Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 30
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 30: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 30. "Tunda kin shigo kin gani ki koma waje ki jirani…
4,105 words
"Tunda kin shigo kin gani ki koma waje ki jirani ina zuwa" amsa mashi tayi da toh tana juyawa daidai wata mace ta shigo wurin dama kopar daya ce tanan kowa ke shigowa sai ya nufi bangarenshi, tana ganin Haisam ta nufo shi tana murmushi, sanye take da tight long sleeve shirt irin rigar nan mai kama jiki mai dogon hannu purple colour kuma bata rufe mata cikinta ba duka sai bak'in wando pant irin dogon wandon nan roba shima mai kama jiki don har shaidar pant d'inta na can ciki ana gani tasa hular gashi baka har tsakiyar bayanta ta d'aure da ribbom purple, kafafunta sanye da kambas farare ba laifi tayi kyau kuma kayan sun fitar mata da shape dinta sosae amman dai da ganinta ba musulma bace,
"Hi zakee" ta fad'a tana ta faman washe mashi baki, kasa kasa ya furta"Anah",kallon Fatuu tayi dake ta faman bin ta da ido tana mata kallon k'urulla tunda ta shigo tayi kafin ta kalli haisam tace "is she ur sis?",kai ya d'aga mata alamar eh, tambayar sunanta tayi yace mata Zarah,jinjina kai tayi ta kalli Fatuu tace "kina lafiya?" mamaki ne ya kama Fatun don bata yi tunanin ta iya hausa ba tace "Lafiya lau", "Gud,tunda kin kawo mana ziyara yakamata kiyi exercise kema" ta fad'a still da fara'a a fuskarta, ita dai Fatuu bata ce mata komae ba, sai ta kalleta sai kuma ta kalli haisam da ta kasa gane yanayin fuskarshi, hannun Fatun ta kamo tace ma Haisam zata je da ita wurinsu don ya samu yayi workout dinshi, "No Anah, she's going now" ya fad'a fuskarshi ba yabo ba fallasa, "Don Allah Ya Handsome ka barni in bita ina son nayi nima" Fatuu ta fad'a kaman zatayi kuka, girgiza mata kai yayi yace ba'a yi da irin kayan jikinta,da sauri tace "to ai sai in nad'e rigar sama" wani kallo ya bita dashi jin wani shirme data fad'a, "Don Allah Ya Handsome ka barni ko irin wannan wanda akeyi mai kaman tafiya ne inje in danyi, wllh dama ina ganin Hajiya Rabi Bawa mai kada na shirin kwana cas'in na hawa irinshi yana burgeni sosae" ta k'arasa tana d'an hade hannu alamar rok'o,
" Tana nufin treadmill kabarta sai in rage mata Speed din k'arshe" Anah ta fad'a,shiru ya danyi kaman bazai ce komai ba da alama nazari yake acikin ranshi, kallon Fatun yayi da ta kafe shi da ido da gani tana Matuk'ar son taje duk tayi kalar tausai, d'an lumshe ido yay yai mata alamar taje, sosae ta saki dariyar farinciki tace mashi ta gode, hannunta Anah d'in ta kama suka nufi bangaren matan bayan Haisam yace mata ta kula da ita sosae don bata ta6a yi ba,
