Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 2

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 2

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 2: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 2. Ajiyar zuciya uwar tayi tace"to kam ina tunanin daya…

4,067 words

Ajiyar zuciya uwar tayi tace"to kam ina tunanin daya daga cikin jikokin hajiyar ne,don jikokinta tubarkallah akwae kyau sosae wllh don kwanaki can da dadewa munje kar6ar tallafi a gidan naga wani Matashin Saurayi mai kyaun gaske har muka gaida shi ya amsa mana kamar baison amsawar..."inna wllh kilan ma shine,shima wannan fa kamar dan dole yake maganar baki gani ba yana wani haka,ta d'an yamutsa fuska ita ala dole yadda yake magana take kwaikwaya gaba daya suka sa Daria harda Kannenta,Innar ce tace"hakan duk cikin gayu ne ai,kinsan su yan gayu komae nasu na daban ne wllh,kai Allah muma yayi mana arziki mai Amfani" ta d'an daga hannayenta sama, "Amman anya shine kuwa wannan fa anyi shekara biyu koma fi dana ganshi kilan dai dan uwan shi ne,kai koma dai waye nagode kwarai wllh Allah ya taimakeni ta silar shi,da bansan ya zanyi in biya kudin Waken nan da Mai ba dama sai da aka ja man rai aka bani,kai Allah ya taimake ni wllh",hannu ta daga tana k'ara gode ma Allah cikin tsananin farinciki,gaba daya yaran suma suka dauka"Allah mungode ma² suna yi suna tsalle ganin Mahaifiyarsu na farin ciki,kar6ar bokitin awarar tayi tana dubawa"Kai yarinyar nan anyi yar....ko da yake inma na zage ta kanmu abun zai k'are,don ba'a son mutum yana abu ana aibata shi da mugayen kalami,to kara lalacewa yake kuma mutanen da ke tare da shi su abun ke shafa,Allah ya shiryata dai damu baki daya" "Amin"yaran suka amsa da karfi" amman duk da haka ji nake kaman inje in fadi ma gwaggon tata don abun Yarinyar yayi yawa wllh" jamila tace"innarmu ki kyale ta kawae shima Mutumin daya bada kudin cewa yayi kar in bita gidansu don in an kara dukanta zata kara 6arar mani tunda bata jin Magana" hakane gara mu kyaleta tunda ma sanadin abunda tayi mana ji bi abun arzikin da muka samu" ta kara sa maganar tana k'ara kirga kudin, wani yaro ne cikin yaran yace "Inna muzo mu karbi sauran mu cinye tunda an samu kudi" yayi maganar yana d'an noke kai gami da yar daria da sauri Innar tace"ehh maza kuzo ku kar6a" tsalle yaran suka fara yi suna murna,marar k'asar ta babbasu Jamila ce tace "Inna don Allah tunda ansamu kudi zaki ban in siyo hoda mai madubin da na tambaye ki kwanaki kika ce sai kin samu kudi" ta karasa maganar tana sussunna kai kasa,da fara'a a fuskar innar tace "Kwarai kam zan ba ki tunda Allah yasa ansamu kudin,ko dama can abunda yasa ban baki ba kudin ne ba isa suke ba sam kina dai ganin yadda ake ta fama,kinga da kika yi hakuri ba gashi Allah ya kawo ba, shiyasa in aka ce ma Mutum yayi Hakuri to yayi din don mataki ne na nasara rashin yin hakurin kuma ba abunda yake ja ma Mutum face asara da dana sani" cikin washe baki jamila tace"Eh hakane Inna" "to sakamakon hakurin da kika yi harda na siyan jan baki zan baki sai kije ki siyo harda sabon bokitin tallan" tsallen murna jamila ta fara yi tana ta faman daria tana shima dan gayu mai mota daya bata kudi Albarka,itama Innar tasu Albarkar take sa ma mai motar yayin da ta nufi daki don adana Kudin. * * * * * * * * * * * * * * * * *

