Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 21

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 21

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 21: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 21. "Yalla6ai ka wa Allah da manzonsa ka yafe mana,wllh…

4,444 words

"Yalla6ai ka wa Allah da manzonsa ka yafe mana,wllh ba halinmu bane sharrin zuciya ne,amman munyi alkawari bazamu sake yunkurin aikata hakan ga kowacce yar......" tun kafin goga ya rufe baki fatuu ta katseshi a fusace"sa6a lamba(sarar su ce a makaranta da mutum yayi k'arya ko ya fad'i abu ba daidai ba,sai suce sa6a lamba),karyane yalla6ai,wllh k'arya yake lokacin da suke k'okarin yi man fyaden wannan gayen na hanashi cewa yayi wllh sai yayi wai rabonshi da ya samu irin damar tun akan wata hajara,to yalla6ai sunan Akuya ne hajaran ba mutum ba?kar ka yarda wayo zai maka"ta k'arasa tana ta huci tana hararar goga,kaman zata kai mashi bugu,hannu Dpo ya d'aga mata alamar ta zauna"it's Okey,bazan bari suyi man wayo ba,nagode da bayani" shi kam Sp khamis d'an juyar da kanshi yayi yana dariya,haisam dai na zaune yayi shiru kanshi na kallon k'asa yanata sauraransu don yasan abunda yafi hakan Fatuu zata fada ne.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oummu Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*4️⃣2️⃣*

Kallonsu Dpo yayi tun kafin ma yayi magana goga yasha jinin jikinshi sai faman zare ido yake, "Wacece ita hajarar??"zare ido goga yayi ya fara inda inda,hannu Sp ya d'aga zai kwasa mashi mari da sauri goga ya idasa durkushewa yace"zanyi bayani..." sauke hannu Sp yayi fusakarshi a d'aure yace "uhun" alamar yayi magana, Juyawa yayi ya kalli Dpo"Yalla6ai ita wannan Hajarar wllh ba fyade nayi mata ba,dama ita ta saba,yar talla ce in dae za ka siye abunta to zata baka had'in kai da ka buk'aci hakan,sau d'aya wani abu ya shiga tsakanina da ita,kuma ko lokacin ta riga ta saba kuma tun daga nan ban k'ara yin wani abu da ita ba,an ma dad'e da hakan ta faru,ni yanzu ma wllh bansan a ina take ba ga 6aure nan ka tambayeshi wllh zai fad'a maka gaskiya don shima yasan hajarar kuma shima wani abu ya ta6a shiga tsakaninsu",