Suna shiga aka fara tambayar Anah wacece ita tace masu sister d'in zakee ce, nan da nan suka shiga d'aga ma Fatuu hannu suna mata welcome don suna yin Haisam, da yawansu sun fada tarkon sun shi sai dae ba fuska, ita kanta Anah din bala'en sonshi take har haisam din ya gane mata don tafi kowa shishshige mashi acikinsu shiyasa bai sakar mata fuska, ita dae Fatuu sai faman binsu take da ido tana ganin yadda suke motsa jikin,Anah da kanta ta tattare ma Fatuu rigar sama dama rigar nada mad'auri ta d'aure mata ita sannan ta cire mata mayafin rigar ta aje shi gefe, dama yar jakarta tunda suka zo ta barta a mota, wurin wani treadmill da bakowa ta nufa da ita, saida ta fara hawa ta nuna mata yadda ake amfani dashi ta tabbatar ta gane sannan tace ta hau bayan ta rage gudunshi karshe yadda zata yi kaman tana tafiya a hankali, sosae Fatuu ke sakin Murmushi tana tayi dad'i duk ya kamata abunda take gani a tv anayi yau gashi itama ta hau tanayi, kallon Anah tayi dake gefenta tace ta d'an k'ara mata gudunshi,ganin tana yi ba wata matsala yasa ta k'ara mata gudun kad'an,tana cikin yi aka kira Anah din waya tace ma Fatuu zata yi waya kar ta ta6a komae ta amsa mata da to, dan matsawa kad'an tayi tai picking call d'in saidai bata ji sosae saboda k'arar kid'an dake tashi a wurin hakan yasa ta nufi can bakin kopar shigowa wurin taci gaba da yin wayar, Fatuu na cikin yi hankalinta ya tafi kan wasu tanata kallon yadda wasu ke yin nasu har bata san ta d'aura hannunta kan malatsin dake d'auke da alamar + ba, wato k'ara gudu saidai taji gudun ya k'aru hakan yasa ta rud'e ta daddafe kan abun ashe tanata k'ara gudunne bata sani ba,lokaci guda ta rud'e ta kidime ta gigice gaba d'aya taga duniyar na juya mata hakan yasa ta saki wata gigitacciyar k'ara ta kwala ma Haisam kira "YA HANDSOME.......!!!" duk tabi ta daddafe kan machine d'in sai falla uban gudu take,k'arar data saki ce ta jawo hankalin Mutane kanta harda masu sanye da earpiece saida suka ji don ba k'aramar k'ara tayi ba, a gigice Anah ta saki wayar ta nufo ciki da gudu sai dai ko kafin ta kai wurin wata wadda ke kusa da fatun tayi kukan kura ta kai ma fatun d'auki cikin zafin nama ta kasheshi, Anah na isowa wurin fatun tayi baya luuu zata fad'i kasa da sauri ta tarbota ta riketa gam adaidai lokacin kuma Haisam ya fado cikin wurin don yana jin k'arar yasan Fatun ce, akasan wurin ta kwantar da ita tanata faman girgizata sai dai ko motsi bata yi ba hakan kuma ba k'aramin tada mata hankali yayi ba har ta fara zubda kwalla,
" Zarah, Can u hear me? Open ur eyes please!" haka Anar keta fad'i tana ci gaba da zubar da kwalla, shidai Haisam tsaye yayi yana kallon Fatuu dake yashe a k'asa bata motsi,tsananin tashin hankali ne yake ciki sai dai ba lalle ka gane hakan ba, yama kasa yin tunanin takamaimai abun yi gashi duk matan sunyi mata rumfa hakan ne yasa bai k'arasa wurin Fatun ba,ko wurin ma don baida zabi ne dole tasa ya shigo saboda maza basa shigowa, a hankali ya matsa kusa dasu yace su d'an matsa duk suka dare ya kasance yana kallon fuskar Fatun, dagowa yay ya tambayi ko akwae ruwa awurin da sauri wasu suka amsa da eh don duk basu yi tunanin ma su samata ruwan ba, bayan wata ta kawo bottle water Haisam d'in ya amsa ya duk'a gaban Fatun ya zuba ruwan ahannunshi dama a bud'e aka bashi robar, yayyafa mata a fuska yayi nan da nan taja wani dogon numfashi don ruwan nada dan sanyi,
