Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 9

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 9

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 9: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 9. Abokin gaye da tunda suka tsaya bai tanka ba kunnansa…

4,476 words

Abokin gaye da tunda suka tsaya bai tanka ba kunnansa d'aya mak'ale da earpiece yana sauraron waka yana dan jujjuya kai,yasa hannu ya cire earpiece din yace"Baabah wai yane? mi tayi ne naji sama sama kana ta mata bayani harda uban lissafi?" Gaye yace "ruwa ta 6allo ma kanta baabah....,nan ya bashi labarin abunda fatun ta aikata, yace "na gidan da muka wuto yanzu ka ke tambayata gidan waye,nace ma gidan Uwar Sanata ne kuma Matar tsohon Ministan tsaro? Abokin ya gyad'a kai alamar"Ehh,gaye yace"to mutumin gidan ne ta yi ma wannan aika aikar,don ni farko ma bansan d'an gidan bane ina dai d'an ganinshi kwanan nan yana wucewa a Motoci kala kala,har wani gangamemen Bike yake hawa,ina jin wannan bike din yayi million goma shima ko ma fi, sai shekaranjiya tsoho yaja ni zuwa sallar juma'a a Masallacin gidan,na ganshi tare da Hajiyar sun zo suma,to nan nagane dan gidan ne ashe" Ya cigaba"Kasan masu kudin nan da shegen wayo,in suka gina tangamemen gida sai suyi dan Masallaci wai Allah ga naka,don kar a masu surutun basuyi ba,duk da dai su nasu babba ne" yana maganar yana watsa hannuwa sai kace mai yin debate, Abokin fuskarshi da mamaki yana jinjina kai yace "kai kace master ce ta rashin ji" Gaye yace"ehh mana,wannan da kake gani furofesa ce ba master ba,don inta 6allo wani aikin yasin ko ni jinjina mata nike,dubi dai abunda ta aikata yanzu ni yaushe zan fara haka,ban aje ba,ban ba wani ajiya ba,Iyaye kuwa sai dai ace lahaula saboda talauci" yana maganar yana wani janta, Abokin ya kwashe da daria yace kama aikatan ai kasan inda za'ai da kai,billahillaxi gidan yari straight inbaka biya ba,aje aita cin gabza.."Gaye ya tuntsire da dariya yana rik'e wando, Yace"Allah yai man tsari da cin gabza baabah,shiyasa nike taka tsantsan,nadai je cell inyi kwanaki in fito don wannan yama zama gida,don ina daraja tuwon gyatuma ta,baka sanin dadin shi sai an had'aka da gabza yasinn..." gaba d'aya suka tuntsire da wata yar iskar dariya,ita dai Fatuu sai kallon su take tamkar yau ta fara ganinsu,zufa kuwa tuni ta lullu6e fuskarta,sai had'iyar miyau mai d'aci take. Abokin gaye ya kalleta cikin nuna tausayi yace"Wayyo baiwar Allah na tausayi maki wllh,yanzu zaki bar tuwon gyatumarki ki koma cin gabza,duk wannan hasken fatar naki da kyawun fuskar ki sai ya disashe qur'an,in kuma kina da gashi to duk kwarkwata sai ta cinye shi,sai dai ko in kuna da kud'i sai ku biya shi abunshi kawae...." Gaye ya katse shi da sauri "yo ina suka ga wani kud'i duk kanwar ja ce yasin,itafa kakarta ke ruk'onta kuma in fada maka kakar attendar ce a asibiti irin masu share share da goge gogen nan,ina zata ga miliyan d'aya ai yasin ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,ko kwatan miliyan bata da" Abokin yace "Kace dai dole sai anje an had'e da gabzar dai...." da sauri Gaye yace "Comfat,don a ranar sai da ya tambayeni nayi masa kwatancen gidansu,shiyasa nayi mamaki dana ganta har yau ba'ai ramm da ita ba, amman nasan kilan sunje basu samu kowa a gidan ba,kuma kaga jiya da yau ba aiki,amman na tabbatar gobe Monday dole azo a damk'e ta",

Ya juya kan Fatuu yace "To Aljana,sai ayafi juna,sai Allah kuma ya k'addara za'a sake ganawa,don can d'in ba sauki, wasu ma wuya ke kashe su, nidai na yafe maki" daga haka ya juya kan abokin nashi yana fad'in "hayya,Baabah mu ware ko.." suka yi gaba abunsu suna wata yar iskar tafia.

