Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 4

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 4

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 4: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 4. Wai nikam ina Amadu ya shige ne,tun d'azun banji…

4,320 words

Wai nikam ina Amadu ya shige ne,tun d'azun banji d'uriyarsa ba ko da na lek'a nemanki naga kes dinsa a rufe" fatuu tace"Nima dana fita a rufe yake kuma har na dawo yana rufen", "To ko ina ya shige,Allah yasa l..." gwaggo bata k'arasa maganar ba suka ji ana bud'e d'akin da ke cikin zaure,da sauri fatuu tace"To gama shi nan ya dawo,"KAWU AMADU,KAWU AMADU..." ta fara kwala masa kira,Wani matashin saurayi ne mai d'an tsawo fari kaman gwaggon sai dai yanayin rashin hutu yasa farin nasa yin kala kala,Shigowa yayi yana amsa kiran da fatu ke masa shima da karfi "Na'aaamm" yace "wannan kira haka Hajia fatuu..."da sauri tace "Maman ka keta neman ka bani ba" tayi maganar tana nuna masa gwaggo wadda ta fito daga inda take yin girkin tuwon tana girgiza kai jin maganar da fatuu tayi,kallon sa tayi da murmushi tace"Ina ka shige ne wai Amadu? Yace "Wllh naje wani wuri ne daga nan na biya kasuwa don akwae abubuwan da suka k'are ana ta nema,lafia dai ko?" ya tambaya,"Eh lafia lau,dama maggi nike so namu na nan ya kare," yace"To" ita kuwa fatuu cewa tayi"Kashh dama baka dawo ba" da sauri suka juya su duka suna kallonta da mamaki ya tambaye ta"Saboda me? tace "Inda baka dawo ba har aka gama tuwon dole abar ni ai inyi kwad'o da mai da yaji tunda ba magin miya" ta k'arasa maganar tana gyad'a kai,Gwaggo ce tace"kar ka biye mata,kaje ka bud'e shagon,tun dazun take shashancin da ta saba,tuwon ne bata so,kuma sai nayi,sai dai mutum kar yaci,ta juya ta koma wurin girkin. Amadu ya kad'a kai zai fita a hanya yake fad'in"Lallai yarinya tuwo ai saiti ne,sai da shi mutum zai ji shi gam gam,adaidai nan ya fice,ta6e baki Fatuu tayi kasa kasa tace"dama ai bakin ku d'aya uwa da d'a,kun daukko ni zaku kashe ni" Gwaggo ce ta katseta"Wai nikam har yau tsakin bai wanku bane? "Ya wankuuu" fatuu ta fad'i da karfi,"To ki kawo man mana da ruwan, kije ki kar6o magin kuma" tace "to, Magin taje ta amso sai da ta rabo shi da biscuit wai yunwa take ji kafin ta kawo magin tace "Gwaggo wai miyasa baki yin tuwon a kan d'an gas dinmu,kinfi son kiyi ta wahalar hura icce ne? "Gas d'in ne yayi kasa,kuma dai ni nafi son yin tuwo kan murhu yafi dahuwa" gwaggo ta bata amsa,"To ki kawo ni inyi miyar asaman gas din" fatuu ta fad'a, "Niba in baki yin miyar ba,k'arshe kije kiyi ma mutane shirme" "Wallahi bazanyi ba" Fatuu ta fad'a,gwaggon tace"aifa dayake ke kike son yi dole ki fad'i hakan,da hakanan ne nace kiyi man abu sai kin gama 6ata man rai sannan, Taci gaba"sau nawa na baki kikai man ba daidai ba,kawae don inason ki iya girkin ne nike sake baki,don kar inyi maki aure baki iya ba..."Wata irin juyowa Fatuu tayi tana ma gwaggo dake talga tuwo wani irin kallo tace"Aure! Wa za'ai ma auren? "ke mana,nan da d'an lokaci kadan mi za'a jira" gwaggo ta bata amsa,da sauri tace"Wallahi ba wanda zai man aure har sai nazama Doctor ehee" Gwaggo ta juyo tana kallonta tace"Likitoci ai nutsattsu ne,a hakan ne zaki zama wata doctor,kece kullum rigima da yaran unguwa ga rashin nutsuwa wurin wauta kuwa kece lamba ta d'aya" "Amman dai ai inada kokari a Makaranta,kuma Malaminmu yace in kana da kokari komae kake son zama zaka zama," gwaggo tace"to nidai ina gaya maki muddin kina son ki zama likita sai kin daina rashin jin magana ki natsu don nidai duk likitocin da nike gani masu natsuwa ne,kije ki daukko kayan miyan in nuna maki wanda zaki jajjagan in kinga dama",Juyawa tayi ta nufi kicin da k'arfi tace"To Kakus zan natsu,amman duk wanda ya raina min wayo bazan yarda ba eheee"daga haka ta shige cikin kitchen din.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY OUMMU IMAM📱*

