Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 25

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 25

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 25: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 25. tana ganin sun shigo ta wani sha murr,saman Desk…

4,496 words

tana ganin sun shigo ta wani sha murr,saman Desk din wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya a tsaye,tambayarta sukae wai haulatu ta gaya mata sak'onsu tace masu eh,nan suka shiga zuzuta haisam din suna fadin basu ta6a ganin mutum mai irin kyawun shi ba a Nigeria,tambayoyi suka rink'a yi mata cike da rainin wayau take basu amsa wani lokacin kuma ta 6a66ake masu da dariya ganin yadda duk suka susuce kan Ya Handsome,ba kamar Binta Musa da Asma'u Kabeer su da gaske sonshi suke sai faman rokonta suke wai ta shigar dasu wurinshi da taga dae bilhakki da gaske suke sai tace masu ita bata iyawa don bai wasa da ita duk wadda ke sonshi in ya k'ara zuwa taje da kanta ta fad'i mashi,nan take duk suka ce gaskia bazasu iya ba,bai yi wasa da ita bama ita dake yar'uwarshi balle su, kuma sunga yasan principal kar su ja ma kansu,fatuu tace to sai suyi hakuri kawae,k'arshe dai atare suka idasa cinye kayan break d'in su Fatun kafin suka tafi.

Kallon Haulat Fatuu tayi fuska a tur6une"banzayen sun zo sun cinye mana abu gashi ma ban k'oshi ba", d'an Murmushi tayi tace"rabonsu ne ya tsaga suma", ta6e baki tayi"to sai kiyi sauri ki taso muje mu siya wani abu kafin adawo",tayi Maganar had'i da mik'ewa tsaye itama Haulat d'in ta tashi suka fita daga cikin class din.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story._

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*4️⃣7️⃣*

Lokacin da suka tunkaro gate d'in,Discipline master na tsaye awurin masu gadi sunata yi mashi zancen Haisam,sai faman yaba kirkinshi suke,Dariya Malam Mahadi yayi yace"ai kufa dama kunfi kowa shaida kirkinshi tunda ya cika maku Aljihunanku,amma dae nima na yaba da kirkin shi gaskiya", adaidai nan su Fatuu suka k'araso bakin gate d'in,kallon masu gadin Malam Mahadi yayi"to ga wadda tayi maku sanadin Alkhairin da kuka samu nan sai kuyi mata godiya" ya yi Maganar yana nuna Fatuu,atare suka kalleta da mamaki Maigadi mai kirki kaman yadda suke cewa ya furta"Dama Fulani ce ya kawo?",sunan da yake kiran fatuu dashi kenan saboda sun sa6a sosai da fulatanci ma yake mata magana duk in tazo bakin gate d'in kuma dayake shi yana a toilet lokacin da fatun ta fito daga Motar Haisam shiyasa baisan itace aka kawon ba,

"Eh Yayanta ne" Malam Mahadi ya fad'a,aikuwa nan suka shiga yima Fatuu godiya gaba d'ayansu suna fad'in Allah ya k'ara Arziki shi d'ayan da fulatanci yake mata godiyar ita dae sai faman sakin Murmushi take ba tare data ce masu komai ba,

"Ku sai yanzu zaku je Break d'in an kusa dawowa"Malam Mahadi yace, turo baki tayi"to ai da a aji zamu yi break d'in bazamu fito ba sai kawai......"da sauri Haulat ta tari numfashinta tace"munci kayan break din tare da wasu ne to sai muka ji bamu k'oshi ba shine zamu je mu siyo wani abu mu k'ara" kai ya jinjina masu daga haka suka wuce, Bayan sun fita gate d'inne Haulat tace"kefa yanzu yakamata ki zama mai aji don d'an gidan Hajiyar Sanata ya kankaro maki girma,shiyasa na katseki da kina ma Malam Mahadi magana don nasan halinki sarai shima kina iya ce mashi banzayen prefects ne suka cinye mana abun break d'in wanda hakan ba girmanki bane kina dangin Senator",ta k'arasa tana tik'ar dariya,itama Fatun kyalkyacewa tayi da dariyar tace"Dangin Senator masu shanu ba,sufa duk sun yarda baki ga yadda Malam mahadin ma ke man magana ba cikin mutunci inda da ne wllh kora mu zaiyi ya hana ni fita break d'in tunda bamu fito da wuri ba",dariya suka ci gaba da yi Haulat nata tsokanarta tana fad'in dangin Senator.