gaba d'aya idanunsu suka koma kan 6aure dake ta zaro ido yayi wuri wuri,tun kafin ma a tambayeshi ya fara magana"Wllh yalla6ai duk abunda ya fad'a gaskiya ne,yanzu mu bama musan a ina take ba", Jinjina kae Dpo yayi,a kausashe ya fara magana"I don't care da ta saba ko bata saba ba,all i know is that kun bada gudummawa wurin lalata rayuwar ita yarinyar,Ku yanzu idan k'anwarku ce ko diyarku zaku so ai mata haka?wato don ita ba wata bace a wurinku shiyasa baku damu da yadda rayuwarta zata kasance ba saboda tsabagen mugunta,kun manta da cewar duk abunda kayi ma yar wani kaima za'ayi ma yarka ko kanwarka ko ma matarka,yanzu idan ku ka auri mata irin ita hajaran na tabbatar bazaku zauna da ita ba,in kuma kun zauna da itan tofa zata rayu ne cikin Wulakanci da kaskanci saboda ta riga ta saida mutuncinta tun awaje bakuyi wannan tunanin ba akan ita hajaran da kuka aikata ma hakan ba saboda son zuciya,kuma da kuke cewa an dade da kuka aikata hakan gareta ai ba bari kukai ba tunda gashi yanzu kunzo kuna yunkurin aikata ma Wata"dakatawa yayi yana maida numfashi,su haisam dae sun natsu suna saurararshi yaci gaba"Addininmu addini ne na yanci,ya bamu damar auren mata daga daya har zuwa hudu,idan son abun kuke why not bazaku yi aure ba...." Fatuu ta katse shi tace"atoh"tayi maganar had'i da gyad'a kae,kallon k'asan ido haisam yayi mata da sauri ta sadda kai, Dpo ya d'aura"gaba daya kun bi kun lalata rayuwarku,look at u don Allah,sam baku da wani buri kuna matasa masu jini a jika amman kuna neman kashe rayuwarku,ku kalle ni,ku kalli kowa dake wurin nan muma mutane ne kaman ku, inda munso sai muma mu lalata tamu rayuwar amman bamu za6i yin hakan ba don munsan ba hanya bace mai 6ullewa,mun tsaya munyi karatu gashi yanzu muna cin ribarshi,gaba daya munyi aure muna da iyali kowa girmama mu yake,kufa ba wani uba na gari da zai baku auren diyarshi a irin halin da kuke ciki,mutane gudunku suke saboda kun zama tamkar liability a garesu da kun gansu sun san da wuya in baku rok'e su kudi ba,yan siyasa su yi amfani daku don su ci za6e a d'irka maku kwayoyi don kuyi hatsaniyar da zata sa dole su ci,da zarar sun samu mulkin shikenan amfaninku ya k'are a wurinsu,wani kuda ku ganshi sai dae ko a TV,yana can yana jin dadi shi da iyalinshi,Wani fa ko da mahaifiyarka da ta tsugunna ta haifeka har yaci moriyarka kaje magashiyyan rai hannun Allah da sunan kana son ganinshi ya taimaka maka baza'a ta6a bari ka ganshi ba,kana ji kana gani karshe sai dae ta fadi ta mutu a gabanka akan wasu yan Kud'in da dakun tsaya kun gyara rayuwarku wallahi tallahi kunfi karfinsu,ko dama ba duka ba baku rasa wata hanyar da zaku samu,ina maku wannan Nasihar ne ba wai don bani da aikin yi ba ko ba za'a yanke maku hukunci ba,na kuma tabbatar ba lalle ku d'auka ba,sai dae duk wani wanda aka kawo mana nan ina kokarin ganin nayi mashi Nasiha,idan Allah yasa yana da sauran dama agaba in ya gadama yayi amfani da ita in bai gadama ba yayi watsi da ita,Amman mu munfi son ayi amfani da itan don ba dad'i muke ji ba ayi ta kawo mana masu laifi,burinmu kowa ya zamo nagari"d'an dakatawa yayi,a hankali fatuu ta kalli haisam ganin ba ita yake kallo ba yasa ta kalli Dpo tace"Yalla6ai,d'azun naji kace duk kuna da mata da ya'ya,shifa Yaya Handsome bai yi aure ba har yanzu" tun da yayi maganar ashe abun ya tsaya mata,tana son tayi masa magana tsoron kallon da haisam yayi mata d'azun ne yasa tayi shiru,amman sam ta kasa jurewaa saida ta tanka,

d'an Murmushi Dpon ya yi, don daga d'an zaman da suka yi tsaf ya karanci halin Fatuu, "To ai k'ilan ra'ayin auren ne shi Yaya h......", kasa fad'in sunan yayi don bai fahimci yadda tace ba,kallon haisam yayi"wai ya sunan yake ne?"kafin ya bashi amsa Sp ya rigashi"Haisam ne sunanshi,ita naji kaman Handsome take cewa"ya k'arasa yana dariya, jinjina kai Dpo yayi da d'an murmushi yaci gaba"Yauwa to kilan bai tashi yin auren bane,amman nasan yana da kudin yin auren tunda yana aiki ko"kai ta d'aga"eh yana aiki "gyad'a kai Dpo yayi"to kinga shima yayi karatunshi yana aikinshi,su wad'annan sun ki tsayawa su yi karatun balle suci moriyarshi,kan Naira hamsin sai su fitar ma junansu jini" dan kya6e baki tayi tana kallon su goga,

