Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 23
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 23: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 23. "Allah ya bata lafiya",yace still idanunsa akanta,…
4,453 words
"Allah ya bata lafiya",yace still idanunsa akanta, hajiya taci gaba"aikam zuwa dubiya ya kama ni,ance wai ka gaida mai gaidaka,sam Fateema bata da kyaliya,kar kaso kaga yadda take tashin hankalinta in ban jin dadi,wani ciwo da nayi kwanaki tasani gaba tayi tana kuka wai bata so in Mutu"takai maganar tana dariya,shima d'an Murmushi yayi bai dai ce mata komae ba,
"Ko zaka je ka dubata ne,kaga ma sai ku gaisa da Gwaggonta don ta sanka sosai,kaima nasan zaka santa,matar akwai kirki wllh",shiru ya d'an yi,hajiya ta bishi da ido can ya furta"Ok", "Yauwa,ka gano ya jikin nata,ko zuwa da daddare ne sai in lek'a",jinjina mata kai yayi daga haka ya mik'e,hajiya tace"in can d'in zaka ko Saude ta zuba abinci ka tafin mata dashi?" Wani kallo ya jefa ma hajiyan kaman harara"ni zaki aika da abinci",
dariya tayi"wai ai naga kaima da baka lpy ta kawo maka abun dubiya ko", "Ba can zani ba yanzu sai after asr,in zaki bada abu akai mata ki bada"daga haka ya nufi hanyar fita hajiya nata dariya dama tsokana ce kawae tasan bazai ta6a daukar warmer din abinci ba da sunan zuwa dubiya,
Yana isa part d'inshi ya fad'a toilet don yin wanka,after some minutes ya fito jikinsa sanye da Bathrobe ya nufi Closet dinshi,within few minutes ya shirya cikin Red polo shirt da farin Jeans itama rigar daga cikin collar dinta fari ne sai faman sakin daddad'an kamshi yake,a corridor ya tsaya yasa fararen takalma,Masha Allah shigar Red and White nasan ba sai na fad'i kyan da yayi cikin kayan ba,a parlor ya d'au wayarsa da ya aje lokacin da ya shigo daga haka ya nufi Masallaci da aka gama kiran sallan la'asar.
Yana fitowa daga masallacin bayan an gama sallan ya nufi gidansu Fatuu,a bakin shagon Amadu ya tsaya shima bai dad'e da ya dawo daga sallar ba,yana ganin haisam d'in ya shiga washe baki yana gaidashi,hannu ya mik'a masa suka gaisa,cikin cool voice d'inshi yace mashi ya shiga ya sanar yazo duba Zarah ne,da sauri ya amsa mashi da toh kafin ya nufi cikin gidan,bai jima ba ya fito yace mashi ya shigo,atare suka shiga Amadu na gaba shi kuma yana binsa a nutse yake yin tafiyar har suka shiga ciki,suna shiga gwaggo dake abakin kopar d'akinta ta tarbeshi da fara'a"Maraba da d'ana Haisam",fuska a sake ya amsa mata nan take kuma ya ga ya santa da Hajiya,gashi ma har ta kirashi da d'anta,cikin d'akin tace mashi ya shigo wanda ke d'auke da gado six by six da wardrobe d'inshi mai gida biyu da d'an k'aramin Dressing Mirror sai kujera two seater da kuma one seater, d'akin sai k'amshin incense stick da aka kunna ke tashi,a bakin kopar d'akin ya cire takalmansa ya shiga da yar sallama,fuskar gwaggo da fara'a ta nuna masa kujera don ya zauna,bayan ya zauna ita kuma ta koma bakin gadon ta zauna,cikin muryarsa mai sanyi ya fara gaisar da ita ta amsa,shiru ya d'an yi can kuma ya d'ago don tunda ya shigo kanshi na a k'asa, "Ya mai jiki",
