Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 27

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 27

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 27: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 27. Sauke ajiyar zuciya yayi yace"Let me see d…

4,325 words

Sauke ajiyar zuciya yayi yace"Let me see d Assignment " aikuwa da sauri ta juya gefenta ta d'aukko littafin,mik'a masa tayi bayan ta bud'o daidai inda tambayar take,hannu yakai ya amshi book din, "Wai wannan tambayar za'a fidda kuma ga amsar da yake so asamo nan a k'asa wai in batayi irinta ba to ba'ayi daidai ba",shiru yayi yana kallon Assignment d'in can k'asan mak'oshinshi ya furta" CALCULUS" janye littafin yayi ya kalleta da mamaki"Ajin ki nawa kika ce ma?" da sauri ta bashi amsa"Js 3 nike kuma ban dade dana shiga bama" d'an jinjina kai yayi ya k'ara d'aga littafin yana sake kallon question d'in,yasan lissafin sosae tun yana 100lvl yake yinshi,yana da wahala amman awurin wasu don shi lokacin yana degree d'insa na farko yana koya ma mutane shi sosae wadanda basu ganewa in akayi masu,yayi mamakin ganin tana js 3 an bata shi, dama a Senior Secondary take anayinshi a Further math ga wad'anda suke yin Subject d'in shima kuma wanda ake yi masun introduction ne ba'a nitsa masu can ciki don lissafi ne mai rikitarwa sosae gashi yana da yawa,

"Mi kika yi aka baki wannan Assignment d'in?" ya tambayeta fuska a d'aure,nan ta fara inda inda tana zaro ido ba abun tayi mashi karya ba don ta fahimci ya gane laifi tayi, "Am asking u Zarah!" ya d'an yi mata tsawa aikuwa a rud'e ta fara kora mashi bayani bata 6oye mashi komai ba,tana gama fad'i mashin kwalla suka zubo mata sharrr,shiru yayi baice mata komae ba,a zahiri ta wani 6angaren tana da gaskiya yadda ya rikesu tsawon lokaci dole su gaji kuma dama lissafi in rana tayi ba kowa ke fahimta ba shiyasa mafi akasari aka fi sa period dinshi da safe,ko kuma ana dawowa break kaman yadda tashi take sai kuma ya had'e masu da double periods d'in malama dole ma su gaji ai,matsalan yadda Fatun tayi Maganar dole zaiga tayi mashi rashin kunya,

"Ke kad'ai ne ajin?" haisam ya tambayeta,girgiza mashi kai tayi idanunta sunyi rau rau, "Ke kika fi kowa rashin kunya kenan", da sauri ta k'ara girgiza kan tace"a'a wllh nifa bada niyyar rashin kunya nayi Maganar ba,kawae gaskiya na fad'i mashi don ya sani"shiru yayi yana ta kallonta fuskarshi still a d'aure hakan yasa ta sunnar da kanta k'asa tana ajiyar zuciya, Sigh yayi"as from today,i don't want u to dat again,ba ko ina mutum keda right na ya fad'i abu ba koda yana ganin yana da gaskiya hakan na iya zama ma mutum matsala like it happens to u now,ki koyi yin shiru understand?", da sauri ta d'aga mashi kai"to ya Handsome wllh bazan k'ara ba",jinjina kai yayi yai shiru yana d'an tunanin yadda zai solving mata don lokacin Sallar la'asar ya riga yayi gashi sai dae ya hakuri da zuwa gym don ko zata fahimta sosae har ta yi bayani a aji sai an d'auki d'an lokaci,ana haka aka fara kiran sallar la'asar mik'ewa yayi tsaye yana gyara rigarshi Fatuu ta d'aga kai tana kallonshi,

