Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 19

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 19

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 19: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 19. Kwantar da kanshi yayi ajikin kujeran ya d'an…

4,483 words

Kwantar da kanshi yayi ajikin kujeran ya d'an zamo"Rav 4,jeep ce,bata da wani kudi sosae just 12 million take..."tun kafin ya k'arasa Hajiya ta waro idanu hannunta d'aya ruke da ha6arta"Million sha biyun ne ba tsada don baka tsoron Allah Haisam,haka kurum jama kai Surutu,aji dadin cewa kudin talakawa yake sata yana kashe man tsofaitsofai dani ko,su Mutane da basa raina abun magana", "Ina ruwanki da Mutane,let dem say what they want,tunda Allah ya baki iko sai ki denying kanki abunda kike so", ta6e baki hajiya tayi tace"Uhm surutun Mutane ai abun tsorone haisam,in dae akwae wata wadda bata kai wannan kudi ba in gani",

"Yeah Akwae wasu,ga wata sunanta Venza" yayi maganar yana nuna mata hoton Motar,Hajiya tace"Oh,kaji sunayen Mota iri iri,kuma masha Allah itama ba dae kyau ba,to ita bata kai waccan ba dae ko?" "Yeah,bata kaita ba,ita 10m take...", da sauri hajiya ta katseshi tana d'an harararshi "yo miye marabarsu,ni nayi zaton Banzar ce ashe ta kirki ce,kaga nifa banson wadda takai miliyan goma gaskia,in dae akwae na k'asa da hakan to sai in za6a,amman bazan za6i wad'annan ba,ita waccan d'ayan taka d'in nawa take ne?"

"Mercedes kike magana,55m take",Wata Uwar harara Hajiya ta wurga mashi"da Allah ni ba ita nike magana ba,yo ni miya rage man yanzu a Rayuwar da zan rinka hawa Motar Miliyan hamsin harda biyar,d'ayar nike Nufi navy blue dinnan" Sigh yayi"Corolla S kike nufi,bai da wani tsada 6m yake..."da sauri ta tari numfashinshi"Yauwa to kaga kamar itan ko wadda ma bata kaita ba yar 5 zuwa 4m" Still yayi ya d'an dage gira yana kallonta, "Kayi man shiru,bakaji mi nace bane?"

Gyara zama ya danyi"Rav 4 da na za6a maki shi za'a kawo period,dama na sanar dake ne don kisan za'a kawo,kina son abu sai ki hana kanki saboda wani Mutane" A harzuk'e Hajiya tace"To tunda nace banso ba sai akawo man irin wadda nike son ba",banza yayi mata saima latsa wayarshi da ya fara,dama tasan tunda har ta nuna Motar tayi mata to fa sai yasa an kawo ta, a k'ule tayi kwafa"To wllh da an kawota bada waccan 406 d'in zanyi",d'age gira yayi ba tare da ya kalleta ba yace"as u wish" tana niyyar bud'e baki ta sake yi mashi Magana Muryar Fatuu ta katse mata hanzari"Assalamu Alaikum,ga bak'uwa daga Makka",

Juyawa hajiya tayi ta kalli entry d'in adai dai lokacin Fatuu ta sake maimaita abunda ta fad'a,d'an girgiza kai Hajiya tayi tace shiryayya kafin ta amsa"Wa'alaikumus Salam Maraba da Mutan Makka ku shigo",shigowa tayi tana Dariya hannunta ruke da yar madaidaiciyar warmer ta yafo d'an bakin gyalenta na gado,da Hijabi ta fito ganin gwaggo zaune a tsakan gida,tana zuwa zaure ta cireta ta sagale ajikin windon Amadu kaman yadda ta saba yi daman ta 6oyo gyalen shine ta yafa kafin ta fito, Tana shiga haisam ya koma inda yake zaune da farko,hakan yasa ta nufi gefen hajiyan ta zauna tana dariya"Hajiyan Sanata ina wuni", "Lafiya lou fateema,yau Allah yayi kenan an kitse kan nan",