"Ah maijiki da sauk'i sosae,oni Hajiya sai da ta taso ka ai nace mata ta samu sauki da bata wahalar da kai ba wllh", shi dai shiru yayi idonshi na kan floor d'in dakin,ita kam gwaggo idonta na akanshi bata ta6a tunanin zai zo gidan ba don iyakarta dashi su gaisa ne in yazo gidan hajiya,
can tace"Mun ga d'awainiyar abun Arziki,inata son inzo in yi godiya wllh jikin nata ne ya hana,don jiya gaba d'aya bansamu na fita bama saboda jikin nata,yau nike niyyar in shigo da daddare sai kuma ga ka,da nasan zaka zo ai da tunda safe na shigo"fuskarta d'auke da fara'a take yin maganar, d'an guntun Murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba yace"ba wani abu ai",
Godiya ta shiga yi mashi sosae tana shi mashi Albarka,tun yana amsawa kasa kasa har dae yayi shiru yana ci gaba da amsawa acikin ransa,tana cikin yin godiyar Amadu ya shigo dauke da plate ya d'auro ruwa pure water da yan k'ananun robobin lemu guda biyu don irinsu kawae yake saidawa saboda yan makaranta don ba freezer gareshi ba a shagon,a gaban haisam ya aje ya k'ara gaidashi kafin ya fita,shiru sukayi na d'an wani lokaci don Mutumin ba gwanin yin fira bane ba kaman kuma a inda yake bak'o,
"Kasha mana", d'an d'agowa yayi"Nagode,bana jin kishi", gwaggo tace"duk da haka ya kamata kasha na zumunci,sai dae kuma kar in matsa ma bansan ko baka shan irinsu ba"da yar zolaya tayi Maganar, sai dae kuma tabbas bai shan ruwan leda da irin lemun da aka kawo masa don ba kowane irin lemu yake sha ba ko a gidansu,daurewa yayi ya cije ya d'auki ledan ruwan gwaggo tai saurin mik'ewa"bari in kawo maka Cup",tsayawa yayi don dama hakanan ya d'auka ba don yana son sha a ledan ba,
dawowa tayi hannunta ruk'e da cup na jug mai kyau,ita ta zuba mashi ruwan kafin ta mik'a mashi ta koma inda ta tashi,kur6a yayi kaman sau ukku ya aje cup d'in,gwaggo dake kallonshi tace"da ina niyyar zubo abinci gashi ruwan ma ka k'i sha sosae",kallonta yayi da d'an Murmushi"a'a Nagode ban jima da naci ba", dariya gwaggon tayi tace"ai nasanka sarai baka son cin abinci shiyasa ma ban zubo ba", bai dai ce mata komae ba,can tace"gashi anzo gaida mara lafiyar tana ta bacci,bari in taso ta...."da sauri ya katseta"No a kyaleta,Allah ya bata lafiya"daga haka ya mike zai tafi,
Shi ya fara fitowa yasa takalmanshi kafin Gwaggo ta biyo bayanshi tana ta faman godiyar zuwan da yayi,suna kaiwa tsakiyar gidan yaji an kwala mashi kira,
"Ya Handsome",
atare suka juya shi da gwaggo inda kiran ya fito,Fatuu ce tsaye a bakin kopar dakinta tana sanye da pink riga da skirt d'in da ya siya mata acikin kayannan kanta a bud'e,ba k'aramin kyau suka yi mata ba musamman skirt din box pleated ne irin mai fad'in nan mai tattara daga sama kuma bai kai har can k'asa ba,kayan sun mata cif a jiki ba kamar daba ramamma bace sai ta koma kamar rainon madara da bournvita itama koda yake rainon madarar shanu ce😂,Slowly ya nufi inda take,tsayawa yayi yana kallonta,ta d'an fad'a ba kamar idanunta da ka kallesu zaka gane bata lpy,
"Ya handsome kai ne a gidanmu" ta fad'a tana mashi murmushi,kafin yace wani abu Gwaggo tace"Eh,ke yazo gaidawa da jiki", kallonshi tayi"to amman shine zaka tafi kuma baka ganni ba",