__________

Misalin karfe 4:30 na ranar,Haisam na zaune a falon hajiya saman Sofa 2 seater yana cin abinci,jikinshi sanye cikin Sportswear da gani gym zai tafi, "Wai wace yarinya ce yau ka kai Wtc ne?" hajiya ta jefo masa tambaya,sai da ya cinye abincin dake acikin bakin kafin yace"Wani abu?", "A'a,dama principal ce ta kira ni muka gaisa shine tace man yau ta ganka a Makarantarta kun gaisa har kake ce mata sister dinka ka kawo shine nike ta tunanin wacece ka kai Makarantar ne?" "Zarah" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba, "Dama saida nayi tunanin itace ka kai", shiru yayi baice mata komae ba,ganin yana k'okarin mik'ewa tace"halan har ka k'oshi?", Kai ya d'aga mata"Yea,i ate too much food at work"d'an ta6e baki tayi"ka dae ci abunda ka saba ci ba dae abinci ba,ni da nasan hali ai saidae ka fadi ma wani hakan ya yarda badai ni ba", d'an murmushi yayi"Am serious yau naci abinci,Zarah tasa nayi alk'awarin zan ci abinci in k'oshi"fuskar Hajiya d'auke da tsananin mamaki tace"Fateemar ce tasa ka yin hakan?"kai ya d'aga mata alamar eh,ganin tana ta binshi da ido har lokacin da mamaki akan fuskarta yasashi fad'i mata yadda akai tasa shi yin Alk'awarin,Lokaci guda tayi Dariya ta furta"Ina ruwan Fateema,ta man daidai itama tasan ba yadda za'ai tarkacen su biskit su ruke Mutum kamar ka", daga haka ya nufi Dining area ya kuskure bakinsa had'i da wanke hannayensa a Washbasin duk da badasu yaci abincin ba,hanyar fita daga parlon ya nufa ya d'aga ma Hajiya dake kallonshi hannu alamar bye bye,itama hannun ta d'aga masa tace"A dawo lpy,Allah ya tsare.

Yana fita parking space ya nufa ya fiddo bike dinsa cikin harabar gidan,jakarshi dake rataye ajikin bike d'in ya curo ya goyata a bayansa daga haka ya tasheshi bayan yasa helmet ya nufi gate da tuni an bude masa shi ya fuce.

**** ***** *****

Bayan Sallar isha'i Haisam ya shigo gidan,parking space ya shige ya parker bike din,jakarshi rataye a hannunsa na hagu ya nufi part d'inshi,yana niyyar shiga cikin corridor wayarsa ta fara ringing alamar ana kiransa,hannu yakai cikin Aljihun wandonsa ya fiddota, tsayawa yayi ganin hajiya ce ke kiran nasa,picking call din yayi ya kara wayar a kunnansa,

"Naji ka shigo ka d'an lek'o nan kana da bak'o", amsa mata yayi da"Ok" daga haka ya cire wayar,yaso ya isa part d'in nasa don ba abunda yafi buk'ata ayanzu face yayi wanka to amman baisan wane bak'o bane kuma baisan tsawon lokacin da ya d'auka yana jiransa ba hakanne yasashi aje jakar anan bakin corridor din ya juya ya nufi part d'in Hajiya,

