Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 45
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 45: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 45. .......Babban d'aki ne mai d'auke da abubuwan…
4,308 words
.......Babban d'aki ne mai d'auke da abubuwan sarauta irin na gargajiya, lokacin data shiga zaune ta iskeshi akan kujerar da yake zama tare da wani babban Mutum yayi shiga ta alfarma yana zaune akan kujera daga gefen ardon da gani kuma wayayyan d'an boko ne kuma kana kallonshi zaka gane shima bafullatani ne, ard'on tsoho ne sosae don duk gashin fuskarsa hurhura ne ba bak'in gashi ko kwaya d'aya haka ma kanshi duk da a rufe yake gashi d'an tsamurmuri dashi wato baida jiki kwata kwata hakan kuma nada alak'a da tsufan da yayi sosae amman k'yam yake yana gani kuma yana ji amman dae tafiya saida sanda yake yi, da zasu shiga mino ce tayi sallama duk suka amsa harda mutumin ta duka k'asa kan shimfida ta gaishe dasu duk suka amsa ita kuwa Fatuu gaban ard'on ta nufa tayi mashi tsaye tana bin fuskarshi da kallo shima idonshi na akanta ya d'an k'ank'ance su da alama so yake ya gane wacece ita, haka shima wanccan mutumin da mino kallonsu suke, tambaya yayi wacece ita maimakon ta bashi amsa sai ce mashi tayi "wai har yanzun kana nan baka mutu ba?" da fullanci tayi Maganar jin hakan yasa nan take ya ganeta don kaf zuriyar gidan ba wanda zai iya mashi hakan in ba itan ba dama kuma yasan da zuwan nasu, hannu ya kai gefenshi ya janyo wata zungureriyar sanda zai buga mata ta ja baya da sauri tana dariya yace mata har yanzu shed'anun da ke kanta na nan kenan, tura mashi baki tayi yace ta girma amman har yanzu bata iya gaisuwa ba bata ga mutum ba in shi bazata gaidashi ba, juyawa tayi ta kalli Mutumin ta gaidashi ya amsa mata yana Murmushi sannan ta juya ta gaida ardon bai amsa mata ba sai ya nuna mata gabanshi yace ta zauna tace ai bugunta zaiyi yace bazai bugeta ba ai ita bak'uwa ce yanzu, zama tayi tana fuskantarshi yace to ta gaidashi yanzu bayan ta gaisheshi ne yace ta dawo ko tace a'a, "Ai kuwa bazan bari ki koma ba aure zanyi maki kin yi girma da yawa" ya fad'a da fullanci cikin dusashshiyar murya ta tsufa, tura mashi baki tayi tace "na rantse ba mai mani aure sai nagama karatu na zama likita har na fara aiki sannan zanyi aure kuma ni zan za6i mijin ba wani ba" jinjina kai yay kafin yace zata gani in zai barta ta koman,wani kallo tayi mashi tace "in ka hana ba sai in gudu ba ai nasan hanya" shiru yay yana ta binta da ido da d'an Murmushi tace "an kawo maka tsarabar dana kawo, koda yake kai bazaka iya cin biscuit ko chocolate da wannan bakin naka ba daba hakora kaman na......" bata k'arasa ba ya k'ara d'ago sandar taja baya daga zaunen tana Fad'in ita fa yanzu budurwar birni ce tafi karfin a bugeta yace ta matso taga in bai bugetan ba, su dai su mino sai Murmushi suke, jin tace sai tagama karatu ta fara aiki ko zata yi aure yasa Mutumin ce mata "What's ur name?" kallon Mutumin da yayi mata tambayar tayi sai kuma ta bashi amsa itama da turancin cigaba da yi mata tambayoyi yay game da alakarta da ardon da inda take da kuma yanayin karatunta duk da turanci ta rink'a bashi amsa itama, sosae ya yaba da yadda take turancin ba wani gargada ko tangard'a har ya tambayeta a Katsinar private skul take yi ne tace mashi a government skul