"Yanzu Sp ina ganin kawae zamuyi filing case d'inne mu mik'a su kotu...." tun kafin ya rufe baki Gaye ya d'aura hannu aka"Don girman Allah yalla6ai ka rufa man asiri,wallahi tallahi ni ba ruwana ba yadda banyi dasu ba akan kar ayi mata ko itama ta fad'i hakan"yana yin shiru Goga ya kar6e"Yalla6ai mun tuba,a yafe mana don Allah zamu yi amfani da nasihar da kayi mana,dama wllh ba wanda ya ta6a zaunar damu ya nuna mana illar abunda muke yi shiyasa...."tun kafin ya rufe baki Dpo ya daka mashi tsawa"karya kake,har ni zaka fad'i ma hakan,duk irin fadakarwar da ake yi ba dare ba rana a kafafen sadarwa, besides,baku da iyayene?ko kana son kace man suna jin dad'in halin da kuka jefa rayuwarku??" shuru goga yayi ya duk'ar da kanshi,sai lokacin haisam ya d'ago ya kallesu tun bayan da aka shigo dasu,Calmly ya fara magana yana nuna gaye"shi wannan babanshi ma is an Imam a Juma'at mosque dake nan Unguwarmu"girgiza kai suka shiga yi gaba dayan su,

"Look at it pls,kana d'an liman kake wannan rayuwar ina amfani don Allah,na tabbatar banda fad'a da yake ma har zubar da kwallarshi bai rasa yi akan ka....."hannu fatuu ta d'an daga alamar zatayi magana,har saida gaban su goga ya fad'i rass duk da basu san abunda zata fad'a ba,kallonta sukai gaba daya Dpo yace"Zarah akwae abunda kike son cewa ne?" kai ta d'aga mashi"na tuno wani abu ne,ai na fad'i maka shi wannan gayen baiso ba ko,shi wanccan gagon ne ya matsa masa,to lokacin da yace mashi a kyaleni babban laifine sai kuma yace na san gidansu in suka aikata man Asirinsu zai tonu ne,to shi gagon sai cewa yayi wai shi wawa ne da zai bari asirinsu ya tonu,wai akwae abunda zasu yi,shine yace ma gayen ya kawo kunnansa ya rad'a masa wata magana ni dae bansan miya ce mashi ba amman naga gayen ya firgita ya zaro ido yana girgiza mashi kai alamar a'a,to Yalla6ai ka tambayesu kaji miye yace zasu yi man don kusan abunda suke aikatawa in suka yi fyaden don kar a gane su",tun kafin takai k'arshen maganarta cikin gaye yayi wani kuka ji kake kuuuu,gaba daya suka shiga tsantsar tashin hankali,da ka kalli fuskokinsu zaka gane basu da gaskia,

Gaba daya idanun kowa ya dawo kansu alamar su ake jira suyi magana,su kam sai faman zare ido suke,gaye tuni jikinshi ya fara kerma,a hankali goga ke dan ta6a cinyarshi alamar ya natsu amman ina tuni zufa ta fara wanke mashi fuska, "Bazakuyi magana bane,miye zaku yi mata bayan kun yi mata fyaden wanda bazai sa agane ku ba???"Dpo ne yayi maganar ya tsaresu da ido ba alamun wasa atattare dashi,inda inda suka fara an rasa wanda zai yi magana sai faman zungurin gaye goga ke yi alamar kada ya fad'a,suna cikin hakan ta bayansu ba zato ba tsammani Sp ya shiga faffaska masu mari hannu bibbiyu,gaba dayansu sai da suka baje suna ta faman zabga salati, Furiously Sp yace"zaku yi magana ko sai ansa ku" gaye ne ya d'ago yana motsa baki kamar zai yi magana,sai dai tsoro ya hanashi, "Kai naga kafi su gaskia,tell me miye yace zaku yi mata" Dpo ya fad'a yana kallon Gaye,baki na kerma ya soma cewa"Yalla6ai zan fad'i maka gaskiya,amman don Allah na rokeka ka yafe man,wllh ni ba ruwana"kai ya d'aga masa alamar to,kafin yace"ina jinka"