"Zanje sallah sai na dawo zan nuna maki yadda yake",jin haka yasa lokaci guda ta saki Murmushi,hanyar Bedroom dinshi ya nufa yana shigewa ta hau yin murna tana bubbuga kujeran kaman sabon kamu, bayan wani lokaci ya fito lokacin ta natsu har ta kwanta ma asaman kujeran,tana ganinshi tayi saurin mik'ewa zaune yana zuwa zai wuce yace"ke bazaki sallan bane?"tana kallonshi tace" to ai banda Hijabi" "Kije wurin Hajiya sai kisamu kiyi sallan inna gama zanzo nan" amsawa tayi tare da mik'ewa tabi bayanshi,

_________________

Lokacin data shiga parlon hajiyan ba kowa aciki hakan yasa ta nufi dakin Saude don tasan Hajiyan Salla take,da sallama ta shiga cikin dakin lokacin Sauden na niyyar tada salla,juyowa tayi ta kalli bakin kopan shigowan tana ganin fatuu ta saki Murmushi, "Fateema ce" "Eh Aunty Saude ina yini" "Lafiya lou ya Makaranta an dawo ko", " Eh,Don Allah hijabi zaki ban zanyi salla",amsa mata tayi da to ta nufi wardrobe din bango ta d'aukko mata wata wadda take tunanin bazata yi mata yawa ba sosae ta aje mata agefen Katifarta don fatun ta riga ta shige toilet.

A tare Haisam da Hajiya suka shigo parlon sai kace tare suka je masallacin,yana ganinta ya sakar mata Murmushi ya nufeta,hannunta ya kamo suka nufi kujera 3 seater ya zaunar da ita kafin shima ya zaunan, "Sai yanzu kaga damar shigowa bacin tun d'azu kana gidan nan" yana niyyar bata amsa Fatuu ta shigo cikin parlon ta nufi kujera one seater ta zauna tana yima hajiyar Murmushi, "Ke kuma yaushe kika shigo?" gaidata ta fara yi kafin tace"da aka fara salla", Kai hajiya ta d'aga sai kuma tace"yau baki zuwa islamiyya ne kuma ina kallabinki?"amsa ta biyun ta bata tana tura baki"ban zo dashi ba,kawu Amadu ne zai bugeni shine na taho haka" "Laifi kikai mashi ko" shiru bata ba ta amsa ba hakan yasa Haisam fad'i mata laifin data yi mashi,girgiza kai hajiya tayi"Fateema hoo,baki dai daina rashin ji wllh,Allah ya shiryeki"maida kallonta tayi kan haisam tana yar dariya"kace yau ba zuwa d'aga karfe kenan,yar gidanka ta jawo aiki,Allah ma yasa kai ka iya ai da tasha punishments ja'ira"ta k'arasa idonta akan Fatuu tana dariya itama dariyar tayi tana sunna kai k'asa, "Ko har kayi mata ka fitan?" hajiya ta tambaya jin baice komae ba, "No,we need enough time,zanje Gra after magrib sai inyi acan", kai hajiya ta d'aga"wannan abu dae shima kaman shaye shaye yake ace dole sai mutum yayi zai jishi daidai ya zauna lafiya"wani kallo yayi mata ba tare da yace komae ba, "a zubo maka Abinci ne ko yau ma yar gidan taka tasa kaci Abinci awurin aiki?"da sauri Fatuu ta d'ago ta kalleshi lokacin shima ya d'an kalleta suka had'a ido ta tura mashi baki,d'an murmushin gefen baki yayi ya janye idonshi Hajiya dai nata murmushi,