ce nan take ya fahimci tana da kokari sosae mino dai na gefe tana kallonsu suna turancin gwanin burgewa don tasan yaren da suke saboda tana zuwa makaranta itama saidae ba wani turanci take ji ba inba dan guntu ba kaman tambayar sunan mutum haka shima ardon yasan yaren nasara ne suke yi bayan sun gama ta juya ta kalli ardo da ya zuba mata ido tace "kai fa baka san mi muke cewa ba ko?" d'an Murmushi yay kafin yace "kin zama nasara bama wanda zai aure ki sai nasaran" da sauri tace "ai nima ban iya auren d'an garin nan don duk basu da ilimi basu iya komae ba sai noma da kiwo samarin birni kuwa irina suke so don haka in na tashi aure sai ma na za6a" ta k'arasa tana murmura mashi baki shidae Mutumin sai Murmushi yake can ardon yace ta tashi su shiga ciki yana tattaunawa da bak'o tace to kafin suka mik'e tare da mino suka nufi hanyar fita, Bayan sun fito waje ta nufa don taga in kawu Amadu na nan ya kira mata Ya Handsome, koda ta duba inda Kamalu ke saida rake bataga kowa ba baima fito da raken ba acan gefe ta hango Mota Jeep dake ajiye ta kalli mino tace Motar mutumin ce tace mata eh tace wanene shi Minon tace "Chairman ne Alhaji lawal shine mai katon gidan gonar bakin gari da ardo ke kulawa" d'an ta6e baki tayi kafin ta juya suka koma ciki ta nufi d'akinsu nan ma basu nan ba don taso ba suka koma cikin gidan ganin sun nufi hanyar 6angarensu yasa mino cewa "Adda Fatuu bazaki gaishe da yaya ba?" tura baki ta d'anyi sai kuma ta tuna da Maganar da suka yi da Haisam hakan yasa ta juya tace suje, lokacin da suka je sashen yayan wadda take uwargidan Ard'o tana zaune gefen gadon karfe babbar mata ce jajur da ita tana da tsaga a bakinta kuma tana da jiki ba laifi ta manyanta sosae daga gefe da gefenta mata ne zaune harda kishiyarta guda da kuma matan ya'yanta guda ukku su biyar kenan dama haka suke wuni wurinta suna mata fadanci aita gulmace gulmace, mino ce tayi sallama suka shiga ba tare da sun amsa ba duk suka d'ago suna kallonsu saidae gaba d'aya idanunsu na akan Fatuu ne itama ta lura da kallon da suke matan hakan yasa ta wani sha kunu don tasan bana arziki bane, k'asa mino ta tsugunna tana gaishe da yayar kaman an mata dole ta amsa kafin ta kalli Fatuu da tayi mata tsaye k'erere aka tace ita bata iya gaisuwa bane tayi Maganar tana k'are mata kallo tun daga sama har kasa dama tunda suka zo aka kawo mata gulmar yadda Fatun ta koma wai kaman yar shekara ashirin, gaida ita tayi kaman yadda ta bukata amman sai tak'i amsa mata wai a haka zata gaishe da ita ba ladabi abunda ake koya mata a binnin kenan rashin da'a, sai kace dama da Fatun na garin ladabin take mata, idonta cikin nata tace "to ai ba abun zama" fuska a d'aure tace su sauran a ina taga sun zauna tace "a k'asa ni kuma ban saba zama kasa ba ai" shiru tayi tana kallonta yayin da sauran suka hau jinjina kai alamar al'ajabi, d'an Murmushi da bakai zuci ba Yayan tayi tace ta manta itafa yanzu yar birni ce ta kalli mino ta nuna mata buzun salla tace ta d'aukko mata, shimfida mata tayi tace adda ki zauna cike da kyankyami tana d'an yamutsa fuska ta hau ta zauna suna dae ta bin ta da ido, ganin ta zauna bata gaishetan ba yasa Babar Altine data ta6a karyama kafar kaza cewa "to sai ki gaishetan ko!" wani kallo Fatun tayi mata dama itama sam basu shiri kafin ta kalli Yayan ta gaidata kasa kasa, d'an