Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 7

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 7

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 7: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 7. Haisam ne ya d'ago da kansa ya kalli kawu Mani yace…

4,451 words

Haisam ne ya d'ago da kansa ya kalli kawu Mani yace "ina yini Uncle" sannan ya juya ya gaida sauran cikin muryarsa mai cike da natsuwa,a tare harda kawun suka amsa mashi da "Lafiya lau", "Haisam ne d'an gidan Hajiya" kawun ya tambaya da fara'a "Eah" haisam yace a tak'aice, kawu yaci gaba da magana "Masha Allah,Haisam ya karatun? Kafin ya bashi amsa Hajiya tace"Ai ya gama,yanzu haka yaci gaba da aiki a nan garin yana nan AIRPORT" da mamaki yace "Wai yanzu har ya gama karatun? Kinsan kafin ya tafi nazo nan muka had'u lokacin kike ceman zai tafi yin Master's Degree a U.S" tace"Aikuwa dai gashi har angama" jinjina kai kawu yayi yace"Time really flies,Allah yasa mudace" hajia tace "Aikam lokaci fa na gudu,Amin ya Allah",sauran ma suka amsa da"Amin", Kallon Haisam yayi yace "Haisam yanzu sai Aure ko,nasan yanzu ai ka kai 30yrs ko?"yayi maganar yana yar daria,d'an guntun murmushi haisam yayi kafin yace wani abu wayarsa ta fara ringing ya mik'e yace masu"Excuse me.." daga haka ya fice, Hajiya dake ta fara'a tace "bai ida shekara talatin ba yanzu ya shiga 29yrs yanayin jikin ne sai ka ce yama wuce 30,dama kuma ga daga karfe yana yi,Auren kuma tukunna dai sai nan gaba in zai koma" Kawu yace "karatun zai k'ara komawa ne? tace"Eh zai koma U.S d'in amman ba karatu zashi yi ba duk dama yace zai kara karatun in ya koman,akwai wani babban Company ne daya danganci karatun da yayi na Computer Engineering suna k'era kwamfutoci da sauran abubuwan su na fasaha dai,shine suke son yin aiki dashi,duk da yanzu haka matsayin Agent d'insu yake anan k'asar,to kasan Uban nashi akwai kishin k'asa,da k'in yarda yayi,sai da Haisam d'in yayi mashi bayanin dalilin daya sa yake son yaje can yayi aiki dasu sannan fa ya aminci amman yace sai ya k'ara yima k'asar shi koda na shekara biyu ne,don gani yake suna iya rik'e shi...." a d'an harzuk'e Kawu Mani yace"Very thougthful of him,wallahi Senator yayi man daidai,don ma bansan dalilin daya sa Haisam d'in ke son zuwa ba,da nace dama gaba d'aya ya hana shi,haba! for how long zamuyi tayin shuka su suna girbe amfaninta,sam wallahi mutanen nan basu son cigaban mu,shiyasa da sunga mutumin mu mai hazak'a sai su bukaci yayi aiki dasu,su kuma mutanen mu sam basu kishin k'asar su,what they're after is the money,su dai kud'i kawai,basu tunanin suma su gina tasu k'asar,koda bazamu iya kamo su ba,mu ha6aka tamu kasar ta yadda zamu daina relying kansu,d'an abunda bai kai ya kawo ba ace sai anfita waje" ya d'an tsaya ya sauke numfashi,sannan ya juya kan mutanen da ya zo dasu ya ci gaba"Wallahi Alhaji Sa'idu