Wani irin Katafaren Gida ne mai tsananin kyau wanda da ka kalla zaka gasgata kyawun gidan,Fentin gidan ya matukar kayatuwa wanda Peach colour ne mai dan duhu had'i da milk colour,Katangar gidan na dauke da peach din fenti yayin da Pillars din dake a jikin katangar ke dauke da Milk din fenti,gaba daya katangar na zagaye da hadaddan Fence wanda ke dauke da farin fenti,daga saman fence din yadan yi tsini kamar mashi anyi mashi adon fenti Golden mai salk'i,cikin fence din kuwa shukan Flowers ne masu kyau da gani suna samun kulawa sosae,gasu a tsare mai tsawo sai ta gabanta gajera haka suke jere gwanin sha'awa,can saman katangar ma zagaye yake da Electric fence bak'i,A k'arshen katangar gidan gaba daya kuwa Masallaci ne mai kyau da girma komai nasa kalan na gidan ne ga Tankunan ruwa manya har biyu a sama da kan Famfuna a jikin ginin da aka d'aura su Yara nata dibar ruwa. Gate din gidan kuwa ya d'an shiga lungu ta yadda in mota ta taho daga bangaren katangar gidan ta dama ko hagu zata shiga gidan sai andan karya kwana, A daidai gidan mutumin ya juya kan motan ya tunkari Dank'areren Gate din gidan wanda shima yake da farin fenti daga saman shi anyi design irin na fence din,ajikin bangon da ke kallon hagu in an shigo kwanar gate din kuwa wata dakakkiyar Kofa ce a rufe itama da farin fenti mai salk'i da kwalliyar irin design din fence din wanda akayi ratsi da golden paint mai daukan ido.

Wasu Jami'an tsaro ne guda biyu dake zauna a saman bencin karfe shima da farin fenti suka mike ganin motar ta tunkaro gate din kowannansu na sanye da Uniform,daya uniform din yansanda ne jikinsa dayan kuma na civil defence had'i da Bindigu rataye a kafadunsu,daya ne ya kama gate din yana Sliding din shi right yayin da dayan ya matso kusa da motar yana washe baki,a hankali gilashin motar ya dan bude "Welcome sir" jami'in ya fada baki washe. Mutumin ya juyo fuska adan sake yace"Thanks Officer,how work" cikin sauri officer din yace"Aiki Alhamdulillah gamu a cikinsa,har lokacin bakin shi a washe yake,"Ok,Allah ya taimaka" mutumin ya fadi a lokacin kuma yaja motar fuuu don angama bude masa gate din,da sauri dayan Jami'in ya daga masa hannu alamar sannu da zuwa lokacin da motar tazo saitin da yake a tsaye,Horn na cikin motar ya latsa alamar ya amsa,Parking Spot ya shiga wanda ke dauke da karafa masu farin fenti anyi masu design mai kyau yayin da saman wurin ke rufe da Alminium roofing sheet yana da girma don yana da wurin parker mota shidda,akwae motoci guda hudu a ciki akwai Hilux mai dauke da tambarin NGO,sai Vibe,peugeot 406,da kuma wata Had'addiya wadda na kasa gane sunanta,a kusa da ita ya parker motar a can karshe kuma wani hadaddan k'aton bak'in Bike ne ajiye, daga gaban parking space din wani dan daki ne wanda ba'a sa kofa ba,daga saman wurin shiga an rubuta GENERATOR ROOM,a gefen ginin wata kofa ce ta k'arafa wadda zata kaika cikin masallacin dake jikin gidan. Wani matashin saurayi ne rik'e da tiyo yana ba Flowers ruwa yana sanye da wani kodaddan Crazy Jeans da bakan T-shirt itama dai ba sabuwa b,kanshi anyi mashi aski irin na gayu,yana ganin motar ta tsaya ya saki tiyon ruwan ya nufo ta da yar sassarfa ya tsaya a gefe yana ta faman washe baki sai da aka dauki wasu seconds kafin na cikin motar ya bude yana kokarin fitowa,da sauri saurayin dake a tsaye ya kama k'opar ya idasa bude ma Mutumin,fitowa yayi a hankali yasa hannu yana gyara necktie din dake wuyansa,saurayin ne yace "Barka da zuwa yalla6ai "yana ta faman washe baki, fuska adan sake ya kalli saurayin daga sama zuwa kasa da alama shigar da yayi yake kallo kafin ya tsaida fuskarsa akan tasa yace " Yauwa T.K Babban Yaro,yayi maganar ta sigar tsokana, Cikin dan jin kunya T.k din ya sunkuyar da kansa yana murmushi yace "Ah haba yalla6ai wane mu Almajirai".Murmushi mutumin yadan yi kafin ya bude back door din motar yadan zura hannu ya fiddo da Briefcase din sa,da sauri T.K ya mik'o hannu ya karbi jakan shi kuma yayi gaba,T.k yasa hannunsa daya ya rufe duka kofofin motar ta gaba da ta bayan kafin yabi bayan mutumin. Wata corner suka shiga wadda ke a bangaren dama inda gate din gidan yake, tafiya Mutumin yake cikin corridorn a nutse, yayin da T.k ke binsa a baya rungume da jakar har suka iso wata kofa ta karafa wato Fence door daga can gaba kuma akwae bayan wata kofa wadda ke a rufe tana kallon bangaren da fence door din da suke k'okarin budewa take da alama bayan hadaddiyar kofan nan ne dake a waje kusa da gate,hakan na nufin in kabi ta kofan zaka fito wajen gidan kwanar da gate yake. T.k ne ya dawo gaban Mutumin da sauri yasa hannu ya zare kubar da ke rufe jikin Fence door din yasa hannu ya tura kofan ciki ya dawo gefe ya tsaya saida mutumin ya shiga sannan ya bi bayansa,dan Flat ne mai kyaun gaske wanda kasan ke malale da Interlocks ga Flowers jere masu kyaun gaske girman su daya,gaban flat din na rufe da fence mai dauke da glass wanda ke dauke da zanen flowers ajikinsa hakan ya bada area din da ake kira da Bolcany.

