya yan ciye ciye maras amfani shi ga bature", ta k'arasa tana turo baki, daman rashin cin abincin nashi na damunta,ita kam fatuu tsura mashi ido tayi tana tunani cikin ranta"ashe abubuwan da ya bata d'azun sune abincin shi bai son cin abinci.."ji yayi ajikinshi idanu na yawo akansa hakan yasa ya juyo ya d'an kalleta tana ganin sun had'a ido tayi masa alamun ya sha fruit d'in da hannu tana yamutsa fuska,wani kallo yayi mata mai kama da harara ya juya yaci gaba da lallatsa wayansa.

A hankali yasa hannu ya d'auki Apple d'in ya kai bakinsa ya gatsa,lokaci guda fatuu dake kallonshi ta saki Murmushin jin dadi dama tasan zai so Apple d'in tunda shi d'an gayu ne shiyasa ta matsa sai da mai kayan marmarin yasa dashi,juyo idanunsa yayi ya kalleta, washe baki tayi tana dariya hakan yasa ya d'an mata side chuck kafin ya mayar da kanshi kan wayar yana ci gaba da cin Apple d'in, "U have a message" Haisam ne yayi maganar,juyowa hajiya tayi tace"sak'on mi?" batare da ya bata amsa ba ya d'an d'aga mata wayarshi lokaci guda wata zazzakar murya ta fara magana,_"Hi Granny!how are u,kin manta dani ko?"_ daga yadda mai muryan tayi magana da hausa zaka fahimci hausar tata bata nuna ba sosae, lokaci guda hajiya dake kallon haisam ta washe baki tana fad'in"Allah sarki Fanan,ai in dae na manta dake na manta da kaina kenan,kira man ita don Allah in wanke kaina" sauke wayan yayi ya fara kokarin kiran fanan d'in,tana fara ringing haisam ya kalli fatuu yayi mata alamar tazo ta amshi wayan ta mik'a ma hajiyan,tasowa tayi ta kar6i wayan kaman yadda ya mata umarni,hajiya na amsa aka d'aga kiran suka fara waya da Fanan din,

A hankali fatuu ta mik'e ta nufo wurin da haisam ke zaune,tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi had'i da yin d'an murmushi,hannu yasa ya daukko ayaba yakai bakinsa yad'an gatseta kafin ya d'ago idanunsa ya kalli fatuu dake atsaye,sauke kafansa guda k'asa yayi d'ayar kuma mai ciwon ya mik'ar da ita kan kujeran,kallonta ya sake yi yace"Seat" a hankali ta zauna d'ayan 6arin kujeran ta d'aura hannunta d'aya kan hannun kujeran tayi tagumi dashi har lokacin da Murmushi akan fuskarta,ci gaba da shan fruit din yayi idonsa akan tv can suka had'a ido da ita,ganin tana ta kallonshi ne yasa shi tunanin ko fruit d'in take so ne,ita kuma yadda yake sha ne abun yayi mata dad'i tayi zaton ba zai sha ba kaman yadda hajiya tace,

d'aukko plate d'in fruit din yayi ya aje agabansa ta yadda ya kasance atsakiyansu kenan,kallonta yayi a hankali yace"eat"da sauri ta girgiza mashi kai"ni da na kawo maka kuma sai in shanye ma" yar harara ya wurga mata"what did i told u yesterday?ba nace in nace kiyi abu ba kawae kiyi"ganin yadda yayi mata maganan yasata saurin cewa"yi hakuri to"hannu takae ta d'aukko 6allin kankana ta fara sha tana satar kallonshi,shikam hankalinshi na kan tv,duk wannan abun hajiya na akan waya sai faman hira suke da Fanan din da aka kira mata,

Hannu fatuu ta kai zata d'auki fruit carab Haisam yaji ta kama yatsan hannunshi,da sauri ya kae idonshi kan hannunta dake ruke da yatsan nasa,da mamaki ya d'ago ya kalleta sam hankalinta na akan tv da ake Indian film,batama san ta kama yatsan nasa ba,jan yatsan ta fara duk a tunaninta fruit d'inne,jin yaki daukuwa yasa ta juyo takai idonta kan fruit din,zaro ido tayi ganin ta kama yatsan Haisam,da sauri ta saki ta dago suka had'a ido dashi a rude tasa tafin hannun damanta ta rufe baki tana girgiza masa kae alamar batasan tayi ba,cire hannun tayi tana kokarin yin magana ya dakatar da ita da hannunshi,cigaba yayi da shan fruit din yana kallo,ganin haka yasa itama taci gaba da sha tana kallon sai dae duk in zata dauka sai ta juyo ta kalli fruit d'in gudun karta k'ara ruke masa yatsa,