Da sallama ya shiga cikin falon lokacin daya isa,Hajiya na zaune tana opposite da wani dattijo sanye cikin manyan kaya riga da wando kanshi sanye da hula harda rawani,amsa mashi sallamar sukayi ya nufi sofa one seater dake kusa da wadda hajiya ke azaune ya zauna,gaida mutumin yayi cikin girmamawa ya amsa mashi, "Yauwa Mahaifin Ashiru ne yazo yana son ganinka" hajiya ta fad'a,shiru haisam yayi yana son ya tuna waye ma Ashirun,kallon Dattijon hajiya tayi"Malam bismillah kuyi magana", Amsawa yayi da toh ya d'an matso daga kan kujeran kafin yayi gyaran murya ya fara Magana "Dama naje can caji office ne don in dubashi to ananne nasamu labarin kaine ashe ka kai case d'in..."d'an dakatawa ya yi,sai yanzu Haisam ya gane Ashirun da ake nufi wato Gaye,

d'agowa Malam Tanimu yayi cikin sanyin murya ya d'ora da fad'in"tun bayan da al'amarin ya faru banyi niyyar sa baki ba saboda babban laifi ne sukayi niyyar aikatawa ba don Allah ya kiyaye ba,kuma yakamata dama arinka bada goyon baya wurin hukunta masu aikata irin wannan laifin ta hakanne za'a samu saukin al'amarin,amman ina kowa baison a hukunta nashi,sai mutum ya aikata mummunan laifi amman kiri kiri kaga danginshi sun shiga sunyi yadda sukai an sake shi ba tare da an hukuntashi ba yadda yakamata,shiyasa kullum k'ara samun yawaitar masu aikata munanan laifuka ake tunda sunga ko an kama ma saki ake ba tare da anyi wani tsattsauran hukunci ba,Allah ya kyauta ya rabamu da son zuciya" gaba daya suka amsa da Amin, Gyaran murya ya k'ara yi kafin ya sake d'aurawa"Yau da naje tasani gaba yayi yanata kuka yana rok'ona akan kar na bari wai akai shi gidan yari shi wllh yasan yana shaye shaye da yan d'auke d'auke amman bai ta6a yunkurin aikata fyade ba,na nuna masa komae ya faru dashi shi yaja ma kansa da ya za6i yin irin wannan rayuwar har yayi abokai gur6atattu irinshi,bayan an maidashi cikine muka tattauna da wani d'an sanda nan mai kirki har yake nuna man ya tausaya ma yaron don ya jefa kanshi cikin matsala gashi yanzu da kyar ne in ba'a kaisu gidan yari ba,kuma matsalan wasu in aka yanke masu hukunci kan laifin da basu aikata ba in suka fito sai kaga sunzo suna aikata laifin saidae wanda Allah yasa yana da sauran imani,wasu kuma sukan had'u da manyan masu laifine sai kaga sun koyo mugayen laifukan da sunfi wanda suke aikatawa muni da sauransu dai..."dakatawa yayi yana maida numfashi kafin yaci gaba"atak'aice dai ni Uba ne,duk yadda naso k'arfafa zuciyata saida tayi rauni,maganganun d'an sandan nan sun tsaya man araina,kullum bani da fata da burin daya wuce inga Ashiru ya shiryu,shin yanzu in aka kaishi gidan yarin ya halayyarsa zata koma kuma?wannan tambayar ita ta tsaya man arai ta kuma saka ni jin tsoron zuwansa can d'in don bazan so yafi hakan lalacewa ba tunda dai ba'a ta6a canja ma tuwo suna,shi d'in d'ana ne ni na haifesa hakan bazai ta6a canjawa ba,ba komae ya bani kwarin gwuiwar zuwa gareka ba face furucin da ya rink'a yi yana kuka na ya yarda zai koma Jos in dae na ku6utar dashi lokacin da za'a maidashi cikin cell....",

"Wani abu ake a Jos d'in?" Hajiya ce ta katseshi da wannan tambayar, "Eh akwai wani Yayana acan babban malamin tsangaya ne,ana tura mashi kangararrun yara ba kamar masu irin halin Ashirun wato masu yin shaye shaye da kuma sata kuma akan dace su shiryu,da farko lokacin da ya jefa rayuwarshi cikin wannan halin nayi tunanin zan iya gyarashi amman ina,ganin abun nashi yana yin gaba ne yasa nayi ma yayan nawa magana akanshi yace in kaishi can,wllh banfi sati guda da kaishi ba sai gashi ya gudo,bayan wani lokaci na sake d'aukarshi na maidashi amman sai ya sake guduwa kuma abunda ya tada man hankali shine da ya gudun ba nan gida ya dawo ba gaba yayi bamu san inda ya nufa ba,hankalinmu ya matukar tashi don ba irin neman da bamu yi mashi ba amman shiru ba labarinshi,haka muka hakura kuma muka dukufa da yin Addu'ar Allah ya bayyana shi kwatsam, wata rana sai gashi kamar an jefo shi,nayi Matuk'ar farincikin dawowarsa duk da canjin dana gani atattare dashi,wai ashe lagos ya tafi bayan ya gudun,to tun dagananne na hak'ura da turashi jos d'in duk da halin nashi saima abunda yayi gaba bayan yaje lagos d'in", sauke ajiyar zuciya suka yi gaba dayansu,