Sai da Mutumin ya wuce saman wurin kafin T.k ya bi bayansa da sauri T.k ya murd'a handle din Dakakkiyar kofar shiga flat din ta bude ya dan ja gefe guda yaba mutumin wuri ya shiga kafin yabi bayansa,Ya Allah!ba karamin had'uwa Parlorn yayi ba wanda gaba daya Fentin cikinsa fari ne mai salk'i,haka Tiles din da ke malale a kasa ma fari ne kar da ratsin baki,kujerun ciki kuwa Leather chairs ne L-Shape bakake wanda ke kewaye a tsakiyan parlorn a samansu akwae Throw pillows Red color masu kyau a jere,daga gefen dama kuwa in ka shigo akwae Armchairs guda biyu suma leathers ne amman red color saman kowacce akwai T-pillow bak'i,daga bayansu kuma wani Had'addan Desk ne manne da bango wanda ke dauke da Drawers gefe da gefe fari ne kal sai faman salk'i yake a samansa akwai Table Lamps (fitilu) guda biyu jajaye kowacce a k'arshen desk din,a tsakiya kuma bakin telephone ne ajiye daga dan gaban desk din tangamemiyar Window ce wadda ke rufe da farin Blinds (irin labulen nan mai yanka yanka,wanda aka fi yawan amfani dashi a office),A tsakiyan kujerun parlon dakakken Carpet ne mai laushin gaske baki dauke da ratsin kwalliya ja da fari a samansa kuwa wani hadaddan Center Table ne na glass fari mai kaurin gaske,daga can bangon dake kallon inda jajayen kujerun suke wata Window dince itama rufe da bak'in blinds,a bangon dake kallon duka kujerun parlor din kuwa wani irin PoP Casting ne manne da bangon mai dauke da Manyan gidaje anan kuma madaidaiciyar Plasma T.V ke manne a gidan tsakiya daga kasanta kuma gidan da Sound systems suke ne da DVD player da reciever,a gidajen dake a gafe da gefen bangon da saman inda T.V din take kuwa,Hotuna ne dasu Agogo da Frames na zane wato Artworks ba karamin kyau wurin yayi ba.A gefe kuma d'an corridorn da bedrooms suke ne,a kofan corridor din flower vases ne bakake dauke da Red flowers masu ratsi da farin kananun flowers,a Angles (sako) din dake a bangon kuwa 6arin hagu Standing A.C ce babba a angle din dama kuwa madaidaiciyar Freezer ce a wurin,a tsakiyan pop ceiling din parlon akwae chandelier babba (irin fitilar nan mai adon sarkoki) kwan fari sol yayin da sarkokin jikinta bakake ne,ba k'aramin haduwa parlorn yayi ba ga sanyin A.C hadi da kamshi mai sanyaya rai da ya gauraye ko ina,da ka shigo parlorn zaka ji gaba daya yanayin ka ya canja koda kuwa kunci kake to tabbas ranka zai yi sanyiii.