"Yanzu nagama cin abu,amman zanci bada yawa ba", Saude hajiya ta kwala ma kira,bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abinci,kallon Fatuu tayi tace" ko kema zaki ci?"kai ta d'aga mata alamar eh dama kuma bata wani ci abincin kirki ba, "bi Sauden kice wai ta zubo harda ke acikin nashin sai kuci tare" amsawa tayi da to ta mik'e ta nufi kitchen d'in,shi dae Haisam shiru yayi bai tanka ba dama Hajiyar da biyu tayi hakan wai ko yaci sosae,bayan ta kawo abincin tashi Hajiya tayi ta koma saman 2 seater tace ma Fatun ta zauna sai su saka abincin a tsakiya,yin yadda tace tayi,ganin Haisam d'in idonshi na akan waya ahankali tace"Ya Handsome ga abincin"ba tare daya kalleta ba yace"ki ci" k'in ci tayi ta bishi da ido fuska a daure alamar fushi can ya d'an d'ago ya kalleta ganin yadda tayi yasashi d'an yamutsa baki ya kai hannu ya d'auki spoon d'in ya fara ci,sai lokacin itama ta d'auki nata cokalin ta fara ci,abun mamaki,in yaci sai taci,in ya tsaya sai ta tsaya itama,duk wannan abun hajiya dake kallo na satar kallonsu sosae abun ya bata dariya amman sai tayi kaman ma bata san abunda suke ba,ganin zata 6ata mashi lokaci yasashi aje wayar ya maida hankali kan abincin,ba 6ata lokaci suka kusa cinyewa ya aje spoon d'in tana niyyar ajewa ya wurga mata wata uwar harara hakan yasa ta idasa cinyewa,

Mik'ewa yayi "ki same ni can" yace mata daga haka ya fara k'okarin nufar hanyar fita daga parlon, "Ba za'ayi anan ba nima in koya" Hajiya ce tayi Maganar cike da zolaya, "Yana da d'an yawa we need to do it on board" ya bata amsa yana tafiya,mik'ewa Fatuu tayi tana niyyar d'aukar tray d'in da aka d'auro kayan abincin ta kai kitchen, "Ki barshi za'a d'auke kije ya koya maki yamma na yi" amsawa tayi da to tana niyyar juyawa Hajiya ta kira sunanta,amsawa tayi tare da kallonta,

"Badai zaki daina rashin ji ki natsu ba ko Fateema!" fuska a Matuk'ar d'aure tayi Maganar, nan da nan Fatuu ta rud'e ta nufi gabanta ta duk'a"Don Allah Hajiya kiyi hakuri wllh na daina ko rannan saida Gwaggo ta fad'i hakan yanzu ba ruwana da kowa", "Amman ai har yanzu kina rashin kunya ko tunda gashi kinyi ma kawun ki da Malaminku",idonta cike tabb da kwalla tace" shi Malam wllh bansan rashin kunya bane nayi tunanin gaskiya ce na fad'i mashi amman Ya Handsome ya man fada yace in rinka yin shiru,shi kuma kawu Amadu raina ne ya 6aci da baiyi man ba kuma yana ta yiman fad'a,amman wllh tllh kinji na rantse bazan k'ara ba",sauke ajiyar zuciya tayi"in kika k'aran fa mi zanyi maki?"da sauri tace"komi"jinjina kai tayi tace"tashi kije" mik'ewa tayi tana goge kwallan da suka gangaro mata ahaka ta fita daga parlon.......

