Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 39
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 39: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 39. Tana zuwa gaban Haisam ta tsaya tana mashi Murmushi…
4,435 words
Tana zuwa gaban Haisam ta tsaya tana mashi Murmushi hakan yasashi dakatawa yana kallonta fuska a sake, hannu ta kai ta kama trolley d'in tace "Kawo na ja Ya handsome" sakar mata yay batare daya ce komae ba suka nufi parking space d'in, "Ya Handsome yaushe zaka dawo?" ta tambaya had'i da d'an kallonshi, "I won't stay long" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba, "Tk zai kai ki duk inda kike so" taji ya k'ara fad'a, kai ta d'aga mashi alamar to sai kuma tace "in ina son yin waya da kai fa?" "Ba Auncle d'inki nada phone no dina ba, ki amfani da wayanshi" turo baki tay "to ai shi wani lokacin sai yayi man wulakanci yake bani wayarshi" "Grandma dinki fa batada waya ne?" "Tana da ita amman yar k'arama ce ni kuma so nike muyi Vedio call don in nuna maka sauran gayun salla na" sai lokacin ya juyo ya kalleta suka had'a ido wai kuma sai tasa tafin hannunta wanda bada shi ta ruk'e trolley d'in ba ta rufe idanunta alamar kunya, d'an Murmushi yay kafin ya juya yana fad'in "in kinyi gayun ask Tk to call me" bud'e idon tay tace to lokacin kuma suka k'araso parking space d'in, amsar trolley d'in Abbas yay ya bud'e boot d'in Motar ya saka alokacin Hajiya da Saude suma suka k'araso wurin, k'ara gaidata sukai duk da dama da suka zo sunje har part d'inta sunyi mata barka da sallah, "Wai ina Tukur ne" Hajiya ta fad'a idonta akan Saude kafin ta bata amsa sai gashi ya taho daga baya yana k'arasowa ta bashi umarnin saka kayayyakin cikin Jeep dinta,
"Yar Bafullatana zaki raka Yayanki ko?" fatuu dake tsaye taji an fad'a a gefenta hakan yasa da sauri ta waiga ta kalli wurin Najeeb ne zaune a back seat na Jeep d'in Saleem kafarshi guda awaje, Murmushi ta d'anyi mashi kafin tace wani abu Abbas dake a kusa dashi yace "ai dole ta raka Ya handsome d'inta ko?" jinjina mashi kai tay alamar eh,
"Fateema taho to ki shiga mutafi kar mu makara jirgi bai jira, in kuka raka mu sai ku sauke Saude a tasha" Hajiya ce tai Maganar tana mik'o ma Fatuu hannu, shiga gaban Motar tayi Hajiya da Saude na a baya sai Tk da zai tuk'a daga haka ya fito da ita cikin harabar lokacin suma su haisam Jeep dinsu ta fito shida Saleem ne agaba sai Najeeb da Abbas a baya, Motarsu ta fara nufar gate da aka zuge masu suka fice sai ta Hajiya ta rufa masu baya bayan ta tsaya sun k'ara yin bankwana dasu Officer ita da Saude dama ita Gwaggo tun kafin su fito ta kirata tayi mata sallama har tana cewa bari tazo tayi masu rakiya tace tayi zamanta taji da bak'in Salla.
A sauka lafiya Hajiyar Sanata 🛫.