Kasa motsawa Fatuu tayi daga inda take don k'afafunta ba k'aramin nauyi sukai mata ba,Kalaman gaye na k'arshe sun matuk'ar razana ta"Ashe mutumin har yasan gidansu...! Shine abunda ya kara tada mata hankali,kallonsu gaye tai tayi har suka 6ace ma ganinta, irin su Gaye sai su kashe mutum,don halin da Fatuu take ciki tsaff zuciyarta zata iya bugawa don tunda take bata ta6a janyo rigima irin wannan ba,iya ta 6arar ma yara abu gwaggo ta biya ko ta bugi mutum har ta raunata shi gwaggon ta biya kudin zuwa chemist ta tsaya,yau gashi ta janyo rigimar da tabbas tafi karfin gwaggon,duk'awa tayi a wurin don kafafunta rawa kawae suke,ga kwakwalwarta sai tariyo mata da maganganun gaye take,bugun zuciyarta na k'ara tsananta ga zufa da ta wanke mata fuska har wuyan Hijab dinta ya fara jik'ewa,da za'a auna jinin Fatuu a lokacin tabbas daba k'aramin hawa yayi ba. Tsawon mintuna Fatuu na duk'e a wurin kafin tayi k'arfin halin mik'ewa ta fara tafiya a hankali,da kyar ta ke taka k'afafunta da sukai mata wani irin nauyi,a ranta kuwa ba abunda take Maimatawa fa ce "Kud'in Shanu Gomaaa..!!!!"

*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝*

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page 21

Wani mutum ne ya shigo kwanar ta bayan Fatun yana zuwa saitin ta yace "Ke bake ki ka yada jaka bane? sam Fatuu bata lura da ba jakarta a hannunta ba,don bata cikin hayyacinta,d'agowa tayi ta kafe Mutumin da idanu tama kasa bashi amsa,ganin yanayinta,ga fararen idanunta sun rikid'e sunyi ja yasa Mutumin cewa"baki lafia ne? d'aga masa kai kawae Fatuu tayi alamar "eh,juyawa yayi ya d'aukko mata jakar ya dawo inda take tsaye yace "Muje" bata ce komae ba tabi bayanshi a hankali take tafiyar har suka fito suka hau hanya Mutumin yace"ina ne gidanku?" da yatsa Fatuu ta nuna mashi, "to zaki iya k'arasawa?ya tambayeta,Kai ta k'ara dagawa,ya mik'a mata jakar yace "Allah ya sawak'e,ni ta can zan bi ne, ki bi a hankali ki k'arasa kinji" nan ma kan ta d'aga,Mutumin ya juya ya tafi, Ikon Allah wai yau Fatuu ce ta kasa magana,lalle ba karamin tashin hankali kalaman gaye suka jefa ta ba, Lokacin da ta iso gida shagon Amadu a rufe yake,tana shiga zaure taga k'ofar dakinshi a bud'e,shigewa ciki kawai tayi, tana shiga ta wuce band'aki tayi fitsarin da tuni ya d'aure mata mara don har ya d'an zubo ma,tana fitowa ta shige ciki,a bakin k'ofar dakinta ta aje jakarta ta shige,bata bi takan gwaggo ba don tasan bata nan tunda safe ta sanar da ita cewa aikin rana take,amman zata fita da wuri don zasu je Walimar d'iyar abokiyar aikinsu da aka d'aura ma Aure jiya Asabar,daga can zasu wuce Aiki, Can k'arshen d'an gadonta ta haye ta had'e kafafuwanta ta tura kanta ciki,tayi zuru tana ta tuna maganganun Gaye, kwata kwata ta kasa yin tunanin Mafita,don tana ganin ba wata mafita tabbas abunda gaye yace sai ya faru,don kud'in gilashin da yawa ba zai yuwu Mutumin ya yafe ba, tunda gashi harma ya tambayi kwatancen gidansu,sai lokacin wasu kwalla masu zafi suka zubo mata don tun d'azun ta kasa ma yin kukan,wani irin d'aci take ji a bakinta,