Mutumin na shiga ya nufi inda bakar kujerar take ya dan fada samanta hadi da aje wayarsa wadda take slim mai dan tsawo bayanta sai shining yake a gefensa,ya kwantar da kansa jikin saman kujerar don bayanta baida tsawo sosae,T.k kuwa yana shigowa yad'an lumshe ido hadi da jan dan dogon numfashi alamar sanyayyan kamshin ya kai masa karo,shiyasa a koda yaushe yake son abunda zai kawo sa part din Mutumin koba komae ka samu natsuwa.Wucewa yayi bayan Red Armchairs din parlorn ya daura jakar saman farin desk din dake wurin kafin ya zagayo tsakiyar parlorn ya tsaya saitin Mutumin yace"Yallabai akwae wani abu? A nutse yayi maganar,Mutumin bai dago ba yana a yadda yake yadan daga mashi hannu hadi da fadin "Thanks T.k,u can go" t.k yace "To a huta lpy" ya kama hanyar fita batare da ya jira amsar Mutumin b,don yasan ma b lalle ya kara cewa komae ba, Yana fitowa yaji wani zafi ya bugi fuskar sa a fili T.k yace " Kai masu kudi dai sun ji dadin su,da ace part din nan yazama nawa ai wllh fitowa sai dole"Ya k'arasa maganar hadi da wurga kafa yace "qur'an kau" a daidai lokacin ya fita daga Part din Mutumin.