"Yanzu mi kake bukata a wurina ne?" Haisam ne ya yi Maganar,shiru yayi ya d'an sadda kanshi k'asa kafin ya d'ago yace"idan zai yuwu ina neman alfarmar ayi mashi duk hukuncin da ya dace amman don Allah kar akaishi kotu don daga can ne za'a iya tura su gidan yari,na dad'e ina mashi Addu'ar shiriya watakil lokacinne yayi don tabbas naga nadama a idanuwanshi kuma sanin basu kaiga aikata laifin bane yasa nayi karfin halin zuwa nema mashi wannan Alfarmar,wallahi tallahi kaji arantse da ace yau sun aikata laifin koda shi Ashirun bai yin ba bazan ta6a nema masa sassauci ba duk kuwa yadda raina zai sosu zan bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan ayanke masa hukunci",

Jin ya dakata yasa Haisam fara Magana"at first munso ayi masu afuwa ne tunda basu kaiga aikatawa ba so bayan munje can da Yarinyar ne kuma ta kawo wani issue wanda yasa dole aka fasa yi masu afuwan da akai niyya bansan ko kasamu labarin hakan ba",da d'an rud'u Malam tanimu ya girgiza mashi kai"bansan wani abu ba bayan abunda ake tuhumarsu dashi,dayake tunda aka kamasu ni banje ba sai yau,yan uwansa dae na zuwa Mahaifiyarsa ma taje",jinjina kai Haisam yayi nan take ya fad'i masa dalilin da yasa aka fasa yi masu afuwar,cike da tashin hankali ya saka salati yana tafa hannuwa,a razane, a kuma firgice yace"Wllh sam bansan hakan abun yake ba da ban fara ma zuwa nema masa afuwa ba,ashe rashin hankalin Ashiru har yakai haka,yanzu ace saboda kayan maye zai goyi bayan wannan aika aikar da suka so yi ba don Allah ya takaita Al'amarin ba",lokaci guda idanunsa suka cuccuko tab da kwalla,girgiza kai hajiya tayi cike da takaici ta fara magana"nima dai na Matuk'ar girgiza wllh da jin hakan,sam Ashiru bai yi man wayo ba,yadda bai goyi baya ba tun farko kamata yayi jin wannan Mummunar niyyar tasu yasashi bujire masu ta hanyar tona masu asiri amman ina,saboda tsabar rashin hankali ya za6i ya jefa kanshi cikin matsala ta hanyar goya masu baya duk da yasan mummunan kudirinsu ",

"Ai Hajiya ni yanzu ma wllh na cire hannuna daga lamarinshi daman rashin sani ne,duk hukuncin da ya dace ai mashi ai mashi kawae shi ya ja ma kanshi" yana kai Maganar kwallan daya taru suka zubo mashi sharrr ya sunkuyar da kan k'asa, Sigh Haisam yayi gently yace"We should thank Allah da bai basu nasarar aikatawa ba gaba daya,lamarin zai fi zuwa da sauki,in sha Allah zanyi ma wanda case din ke ahannunsu Magana za'a duba ayi abunda zai yuwu",