"Zarah" haisam din ya kirata, a hankali idonta ya fara motsi,Anah na ganin haka ta ci gaba da kiranta tana cewa ta bud'e idonta, bud'e idon ta fara yi tanayi tana lumshe su, "Zarah look at me" haisam ya fad'a, a hankali ta d'an ware idon akanshi, kura mashi ido tayi kamar bata sanshi ba can kuma sai ta fashe da kuka tana wani dashe baki dama haka take kukanta kamar yar k'aramar yarinya, Sai lokacin ya kalli Anah fuska a d'aure yace "how does it happened?" baki na rawa ga kwalla a fuskarta ta kora mashi bayani, tana kaiwa karshe yay ma Fatun wani kallo hakan yasa cikin sheshsheka ta fara mashi bayanin yadda abun ya faru "Wllh Ya Handsome bani na k'ara gudun ba, bansan na d'aura hannuna kan abun k'ara gudun ba, da naga gudun na karuwa shine na rurruke kan abun ashe na k'ara latseshi ban sani ba" shiru yayi don yama rasa abunda zaice,wad'anda suka ji abunda tace sai faman yi mata sannu suke yayin da wad'anda basa jin hausa suka shiga tambayar abunda tace aka fad'a masu suma suka shiga ce mata sorry,
"Zan sha ruwa" ta fad'a da disashshiyar murya, sauran ruwan dake hannunshi ya mik'a mata Anah ta d'an d'ago kanta ta kafa baki saida ta shanye shi tas tasa hannu ta cire robar daga bakinta Anah ta amshi robar ta aje gefe guda, "Zaki iya tashi" haisam ya tambayeta, d'aga mashi kai tayi alamar eh ta fara k'okarin mikewa tsaye da taimakon Anah shima ya mik'e tsaye,hannu Anah takai ta kwance mata rigarta ta d'aukko mayafinta ta yafa mata tana k'ok'arin kama hannunta Haisam yace ta bashshi, kallon Fatuu yayi yace suje ta fara tafiya ahankali tana jan k'afa matan wurin na k'ara yi mata sannu, ita kam Anah tayi tsaye sototo duk ta d'aura ma kanta laifin faruwar hakan gashi ma taga haisam d'in kamar yayi fushi, tai tsaye tana kallonsu har suka fita daga wurin, a hankali take taka matattakalar benen hannunta dafe da bango haisam d'in na bayanta, haushi yaji shiyasa yace Anah ta kyaleta don tun farko shi dama baiso fatun taje wurinba jin tace zata kula da ita ne yasa ya bari dama kuma ita taja hankalin fatun har tasa ran zuwa wurin, suna fitowa waje Fatun ta duk'e don tunda ta saukko daga kan benen taji amai na tuk'arta,
"Lafiya Zarah?" haisam dake gefenta ya tambaya, "Amai nake ji " ta bashi amsa, "Ok ki d'aure ki matsa can kada kiyi masu amai nan",tashi tayi tana daddafe cinyoyinta ta nufi can gefe guda ta duk'a shi kuma yana bayanta bai kallon fuskarta don arayuwarshi ya tsani amai ko kusa da mai yinshi bai zuwa don yanzu zuciyarshi ta tashi shima yaji aman,kuma in har hakan ta faru ba k'aramar wahala yake sha ba don ba k'aramin abu ne ke sashi amai ba, shiru aman yak'i zubowa hakan yasa ta mik'e ta juyo, Haisam ya tambaye ta ya akai, tace bai zubo ba yace mata su tafi to, wurin da yayi parking d'in motarshi ya nufa suna zuwa bakin motar Fatuu tace" Ya Handsome ina zamu?"