Duk ranta ba dad'i suka baro Airport d'in, su Abbas sun wuce su kuma suka nufi tasha don sauke Saude, suna zuwa ba 6ata lokaci ta samu mota sukai mata sallama daga nan Tk ya bazama dasu cikin gari, yawo sosae yay da ita don har gidan abokansa ma Makaranta ya kakkaita harda gidansu budurwarshi, sosae Fatuu ta samu barka da sallah don har jakarta ta cika da kud'i ga kayan kwalama da aka babbata iri iri ba kamar agidansu budurwar Tk d'in, basu suka dawo gida ba sai da akai Magrib lokacin tuni su Haisam sun sauka Abuja don har tayi waya dashi, lokacin data dawo gida ta nuna ma gwaggo kud'ad'en data samu sosae ta girgiza da ganin uban kudin ta hau tambayar a ina ta samu kudi haka nan ta kwashe duk inda ta samun ta fada mata harda wanda abokan Haisam suka bata karshe dae gwaggon taba kudin bayan ta ciri yan kad'an wanda zata ruke gwaggo kuma tai mata fadan banda rokon Mutane kudi ta rantse mata kan bata rokon kowa kuma in aka bata ma sai tace abarshi in aka matsa ne take amsa, tsakar gida ta baje tanata cin abubuwan data samo tanata zuba surutu gwaggo nace mata ta bi ahankali da ciye ciyen nan, karshe saida gwaggon tace in cikinta ya lalace ai taga yadda za'ai tayi yawon sallan sannan ta lafa da ciye ciyen don ta gaya mata Ya Handsome yasa Tk ya kaita duk inda take so.
Washe gari tun 9 ta shirya cikin riga da skirt na lace dinta, tayi kyau har ta gaji kuma suma sun kamata sosae hakan yasa koda ta gama shiryawa bata shiga dakin gwaggo ba tai ficewarta dama kuma bacci take, gidan Hajiya ta nufa bayan sun gaisa da Officer dake zaune shi kadai yana ta yabon gayun data yi, ce mashi tay wurin tk tazo zasuje kallon hawan bariki yace ta shiga ta duba in ya tashi, tana shiga ta nufi Bq can bayan part d'in Hajiya don acan yake da zama, koda taje kopar dakin nashi a rufe take hakan yasa ta hau kwankwasawa shiru ba'a bud'eba har saida ta k'ara sautin bugun sannan taji muryarshi yana tambayar waye, ce mashi tay itace sannan yazo ya bud'e da ka kalleshi kasan daga bacci yake, yana ganin Fatun ya d'an buda idanunshi cikin muryar bacci yace " ya mukai dake jiya, ba sae goma nace zamu fita ba?" gaidashi tay tana tura baki tace " to ai goman ya kusa ko tunda yanzu tara fa ta wuce ba sai ka tashi ka shirya ba" d'an jujjuya kanshi yay alamar baccin bai isheshi ba, "Kije to in nagama shiryawa zanzo" "To ka kira man Ya handsome" amsa mata da ok yayi kafin ya juya cikin d'akin, hannunshi ruk'e da wayarshi ya dawo bakin kopar ya fara kokarin kira mata Haisam din, "Vedio call zaka kira shi" ta fad'a cike da zumud'i, "No bari dae in kirashi in ya d'auka sai kice ya kira ki Vedio d'in don bamma tunanin ya tashi bacci yanzu" sau biyu ya kira ba'a d'aga ba hakan yasa yace mata gaskiya bai tashi bacci ba amman tace wai a k'ara kira har ya tashi jin hakan yasashi bata wayar yace taje ta kira da kanta in ya fito zai amsa cike da murna tace to, gida ta koma ta shige d'aki tana ta kira dama tun kan hanya take kira bai d'aga ba sai can yai picking call d'in lokacin tana zaune gefen gadonta, da sauri ta kara wayar a kunne ko sallam bata yi ba ta kira sunanshi,