ta6e baki tayi ta amsa tace ya birnin ta bata amsa da lafiya lou daga haka kuma suka d'an yi shiru Fatun na kallon gefe yayin da Yayar ke k'are mata kallo can tace "amman kin dawo ne ko" ba tare data kalleta ba tace "a'a ai karatu nike" jinjina kai tayi sai kuma tace "amman yakamata yanzu ace kinyi aure har kin haihu ma" wani kallo ta juyo tayi mata mai kaman harara a d'an harzuke tace "ni ba wani aure da zanyi sai na gama karatu na fara aiki" gaba d'aya kowa kallonta yake da mamakin yadda take ma Yayar Magana, d'an Murmushi tayi bata ce mata komae ba ta kalli d'aya daga cikin matan dake zaune tace "Bimbi in kin gama dama furan ki zuba ma bak'uwar birni" Fatuu na jin hakan tace ta koshi don tasan ba har zuci tayi maganar ba, mik'ewa tayi tace ma Mino ta taso su tafi tayi masu sallama suka tafi, tana fita matan suka hau jinjina kai suna fad'in an idasa lalata yarinya kawae wata tace yo dama an kai yarinya birni ai dole ta lalace Allah ma yasa bata san maza ba don yadda take Magana tsaitsayen nan sai dae ace Allah ya kyauta kawae wata tace ai tabbas ma wannan tasan maza daga ganin jikinta, ita dae Yayan nata saurarensu Allah kadae yasan abunda take kullawa acikin ranta don gani take fatun ta wulak'anta tane duk da ba yanzu ta fara yi mata hakan ba amman tafi jin ciwo don tana ganin yanzu ai ta mallaki hankali. Duk yadda taso tayi Video call da Haisam ranar abun ya faskara don yinin ranar Amadu bai nan sun fita tare da kamalu basu suka dawo ba sai bayan Magrib saidae tayi waya dashi kawae, washe gari ya kama Monday kwanansu biyu da zuwa a ranar gwaggo taso komawa saboda aiki amman suka rok'eta ta d'an k'ara ko kwana biyu ne cikin masu rok'on nata harda Fatuu kaman zata yi mata kuka hakan yasa ta hakura sai ranar laraba zata tafi, ranar da yamma tana sanye cikin Jallabiya ta d'aura kallabi akanta ta nufi kopar gida tana zuwa ta iske Amadu zaune saman benci gaban teburin raken Kamalu, gaidasu tayi tace don Allah ya kira mata Ya Handsome video call yace dama yasan ba gaisuwar Allah da Annabi bace to bai kira, rokonshi ta fara yi harda tsugunnawa k'asa Kamalu dae nata dariya don yar tsamarsu burgeshi take, saida ya gama ja mata rai sannan ya kirashi ya bata ta sanar mashi zasu yi Video call din bayan ya d'auka ta gaidashi ta sanar mashi ya amsa da owk, mik'a ma Amadu wayar tayi tana ta faman washe baki ya fara kokarin kiran nashi sai dae da yayi connecting sai kuma yayi disconnecting da kyar ya samu yayi ya mik'a mata, ta fara murnar ganin haisam d'in kenan kiran ya datse rai 6ace ta sanar ma Amadun yace to sai tayi hakuri ba network mai kyau, rokonshi ta fara yi ya daka mata tsawa yace to shine zaisa shi yayi, Kamalu yace in suna son network sai sunje bakin gari acan ake samu ta fara rok'on Amadun ya bata wayar taje can tayi, wani kallo yayi mata yace "matsalata dake baki da cikakken hankali nine zan baki wayata kije bakin gari salon a kwace man waya ko" Kamalu na dariya yace " a'a mu garinmu ba'a kwacen waya wama yasan yadda zai yi amfani da ita balle ya kwace ai sai d'aid'aikun Mutanan da yawanci ma ba a garin suke zaune ba" jin haka ta hau yi mashi magiya da k'yar ya bata yana jaddada mata tabi mai waya a hankali ta amsa da to cike da zumudi ta juya da gudu ta nufi bakin garin Amadun ya d'aga murya yana karfa ta fasa mashi waya, yar tafiya