"Daga ina muka zo?" shima ya tambayeta, "Daga gida" ta fad'a tana yin nishi, yace to can zamu, da sauri tace "Don Allah Ya Handsome kar mu koma gida yanzu, wllh in gwaggo taji abunda ya faru har buguna tana iya yi dama saida ta gargad'eni kan kar inyi wani abu ba daidai ba, yanzu ko na fad'i mata yadda abun ya faru ba lalle ta yarda ba" da ganin yadda take yin Maganar tana d'an jin jiki, shiru yayi yana nazarin maganarta don shi kanshi bazai so ya maida ita gida haka ba don kallo d'aya za'ai mata a fahimce wani abu ya faru da ita, Allah ma ya tak'aita abun don irin wannan har zuciyar mutum sai ta buga saboda firgici,
" To ya kike so ayi" ya tambaya idonshi akanta, " Mu koma inda ka fara kaini naga akwae kujerun siminti sai in d'an k'ara hutawa yanzu juwa nike gani" jinjina kai yayi yace suje can d'in, a daddafe suka isa wurin masu tsaron gate d'in wurin nata tambayar miya sameta ganin lafiya lou ta fita bayan ta gama yi masu masifa, Haisam yace masu ta fad'i ne suka shiga yi mata Allah ya kyauta, wani ticket ya siya masu kafin suka shiga ciki, a gefe gefen cikin wurin dogayen kujerun suke,nufar guda sukai yace mata ta zauna zaije ya dawo, bayan ya tafi tabi wurin da kallo wai ko zata ga abokanta da tayi saidai duk babu su sun tafi dama sun rigata zuwa wurin, bai jima ba ya dawo hannunshi ruke da robar ice cream da bottle water tana zaune ta d'age kanta saman bayan kujerar,zaunawa yayi gefenta ya kira sunanta ta d'ago tana kallonshi, ice cream d'in ya mik'a mata ta girgiza mashi kai da sauri alamar bazata sha ba, shiru yayi yana kallonta don hakan ya tabbatar mashi batajin dad'i sosae tunda har tai rejecting ice cream saboda yasan tana sonshi ne ma ya siyo mata,
"Zan sha ruwa" ta fad'a, bud'e mata yayi ya mika mata, ta kafa baki ta shiga kwankwad'a har saida yace kar yasata amai sannan ta daina sha, amsar robar yay ya rufe ya aje su agefenshi harda ice cream din,shiru sukai na d'an wani lokaci ya jingina bayanshi da jikin kujeran yana kallon yadda yara keta wasa, ba zato ba tsammani yaji Fatuu ta kwantar da kanta saman kafadarshi, d'an juyo da fuskarshi yayi ya kalleta sai kuma ya d'ago yaci gaba da kallon yaran, a hankali ta rinka shakar daddadan turaren jikinshi mai sanyin kamshi da yaketa kaima hancinta ziyara, nan take kuma tashin zuciyar da take ji ya fara raguwa ta fara lumshe ido, bayan wasu mintuna Haisam ya fara tunanin ko dai ya kaita asibiti don ya fara gajiya da zaman hakan yasa ya kira sunanta don yaji ya take ji yanzu, jin shiru bata amsa bane yasa ya k'ara kiran nata still shiru bata amsa ba, d'an juyawa yayi ya kalleta sai dae bai iya ganin fuskarta don ta d'an dukar da ita kasa, dago fuskarshi yay yaci gaba da kallon wurin can kuma sai ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake gefenshi, camera din wayar ya shiga ya maida camerar ta gaba ya kaita saitin fuskar Fatuu, nan take ya saki d'an Murmushi ganin yadda taketa bacci abunta numfashinta na fita a hankali ga gashin idonta yai wani irin tsawo da tana baccin, janye wayar yayi ya fita daga camera d'in ya ajeta agefenshi, gyara