*Paid Book*

*Free Page8️⃣*

Officer Civil D,ne ya dawo saman benci ya zauna bayan ya rufe gate d'in har lokacin suna dariyar abunda ya faru lokacin da Haisam ya fice,ya kalli Abokin aikin nasa yace "kasan mi? Officer P yace "A'a" Officer CD yace "Wallahi tunda nike ban ta6a ganin mutumin da ke burgeni sosai ba irin mutumin can Haisam,"Mike burgeka a tattare dashi ne? ya tambaya, "gaba d'aya lifestyle din shi,kai wallahi ba don ance mutum tara ne bai cika goma ba da nace shi din ya cika goma cib,ga kyau,ga ilimi,uwa uba kuma ga kud'i,ga iya daukar wanka malam ko a mata sai anyi dogon bincike za'a samu kamarsa he's a very handsome and classy guy, da kuwa za'a bada kyautar wanda yafi kowa tsafta a Nigeria to wllh ba wanda ya dace sai shi,Daria Officer P,ke yi sosae ganin yadda Abokin nasa ya dage sai faman bayani yake,yace "Kai dai shi ka sani ne shiyasa kake ganin hakan, duk da dai duk abunda ka fad'a game dashi ba k'arya kayi ba gaskia,Amman ni kasan mi ma ya burgeni da shi sosae? Da sauri d'ayan yace "Sai ka fad'a..." yaci gaba "Rashin girman kansa,a fuska idan ka ganshi lokaci guda zaka yanke mashi hukuncin yana da girman kai,sai kayi mu'amala dashi zaka fahimci yana da saukin kai,ji fa ranar nan yadda yazo ya zauna nan muna yin fira har d'an sa baki ya rink'a yi,duk da ba wani dad'ewa yayi ba wallahi nayi mugun mamakin hakan don ban ta6a zaton hakan b,su kam dai sunji dad'i wllh,itama hajia badai kirki ba, Officer CD, yace"Wallahi kam ai wasu mutanen are very lucky,kaga kaman su suka tsarawa kansu rayuwa"cikin tsananin daria d'ayan yace "kai baka cikin su ne? "Uhm inda ina cikinsu ai baka ganni nan kullum tsugunna bakin gate ba,in za'a shiga in bud'e,in aka fito in rufe....d'ayan yace "A dai rik'a gode ma Allah,don shi gwanin hikima ne daga haka sai kaga ka kai inda baka ta6a mafarkin kaiwa ba,duk rayuwar da ya za6a ma bawa ita ta dace dashi,in ka kasance mai gode masa sai ya kara inganta maka...da sauri Officer CD ya katse shi da cewa "Wannan gaskia ne,Alhamdulillahi ala kulli halin,ya cigaba"yauwa nikam inata son intambaye ka..."Officer P yace "game da me fa?" yace "wai mike tsakaninka da Saude ne? Wani irin kallo yayi masa yace"Wace Saude? d'an harararsa yayi yace "ni zaka ma duniyanci kace baka san wace Saude nike magana akai ba" daria Officer P yayi yace "Oh wai ko Saude ta nan gidan kake nufi,to ni mike tsakanina da ita banda alakar wurin Aiki daya da muka hada" ya k'arasa maganar yanata daria,Officer CD yace"don kun had'a wurin Aiki d'aya shiyasa take baka kulawa ta musamman kenan" daria sosae yake yace "ni banga wata kulawa ta musamman da take bani ba kawae dai Sharri zaka man,in don Abinci da take kawowa wannan ai mu duka take kawo mawa,kuma da izinin masu gidan" ta6e baki yayi yace "Uhm kaji nayi maganar Abinci,kuma ko a Abincin ma ai akwae ayar tambaya don ba iya Abinci take kawo ma ba duk wani kayan kwalam da makwalashe da akaci aciki sai ta kawo maka,rannan fa ina ji tana tambayarka wae mi kake so a dafa,ni mamaki ma yasa na kasa yima magana a lokacin" daria sosae Officer P yake yace "nidai ba abunda ke tsakanina da ita,ka rufa man Asiri kada Matata taji kasa a hanamun kwanciyar hankali" ta6e baki yayi yace "in tayi wari maji ai" Yace "ba abunda zai yi wari bare har kaji.