ce tayi ta isa wurin cikin sa'a tana kiran nashi yayi lafiya lou lokacin haisam d'in na kishingide kan gado tana ganinshi ta washe baki ta kira sunanshi, amsa mata yayi yace tana lafiya tace lafiya lou, "Ya Handsome ka koma Katsina ne?" girgiza mata kai yay tace "har yanzu kana Lagos d'in kenan" yace "Yeah ban gama abunda nazo yi ba sai tomorrow zan tafi, "to yanzu kana ina na ganka kwance ko Hotel?" girgiza mata kai yay "Nah" ta k'ara cewa to yana ina yace yana gidan Mommynshi ta Lagos tace mai auren Bature ya d'aga mata kai alamar eh wai harda cewa ina yake ta ganshi yace bai Nigeria, fira suka ci gaba da yi harda ce mashi wllh tayi missing d'inshi shima yayi nata yayi mata Murmushi kawae, can tace "Yauwa Ya Handsome don Allah jibi gwaggo zata taho kace ta taho dani pls" da d'an Murmushi ya girgiza kai yace "why, ba already kun gama magana ba" turo baki tayi sai kuma tace "to kai ka biyo ka d'aukeni" yace mata ai ba'a Mota zai dawo ba tace a jirgi yace eh,
"Yauwa to tunda a jirgi ne ma kaga sai kace a biyo nan da kai zaka d'auki k'anwarka in kuka zo sai a zuro man igiya yadda ake yi a film sai kawae mu tafi in muka koma gida sai in kira su gwaggon in sanar dasu ni na koma gida" shiru yay kawae yana binta da kallo kaman zai yi dariya a shagwa6e ta langa6ar da kai tana ce mashi don Allah da bud'ar bakinshi sai ce mata yay "yaushe zaki girma Zarah" wani kallo tayi mashi tace "bana girman ba" d'an shaking head d'inshi yay alamar a'a bata girma ba ta tura baki tana cewa ita ai ta gaji da garin ne gida take son dawowa yace ta kwantar da hankalinta kaman gobe ne, ganin suna ta Magana bai ganin komae sai shuke shuke yasashi tambayarta tana ina ne tace tana bakin gari nan keda network ta juya wayar tana nuna mashi wurin yace bata jin tsoro ita kadae tace tsoron mi ai koda daddare zata iya zuwa wurin ba abunda zai sameta, yar hira suka k'ara yi yace ta koma gida Magrib ya kusa tace to amman kar ya kashe zata tafi suna hira har tazo inda ba Network yace owk, tafiya take ta raba hanya biyu tana bashi labarin garin nasu da yadda kowa ke mamakin girman da tayi a haka har tazo inda ba Network kiran yay disconnect da kanshi lokacinne kuma aka danna wani irin Horn mai karfi a bayanta har saida ta tsorata ta juya da sauri, da mamaki take bin Motar da tayi mata horn d'in da kallo wadda peugeot ce 406 irin wadda ta fasa ma glass lokacin da haisam ya mareta saidae ba Colour d'insu d'aya ba Wannan Navy blue ce, ganin tayi tsaye kan hanyar yasa na cikin Motar sauke glass a harzuke yace "ke mahaukaciyan inane nan d'in d'akin uwarki ne da zaki raba hanya biyu anata maki horn bazaki matsa ba!!" da hausa yayi mata Maganar don daga yanayin shigarta ya fahimci ba lalle in yar rugar bace, sototo tayi tana binshi da ido da alamar mamaki a fuskarta taji ya k'ara cewa "bazaki tashi man a hanya ba sai na bi ta kanki ne", a fusace tace "to shine sai ka zagar man uwa dake kwance cikin k'asa" bud'e Motar yay a fusace ya fito, dogo ne sosae don har yafi haisam tsawo saidae sam baida jiki yana sanye da jeans da t-shirt kallo d'aya zakai mashi ka gane bafullatani ne daga yanayin fatar jikinshi dake fara sannan sumar kanshi ma a nad'e take duk da bata da tsawo sosae kallonta yay a k'ule yace "Who d hell are u da baza'a zageki ba!" kallon up and down tayi mashi kafin tace "to