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣0️⃣

Lokacin da ta shiga parlon yana zaune saman kujera yana daddana Laptop d'inshi,yana ganin ta shigo ya mik'e, "ki daukko Book d'in" yace mata yayin da ya nufi corridor d'in Bedroom,d'akin da Fatun ta ta6a zuwa yin fitsari ya tura ya shiga itama tabi bayanshi bayan ta dauko littafin da biro,d'akin kaman d'an Computer Lab yake duk IT tools ne aciki gaba d'aya d'akin zagaye yake da Desk,abud'e yabar d'akin ya tokare k'opar da kujera,Desk chair ya jawo ya nuna mata alamar ta zauna ta yadda zata iya kallon d'an madaidaicin whiteboard d'in dake manne a bango,wata drawer dake jikin desk ya jawo,marker ya fiddo ya dawo gaban allon ya fara yin rubutu,abun mamaki tambayar ya rubuta ba tare da ya duba littafin ba kenan har ya haddace tambayar,ak'asan tambayar ya rubuta Solution yaja layi kafin ya fara fidda mata tambayar a nutse yake mata bayani kai kace shi d'in Malami ne gashi ko Calculator bai dubawa da ka yake fidda komae ita dae tayi kasak'e tanata kallon ikon Allah,Abunfa ashe aiki ne ja,ashe sai anyi amfani da wasu formulas da wasu rules an gano wace tsiyace,kai ni dai bama ganewa nike ba balle in ma masu karatu bayani🤣,tambaya guda d'aya amman sai da ya kusa cika allon wai ahakan ma don yayi mata shi atak'aice ne yadda zata gane,lokacin daya fitar da amsar k'arshen kallonta yayi yace ta duba taga tayi iri d'aya da wadda Malamin ya bata, cike da mamaki tace"Kai Ya Handsome, kodae kaima Malami ne?kaga yadda kake yin bayanin wllh har kafi duka malamanmu iyawa ma" goya hannuwansa yayi a k'irji yana kallonta fuskarshi ba wasa yace"is dat what i asked u to do?" da sauri ta girgiza mashi kai ta bud'e littafin daidai inda Assignment d'in yake tana kallon amsar da malamin yace ta samo,d'agowa tayi ta kalli wadda haisam ya gano ta sake kallon ta littafin nata,cike da Al'ajabi ta d'ago tafin hannunta guda rufe da bakinta ta mik'e tsaye,wani tsalle tayi cike da farinciki tace"wllh tllh iri d'aya ne ba bambanci Ya Handsome, kai innalillahi....? "Sosae take washe baki tana dan d'add'aga hannuwa,

"Can u do it?"ya tambayeta, hakan yasa ta tsaya cakk jin yace zata iya yi,zaro ido tayi tana kallonshi ya d'age mata gira alamar amsarta yake jira,a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Baki da baki ne!" "A'a,bazan iya yi ba don ban gane ba sosae" wata uwar harara ya wurga mata"taya zaki gane dama tunda attention d'inki bai anan"ganin kaman ransa ya 6aci yanata kallonta yasa ta duk'ar da kai,

"I will explain it one more time,idan baki maida hankali kika iya ba,ba k'ara maki bayani zanyi ba" ya yi maganar yana jaddada mata abunda yace d'in da marker din hannunshi,hakan yasa ta tattara dukkan natsuwarta guri guda ta goya hannayenta a kirji ta k'ura ma allon ido,su fatuu an natsu kaman duka kenan,goge wanda yayi akan allon yayi ya faro mata daga farko,a nutse yake mata bayanin dalla dalla kuma sau biyu yake fad'i mata abu kafin ya wuce gaba ahaka har ya sake fidda irin amsar da malaminsu ya batan,kallonta yayi yace akwae abunda bata gane ba tace ta gane,hakan yasa yace mata ta taso tayi mashi bayani kaman yadda yayi ba tare daya goge ba,tsayawa yayi ajikin bango ya goya hannayensa akirji yana kallonta ta fara yin bayanin kaman yadda yayi har tazo k'arshe,jinjina kai yayi ya nufi board d'in yasa duster ya goge ya bar iya tambayar daga haka ya nufi kujerar data zauna da farko ya zauna,mik'a mata marker d'in yayi yace ta fidda da kanta har saida gabanta ya d'an fad'i jiki asanyaye ta amshi marker d'in ta koma gaban allon,a d'arare ta fara fiddawa hannunta har Dan kerma yakeyi ganin hakan yasashi kiran sunanta ta waigo yace ta kwantar da hankalinta ta natsu zata iya,jinjina kai tayi ta juya taci gaba da solving a nutse har saida ta wuce rabi sannan ta kakare,tayi tayi ta tuna abunda zatayi agaba ta kasa,jiki a sanyaye kaman zatai kuka ta juyo ta kalleshi ga mamakinta sai taga yayi mata d'an murmushi don ba k'aramin kokari tayi mashi ba data kawo har nan d'in ma,daga inda yake ya tadata taci gaba ahaka yana d'an tada ita in ta kakare har tazo k'arshe,mik'ewa yayi ya amshi marker d'in ya sake yi mata bayani a wawware yadda zata gane sosae har kusan sau ukku yana maimaita mata sake gogewa yayi ya bata tayi shi kuma ya zauna,wannan karon a nutse ta fara fiddawa har ta samo amsar k'arshen,juyowa tayi asanyaye ta kalleshi ya d'aura kafa daya kan daya still hannuwanshi na goye a kirjin sam ta kasa karantar ko tayi daidai daga yanayin fuskarshi,ganin yak'i cewa komae yasa tasha jinin jikinta,

