Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 42

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 42

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 42: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 42. Lokacin da su Abbas suka k'arasa gidan Najeeb dake…

4,061 words

Lokacin da su Abbas suka k'arasa gidan Najeeb dake a Gra wanda katon gidane na gaske, sosae yay farinciki da zuwan nasu haka ma Matarshi Sofeeyat wadda irin matan nan ne da suka waye over tana da kyau daidai gwargwado kuma tana da haske saidae kana gani kasan hasken harda na kanti, taci gayu cikin k'ananan kaya wando da riga sun kamata hakan ya bayyanar da d'an dirin dake gareta, kanta anyi mata kitson k'arin gashi miri miri amman yay kyau sosae ta d'aura bak'in veil ta zameshi daga gaban yadda kitson ya fito sosae haka k'umbunanta an k'ara mata dana kanti shima Najeeb d'in yana sanye da kayan shan iska armless da wando 3 quarter,suna shiga cikin tangamemen falon wanda yake shak'e da kayan alatu suka zauna asaman d'uma d'uman sofas d'in dake kewaye acikinsa set biyu, zama itama soffyn tayi tana facing d'insu cike da kisisina ta shiga gaidasu idonta akan Haisam amman Abbas ne kawae ya kalleta shikam Haisam bai ko kalleta ba ya amsa mata a takaice, "H,zakee manyan gari ashe ka dawo nan da aiki rannan My ke gayaman" ta fad'a cike da salo, shiru bai ce mata komae ba da alamu ma bai jita bane don ya sadda kanshi yana danna wayansa, d'an ta6a shi Abbas yay yace mashi ana magana sannan ya d'ago ya kalleshi kafin yace wani abu ta k'ara cewa "da alama ta janye mashi hankali ne" kallonta ya d'anyi da d'an Murmushi ba tare daya ce wani abu ba, Najeeb ne yace tasa akawo masu drinks mana tace dama yanzu zata sa ta bari su gama gaisawa ne, mai aikinta ta fara kwalama kira "Murja,Murja" ta kirata har sau biyu sannan ta fito yar dattijuwar mata ce in a auren k'auye mane zata haifeta, "Baki ji anyi baki bane" ta fad'a ta d'aure fuska had'i da d'aura kafa d'aya kan daya, murya na rawa Murjar tace "ayi man afuwa Hajiya ina can ciki ne banji shigowarsu ba" shiru ta d'anyi kafin cike da bada umarni tace taje ta kawo masu abun sha kuma ta shirya abinci akan table Abbas na jin hakan yace "adai bamu abun shan amman abincin dae abarshi basai an shirya ba....." katseshi Najeeb yay "kana nufin bazaku ci abincin gidana ba?" yar dariya yayi yace "ba haka bane kaima kasan by dis time mutum yaci lunch so duk a k'oshe muke" d'an ta6e baki yayi baice mashi komae ba adaidai lokacin murja ta karaso ruk'e da babban tray ta d'auro bottle water da drinks da glass cups, daurashi tayi kan c-table kafin ta kinkimeshi da k'yar don murtukeke ne ta matsar masu dashi gabansu, tana shirin juyawa ta tafi aikuwa soffy ta daka mata tsawa tace "wai ke dak'ik'iyan inane,da kika aje masu waye bawanki da zai zuba masu?" har saida ta d'an tsorata jiki na kerma ta hau bata hakuri ta juya zata zuba masu Abbas yace ta barshi zasu zuba shidae haisam baima d'ago ba balle ya kallesu saidae yaji tsawar da tayi matan har cikin ranshi don ya tsani wulak'anta dan'adam don shi a wurinshi duk d'aya muke,tsaye Murjar tayi tana binta da ido ta kasa tafiya ita kuma Soffyn taba banza ajiyarta sai juya k'afa take tana wani shan kamshi, a hankali Haisam yay ma soffyn kallon kasan ido cikin sa'a suka had'a ido don dama bunu