"Ai ba duka akayi ba iya biyun nan ne,tace sai gobe da yamma tunda ba islamiyya zata k'arasa man sauran", Jinjina kai hajiya tayi kafin tace"wani abun arzikin nasamu da daren nan" tayi maganar idonta akan kulan da fatuu tazo da ita,janye kulan fatuu tayi gefe"Ba naki bane,Yaya handsome na kawo mawa,naje part dinshi naga bai nan shine na kawo masa nan", Hannu Hajiya tasa ta ruke baki alamar mamaki tace"iyee, yanzu Fatima ni zaki gwasale,duka yaushe kika san haisam d'in da zaki man tawaye,lalle Nagode da wannan babban dizgin da kika man,amman zamu had'u ne",langa6ar da kae tayi tana ma hajiyan dariya kafin ta mik'e tana niyyar nufar inda haisam d'in yake,kwafa hajiyan tayi tana jinjina kai,ganin dae da gaske haisam d'in ta kawo mawa yasa Hajiya juyawa side d'in kitchen ta fara kwalama Saude kira"Saude,Saude lek'o ki tayani Jimami,yau ni Fateema ta wulak'anta",fitowa Sauden tayi ta tsaya bakin kopar kicin d'in hajiya ta shiga fad'i mata abunda fatuu tayi mata,Dariya ta fara yi daga inda take tsaye,

A gabanshi ta tsaya tana ta Murmushi,shima kallonta yake don duk draman da suke da Hajiyan yana sauraransu,hannu tasa tana d'an kange bakinta"kai na kawo mawa Yaya Handsome"ta fad'a da alamun kunya,kai ya d'aga mata,hakan yasa ta d'aura warmer d'in kan hannun kujera ta kinkimo sofa table kafin ta d'auko kulan ta d'aura,Hajiya dae nata bin ta da ido haka Saude ma har lokacin tana a bakin kicin sai faman Murmushi take,

A hankali Fatuu tasa hannu ta fara k'okarin bud'e kulan,k'amshin daddawa ne ya kaima hancin haisam karo bayan ta bud'e,da Sauri ya juyar da fuskarshi gefe had'i da runtse Idanuwanshi,waro ido Fatuu tayi ganin abunda yayi,

"Miya faru ne naga Wanda aka kawo mawan ya kauda kai hada rufe idanu??" hajiya ce tayi tambayar,a sanyaye fatuu ta juya ta kalleta"nima ban sani ba,dana bud'e ne sai naga yayi haka", "Miye kika kawo masa ne?" Fatuu tace"Taliyan hausa ce mai daddawa",bud'e idanu hajiya tayi hannunta ruk'e da ha6arta"ai baya son daddawa Fateema,kamshinta tada mashi Zuciya yake yi shiyasa bai cin duk wani abu da akayi da ita", Damm gaban fatun ya buga,juyawa tayi ta kalleshi,ya bud'e idanun sai dai kwata kwata bai kalli bangaren da take ba idanunsa na akan TV,jikinta ba k'aramin Sanyi yayi ba,a hankali tasa hannu ta d'auki kulan,juyawa tayi ta kalli hajiya dake kallonta fuskarta d'auke da Murmushi,a hankali ta nufi wurinta,agabanta ta tsaya ta mik'a mata kulan"gashi to Hajiya ki ci" fuskarta a yamutse tayi maganar,

Dan ta6e baki tayi"saida shi bazai ci ba sannan zaki kawo man,wato ni ga kwad'ayayya ko,to nima bazan ci ba...."fuskarta kaman zatayi kuka ta katse Hajiyan"Don Allah kiyi hakuri ki ci", "Uhm dama kin daina Wahalar da kanki Fateema bafa zanci ba,har ni zaki ma Wulakanci,wato ke mai Yaya ko,to tunda ba zai ci ba sai ki koma dashi kawae" ba alamun wasa a fuskarta tayi maganar,ganin haka yasa Fatuu d'aga kai ta kalli Saude da har lokacin take tsaye a bakin kicin ta dan d'aga murya"Aunty Saude in kawo maki zaki ci?" kafin Sauden ta bata amsa Hajiya ta amshe"bazata ci ba itama tunda tun farko bamu kika kawo mawa ba,saida aka gwasale ki shine zaki mana neman kai da ita,to ba wanda zai ci"maido kallonta tayi kan hajiya da tayi maganar ganin ba alamun wasa a fuskarta yasa ta fara ta6e baki alamar zata fara yin kuka,ganin haka yasa Hajiyar juyar da kanta gefe alamar ko a jikinta,a hankali ta juya ta nufi hanyar fita idanunta cike tabb da kwalla,sharr kwallan ta fara zubowa,gefen gyalenta tasa tana gogewa yayin da hannunta guda ke rungume da kulan taliyan,