karka so kaga yadda mutanen nan ke cin moriyar mutanenmu sai ma kaje asibitocin su zaka sha mamaki yawanci sai kaga manyan likitocin da suke masu aiki duk mutanenmu ne....." Hajiya ta katse shi da fad'in "tabbas,don akwai lokacin da muka kai marigayi Minister da yayi wani ciwo kasar Germany,wallahi likitan dake duba shi mutuminmu ne,kuma ma d'an nan Katsina don bayan mun dawo har zuwa yayi duba lafiyar tasa..."Kawu Mani yace "You see...shine maganan da nike,suna can wasu na amfanuwa dasu sun bar mu nan munata fama da rashin k'wararrun likitoci". Ya juya kan hajia"Wallahi hajjaju mostly likitocinmu yanzu ain't qualified,yan kad'an ne suka san aikin su,wai sai kaje asibiti ko ka kai wani naka,abun haushi kana ma likita bayanin matsalarka sai kiga ya fiddo waya yana googling...wai sai ya tura ma google duk abunda aka bashi shi zai jibga maka kuji fa don Allah wanda ada sam ba haka likitocinmu suke ba k'wazo ne dasu" gaba d'aya suka jinjina kai cike da takaici, Wanda kawu ya kira da Alhaji sa'idu ya fara magana "A haka kuma wasun nasu sai d'an karan wulakanci,haka zakai ta jin Labaru maras dad'i da suka faru a dalilin wulakanci da kuma sakacin da bai kamata ace ma'aikacin lafiya ne yayi hakan ba,wanda na tabbatar in a k'asar wajen suke yin aikin kwatankwacin hakan basu isa suyi ba,ba tare da an d'au kwakkwaran hukunci akai ba" gaba d'aya suka jinjina kai hadi da fad'in "Sosai kuwa", Na karshen ne wanda bai kai su girman jiki ba,shima ya fara magana"Wato Alhaji Mani duk matsalolin nan sun fara ne tun daga tushen fara karatun,yadda yakamata ace ana koyawan ba haka ake koyawar ba ayanzu karatun duk ya ta6ar6are shiyasa masu halin sai su d'auke yaransu su tura su kasar waje karatu,su kuma da sun ga mutum nada basira sai su rik'e shi suna biyan shi kud'i masu yawa,wanda yasan baza'a iya biyansa kwatankwacin su ba a k'asar shi dama kuma ba itace a gaban shi ba,taci gaba ko karta ci gaba shi ba ruwanshi,su kuma maras halin da basu da wani zabi da ya wuce dole su tsaya nan suyi karatun a wahale gashi yawancin malaman sun maida karatun kasuwanci,da abunda d'alibi yakamata ya kashe kudi da wanda bai kamatan ba duka kashe kudin yake,gaba d'aya yanzu karatun d'an talaka ya zama wahala yan kadan ne ke iya jurewa su gama,shiyasa in suka fara aikin sai kaga kaman suna ramuwar gayya ne,ba malaman asibitin ba,ba malaman makarantar ba da dai sauransu,kowa bai tunanin duk abunda yayi ma wani zai iya juyewa kan nasa...., "To Al'amarin kasar tamu dai sai Addu'a kawai amman muna bukatar mu canza halayenmu inba haka ba,haka zamuyi ta zama jiya iyau abubuwa duk suna ta ta6ar6arewa,kowa damuwarsa taya zai samu kudi ba ruwanshi da kasar ta gyaru ko akasin hakan kuma dai ko mun k'i ko mun so k'asarmu ce ba yadda zamu yi,in ta gyaru mu zamu ji dadi akasin hakan ma mune a ciki" lokaci guda su duka sukayi ajiyar zuciya,