Ta dau tsawon lokaci a haka, ta kasa ko kwanciya don komae bai yi mata dad'i,tana a haka har aka kira sallar Azahar,tana ji ana yin sallar amman ta kasa saukkowa daga gadon ga yunwa tana ji amman bata jin ma zata iya cin abinci, Amadu ne ya shigo cikin gidan don d'ibar Abinci bayan ya dawo daga salla,ya hango jakar Fatu da takalmanta a bakin k'ofar daki a ranshi yace "Yanzun haka tana can tana baccin tsiya bata tashi tayi Sallah ba" ya nufi dakin Fatun ya d'age labulen,kafin yace wani abu Fatuu tayi zumbur ta d'ago,hawaye duk ya wanke mata fuska,ganin haka yasa Amadu shigowa cikin d'akin yana kallonta yace"Miya faru?" dakyar murya can ciki tace "ban lafia.." Amadu dake ta kallonta har ranshi ya yarda bata lapiyan don da ganin fuskarta ma,yace"mike damunki", Tace"zazzabi da ciwon kai" yace"kinsha magani" girgixa masa kai tayi alamar "a'a" "To ai ba kwanciya zaki yi kita wani kuka ba,ba kinsan inda Gwaggo ke aje magunguna ba sai ki d'auka kisha ko" har ya nufi k'ofa zai fita ya juyo yace "Kinci Abinci" tace "a'a" juyawa yayi ya fice,ba'a jima ba ya dawo,hannunshi rik'e da plate d'in abinci yace"saukko ki ci" aje mata yayi a k'asa ya sake fita,sai gashi ya sake dawowa da Cup d'in ruwa da magani Panadol,tsayawa yayi yana mata wani irin kallo ganin bata saukko ba yace "ba saukkowa nace kiyi bane,in ki ka ban haushi sai in kyale ki kiyi ta zama da ciwon..." A hankali ta saukko cikin zuciyarta tana fad'in"in kayi hakuri ma daga yau ba sake ganina za kai ba" aje mata ruwa da maganin yayi ya nufi k'ofa yana fad'in "kafin in sake dawowa ki tabbatar kin cinye shi kinsha maganin"daga haka ya fice, Tunda ya fita ta kafe abincin da idanu,ta zabga uban tagumi tana ta faman tunanin a ina za'a samu kudin shanu gomaaa a biya mutumin nan,ita dai bata so akaita gidan yarin nan,gashi Gaye yace wasu wahala ke kashesu acan....,Zuciyarta ce ta raya mata "ARD'O" dammm gaban Fatuu ya fad'i,lokaci guda kuma ta fashe da matsanancin kuka,a fili take fad'in "Shi kadai ne zai iya biyan wadannan kudin,amman nasan ko kashe ni za'ai a gabansa da kwarankwatsa ba zai biya ba...." a zuciyarta tace "to ko in fad'ama Kawu Amadu ne..."da sauri ta girgiza kai a fili ta sake cewa"kafin gwaggo ta dawo nasan ya karairaya ni, don dama shi ake sawa yana zaneni"haka dae Fatuu tayi ta tufka da warwara,k'arshe ta maida hankalinta kan Abincin wanda jallof din shinkafa da taliya ne,a hankali tasa hannu ta d'iba ta kai baki ta fara taunawa da kyar take hadiye abincin,tana yin loma ukku ta tsame hannunta,sam bata jin dad'in abincin,shima d'aci yake mata a baki,tayi zuru tana kallon shi don tana jin yunwa sosae,a ranta tace "dama tuwo Gwaggo tayi kilan in fi jin dad'in shi...."Wata zuciyar tace"A ina zaki k'ara ganin tuwon ma,dama kinci Abincin don daga yau shima ba sake ganinshi zaki ba sai dai ki rink'a ganin gabza" da sauri ta jawo Abincin ta shiga turawa a baki ba don dad'i ba.