Juyowa hajiya tayi bayan ta gama wayan ta kallesu, mamaki ta shiga yi cikin ranta na yadda akae suka san juna haka,shidae haisam tasan ba mai shiga harkar mutane bane balle kuma yarinya kaman fatuu,tunowa da halin fatun na sam bata jin magana kuma bata da shariya sannan tana da saurin shiga ran mutum yasa ta kawar da mamakin,

"Abun yar wariyar launin fata ce kenan" hajiya ce tayi masu maganar,juyowa fatuu tayi ta kalleta tana dariya hajiyar taci gaba"wato don kun ganku farare shiyasa ni bak'a aka ware ni ko"sosae fatun ke dariya,shima haisam d'in da idonsa ke akan tv d'an murmushin gefe yayi jin abunda hajiyan ke cewa,fatuu tace"ai akwae saura a kitchen in kawo maki ne?" kafin hajiyan ta bata amsa haisam ya maida dubansa kan fatuu da ta juyo ta kalleshi tana dariyar maganar hajiya"d'auka kikae mata" da sauri tace"da gaske fa akwae saura bari in..." katseta yayi"ki kai mata wannan na koshi" sukuku tayi da fuska ganin haka yace"zan sha sauran anjima" yayi maganar idanunsa ad'an lumshe,mik'ewa tayi ta dauki plate din ta nufi wurin hajiyan,

"Sauranku zaku ban in sha don kun raina ni ko" d'an murmushi fatuu tayi"to ai shi yace in kawo maki ya koshi"ta aje plate din a gefen hajiyan itama ta raku6a gefe ta zauna,hannu hajiya takai ta fara shan fruit din,itama fatun tasa hannu zata ci gaba da sha,da sauri hajiya tace "a'a sauran ma bazaki barman ba,ke baki koshin bane?"dariya fatuu tasa ta jingina kanta da kujeran,atare suke shan fruit d'in suna kallon Indian film d'in da ake a Bollywood da alama yana masu kyau ne,

Haisam ne ya fara k'okarin gyara kafarsa mai ciwo jin ta sage masa,hakanne ya jawo hankalinsu kanshi, "Sannu kabi a hankali" hajiyace tayi maganar,d'aga mata kai kawae yayi taci gaba da magana"ni wllh har yanzu mamakin yadda ka taka wai kwalba nike,muda ko lemun kwalba bama amfani dashi,in kaga kwalba a gidan nan sai ta turare ko tasu salad cream su kuma wannan dama iyakarsu cikin kicin ne,da sun k'are kuma sai cikin dustbin amman sai gashi wae ka taka kwalba a part d'inka,abun ya d'aure mun kai,wae ko dai ka fita waje ne?" ta k'arasa maganar idonta akan haisam tana jiran ya bata amsa,fatuu kau gaba d'aya ta zaro idanu ganin kaman hajiyan nason gano gaskia,

da sauri fatuu tace"a...ai hajiya k'ilan a k'asan take fa"a rude tayi maganar, "taya hakan zai yiwu bacin harabar part d'in nasa interlock ne,bafa k'asa bace balle ace kwalbar ta shige ciki ne" sosae gaban fatuu yake bugawa"ai ko shi d'in kwalbar zata iya shiga..." hajiyar ta katseta"bulo ne fa fateema" duk maganganun da suke Haisam d'in na jinsu don yana niyyar yaba hajiyan amsa lokacin da ta tambayeshi fatun ta rigashi yin maganar shiru yayi yana sauraransu idanunsa akan tv,so yake yaji yadda zata fidda kanta,

Fatuu taci gaba"ai a bulonma kwalba na mak'alewa" hajiya tace"kai fateema anya kuwa,su masu yin bulon har basu gani ba lokacin da suke yi su cire" fatuu dake ta zare ido tace"to ai ba inji bane yake kwa6a masu simintin da yashin ba,ai ba lalle fa su gani ba,ni nasha ganin kwalba ajikin bulo a gidajen da ake ginawa a hanyar islamiyyarmu" cike da al'ajabi hajiya ta ruke ha6arta"kuma fa hakane wllh,dama kinga part d'in nasa sabone kafin ya dawo akulle yake,ko ada in yazo kafin ya dawo nan,acikin nan yake zama,yanzu saboda zai dade ne aka idasa gina can d'in.."fatuu dae sai gyad'a kai take,hajiya taci gaba"aikuwa bari zansa Tk ya samo almajirai abi k'asan part d'in nasa adudduba inma akwae saura su cire saboda gaba kar ya k'ara takawa..." fatuu ta kar6e"haka yakamata nima zan tayasu aduban",