"Ya handsome " shiru bai amsa ba har saida ta k'ara kira sannan cikin murya mai tattare da bacci ya fara Magana "Zarah hope u'r ok" maimakon ta bashi amsa sai cewa tay "tun d'azun nike kiranka amman kaki ka daga", "Wayan yana vibrate ne, any problem?" "A'a dama kwalliyata ta yau zan nuna maka ka maida Vedio call kaga uban gayun dana yi", ba tare daya k'ara cewa komae ba ya shiga maida kiran Vedio, yana kwance akan wani katafaren gado ya lullube rabin jikinshi da wani lallausan katon bargo blue don yanayin weather d'in can akwae d'an sanyi saboda samun ruwa da suke ba kamar Katsina ba gashi ya saba da Ac indae ba sanyi yayi tsanani sosae ba to bai zama ba tare da ya kunnata ba, Fatuu na ganinshi ta waro ido had'i da washe baki tana mashi dariya shima Murmushi yake mata yana daga kwance kanshi saman farin pillow haka rigar jikinshi kimono robe ce fara sol, "Ya Handsome wannan gadon kane?" kai kawae ya d'aga mata alamar eh, "To ina Hajiya da sauran yan gidanku,?" lumshe ido yay kaman bazai bata amsa ba da gani still da sauran bacci a idonshi a hankali kuma ya ware idon slowly yace "suna apartment nasu" "Kenan anan ma bangarenka dabanne?" kai ya d'aga mata alamar eh, "da an shigo bangaren naka yake kaman gidan Hajiya?" kai ya girgiza mata kafin cikin muryar bacci ya furta "Upstairs", zaro ido tay da mamaki tace "kai, gidanku na nan Abuja kenan benene tunda kace a Saman bene kake" kai ya sake d'aga mata ya fara kokarin tashi zaune don wani irin bacci ne ke fuzgar shi gashi sam baijin dad'in Vedio call d'in a waya don yafi sabawa da yayi a laptop, jingina bayanshi yay da kan gadon ya ruk'e wayar kan cinyoyinshi dake lullu6e da bargo, yana tashi zaunen da mamaki Fatuu ta kira sunanshi "Ya Handsome" bud'a mata ido yay ba tare daya amsa ba, "Ashe yadda kake da gashi a hannunka har anan ma kake dashi" cike da al'ajabi tay Maganar tana nuna kirjinta alamar inda take magana akai, a hankali ya d'an duk'ar da kanshi ya kalli kirjin nashi dake abude sakamakon rigar dake jikinshi haka take bata rufe kirji in ba'a sa wata a ciki ba ga gashin nan liya liya a kwance saidae baida yawa sosae don yana rageshi, d'agowa yay ya kalleta ganin ta kafe wurin da ido tanata kallo yasashi kai hannu ya idasa jawo bargon sama, kallon fuskarshi tay suka had'a ido don kar ta sake yin Magana kan gashin yasashi cewa "kince zanga kwalliyanki" da sauri tace eh tare da saukkowa daga kan gado ta mik'e tsaye tun daga kan k'afafunta ta fara nuna mashi har saman fuskarta tana ta dariya, "Nayi kyau sosae ko?" ta tambaya, fuska a sake ya furta "Yeah" shiru sukae na wani lokaci tana ta kallon fusakarshi tana dariya don dad'in Vedio Call din take ji shi kuma sai faman lumshe ido yake can yace "bazaki je yawo sallan ba?" da sauri tace "zanje, yanzu ai naje wurin Tk d'in don mu tafi kallon salla na iskeshe bai shirya ba amman yace yanzu zai shirya sai mu tafi" kai ya jinjina mata, "Kai bazaka kallon Sallan ba", " ba'a yi anan" "Hawan barikin?" d'aga mata kai yay, "Ai da yake ance Abujan duk yan gayu ne k'ilan baku zuwa kallo shiyasa ba'ayi, yanzu saidae kaita zama a gida kenan?" d'an Murmushi yay "No zan fita ba yanzu ba" gyad'a kai tay sukae shiru ita dae tana ta Murmushi shima fuskarshi a sake take yana cigaba da lumshe ido alamar dai har yanzu baccin yake ji can ya d'an langa6ar da kanshi da alama baccin yake, tsuru Fatuu tay tanata kallon fuskarshi,