Ya dau tsawon mintuna a haka da alama dai ya gaji ne sosae kafin ya mike ya tunkari hanyar da zata kai shi Bedroom dinsa har zai shiga cikin koridon ya tsaya cak sakamakon karar da Telephone ke yi,a hankali ya juyo gami da kai idonsa saman desk din da telephone din yake yanata faman kara alamar ana kira,tafiya ya fara yi a hankali saida ya zauna saman daya daga cikin Armchairs din dake gaban teburin sannan ya mikar da hannunsa ya dauko kan telephone din,da murmushi a fuskarsa ya kara shi a kunnansa da alama yasan mai kiran nasa cikin murya mai tattare da gajiya ya fara magana"Hello sweetheart" dan saurarawa yayi kafin yaci gaba da magana "Ok ganinan zuwa yanzu" daria yayi har Hakoransa masu kyau da tsari suka bayyana cikin jaddada abun da ya fada ya k'ara cewa "Don't worry, I'm coming right away" yana fadin hakan ya maida telephone din ya mike har lokacin fuskansa da dan murmushi,Corridorn ya shiga kofa biyu ce a ciki daya tana kallon mutum in ya shiga wurin,dayan kuma na a bangaren bangon dake dama,sai da ya tsaya ya cire takalmin kafansa ya daura sa saman Shoe rag din dake ajiye a wurin anyi mashi design mai kyau da daukan hankali yabar safar dake a kafarsa bai cire ba kafin ya tura kofan dake a bangaren dama ya shiga,masha Allah Bedroom ne mai kyau da tsari bai da hayaniya Italian Bed ne da Bedside drawers din shi sai Dressing mirror wanda ke dauke da yan kwalaben turare da yan mayukan shafawa saidai da gani masu tsada ne don jikinsu kadai abun kallo ne,a bangon dake kallon gadon kuwa Wardrobe ce gaba daya bangon wadda ke rufe ruf a iya hangena nakasa gane yadda ake budata don banga hannun da za'a kama a bude ta ba, gaba daya Furniture din Coffee brown ne masu duhu sosai don inba ka shigo sosae ba zaka yi tunanin kayan bakake ne,haka Labulen dake a jikin katuwar Window din d'akin ma coffe ne mai kyaun gaske ga kauri wanda tsakiyan sa ke a tsage anyi hanging din bari daya,a Angles (sako) din bangon da gadon yake kuwa Floor lamps (dogayen fitilun kasa) ne dogaye ko ina an aje daya. Gaban dressing mirror din ya tsaya ya cire agogon hannunsa ya daura a saman wurin kana yasa hannu cikin Aljihun wandon sa ya fiddo da wallet dinsa itama ya daura ta a wurin ya juya ya tunkari wata kofa dake a rufe da alama kofan Bandaki ce,kofan na budewa na tsaya kallon Ikon Allah don kuwa ba toilet bane wani dan daki ne mai tsawo sai dai bai cika fadi ba akwai Wall Cabinet (durowar bango) a jikin dogon bangon dakin wadda ke a bude ga kaya nan iri iri wasu a sagale a jikin hangers wasu kuma a ninke daga gafen cabinet din kuma madaidaicin injin wanki ne wato Washing Machine a jiye.a bangon dake kallon inda cabinet din take katon Madubi ne manne da bango daga kasan shi kuma wurin d'aura mayuka ne dasu Shampoo da sabulai kala kala da alama wurin laundry ne,wato wurin wanki dasu kayan dauda,tsayawa yayi gaban tangamemen madubin wurin yana kallon fuskarsa kafin yasa hannu ya ciro wipe daga cikin wani kwali mai kyau a hankali ya fara goge Fuskansa da ita,nikam zuru nayi ina kallon ikon Allah,ya gama goge ko ina ya jefa ta cikin dustbin sannan ya tunkari Wall Cabinet din ya fara cire kayan da ke jikinsa tun daga kan rigan saman zuwa ta cikin da safar dake a kafafunsa yayi hanging dinsu jikin hangers din Cabinet din ya rage daga shi sai Vest da Short acan sama cikin wani gida ya mika hannunsa ya dauko wani abu dake a linke fari sol cikin kayan da ke wurin da alama Bathrobe ce wato rigan wanka wadda duk jikinta gashi gashi ne mai laushin gaske daga haka ya tura kopan Toilet din dake cikin wurin ya shige.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*By Oummu Imam📲*

*Free Page5️⃣&6️⃣*

Sanye da Bathrobe din da ya d'auka ya fito,sai da ya cire Slippers din dake k'afar sa a bakin kofan toilet din yasa wasu flip-flops dake a waje cikin laundry din,K'arasowa yayi gaban Mirror din dake a Laundry room d'in ruwa na dripping daga cikin sumar kansa da alama wanke kan yayi,Juyawa yayi ya d'aukko d'an farin towel a cikin Cabinet din bangon ya dawo gaban mirror din yana tsane ruwan cikin sumar kafin ya jawo Stool ya zauna ya rataya towel din a wuyansa a can gefen mirror din ya mika hannunsa ya d'aukko Hair dryer wadda dama a jone take ya fara busar da sumar tasa yana dan jujjuya ta da d'ayan hannun yan mintuna ya dauka yana busar da sumar kafin ya maida dryer din inda ya d'aukko ta,Hair Oil ya matsa a tafin hannunsa ya shafa ma sumar sannan ya bude robar da Cotton buds suke ya zaro daya yana kwalkwale Kunnansa ya gama goge duka kunnuwan ya jefa abubuwan wadanda ba wani dirty a jikin su cikin Wastebin. Daga haka ya mike ya nufi kofar shiga Bedroom din har lokacin Bathrobe din na a jikinsa,gaban dressing mirror ya tsaya ya fara matso mayuka yana shafe jikinsa bayan ya gama wardrobe d'in dakin ya tunkara wadda na k'osa inga ta yadda ake buda ta gefenta na dama ya tsaya,sak'a hannunsa gefenta yayi ya latsa sai ga shi ta fara zugewa da kanta,Iko sai Allah ashe Sliding ce,a tsakiyan murfin ta akwae tsaga wadda ta raba marfin biyu daidai,in ta daman aka bud'e sai ta zugo ta rufe ta hagun haka ma in ta hagun aka bud'e,komai dai na masu arziki na daban ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin. Kayan sawa ne birjik a cikin ta wasu a rataye jikin hangers,wasu a ninninke gasu nan a tsare abun gwanin burgewa. Kowane kaya da wurinsu,Jeans,Shirts,Suits,Shaddoji,Yadiddika,wasu ma kayan a cikin leda suke alamar sabbi ne,ga Underwears suma wurin su daban tsarin kayan dai kaman Boutique,fiddo kayan da zai sa yayi had'i da underwears sannan ya latsa jikin marfin daga ciki ta fara rufewa ya juya ya nufi gefen gadon ya d'aura kayan.......