Hajiya ce ta shiga bashi baki tana cewa kar yasa damuwa aranshi yaci gaba da yi mashi Addu'a kawae don ita kadai ce magani inda rabon shiryuwa wataran komae zai zamo tarihi. Mik'ewa Haisam yayi ya kalli Hajiya"is that all?"ya tambayeta,kallon Malam tanimu dake ta matsar kwalla tayi tace"Malam ko akwae wani abu?"da sauri ya girgiza mata kai"Babu komae hajiya Nagode kwarae,Allah ya k'ara girma",jin hakan yasa Haisam yi mashi sallama ya nufi hanyar fita daga falon don duk a takure yake bazai ta6a samun natsuwa ba har sai yaji saukar ruwa ajikinsa,d'an k'ara tattaunawa sukai kan halin da yara matasa ke jefa rayuwarsu daga bisani Malam Tanimun yayi mata sallama ya tafi.

____________

Washegari da Safe misalin k'arfe 7:30 Fatuu ta fito kopar gida jikinta sanye da kayan makaranta,tsaye tayi gefen kiosk d'in Amadu tana d'an tunanin ko Ya Handsome ya wuce,zuciyarta ce ta raya mata wani abu hakan yasa ta mik'i hanyar zuwa gidan Hajiya,tana karya kwanar Gate aka zuge gate d'in,tsaye tayi tana kallon Motar da ta fito wadda suka je Police Station da itace,adaidai inda take tsaye Motar ta tsaya glass d'in ya fara sauka ahankali tana had'a idanu da Haisam ta sakar mashi Murmushi,shima murmushin ya maida mata yana sanye cikin Suit Ash and black colour,alamar ta shigo yayi mata da kai hakan yasa takai hannu da sauri ta bud'e Motar ta shiga,rufe glass d'in yayi bayan ta rufe kopar,daga haka yaja Motar suka fara tafiya,

"Gud Morning Ya Handsome",fuskarshi asake yace" Morning,how a'r u", "I'm fine" ta bashi amsa,jinjina kai yayi ba tare da ya k'ara cewa kamae ba, "Ya Handsome ashe kasan Principal d'inmu?" kai ya d'aga mata alamar eh, "Ashe shiyasa kasan Makarantar da nike"nan ma kai ya d'aga mata,ganin sun wuce kwanar gidansu Haulat yasata sakin salati "kai innalillahi...."kallonta yayi yace"What?", "Wllh jiya mantawa nayi ban biya ma kawata Haulatu ba hakan yasata ta makara aka tareta,ranta ya 6aci har tana ceman wai tunda an kawo ni a Mota sanyin Ac ya ratsa ni ai dole in manta da ita",

d'an bud'a idanu yayi yace"baki kyauta ba" turo baki tayi cike da shagwa6a"to ai mantawa nayi ko,kowa ba yana yin mantuwa ba",d'an ta6e lips d'insa yayi sai kuma yace"to yau sai ki biya matan ko", "To ai saidae ka aje ni sai inje in biya mata mu hau Bus" kallonta ya d'anyi "Why,ko wannan ba Mota bane?", langa6ar da kai tayi idonta akanshi"to ai kai naga baka son ana zauna maka a bayan mota to kuma in tazo ita a ina zata zauna?"d'age mata gira yayi yace"mukai dake ba'a zauna man a bayan Mota?" zaro ido tayi cike da mamaki"to amman jiya dana zauna ba k'in tafiya kayi ba kace sai na zauna a inda ya dace ka nuna man gaba",

"Yea,ai ni ba Driver dinki bane da zaki zauna a baya kuma gaban ba kowa" bud'a baki tayi alamar mamaki"wai dama saboda hakan ne kace in dawo gaba?'kai ya d'aga mata kafin yace"ina ne gidansu Friend d'in naki?", "To ai mun fa wuce kwanar tana baya" gyad'a kai yayi ya fara k'okarin juya motar,kallonta yayi bayan ya juya"shi center d'in nasu yana fita titi ne?" "Eh,amman fa bansan ko Wannan k'atuwar motar zata wuce ba don lungun nasu d'an tsukuku ne,yauwa ga lungun nan" takai Maganar tana nuna masa lungun da yatsanta,kallon lungun yayi nan take ya fahimci motan zata iya wucewa hakan yasashi kutsawa ciki,suna zuwa daidai gidansu Haulat tace "wait, wait ga gidan nan",tayi Maganar tana nuna gidan,ganin tana k'okarin fita yace"ki bari ayi mata horn mana ta fito",da sauri ta kalleshi ido waje"Haulatun za'ai ma horn,ita da ba mota garesu ba taya zata gane ita ake kira bari dae inje in kirata" yadda tayi Maganar sai kace ita Motar garesu,tana shiga cikin zauren gidan suka kusan cin karo da ita ta taho tana sanya hijabin Makaranta,tana ganin fatuu tace"ai na zata yauma a Motar aka daukeki kin manta dani..."da sauri Fatuu tasa hannu ta rufe mata baki,