"Wllh Allah Ya Handsome kanada bala'en kyau" yaji Maganar ta doki dodon kunnanshi, a hankali ya bud'e idanun akanta yana kallonta tana ganin ya bud'e idon taci gaba da cewa "bakaga da ka rufe ido ba yadda ka k'ara kyau" shiru kaman bazaice komae ba can kuma yace "kije kiga if he's ready" "Tk d'in?" ta tambaya, kai ya d'aga mata alamar eh, "To amman in bai shirya ba zan k'ara kiranka" shiru ya d'anyi sai kuma ya d'age gira yace "bazaki barni nayi bacci ba ko" kyalkyacewa tay da dariya ganin yadda yai mata Maganar tace "to na barka kayi bacci Sweetheart Ya Handsome d'ina, amman fa in muka dawo zan kiraka kaima ka nuna man gayun sallan ka" tay Maganar tana jaddada mashi da kanta, d'an guntun Murmushin gefe yay ya daga mata kai alamar to daga haka ta daga hannu tana yi mashi bye bye shima ya d'aga mata hannu guda kafin ya katse kiran, Lokacin data maida ma Tk d'in wayar yana cikin shiryawa don bayan tafiyarta kwanciyarshi yay ya k'ara yin bacci, cewa tay zata jirashi a parking space yay sauri ya fito yace mata to, bayan wani lokaci tana jingine da Motar Hajiya sai gashi ya fito ya dau wankan voile sai kamshi yake zabgawa, tana ganinshi ta fara kokarin bud'e Motar ya dakatar da ita da fad'in "Yau ba cikinta zamu fita ba" "To a wacce zamu?" ta tambaya, Corolla S d'in Haisam wadda ranar data fara ganinshi ita ya hau tk ya nuna mata, da mamaki tace "To baya rufe abunshi ba taya zamu hau ta?" "Ai ya bani makullinta yace ko zamuyi amfani da ita" ya fad'a yana kokarin zura key d'in ya bude Motar,Murmushi ta saki tana jinjina kirkin Haisam a ranta, Bayan sun fita saida suka tsaya suka d'auki Haulat kafin suka wuce.
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
6️⃣3️⃣
.......Bayan sun gama kallon sallan bazama sukae cikin gari ana yin la'asar Tk yace bari ya maidasu gida don akwae taron da zaije shida abokanshi Fatuu tace to ai basu gama zuwa inda suke so ba yace ta bari gobe tunda ba wani hawan za'a k'ara yi ba sai su fito da wuri suje duk inda suke so sannan ta amince ya maidasu gida, a gidansu Haulat suka sauka sai Magrib ta koma gida ana gama sallan isha taje shago wurin kawu Amadu tace don Allah ya kira mata Ya Handsome, tsawon lokaci ta d'auka tana waya dashi duk da shi ba wata Magana yake ba itace mai surutun wani lokacin tayi Maganar arziki wani lokacin kuma mara kan gado shi dae sai dai yay murmushi ko ya bata yar gajerar amsa har tambayarshi Hajiya tayi yace bai gidan ta kira wayanta, karshe dae saida ya nuna mata zaiyi wani abu sannan ta kyaleshi sukayi sallama, Washe gari ma kaman jiya tunda wuri ta shirya taje wurin tk lokacin ya tashi amman bai gama shiryawa ba tace bari taje wurin Haulatu in ya fito sai ya kirata a gidan harda jaddada mashi kar ya dad'e fa ya dai amsa mata da to, bayan yaje ya d'aukesu sosae sukayi yawo don duk wani wurin shakatawa kama daga park, zoo da sauransu dae har wani had'addan eatery ya kaisu suka ci duk abunda suke so suka kuma dauki wanda zasu tafi dashi duk ya biya kud'in, dama kuma duk inda suka je shike biyan kudin shiga da sauran abubuwan don Musamman Haisam ya bashi kudi saboda hakan, sai Magrib suka koma gida sun gaji likis sun kuma yo guzurin abubuwa sosae sannan duk inda suka je saida Fatuu tasa photographer dake wurin yay mata hotuna za'a turo ma Tk shi kuma sai ya tura ma haisam wad'anda akayi masu kuma da Haulat tace in an turo zata yi ma kawu Amadu magana sai ya tura mashi su,