dan Murmushi yayi calmly yace"kina bacci ne,ya jikin naki?" "na samu sauk'i",jinjina kai yayi, "To ka shigo d'akina tunda gaida ni kazo", still da Murmushi akan fuskarshi"to ba gaki na gan ki ba", turo baki tayi ta langwa6ar da kae"to ka shigo kaga d'akina",d'an bude mata idanu yayi,tana ganin hakan ta fara mashi magiya harda buga kafafu,shi dae still yayi yana kallon ikon Allah,
"Ina ruwan Fatuu uwar rikici tana lafiya ma ya aka cika balle bata lpy,ka shiga d'ana Haisam"Gwaggo dake jingine da bangon d'akinta ta fad'a,dariya fatuu ta fara"to an dae ce ka shigo ato", d'an girgiza kai yayi kafin ya fara k'okarin cire takalmanshi gwaggon na cewa ya shiga dasu amman saida ya cire,sai da ya d'an duk'a da zai shiga cikin d'akin,tsaye yayi atsakiyar d'akin bayan ya shiga,ita kuwa sai faman dariyar jin dad'i take yau Yaya Handsome acikin dakinta,
"Ya handsome kaga dakina ni kadai nike kwana acikinshi,wannan kayan fa cikin na Mamata ne da ta rasu aka bani gado"Murmushi yayi yana bin d'akin da kallo,
"gashi ma baki gyarawa"da sauri ta juya tana kallon dakin kafin ta juyo"wllh kuwa ina gyarawa fa", Yatsanshi ya mik'a yana nuna kayan dake a gefen gadonta"wannan nan yakamata a aje su?" da sauri tace"wanki ne jiya kawu Amadu yayi man,to ban lafiya shiyasa ban ninninke su ba amman gwaggo tace zata ninke man su"ganin yana mata wani kallo tace"wllh Allah ina yin tsafta,ai gwaggo ma bata bari in yi kazanta",nodding kai yayi,
nufar gadon tayi ta ture kayan can k'arshen gado ta kalleshi"kazo ka zauna Ya handsome kana ta tsayuwa",hannu ya d'an daga"No zan tafi ne,Allah ya baki lpy",daga haka ya nufi hanyar fita ta biyo shi,yana niyyar sa hannu ya d'aga labulen d'akin yayi tuntu6e da inda ledan k'asan ta fashe,da sauri Fatuu ta ruko hannunshi tace"kai Ya Handsome kabi a hankali,wllh kada Mutum take yi,rannan fa na shigo da gudu ta tad'iye ni na fad'i baka gan yadda hancina ya bugu ba,ni nama yi tunanin ya ta6e wllh", he couldn't help it but laugh,Calmly yace"My hand"da sauri ta saki hannun"Yi hakuri,don karka fad'i ne na ruke ka"d'an ta6e baki ya yi wato in ma faduwar zai yi ita a tunaninta zata iya ruke shi ne,daga haka ya fita itama ta fito gwaggo da ta shige d'akinta ta fara kwalama kira,
"Gwaggo!gwaggo..."fitowa tayi tun kafin tace wani abu fatuu ta fara magana, "Kinga ina ta fama dake ki canja man leda kin k'iya,ai gashi nan sauran kad'an ta kada Ya Handsome wllh"waro ido gwaggo tayi kafin tace wani abu haisam dake kallon fatuu yana Murmushi yace"ko an canja zaki lalata ne,gara abar maki shi ahaka", Da sauri gwaggo ta kar6e"Wllh kaman kasani,mutum kullum shine shigowa da fita da gudu ba dole ta lalace ba,shiyasa nace ban canja mata ai"tana dariya tayi maganar,ita kam fatuu turo baki tayi"Wayyo don kun ga ban lafiya shine zaku yi man taron dangi ko"gaba d'aya su kae dariya,kallon gwaggo haisam yayi ya k'ara mata sallama daga haka ya nufi hanyar fita fatuu na biye dashi a baya,ita kam gwaggo tana rako shi bakin kitchen ta juya ta koma d'aki,