zamanshi yay ya d'an zamo kafin ya kai hannun damanshi ya gyara mata kan nata yadda zai kwanta kan kafad'ar sosae,almost 30mins ta d'auka tana yin baccin kafin ta fara motsa kanta lokacin yanata latsa wayarshi, kallonta yay ya kira sunanta don dama ko bata tashi ba yana niyyar tadata saboda Magrib ta gabato wurin ma duk an yaye sauran mutane kadan, "Zarah how are u feeling now?" ya tambaya bayan ta amsa kiranta da yayi, d'ago kanta tayi daga kan kafadarshi tana kallonshi shima ita yake kallo ya dage mata gira alamar uhhuym, "Na daina jin juwar, aman ma ya koma" ta fad'a da sanyayyar murya, jinjina kai yayi ya juya,
"Ya Handsome..." yaji ta kirashi, juyawa yayi ya kalleta ba tare daya amsa ba, "Don Allah kayi hakuri naja baka yi abunka ba, wllh ni bansan na ta6a wurin ba" shiru bai ce komai ba yana dai ta kallonta acan kasan zuciyarshi kuma mamakin yadda tayi mashi Maganar yake, ba yau ta fara bashi hakuri ba sai dai ba anutse kaman yanzu ba, "Kayi hakuri" ta kara fad'a ganin baice komai ba, jinjina kanshi yayi "it's ok", " To zaka kara fitowa dani?" ta dan bud'a ido, Murmushin gefen baki yayi sai yanzu ya gano dalilin natsuwar, "Ki tashi muje magrib yayi" yayi maganar yana kokarin tashi, da sauri ta kai hannu ta kama hannunshi tace "bakai man hotunan ba" yar harara ya wurga mata, wato ta samu har Maganar pics take, fasa mik'ewar yayi dama wayar na ahannunshi, camera ya shiga ya juya zai mata hoton amman sai ta d'aga mashi hannu alamar ya tsaya,tace "To ai da fa nida abokai na zaka yi man yanzu kuma basu nan sun tafi sai kayi mana tare ni da kai" ba tare daya ce komae ba ya maida camerar ta gaba yayi mata alamar ta lek'o kawai sai ji yayi ta dafe kafadarshi, ta cikin camera d'in yayi mata wani kallo hakan yasa da sauri ta cire hannun tana d'an murmushin da ba har Zuciya take yinshi ba tana d'an kallonshi, alamar ta maida hannun yayi mata da kanshi, a sanyaye ta d'an dafa shi yayi masu hoton, ya d'auku sosae saidai ba wanda yayi dariya,sake shiga camerar yayi kafin ya d'auka yace "baki iya dariya bane" jin hakan yasa tayi dariya duk dimples dinta suka lotsa, yana shirin sake d'auka itama tace "to kaima baka iya dariya bane" jin Maganar tata yasashi yin d'an murmushin da bai shirya ba, tana ganin hakan da sauri tace "yauwa to kar ka daina yi" ta k'ara dafeshi sosae ta d'an kwantar da kanta tana k'ara yin irin dariyar da tayi daga haka ya dauka, lokacin da ya bud'e hoton har wata yar k'ara fatuu tayi don murna saboda hoton ya matukar yin kyau gashi ya d'auku tar tar dashi, ita tayi dariya shi kuma murmushi gaba daya dimples dinsu ya fito sosae, kitson fatun na gaba daya zubo gefe da gefe yasa tayi kyau sosae dama tunda ta gigice har ta suma ya warwaro daga daureshin da gwaggo tasa tayi, (Nima dae saida na leka hoton, Ma Sha Allah shine abunda nace kuma masu karatu duk wanda ya kalla yace Ma sha Allah kar a lashe masu kyau 🤪)
"Ya Handsome bari in hau lilo ka dauke ni hoton" tana fad'in hakan ya mik'e yace"Next time" daga haka yace ta daukko ice cream da robar sauran ruwan da ta rage suka fita daga wurin.