Bayan ta cinye Abincin tana cikin shan Maganin Amadu ya d'aga labulen ganin ta cinye yace" Yauwa,yanxu sai kitashi ki yi sallah inkin gama sai ki kwanta,insha Allahu zaki ji kin wartsake",a hankali tace "toh" ta mik'e don yin sallar, Bayan ta gama sallar ta d'aga hannuwa sai Addu'a take tana fadin,"Allah don Allah na rok'e ka kada kasa a kaini gidan yari,don Allah,don masoyinka Annabi Muhammadu kasa Mutumin ya manta da abunda ya faru kwata kwata,nayi maka Alkawari na daina rashin ji,zan zama kamar Haulatu....." haka tai ta rok'on Allah tana kuka har tagama ta tofe a hannuwanta ta shafa,A saman abun sallan ta kwanta ta takure jikinta tana ta ajiyar zuciya a haka bacci ya kwashe ta. Bayan an kira Sallar la'asar Amadu yazo ya tada ta yace"ki tashi ki watsa ruwa kiyi Sallah,naji ruwan bokitin wurin wanke wanke nada d'umi sai ki d'ibe shi" kai ta daga masa kawae,ya juya ya fice. Bayan ta gama sallar tayi zaune a wurin ta buga uban tagumi,ba laifi ta dan ji dad'in jikinta,tunani ta fara yi ko ta tafi islamiyya taje tagani in Haulat tazo ta fadi mata halin da take ciki...,d'an tsoki tayi a fili tace"koma na fad'a mata,ba abunda zata iya yi,karshe ma ta kama man nasihar banza,baccin lokaci ya rigada ya k'ure" can kuma wata zuciyar ta raya mata"ba gara kije ba,watakil dalilin zuwan Allah ya tausaya maki yasa a k'i zuwa kama ki,amman in kika zauna kina iya ganin anzo yanzu an tafi dake.." zumbur ta mik'e ta nufi yar wardrobe dinta ta ciro wasu kayan Islamiyyar tasa, tunda ta nufo zaure take jin tashin kida a waje,Amadu ne ya kunna wakar india a shagonshi,a hankali take tafiyar don yadda take jin jikinta kaman ta tashi daga ciwo sam ba karfi,lokacin da ta fito waje ta girgiza kanta tace "Shi sam baida matsala,waka ma yake ji" hannu tasa ta share dan siririn hawayen da ya zubo mata a ido daya,tace"in sha Allahu nima indai Allah ya ku6utar dani ba ruwana da kowa" Allah sarki Fatuu har kin bani tausayi,sai dae Allah yasa ba tuban mazuru kike ba. Amadu ya hangota zata wuce ya leko da kansa yace "zaki iya zuwa islamiyyar ne? tace "ehh naji nasamu sauki" yace "dan jira" miko mata biscuit pure bliss yayi da sweet guda biyu yace"Sai kin dawo,kibi a hankali" daga haka ya maida kanshi ciki yana ci gaba da bin wak'ar da yake saurare hadi da dan jujjuya kai,tafiya take tana ta kallon abunda Amadu ya bata tana mamaki wai yau ba tare da ta rok'e shi ba ya bata,ko ya zage ta kaman yadda yake mata inta tambaye shi,wani lokacin har rankwashinta yake kafin ya bata yace ita zata cinye masa jari,dan murmushin takaici tayi a fili tace "tabbas shima yaji a jikinshi ya kusa rabuwa dani" taci gaba da tafiya tana yi tana goge kwallan dake zubo mata da gefen hijab dinta.

Tunda ta zauna a aji kanta na k'asa,Haulat sai kallonta take tana nazarin yanayinta gashi akwae malami balle ta tambayeta abunda ke damunta,sam ta kasa natsuwa ganin kwalla na zubo ma Fatun tana sa hijab tana gogewa,tana sauraron bayanin malam dake masu Ahalari tana kuma satar kallon Fatuu, "FATIMA MUHAMMAD ARDO" Malam ya kira sunan fatuu,sai dai sam bata ji shi ba, Haulat ta ta6o ta,lokacin yana k'ara kiran sunan,da sauri ta d'ago Manyan idanunta da su kayi ja ta kalle shi hadi da fad'in "labbaika...." tashi ki k'ara yi mana bayanin da nayi" Malam yace,tsuru tayi ta kafe sa da idanu,don bata san akan mi yayi bayanin ba,gaba daya ajin anyi tsit ana ta kallonta, Haulat ta d'an dukar da kanta murya can k'asa tana fadi mata bayanin da yayi,Fatuu ta saci kallonta sai dai sam bata san mi take cewa ba, A fusace malam yace"ke muke saurare!" Fatuu ta dukar da kanta jin kwalla zata zubo mata,hakan ya kara fusata Malam din yace "fita kiba mutane wuri,tunda ba karatun kika zo dauka ba" ba musu ta nufi hanyar waje har lokacin kanta na k'asa,Malam yaci gaba da magana"don iskanci yara k'anana daku sai kuje kuyi samari,in kuka yi fad'a kuzo kuyi ta tunane-tunanen banza,in baku son karatun kuje kuce Aure kuke so mana" Sauran yan ajin suka sa dariya suna sussunna kai kasa alamun kunya banda Haulat da sam bata ji dad'in maganar da yayi ba,don tasan ba abunda ke damun Fatuu ba kenan,tabb ita da koda wasa akace ana sonta yanzu ta fara masifa da zage zage tana fadin ita bazata yi saurayi ba sai ta zama likita",haulat ta fada a ranta,ita kam Fatuu kallon Malam din tayi da runannun idanuwanta suka hada ido yace"ko zaki zo ki buge ni ne?" batace komae ba ta juya ta fice....