"Dalla kiyi shiru da Ya Handsome d'in fa muka zo" da mamaki Haulat ta d'an bud'a idanunta"bangane ba?", "Shi d'an gidan hajiyan nike nufi gashi nan kopar gidanku shi yace in kirawo ki zai kaimu Makarantar" zaro ido Haulat tayi ta kasa magana,ita kam Fatuu hannu takai tana gyara mata wuyan hijab d'inta da ya jirkice ta goge mata maikon kosai data gama ci agefen bakin, "Ki taho mutafi kada yayi ta jiranmu,amman fa kada kiyi mashi hauka ko kauyanci da kin shiga motan ki gaidashi sai kija bakinki kiyi shuru don shi baison Surutu" daga haka tayi gaba Haulat da tayi sototo tana saurarenta tabi bayanta,har zata fita ta juyo da sauri"ki saka wannan jakar ledan taki cikin hijab ki 6oyeta har muje class don kauyanci ne ki shiga wannan had'addar Motar da Jakar leda",kai kawai ta gyad'a mata tayi yadda tace daga haka suka fita,nuna mata kopar baya Fatuu tayi tace"ki bud'e ta ki shiga,in baki iya ba in bud'e maki kuma in kin shiga ki kulle da karfi don kar taki rufuwa" d'an Murmushi kawai Haulat tayi takai hannu taja Door handle d'in sai gashi kopar ta bud'e fatuu na ganin ta shiga itama ta bud'e gaban ta shige,

"Ya Handsome gata nan na kirata" kai ya d'aga mata yana k'okarin jan motan Haulat data kame kanta agefe guda tace"ina kwana",kai kawae ya jinjina mata daga haka suka tafi,tunda suka hau hanya Fatuu keta faman zuba kaman burkakkar radio,cike da mamaki haulat ke kallonta ita data gama mata hud'ubar taja bakinta tayi shiru baison surutu amman ita ji yadda ta cika su da surutun,ita dai saidai ta d'an girgiza kai kawae kai kace bata acikin Motar ma.

Yauma har gaban Administrative Block ya kaisu,yana tsayawa Haulat ta rasa yadda zata bud'e Motan ta fita hakan yasa tayi zugudum kirjinta na bugawa, kallon haisam Fatuu tayi tace"Yauwa Ya Handsome inata son in tambayeka wai jiya kuwa ka cika alkawarin daka yi man?" Kwantar da kanshi yayi jikin headrest ya d'aga mata shi alamar eh, "To kaci ka koshin?" daga yadda yake ya d'an juyo ya kalleta"Yea,sosae naci i can't even remember when last dana ci abinci haka",kyalkyacewa tayi da Dariyar farinciki harda d'age kai sama,shi dae sai kallonta yake yana d'an Murmushi, kallonshi tayi bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"to yauma ka d'aukko biscuit d'in?"kai ya daga mata alamar eh, "To ka bani shi sai mu sake kulla Alkawarin yauma" yar harararta yayi"nak'i wayon yau ni zanci abuna in kina so sai ki siya", Magiya ta fara yi mashi tana jujjuya kai wai ya bata ai anan ba'a saida irinshi,Haulat dake baya batasan lokacin da ta fara sakin Murmushi ba ga mamaki tanayi yadda ya sake ma Fatun sai kace dan'uwanta da gaske,