(Uhmmm Allah ya kyauta gaba to, ni dama jinina kan akaifa yake game da wannan zuwa Gym din, team Fatuu ina mik'o sakon jaje su Fatuu anga bala'e harda su suma😹)
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣4️⃣
......Suna niyyar shiga mota Anah ta fito tana rataye da jakarta, nufo su tayi fuskarta a kwa6e ba walwala, agaban Haisam ta tsaya yana ganinta ya dakata don har ya bud'e kopar Mota, a sanyaye ta fara Magana, "Am so sorry Zakee about what happened, i know it's all my fault but it was a mistake" ta k'arasa idonta cike da hawaye, Sigh yayi a tausashe don yaga hankalinta ya tashi sosae yace " it's ok Anah, just let it be past " d'an guntun Murmushi tayi tace "thank u" kai ya d'aga mata kawai ta nufi inda Fatuu take tsaye ta dafa kafad'arta, " Zarah ina fata kina lafiya?" jinjina mata kai tayi alamar eh,, " akwae abunda ke maki ciwo yanzu?" girgiza mata kai tayi alamar babu,
"Am sorry kinji, ki hakuri pls" ta fad'a a marairaice, Murmushi Fatuu tayi mata hadi da d'aga kai, maida idonta tayi kan Haisam tace mashi sai gobe, kai ya d'aga mata ta wuce wurin da ake aje mashina don mashin take hawa roba roba, har ta d'anyi nisa Fatuu ta kwala mata kira " Aunty Anah", juyowa tayi ta kalleta Fatun tace " zan k'ara dawowa ki koya man wani kala", zaro ido tayi sosae jin abunda fatun tace hakan yasata kyalkyacewa da dariya, itama Anar dariyar tayi ta girgiza kai daga haka ta juya ta tafi, shiga cikin motar tayi donshi tuni ya shige ya jata suka bar wurin,
saida ya tsaya yayi mata siyayyar kayan kwalama yayi sallar Magrib a wani Masallaci sannan suka wuce, A bakin kopar gidansu ya tsaya da motar Fatuu ta fito shima ya fito ya zagayo bangaren da take, kopar baya ya bud'e ya fiddo ledojin siyayyar da yayi mata harda ta littattafan, Amadu na hango su ya fito ya nufo su, gaida haisam yayi ya amsa kafin yace ya tayata shiga dasu ya amsa da to,bayan ya tafi Fatuu ta kalleshi tana Murmushi tace "Nagode Sweetheart", wani kallo yayi mata ta kyalkyace da dariya, tana ganin zai juya tace "Don Allah Ya Handsome karka fad'i ma Hajiya abunda ya faru fa", d'an juyawa yayi ya kalleta sai kuma ya d'aga mata kai alamar to, har zai shiga cikin motar ya dakata ganin tayi tsaye bata shiga gida ba yace "ki shiga kiyi sallah sai ki kwanta, in kinyi bacci sosae u wll feel much better" kai ta d'aga ta kai hannu ta d'auki ledar data rage, ganin zaija motar yasa ta d'aga hannu tana mashi bye bye yay mata horn daga haka yaja motar,
Washe gari Friday bayan ya ajesu a Makaranta ya bata wata envelope yace in ta kaima malamin nasu littattafan ta bashi, lokacin da ta kaima Auncle Bash sak'on Haisam d'in da mamaki ya bude, kudi ne ya gani a ciki yan dubu duba har saida gabanshi ya fad'i, kallon fatuu yayi ya tambayeta ta tabbatar shi akace taba tace mashi eh, sosae ya jinjina abun kafin yace in tasan lambar wayarshi ta bashi tace batasani ba, ba haka yaso ba eson gobe ba makaranta balle yayi mashi godiya, mik'a mashi littattafan da aka siyo Fatuu tayi ya amsa yace sai zuwa Monday za'a fara mata amfani dasu amman duk da haka saida ya bata wani English Grammar ya nuna mata inda yake so ta duba cikin weekend, kamar yadda Haisam yace mata tayi da abubuwan da ya siya mata da yawa hakan tayi, ta babba wasu wanda basu dashi harda ma wad'anda suna dasu ta k'ara masu hakan ba k'aramin mutunci da girma ya siya mata ba, Haulat ma ta d'ibar mata duk abubuwan dasu Calculator d'in da yace ta bata sosae tai farinciki tanata gode masu su duka har Fatuu nace mata ai itace silar komae da ta bata shawarar zuwa bashi hakuri, ita dai Haulat d'in d'an Murmushi kawai tayi tace dama Allah ya rubuta hakan.