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page22⃣*

Fatuu na tsaye ta jingina da karfen barandar gaban ajinsu ta tafi duniyar tunani,Malam ya fito,tsaye ya yi a bayanta yana kallonta kafin yace "ke cewa nayi ki fito ki tsaya? Wato kinfi karfin ki rage tsawon ki ko? Juyowa tayi ta kafe shi da idanu batare da tace komae ba,hakan yasa ya k'ule cikin daka tsawa yace " ba dake nike bane! Sunkuyar da kanta tayi k'asa tace"baka ce in rage tsawo na ba ai,cewa kayi in fito waje kawae....." katseta yayi "da yake ke dak'ikiyace komai sai ance ki yi ko?" kallon k'asan ido tayi masa suka hada idanu,a fusace yace "kee! ni kike harara...." daga bayansa yaji ance"abunda yafi harara ma yi maka zatai indae wannan ce" a tare suka juya don ganin mai maganar,wani matashin malami ne ya tunkaro su yana sanye cikin farar shadda jamfa hannunsa na dama rungume da Qur'ani dayan kuma rike da zungureriyar dorina,shine displine a Islamiyyar,ya iso inda suke fuska tamke,wanccan malamin yace"Yauwa Malam Nazifi,gatanan kayi mata hukuncin da ya dace,ina bayani hankalinta na wani wuri,nace ta fito kuma tafi karfin ta rage tsawonta", jinjina kai Malam nazifin yayi daga haka d'ayan malamin ya juya ya tafi,

Kallon Fatuu yayi fuska A d'aure yace "bani hannuwanki! ta d'an marairace fuska tace"Malam don Allah ka buge ni a jiki' dama malam nazifi yasan bata son bugu a hannu,hakan yasa ya k'ara tamke fuska yace"ina wasa dake? Girgixa masa kai tayi,ya d'aga bulalan ba tare da yace komae ba,a hankali Fatuu ta mika hannuwan suna dan rawa ta runtse idanunta ya fara bugunta tamkar da gayya,yana yi mata bulala biyar ta janye hannuwan tana dan yamutsa fuska don ba k'aramin zafin bugun take ji ba" yace"nace ki sauke hannuwan ne?" turo baki tayi tamkar zata fashe da kuka tace "don Allah malam kayi hakuri....."ya katse ta "kinsan kina tsoron bugun kike ma mutane iskanci,bulala goma zanyi maki amman wllh kika yi wasa zata koma ishirin", sanin da gaske yake yasa ta sake mik'a masa hannu daya tana yi tana canjawa har ya gama,ta juya tana yayyerfe hannu don sosae ya bugeta hannuwan duk sunyi jawur,malam nazifi ya dakatar da ita daga tafiya ta hanyar fad'in "ban sallame ki ba" ta juyo tana kallonshi cikin ido ta d'aure fuska,"kije Office dinmu ki cika mana bokitinmu na ruwa,sannan kije ki wanke gaba d'aya bandakin ku na mata,basai nace kiyi ba,inkin so kina iya kin yi" daga haka ya juya ya shige Class dinsu don shine Malaminsu na Al'Qurani da tajweed,da sauri Haulat ta koma gun zamansu don dama tana a la6e bakin kofa tana ganin duk abunda ke faruwa.