"Banyi daidai ba ko Ya Handsome?" murya na rawa ta tambayeshi,daga yadda yake yace"check your book"da sauri ta nufi saman Desk inda ta aje littafinta ta d'aukko shi ta dawo gaban allon tana duba amsar data samo da wadda Malamin Maths d'in ya bata,sai ta kalli cikin littafin sai ta d'ago ta kalli allon,wata uwar k'ara ta fasa ta daka uban tsalle kai kace zata ta6o ceiling d'in dakin ne,cike da farinciki ta fara fad'in"Wllh iri d'aya ne,nayi daidai...."sai faman tsalle take wutsiyoyin kitsonta na tashi sama suma,sai lokacin ya saki wani k'ayataccen Murmushi ya sauke hannayenshi daga kan kirjin ya d'an had'a tafin hannunshi ya tafa mata sau ukku kafin ya saka yatsun cikin na juna yana ci gaba da kallonta da d'an murmushi,(Jama'a wai Fatuu bata san ta fara girma bane wannan uban tsalle haka,yakamata team Fatuu kuyi mata karatun ta natsu fa😂),cike da murna tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae ta nufi haisam dake zaune yana kallonta,tana zuwa ta d'aga mashi hannu alamar su tafa,d'an bud'a mata ido yayi had'i da dage gira hakan yasa da sauri tasa bayan hannunta ta rufe bakinta,ganin yana mata wani kallo yasa ta sunnar da kai k'asa alamar taji kunya,

"Zarah!" taji ya kira sunanta,koda ta d'ago abun mamaki sai taga ya bud'e mata tafin hannunshi fari kwal dashi,bud'a ido tayi alamar mamaki shi kuma ya d'an lumshe nashi had'i da jinjina mata kai,washe baki tayi ta buda tafin hannunta na dama ta buga a nashin da k'arfi ji kake fasss har saida ya d'an cije baki,tana ganin abunda yayi ta kyalkyace da dariya tace"thank u,God bless u Sweethrt"girgiza kai kawae yayi tare da mikewa, "Ki copying solution d'in Magrib ya kusa" daga haka ya fita daga cikin d'akin,da sauri ta d'aukko littafinta da tuni ya fad'i a k'asa da tana tsalle ta zauna saman kujeran ta fara kwafar rubutun kaman yadda yace mata tana yi tana sakin Murmushi,

Yana fita fridge ya nufa ya daukko bottle water mai sanyi da glass cup ya nufi kujera ya zauna inda ya tashi lokacin da Fatuu ta shigo,tsiyaya ruwan yayi kaman rabin cup d'in kafin ya rufe robar ya kai cup d'in baki ya fara shan ruwan ahankali,yana niyyar aje robar ruwan akan c-table Fatuu ta fito har ta gama kwafar rubutun dama saurin rubutu ne da ita,kan d'aya daga cikin armchairs ta zauna idonta akanshi, "Ko zaki sha ne?" ya tambayeta bayan ya cire cup d'in ta d'aga mashi kai alamar eh, sauran na cikin robar ya mik'o mata ta mike ta kar6o kafin ta dawo ta zauna, "Ki d'aukko cup acikin fridge" girgiza mashi kai tayi"ai shanye shi zanyi bari insha a robar" kai ya gyad'a mata shiru ya biyo baya na d'an wani lokacin, "Wai Ya Handsome kodae kaima malami ne naga ka iya bayani fa sosae"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ganin tana ta binshi da ido yasashi cewa" hakan is part of my work,ina yawan presentation kinsan miye hakan ko?"ya tambayeta idonshi akanta,d'aga mashi kai tayi"eh yima mutane bayani"jinjina kai yayi daga haka ya d'aura kafarsa d'aya akan c-table d'in gabanshi ya d'age kanshi yana facing saman d'akin,duk jinshi ake wani iri ya saba kaman yanzu yana gym,