bunu sai ta kalleshi, ganin kallon da yayi mata ne yasa tasha jini jinkinta ta kalli murjar tace taje amman karta shirya table d'in ta kawo masu abunda zasu ta6a ta amsa da to harda dan rissinawa tayi mata godiya soffyn ta d'aga mata kai kafin ta juya ta tafi, bada jimawa ba ta dawo d'auke da wani hadaddan trayn ta d'auro plates d'in soyayyan naman kaza da kuma na snacks ta aje masu gefe tayi masu aci lafiya gaba daya harda haisam suka d'aga mata kai, fira suka shiga yi ganin haisam bai ta6a komae ba yasa Soffy yunk'urawa tana fad'in "kunsan fa H,zakee saraki ne bari nai serving nashi" dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace ba yanzu zai ci ba, bata san shi k'yamar k'umbunan hannunta ma yake ba, tana zama wayanta ya fara ringing alamar ana kiranta mik'ewa tayi tace masu "excuse me" Abbas ne ya d'aga mata kai ta nufi ciki tana wani karairaiya jiki ba kunya ba tsoron Allah, suna cikin hiran Najeeb ya kalli Haisam yace "H,zakee ina Mom d'inka bafullatana?? Kafin ya bashi amsa cike da tsokana Abbas yace "aikuwa kasan tana gidana ya kawota da har nace mashi mu taho tare ku gaisa" Najeeb yace "halan yak'i ko?" dariya Abbas d'in yasa yace "nidae ai baka ji na fad'i haka ba" d'an ta6e baki kawae yay baice komae ba, hira suka cigaba da yi har aka kira sallar la'asar sukaje masallaci suka yo salla suna dawowa suka ce bazasu shiga ciki ba zasu je wurin Saleem ne Najeeb na jin haka yace su jira su tafi tare ya nufi cikin gidan yana fad'in bazasu yi sallama da soffy ba Abbas yace ya gaya mata sun wuce, bayan wani lokaci ya fito sanye cikin jeans da t-shirt hannunshi ruke da wayarshi yasa bak'in glass ya fito a d'an madararshi, yana k'arasawa wurunsu suka shiga cikin Motar suka fuce, Bayan sunje har wurin Mahaifiyar Saleem d'in sukaje suka gaidata kafin suka shiga part d'inshi sai karfe biyar da wani abu suka baro wurin Saleem d'in Abbas ya tambayi Najeeb gida zasuyi dropping nashi ne dayake shi ke tuk'a Motar Haisam na gefenshi sai Najeeb d'in a baya, ce mashi yay su wuce gidanshi ya gaisa da Feenah, Murmushi kawae Abbas yayi don yasan ba wata Feenah kawae Zarah yake son gani, lokacin da suka isa bakin gate d'in gidan Abbas d'inne ya fita ya bud'e gate kafin ya dawo cikin Motar ya kutsa cikin gidan, suna shiga ciki daidai lokacin Abdul ya fito da gudu sai kuma ga Fatuu ta biyo bayanshi da gudu gaba d'aya gashinta a tarwatse ya zubo mata gefe gefe da kuma bayanta, tun kafin su tsaya Najeeb ya zuba mata idanu, suna yin parking suka firfito da gudu Abdul ya nufi bayan Haisam ya 6oye yana fad'in "Baba zakee kaga Aunty Zarah zata bugeni" d'agowa yay ya kalleta tayi tsaye agabanshi ba damar ta kamo Abdul d'in cikin cool voice d'inshi ya tambayi abunda yayi mata tana tura baki tace "ba game mukeyi ba duk wanda yay winning ya bugi mutum tun d'azun nike cinyeshi amman sai yak'i bari in bugeshi kuma ni da shi yay winning na tsaya ya bugeni har ma ya cire man ribbom" still yay yana kallonta Abbas kuma sai dariya yake Najeeb ma murmushi yake don ba k'aramin burgeshi take ba ba kaman yadda ya ganta a yanzu gashi tana Magana cike da sangarta, "Baki ga yaro ne ba kiyi hakuri" Haisam ya fad'a, tura mashi baki tayi alamar bata yi hakurin ba, ruk'o hannun Abdul d'in yayi ya dawo dashi gaba yace mashi "Say sorry to her" da sauri yace "Aunty Zarah Sorry" yayi