Hajiya tace"Allah ya bamu ikon gyarawa gaba d'ayanmu harda shuwagabannin mu,yasa mana tausayin junanmu,Amin" suma suka amsa da "Amin", taci gaba da magana "Shi Haisam ma ba kudi ne zasu kaishi ba,sam ba sune damuwarsa ba wllh,dama yana da burin gina katafaren Company wanda ya danganci technology d'in anan k'asar,to shiyasa yake son yaje yayi aiki dasu don ya k'ara samun Experiences,don bama shine Company na farko da suka yi mashi tayin aiki ba,ko lokacin da yayi Degree d'insa na farko a can k'asar Singapore,akwai wani Company daga k'asar China da suka so yayi aiki dasu Uban nasa ya hana yace ya dawo nan gida yayi aiki,to lokacin ya fara a matsayin Engineer mai zaman kansa daga baya ya fara aiki ak'arkashin Ministry of Communication Technology, Kawu Mani yace "haba ni daman nasan badai kud'i ne zasu sa Haisam din son yin aikin ba,ashema babban dalili ne,aikuwa gara yaje kinga sai ayi abunda ake cema ban gishiri inbaka manda" ya d'an dakata kafin yaci gaba"Ai sanata akwai kishin k'asa,wallahi nike gaya maki hajiya da Allah zaisa ya zama shugaban k'asa da munji dadi" dariya hajiyar tayi, ya juya wurinsu Alhaji Sa'idu yace "Allah daba k'aramin adalin shugaban k'asa za'ai ba mai kishin cigaban kasarsa,ga dai misali nan kan Iyalinshi" suka jinjina kai had'i da fadin "gaskiya ne" ita kam hajiya dariya kawai take tace "tau da kamar wuya dai ya fito takarar shugaban k'asa,don takarar Senator d'in ma da yaya ya fito sai da mutane suka taso shi gaba da kyar ya aminci,haka da tenure d'insu ta kare ma so yayi yaki ci gaba,a cewarshi yafi son ya cigaba da aikin shi da kuma kasuwancinsa". Kawu yace "Ai shugaban k'asan ma sai a matsa masa ya fito in Allah yasa da rabo sai kiga ya zama,ni ba don komai bama wallahi sai don fatan samun sauk'in matsalolin nan da suka yima k'asarmu katutu..." ajiyar zuciya Hajia tayi tace "Allah dai ya za6a mana dukkan abunda yafi zama alkhairi" gaba d'aya suka amsa da "Amin ya Allah". "Oh munata tattauna matsalolin da in shekara zamu yi ba lalle mu gama ba,an barku ko ruwa ba'a kawo maku ba" hajiya tace tana kallon su Alhaji Sa'idu da murmushi,suma murmushin suka yi,ta kalli Kawu mani tace "ga Abinci can saman table,dama bamu dad'e da saukkowa ba nida Haisam,don da ana gama sallan juma'a ku ka zo ma a tare zamu ci" Kawu yace"Wallahi nan naso muyi sallar juma'an,to bamu gama abunda muka je yi ba da wuri,dole acan dai mukayi" hajiya tace"Wani wuri kuka je ne? Yace "Eh,Ministry of Agriculture muka je" tace "Allah sarki,ya noman ana tayi ko? Yace "Eh,Alhamdulillah muna ta k'okartawa" "To Allah ya k'ara taimakawa,wasu yankunan ma naga noman ya gagaresu saboda matsalar rashin tsaron nan,gona ta ma da ke hannun baban tukur bara ai noman bai samu ba,Allah ya kawo masu d'auki da mu gaba daya" suka amsa da "Amin" "Jama'a ku tashi kuci abinci don Allah" ta fad'a tana kallon su Alhaji sa'idu,Kawu Mani ne yace "ai inaga Hajiya kaman a sakko mana dashi nan zai fi" tace to,ta fara kiran Saude,daga cikin corridorn da bedrooms suke Saude ta fito tana yafa kallabinta,hajiya ta bata umarnin ta kawo masu Abinci cikin parlor,ta juya ta fara kawo masu,kafin ta gama jerawa Kawu Mani ya juya yana tambayar hajiya"hajjaju ya wajen mutanen Lagos,hajiya Maryam da k'waran mijinta kwana biyu bamu gaisa ba? Daria hajiya tayi tace "suna nan lafiya lau",a lokacin Saude ta gama serving abincin saman lallausan Carpet d'in parlon bayan ta gaishe su tace masu"Bismillah" suka amsa da "to" had'i da yi mata godia,ta juya ta koma ciki Hajiya ma tace masu zata d'an shiga ciki kafin su gama.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)*