"Ya Handsome" Fatuu ta kira shi,amsa mata yayi ba tare daya d'ago ba, "In tambayeka?" ta sake cewa,shiru ya d'an yi ya maimaita abunda ta fad'an acikin ranshi,saboda duk in zata tambayeshi kai tsaye take jefo mashi kowacce irin tambaya,daga yadda yake ya d'an juyo da fuskarshi side d'in da take, "Am all ears" ya fad'a, "Wai don Allah da wane irin dutsen goge kaushi kake amfani ne kafanka tayi haka kaman ta jarirai sumul ba kaushi?" ta k'arasa tana nuna kafarshi da ya d'aura saman c-table, kai jama'a ashe tunda ya dauran ta k'ura ma k'afar ido tanata kallonta har ta kasa daurewa saida ta tambaya, shi kuma sam bai gane ma mi take nufi ba,ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata"miye shi abun da kika fad'in?"idanunshi a lumshe ya tambaya, "Dutsen goge kaushin kake nufi?" kai ya d'aga mata alamar eh, "Wannan fa dutsen mai gurjigurji wanda ake sakawa acikin kwandon wanka ana gurje tafin k'afa dashi mai kaushi ko faso"tayi maganar tana kwatanta mashi yadda ake goge k'afan dashi da tafin kafanta da ta d'an d'age sama,still idanunshi alumshe suke ahakan yake kallonta,yanzu ya gane abunda take nufi duk da shi bai san ma dutsen ba, "kina son abunne?"da sauri ta girgiza mashi kai "a'a bani ke so ba Kawu Amadu zan sai ma irin nakan k'ilan ya gyara mashi k'afarshi ta koma kaman taka, wllh baka ga kafarshi bafa, ina...kasan dawon fura in ya kwana,to haka k'afarshi ke komawa cikin sanyi haka zaka ga yanata dirzarta a gefen inda nike yin wanke wanke,har wani k'aton dutsen goge kaushi gwaggo ta siyo mashi a kasuwar yar kutungu yana amfani dashi,kwanaki fa cewa tayi in kafarshi nayin hakan in yayi Amarya zai rinka yaga mata zanin gado"ta k'arasa tana 6a66aka Dariya,d'an bud'e idanun yayi yana kallonta fuskarshi d'auke da dan guntun Murmushin gefen baki, "Shiyasa na tambayekan in ka fad'i man inda ka siyo naka sai in siyo mashi k'ilan ta daina tunda ni dai banso yayi Amarya ya yaga mata zanen gado kuma in ta canja wani taga ya k'ara yaga mata ai kaga tana iya yin yaji ko?" tsakaninta da Allah take yin Maganar😂,

d'ago kan yayi gaba d'aya daga saman bayan kujeran yace mata"bani amfani da abun ina kaita ana wanke man ne" wata zabura tayi ta zaro ido tace "kafan kake kaiwa wanki sai kace kayan wanki!" tayi maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta alamar mamaki,kai ya d'aga mata kafin yayi mata bayanin yadda ake pedicure d'in,cike da Al'ajabi take kallonshi hakan yasa ya d'age mata gira"zaki kaishi arika wanke mashi kafan ko?" a razane tace "wa!ba ruwana wllh,ban shirya zuwa gidan yari ba,haka kawae muje kafan tashi ta lalata masu inji ace sai na biya miliyoyi,ai ma yanzu ta d'an gyaru tunda zafi ake sai sanyi yazo take tsatstsagewan sosae zan dai gaya mashi in yana so to sai yaje amman ba ruwana ni dai" tana Maganar tana d'aga hannuwa sama alamar ba ruwanta,gyad'a kai yayi kawae yana niyyar k'ara kwantar da kan nashi aka fara kwala kiran sallar magrib hakan yasa ya dakata,