Fatuu ta sauke ajiyar zuciya ta juya don zuwa yin purnishments din da Malam ya bata,a hankali ta ke sa hannu ta na goge kwallar dake zubo mata cikin ranta tana fad'in "Mugu kawae,dama yafi kowa tsanata a makarantar nan,daga yau ba sai ka sake gani na ba zaka bugan..."a fili tace"dama ban zo ba,tunda ba za'a kyale mutum da abunda ya isheshi ba,a daidai nan ta iso bakin staffroom din,Haulat nata faman zuba ido don ganin shigowar fatuu,lokaci bayan lokaci ta ke kai dubanta kan k'opar shigowa amman shiru gashi har an kusa tashi kuma har lokacin malam Naxifi na cikin class d'in saboda abu biyu yake masu,sai lokacin da aka tashi Mlm Nazifi ya fita,da sauri Haulat ta d'auki jakarta had'i da ta Fatuu ta fice da sauri baiwar Allah har tana yin tuntu6e wurin fita,hanyar kewayensu ta nufa don taji Aikin da aka sa fatun,bata k'arasa isa ba ta hangota a hanya tana tahowa,Haulat ta ja ta tsaya tana kallonta itama Fatun kallon haulat d'in take har ta iso wurinta,hannu kawae ta mik'a mata alamar ta bata jakarta haulat ta mik'a mata jakar a hankali fatuu tace "nagode" daga haka tayi gaba, haulat itama ta bi bayanta har suka fita daga cikin Islamiyyar suka mik'i hanya,haulat a ranta tana ta tunanin mike damun fatuu haka,don tunda tazo ta lura da yanayinta tana cikin damuwa ga bugu da kuma aikin da aka bata, A fili tace"ba abun mutum ya tambayeta ba tayi man wulakancin da ta saba,gara ma in kyaleta,da tana son in sani ai da ta sanar dani" can dae haulat ta kasa daurewa ta kira sunanta da yake ba tazara sosae a tsakaninsu don a hankali fatun ke tafiya ba kaman yadda ta saba wuwwurga kafa ba,bata juyo ba haulat ta sake cewa"Fatuu"a hankali ta juyo tace"minene"haulat ta k'arasa gabanta tace "mi yake damunki ne naga kaman kina cikin damuwa tunda kika zo" fatuu tayi yar ajiyar zuciya ta ta6e baki tace"Uhmm,in na gaya maki damuwar zaki man magani ne" d'an murmushi Haulat tayi tace"ai bansan mike damunki ba,balle in san ko zan iya yi maki maganin" girgiza kai Fatuu tayi cikin karewar murya tace "koma kinsani bazaki iya man magani ba,don haka ba sai kin ji ba" ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali, Haulat tayi tsaye sototo tana mamakin abunda Fatuu tace ma ta,don tasan bata 6oye mata abu in yana damunta,koma ta 6oye zata dawo ta bayyana mata,a ranta tace" to mike damunta haka da bazata fadi man ba...?cikin d'an d'aga murya haulat tace "Amman ko da bani iya yi maki maganin ai kilan in baki shawarar da zata iya yi maki maganin ko" shiru bata ce mata komae ba kuma bata juyo ba,hakan yasa Haulat juyawa tabi d'ayan 6arin dake kallon wanda fatuu tabi ta fara tafiya,Fatuu nata juya maganar haulat aranta na shawarar da tace zata bata,tabbas Haulat na bata shawara kuma shawarar nayi mata aiki,ta tuna wani laifi da tayi kwanakin baya wanda ta tsorata sosae hakan yasa Haulat ta bata shawarar yadda zata yi ta ku6uta bayan tayi mata fad'a,aikuwa shawarar tayi mata Amfani don ta tabbatar lokacin ba don aiki da abunda haulat din ta fadi mata ba Kawu Amadu sai ya karyata....,da sauri ta juya "Haulat,haulat.." ta k'wala mata kira har sau biyu,sannan haulat taja ta tsaya ta juyo fuska a d'aure da alama tayi fushi ne,ganin haka yasa Fatuu ta nufeta ta tsaya gabanta tace"bari in fad'a maki to,amman shawarar zaki bani kar kice zaki man fada don aikin gama ya rigada ya gama, kuma ko baki man fada ba ma nayi dana sani bazan kara aikata irin hakan ba..."ta sunkuyar da kanta jin kwalla zasu zubo mata,ajiyar zuciya haulat ta sauke ta kai dubanta gaban wani gida dake agefensu,ta kamo hannun fatun tace"muje can to ki fadi man nan akan hanya muke" daga haka suka nufi jikin bangon gidan suka jingina,