Bayan ya gama sa kayan wanda T-Shirt ce coffe brown da bakin wando tracksuit wanda yad'an tsuke daga k'asa gafe da gefensa akwai zip wanda sai ka k'ura idanu zaka gani,rigan kuwa ta zauna cib ajikinsa hannun rigan ya kama cinyar hannunsa wadda take a murd'e da gani yana Bodybuilding,gaban Dressing mirror ya koma ya matso wani hadaddan mai ya shiga mutsitsika ma tafin hannuwansa,bayan ya gama ya dauko Hair Spray ya fesa ma gashin kansa sannan ya daukko turaren jiki wanda kwalbar shi kanta abun kallo ce ya faffesa ma jikinsa maida kwalbar yayi ya daukko wata itama mai matukar kyau ya fesa.....saida ya fesa turare kala ukku kafin ya dau Comb yana sharce kanshi wanda yake nad'e ko ba'a sharce ba bai yamutsewa,Drawer chest ya jawo ya fiddo da wani kwali mai kyau da k'yalli ya d'aura shi gaban mirrorn sannan ya bude,wasu irin agoguna ne masu kyaun gaske designers kala daban daban kowacce a dan gidanta ya fiddo mai fata kalan rigarsa ya daura sannan ya dauki wadda ya cire d'azun ya maida ta ciki ya mayar da kwalin hadi da rufe drawer. A corridorn ya tsaya ya ciro takalma Slide Sandals bak'ake daga cikin Shoe rag kafin ya fito parlor a daidai nan kuma telephone din ya sake fara ringing,dan girgiza kai yayi yana murmushi bai kalli inda yake ba yasa hannu ya dauki wayarsa da ya aje dazun ya fice. Ta Corridorn daya bi dazun ya fito cikin farfajiyar gidan mai girman gaske cikin natsuwa yake tafiya ya tunkari k'aton flat din dake a cikin farfajiyar wanda sak fentin shi kalar na gidan ne,Wani farin d'awisu ne ya fito daga bayan flat din ya bude jikin shi yana kuka gwanin burgewa,bansan lokacin da ni mai rubuto maku labarin na furta"lah kuga wani hadaddan dawisu,abun ka da ba'a saba gani ba,shi kau yalla6an ko kallon shi bai yi ba ya shige Entrance din,a wani dan corridor ya tsaya ya cire takalmansa da alama nan ake aje takalma kafin ashiga main Parlour din don akwai wasu takalman jere a gefe,shiga yayi cikin parlon wanda yake mai girman gaske fentinsa milk colour yana dauke da Royal Sofas masu kyau yadin su Maroon design din kwalliyarsu golden mai kyau ga Table dinsu aje a tsakiya daga can bayan kujerun kuwa dining area ce mai dauke da dinning table da kujerun shi irin design din kujerun parlorn, gaba kad'an da dining din kofa ce ke kallon su wadda corridor ne anan kuma kofofin bedrooms suke,Pop Casting din dake a bangaren da kayan kallo suke irin na d'akin mutumin da ya shigo ne sai dae hotunan dake wurin sunfi yawa har a sauran bangarorin bangon parlourn duk an kafe hotuna manya manya,hotunan wata dattijuwa sunfi yawa wasu tayi da family dinta wad'anda suke kyawawan gaske,wani kuma tayi da turawa akwai wanda tayi da Governor yana bata Award,da kuma wanda tayi da mutananmu na nan da alama a wurin aiki ne,akwae wanda take ita kadai ta nad'a lifaya fuskanta sanye da glasses tayi daria har hak'orin makkan ta ya bayyana daga kasa an rubuta sunanta,HAJIA HAUWA ADAMU ZAKEE,Akwae hotunan wani babban mutum wanda yayi suna gaisawa da shugaban k'asa,wani kuma tare da dattijuwar matar ya riketa fuskarsu d'auke da fara'a,akwae wanda kuma yake zaune a majalissar tarayya wato National Assembly k'asan hoton an rubuta sunan shi,SENATOR ALI ADAMU ZAKEE. Akwae flowers a Angles din parlorn da A.C manne a jikin bango,Labulayen cikin parlorn kuwa maroon ne da ratsin golden masu shegen kyau.