"ZARAH....",Haisam ne ya d'an d'aga Murya ya kirata,a hankali ta waiwaya ta kalleshi,alamar tazo yayi mata da kanshi hakan yasa ta koma cikin parlon tana yi tana goge kwallan dake zubo mata,A gabanshi ta tsaya kanta na kallon k'asa, "Keep it" yayi Maganar yana nuna Sofa table,a hankali ta d'aura kulan saman table d'in kaman yadda yace,d'agowa tayi bayan ta aje ta saci kallonsa,shima ita yake kallo saidai bazaka iya gane tak'amaimai yanayin fuskarsa ba, "Go and bring plate with fork" gently yayi maganar,da alamun mamaki ta idasa d'agowa tana kallonsa hakan yasa ya d'an lumshe idanunsa alamar eh,da sauri ta juya don daukko Plate da cokali mai yatsu,suna had'a idanu da Hajiya ta wani sha kunu ta nufi hanyar kicin,hakan ba k'aramin dariya yaba hajiyan ba,tana shiga kicin d'in Saude ta mik'o mata abunda taje d'aukan kallon Sauden tayi fuskarta ba yabo ba fallasa ta kar6a,daga haka ta juya ta fuce,

Ba k'aramin daurewa Haisam yayi ba lokacin da ta bud'e kulan zata fara zuba mashi, don ma ba sosae aka cika daddawan ba sannan ga k'amshin Curry da aka sa hakan ya rage mata kaifi sosae,tana zuba kamar cokali biyar ya dakatar da ita alamar ta isa,maida marfin kulan tayi ta rufe ta d'an ja gefe ta tsaya,Slowly ya kai hannu kan fork din ya d'ebo yar kad'an,lokacin da zai kaita bakinshi har saida ya d'an dauke numfashin shi kafi ya sakata ciki,a hankali ya fara chewing dinta kafin ya had'iye,abunda ya bashi mamaki kwata kwata baiji daddawan ya canja taste d'in abincin ba,kamshinta ne kawae ake ji,k'ara kai fork d'in yayi ya debo har ta dan fi ta farko yawa ya kai bakinsa,bayan ya hadiye ya d'ago fuskarshi ya kalleta a inda take tsaye ta zuba mashi idanu,fuskarshi ad'an sake kaman zai yi Murmushi yace"it tastes good",

Waro idanu tayi"Kenan tayi maka dad'i Yaya Handsome?, Kai ya d'aga mata da d'an murmushi alamar eh,wata k'arar farinciki Fatuu ta saki lokaci guda ta fara tsalle had'i da juyawa saitin da hajiya take tana fad'in"Yeeee,an gwasale hajiya,an gwasale hajiya....",Sosae take tsalle kitson gaban kanta sai dagawa yake sosae, gaba daya ma gyalen ya zamo k'asa,ita kam hajiya mi zata yi in ba Dariya ba,sosae take tik'ar dariya,hakan ya jawo hankalin Saude ta leko,cike da farinciki fatuu ta tsaya da yin tsallan tace"Aunty Saude Yaya Handsome yaci abincin hajiya taji Kunya",hannu Saude tasa ta rufe baki tana dariya,ita kam Hajiya throw pillow ta d'aukko ta jefo ma Fatun,abunda bata sani ba Hajiyar ita tasa haisam d'in yaci abincin,dama da biyu taki ci lokacin da fatuu ta nufi kopar fita daga falon hajiya ta kalli haisam d'in da kai ta rinka lallashinshi tana magana kasa kasa akan ya daure ya ci abincin,

"To a samman in ci nima tunda wanda aka kawon don shi yaci" hajiya ce tayi maganar tana kallon Fatuu dake zaune a gefen Haisam,mak'e kafad'a tayi"baza ki ci shi ba kuwa,shi zai cinye abunshi"ta k'arasa tana murmura ido,