Daukar takalman da Haisam ya cire T.k yayi ya koma cikin parking space din ya k'arasa goge motar,sannan ya nufi part d'in sa don kai takalmin ya kuma gyara masa dakin,a ka'ida dama indai Haisam din ya shiga part din bayan ya fita sai an shiga an gyara masa,kuma t.k ne mai gyarawa.Yana shiga ya aje takalman a gefen kofa ya nufi saman kujera L-shape ya zauna ya d'aura kafa daya kan daya ya wani sha murr,can ya kece da dariya a fili yace "yasin dole ake ganin masu kudi kaman suna da girman kai,yo mutum na kwana yana tashi cikin wannan daular ai dole aga yana fad'in rai koda shi ba haka bane a wurinshi....haka t.k yayi ta sokana dama ya saba duk yazo gyaran sai yagama shiririta kafin yayi abunda ya kawo shi,don yana da tabbacin ba CCTV a cikin parlon sai a waje. Mikewa yayi yana fadin"to mima zan gyara anan,ba abunda parlon yayi" Bedroom ya nufa nan ma dai tsaf yake,kwalaben turaren da Haisam yayi amfani dasu ya maida ya jera su,ya dau Bathrobe din daya aje gefen gado ya maida ita cikin laundry ya shanya,ya shiga cikin toilet din wanda yake Had'addan gaske ne mai matsakaicin girma,irin toilet din daya amsa sunan Toilet din yan gayu,komae na cikinsa fari ne tun daga kan,bathtub,toiletseat,washbasin,shower curtains,bathroom cabinet,soap dispenser,hatta tiles d'in dake a k'asa da kuma bangon toilet din fari ne kal sai yan abubuwa k'alilan ne Silver kaman su Mixer tap,detachable shelves,abun saka tissue wato Toilet roll holder,da Towel rack wanda ke dauke da fararen towels k'arami da babba rataye a saman shi,sai salk'i kewayen yake yi yana daukan ido,tamkar ba'a amfani dashi,tsaye t.k yayi yana tunanin to mima zai ma toilet din? d'igo-digon ruwan da Haisam yayi wanka ne kawae a k'asa shima ba wani mai yawa ba don akwae bath mat a gaban bathtub din wadda ke absorbing ruwa in an fito daga cikin kwamin, itama fara ce sol,ka'ida ya fito daga kwamin wankan sai ya fara taka ta kafin ya taka tiles d'in kasan don bayan tsane ruwa tana preventing zamewa.