Maganar yana dariya, harararshi tayi kawae haisam yace taje ta d'aukko Abaya dinta su tafi tace to, tana shirin juyawa Najeeb yace "yar bafullatana ba gaisuwa" dakatawa tayi ta juya ta kalleshi sai lokacin kuma tama ganshi don da duk bata lura dashi ba,ganin yana mata Murmushi yasa itama tayi mashi don ta ganeshi ta gaidashi ya amsa mata bayan ya cire glass d'in fuskarshi, nufar cikin gidan tayi Abdul yabi bayanta yana tambayarta tafiya zata yi tace mashi ehh, bada jimawa ba ta fito Feenah da Abdul na biye da ita suka k'araso wurin Motar, gaida Najeeb Feenah tayi tana cewa shine yazo gidan amman bazai shiga su gaisa ba Abbas yace kuma dama wurinta yace zai zo Najeeb d'in yace to yaga ya tafi bai shigan bane ita dae dariya kawae tayi ta mik'a ma Fatuu yar babbar ledar data ruk'o a hannunta, amsa tayi ta lek'a ciki kafin tasa hannu ta fiddo wani Material mai kyau tare da veil d'inshi can k'asa kuma kayan shafa ne wai sai ta rungume Material d'in ta mik'a mata ledar kayan shafan tace "Aunty Feenah ki bar wad'annan na d'auki wannan" d'an waro ido Feenah tayi tace "saboda me ki tafi dasu duka" tace "ai inada su da yawa Ya Handsome yana siya man" kafin tace wani abu Abbas ya riga cewa"ai na Ya Handsome daban wannan daban Mom Zarah don haka ki tafi dasu" kallon Abbas d'in tayi kafin ta kalli haisam ta d'age gira tace "in tafi dasu??" har saida tasa ya d'anyi murmushi yadda tayi mashi tambayar, ganin tayi mashi tsuru tana jiran amsa kuma kowa shi yake kallo yasa ya d'aga mata kai alamar eh, maida Material d'in tayi tace mata ta gode ta nufi Motar da sauri Abdul ya nufi Haisam yace "Baba zakee zaka k'ara kawo man ita?" kai ya d'aga mashi alamar eh ya juya gun Fatun ya kama hannunta yana tambayarta yaushe zata dawo tace sai Ya Handsome ya kara kawota daga haka ta nufi gaban Motan zata shiga Najeeb yace ta shiga baya zasu tafi tare tace to ta shiga bayan shi kuma ya shiga gaban Haisam ya zagaya side din driver ya shiga, lek'awa Abbas yay yana yi masu sallama yace ma Najeeb sai sunzo rakiya Airport, tada Motar yay su Feenah nayi ma Fatuu bye baye Abdul kamar zaiyi kuka suka fuce daga gidan........

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*6️⃣6️⃣*

......Suna komawa cikin parlon Abbas ya fad'a kan 3 seater Abdul ma ya haye saman jikinshi yana mai rigimar shidae adawo mashi da Aunty Zarah d'inshi Abbas d'in ya shiga rarrashinshi yana ce mashi zata k'ara zuwa, zama Feenah tayi gefenshi tana dariya kafin tace "kasan mi Dear?" girgiza mata kai yay alamar aa, tace"wllh ni kaina yarinyar ta shiga raina sosae d'an zaman da nayi da ita nima na fara jin kewarta" fuskarshi d'auke da dariya yace "ai haka take shiyasa suke shiri da H,zakeen sosae though dae dama shi sai kayi mu'amala dashi zaka fahimci sauk'in kanshi" jinjina kai tayi alamar gasgata zancenshi sai kuma tace "dama ya aureta don sun matuk'ar dacewa wllh kuma a yadda take yanzu kaga sai yay playing role biyu, gashi matsayin Yayanta kuma mijinta, kai abun zai bada citta fa" ta k'arasa tana dariya shima Abbas dariyar yake yi yana ayyana yadda zamansu zai kaya matsayin miji da mata kafin yace "kema kinsan hakan bamai yuwuwa bane ai", da sauri tace"yo dear mi zai hanashi yuwuwa sai dae in bai sa kanshi auren nata ba but it's possible" d'an ta6e baki kawae yay yana murmushi bai dae ce komai ba.