"Yauwa haka kawae za'ayi ma..." hajiya bata k'arasa maganarta ba sakamakon sautin yar dariyar da haisam ya saki,abunda ya bashi dariya shine yadda yarinya k'arama ta zauna tana mata wayo,

"kaji wulakanci muna tattauna yadda zamu kare lafiyarsa yana mana dariya" Hajiya ce tayi maganar idonta akan haisam,d'an juyowa yayi ya kalleta suka hada ido tace"mu kake ma dariya don mun damu da lafiyarka" d'an girgiza mata kai yayi"baki ga ina kallo bane",ya kai idanunsa kan fatuu bayan yayi maganar,tayi wuki wuki gaba daya tayi kalan rashin gaskiya,wani kallo yayi mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ya ci gaba da kallonshi,

"Fateema yakamata kizo ki tafi gida dare yayi sai kuma Allah ya kaimu" hajiyace tayi maganar idonta akan agogon dake parlon, "Ni yau nan zan kwana" ta ba hajiyar amsa,kallonta tayi"amman dae kinsan gobe akwae makaranta ko,ki bari ran juma'a in Allah ya kaimu sai kizo nan kiyi weekend ma tunda ita islamiyyar bada sassafe ake zuwa ba" turo baki tayi tana niyyar yin magana haisam ya jefo mata wani kallo nan da nan taja baki tayi shiru,dama abunda yasa tace anan zata kwanan saboda ta kasa ta tsare don kada ta gano gaskiya,jiki a sanyaye ta mik'e zata tafi,hajiya tace"gashi ko abinci ma baki ci ba,mun zauna munata zance....",

"na koshi"ta fada fuskarta a yamutse, "A'a bari dae a zuba maki ki tafi dashi in ke bazaki ci ba ai Dije da Amadu sa ci" tana kai maganar ta juya tana kwala ma Saude kira,fitowa sauden tayi ta nufo cikin parlon hajiya ta dakatar da ita"ki zubo ma fateema abinci cikin kula"amsawa sauden tayi da to ta juya ta nufi kicin,sai lokacin fatuu ta tuna da jakarta dake a d'akin sauden taje ta daukko,lokacin da ta fito sauden ma ta fito daga cikin kicin wurin fatun taje ta mik'a mata,amsar kular abincin tayi ta rungume a hannunta d'aya,gudan kuma yana rataye da jakarta,daga haka ta dawo cikin parlon kallon hajiya tayi"sai Allah ya kaimu hajiya", "To fateema Allah ya tashemu lafiya,ki gaida dije",kai kawai ta d'aga mata,hajiya ta maida kanta kan tv,juyawa tayi ta kalli haisam da idanunsa ke kan tv shima"Yaya handsome sai da safe" jinjina mata kai yayi batare da ya kalleta ba,ba haka fatuu taso ba,so tayi ya kalleta don ta k'ara rokonshi akan karya fad'a ma hajiyan,

Hanyar fita daga parlon ta nufa tana yi tana waiwayen haisam wai ko zai juyo amman har takae bakin kopan bai juyo ba,tsaye tayi tana ta kallonshi ta kasa fita,kaman yaji ajikinsa ne yasa shi waiwayawa ya d'an kalli kopan fitan,da sauri fatuu ta aje kulan abincin ak'asa ta had'a hannayenta ta fara rokonshi tana magana kasa kasa had'i da jujjuya kanta,still yayi yana kallonta fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi,suna cikin haka hajiya ta juyo da niyyar yi mashi magana,ganin inda yake kallo yasata juyawa ta kalli bakin kopan karaf idanunta suka sauka akan fatuu,cike da mamaki ta furta"Fateema......."aikuwa da sauri fatun ta d'auki kulan ta fice.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

_Gashi nan 2 pages ne,ku da update sai Next week in Allah ya kaimu kar inji wani yace yau ba'a posting ne,within the Weekend🤨_