"kije gida kiyi salla sai ki kara duba Assignment d'in karki manta ko" kallonshi tayi ta d'an marairaice "to ai yanzu gwaggo bata isa dawowa ba, kuma wllh in na koma kakkarya ni kawu Amadu zaiyi kaman kara dama ya ta6a gota ni a hannu,kofa Gwaggon na nan yana buguna balle yanzu da bata nan"shiru baice komae ba can ya mik'e tsaye yana gyara rigarshi ta daga kai tana kallonshi, "Ki jira in dawo" yace mata ganin bata da kallabi kuma magriba tayi bai kamata ta fita haka ba,da sauri tace mashi toh tana gyara zamanta,Bedroom d'inshi ya nufa yayo alwala,yana fitowa zai wuce tace ya kunna mata kallo,remote ya dauka asaman c-table ya latsa power daga haka ya mik'a mata ya fita.

Ana gama sallan ba 6ata lokaci ya dawo part din nashi,lokacin daya shigo parlon iske Fatuu yayi ta baje a d'ayan 6arin L-shape sai sharar bacci take,(nima inyi ta hajiya ja'ira ta gaji),dama tun agida take jin baccin amman tak'i yi saboda rashin yin Assignment,tsaye yayi tsakiyan falon yana kallonta yayinda ya shiga tunanin yadda zaiyi da ita don fita yake son yi gashi da gani tana enjoying baccin,tunanin ko ya barta yaje ya dawo ya shiga yi sai kuma yayi tunanin za'a iya zuwa nemanta wurin hajiya kuma bata san har yanzu tana wurinshi ba kuma ma is'nt proper taci gaba da zama anan wannan lokacin, yin wannan tunanin yasashi fara kiran sunanta daga nan inda yake atsaye sai dai ko motsi bata yi ba tun yana kiran ahankali har ya d'an k'ara d'aga murya amman ina tuni sanyin Ac yasa tayi nisan kiwo acikin barcin da alama ma bata Nigeria,d'an k'ara matsawa yayi gabanta ya k'ara kiran sunanta nan ma shiru,still yayi da alama baison zuwa kusa da ita ne balle yasa hannu ya tasheta,har zai juya yaga ta motsa zata gyara kwanciya da d'an karfi ya furta"Zarahh"slowly idanunta suka fara bud'ewa suna kuma d'an lumshewa duk alokaci d'aya alamar dae baccin take ji sosae, yana ganin zata juya mashi baya ya sake kiranta wannan karon da k'arfi yace"Zarah!" amsawa tayi tare da bud'e idon sosae cikin Muryar bacci tace"Na'amm",

"Tashi muje na raka ki gida" amsawa tayi da toh ta fara k'okarin tashi zaune idonta akanshi tace"wai bacci nayi?"kai ya daga mata alamar eh, "Wllh bansan ma nayi ba,kallo fa nike yi shine ya sace ni shiyasa ma ake ce mashi 6arawo ashe"da wata irin kasalallar murya take maganar,d'an murmushin gefe yayi yace"tashi muje", "Gidan zaka kaini" kai ya d'aga mata alamar eh, "To amman fa gwaggon bata isa dawowa ba yanzunma kar kawun ya dokeni",

"zamu je sai ki bashi hakuri",da sauri ta jinjina kai ta fara k'okarin tashi tsaye,har zai nufi kopar fita sai kuma ya juya yace mata yana zuwa,Bedroom d'inshi ya nufa bada jimawa ba ya fito lokacin har ta zauna don jikinta ba kwari,hannunshi ruke da wani bakin abu ya nufi inda take,mik'a mata yayi"kisa wannan akan ki" amsa tayi tana dubawa,hula ce skullcap irin mai matse kai,sawa tayi akanta kuma tayi mata da yake roba ce,kallonshi tayi tana da murmushi tace"thank u Sweethrt ya handsome"d'an kya6e baki yayi da Murmushi ya nuna mata hanya alamar su tafi, saida ta d'auki littafinta data aje kan armchair kafin ta wuce yabi bayanta suka fita daga parlon.