*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝*

*Free page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣*

Haisam na fitowa daga part d'in Hajiya ya nufi Part d'insa yana amsa wayan da aka kira shi,a daidai stairs din balcony ya gama wayan,tura kofa yayi ya shiga cikin parlon ya zauna kan kujera hadi da daukar Remote yayi powering tv On,ya d'an kishingida yaci gaba da kallon American film d'in da yake kallo a MBCMAX, bayan wani d'an lokaci ya dau wayarsa ya duba time,sake d'aukan remote yayi yai Offing tv sannan ya mik'e ya nufi bedroom. Sanye cikin Sportswear ya fito,red t-shirt da wandonta black daga gefen hagu na rigan na dauke da tambarin ADIDAS wanda akayi da bakar sak'a haka wandon ma adai dai gefen da akayi rubutun rigan shima akayi da jar sak'a daga k'asa yad'an matse,ba k'aramin kyau yayi cikin shigan kayan ba,kuma da ganin laushin kayan tabbas zasu yi kudi,saida ya tsaya yasa takalma a corridor kafin ya iso cikin parlon ya dau wayansa ya fice zuwa masallaci wanda liman ke ta kwalla kiran sallah, Tare da su Uncle Mani ya fito bayan angama sallan la'asar d'in ya nufi cikin parking space don fiddo da Bike d'insa bayan yayi ma T.k da ya fito daga masallaci bayan sun fito umarnin ya daukko masa jakarsa kaman jiya,

Uncle Mani ya nufi part d'in Hajia don yi mata sallama su kuma su Alhaji Sa'idu suka tsaya gefen motar da suka zo da ita suna jiran ya dawo gaba daya hankalinsu na kan Haisam daya fiddo bike d'in cikin harabar ya haye yana kokarin sa helmet,adai dai lokacin da t.k ya kusa k'arasowa da jakar, Hajiya da Kawu Mani suka fito suka nufo parking space din,Kawu Mani dake ta kallon Haisam tunda suka fito ya fara magana"Yanzu Hajjaju shima Haisam na hawa irin mashin d'in nan? Hajia ta ta6e baki tace " Unn" adaidai lokacin da suka k'araso wurin su Alhaji Sa'idu ya kunna mashin d'in gaba daya suka toshe kunnuwansu da hannayensu da sauri,haisam ya d'an juyo ya d'aga ma Uncle Mani hannu alamar yana masa sallama bai jira ya maido masa ba yaja mashin din da gudu ya tunkari gate d'in da tuni an wangale masa shi. Uncle Mani ya sauke ajiyar zuciya bayan Haisam ya fice yace"I don't know what's wrong with our Youths,abu mai had'ari shi suke mayarwa abun adon su,and what really baffle me with them shine duk irin mummunan had'arin da mashin d'innan ke haddasawa hakan bai serving dinsu misali su daina hawan...Alhaji Sa'idu ya kar6e"Sam basu bi dashi yadda yadace ne,haka zaka ga suna ta falla uban gudu kai kace zasu kiyama..."Mutumin na karshe ya katse shi da cewa"Ai wasu kam kiyaman suke tafiya wllh sam basu la'akari da irin titinan mu ba kaman na waje bane,su yi ta tuk'in ganganci,gashi naji ance mashin d'in tsada ne dashi sosae..."Hajiya dake tsaye hannuwanta goye a bayanta ta amsa "tsada kam! Miliyan biyar ya zuba kafin ya mallaki wannan nasan..."gaba daya suka zaro ido a tare suka maimaita kudin da hajiyan ta fad'a,ita kam kai ta jinjina masu Uncle Mani yace "to Allah ya kyauta,Allah ya k'ara tsarewa,gaba d'aya suka amsa da Amin" daga haka ya kalli hajia da d'an murmushi yace "to hajjaju mu zamu wuce sai wani lokaci kuma in Allah yasa rayuwarmu ta kai" hajia tayi murmushi tace"To Allah yasa rayuwar tamu ta kai" ta fiddo hannayenta dake goye a bayanta ta mik'a ma Alhaji Sa'idu kud'i dake cikin hannunta na dama da fara'a tace"gashi ayi ma iyali tsaraba nagode da ziyara,Allah yabar zumunci" hannu biyu yasa ya kar6a harda d'an russunawa suna ta godiya shida dayan,Uncle Mani yace"To ni hajjaju ba'a sallame ni ba" dariya tayi tace banda kai ai sune bak'i na, kai na gida ne" shima dariyar yake ya bud'e mota yace"ba wani abu nasan tawa sallamar babba ce tafi karfin hannu k'ilan,zan turo Account details" daga haka ya shige Abokan tafiyarma suka shiga suna ta kara godiar rafar 50k da hajia ta basu cike da farinciki hannu ta d'aga masu bayan sun fita daga cikin parking space din tace"Agaida Iyali",daga haka ta juya ta koma ciki.