Duk yadda goga yaso hana gaye ya k'asa,don gaba daya idanunsu na akan gayen,cikin en ina gaye ya fara magana "C...ce...cew...cewa ya..yi in munyi mata mu k....kashheta" Wata zabura fatuu tayi lokaci guda kallabinta ya fad'o kasa,ya rage daga ita sai riga da skirt din jikinta dama gyalenta tuni yabar jikinta,lokaci guda ta furgice ta gigice,kwayar idonta kaman zasu fad'o kasa,ta matukar razana,nan da nan jikinta ya fara rawa kamar mai jin sanyi da kyar ta iya bud'e baki ta fara magana"Yalla6ai DOP kaji da kashe ni zasu yi in sunyi man fyaden,Yaya handsome da baka zo ba kashe ni zasu yi...."maido idonta tayi kan Sp"d'ayan Yalla6ai kaji wai kashe ni suka so yi acikin kangon in sun gama...."baiwar Allah duk ta furgice,sai kiran Dpo take da dop,dama tunda zasu shigo taga sunanshi asaman kopan shiga office d'in,gaba daya hankalinsu ya matukar tashi haik'am da jin abunda su gaye sukai niyyar aikata ma fatuu,gaye kam kuka yake wi wi yana fad'in shi ba ruwanshi wllh,Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa masa had'i da buga table"ka rufe mana baki,idan ba ruwanka uban miyasa ka bashi had'in kai,shi ubanka ne da zai tursasa maka dole ka aikata ba daidai ba,ko ubanka yace ka aikata ba daidai ba ba'ace kai masa biyayya ba bare wani,duk zaku yabawa aya zakinta wllh",

shi dae dpo zuru yayi yana kallonsu hakan yasa goga fara yi mashi magana"Wallahi tallahi Yalla6ai,na rantse da sarkin da yake busan numfashi ba ina nufin zamu aikata mata hakan bane,shi gaye ne naga kaman bazai bamu hadin kai ba saboda ta sanshi,shiyasa na fad'i masa hakan,amman wllh bani da niyyar kashe ta kaji na rantse"Dpo da yayi still yana sauraranshi ya daki table yace"Ubanku zaku ci"d'ago kai yayi ya kwalama sergeant dake bakin kopa kira,shigowa yayi ya sara mashi,dpo yace"take dem back,where is corpral Gajere?", "Ya fita siyo abu ne", "Ok,in ya dawo tell him to have meeting with dem", "Okey Sir"daga haka ya tasa su gaba,gaye nata kuka shida 6aure,goga kam idanunsa sun kad'a sunyi jawur tsananin tashin hankali,Allah sarki Gaye,dama ance son zuciya bacin zuciya,Saboda kar a hanashi kayan maye ya jefa kansa a tsaka mai wuya,Allah ya rabamu da aikata aikin danasani,Ameen.

Ana fita dasu gaye fatuu dake tsaye tayi tsuru har lokacin jikinta kerma yake,ta kalli Dpo tace"Yalla6ai Dop fitsari nike ji"jinjina kai yayi kafin yace wani abu Sp ya leka waje yana kwalama Corpral Jummai kira,ba tare da 6ata lokaci ba jumman tazo sanye cikin uniform,tana da d'an tsawo da jiki,hakan yasa kayan suka yi mata cuf cuf,sara masu tayi had'i da fadin"Sir",nuna mata Fatuu Sp yayi"ki kaita Toilet ",ta amsa da Ok,daga haka ta nufi fatuu idanunta akan haisam da ya sadda kai yana ta6a wayarsa,ruko hannun fatuu tayi tace ma haisam" Barka da rana",Slowly ya d'ago suka had'a ido,cikin cool voice dinsa yace"Yauwa,ya aiki",da sauri tace"Alhamdulillah,gamu a cikinsa",kai kawae ya jinjina kafin ya maida idonsa kan wayarsa,still dpo yayi yana kallonta,shikam Sp khamis juyar da kanshi yayi yana dariya,cikin ransa yake fad'in"su jummai anga kyakkyawa",

Tsaye Jummai tayi tana jiran fatuu ta fito daga cikin toilet",fitowa tayi tana gyara skirt dinta,jummai ta kalleta da murmushi"har kin gama?" kai fatuu ta d'aga mata, "Ya sunanki ne" tace"Fateema"dama abunda yasa tace ma su Dpo sunanta Zarah saboda haisam ne kada ta fad'i sunan mamanshi a gabanshi,jinjina kai corpral jummai tayi,kafin tace"Wannan da kuka zo dashi yayanki ne?" kai ta kara d'aga mata, Inda inda jummai ta shiga yi kafin ta kuma cewa"kinsan Number d'in wayarshi ki bani?"wani kallo fatuu tabi ta dashi har sai da tasha jinin jikinta,a hankali ta girgiza mata kai"ni bansan number din shi ba,nida ba waya gare ni ba", Hannu jummai ta kai ta dafa kafadarta"Ok muje,amman karki fad'a ma kowa na tambayi no dinshi kinji",a hankali tace toh,uhmm jummai bata san wacece fatuu ba,ba don halin da fatun take ciki ba nasan tana komawa cikin Office din sai ta fallasa ta,