Detachable shelves t.k ya nufa wadda ke like a sama d'auke da toilet cleaning items,ya ciro safar roba yasa kafin ya daukko liquid cleaner da scrub sponge komawa yayi gaban bathtub ya d'iddiga liquid cleaner din ya wanke,bayan ya gama ya maida robar cleaner din ya daukko disinfectant spray ya fesa a saman tiles din kasa yasa mop ya goge fess,ya ciro karamin towel dake sagale a jikin rack ya goge bathtub din da ya wanke,ya dawo ba ko digon ruwa jikinsa,ya juya ya bud'e seat shima dai fess yake ba wani dirty illa ruwan cikinsa da kalarsu take blue kaman ruwan swimming pool hakan kuma ya faru ne sakamakon cleaner tablet da t.k ya saka ciki lokacin daya gyara part din da safe,hakan na nufin ba'ai amfani da seat din bama,flushing yayi har saida ruwan suka koma fari kal sannan ya rufe,ya yago wipe daga cikin wipe dispenser dake manne a gefen seat din ya goge jikin seat din dan damshin jikin wipe din yasa nan da nan seat din ya rinka wani irin sheki gwanin burgewa,ya jefa wipe din da safar hannunsa a cikin farin wastebin dake a bayan kofan toilet din,har zai fita sai kuma ya hango cabinet a bude,komawa yayi ya duba ciki ko akwae abunda ke bukatan gyara,su toothpaste brushes,sabulai,da turarurrukan wanka ne shake a cikinta,ganin komae a jere lpy lau yasa ya rufe ta ya juya ya fice hannunsa rike Mop da yai amfani ya maido ta cikin laundry ya aje. Washing machine ya nufa ya bude,ba wasu kaya aciki sai underwears din da Haisam ya cire dazun,juyawa yayi ya duba cikin cabinet din laundryn ko akwae wasu kayan daudan pajamas kala daya ne da Haisam ya cire da safe,ya daukko su ya saka cikin machine din,a ranshi yace "bari da safe in ya cire wasu sai in hada in wanke"ya rufe,dan karamin farin towel mai laushin gaske ya dauka ya koma bedroom din ya goge furniture din ciki wadanda dama suke ta kyalli,bayan ya gama ya fita parlour desk kawae ya goge sai ya dan tattara bakin kofan shigowa ya dau takalman daya aje na Haisam da floor wiper da dan towel din da yayi Amfani ya maida kowanne wurin da ake aje shi,ya dawo parlon hannunshi rike da Air freshner ya feshe parlon wanda dama yake ta sakin k'amshi mai sanyin dadi,maida freshner d'in yayi ya dawo cikin parlon sai da ya bud'e fridge ya dau lemo Fanta ya bud'e yana sha daga haka ya fice bayan ya jawo kopan ta rufe. T.k,yaron gidan Hajia ne,tun yana d'an karami,Almajiranci aka kawo sa daga wani kauye dake a k'aramar hukumar birnin magaji jahar Zamfara,ta sanadiyar wani dan garinsu Isiyaku wanda ada shine ke Aiki a gidan,to sukan je tare da t.k yana kama masa suna yin shara,da goge gogen motoci sai Aike in Hajia na bukatan wani abu,daga baya isiyaku ya sanarma Hajia cewa zai koma gida don zasu tafi da yayansa neman kudi lagos,Hajia ta bashi shawaran ya tsaya zata sa shi a makaranta yafi tafiya neman kudin nan,amman yaki tsayawa don ba son karatun yake ba,to a lokacin ne t.k ya ce ma Hajia shi ya rika zuwa yana yi mata Aikin? Hajia na Murmushi tace "d'an malam ai harabar gidan nan tayi maka girma baka iya share ta...da sauri t.k yace "da kwarankwatsa zan iya,a gonar babanmu kunya goma nake nomewa kuma wani lokacin har in kara" Hajia taita yin daria jin zancen shi tace "ya sunanka? Yace"Tukur Halliru,ta amince ya cigaba da yin Aikin amman tana shakkun in zai iya don lokacin baifi shekara 11 ba. Aikuwa t.k yaba hajia mamaki don sosae yake yin aikin ba wani kuskure,gashi akwae ladabi,daya ci ya koshi to fa ba zama Aiki kawae ko ba'ace yayi abu ba yaga ya dace yi yake,a lokacin hankalinsa da karfinsa sun girmi shekarunsa,nan da nan ya shiga ran Hajia tasa shi makaranta ya fara daga primary 4 don ya fad'a mata a garinsu ya fara karatun kafin aka kawo sa karatun Allo,sosae t.k yake fahimtar karatu don lokacin ya dawo gaba daya gidan Hajia da zama tasa shi a wata makarantar Allo dake nan cikin unguwa amman kafin ta aikata hakan sai da taje da kanta har makarantarsu ta sanar da Malaminsu niyyarta ta bukaci ya bata number din baban t.k,aka kuma ci sa'a baban nada waya lokacin ta kira babanshi sosae ta fahimtar dashi tace in yana son karin bayani game da ita ya tambayi Isiyaku,ta ba t.k wayan ya k'ara yimasa bayanin Isiyakun da take nufi,Sosae baban t.k yaji dadi don kafin ta kira sa malaminsu t.k din ya kirasa yayi masa bayanin abun Arzikin data kaima makarantarsu,na kayan abinci,omo da sabulai,da takalma silifas,harda kudi masu yawa tace a rarrabawa Almajirai. Cike da zumud'i malam halliru ke sanarma matansa guda ukku abun Arzikin daya samu t.k,mahaifiyar t.k wadda itace ta karshe cikin matan tayi tsananin farinciki yayin da sauran kuma bakin ciki ne ya turnike zuciyoyinsu,dama sun takura ma mahaifiyar t.k don suna ganin mijin yafi ji da ita,don uban gidansa ya bashi auran ta,kullum suyi tayi mata gori suna cemata yar sadaka,ladan noma,ita dae bata biye su don hakuri ne da ita.