Dan gyaran murya haisam yayi ta juya ta kalle shi"ki yi hakuri ki bata", "To ai baka ci da yawa ba fa" a shagwa6e tayi maganar,yace"Owk ki d'an kara man kad'an sai ki bata sauran" mik'ewa tayi taje gabanshi ta k'ara masa kafin ta nufi Hajiya da kulan,a gefenta ta dangwarar da kulan"gashi nan don ba Halin ki ba...."bata k'arasa ba sakamakon damkota da hajiya tayi ta daddage ta d'uma mata dundu tana fad'in"Kin raina ni ko Fateema"Fatuu dake ta dariya tace"to ai ke ba kakata bace ba",Sakinta tayi tace"Je ki d'aukko man fork nima in ci inji in kin iya girkin"cike da Zumudi tace to,har ta nufi kicin ta juyo"banda plate hajiya?"kai ta d'aga mata"eh bani cokalin kawae zanci acikin kulan,

Bayan ta kawo mata cokalin a gefenta ta zauna ta k'ura mata ido tana jiran taji mi zatace game da Abincin,jinjina kai hajiya tayi lokacin da takai lomar farko"Ah Masha Allah, tayi dadi sosae wllh,amman dae nasan dije ce tayi shi....."da sauri fatuu ta katseta"Wllh ni nayi shi na rantse da Allah,ita kawae nuna man yadda zansa abubuwa tayi amman tana zaune nayi har na gama" hajiya tace"lalle kinyi kokari"sosae fatuu ta washe baki alamar taji dadi.

Yana gama cin Abincin ya mik'e don gaba daya jin bakinsa yake yana warin daddawan,Bedroom d'in Hajiya ya nufa fatuu ta bishi da kallo har ya shige corridor kafin ta maido idonta kan hajiya"Wai hajiya da gaske Yaya Handsome baison daddawa?" cinye abincin bakinta ta fara yi tace"Wllh kwata kwata baisonta tun yana yaro,warinta yake ji sosae,wani lokacin har Amai yake yi in yaji kamshinta,shiyasa ma bai shan miyan duk da akasa ma daddawa yanzu haka da kika ga ya nufi dakina na tabbatar Brush zai je yi", Jinjina kai fatuu tayi a sanyaye tace "ai da bai ci ba tunda bai so,ni fa koda nayi kuka saboda ke kinki kici ne", dariya hajiya tayi" karki damu,yaji zai iya ne shiyasa yaci,nima kuma dama don yaci d'in tunda shi kika kawo mawa yasa nace maki bazan ci ba,yanzu da yaci ba gashi nima ina ci ba"gyad'a kae fatuu tayi sai faman fara'a take ba k'aramin dadi taji ba da suka ci,

Fitowa yayi yana goge face d'inshi da tafin hannunshi da alama ruwane a fuskar,hanyar fita ya nufa don duk da yayi Brush d'in still jin bakinsa yake ba dai dai ba,Part dinsa zaije Don ya fesa had'addan Mouth spray dinsa ko zaiji daidai, "in fita zaka yi don Allah ka d'an raka Fateema dare nayi"hajiya ce ta katse mashi hanzari,kai kawae ya d'aga ba tare daya kallesu ba, "To Fateema tashi ki bi shi sai kuma Allah ya kaimu,Nagode duk da bani aka kawo mawa ba", mikewa tayi ta dauki kulan don tuni hajiyan ta gama ci, "Sai da safe Hajiya" kai ta d'aga"Allah ya tashe mu lafiya", har Fatuu ta nufi hanyar fita cike da tsokana hajiya ta dan d'aga Murya"Gobe ki kawo ma Yaya Handsome Tuwo da Miyan kuka",a sukwane fatuu ta juyo ta kalli hajiya dake ta dariya,ganin haka yasa itama tayi dariya tace"ai bazan k'ara kawo masa abu mai daddawa ba",daga haka ta juya tabi bayan haisam wanda tuni ya fice,

Da sauri ta isko shi don a hankali yake tafiyan,jerawa tayi dashi ta d'ago kae ta kalleshi"Yaya handsome don Allah kayi hakuri nasa kaci abunda baka so,wllh ni bansan baka sonta ba"d'an juyawa yayi ya kalleta da dan Murmushi calmly yace"Don't worry ur self,naji dadin abincin ai,thanks",jinjina kai tayi tana ta zabga uban Murmushi daga haka suka fuce daga Gate din gidan,

Fatuu na ganin har sun wuce katangar gidan Hajiya bai tsaya ba tace"Yaya handsome yau har gida zaka rakani ne?"kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"ko dae don kar na sake zuwa kangon nan ne,ai bazan k'ara zuwa ba duk da ma an kamasu,oh lemunana ko suna can ko wani ya d'auke su"tayi maganar hannunta ruk'e da ha6arta,