Tunda ta shige gida take kunshe a daki,bayan tayi sallar Azahar bacci yayi awon gaba da ita,ko Uniform d'in bata cire ba,bugun kofar da ake tayi ne ya farkar da ita a tsorace ta fito daga d'akin tana tafiya cikin sand'a har Lokacin kuma ana ta buga kofar da k'arfi,tsayawa tayi cikin zauren tana tunanin waye ke buga kofan haka? kodai mai Motar ne ya kawo k'ara,ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa nan take tsoro ya kama ta tace a ranta "to ya akai yasan gidanmu bayan lokacin da na jefi motan ba kowa wurin..." wani bugu aka yima k'ofar wanda daji mai buga kofan ya k'ule yasa ta tunkari kofar da sauri ta d'an leka idonta d'aya ta ramin makulli nan take ta gane waye da sauri takai hannu sama ta cire sakatan sannan ta d'an ja baya,aikam da karfi aka bugo kofan don da bata matsa ba daba k'aramin buguwa zatai ba,rai a6ace yake kallonta Kawu Amadu ne hannunshi daya rungume da kwali d'ayan kuma katuwar leda ce,Fatuu dake ta faman zare ido tace "sannu da zuwa Kawu Amadu...."da sauri ya katseta da fad'in "sannu da zuwan uwarwa,don iskanci daman kina cikin gidan kika barni inata bugun k'ofa tsawon lokaci,to waima uban me kike a cikin gidan daba zaki zo ki budan ba? d'an turo baki tayi tace "ba komai,bacci ne ya d'auke ni fa" a harzuk'e yace"to miye na kulle kofa don zaki yi bacci" da sauri tace "ina gudun kar a shigo ayi sata ne ina baccin...." "k'arya kike" yace yana k'are mata kallo kafin yaci gaba "fad'a kika jawo ko? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a,kwafa yayi yace "ai na dawo gidan inma rigima ki ka jawo zan gani,kuma uban miye na zama da Uniform har yanxu a jiki da alama ma ko wanka baki yi ba,bare kiyi sallah" ya k'arasa maganar yana kokarin aje kayan hannunsa a bakin kofa,d'agowa yayi ya daka mata tsawa"wuce kije ki wanka kafin na buge ki a wurin" juyawa tayi ta nufi cikin gida tana d'an k'unk'uni har ta nufi d'aki taji yace"bakiji mi nace kiyi bane? Da sauri tace "naji.." yace"to wuce ki dau bokiti ki d'ibi ruwa" ta wuce ta xuba ruwan ta shige band'aki,shima yana shiga wankan yayi a d'an band'akin cikin d'akin nasa ya shirya ya kwashi kayan da ya siyo ya nufi shago don jera su.

Sai can bayan Issha gwaggo ta dawo,fatuu dai na k'unk'ume a d'aki cike da zullumin kar akawo k'ararta, koda ta fito tayi ma gwaggon sannu da zuwa dakin ta koma ita kam gwaggo a gajiye take hakan yasa ko ta kan Fatuu bata bi ba balle har ta fahimci wani abu,sai can dare gwaggo tayi bacci sannan ta fito taci abinci tayi sallah ta koma ta kwanta tare da yankewa ranta cewa baza'a kawo k'arar tata ba tunda har aka kai wannan lokacin.