"Zarah bafa zan baki ba,in kuma na bakin i won't promise u zanci wani abinci a wurin aiki"turo baki tayi ta kai hannu ta d'aukko jakarta dake ajiye akasan seat ta juya zata fita, "Zarah" ya kirata,juyawa tayi ta kalleshi fuska a d'aure alamar tayi fushi,d'an Murmushi yayi ya girgiza kai daga haka yakai hannu baya gefen haulat ya d'aukko jakarshi,budeta yayi ya fiddo biscuit har yafi na jiya girma,mik'o mata biscuit d'in yayi ganin tak'i amsa yace"take it!" tana tura baki tace"to ai baka yi alkawarin ba" shiru ya danyi yana kallonta,karfin halinta na bashi mamaki,sigh yayi"to zan ci wani abu in naje wurin aiki shikenan?"

"Abinci ko mi?" "Duk abunda na samu zanci kedai ba so kike in ci in koshi ba?" da sauri ta d'aga mashi kai, "Owk zanyi hakan,ki amsa kina sani ina makara fa", da sauri takai hannu ta kar6i biscuit d'in tasaka acikin jakarta tana d'agowa ya sake mik'a mata N500 yace su samu drink su had'a batare da musu ba ta amsa tayi mashi Godiya, Haulat dai nata bin ta da ido,so take kawai taga yadda zata bud'e kopar,aikuwa tana ganin yadda Fatun tayi itama tayi sai gashi kopar ta bud'e,wani irin sanyi taji aranta dama bata son agane bata iya bud'ewarba ba kamar Fatuu yanzu tayi mata surutu,

tsaye Fatuu tayi tana mashi bye bye yayinda aketa faman binsu da ido saida ya gama juya kan Motar ta kalli Gate sannan ya sauke glass d'in side din da Fatuu take tsaye,alamar tazo yayi mata da kanshi,mik'a ma Haulat jakarta tayi ta nufi Motar,tsaye tayi abakin kopar tace"gani" hannu ya kai cikin jakarshi dake a gefe sai gashi ya fiddo wani Biscuit d'in irin wanda ya batan fuskarshi d'auke da k'ayataccen Murmushinshi yace"I ave another biscuit,so shi zanci in naje aikin tunda ban yi alkawarin cin wani abu daban ba" zaro ido tayi tasa tafin hannun damanta ta rufe baki alamar mamaki,ganin yanata Murmushi yasa ta cire hannun rai a 6ace kaman zatai kuka tace"ni za kaima wayo Ya Handsome?"d'an harararta yayi"ke kika so yi man wayo bare ni,C'mon Go Class Yar Yarinya", daga haka glass d'in Motan ya fara rufewa sama a slow yana gama rufewa yaja motan ya tunkari gate,yana zuwa gate masu gadi suka fara d'aga mashi hannu don sai yanzu suka gane ko waye ganin Fatuu da sukai,tsayawa yayi ya sauke glass d'in side d'inshi yana amsa gaisuwar da suke mashi har wani d'an russunawa suke,ganin ya tsaya yasa Fatuu tsallakawa side d'in masu gadin taci gaba da kallonshi fuska atur6une ita ala dole ya 6ata mata rai yayi mata wayau,ta cikin side mirror ya hangota hakan yasashi d'an lek'o da kanshi suna had'a ido da ita ya saki Dariya ganin yadda ta cika fam kaman zata fashe,Sauran Mutanen dake kallonshi suma basu san lokacin da suka fara yin dariyar ba duk da basu san tak'amaimai dalilin yin dariyar tashi ba kawae ya burgesu ne,Wohoho mai kyau ya huta(Allah sarki,sarar kawayena na sec skul😍),maida kanshi yayi yaja motan ya fuce daga cikin Makarantar.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

4️⃣8️⃣

.......tsallakowa Haulat tayi inda take tsaye ganin tak'i tahowa su tafi aji,

"Mu tafi" tace mata, k'wafa tayi "Wllh Ya Handsome sai yasan ni ya yi ma haka" Murmushi Haulat tayi tace"wai mi yayi maki ne?" tana tura baki ta fara bata labarin rashin cin abincinshi da Hajiya ta fad'i mata da yadda suka yi jiya daya bata Biscuit d'in da sukai break da kuma yadda yau yayi mata wayo ya bata ashe yana da wani, Dariya sosae Haulat ke yi,ita mamaki ma fatun ta bata wannan k'arfin hali har ina,