"Ko zaki je ki duba ne" haisam yayi maganar idonshi akan hanya,dariya kawae tayi don ta gane gatse ne yayi mata,gab da kiosk d'in kawu Amadu Haisam ya ja ya tsaya,hakan yasa itama ta tsaya tana kallonshi"kije sai da safe"fatuu tace"to bari inma kawu Amadu magana ku gaisa,bata jira cewarshi ba ta juya tana kwala ma Amadu kira"Kawu Amadu ka lek'o ku gaisa da Yaya handsome", lek'o da kai ta cikin kiosk d'in Amadu yayi tun kafin yayi magana Fatuu ta nuna masa haisam dayake an maido da wuta akwae haske sosae,,Haisam na ganin Amadun na k'okarin fitowa ya matso ya mik'a masa hannu suka gaisan,fatuu na ganin zai juya bayan sun gaisan tace"Yaya haisam bari abaka biscuit da sweet" yadda tayi maganar sai kace wani k'aramin yaro,wani kallo yayi mata da sauri tace"pls"ta marairaice fuska,jin baijin dad'in bakinsa yasa shi cewa"just a Sweet"da sauri tace to,ta juya ta nufi cikin shagon,can sai gata da ledan sweet ta mik'a masa,d'an bude ido yayi batare daya amsa ba,

"Gashi nan duka yace a baka" girgiza mata kai yayi"yayi yawa inada shi a d'aki,just one ya isa"Wani kallo tayi masa"kai Yaya Handsome ya zaka ce d'aya ya isa,don Allah ka amsa duka" k'in amsa yayi ya bita da ido tace"to in d'ibar maka rabi?"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ya d'aga mata dogon yatsansa guda alamar guda daya zata bashi,

"To bari kagan yanda za'ayi,zan baka na yawan sunanka ka yarda?" kai ya d'aga alamar eh, "YAYA HANDSOME"ta d'aga hannunta tana k'irga yawan sunan da yatsunta kafin ta kalleshi"guda sha biyu kenan zan baka"jinjina kai yayi cike da mamakin wai shi zata ma wayo, Fatuu tace"Kawo hannunka to"ba musu ya bud'e kyakkyawan hannunsa mai d'an fadi da tsawo,tafin hannun sumul dashi tamkar ka ta6a jini ya fito,bud'e ledan sweet d'in tayi ta fara saka mashi da dai daya tana saka gudu shidda ya rufe tafin hannun,da sauri ta d'ago ta kalleshi tun kafin tayi magana ya rigata da fad'in"HAISAM is six letter word,so guda shida ne daidai sunana" cike da shagwa6a ta d'age kai"Wayyo Yaya handsome ni zaka ma wayo..."katseta yayi cikin Sanyayyar Muryarshi yace"Nima ai wayon kika so yiman ko"jin haka yasa fatuu kyalkyacewa da dariya tana fad'in"ashe ka gano ni"shima dariyar yayi har jerarrun hakoransa masu tsari suka bayyana,dimple dinshi guda d'aya ya lotsa sosae"kije dare yayi,Gud nyt" kai fatuu ta d'aga"Gud nyt yaya handsome kabi a hankali kar ka sake taka kwalba"Wani kallo yayi mata mai kaman harara kafin ya juya,

Tana ganin ya tafi ta juyo,tsayawa tayi ta bud'e kulan hannunta ta fara zazzaga sweet d'in ciki,kamar ance Amadu ya lek'o,ya ganta da karfi yace"Fatuu dama bashi zaki ba...."bai k'arasa maganar ba ta wurga ledan sauran sweet din cikin shagon ta nufi gida da gudu.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*4️⃣0️⃣*

Washegari Misalin karfe biyu da rabi na rana,Haisam zaune a parlor ya tasa laptop d'insa gaba yana lallatsa ta,Tun bayan da ya samu rauni daga gida yake aiki don bai iya zuwa wurin aikin,gaba daya ya gaji Don aiki biyu yake yi, gana nan ga kuma na U.S,Kullum wuni yake aikin latsa Computer,Wani irin bacci ne ke fizgarshi don ya gaji Sosae,A hankali yasa hannu ya d'an ture laptop din gefe ya idasa hayewa kan kujeran ya kwanta,hannu ya kai ya d'aukko throw pillow ya tura ak'asan kanshi ya mik'ar da kafafunshi,A hankali idanunsa suka fara lumshewa alamar bacci ya fara zuwa.