Washe gari asabar da safe Fatuu ce da Haulat zaune cikin ajin su na islamiyya,Haulat ta kalli Fatuu da murmushi tace"sannu hajiyar fad'a" wata yar dariyar iskanci fatuu tayi tace "waya ce maki nayi fada" d'an ta6e baki Haulat tayi tace "har gida akazo aka fad'a mana irin fadan da kuka yi, wai har kin fasa ma Murja baki da hanci" murmura idanu Fatuu tayi tace"Yessss,gobe ma ta k'ara gaya man banzan maganganu harta kirani da yar kauye" girgiza kai haulat tayi tace"ni wllh don kince Gwaggo bata nan amman a lokacin da sai na kai k'arar ki tunda ke dai baki da hakuri" harararta Fatuu tayi tace "aida da ta dawo kinzo kin kawo k'arartawa sarkin masu hakurin duniya" haulat tace "tunda ya rigada ya wuce miye na inzo,Amman ai naji ance wani mutum ne yayi maganinki da ki ka k'i barin fadan ya wanka maki mari" ta kai maganar tana tik'ar daria,wata yar iskar dariya Fatuu ta sake yi tace"hehehe ashe yai maganina,muka dai yi maganin juna don shima yayi asara ehe" haulat ta dakata da dariyar da take tace "what do you mean da ku kai maganin juna?wace irin asara kuma? Fatuu ta gyad'a kai da turancin ta na yar sakandire tace "what u hear" Still haulat tayi tana ta kallonta can tace "don Allah Fatuu fad'a man abunda kika yi masa" fatun na shirin yin magana Malaminsu ya shigo hakan yasata yin shiru daga nan kuma basu sake samun daman yin magana ba don yana fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi,akan hanyar su ta komawa gida Haulat tace "d'azun na tambaye ki mi kika yiwa Mutumin baki gaya man ba" banza fatuu tayi mata,haulat ta sake cewa "kinji,mi kika yi masa ne" ba tare data kalleta ba tace"ke dalla bafa komai,wasa nike,ba abunda nayi masa kawai don kar kiyi tunanin yayi nasara akaina ne" haulat tace "kawai dai bazaki fadan bane Amman ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba tunda kika ce yayi asara da akwai abunda kika yi masa...." cikin tsiwa tace "ehh d'in nayi, tunda ba ki yarda ba abunda nayi masa ba" shiru haulat tayi amman ba don ta yardan ba,can tace "to ki kar6i jakar ki ko,kince in taho maki da ita kuma kin barni inata kayanta" juyowa Fatuu tayi ta figi jakar ba ko nagode tayi gaba abunta sai wurga kafa take da alama dai ta saba da yin tafiya haka,girgiza kai haulat tayi tace daga abun arziki,tabi bayanta har suka zo bakin lungun da suke rabuwa,haulat ta d'an daga murya tace "sai munhade Anjima hajia Fatuu ikon Allah" Fatuu ta juyo tayi mata kallon up and down ta k'ara gaba,Haulat dai dariya tayi a fili tace"Allah ya shirye ki" daga haka ta nufi hanyar gidansu, adai dai kofar shiga gida fatuu ta waiga tana kallon hanyar da haulat ta bi a fili tace "don ina sakarya Allah ya rufa man asiri in tona ma kaina,don na tabbata na fad'i mata sai ta fad'a ma gwaggo ko kuma tayi ta ma mutane nasihar banza ita ga mai hakuri yen-yen-yen" ta d'age baki daga haka ta shige gida.