Yana shiga cikin zauren gidan ya juyo ya kalleta"ki koma,a ina kika ga patient na rakiya" dariya tayi tace"ai na warke",
shiru yayi yana ta kallonta itama shi take kallo,d'age mata gira yayi"damuwa kika sa aranki shiyasa kike ciwo ko?" turo baki tayi tace"to fa so sukayi su kashe ni ba dole in damu ba,da shikenan washe garin ranar sai dae a tsinci gawata acikin kangon,wllh nasan gwaggo itama sai ta mutu inta rasa ni kaman mamana,kawu Amadu ma ko bai mutu ba nasan sai ya sume,kai nasan bazaka damu ba ko?"still kallonta yake yace"Why", "Saboda baka dad'e daka sanni ba", d'an Murmushin gefen baki yayi"Yanzu dae ai bai faru ba,so stop worrying ur self en" kai ta d'aga mashi kafin tace"ai daman hakanan naji ciwon yazo man aranar da daddare"jinjina mata kai yayi yana niyyar juyawa tace"baka ga kayan dake jikina ba?",
tsayawa yayi"na gani sunyi maki kyau", ruke ha6a tayi alamar mamaki tace"wai Ya handsome ya akai kasan kayan da zasu yi man ba tare da ka gwada ni ba,kasan fa duka kayan sunyi man daidai wllh", fuskarshi a sake yace"Ke in naje dake wurin siyan kaya bazaki iya za6ar man daidai dani ba?"kallonshi ta fara yi from head to toe can tace"gaskiya sai dae in kanga maka kayan inga in sunyi maka,kuma ma sai dai inyi d'agyal,ko nayi ma ba lalle in kamo ka ba don tsawo gare ka nikuma yar gudul ce"ta k'arasa tana ta dariya shima yar dariyar ya yi,abunda fatuu bata sani ba shine tsananin lissafin dake akan haisam yasa daya kalli Mutum zai iya estimating abunda zai mashi daidai saboda karatun da yayi ya kunshi lissafi sosae,
"Go back Zarah"ya fad'a yana niyyar fita,maimakon ta koma d'in sai ta biyoshi tana fad'in"bari in raka ka waje sai in dawo,tun ranar juma'a da muka dawo ban sake lek'o waje ba"shiru baice mata komae ba har suka fita,adaidai gefen kiosk d'in Amadu ya juyo yace to ta koma,murmushi tayi mashi tace"Nagode Ya Handsome mai kirki"kai kawae ya d'aga mata,da baya baya ta fara komawa ciki tana mashi bye bye,yana dae tsaye yanata kallonta da d'an murmushi akan fuskarshi,cikin rashin sani ta tafi zata bugi bangon kopar shiga cikin gidan,da d'an k'arfi ya furta"Zarah!be careful"juyawa tayi ta kalli bayanta sai kuma ta juyo tana ta dariya,girgiza mata kai yai yayi mata alamar ta shige daga haka ya juya ya tafi.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH*_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣5️⃣*
Misalin karfe takwas da wani abu na dare Haisam ya parker motarsa abakin shagon Amadu,fitowa yayi ya zagaya d'aya bangaren ya bud'e back door,wata k'atuwar farar leda ya fiddo ya nufi kiosk d'in bayan ya rufe kopar Motar,yara guda biyu ne ke yin siyayya,saida ya d'an jira a gefe aka sallamesu kafin ya matsa,Amadu na ganinshi ya fara washe baki ya shiga gaisar dashi,hannu ya bashi suka gaisa kafin ya d'aura ledan agaban kiosk d'in yace ya kai ciki,juyawa yayi ya nufi motarshi Amadu sai faman godiya yake mashi,hannu kawai ya d'aga mashi daga haka ya bud'e Motar ya shige ya jata,