Washe gari ya kama kwana ukku da salla tk na cikin sharar baccinshi da safe ya jiyo sautin bugun kopar dakinshi koda yace waye Fatuu tace itace har saida gabanshi ya fad'i kafin ya taso ya bud'e mata, bin ta da ido yay bayan ya bud'en tana tsaye taci gayu da shaddar da hajiya ta d'inka mata don jiya voile d'in tasa, tana ganinshi ta turo baki tace "kai Tk wai bacci ma kake yi baka shirya ba kullum sai na jira ka" "Ina zamu kuma" ya tambaya da mamaki, "Yawon salla mana" jinjina kai yay yace "yanzu duk uban yawon da muka yi bai isa ba, ko inafa munje ina kuma zamu k'ara zuwa?" "To ai kayan sallan nawa basu k'are ba, ko sai in sanyasu in zauna gida" ta fad'a tanata faman tura baki, d'an Murmushin yak'e Tk yay kafin ya tambayi kayan sallan nata kala nawane tace mashi kala tara ne yau tasa na biyar yanzu saura kala hud'u, waro ido Tk yay jin har nan da kwana hud'u masu zuwa sai sun fita, ce mata yay ta bari to sai zuwa d'an anjima sai su fitan tunda jiyan sun je wurare da yawa, da farko k'in yarda tay sai daga baya ta amince akan kafin sallar azahar zai zo su fita yace to, tana tafiya ya fara tunanin nemawa kanshi mafita don tsakani da Allah ba k'aramin takura zaiyi ba ace har nan da kwana hudu masu zuwa yana fita da ita kuma dae ba yadda zaiyi dole yai mata yadda yake so in ba haka ba yasan fad'i ma Haisam zatayi shi kuma ba zai so hakan ba koda kuwa haisam d'in ya fahimce shi, Wuraren karfe 12 yaje ya dauketa koda suka biya ma Haulat cewa tai su tafi kawae Innarta tace yau bazata fita ba ita zata kula da gidan don innar tasu ta tafi Unguwa hakan yasa suka tafi,
Gaba d'aya Tk baiji dad'in fitar ba har saida ta k'ule shi don gidaje tasa ya rink'a kaita na yan'uwansu su Zaliha da gidan Baba shehu har gidansu Nana saida taje da gidajen wasu k'awayenta gashi in ya ajeta yace zaije ya dawo sai tace a'a sai dae ya jirata ta fito abunda kuma yafi 6ata mashi rai kenan yadda ta maidashi kaman driver d'inta don ko Hajiya bata ta6a yi mashi haka ba ita iyaka in ma zai jirata in ya kaita wani wuri to baifi suje gida biyu ba, sam bai nuna mata 6acin ranshi ba amman yana ta sak'a yadda zai yi daga yau kar su k'ara fitowa, yau ma dae sai wuraren Magrib suka dawo da daddare bayan sallan isha suna zaune a tsakar gida gwaggo ke ce mata amman dai daga yau sun gama yawon sallan ko tace mata a'a ai bata sanya sauran kayanta ba gwaggon tace yakamata dae ta kyale tukur ya huta hakanan amman sai ta turo baki tace to ai dai Ya Handsome yace ya kaita duk inda take so don haka ita sai tagama sanya kowanne kaya sannan zata gama yawon sallan, washe gari ganin jiya basu fita da wuri ba yasata bari sai kaman lokacin sannan ta nufi gidan Hajiyan bayan taci gayu da d'aya daga cikin atampopin da Babanta ya kawo mata anyi mata riga da skirt ga gyale wanda gwaggo ta siya mata da takalma yauma dae tayi kyau abunta atamfar ta amshi fatarta sosae da yake adon flowers pink gareta, lokacin da ta je bakin Gate bayan sun gaisa da Officer ne yake ce mata anya kuwa Tk zai iya fita yau, cikin rashin fahimta ta tambayeshi dalili, "Ai jiya kwana yayi ba lafiya don da daddare har saida na kaishi asibiti" cikin rashin yadda take bin shi da wani irin kallo bayan ya gama Maganar tace "Tk d'inne bai lafiya bacin ko jiya lafiya lou muka dawo"