Turo kopar falon akayi tare da sallama,Cikin zuciyarsa ya amsa ba tare daya kalli mai shigowan ba don yaji Muryarta,k'arasa shigowa tayi jikinta sanye cikin Uniform amman yau da Hijab,kitsonta sun fito gefe da gefe yayin da k'asan kitson ki acikin hijabin,ba k'aramin kyau hakan yayi mata ba,

gaban kujeran da yake kwance ta tsaya tana kallon fuskarshi,Slowly ya bud'e idanunsa akanta,murmushi ta sakar masa hakan yasa shima ya d'an yi mata wanda iyakarsa saman lips d'inshi,ganin tayi tsaye k'erere yasa shi mik'ar da yatsansa yana nuna mata 6arin da armchairs suke alamar taje ta zauna,girgiza masa kai tayi tace"bari in Zauna anan"tana fad'in hakan ta zauna a saman Carpet ta lankwashe kafafunta tayi zaman cin tuwo still idanunta na akanshi,

kallonta yayi a kasalance yace"kindawo",kai ta d'aga masa "eh yanzun nan na dawo na iske ba kowa a gidan,Gwaggo tana wurin aiki,kawu Amadu kuma har yanzu bai kaiga dawowa ba,shine nace bari nazo na tayaka fira",nodding kai yayi kawae,hannunta ta fiddo daga cikin hijab ta mik'a masa ledar dake ruke a hannun,bin abunda take mik'o masan yayi da ido kaman bazai kar6a ba,can kuma ya mik'o hannu ya amsa,jujjuya faran ledan yayi kafin ya d'ago ya kalleta da gani bai gane miye aciki ba,

"Tsaraba ce nayo maka,su tuwon madara ne,da gwullisuwa da baban dudu da mandako sai kantun gana" d'an bud'e idanu yayi jin wasu sunaye da take fad'a,yasan tuwon madara da gwullisuwan don akwae wata Abokiyar aikinsu dake kawo su,sai dae sam ba irin wannan bane,nata masu aji ne,wurinta ne ma ya siya Popcorn d'in da ya ba fatuu rannan,sauran abubuwanne bai sani ba bai ma ta6a jin sunansu ba,

ganin yana ta jujjuya su tace"ko bazaka sha ba" d'ago idanunsa yayi"zan sha,but ba nace ki daina kashe kudi kina siyo man abu ba"da sauri tace"ai kudi nane nasiyo maka dasu ba na wasu na ta6a ba,kuma duka Naira d'ari ce ma,komai na ishirin ishirin",kallonta kawai yake da lumsassun idanuwansa kafin Calmly yace"thanks zaraah"daga haka ya aje ledan a gabanshi,

"Nafa san miyasa kake ce man Zarah" kallonta yayi ba tare daya ce komae ba,taci gaba"Gwaggo tace man sunan mamanka gareni hakane wai??"ta d'an bud'e idanu alamar amsa take jira,kai ya daga mata alamar eh, "Kenan nazama mamanka",

Yace"ko",

"Eh mana,tunda ina da sunanta ai kaga nazama mamanka ko",still yayi yanata kallonta, "Mom zaraah yakamata ka rinka ce man,kuma ka rink'a yiman Dariya kana man Magana sosae"ta kai maganar tana d'an tura baki alamar shagwa6a,d'an muskutawa yayi ya juyo sosae"ai ina maki wannan ko" tace"to ai ba sosae kake yi ba,in zaka yi dariyan haka kake ko kayi haka"tayi maganar tana nuna mashi yadda yake dariyan,sosae ta bashi dariya yadda ta wani d'age baki amman sai yayi murmushi kawae, "To ai hakan ma normal ne" d'an girgiza kai tayi"a'a,haka yakamata ka rink'a yi..."ta washe baki tana nuna mashi wai hakan zai rinka yin dariyar,Fuskarshi a sake yace"Wannan ai irin naku ne na Manya Mom zaraah"sosae ta washe baki jin ya kirata da sunan da tace ya rink'a ce mata,