"To kema in banda abunki ga abunda ya saba ci sai kice lokaci guda sai ya canja ya rink'a cin abunda kike so" a harzuk'e tace"To Wannan biscuit d'in abinci ne,ta ina Mutum zai wani k'oshi da biscuit ", "To ai tunda ya saba cinsu yana k'oshi dasu ne,kinsan kowa da kalar halittarshi akwae Mutane da yawa da basu son cin abinci gara ma shi yana d'an ci kuma duk da ba sosae yake ci ba zaki ga ahakan yana k'oshi halittarsa ce shima haka", ta6e baki tayi "sai yaje yai ta cin su in Ulcer ta kamashi ba shi ya sani ba"daga haka suka iso bakin class d'insu ta shige ita kam Haulat girgiza kai tayi cikin ranta ta ayyana"Fatuu ta cika rigima,ko ina ruwanta da wani cin abincinshi ma"daga haka itama ta shige cikin ajin.

Bayan sun dawo daga Break Malaminsu na lissafi ya shigo,single period gareshi yana cikin yi masu bayani Malamar Basic science dake da Next period tazo ta sanar cewa bazata samu shigowa ba saboda wani uzuri daya taso, don haka in period d'inta tayi su d'aukko darasin da tayi jiya su k'ara karantawa daga haka tayi ma Malamin Maths d'in godiya ta fita,lokacin da period d'inshi ta kar'e maimakon ya fita sai yace masu zaiyi amfani da lokacin Malamar tunda bazata samu shigowa ba yana so su gama topic d'in yau gobe sai kawae su shiga sabon darasi,duk ba haka suka so ba don da har sunji dad'i zasu wataya in ya fita don period din Malamar Double ce,

Tun yana masu bayani suna ganewa har abun ya gundiresu dama kuma mafi akasari ba son lissafin suke ba don ba kowa ke ganewa ba,juyawa Fatuu tayi tana k'arema sauran yan ajin kallo ganin kowa ya tur6une fuska da gani sun gaji yasa ta juyo ta kalli malamin rai a6ace,can taja d'an guntun tsoki a hankali,da sauri Haulat ta kalleta,hannu biyu tasa tayi tagumi ganin Malamin baida niyyar tsayawa da alama duka double periods d'in yake son yin amfani don har ya shiga sabon Darasi,

"Malam gaskiya mun gaji fa" Fatuu ce tayi maganar,a fusace ya juyo don lokacin da tayi Maganar yana cikin yin rubutu a board ne,

"Who said that" ya tambaya, gaba d'aya yan ajin suka yi tsit kamar bada su yake ba, "Wacece tayi wannan Maganar" nan ma shiru kowa yayi suna jin tsoron su nuna Fatun,aikuwa nan take ya harzuk'a cikin tsawa yace"U're Very Stupid!baku ji mi nace bane,ko ku nunata ko kuma ku ja ma kanku ku duka wllh,

"Sir ni ce" Fatuu ta fad'a fuska a d'aure,wani kallo ya bita dashi cike da mamaki ya furta"kece!" kai ta d'aga mashi alamar eh, "Ke mara kunya ko?" turo baki tayi "a'a ba rashin kunya bane,duk mun gajine kuma ko ganewa ma bama yi yanzu,kace so kake ka gama topic d'in gashi har ka fara wani",still yayi yana kallonta da alama ta d'aure mashi kai,can yace"su yan Class d'inne suka ce maki sun gaji kuma basu ganewa?"kai ta d'aga mashi alamar eh, jinjina kai yayi ya kalli sauran yan ajin fuskarshi a murtuke"Class ku kuka ce mata kun gaji baku ganewa?"tsiit suka yi kowa ya kasa tanka mashi saboda sabon Malami ne d'an bautar k'asa ne shima kanshi rawa yake gashi ya cika zafi, tsawa ya daka masu"baku ji mi nike tambayarku bane!"gaba d'aya suka had'a baki wurin cewa "a'a",

Readers Also Read