Malam halliru yaso barin t.k yayi karatun boko don wani malaminsu t.k d'in lokacin har gida yazo ya roki uban daya bar yaron yayi karatu mai zurfi don yana da kokari,amman sauran matan suka tada balae wai sam basu yarda ba yadda aka tura yaransu sukaje suka yi karatun Allo,to dole shima t.k din yaje,ba yadda bai ba ya fahimtar dasu hakan k'aruwarsu ce gaba daya,amman firr suka ki amincewa don bakin ciki,ba k'aramin tashin hankali ya fuskanta ba,ba yadda ya iya haka ya turasa,mahaifiyarsa Hasiya nata kuka,don ta so yayi karatun,dayake Allah hakimun ne sai gashi tafiyar tasa ta zame masu Alkhairi,rabo kuma ya rantse,Malam halliru ba k'aramin girgiza yayi ba lokacin daya kaima t.k ziyara,ganin cikin daular da d'an nashi yake,bada niyyar kwana yaje ba,amman hajia ta matsa ya kwana,da zai tafi ta hada masa sha tara ta Arziki harda Atamfofi ya kaima matansa. Zaune malam halliru yayi a tsakan gida yana basu labarin irin Arzikin da t.k yake ciki,ya sanar masu mahaifiyar sanata ce yake wurinta kuma matar tsohon ministan tsaro Gen.Adamu zakee,kaman yadda t.k ya fad'a masa,murna wurin Hasiya kam ba'a magana,sai ma da t.k din yazo da Sallah,har gida aka rinka zuwa ganin tukur dan gidan sanata,haka mutanen gari ke fada. Private school hajiya tasa shi yayi secondary,bayan ya gama kuma ya tafi Polytechnic dake nan katsina inda yanzu ya shiga ND2 yana karantar SLT,ba faman da Hajia bata yi dashi ba akan aikin da yake ba kaman wankinta da ya hana kaiwar da ake dry cleaning shike wanke mata su fess ya goge a cewarsa baiga abun wahala ba abunda da injin ake yin wankin,Manyan abubuwa irinsu barguna,labulaye da carpet kawae ake kaiwa wurin wanki. Lokacin da Haisam ya dawo hajiya tace ma tk ya samo wanda zai rink'a gyara masa part dinsa acikin abokansa yan makarantar allon su dake kawo masa ziyara akai akai,nan ma cewa yayi shi duk zaiyi ai ba wani aiki ne mai wahala ba,kuma dama yana bala'en son Haisam,ba k'aramin burgesa yake ba,shiyasa in yana gyara masa part din nasa cike da himma yake aikin,ba algus don dama shi tun yana k'arami aikinsa ba ha'inci,shiyasa in ya dage shi zaiyi abu sai hajia ta kyalesa don tasan zai iya din,kuma ba'a ganin ba daidai ba wani lokacin takan tsokane shi tace "na manta jikan nawa fa kakkarfa ne don tun yana karami kunya goma yake nomewa" sukan yi dariya atare, Shikam t.k duk yana yin hakanne don hud'ubar da mahaifiyarsa ke masa duk in yaje ganin gida,takan ce ba abunda zamu iya saka masu dashi,haka zakaga ana zuwa gaida t.k in yaje tamkar shine Senator din,iyaye har tura yaransu yanmata suke wae ko zai taya,basu san t.k ya wuce ajinsu ba sai yar birni,in ya tashi dawowa haka mahaifiyarsa zata bashi,su kuka,kubewa,daudawa,barkono da sauran su ya kawo ma hajiyar,mahaifinsa da har hatsi yake bashi ya kawo,Hajiar ta hana tace iya su kayan miyan ya isa ta gode. Wannan kenan game da Tukur Halliru Birnin magaji,wanda tuni yazama dan gida a gidan Hajiyar sanata don har Senator Ali Adamu zakee yasan da zamansa.