wllh duk da an hana ni rashin kunya bazan kyaleka hakanan ka zagar man uwa ba don haka badae uwata ba" kallon mamaki ya bita dashi yace "badae zagina zaki ba!" tace "ai baka ji na zage kaba ko amman dae kasan in Mutum ya zagi iyayen wani bai rama ba to nashi ya zaga don haka taka ka zaga" a fusace ya idasa fitowa tana ganin hakan ta fara tattare rigarta dama akwae dogon wando a ciki nan take ya gane guduwa zatayi hakan yasashi tsayawa suna kallon kallo ta kumburo mashi baki, juyawa yayi ya koma cikin Motar dama a kunne take ya rufe tana dai tsayen bata kauce ba aikau ba zato ba tsammani yayo kanta da Motar tayi tsalle gefe guda hakan baisa ya kyaleta ba yayi kanta gadan gadan aikuwa ta watsa a guje don ta lura yafita hauka kan kace mi tayi mashi nisa don hanyar akwae yashi ya hanashi yin gudu sosae yana ganin ta 6ace ma ganinshi ya wani daki steering Motar yaja dogon tsoki abunda yafi bashi takaici wai ace wannan yar kankanuwar yarinyarce zata zageshi jan Motar yay ya k'ara yin gaba kafin ya karya wata kwana,
Ranar laraba tunda sassafe gwaggo tayi sallama da kowa bayan an had'a mata sha tara ta arziki su Fatuu ne yan rakiya saboda Baffanta ne zai kaita jimeta a Motarsu Hijet da suke kai kaya kasuwa daga can sai ta hau Motar Katsina ko Kano, ita da Fatuu da kamalu da Mino ne abaya sai gaba Baffanta da Amadu Fatuu harda kukanta na atafi da ita, banza gwaggon tayi da ita sai yadikko ce ke rarrashinta tana cewa tayi hakuri ta k'ara kwanan masu biyu basu gaji da ganinta ba kuma in ta tafi ai sai an k'ara ganinta ko, Bayan sun dawo daga raka gwaggo kwance tayi saman gadon tana matsar kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita lokacin data farka ne yadikko ta nuna mata abun karin kumallonta, bayan ta wanko bakinta rai a jagule take tsakuran abincin ganin tak'i sakin jiki yasa yadikkon ce mata tayi sauri ta gama ta shirya suje cin Kasuwar babbar hanya ita dasu mino tace bari ma tayi ma Kamalu Magana don tasan duk sati yana zuwa sarin rake, tana jin hakan ta d'an ji sanyi bada jimawa ba yadikkon ta dawo tace tayi ma Kamalun Magana zasu tafi tare, wuraren karfe sha biyun rana sun gama shirin zuwa kasuwar Fatuu tasha ado da shaddar da haisam yayi mata da babbar salla sosae yadikko da k'annenta ke yaba kayan bata 6oye mata ba tace ai Ya Handsome ne yayi mata don dama kullum ne sai tayi masu firarshi kaf ta basu labarin abubuwan da yake mata sosae suke yaba kirkinshi da kakarshi Hajiya, cike da tsokana yadikko tace kodae saurayinta ne don wannan hidiman tayi yawa, da sauri ta girgiza mata kai tace a'a ita ai bata da saurayi don karatu take son yi ta zama likita kuma shima baiyin soyayya koda ma zaiyi bazai yi da ita ba tunda ita karama ce shi kuma babbane kuma d'an gayu ita yadikko dan ta6e baki kawae tayi, itama Mino kwalliyar shaddar tayi cikin kayan da aka bata gwanin sha'awa yadikko ke kallonsu inda so samu ne Fatun ta dawo hannunta saidae ita kanta tafi mata sha'awar zama acan hannun gwaggon, lokacin da suka fito tsakan gidan gaba daya wadanda ke wajen sakin baki sukae suna kallonsu ciki harda Altine da tayi ado da kayan fulani suma zasu cin kasuwan ko ta kansu Fatun bata bi ba sukae fucewarsu a waje suka samu Kamalun harda ma Amadu shima yayi gayu da kananun kaya ba 6ata lokaci suka kama hanya, tun akan hanyar ake ta faman binsu