Suna hawa hanya Najeeb ya fad'i mashi sunan wata shopping mall yace ya kaisu zaima Zarah shopping, kai ya d'aga mashi kawae, bayan sun k'arasa awurin da ake yin parking ya parker Motar Najeeb ya bud'e ya fita kafin ya bud'e ma Fatuu yace ta fito, k'in fitowa tayi ta bishi da ido yace "ko nima sai Ya Handsome din ya baki izini ne?" shiru bata ce komae ba hakan yasa ya duk'a yace ma Haisam "ka bata permission" kallonta Haisam yay ta cikin madubi suka had'a ido da ita ya lumshe mata ido alamar taje sannan ta fita daga cikin Motar Najeeb yai wani Murmushi had'i da jinjina kai yay mata alamar suje,maimakon ta tafin sai ta lek'a ta kopar data fito tace ma Haisam "Ya Handsome banda kai zamu?" d'aga mata kai yay kafin yace "kuje ina nan" janye kan tayi ta rufe kopar tabi bayan Najeeb d'in suka nufi cikin Mall d'in, da kanshi ya d'aukko shopping cart yace ta d'auki duk abunda take so,tsaye tayi mashi tana kallonshi yace "Zarah baki ji mi nace ba?" yay Maganar ya kafeta da lumsassun idanunshi, d'an yamutsa fuska tayi kaman zata yi kuka tace"to ai fa ni ba abunda nike so ina da komae" d'an murmushin gefen baki yay yace"i know,amman ai k'ari baya k'in dad'i ko,ko dae ni baki d'auke ni kaman yayanki bane?" tace "to ai shi an sanshi a gidanmu kai kuma ba'a sanka ba in ka siya man abu fad'a za'ai man", "Owk in muka siyan sai in biki muje gidan in fad'a masu nine na siya maki don kar ayi maki fad'an hakan yayi maki?" shiru tayi sai kuma ta d'aga kai alamar ta yarda, zagayawa suka fara yi yana tura cart d'in saidae sam ta kasa d'aukar komae hakan yasa ya fara daukar mata da kanshi, sosae ya jidar mata kaya har saida tace mashi amman dae duk ba nata bane ko yace to na waye, tana jin hakan tace ita gaskiya sunyi yawa ganin zata yi mashi rigima ne yasashi dakatawa ya nufi wurin biya tana ta faman tura baki sai kace ba abun arziki akai mata ba, bayan ya biya aka juye kayan acikin manyan shopping bags ma'aikatan wurin suka biyo su dasu, boot yace ma Haisam ya bud'e aka zuba kayan kafin ya shiga Motar suka tafi, tambayarshi Haisam yay gida zai dropping nashi ne yace a'a ya fad'i mashi yadda sukae da Fatuu na zaije gidansu ya fad'i shi ya siya mata kaya kar a doketa yayi Maganar yana dariya ya dan juya ya kalleta ta tura mashi baki, shima haisam Murmushi yayi kafin yace ya rabu da ita kawae, gida ya maidashi suna isa mai gadi ya wangale masu k'aton gate d'in ya nufi parking space, tunda suka shiga Fatuu ke bin gidan da kallo har suka tsaya, juyawa Najeeb yay ya kalleta da Murmushi yace "to Zarah gaki a gidana zaki shiga ku gaisa da matana ko?" d'an murmushi tayi batare data ce komae ba hakan yasashi cewa "Oh I forgot, ashe kefa sai Yayanki ya baki permission d'in yin abu kike yi" kallon Haisam yayi yana niyyar magana ya rigashi cewa "permission not granted" dariya Najeeb yasa yace"gaisawa kawae zasuyi nothing else" Haisam yace "Inason na kaita gida before Magrib and it's almost time" ya kai Maganar yana duba wrist watch d'in hannunshi, jinjina kai Najeeb d'in yayi alamar gamsuwa kafin yayi mashi sallama yace sai sun had'u gobe ya juya kan Fatuu yace "to yar bafullatana sai watarana ko don ni gobe zan bar kasar nan" zaro ido tayi alamar mamaki sai kuma tace "ina zaka?", da Murmushi yace "k'asan da nike zaune" da mamaki ta k'ara cewa "amman ba kace nan ne gidanka ba?" "Yeah but bamu cika zama nan ba saboda acan nike aiki sai in munzo" cike da jin dadin yadda ta bud'e baki tana yi mashi Magana yake bata amsa, gyad'a kai kawae tayi yace "ko kina da waya ne mu rik'a gaisawa tunda nima na zama yayanki" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a yace "to ya za'ai,ko shikenan bazamu k'ara