A next page zamu fara nitsawa cikin labarin In shaa Allah,aci gaba da share pls. Thanks as u do so🤝🥰

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY OUMMU IMAM📱*

*Paid Book*

*Free Page9️⃣&🔟*

Washe gari juma'a,daga cikin d'aki gwaggo ke magana"Wai fatuu bazaki fito ki tafi ba sai kin makara,kuma a buge ki kizo kina cewa malami kaza ya tsaneki ko" fitowa fatuu tayi sanye da uniform din makaranta hannun ta d'aya dauke da jaka School Bag dayan kuma takalma ne Sandals na roba,a k'arkashin hammatarta ta sak'a jakar ta duk'a tana kokarin sa sandals din saidai igiyan tak'i sawuwa sai faman kici kici take yi dashi a fili tace"Wannan shegen takalmin ni wallahi na gaji dashi" haushi taji ta buga shi da k'arfi a k'asa tace banzan takalmi yaki sanyuwa.

Duk maganganun da take a kunnan gwaggo,fitowa tayi ta tsaya a bakin k'ofa hannunta d'aya dafe jikin bango tana kallon Fatun sai kiciniya take. "To taya zai sanyu kin kasa natsuwa kisa shi sosae,ji bi yadda kika wani takure kin cusa jaka a hammata,d'agowa tayi tace"to yaya zanyi" fuska a tur6une da alama takalmin ya k'ule ta, "Ki aje jakar mana a gefe,ki zauna sosai kisa" Aje jakar tayi ta dan zauna a bakin k'ofa kamar yadda gwaggon tace,aikuwa sai gashi takalmin ya sanyu ba wani 6ata lokaci,da sauri fatuu ta d'ago ta kalli gwaggo tana daria tace "Kinga d'an banza ya sanyu kuwa" gwaggo ta dan ta6e baki"Uhm ba wani d'an banza,dama ba ki yadda ya kamata ya sanyun bane,ace komi mutum zai yi bazai sa natsuwa ba, Mik'ewa fatuu tayi tana kokarin goya yar jakar goyon a bayanta tace"zan tafi" gwaggo tace"To adawo lpy,Allah ya tsare" wani irin kallo fatuu tayi mata tace adawo lafia kuma? Gwaggo tace"Eh mana ko baki son Addu'ar ne?, "A'a ina so mana amman ai banji bayani ba" tayi maganar tana yi ma gwaggo alamar kud'i da hannuwanta,gwaggo tace"wai don Allah ba ranar da zaki ce yau dai gwaggo kibar kudin ki ne? Da sauri fatuu tace "iyeee,to kuma dami zan hau mota kuma inyi break,in baki bani ba? Gwaggo tace "to acici baki da magana dama sai ta abinci,a duk satin duniya sai kin cinye mani naira d'ari biyar wani satin ma sai sun fi haka tunda sai ki dawo kice man baki samu bus ba kin ranci kudi kinyi ciko kin hau Napep ko mashin", Fatuu da ke tsaye ta k'agara gwaggo ta sallameta ko ta tafi tace"Don Allah gwaggo kiban,taya karatun zai yiwu da yunwa to ko mota dai