Lokacin da ya shiga gidan,gwaggo na zaune saman darduma dake shimfide'e akan tabarma a can k'arshen bangon dake tsakankanin d'akunansu da alama salla tayi gashi ba wutan Nepa amman tsakar gidan akwai hasken globe mai caji,Fatuu na kwance agabanta ta d'aura kanta saman cinyar Gwaggon suna fira tana d'an shafa mata kai,wurinsu ya nufa ya aje ledan agabansu,
"gashi Yaya Haisam yace in kawo",
zumbur fatuu ta d'ago jin ance haisam,ita kuwa gwaggo da mamaki ta bud'e ledan tana fad'in"yace ka kawo...", d'agowa tayi ido waje ta kalli Amadu bayan ta duba abunda ke a ciki tace"shi bai gajiya ne,wannan hidima ai tayi yawa",
Amadu yace"wllh yanzun nan ina shago ya tsaya da Mota yazo har bakin shagon yace in kawo ciki....", katseshi fatuu tayi"gwaggo miye aciki?", fiddo kayan cikin ledan ta fara yi tana fad'in"abubuwan ciye ciye ne", zaro ido fatuu tayi ganin kayan da aka kawo,Manyan gasassun kaji guda biyu,manyan robobin yoghourt da ice cream guda ukku ukku sai wata leda shak'e da kayan Marmari ba abunda babu su kankana,Apple,Abarba,lemu, Ayaba,shamman,pear da sauransu dae wasu ma bata san su ba,fatuu na ganin fruit d'in tasa hannu ta rufe bakinta,
"Wannan dai da gani kayan mara lpy ne" gwaggo ce tayi maganar, "To gwaggo wake da lpy,ai yanzu kowa kika gani ba lafiya ne dashi ba,in d'aukko Plate ki zuba man kasona na baro shago ba kowa", kallonshi gwaggo tayi tace"Oh ni bansan wane kalan uba bane kai,yarinya bata lafiya baka siyo mata ba,an kawo mata kuma kana niyyar cinye mata",
"amman dai ai kinsan wannan kayan sunyi mata yawa ko,dama can harda mu aka kawo shiyasa ma wasu abubuwan aka sako ukku ukku", dariya gwaggo tayi tana girgiza kai tace"Wannan dae da sunanta aka kawo don haka nata ne",tana kai Maganar ta tura ma fatuu ledan kayan,da sauri Amadu yace"Gwaggo ya da haka,kinsan fa Yarinyar nan ba hankali ta cika ba kin tura mata ledan kuma gaba d'aya",ita dai dariya kawai take ganin yadda ya harzuka,
Hannu fatuu ta kai cikin ledan kayan ta fiddo duka ice cream d'in ta aje agabanta daga haka ta tura ma gwaggo ledan tace"ni su nike so", kallon Amadu gwaggo tayi"to kaga ita abunda ma ya dameta nan,sai ka d'aukko plate a kicin in zuba maka ko ka koma shagon,juyawa yayi ya nufi kicin d'in yana fad'in"atoh yanzu naji bayani,amman kyace wai kayan mara lafiya ne", Bayan ya kawo plate d'in ta yagar mashi naman mai d'an yawa,ta bashi robar Yoghourt d'aya tana niyyar dibar mashi fruit d'in yace ta barshi ba yanzu ba sai ya gama da wad'annan tukun,daga haka ya nufi hanyar fita kopar gida gwaggo nata mashi tsiya,ita kam fatuu tasa ice cream d'in tayi gaba taita sha gwaggo na ce mata kada sanyi ya kamata fa,har saida ta shanye roba biyu sannan ta fara cin naman,gaba dayansu ba wanda yaci abincin dare don ba k'aramin k'oshi sukai ba,d'ayar robar Yoghourt d'in data rage gwaggo tace ma fatuu ta k'ara da ita tace to saidai ta tafi da ita Makaranta gobe,acikin d'an tsohon fridge d'insu dake acikin kicin suka saka sauran abubuwan da suka rage harda fruit masu yawa don basu sha su sosae ba,naman ma sun rage,daga haka gwaggo tasata ta d'aukko magunguna ta sha suka ci gaba da yin hira har aka maido da wuta suka nufi d'akin gwaggon gaba d'aya don su kwanta dama tunda ta fara ciwo anan take kwana.