Zaune saman kujera 2 seater dattijuwar matar dake jikin hotunan parlon ce gafenta telephone ne ajiye hannunta rike da magazine yayin da idanunta ke cikin glasses da alama Medical glass ne,da ka kalleta zaka fahimci ta manyanta sosae sai dae yanayin hutu yasa ba lalle ka iya kiyasta ainihin shekarunta ba,tana da haske don ba baka bace,ba kaman kuma da jikin ke samun hutu sosai, Tsaye mutumin yayi a bakin kofar shigowa ya dafa bango da hannunsa d'aya yana kallon matar da murmushi a fuskarsa. Sarai taji shigowar shi amman ta share taki d'agowa ta kalle sa idanunta na kan jaridar hannunta. Dan gyaran murya yayi,still tak'i dagowa ta kalle sa hakan yasa ya dan d'aga kafadarsa cikin ransa yace"Mun saba aii..." cikin parlon ya shiga ya tunkari inda take zaune yasa hannu ya dauke Telephone din dake gefenta ya maidashi adan sak'on da table dinshi yake, Zaunawa yayi gefenta ya d'an kwantar da kanshi a saman kafad'arta yace "Sweetheart fuskan shanun na miye ne? "What happen?" Ya kara tambaya,banza tayi dashi hakan yasa ya juya yana kallon fuskarta hannu yasa yana gyara mata bakin da ta turo alamun fushi,ya cigaba da magana, "Haba Beb fushin na miye ne..? kin wani turo baki,baki gan yanda kika yi muni ba,Smile plss..." ya fad'a har lokacin hannun shi na a gemun ta yana dan jan shi.Hannu tasa ta buge hannun shi kafin tace"Wato don kaga na damu da kai shiyasa nazama abun wulakanta wa ko? "Oh no Sweethrt ya zaki ce haka..,Am not hoping to see that day,dani zan wulakanta ki,ai ko wani nagan zai wulakanta man ke sai inda karfi na ya k'are" ya k'arasa maganar yana kara kwantar da kansa a kafad'an ta. "To amman miya sa na kira ka kace man kana zuwa harda wani cewa right away,Amman shiru ka k'i zuwa tsawon lokaci,akarshe na sake kira kak'i yin picking" tayi maganar tana dan harararsa. D'agowa yayi daga kan kafad'arta ya rik'e hannunta guda yace "Lokacin da kika kira I just came back and I was so tired shiyasa na bari in dan rage kayan jikina in watsa ruwa don insamu karfi" ya kai maganar da d'an murmushi, "To miyasa na sake kira baka dauka ba?" har lokacin bata saki fuska ba, "I was about to come here,lokacin da kiran ya shiga shiyasa naga no need in daukan"ya karasa maganar yana wani lumshe ido,

Readers Also Read