yar dariya Officer yay kafin yace "in baya ga abunki hajiya fatuu ai yanzu yanzu sai Allah ko, ina tunanin wani abu yaci ya lalata mashi ciki shine ya d'ingi gudawa harda amai gaba d'aya yau da safe dana duboshi baida kuzari don ko Magana ma da k'yar yake yi" sototo tay tana kallon Officer alamar kaman dae bata yarda ba ganin hakan yasahi cewa ta shiga ta ganshi, wucewa tay ta nufi cikin gidan yana ganin ta tafi ya d'aga waya da sauri ya kira Tk lokacin yana kwance yanata sharar baccinshi kiran wayar ya tada shi don tana kusa da kanshi, bayan ya d'auka ne da sauri Officer ya sanar dashi ga Fatun nan ai kuwa wata wuntsilawa yay ya saukko daga kan k'atuwar katifarshi ya d'aukko wasu tarkacen Magunguna acikin drawer ya watsasu agefen katifar, bottle water dake saman drawer d'in ya d'aukko ya ajeshi a k'asa kusa da katifar, da sauri ya nufi kopa ya bud'e kafin ya koma kan katifar agurguje ya kwanta hadi da lullu6e jikinshi gaba d'aya da bargo yaba kopar baya, sai bayan d'an wani lokaci ta k'araso don akwae yar tazara daga gate zuwa bayan, tana niyyar kwankwasa kopar ta ganta a bud'e, d'an tura kopar tay ta rafka sallama shiru bai amsa ba ta k'ara yin sallamar sannan ta jiyo muryarshi can kasa yana cewa ta shigo kopar a bud'e take, a hankali ta tura kai ta shiga tana hango shi taja ta tsaya kaman taga abun tsoro ganinshi a kudundune cikin bargo, d'an matsawa tayi ta kira sunanshi shiru bai amsa ba ta k'ara sannan ya amsa da kyar, "Ashe wai baka lafiya?" ta tambaya tanata zare ido, kai kawae ya jinjina mata ba tare da yayi Magana ba, "Mike damunka?" shiru kaman bazai bata amsa ba can ya dan fiddo fuskarshi amman bai juyo ba don yasan daya kalleta yana iya yin dariya don dama akwae shi da yawan yin dariya, da kyar cikin irin muryar mara lafiya yace "ina tunanin Food poison ne naci ya lalata man ciki, jiya nasha wahala dakyar na samu na kira Officer ya kaini hospital har saida akai man k'arin ruwa na d'an samu sauki" yadda yake Maganar sai ka rantse da Allah bai lafiyar ita kau Fatuu k'ara zaro ido tai a rud'e jin harda k'arin ruwa akai mashi don ita a wurinta da anyi ma Mutum drip to ciwon yayi tsanani, kaman zatayi kuka ta shiga yi mashi sannu don dama ita badai tausai ba in taga mutum na ciwo duk ta damu, da kai ya rinka amsa mata can tace ya kawo wayarshi ta kira Ya Handsome ta fad'i mashi, da sauri yace " a'a ki kyaleshi kar a tada masu hankali tunda Officer ya kaini asibiti" "To bari inje in fad'i ma gwaggo, in ta gama abinci kuma zan kawo maka" ta kai Maganar tana nufar hanyar fita da sauri, yana jin k'arar rufe kopa alamar ta fita ya yaye bargon daga jikinshi tare da juyowa yana dariya a fili yace "haka kawae ki nemi maida ni bawanki, ko shi Yaya Haisam d'in nasan da yasan wahalar dani zaki bazai sani kaiki wani yawon salla ba" ya kai hannu ya d'auki wayarshi ya hau yin chat abunshi,
Ko ta kan Officer dake tambayarta ta gano shi bata bi ba iyaka ta d'aga mashi kai kawae tayi gaba, gaban kiosk din Amadu ta tsaya da damuwa ta fad'a mashi Tk bai lafiya don Allah ya kira ya Handsome ta fadi mashi, ganin yadda ta damu ne yasashi tambayarta miya samu Tk din ta fadi mashi, kiran Haisam din ya shiga yi bugu d'aya ya d'aga ya mik'a mata wayar bayan ta gaidashi ne ta kwashe komae game da ciwon Tk din ta fadi mashi a rude tana ta zuzuta ciwon yace zai kirashi daga haka sukai sallama, tana shiga gida ta iske gwaggo cikin kicin itama ta hau fad'i mata, sosae ta shiga jimami har tana cewa ko wannan yawon ai yasa ma mutum ciwo, jin abunda gwaggon tace ne yasa fatun yin wuri wuri da ido jin kaman harda laifinta yake ciwon.