MONDAY
Wuraren k'arfe 7:00 na safe Haisam tsaye agaban Dressing Mirror d'in bedroom d'inshi ya gama shiryawa cikin tsadaddun suit black color,yar cikin fara ce sai Bow tie red color,daga gaban aljihun ta saman anyi adon red harda wata yar sarka mai walwali,k'afafunshi na sanye da dakakkun takalma penny loafer na zallar bak'ar fata wad'anda sababbi ne fil yau ya fara saka su harma da suit d'in,ba k'aramin had'uwa yayi ba acikin kayan,da ka kalle shi zaka yanke cewa ba d'an Nigeria bane sai kaji yayi magana sannan zaka iya gasgata hakan,bayan ya gama gyara sumarshi ya kai hannu ya d'auki kwalbar turare ya shiga feshe jikinshi dashi,aje shi yayi ya d'aukko wata kwalbar ya k'ara fesawa sai da ya fesa kala ukku kana ya dakata ya feshe sumarshi da hair spray mai daddad'an kamshi,agogon Diamond d'inshi dake a ajiye ya d'auka ya sanya a wrist d'insa daga haka ya nufi kopar fita,
Bayan ya fita kopar d'akin da Fatuu taje fitsari ya bud'e ya shiga,bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da wata yar babbar bak'ar jaka irin ta ma'aikata,cikin parlon ya fito daga haka ya nufi kopa ya fice,
A nutse yake tafiya cikin harabar gidan bayan ya fito ya nufi part d'in hajiya,tunda ya fito Tk dake tattara busassun ganyayyakin da suka fad'o a harabar ya dakata da aikin da yakeyi gaba d'aya ya zuba ma Haisam na mujiya,ba k'aramin tafiya yayi dashi ba,yadda Haisam ke d'aukar wanka in zaije aiki yasa tk k'agara yaga ya fara aikin shima don ya rink'a daukar wankan kamar yadda yake yi,lokacin da yazo saitin tk d'in da hannu yayi mashi alamar yazo aikuwa da sauri ya wurgar da tsintsiyar kwakwar ya nufe shi,gaidashi ya shiga yi bayan ya isa,amsa mashi yayi fuska asake ya mik'a mashi jakarshi had'i da bashi Umarnin ya k'ara goge masa Mercedes Benz kafin ya fito daga haka ya wuce,juyawa tk yayi hannunsa ruk'e da jakar ya tunkari parking space d'in bakinshi a washe kaman gonar auduga,a fili yake fad'in"Yau shegiyar za'a hau..",
yana isa ya bud'e d'ayan side d'in driver ya aje jakar ya maida kopar ya rufe,lallausan farin yadin da yake goge motoci dashi ya d'aukko acikin wurin ya fara goge jikin Motar wadda dama tuni agoge take sai faman kyalli take don kullum ne sai Tk ya gogeta duk da ba hawanta Haisam d'in ke yi ba tun bayan da ya zo da ita.
Bakinshi d'auke da Sallama ya shiga cikin parlon,Hajiya dake zaune saman Sofa 2 seater jikinta nad'e da lifaya Milk Color mai Manyan fulawoyi light blue idanunta sanye cikin glasses ta amsa mashi had'i da kai idanunta gareshi,suna had'a ido ya sakar mata k'ayataccen Murmushinshi itama Murmushin takeyi,nufar inda take zaune yayi yana fad'in"Gud Morning My Sweethrt ", Hannu ta mik'o mashi" Morning a Shining Star,How was ur nyt?", "Alhamdulillah"ya fad'a yayin da ya kai hannu yana tattara takardun dake gefenta ya zauna,
"Yau zaki fita kenan",
"Eh,muna da bak'in turawane, shiyasa zan fita da wuri don mu tar6esu",jinjina mata kai yayi, "Bari akawo maka ko tea ne ka sha", hannu ya kai Saman Sofa table dake gabanta ya d'aukko tea cup dake d'auke da kakkauran tea mai zafi yana d'an tiriri yace"let me take this" kai ta d'aga masa ya fara sipping tea d'in,yana cikin sha Saude ta k'araso inda suke hannunta d'auke da d'an babban plate an rufeshi ta aje asaman table din,kallonshi tayi tace"Barka da Safiya Yalla6ai", "Barka"ya amsa mata,juyawa tayi gun hajiya"Hajiya gashi nan,za'a zubo masa ne?" kafin ta bata amsa Haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,hajiya tace ta tafi kawae,
Hannu hajiya tasa ta bud'e plate din,kallon haisam tayi"ka d'an had'a da wad'annan kafi jin nauyin cikinka", kallon plate d'in yayi,sliced bread ne da wainar kwai,ganin bai ce komai ba yasa hajiya kai hannu ta d'aukko yankan biredi d'aya ta yago wainar tasa aciki ta fara k'okarin bashi a baki,a hankali yake gatsar bread d'in yana sipping tea d'in har ya cinye ahaka yaci guda biyu ganin tana kokarin d'aukko wani yasashi mik'ewa da sauri yace"am Ok Sweethrt",k'yaleshi tayi don tasan baison cin abinci da sassafe wannan bread d'in ma da ya ci sa'a aka ci,duk'awa ya yi saitin fuskarta ya manna mata kiss a gefen fuskar wanda hakan yake mata kullum in zai tafi aiki,mik'ewa ya yi ya tunkari Corridor d'in dakinta bayan d'an wani lokaci ya fito da alama bakinshi ya wanko,hanyar fita daga falon ya nufa yana fad'in"Till i come back", Hajiya dake Murmushi ta fara yi mashi Addu'ar da ta saba yi mashi kullum"Allah Ubangiji Ya tsare,Ya baka ikon yin abunda kaje yi,ya kuma maido man da kai lafiya",
Hannu ya d'ago mata"wish u same Sweethrt",daga haka ya fuce,hajiya dake kallon bayanshi tana ta murmushi ta d'an girgiza kai,tana matuk'ar kaunar Haisam ba kamar kuma da ya kasance akwae yanayin Mijinta da ya d'aukko wato Gen. Adamu Zakee.