Hannu ya kai ya dafe gaban kanshi don rashin baccin da baiyi ba har ya fara developing headache,sosae ya runtse idonshi yana d'an yamutsa bakinsa,ganin hakan yasa Fatuu cewa"Yaya handsome mike damunka ko baka lafiya ne?"sai da ya d'an dauki lokaci kafin ya janye hannun,a hankali ya fara bud'e idanun,yana son yace mata bacci yake ji amman baison taga kaman yana korarta ne don wani lokacin kaman bata fahimtar abu daidai, K'ura mashi ido tayi"idanunka sunyi wani iri yaya handsome,baka lpy ko?"girgiza mata kai yayi yace"lafiya na lou,kawae ina jin bacci ne"d'an murmushi tayi"to bari in tafi"tayi maganar tana k'okarin mikewa,bin ta da kallo yayi kaman mai son gano wani abu har ta karasa mikewa zata tafi,

"Zaraah..." ya dakatar da ita,tsayawa tayi tana kallonshi,shima kallon nata yake yana nazarin fuskarta sai dae sam ya kasa fahimtar yanayinta,"Yaya handsome ka tsaida ni",

"Yeah,dama ba ina nufin ki tafi ba,ba kince gidan ba kowa ba?" kai ta d'aga mashi alamar eh, "Owk,ko ki je ki gaida hajiya sai ku d'an yi firan kafin in tashi" yayi maganar idanunshi akan fuskarta yana nazartarta,d'an murmushi yaga tayi"to Yaya Handsome bari inje"murmushi yayi don yaji dad'i da bata fahimce shi ba daidai ba,har ta fara tafiya ya sake kiran sunanta,juyowa tayi ta kalleshi ya d'ago ledan abubuwan da ta kawo mashi ba tare daya kalleta ba yace"ki kai ma hajiya"shiru tayi tana bin shi da ido, jin bata amsa ba yasa shi d'ago da kai ya kalleta,lokaci guda ya gane bata ji dadin hakan daya ce ba, "Ki kai mata kice ta dauki rabi sai ta aje man sauran,kinga itama duk in ta samu abu sai ta bani" sai lokacin ta mik'o hannu ta kar6i ledan tana fad'in"to ai leda biyu ce,bari in raba maku",raba masu ta fara kokarin yi shi dae yana ta bin ta da ido, bayan ta gama ta mik'o mashi"to ga nakan ita kuma sai in kai mata wannan"hannu yasa ya amsa Fuskarshi ad'an sake ya furta"Thanks"daga haka ya aje ledan gefenshi,ita kuma ta nufi kofa ta fuce,

____________________

Sam baijin dadin Baccin da yake kan kujeran,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,A hankali ya fara bude idanunsa kafin ya idasa ware su sosae,k'uri yayi cike da mamaki yake kallon abunda ke gabansa har saida ya d'an sa bayan hannunsa ya goge idanunsa don ya tabbatar,Fatuu ce zaune saman C-table d'in parlon tayi dare dare a sama tana facing dinshi hannunta guda tayi tagumi dashi gaba daya ta k'ura masa idanu, A kasalance ya furta"Zarah!what are u doing up there,ba nace kije kuyi hira da hajiya ba?",

Cire tagumin tayi ta zuro kafafunta k'asa a shagwa6e tace"to ai naje na iske itama hajiyan bacci ya kwashe ta a Parlor,baka gan yadda ta saki baki ba sai munshari take wllh kaman rago"bud'e idanu yayi sosae yace"Hajiyan ne rago!" da sauri ta shiga girgiza kai"a'a,wllh na manta rago Namiji ne,kaman shanuwa nike son cewa",Still yayi yana mata wani kallo hakan yasa tasha jinin jikinta duk da ita gani take wai ta gyara,yunkurawa yayi ya tashi daga zaune ya jingina bayansa da jikin kujeran,ita kam tayi tsuru tana bin sa da ido,ya fahimci gani take abunda ta fad'a daidai ne hakan yasa shi cewa"ba'a kwatanta Mutum da dabba kar ki k'ara"da sauri ta d'aga masa kai"to Yaya Handsome bazan k'ara ba",jinjina kai yayi,yana jin dadin yadda da yayi mata gyara take cewa bazata kara ba,kuma ya tabbatar bazata k'aran ba.