A cikin wani satin daya kama Haisam ya siya ma Tk sabon mashin d'in daya tura mashi sakon yana so kaman yadda sukai dashi duk da dak'yar yayi k'arfin hali ya tura mashi Message d'in don bukatar tashi yana ganin babba ce don mashin din yayi wurin dubu dari biyar, sosae Tk yay farinciki har ya kasa 6oyewa ba kamar da ya kasance shima zai biya ma kaninshi bukatarshi na mashin d'inshi da yaketa so ya bashi, sam Haisam bai bashi damar yi mashi wata doguwar godiya ba, bai 6oye ma Hajiya komae ba yay mata bayanin yadda akai Haisam ya siya mashi mashin din, batace komai ba sai murna ma da ta tayashi don tasan halin tk yana da kawaici kan abu irin hakan sam baida zari, tambayarshi ma tayi yadda zai aika ma kaninshi da nashin yace mata akwae wasu yan garinsu dake zuwa cin kasuwa nan to da babbar mota mai bud'addan baya suke zuwa su zai ba su kai mashi tace hakan yayi.
A cikin satin kuma aka sako su Gaye bayan anyi tsatstsauran rubutun cewa za'a saka masu idanu in aka k'ara kama kowannansu ya aikata ko k'ara yunkurin aikata laifi makamancin wannan to za'a tado wannan ahad'a ayi masa hukunci, daka kallesu zaka fahimci sunji jiki ba laifi duk sun k'ara yin bak'i sun jeme ga wata uwar rama (ba tuwon gyatuma), gaye har wasu kuraje suka fito mashi banda uban cizon sauron dake kan fatarshi, A daren ranar da aka sakosu mahaifinsa Malam tanimu ya tasa shi gaba suka je gidan Hajiya don yi mata godiya, sosae ya shiga yi mata godiya hajiya tace ba wani abu ai d'a na kowa ne, yace in ba damuwa yana son ganin Haisam, Hajiyar na niyyar kiransa awaya sai gashi ya shigo cikin parlon don lokacin ba'a dad'e da gama sallar isha ba, sosae malam tanimu yayi mashi godiya shima had'i da sama rayuwarshi da iyayenshi Albarka, yayi masa Addu'oi sosae kafin yace ma Gaye dake ta faman sussunar da kai tunda Haisam d'in ya shigo yayi mashi godiya, kallonshi ya d'anyi cike da jin kunya yay mashi godiya, sai lokacin ya bud'e baki yay Magana dama shi baison ayi tayi mashi godiya shiyasa koda Malam tanimu nayi saidae ya jinjina mashi kai in kuma Addu'a ce can kasan makoshi yake amsawa da Amin, yar nasiha yayi ma gaye ya nuna mashi yana da damar da zai gyara rayuwarshi a yanzu tun kafin lokaci ya k'ure mashi don a rayuwa komae yana da limit idan lokaci ya k'ure mashi koda ya gyara hakan bazai amfaneshi da komae ba, bayan ya gama ya kalli Mahaifinshi yace idan ya gyara halinshi ya natsu zai d'auki nauyin karatunshi in yana son yi, in kuma kasuwanci yake so to zai bashi isasshen jari, sosae Malam tanimu yaji dadin wannan Maganar don harda yar kwalla yayi ya kalli gaye yace mashi yaji dai da kunnanshi wannan dama ce agare shi, bayan ya gama yi mashi magana Hajiya ta tambayeshi yanzu Jos d'in zai kaishi yace ehh, duk da Ashirun yace mashi wai ya bari amman yasan in ya kyaleshi ruwa zai koma saboda gurbatattun abokai don haka gobe in Allah ya kaimu zasu tafi zuwa wani lokaci in yaga ya gyara halin da gaske sai ya maido shi nan, Hajiya tace hakan yayi, da zasu tafi ta basu kud'i masu yawa tace su sha ruwa a hanya Allah ya kiyaye bayan itama tayi ma gayen nasiha, Bawan Allah harda yar kwallarshi yace in sha Allahu zai yi amfani da nasihar da suka mashi zai dage don ganin ya gyara rayuwarshi daga haka suka yi masu sallama suka tafi,
(Allah sarki Gaye inayi maka fatan Alkhairi, Allah ya baka ikon gyara rayuwarka ya shiryi duk masu irin halinka ya shirya Al'ummar Annabi(SAw) gaba d'aya Amin, nasan masu karatu ma nayi maka fatan Alkhairi don ka taka muhimmiyar rawa a labarinnan muna godiya)