*3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣*

Da sauri Fatun ta d'auki kulan ta fice,maido idanunta tayi kan haisam da shima ya d'an kalleta kafin ya mayar da idanunsa kan tv,kanta ne yai matuk'ar d'aurewa,tunanin anya ba wani abu suke 6oye mata ba ta shiga yi,tasan halin kowannensu sarai shiyasa tun farko tayi mamakin ganin suna shiri sosae, "Haisam" hajiya ta kira sunanshi,juyowa yayi ya kalleta ba tare da ya amsa ba,taci gaba"mike tsakaninka da fateema ne?" d'an guntun murmushin da iyakarsa kan lips dinsa yayi"kinji ki da wani magana sweetheart mike tsakanina da ita fa..." katseshi tayi"ina nufin ya akai kasanta,ko tayi ma wani abunne don nasan halinta bata jin magana,kuma naga kaman kuna 6oye man wani abun" shiru haisam yayi yana tunanin ko ya fad'i mata kawae don ta san halin da ake ciki agame da yaran da yasa aka kama,yasan dole zata fi shi sanin abunda ya akamata ayi dangane da case din don ita aikinta ne,

Ganin yayi shiru yasa hajiya fad'in"talk to me haisam ka kafe ni da idanu,da akwai wani abu ne???" kai ya d'aga mata alamar eh,kafin a nutse ya soma magana"I first saw her On Thursday when i was Coming back frm Work........"nan take ya kwashe duk abunda ya faru tun ranar daya fara ganin fatun har zuwa jiyan"tunkafin ya rufe bakinshi hajiya ta shiga zabga salati,hannuwanta duka biyu dafe da kirjinta"innalillahi wainna ilaihir rajiun,hasbunallahu wa'niimal wakeel!!yanzu fateeman ce jiya mutum ukku suka kusan hakke mata?"cike da tashin hankali tayi mashi tambayar,lumshe ido yayi alamar eh,

"Kai jama'a wannan masifa dami tayi kama ni Hauwa'u,rape cases everywhere,everyday,fyade dae fyade dai,duk gargad'in da ake ana fadakarwa a banza kaman ma ana tunzura mutane" cike da takaici take maganar ci gaba tayi"Amman fateema bata yi wayo ba,wannan sakarci har ina,ina ganinta kaman mai wayau bazata bari a cucetaba ashe doluwa ce" sigh haisam yayi"tace Guy din wae bai ta6a ko ruke mata ko hannu ba shiyasa bata yi tunanin zai cucetaba",

Tsoki hajiya taja"sakarci dae kawae,wannan har hujjace da zata sa tabi shi kango karfe goman dare bacin tasan bashi kadae ke yin shaye shaye a wurinba kuma don bai ta6a ruke taba ai baikamata shima ta yarda dashi ba tunda tasan halinshi sarae daya samu dama zai iya cutar da itanne..."kwafa tayi kafin taci gaba"zata zo ta same ni ne,wato shiyasa ta zauna tana ta tsaran zance ta maida ni shashasha....harda cewa wani nan zata kwana,haba nifa wllh nayi mamakin ganinku tare don nidae nasan ba saninta kayi ba", Sauke 6oyayyar Ajiyar zuciya haisam yayi"ina ganin ki kyaleta kawae...."da sauri hajiya ta tari numfashinshi"ta tafka wannan rashin wayon amman kace wai a kyaleta...", "No kingane,duk wani abu da yakamata afad'i mata don ta kiyaye gaba i hv done dat,kuma nasan bazata k'ara yin makamancin hakan ba tunda nace mata nasa shi a yarjejiniyar glass da ta fasa man and kinga tana tsoron ki sani hakan zaisa ta k'ara kiyayewa sosae",

Cike da takaici hajiya tace" Fateema bata jin magana wllh,kar kaso kaga yadda kakarta Dije ke k'okari akanta,ni kaina nan kullum cikin yi mata fadan ta daina rashin ji nike,yanzu ina amfanin hakan,sannu kaima kayi Babban taimako,Amman ka tabbatar dae basu cutar da ita ba?ko dae akaita asibiti ne??"Hajiya ta tambayeshi fuskarta a yamutse,Al'amarin ya Matuk'ar tashi hankalinta, D'an girgiza kai yayi"gaskia basu yi mata komae ba,kawae dai sunyi tying Bakinta da Hannu so tana ta basu wahala don naji wani cikinsu yana magana kan hakan lokacin da naje,Da sunyi matan ma i think da ba'a ganta haka ba",

jinjina kai Hajiyan tayi"yanzu wani mataki kake ganin ya dace a daukar masu?" gyara zama Haisam yayi"shiyasa ai na fad'i maki don ke aikinki ne,d'azun da Sp khamis ya kirani ya sanar dani sunyi arresting nasu gaba daya so suna bukatan akai ita Zarah station d'in,na sanar dashi sai zuwa Friday lokacin kafana ya k'ara warkewa yace ba matsala"Jinjina kae tayi"shikenan before then zamu yi magana"

Readers Also Read