__________________
Mik'ewa tayi bayan ta gama sanya igiyoyin Sandals dinta ta goya yar jakarta ta makaranta, kallon gwaggo tayi dake tsaye abakin kopar d'akinta, "Zan tafi Gwaggo",
"kindai matsa sai kinje Makarantar nan,da kin bari kin k'ara samun sauki sosae", turo baki tayi tace"ai na samu sauk'in zan iya zuwa,kuma in na zauna ma ai ni kad'ai za'a bari tunda kema aiki zaki ko",
"Ai shikenan,dama ina gudun kar jikin ya dawo maki ne a Makarantar...." katseta Fatuu tayi"in ma ciwon ya dawo ba ga Haulatu ba ai sai ta rakani clinic ko akan dae in zauna ni kadai a gida", gyad'a kai gwaggo tayi kawae dama ita niyyarta ta tura Fatun gidan hajiya in zata aikin to ta matsa sai taje makarantar,kud'i gwaggo ta mik'o mata ta amsa daga haka ta juya ta nufi hanyar fita,
"ba kin ajiye abu ba a fridge jiya kince dashi zaki makarantar",Gwaggo ce tayi Maganar,da sauri ta juyo ta nufi kicin tana fad'in"Yauwa kakus nagode da kika tuna man don har na manta",d'aukko robar youghout d'in tayi ta hado da fruit a bakin kicin ta saukko da jakar ta zuba su ciki kafin ta maidata bayan,nufar kopar fita tayi tana fad'in"na tafi kakus", "A dawo lpy,Allah ya tsare", juyowa tayi ta kalli gwaggo,"yau baki cewa banda rigima don Allah Fatuu?",
Yar dariya gwaggon tayi tace"ai na lura dae kaman da gaske kin daina rashin ji,da alama Allah ya kar6i Addu'ata",dariya kawai tayi ta d'aga mata hannu tana mata bye bye itama gwaggon hakan tayi mata har ta fuce,girgiza kai Gwaggon tayi,tana Matuk'ar jin Fatuu cikin ranta,tamkar Aysha d'inta take kallonta,juyawa tayi ta shige cikin d'aki don ta idasa shiryawa itama ta tafi wurin aiki.