Shuru suka yi na wani d'an lokaci tana ta kallonshi tana faman sakin Murmushi,shi kuma fuskarshi ad'an sake yake kallonta, "Duk kujerun dake parlon nan baki iya zama sai nan,in kika fasa man abu fa", Hannu tasa tana shafa saman C-table din"Ai yana da kwari bazai fashe ba kuma ni bani da nauyi ma,kasan mi?" kai ya girgiza mata alamar a'a,taci gaba"nafa dad'e da dawowa ina shigowa nagan kanata bacci...." katse ta yayi"shine kika zauna kina bina da ido"fuska ad'an d'aure yayi maganar,

Da sauri tace"a'a Yaya handsome lokacin da na shigo naga kana baccin wllh har zan tafi gida kawae sai naga wani abun mamaki,kasan mi?"kai ya girgiza"wllh dana kalle ka kana baccin sai naga ka koma man kaman Karan na cikin Kaddarar rayuwa da ake a Arewa 24,ka gane shi"shiru yayi mata,tace"au ashe fa kace baka kallon tashar,amman wllh kunyi kama shiyasa na haye nan ina k'ara kallonka sosae har gashin kanku iri daya ne,kuma shima yana da dimple amman kai kafi shi tsawo gaskia shi kuma yafi ka yin dariya sosai"ta k'arasa tana ta watsa hannuwa,shi dae zuru yayi mata don bai ma san wanda take magana akai ba,ganin yayi mata shiru tace"Ka bari lokacin da ake yin shirin zan nuna maka shi",kai ya daga mata alamar toh,daga haka ya d'age kansa sama yana kallon ceiling gaba daya baijin dadin jikinshi,baccin sam bai ishe shi ba,

"Yaya handsome ka gama baccin ne?"a yadda yake ba tare da ya d'ago ba ya girgiza mata kai, "to ka kwanta ka cigaba da baccinka",still bai d'ago ba yace"I can't sleep if there's someone around", jin tayi shiru yasa shi d'agowa ya kalleta,don kar tayi tunanin korarta yake yasa da sauri yace"Hajiya ma in tana kusa dani ban iya yin bacci" jinjina kai tayi alamar ta gamsu kafin tace"to ka tafi d'aki mana ka kwanta", "In barki ke kad'ai?" tace"Eh mana ba sai in yi maka gadi ba kar wani ya shigo ta katanga su Officer basu sani ba",d'an murmushin gefe yayi jin abunda tace kafin yace"Yau ba aikin da zaki yi ne"hannu tasa ta ruke ha6a ta d'age ido sama alamar tunani"ba aikin da zan yi,amman yau gwaggo tace zata k'arasa man kitso bansan ko ta dawo ba yanzu",

"Ok,kije ki gani in ta dawon ko", "To,amman sai na fara gyara ma d'ana parlon shi", tayi maganar tana kare ma falon kallo,shima d'aga ido yayi yana kallon falon kafin ya maida idon kanta"ai ba abunda yayi" jinjina kai tayi"eh amman dae akwae abubuwan da ya kamata a gyara",d'an ta6e baki yayi ya dage shoulders d'inshi daga haka ya mik'e ya nufi Bedroom dinshi,yana kaiwa daidai Corridor fatuu ta juya kai daga kan C-table d'in da take tace"My son kayi bacci mai dadi kuma kayi mafarkin mamanka",d'ago mata hannu yayi murya a kasalance ya furta"Owk,Mom Zaraah",daga haka ya tura kofa ya shige Bedroom d'in.

*** **** ****

Ba k'aramin bacci yayi ba don sai can bayan la'asar ya farka,hannu ya kai ya d'auki wayansa yana duba time,da sauri ya mike zaune ganin karfe hudu da rabi hakan na nufin yayi missing Sallan la'asar,da k'yar ya saukko da kafafunsa ya nufi Toilet don ya watsa ruwa saboda duk kasala ta baibayeshi,

Sanye cikin jeans da T-shirt ya fito ya nufi masallaci duk da lokaci ya kure,bayan ya gama sallan zama yayi cikin Masallacin yana yin azhkar d'in yamma,bayan ya gama yana fitowa daga cikin Masallacin wayarsa dake ruke a hannunsa ta fara ringing,duba mai kiran yayi kafin ya d'aga,tun kafin yayi magana on the other hand akace"Kana ina ne naje part dinka baka nan,nazo na Hajiya ban samu kowa ba",

Readers Also Read