gaisawa ba?" shiru ta d'an yi sai kuma tace "in ka kira Ya Handsome in ina nan sai mu gaisa" jinjina kai yay ya sakar mata kayataccen murmushi kafin ya juya ya bude Motar ya fita yace ta dawo gaba, bayan ta koma Haisam yaja Motar Najeeb na d'aga mata hannu har suka fice daga gidan. Tunda suka hau hanya ba wanda yace komae shi idonshi na akan hanya ita kuma tana ta kalle kallenta har suka karaso gida, bud'e Motar tayi ta fita yace ta d'auki abunta data aje a bayan tace to, bayan ta d'aukko ledar kayan da Feenah ta bata juyawa tayi zata nufi gida don duk a gajiye take ganin haka yasashi sauke glass ya kirata, komawa tayi ta tsaya tana kallonshi ta gaban yace "kayan boot wa kika bar mawa ne?" ita sai lokacin ma ta tuna dasu don ta manta tace "to duka zan d'auka?" wani kallo ya bita dashi kafin yace "ke dawa aka siya mawa?" shiru tayi tana kallonshi bata ce komae ba, bud'e Motar yay ya fito ya nufi baya,bud'e boot d'in yayi ya fito da jakunkunan ya aje gefe bayan ya rufe yace ta kai wasu sai ta dawo ta d'auki sauran, maimakon ta daukan sai ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace "to ai gwaggo na iya buguna in taji wani ne ya siya man wannan uban kayan" shiru ya d'anyi sai kuma yace taje ta kira mashi uncle d'inta in yana nan don shagon a rufe yake tana shirin nufar gidan Amadun ya fito yana gyara hannun rigarsa da alama alwala yayi yana ganinsu ya nufi Haisam yana washe baki ya shiga gaisar dashi, bayanin kayan yayi mashi yace ya fad'i ma gwaggon ya amsa mashi da to da sauri ya d'auki shopping bags guda biyu ya nufi gidan Haisam yace ta d'auki dayar ta bishi ya juya zai shige Mota sai yaji tace "kai bazaka dauki komae ba?" d'an kallonta yay bai ce komae ba hakan yasa tace "akwae turare da yawa" sai lokacin ya d'an girgiza mata kai da d'an Murmushi alamar a'a yay shigewarshi Mota,ganin bata tafi ba yasashi sake fitowa yace ta shiga gida sai lokacin ta kai hannu ta dauki d'ayar jakar ta nufi gida tana yi tana waiwayenshi har ta shige sannan ya tafi, Lokacin data shiga a gefe ta samu kayan da Amadu ya shigo dasu gwaggon kuma tana band'aki, aje d'ayar jakar da wadda Feenah ta bata tayi a wurin sauran kafin ta shige cikin d'akinta ta canja kaya zuwa doguwar riga ta fito lokacin gwaggo tayo Alwala tana shirin tada salla tana ganin Fatun tace an dawo d'aga mata kai tayi alamar eh tace taje tayi salla to, saida suka gama sallan ne gwaggon ta jawo jakunkunan ta fara duba kayan ciki fatuu dai na gefe sai zare ido take, uban kayan shafa ne kala kala da turarurruka, takalma jakuna yan kunne fashion harda jallabiyu guda ukku da kuma kananan kaya, tana cikin dubawa Amadu ya shigo don shima yana son ganin kayan da abokin haisam d'in ya siya mata, da tsananin al'ajabi gwaggo ta d'ago ta kalleta kafin tace "yanzu duk wannan uban kayan abokin nashi ne ya siya maki?" da sauri ta d'aga mata kai ta kuma cewa "to hakanan zai kashe uban kud'i ya sai maki kaya har haka sai kace lefe?" da sauri Fatun ta fara mata bayanin yadda ya siya matan har zuwa gidanshi da suka maidashi ta kuma ce mata shine ya bata kud'i masu yawa barka da salla ranar salla, shiru gwaggon tayi tama kasa Magana don mamakine kunshe cikin ranta har fuskarta ta bayyana, Amadu ne yace "su fa masu kudin nan basu d'auki wannan a wani abu ba wllh don haka kar ma ki wani damu" ya juya kan Fatuu yace "inyee kefa yanzu kin zama mai sa'a abun arziki kota ina samu kike bari nima in d'auki rabona to duk da ma bai wuce turare tunda duk abubuwan kune na mata" ya kai hannu bayan ya gama Maganar ya d'auki manyan turare guda biyu yace "na d'auki wad'annan don turaren ma duk na mata ne, daga yanzu in za'ai maki siyayya ki rink'a d'aukko