Parking Space ya nufa bayan ya fito,a tsaye ya iske tk yana d'an k'ara kakka6e jikin Motar, yana ganin haisam ya dakata da abunda yake yana mashi dariya,yana isowa kusa dashi yasa hannu da sauri ya bud'e mashi Motar,har zai shiga ya juyo ya kalli tk dake ta faman bin sa da ido, "Any problem?"ya tambaya fuskarshi a sake,maimakon ya bashi amsa sai yasa hannu yana d'an sosa k'eya,a zahiri tabbas yana da buk'ata,sai dae bazai iya fad'i mashi ba don gani yake buk'atar tashi tana da d'an girma,wani mashin ne da ake yayi yake so ya mallaka sai yaba kaninshi nashi da yake da,tuntuni yake rok'onshi ya bashi mashin d'in yace mashi ya bari sai ya siya wani to kuma yanzu baida kudin da zai siya wanccan din don ba wata sana'a yake ba illa kud'in da hajiya ke saka mashi a Account a duk k'arshen wata saboda Karatunshi da yan hidindimun kanshi,duk da yana balaen son mashin d'in bai ta6a tunanin tambayarta ba don dama tk yana da hangen nesa sam baida had'ama ya iya bin komai a hankali kuma hada hakan yasa yake zaune lafiya da hajiya,
Jin yayi shiru yasa Haisam gane akwae wani abu, "tell me,kana da matsala ne?", Haisam da ya rik'e murfin motar ya sake tambaya,d'an Murmushin yak'e Tk yayi yace" ba wani abu Yaya haisam",
shigewa yayi cikin Motar tk ya matsa don ya rufe masa kopar,
"U can send me a message",
Haisam ya fad'a ba tare da ya kalli tk d'in ba,rufe masa kopar yayi bayan ya amsa mashi da toh,sai da yayi Warming d'in Motar kafin ya fita daga cikin parking space din,shima tk fitowa ya yi ya tsaya gefe guda yana kallon Motar,da gudu ya ja Motar ya fice daga gidan su officer na d'aga mashi hannu ya sakar masu Horn.
************, Tafe take ta raba hanya biyu tana ta tafiya sai dai yau tafiyar tata da yar natsuwa ba kaman yadda ta saba wurga k'afafu ba in tana tafiya,horn d'in da aka yi mata da k'arfi ne yasa ta koma gefen hanyar da sauri ba tare data waigo ba,cigaba da tafiya tayi aka k'ara yi mata horn d'in aikuwa a fusace ta juyo cike da tsiwa ta bud'e baki zata yi magana,tana yin arba da Bak'ar Motar dake a bayantan ta kasa magana,bin ta kawae tayi da ido ba tare data san ko waye a ciki ba,slowly glass d'in kopar gaban ya fara sauka k'asa,tana yin arba da fuskar Haisam tasa duka tafukan hannayenta ta rufe baki alamar mamaki,jingina kanshi yayi ajikin headrest d'in seat yana kallonta fuskarshi a sake,
"Ya Handsome ashe kaine kake ta man horn" fatuu ta fad'a bayan ta cire hannun,
"Yea,ni ne za'ai ma masifa" ya bata amsa, Tura baki tayi"ni fa ba masifa zanyi ba,da naji an k'ara yi man horn dinne shine na juyo ince ai na kauce",d'an ta6e baki yayi don yasan ba gaskiya ta fad'a ba, "Kin samu sauki ne zaki school?" "Eh,kuma ma in ban je ba ni kad'ai za'a bari agidan", jinjina kai yayi"Ok,get into d car", hannu ta d'aga tana nuna motar tace"in shigo kace?" kai ya d'aga mata alamar eh,matsawa tayi ta kai hannu zata bud'e kopar baya taji ta a rufe,komawa tayi saitin haisam tace"Ya handsome tak'i bud'ewa ko ba ta nan ake shiga bane?",daga yadda ya kwantar da kanshi ya daga mata kai alamar eh,
"To ta ina ake shiga?",ta tambaya, yatsanshi guda ya d'aga sama,zaro ido tayi"kenan ta sama ake hawa?",gyad'a kai yayi,cike da mamaki take kallon saman Motar can tace"itama kaman jirgi ce kenan ta,to mi zan taka in hau,ko itama tsani ke gareta?" Still yayi yana kallonta ganin da gaske ta d'auka ta saman ake hawa,tunanin ranar da zata daina wauta ya shiga yi tana ganin handle ajikin kopan bayan amman take tambayan ko bata nan ake shiga ba,ganin tana ta kallonshi tana jiran amsa yasashi cewa"ke zaki hau da kanki", hannu tasa ta ruke ha6arta ta fara tunanin yadda zata hau saman Motar,kallonshi tayi tace"Ya Handsome kodae ka idasa sauke glass d'in sai ka matsa man in shigo ta nan inda kake",wani kallo ya bita dashi kafin ya kai hannu ya bud'e k'ofofin ta gaba,juyawa yayi yace"ki shigo", "Ta ina?"ta tambaya,