dana mujiya don ba'a saba ganin irin shigar da suka yi ba wasu mutanen da basu iya hakura har tambayar Kamalu suke wai bak'i sukae ya basu amsa da eh wadanda suka san Fatuu kuma ya gaya masu itace da al'ajabi suke kallonta koda suka isa kasuwar ma nan ma dae abun kallo suka zama sai kace ansamu tv anan kuma suka hade da Jibo Mutumin da shine sanadin komawar Fatun Katsina wato wanda ta jefar ma Akuya ta mutu, yana sanye cikin shigan Fulani riga da wando da takalma fatalo shima kasa hak'uri yay ya tambayi Kamalu bak'in binni sukae yana dariya yace ya kalli Fatuu da kyau ya santa, k'ura mata ido yay saidae sam ya kasa gane wacece har saida Kamalun yayi mashi bayani sannan ya ganeta, cike da al'ajabi yake kallonta baki bude harda cewa ai shi yaga Mata wllh a tsiwace Fatun tace mashi Allah ya kyauta ta aureshi ko maza sun k'are mi zatayi dashi yadda tayi maganan yasashi cewa da kwarankwatsa itace kuwa sudae su Kamalu nata dariya, zagayawa sukae cikin kasuwa suka danyi siyayya yawanci duk abubuwan ci ne akafi saidawa su Awara, kosai, rake, danyen nono harda madarar shanu da kuma kayan noma sai yamma liss suka koma gida don daga kasuwar zagaya garin sukae har k'oramar dake bayan gidansu suka je mai tarin ni'ima da wadatar kayan itatuwa suka yi hotuna.
_____________
Ranar Juma'a lokacin kwanansu Fatuu shidda da tafiya bayan sallan juma'a iyalan Senator harda shi sanatan da kuma Hajiya Maryam itama da nata iyalin suka sauka Katsina, Senator da Matansa guda biyu Mahaifiyarsu Haisam sai kishiyarta da suke ce ma Aunty da k'annen Haisam d'in guda bakwae don su takwas ne ya'yan Senator d'in ita Aunty bata haihu dashi ba sai dae akwae diyarta guda d'aya data Haifa da tsohon mijinta a wurinta don ba'a budurwa ya aureta ba kuma likita ce sa6anin Mahaifiyarsu Haisam ita full house wife ce bata aiki tunda Senator ya aureta da k'yar ya barta ta k'ara yin karatu anan amman tun lokacin data gama ya hanata yin aiki, k'annen haisam akwae Laila ita ke bi mashi wadda yanzu haka take karatun likitanci a k'asar Malaysia kuma ita Mahaifinsu ta biyo saidae ba bak'a bace ta d'an d'aukko hasken Mahaifiyarsu ba sosae ba sai Nameer shi yanzu ya gama Secondary skul sai kuma Hauwa'u mai sunan Hajiya suna ce mata jidderh zata yi shekara sha biyar zuwa sha shidda yanzu zata shiga s.s two sai Yasmeen dake j's 2 sai Adams mai sunan kakansu suna ce mashi Affan sai twins wanda sune auta wato Mubeen da Mubeena zasu yi shekara hud'u kusan gaba d'ayansu hasken Mahaifiyarsu suka d'ebo ba kamar Haisam Nameer jidderh da twins sun fi sauran fari sosae, a 6angaren Hajiya Maryam kuwa yaranta biyar saidae da guda hud'u tazo don cikon d'ayar wato Fanan bata k'asar sai Farha wadda ita ke bima Fanan d'in sai ibraheem suna ce mashi abraham sai muhammad da yar auta Noor itama sunan Hajiya gareta, a wata dankareriyar Hummer jeep aka je d'aukar Senatorn sai Haisam da shima yaje da Benz d'inshi sai kuma Tk da yaje da Jeep d'in Hajiya, cikin shiga ta Alfarma suka iso Arrival daka kallesu ko baka san su waye ba zaka fahimci akwae masu gidan rana ba kad'an ba a tattare dasu, Mahaifiyar Haisam wato Fateema tana sanye da wata jugunannan jallabiya da tasha adon stones sai d'aukar ido take tayi rolling veil d'in kallo d'aya zaka yi mata ka shaida balarabiya ce tun daga kan kalar fatarta da kuma suffarta