Haulat ce keta faman sauri da yamma zata islamiyya don ta makara sakamakon aikenta siyen gero da Innarsu tayi,tana k'okarin shiga lungun da zai kaita har islamiyyar taji daga gefenta ana magana "Ke,ke yar liman wait" da sauri ta juya tana kallon mai maganan,ya nufota yana wata irin tafiya irin ta nigas,da mamaki haulat ke kallonsa tana tunanin ita miye had'inta da Gaye da zai tsaida ta,yana k'arasowa yace"Ke dalla tambayanki zanyi kike ta faman zare ido uwa mujiya" ita dai haulat shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce,ya ci gaba "dama tambayanki zanyi k'awarnan taki an kamata tana can cikin cell ne ko har anyi gaba da ita? cikin rashin fahimtar zancen shi haulat tace "wace kawar tawa kuma? Wata yar iskar daria yayi yace "kina da wata k'awa ne bayan Aljanar yarinyar nan mara jin magana, kullum ba tare nike ganinku ba" nan take ta gane Fatuu yake nufi don duk in suna tare suka had'u dashi Aljana yake cema fatun,da sauri haulat tace "to mitayi da za'a kai ta cell kuma? tayi maganar cike da fargaba tana ta zare ido, rik'e ha6a gaye yayi yace "wai kina nufin baki san aika-aikar da aljanar nan ta aikata ba...? da sauri haulat ta girgiza masa kai alamar a'a, jinjina kai yayi yace"tabb,to wllh ruwa ta 6allo ma kanta don ina tabbatar maki sai taje gidan yari..." da sauri haulat ta dafe k'irji tana salati tace"don Allah Gaye ka gaya man abunda tayi,ni sam wllh bansani ba" sai da ya gyara tsayuwa ya karkace baki yace "to bari kiji wani mutum ne jiya hakanan Aljanar nan ta jefar masa glass d'in bayan mota,gaba daya ta dagargaza glass din don wannan glass din yayi konden..." cikin tsananin tashin hankali haulat tasa hannuwanta duka biyu ta rufe bakinta ya ci gaba "atoh kima fad'a mata ta shirya don comfat (confirm) in ba'a biya shi ba har yakai k'ara na rantse da Assamadu sai taje fursun,yo motar fa ba k'aramar mota bace,to tsaya ma kiji,mai motar dan gidan Hajiyar Sanata ne kinsan kuwa ba'a k'aramar harka a gidan nan......" daga haka ya kad'a kai yayi gaba abunshi,

kasa motsawa haulat tayi na tsawon lokaci da k'yar ta juya taci gaba da tafiya a hankali gabanta sai fad'uwa yake tamkar itace akace zata gidan yarin,cikin zuciyarta kam mamaki kawai take na abunda fatun ta aikata,ashe asarar da take nufin mutumin yayi kenan,"tabb lallai Fatuu bata da hankali!" ta fad'a a fili tana jinjina kai. A daidai bakin ajinsu ta tsaya tana tunanin shiga don tasan ta makara gashi akwae malami cikin ajin,can dai tayi shahada ta kutsa kai tare da yin yar sallama,d'an kallonta malamin yayi yaci gaba da bayanin da yake hakan yasa haulat yin saurin shigewa ta nufi wurin zamansu sai dai ga mamakinta Fatuu bata a wurin,tunani ta fara yi a ranta bayan ta zauna"to Fatuu bata zo bane? Kodai anje an kamata...wani irin bugu gabanta yayi da sauri ta d'ago da kanta a lokacin kuma ta hango fatun acan dayan bangaren,tunda haulat ta shigo ta wuce Fatuu ta ganta a ranta tace "da nice na makara da ya buge ni,ni da kowa ya tsana"ta saci kallon malamin ta d'an hararesa kafin ta juya inda haulat take nan take suka had'a ido don tunda ta hango fatuu take ta kallonta cike da al'ajabin abunda gaye yace zai sameta,murgude fatuu tayi mata ta juya,haulat ta girgiza kai cike da tausayinta,ta kuma fahimci dalilin da yasa fatun ta canja wurin zama don ta saba hakan da d'an abu ya hada su wanda bai kai ya kawo ba sai ta canja wurin zama sai tagadama ta dawo ko haulat taje ta bata hakuri sannan ta dawo,haulat ce kad'ai ke iya jure halin fatuu don ta karanci halayenta tsab shiyasa ma bata biye ta.