Unguwar ko ina da haske da yake akwae wutan nepa,lokacin da suka iso bakin shagon Amadun ba kowa sai sautin waka dake tashi saidae bai k'ure sautin ba ta yadda har zai takura Mutane,Fatuu ce agaba Haisam na bayanta tana zuwan gaban shagon ta tsaya lokacin ya juya baya da alama wani abun yake nema ko zai daukko, "Kawu" Fatuu ta kirashi, aikuwa a fusace ya juyo ya kalleta fuska a tamke yace "kin gama guje gujen naki kin dawo ko,to sai ki shiga ciki zanzo in samek...." bai k'arasa ba sakamakon Haisam da idonshi ya hango mashi a gefen kiosk d'in don da duk bai ganshi ba,washe baki yayi ya fara gaidashi,hannu ya mik'o masa suka gaisa kafin calmly yace"naji laifin da tayi maka bata kyauta ba,but u know she's still a child dat's why take behaving haka sai kana hakuri and she's here to apologize" maida kallonshi yayi kan Fatuu yace"Say sorry to him" tana jin haka da sauri ta kalli Amadun"Kawu pls Sorry,wllh raina ne ya 6aci saboda ba'a fidda Assignment d'in ba shiyasa har bansan lokacin dana fad'i ma abunda nace ba amman don Allah ba don ni ba kayi hakuri bazan k'ara ba" takai Maganar tana girgiza mashi kai,wani kallo yai mata mai kaman harara sai kuma yai saurin sakin fuskar don mugun nauyin Haisam d'in yake ji,d'an Murmushin yak'e yayi mata yace"shikenan ya wuce" Dariya tayi cike da farinciki tace"Nagode kawuna kuma yayana"yar harararta yayi cikin wasa da sauri ta bud'e mashi littafinta tana nuna mashi Assignment d'in da aka fiddan"kawu kagani Ya Handsome ya fidda man shi, ashe ya iya shi sosae baka gani ba" kai ya d'aga fuska asake yace"na tayaki murna",

"Ki shiga gida Zarah" Haisam yace mata,amsawa tayi da to ta rufe littafin kafin ta nufi gidan tana yi mashi bye bye sai lokacin da zata shige ne ya d'an d'aga mata hannun shima,bayan ta tafi ne Amadu ke ce mashi wllh Assignment d'in da aka ba Fatun shi bai ko ta6a ganin shegenshi bama anan Haisam ke mashi bayaninshi yace itama don tayi laifi ne aka bata irinshi,Amadu yace shi dama yayi tunanin hakan wllh,hira yaci gaba da yi ma haisam d'in shi kuma yana tankawa jefi jefi hakan kuma ba k'aramin dadi yayi ma Amadun ba don bai ta6a tunanin ma watarana haisam zai tsaya agaban kiosk d'inshi ba balle har su danyi fira haka,

"Yaya Haisam ko abaka wani abu kad'an ta6a gashi ma kanata tsayuwa"Amadu ya fad'a yana washe baki, "Don't mind,zan tafi ne yanzu", "To kad'an ci wani abu don Allah" yayi Maganar cikin marairaicewa,shiru haisam din yayi,yasan in ya amsa zaiji dad'i don da dad'i kaba mutum abu ya amsa hakan yasa yace ya bashi sweet guda d'aya duk yadda yaso ya k'ara mashi yaki amincewa daga haka yayi mashi sallama ya tafi,yana komawa gida ya fiddo bike dinsa don tafiya gidansu na GRA ko kaya bai canza ba don acan akwae wanda zai iya amfani dasu.

Readers Also Read