ai sai an zuba mata mai take aiki ko" yar daria gwaggo tayi, fatun tace "yau baki zuwa aikin ne? "Zanje,amman sai da rana", Fatuu tace"kenan zan dawo in iske ki? Gwaggo tace "Anya kuwa kinsan yau juma'a,da wuri zan tafi,wurin k'arfe d'aya haka", "to ammn dai zaki yi mana abinci ko ba sai na dawo ba inyi"tayi maganar da sigar shagwa6a" gwaggo ta rike baki tace"Ah kajita ko da yaushe-da yaushe nike tafiya in bar mata wani yin abinci,ai sai dai in ina aikin safe ne kuma shima kusan tare muke dawowa,kamar wadda ta iya wani abincin arziki", Fatuu tace "ai dai ina yi kuma ki ci har kice yayi dad'i" daria gwaggo take tace"Mai karya.....fatu tace"d'an Aljanna,tana daria,"gwaggo kiban don Allah" mik'o mata naira d'ari tayi wadda ke cikin hannun da ta dafa bango dashi,da sauri fatuu ta amsa tace"daman kudin na a hannun ki,amman sai kinja man rai,juyawa tayi ta fara tafia,sannan tace "Kar ki damu kakus,zan biya ki duka kud'aden da kika kashe man in nazama Doctor" har lokacin gwaggo daria take ta girgiza kai tace"nadai fad'a maki ai natsattsu ne ke zama likitoci,in baki natsu ba,ba wata Doctorn da zaki zama" da d'an karfi tace"Insha Allahu zan zama harna rik'a yima ki Allura ma,na tafi" ta karasa fada yayin da ta kusa isa zaure. Gwaggo tace" To Allah ya tsare adawo lafia ban.......,Fatuu dake cikin zaure ta k'arasa abunda gwaggon zata fadi da karfi"BANDA RIGIMA DON ALLAH FATUU" daga haka ta fice daga gidan,girgiza kai gwaggo tayi tana ta daria tace" Shiryayya,a haka ko nace d'in wani lokacin kafin ta shigo gidan an kawo man k'ararta,Allah dai ya shirya"daga haka ta koma cikin d'aki.

Tafiya fatuu take ta raba hanya biyu,sam ba natsuwa a tafiyar,hanyar shiru dayake safiya ce sai yara jefi jefi yan tafiya makaranta kamar dai ita,sai wani cilla k'afa take kamar zata tashi wai ita nan sauri take,Horn d'in da akai da k'arfi ne a bayanta yasa tayi saurin komawa gefe,sannan ta juyo tana kallon motar da ta taho,Peugeot ce 406,Maroon color,cikin ranta tace"dama mai motar nan ya rage man han....bata k'arasa ba sakamakon mutumin data ga ya wuce fuuu a cikin motar bai ko kalleta ba,da sauri fatuu ta zaro ido had'i da rike ha6arta tace"Kai! Wancan ai mutumin nan ne na jiya mai kama da Aljani,ba dai a layin nan yake ba? ta karasa maganar da sigar tunani harda d'an waigawa baya,tace"Uhm inma nan din yake,shi dai ya sani"