Suna zuwa bakin office din,jummai tace mata ta shiga ita kuma ta wuce,bayan fatuu ta shiga iske su tayi su ukkun suna cikin tattaunawa,nuna mata kujerar da ta tashi Sp yayi alamar ta zauna,idonta akan haisam ta zauna,d'an kallonta yayi kafin ya janye idonshi,gyaran murya Dpo yayi"Kema Zarah kina da laifi"a firgice ta kalleshi,yaci gaba"miyasa zaki je wurinsu karfe goman dare bacin kinsan me suke aikatawa awurin,ko bama shaye-shaye suke ba bai kamata kije wurin wani a irin wannan lokacin ba",ta marairaice fuska kaman zatayi kuka tace"ai ni banyi tunanin zai cutar dani ba don ko hannuna bai ta6a kamawa ba shiyasa naje,amman Yaya Handsome yayi man fad'a ya kuma ce ko yayana ma wanda muke uwa daya uba daya zai iya cutar dani,yanzu bazan kara yarda da kowa ba,duk wanda ya ta6a man jiki yaya handsome yace in fad'i ma gwaggota kuma yace har shima",jinjina kai sukayi bayan ta gama,dpo yace"Gud,kuma ki daina rashin ji,in ba haka ba duk ranar da aka kawo mana ke zamu kulleki ne"a rude tace"ai na daina tuntuni wllh yanzu ba ruwana ka tambayi yaya handsome ma", "Owk,kin kyauta,yanzu ina son zaki yi mana aiki..." zaro ido tayi"kana nufin in zama yar sanda?"d'aga mata kai yayi da sauri tace"to ai ni fa likita nike son zama ya zaka ce kuma in zama yar sanda",

"Ai lafiya lou,dama mutum zai iya yin aiki biyu,kuma ai sai kin girma zaki zama likitan shi kuma aikin yar sandar yanzu zaki yi mana shi" Sp ne yayi maganar, Kallon Dpo tayi"to na yarda,mi zanyi?" "Yauwa,zaki zama Jami'ar mu ta sirri ne,ina son kisa mana ido anan unguwar taku,duk wanda kika ga ya shiga kango da wata indae kinsan yarinyar to ki ruga gidansu ki fadi ma iyayenta,in kuma baki sansu ba to kije ki fad'i ma yayanki cewa kinga wani ya shiga da wata kango kar kice zaki bisu fa,sannan k'awayenki da kuke tare suma ki fad'i masu abunda yayanki ya fad'a maki game da yadda zasu kare kansu kuma kada su yarda da kowa", "To zanyi,sai abani kayan yan sandan nima"yar dariya su kae harda haisam, "to ai ke aikin sirri zaki yi mana,in kika sa Uniform kuma ai za'a gane ke yar sanda ce,kuma kinga masu aikata laifin zasu guji aikatawa a inda zaki gansu,wasu kuma suna iya zuwa gida suce zasu yi maki wani abun,amman kinga in babu Uniform d'in ba wanda zai sani sai iya mu kawae"kai ta d'aga mashi cike da gamsuwa, "To Albashi fa" gaba daya suka tuntsire da dariya shi dae haisam d'an Murmushi yayi,Sp yace"ai mun zata zaki yi mana kyauta ne,to ga yaya handsome ne shi zai rink'a biyanki" zaro ido tayi"shi kuma,a'a abarshi to zanyi kyauta",had'a baki sukai wurin ce mata sun gode, daga haka haisam ya kalli Dpo"Sir,are u done wit her?" d'aga mashi kai yayi"yes"kallon fatuu yayi gently yace"Zarah ki jirani a Mota"kai ta d'aga mashi daga haka ta mike ta nufi hanyar fita,Sp yace"ba ki d'auki gyalenki ba"sam ta manta ma da tazo da wani gyale harda yar jakarta duk suna akasa,komawa tayi ta d'aukko daga haka ta fuce su Dpo na mata sai anjima,