abubuwan maza ba naki kadae ba" ya kai Maganar yana jaddada mata da hannu kafin ya nufi hanyar fita gwaggo ta dan ta6e baki ta bishi da ido har ya fuce, juyawa tayi ta kalli Fatuu data yi mata k'uri da ido ta sauke ajiyar zuciya kafin tace ta kwashe kayan ta kai cikin d'aki an gode Allah ya saka da Alkhairi, a sanyaye fatun ta amsa da Amin, bin ta da ido tayi tana kwashe kayan har ta gama, bayan sallar isha gwaggon ta bata warmer guda biyu babba da k'arama mai dauke da abinci tace ta kai ma Amadu tace ya kai ma Haisam Fatun tace ita takai mashi mana tace a'a dare yayi ta kai ma Amadun, ba don taso ba taje ta kai mashi, lokacin daya kai mashi abincin yana zaune a falonshi yana operating laptop, bayan ya gaida shi yace dama abinci ne gwaggo tace ya kawo mashi shiru ya d'anyi don shi ba kowane abinci yake ci ba da daddare yafi son mara nauyi duk da baisan miye aciki ba, godiya yayi mashi bayan Amadun ya tafi ne ya bud'e babbar warmer din mai dauke da farar shinkafa da taliya sai k'arama kuma miya ce aciki harda nama rufewa yayi ya d'auki wayarshi ya kira tk, tambayarshi yayi yana gida yace mashi eh yace ya kawo mashi plate da spoon ya amsa da to, bada jimawa ba sai gashi ya kawo masan bayan ya gaidashi yana kokarin d'aura plate d'in kan c-table haisam din yace ya wanko mashi su a basin ya amsa da to, bayan ya dawo ya d'aura kan c-table d'in yace "shikenan Ya Haisam?" alamar ya tsaya yayi mashi da hannu saida ya k'arasa abunda yake a laptop d'in sannan ya kalleshi yace "a ina kake cin abinci ne?" dariya tk yayi yace ina dafawa ne" jinjina kai yayi ya bashi umarnin ya zuba mashi abincin dake a cikin warmer d'in ya amsa da to, yana zuba d'an kad'an yace ya barshi haka ya bude miyan ya zuba mashi naman ma yana sa tsoka biyu yace ya isa,umarnin ya d'auki warmers din abincin yaje yaci ya bashi yace in ya gama ya kai warmers din gidansu Zarah ya amsa da to, har zai tafi sai kuma ya dakata cike da kulawa yace "amman ya Haisam wannan abincin kaman yayi kad'an ba zai kosar da kai ba" maida bayanshi jikin kujera yayi fuskarshi asake yace ba wani abu zai ishe shi yaje kawae,

"to ko in had'o maka tea?" Tk d'in ya tambaya, shiru ya d'anyi sai kuma ya d'aga mashi kai alamar eh, cike da jin dadi ya nufi hanyar fita shi kuma ya fara cin abincin ba'a dau wani dogon lokaci ba Tk ya kawo mashi tea d'in ya zauna yana mashi yar fira har ya gama ya dauke abubuwan abincin kafin yayi mashi saida safe, cigaba da abunda yake yayi wayarshi ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka, Murmushi ya saki ganin mai kiran nashi wato Hajiya, handsfree yasa ya aje wayar agefe hajiyar tayi mashi sallama, "Sweetheart hope u'r work" ya fada idonshi akan screen, "Lafiya lou nike kaifa?" "Same" ya bata amsa a takaice,

"Yau mi kaci ne?" ta tambaya, har saida ya d'anyi Murmushi kafin yace mata abinci, tace "da safe kaci abinci?" yace mata eh yaci a wurin aiki, ta tambayi da rana fa yace mata yaci a gidan Abbas, "To yanzu da daddare fa?" ta sake tambaya, d'an girgiza kai yay kafin yace "in kin damu da wannan ki dawo mana" a d'an fad'ace tace "nima ai nan d'in kaman akan k'aya nike kawae banda yadda zanyi tunda an fi karfi na" dariya yayi har hakoransa suka bayyana kafin yace gidansu ne k'ayar tace eh mana, "Pls tell me kaci abinci yanzu kuwa, kodae insa Saude ta dawo ne dama don nasan tukur ya iya dafa abinci shiyasa nike kyaleta sai na dawo itama ta dawo amman yanzu ko don kai inaga zan sa ta dawo kawae tunda a gaban idona ma ba son ci kake ba balle yanzu da bani ba kuma mai dafa makan" d'an ta6e baki yay kafin yace ta kyaleta kawae sai ta dawo tace to ya fad'i mata abunda yaci yanzu,

Readers Also Read