taci gaba da tafiya har tazo wata kwana d'an nesa da gidansu,tana karya kwanar ta tsaya da alamun mamaki a fili tace"lallai ma wannan haulatun,har yanzu bata fito ba,tana nufin in bita har cikin gida kenan" kwafa tayi sannan taci gaba da tafia,ad'an gaba kadan daidai wani gida inda yaro ya fito dauke da d'an bokitin plastic ta tsaya tace ma yaron "Kai haulatu na nan ciki" yaron yace "Eh naganta tazo ta karbi koko a rumfar da Innarsu ke saidawa" ya wuce,ita kuma fatuu ta kad'a kai ta shige cikin gidan wanda gaba daya k'asan gidan kasa ce,sai daga can gaban dakuna ne akai ma k'asan shafen siminti shima duk ya farfashe,a gefe guda wata mata ce cikin wata yar baranda da yara tsaitsaye tana zuba masu koko,matsawa fatuu tayi bakin barandar tace "Innarsu Haulatu ina kwana" da washe baki ta amsa"lafia lau fatee yan makaranta,haulatun na ciki" kad'a kai fatu tayi ciki,tana hawa saman simintin wata yarinya ta lek'o tana daria,wankan tarwad'a ce tana da kyau ba laifi,hannunta d'aya rike da hijabin Uniform dinta dayan kuma kofi ne tana shan koko,tsayawa fatuu tayi tana harararta,fuska daure tace"Ashe ma baki shirya ba don wulakanci kika sa inata sauri" haulatun wadda keta faman daria tace"wallahi markad'e innarmu ta aikan kuma sai na iske layi,amman ai na shirya hijab kawai zansa da Sandals",da yar tsawa fatuu tace "Da Allah to kisa mu tafi,salon sai mun makara wannan banzan displine d'in ya bugi mutane, daman ya tsane ni" ta k'arasa tana murgud'a baki,

Haulatu tace"bafa kyau zagin malami fat...." ta katseta"naji,wayace ya tsane ni"fatuu ta haulatu tace"bafa tsanarki yayi ba,kece kike ja ai yana dukan ki,ni kinga yana duka na?" ta kai maganar tana kurbar koko,"dalla ki fito mutafi ko inyi tafiya ta wallahi,daman ke ai baki ganin laifin kowa sai nawa"da alamar ranta ya 6aci, Haulat tace"Haba kawata daga fad'ar gaskia...." "to ki rik'e gaskiyar banso" inji fatuu,mik'o ma fatuu kofin kokon haulat tayi tace ida shanye wa",harararta Fatuu tayi da sauri tace "Wa!Ni zan sha wani koko,kokon ma sauran ki,Allah ya kiyaye,ta tofar da miyau gefe" girgiza kai haulat tayi da d'an murmushi ta idasa fitowa,aje kofin tayi a k'asa ta sanya hijab din da Sandals din dake aje bakin kofar d'akin,ta d'auki jakar ta,ta leda irin ta biki tace"Mu tafi" atare suka nufi hanyar fita,haulat ta shiga rumfar da innarta take,ta ajiye kofin data sha koko tace ma Innar "zan tafi" kud'i innar ta miko mata naira sittin tace"A dawo lpy" Allah yasa" haulat tace ta nufi hanyar k'ofar gida,don ita fatuu tuni ta fuce.

A kan hanyarsu ta zuwa bakin titi inda zasu hau Bus fatuu sai faman masifa take ma haulat tana cewa ai in suka rasa Bus itace a matsala don tasan bata da isassun kud'in da zata hau Napep ko mashin,baiwar Allah haulatun ita dai tayi shiru tana sauraranta da alama tana da hakuri,gashi da gani ta girmi fatun ko a yanayin jiki tafi fatuu tsawo a sanyaye tace"Insha Allahu ma zamu samu,in kuma ba'a samun ba sai in dawo ba wani abu,in Allah ya kaimu Monday naje"daga haka ba wanda ya kara cewa wani abu.

Suna isowa bakin hanyar kuwa sai ga Bus din da yar fara'a haulat tace "Alhamdulillah",juyowa fatuu tayi tai mata wani kallo fuska a d'aure.

Readers Also Read