Bayan fitarta suka ci gaba da tattaunawa akan su Gaye,da shi haisam tunkan su zo ma ya sanar da Sp so yake a yafe masu tunda basu kaiga aikatawa ba,ayi masu horo sannan suyi rubutun cewa bazasu kara ba sai kuma ga wata babbar maganar,don haka yace ma Dpo ya bar komae a wurinsu su yanke masu hukuncin da ya dace kawae,duk hadin kan da suke bukata zai basu,daga haka suka yi sallama da Dpo din suka fito,

Atare suka nufo cikin station d'in bayan sun fito daga cikin corridorn Office d'in Dpo, "Kawai ni a tura mu kotun zaifi don wasa da hankali zai tayi mun,tun yaushe yake cewa a k'ara mashi lokaci zai kawo amman shiru" atare Sp da Haisam suka juya inda suka ji anyi maganar,wani babban mutum ne sanye da malum malum a tsaye gaban kanta yake yin maganar daga gabanshi kuma wani dattijo ne sanye cikin tsohon yadi duk yaji jiki kanshi sanye da wata tsohuwar hula duk ta yankwane gashin fuskarshi da kanshi duk hurhura, "Sergeant mike faruwa ne?" Sp ne yayi tambayar, "Sir game da case din su Alhaji Ubale ne,shi wanda zai kawo masa kudin gashi nan ya zo,sai dae dubu biyar kawae ya kawo,to shine yace wai a tura su court kawae" jinjina kai Sp yayi yana niyyar juyawa su tafi muryar dattijon ta katse mashi hanzarinsa"Yalla6ai wallahi tallahi bani da halin kudinne ba irin kokarin da banyi ba don insamo su in kawo amman abun yaci tura,wannan dubu biyar din ma dana kawo wllh yar wayata ce naje na sayar,yanzu haka gidana ko abincin rana ba'ayi ba ga yarana guda biyu kwance,don su na siyar da wayar amman saboda ba yarda zanyi na kawo kudin nan"cikin karyayyar murya yake magana,yana kaiwa karshe kwalla suka fara zubo mashi yasa tafin hannunshi yana gogewa,ba k'aramin sanyi jikin Sp yayi ba,kallon Sergeant yayi"let me come back"daga haka suka fita,

tunkarar inda motar haisam take sukai bayan sun fito daga cikin station din, "Miye case dinshi ne?" haisam ne yayi tambayar idonshi akan hanya, "Wllh wai wannan Alhajin ne ke yin gini a unguwarsu shine yaronshi da abokinshi suka je gidan suka sace kofofi da winduna so bayan asirin yaran ya tonu an kamosu shine aka yi ma abubuwan da suka sata kudi don tuni sun salwantar dasu,to shi d'ayan yaron mahaifinshi ya biya,wannan dattijon ya rage ya biya nasu,d'azun da nazo ne na iske shi Alhajin nata korafin wai sau ukku ana mashi uzurin ya kawo bai kawo ba,lokacin dattijon bai kaiga zuwa ba" jinjina kai kawae haisam yayi a lokacin suka iso bakin motar,jingina bayanshi yayi da murfin motar ya kalli Sp,"Nawa ne kudin?" "Gaba daya 150k ne so da aka raba kowa zai bada 70k an cire 10k" d'aga kai haisam yayi kafin ya maida idonshi kan wayarshi dake a hannunshi ya fara daddannata, "Your Account no pls", "U mean my account details?"Sp dake kallonshi ya tambaya,kai haisam ya daga mashi ba tare da ya d'ago ba,nan take ya fara karanto mashi acct details din, Da sauri Sp yasa hannu cikin trouser pocket dinsa ya fiddo wayarsa jin k'arar shigowar message,duba wayar yayi da sauri ya dago ya kalli haisam"naga ka turo kudi har 200k,na minene?" A nutse yace"kaba mutumin 150k sai ya biya kudin sauran kuma ya yi amfani dasu"daga haka ya juya yana k'okarin bude Motar, "What about d remaining 50k,mi za'ayi da ita?",banza yayi mashi,ganin hakan yasa Sp k'ara tambayarshi don yayi tunanin ko bai ji shi bane,d'age mashi kafada yayi"i ave no idea"lokaci guda sp ya gane bashi yayi,shine ba zai iya fadi mashi hakan ba, Girgiza kai Sp yayi" H,zakee u will never change",fuskar haisam da d'an Murmushi yace"I was born like dat"hannu Sp ya kai ya d'an bugi shoulder dinshi suka yi dariya gaba daya da alama wata sarar su ce ,godiya ya shiga yi mashi sosae shi dae bai tanka mashi ba,saima bud'e mota da yayi ya shige, Lek'awa ciki Sp ya yi"To sabuwar ma'aikaciyarmu sai munji daga gareki ko"da fara'a yayi maganar,kai kawae fatuu dake zaune ta d'an kwantar da kanta ajikin seat ta d'aga mashi,daga haka sukayi sallama da haisam ya tashi Motar Sp na d'aga masu hannu ya jata suka tafi.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*_RAMADAN KAREEM_☪️*