Tk na cikin yin chat kiran Haisam ya shigo har saida gabanshi ya fadi don yasan tabbas Fatuu ta gaya mashi bai lafiya ne, a d'arare ya d'aga kiran bayan sun gaisa ne ya mashi ya jiki yace da sauki sosae jin hakan yasa haisam din cewa Zarah tace har drip aka mashi shiru yay ya kasa cewa eh don mugun jin nauyin yi mashi k'arya yake kuma yasan in yace eh zai iya tada masu hankali ba kaman Hajiya in taji,
"Any problem?" yaji haisam d'in ya tambaya, cikin sanyin murya yace "ba wani abu daman ba ciwo nike ba ita na fad'i ma hakan kawae" shiru Haisam d'in yay kaman bazaice komae ba can kuma ya furta "why", ba tare daya yi mashi karya ba ya kwashe yadda sukae da Fatun na cewa sai kayan sallanta sun kare zasu daina yawon sallan kuma duk inda ya kamata suje sun je, sigh Haisam yay ta cikin wayar jin rikicin Fatun,
"kayi hakuri Ya Haisam in banyi maka daidai ba" Tk ya fad'a cike da girmamawa, gently yace "No, i understand, amman kana ciwon k'arya in ya kamaka fa?", yar dariya Tk yay yace "ai ya haisam akwae inda dole saida karyar" d'an guntun murmushi yay ta yadda har saida Tk d'in yaji daga haka yay mashi sallama tare da rejecting call din, cike da murna Tk ya fad'a kan katifarshi don sai yaji kaman wani nauyi ya sauka daga kanshi, yana kwancen Amadu ya turo kopar ya shigo, turus yay ganin Tk d'in kwance yana mashi dariya hakan yasa Amadu murza idonshi don wai ko ba daidai yake gani ba, "Kaga patient na dariya ko" Tk ya fad'a yana tashi zaune, nufarshi Amadu yay yace "to ai ni waccan burkakkar ce man tayi wai kana kwance magashiyyan fa" k'ara sautin dariyar tk yay "ai hakan ta ganni ne, amman fa lafiya ta garas wllh" nan ya yi ma Amadun bayani dalilin ciwon karyar "Yarinyar nan fa ba hankali ne da ita ba wllh kai jakinta ne, amman baka ce mata ka gaji sai kayi ciwon karya?"
"Ai hakanne kawae zaisa mu rabu da ita lafiya tunda kaga sani akai yi mata hakan" jinjina kai Amadu yay alamar ya fahimta suka k'ara d'an yin fira kafin ya mik'e zai tafi,
"Amman ya baka kawo man abun ciwo ba to" Tk ya fad'a yana dariya, "Wake ta wani abun ciwo nida akace ma cikin ka ya lalace kana ta amai da zawo har na fara tunanin ko wucewa zakai" Amadu yay Maganar yana dariya shima,
"to na biyo ka bashi ka aiko man da kayan dubiya" Tk ya fad'a lokacin Amadun zai fita, akan hanya ya had'u da Fatuu ruke da kula zata kai ma Tk Abinci kallonta kawae yay ya d'an girgiza kai ita kuma ta tura mashi baki, tana wucewa ya kira tk a waya yace sai ya shirya ga Boss dinshi nan zata kawo mashi Abinci, koda ya isa bai tsaya shago ba dama wani yaro ya bari ya jire mashi, cikin gida ya nufa ya sanar ma gwaggo game da ciwon Tk din don ta tashi hankalinta har lekowa tay waje bayan Fatuu ta sanar da ita tace don Allah yay sauri yaje ya gano ya jikin nashi yana ciwo shi kadae a gida ya sanar mata dama yanzu yake niyyar zuwa, Salati Gwaggon ta saka ta shiga tafa hannu jin ciwon bana gaske bane,