don giant ce tana da tsawo da kuma jiki sai dai ba jiki sosae ba daidai, sai Hajiya Maryam ma tana sanye da dandatsetsen leshi red color mai touch din ash tasa gyale ash da takalma da jakka ash sai sarkar diamond dake wuyanta da agogo harda zobensu itama babbar macece saidae bata da tsawo sosae daka kalli fuskarta kuma zaka shaida kamanninta da Hajiyar Sanata sosae, shima mai gayya mai aikin wato Senator Alee zakee yasha farar shadda ta alfarma wanda basai na tsaya fadan kalan takalmi da hula da agogon hannunshi ba don kowa yasan na alfarma ne suma, Mutum ne mai tsananin haiba da cikar kamala ga kwarjini shima giant ne don sak Mahaifinsu shi kuma ya biyo wato Gen. Adamu zakee, su Jidderh da Laila sun ci gayu da had'addar embroidery atampa anyi masu riga da skirt kowacce ta d'aura gyalenta a kafada su kuma mazan suna sanye da jeans da t-shirt wasu rigunan polo ne sabbi dal, a 6angaren yaran Hajiya Maryam kuwa gaba d'aya yaran Mahaifinsu suka biyo hakan yasa daka kallesu zaka gane turawa ne tun daga kan kwayar idanuwansu da kuma sumar kawunansu, Farha na sanye da skinny jeans ya kamata had'i da farar top ta d'aura boyfriend jacket wadda gabanta ke hangame haka kafad'ar rigar a zame take, kaman yadda k'wayar idonta ke ash haka ma gashin kanta daya fito duk da akwae gyale bak'i akanta haka kafafunta na sanye da takalma bak'ak'e masu tsini sosae tana ruke da yar purse silver, shima Abraham kwayar idonshi brown ce kalar ta Fanan haka sumarshi ma take, Mohammed irin kwayar idon farha gareshi wato ash amman sumarshi bak'a ce sai yar auta Noor wadda ba k'aramar kyakkyawa bace tana da kwayar ido blue ga yalwatacciyar sumarta bak'a ce, suna hango haisam dake tsaye yana sanye da bak'in jeans da polo shirt yellow haka agogon hannunshi baki ne yayin da glass d'in ke bada launin yellow mai shining haka idanunshi ma na rufe da glass shima mai d'an launin yellow abun saidai ace ma sha Allah kawae, su Jidderh na hango shi suka nufo shi da d'an gudu gudu suna fad'in "Bro...." da Murmushi ya bud'e mata hannuwa ta fad'a jikinshi tana ta dariya side hug Laila tayi mashi tana murmushi, janye Jidderh yayi daga jikinshi ya janyo Yasmeen dake ta kokarin ture Jidderh don itama ta rungume Haisam d'in, yana rungume da ita ya hango su twins da sukae tsaye gabanshi sun kumburo baki alamar fushi dama gasu tubarkallah bul bul dasu da gani ba k'aramin 6arna da Madara suke ba kuma identical twins ne suna bala'en kama da juna gwanin sha'awa suna sanye da jeans da t-shirt kala d'aya wato unisex, janye Yasmeen yay ya duk'a ya bud'a masu hannu alamar su taho kawae sai suka had'e bayansu suka kalli 6angare daban daban, sanin halinsu rigimammu ne yasa ya nufesu duk da k'ibarsu suna a had'en ya d'agasu sama gaba d'aya aka sa dariya harda su, sauke su yayi ya nufi Mahaifiyarshi wadda sak ita ya biyo daka kalleta zaka gane cewa mahaifiyarshi ce rungume juna sukae a gefen kunnanshi a hankali ta furta "Habibie", d'agowa yay yana Murmushi kafin yace wani abu Hajiya Maryam tace "dayake bani na haife ka ba shiyasa ko kallo ma bazan samu ba ko" k'ayataccen Murmushin gefe ya sakar mata kafin ya yi mata side hug yana fad'in "So sorry lovely Mom", kallon Auntynsu dake gefe yay tanata Murmushi itama Maroon Abaya ce ajikinta murmushi yay mata ya gaidata tare da dan kama hannunta ta amsa mashi,