_Allah ya kar6i ibadunmu yasa muna daga cikin yantattun bayi,Amin ya Sami'ud dua🤲_

*4️⃣3️⃣*

Lokacin da Sp khamis ya koma ciki dattijon nan nata matsar kwalla don kuwa Alhaji Ubale ya matsa akan a turasu kotu kawae,

"Ya Allah na dogara da kai,fadar kace,duk wanda ya dogara da kai ka isar masa,Ya Ubangijina kafi kowa sanin halin da nake ciki na rashi,nayi imani da jarabani da kake yi, nasan ba don baka sona bane sai don ka gwada imanina,Allah ka shirya man yarona da ya saka ni acikin wannan halin da Sauran Al'ummar Annabi(S.A.W)", Dattijon na gama yin Addu'ar ya kalli Sergeant cike da k'warin gwuiwa yace"Ku tura mu kotun,duk da nasan ko anje banda halin biyanshi, Amman ubangijin dana dogara dashi nasan zai kawo man Mafita",ta6e baki Alhaji Ubale yayi ya juyar da kanshi gefe irin ko ajikin shin nan,

duk wannan abun akan idon Sp,yaji duk maganganun da dattijon yayi,nufar inda suke ya yi fuskarshi d'auke da Murmushi,yana isa gaban Dattijon ya mik'a masa hannu,kasa kama hannun SP yayi ya bishi da ido yana mashi kallon mamaki,hakan yasa SP jinjina mashi kai alamar ya bashi hannun,jiki na kerma ya mik'a masa hannu suka yi musabaha SP yace"hak'ika fad'ar Allah ce acikin Suratul D'alaq aya ta ukku'....Waman yatawakkalu alallahi fa huwa hasbuun....,ka dogara dashi ya kuma isar maka ta hanyar kawo maka Mafita"fuskar Sp d'auke da Murmushi yake maganar don ba k'aramin burgeshi dattijon ya yi ba, gaba d'aya bin Sp sukayi da ido cikin rashin fahimtar abunda yake nufi,dattijon kuwa har lokacin hannunshi dake acikin na Sp sai kerma yake yi,

"Baba Mutumin da muka fita tare dashi ya baka Kud'in,ya turo su ta Account d'ina don ka biya shi" lokaci guda su Sergeant suka fara sakin Murmushi had'i da fad'in Alhamdulillah,don suma ba k'aramin tausayi dattijon ya basu ba,

Murya na rawa ya fara Magana"Yalla6ai ban fahimce ka ba,wani ya biya Kud'in kace? ko dae ba daidai kunnena suka ji ba?"