Haulat ce keta sauri ta isko Fatuu don da aka tashi ta tsaya copying rubutun da malam yayi bata nan daga littafin wata kawarta da suke zama tare,ita kuwa Fatuu ana tashi tayi gaba abunta don guje ma haulat din take karta k'ara tambayarta game da asaran da tace Mutumin daya raba su fad'a yayi don tasan halinta wani lokacin nacin tambaya ne da ita kuma karshe inta gano tana iya zuwa ta fadi ma gwaggo "Fatuu!fatuu ki tsaya" haulat dake biye da ita a baya tace,ganin bata da niyyar tsayawa yasa haulat yin dan gudu tasha gabanta,cak fatuu ta tsaya fuska ad'aure tace "miye haka zaki wani shage gaba na" kasa magana haulat tayi don k'arfin halin fatun mugun mamaki yake bata ta aikata irin wannan babbar ta'asar amman hankalinta akwance,tsoki fatuu taja tana kokarin bin ta gefen haulat din,taji tace "To ai yanzu nasan abunda kike 6oyewa hajia" da sauri fatuu ta kalleta sama da k'asa tace "ni mi nike 6oyewa? Haulat ta jinjina kai cike da takaici tace "asarar da kika ce mutumin nan yayi na tambayeki wace asara ce kika k'i fad'a man to yanzu nasan komai,ke yanzu fatuu abunda kika yi kin kyauta?hakanan ki jefar ma mutum mota har ki lalata masa glass....."katse ta Fatuu tayi da fad'in "naje na fasa d'in,dama nasan ai sai kin bi diddigi don kin saba sa man ido,to na fasan kuma ko gobe ya k'ara shiga harkata har ya d'aga hannu ya mareni sai na kara ja masa asara don ni ba ai man na kyale ehe" daga haka ta kad'a kai tayi gaba,cikin d'aga murya haulat tace "to kinsan wanene kika fasa ma gilashin mota.....? a fusace ta juyo tace"ina ruwana da ko waye,Allah yasa d'an sarkin makkah ne" ta juya taci gaba da tafiya abunta don ita tayi tunanin tambayarta haulat d'in tayi,cike da takaici haulat tai tsaye tana kallon bayanta a fili tace "lallai Fatuu bata da hankali wllh bata san bala'en da ta jawo ma kanta bane,tama k'i ta tsaya ta saurare ni...." girgiza kai tayi ta fara tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "ko dai inje in sanarma gwaggo don tasan halin da ake aciki..." girgiza kai ta sake yi da sauri a fili tace "kai a'a,bai kamata ta fara jin wannan mummunan labarin daga baki na ba gaskia" can kuma tace "to wai ma ni ina ruwana da zan damu,ita wadda ta aikata laifin ma ko a jikinta,kawai dai ba dad'i ne kana tare da mutum wani mummunan abu ya same shi,to amman tunda ita taja ma kanta ai ita ta sani" ta watsa hannuwa,daina bin bayan fatun tayi,ta canza hanya,lokacin da fatuu zata sha kwana ta juya bata ga haulat d'in ba ta6e baki tayi a ranta tace gwara da nayi mata haka inba haka ba sai tace zata zo ta gaya ma gwaggo,a fili tace "inma tazo ta fadan sai in k'aryata ta tunda dai ba a gabanta akayi ba kuma bata da shaida" tayi k'wafa tace "ta sake ta gaya ma gwaggo wllh 6atawa zamu yi ba ruwana da ita" tayi maganar tana mummurgud'a baki,To hajia Fatuu ba dai yau kika fara fadin haka ba,kuma ko kun 6ata da kanku dai kuke shiryawa don keda haulat sai Allah.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)*

Free Page1️⃣8️⃣

Readers Also Read