"Baba daidai kaji,ai kasan bazan zolaye kaba da magana irin wannan kuma a irin wannan lokacin" jin hakan yasa dattijon duk'awa k'asa yayi Sujjadar godiya ga Allah ,mik'ewa yayi hawaye cike a idanuwansa"Don Allah waye wannan d'an arzikin,waye mai kirkin nan haka,bai sanni ba, hakanan ya d'auki wannan uban Kud'in ya bani...."yana Maganar kwallan idonshi na zubowa ga kuma Murmushi yana yi duk alokaci d'aya,Sp shima dake Murmushi yace"Baba kada ka damu da sai kasan ko waye,don Allah ya baka",

"Nasani Yalla6ai,amman dae yakamata ai insan waye wanda yayi man wannan abun alkhairin da bazan ta6a mantawa ba asauran rayuwar data rage man",

"Ok shikenan tunda kana son sanin ko waye bari in fad'i maka,Sunan shi Haisam,shi d'an gidan Senator Ali Adamu Zakee ne" Sp na rufe baki Alhaji Ubale ya kar6e, "ahaf d'an gidan dan siyasa ne dake kan mulki,su da ake satar kudinmu ana tara masu ai dole su rinka bada su yadda suka gadama.....",

Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa mashi"Enough!!!kai ka tabbatar kud'in sata ne ya bada?shikenan duk wani mai mulki ya zama 6arawo?idan har cikin mutane akwae na kirki da kuma na banza to tabbas suma shuwagabannin dole asamu na kirki da kuma na banzan tunda daga cikin mutanen ake za6arsu,kuma da kake maganar wai an tara mashi,tabbas kuwa zancenka gaskiya ne an tara masa,sai dai ina son ka sani kud'in halal aka tara masa,kowa anan nasan ya san Mahaifinsa Shahararren mai kud'i ne wanda ya tara dukiyar da har su kare rayuwarsu zata ishesu yin rayuwa cikin jin dad'i,amman hakan bai hana Wannan bawan Allahn tashi ya nemi na kansa ba,injiniya ne na na'ura mai kwakwalwa,aiki yake ba dare ba rana,Kamfanoni da Manyan Ma'aikatu har ma da kananu wad'anda suka danganci aikinsa dake a Jahohin k'asar nan ake gayyatarsa yaje yayi aiki ba tare da girman kai ba ana biyansa kudin da ba komae yake dasu ba face yin aikin Alkhairin da yafi kowanne lada kamar yadda Manzon Allah(S.A.W) yace,Ka Shigarwa da Mutum Farinciki a rayuwarsa,ko ka yaye masa bakinciki,ko ka d'auke masa wata damuwa,babu aikin da yafi Wannan lada,ban tsaya ina maka wannan dogon bayanin ba don baka cancanci hakan ba,inda naso zan iya sa a kulle man kai saboda wannan maganar da kayi akanshi,amman banyi hakan ba don nasan da yawan Mutane irin wannan tunanin naka garesu akan duk wani mai Mulki,a k'arshe ina mai gargad'inka da ka rink'a kiyaye harshen ka don Mutum irin wannan da kayi ma kazafi nada daraja ba awurin Mutane kawai ba har a wurin Ubangiji don yana daga cikin mafi Alkhairin mutane kaman yadda Manzon Allah(SAW) yace,khairun nas man yan faun nas,khairun nas anfa'uhun lin nas,(Mafi Alkhairin Mutane wanda yake amfanar mutane,mafi Alkhairin Mutane wanda Mutane suke amfanuwa dashi).

Ranshi a Matukar 6ace ya k'arasa Maganar,shikam Alhaji Ubale yayi wuri wuri da ido sai faman bashi hakuri yake yana fad'in su6ul da baka ne,banza yayi mashi,ganin yanayinshi yasa su Sergeant had'a baki wurin fad'in"Sorry Sir," shima Dattijon Mutumin hakurin yake bashi,sai da ya d'auki d'an lokaci ba tare daya tanka masu ba kafin yaba Alhaji Ubale Umarnin ya fad'o masa Account details d'inshi,baki na rawa ya soma fad'i mashi,ba tare da 6ata lokaci ba Kudin suka shiga yace mashi ya duba,dubu 70 cuf ya gani ya d'ago ya fadi mashi cewa sun shigo,shiru Sp yayi mashi don ba k'aramin kule shi yayi ba,ba don ya kai Zuciya nesa ba da sai ya hukunta shi, k'okarin barin cikin Station d'in Alhaji Ubale ya fara,dakatar dashi Sergeant yayi"Hey,Alhaji waya baka izinin tafiya ne?"da sauri ya dawo yana fad'in"Oh kuyi hakuri pls,nazata shikenan" a rud'e ya yi Maganar,

Readers Also Read