Haulat tace "ina jinki,mike damunki?" Fatuu dake ta matsar kwalla kamar jira take haulat ta tambaye tan ta rushe da kuka tace "Haulat na bani na lalace,gidan yari za'a kai ni,kuma kilan acan zan mutu ma.." zaro idanu haulat tayi gabanta ya fara faduwa,cikin rashin fahimtar zancen fatuu tace"waye zai kai ki gidan yari?" cikin kuka Fatuu ta zayyana mata duk yadda sukai da Gaye harda aikenta da akai gidan Hajia jiya da daddare harta ga Haisam d'in. Ajiyar zuciya mai karfi Haulat tayi tace "nasan maganar ma" da sauri ta kalleta tace"kinsan za'a kaini gidan yarin dama kuma baki fad'a man ba.." jinjina kae Haulat tayi tace"jiya da yamma nima na hadu da gayen kuma shine ya sanar dani abunda kika yi har da aka tashi nayi maki maganar, kuma naso in sanar dake Mutumin dan gidan Hajiyar Sanata ne amman kika k'i saurarata k'arshe ma sai cewa ki kae wai ko dan sarkin makka ne ke ina ruwanki...."

cikin kuka Fatuu tace"ai ni nayi zaton tambayana kike ko nasan mutumin" taci gaba da rusa kuka,Haulat tace "ki daina kuka,ki kwantar da hankalinki..." a fusace Fatuu ta katseta tace"amari hakkilo?ya za kice wai na daina kuka,kuma taya zan kwantar da hankalina bacin nasan tabbas duk abunda gaye ya fad'a gaske ne.." Haulat ta juyar da kanta gefe ta dan gwalo ido cikin ranta tace"tabb lalle abu yayi abu,yau su Fatuu harda yin fullanci,ita da bata son yi,wani lokacin inta fama da ita tayi man ta k'i yi" Fatuu dai sai kuka take tana sambatu "ni wllh bansan haka motan keda tsada ba,da bazan ma fara fasa masa gilashi ba,ace kudin shanu gomaa har sau goma ne kudin motar,ba dole gilashin ma yayi tsada ba" Haulat ta jinjina kae ta kalleta tace "nawa yace motar take ne" da sauri fatuu tace"Miliyan goma faaa" haulat tace "bama tada tsada sosae...",a fusace fuska jage jage da hawaye fatuu tace" miliyan goman ne ba tsada,shiyasa nace baki da hankali,koda yake nasan baki taba sanin yawan miliyan a hannu bane shiyasa zaki ce haka,yo inama zaki gansu" girgiza kae haulat tayi sam bata ji komae ba don dama ta saba datsa mata magana,tace "dama ban ce ai na ta6a ganinsu ba ko,kawae dae nasan akwae motoci masu tsada sosae da yan gayu ke hawa,don na ta6a ji yaya Osman dinmu yace harta miliyan d'ari akwae" da sauri Fatuu ta dafe kai tana fitar da numfashi mai karfi a rude tace "kice Allah yaso ni da ba irinta na fasa ma gilashi ba,yasin nasan wannan sai dae a harbe ni kawae" ta k'ara fashewa da kuka,ita kam haulat dan juyar da kanta tayi tana murmushi don dariya maganar ta bata, Zamewa k'asa Fatuu tayi ta zauna dirshan taci gaba da kuka tana sambatu"mi woni ni fatuu,mi woni..,na bani na,in Gwaggo taji wannan maganar nasan sai tasa kawu Amadu ya kakkarya ni kafin awuce dani kuma gidan yari inje in rink'a cin gabza kwarkwata kuma ta gwaigwaye man gashi,tunda nasan ba yafe man zai yi ba,gaskiyar Gaye wllh nasan ko kawu Amadu nayi ma haka ba zai ta6a kyale ni ba sai ya dau mummunan mataki akaina,balle wannan da ba abunda na had'a dashi,nasan ko hajia taji bazata hanashi ya dau mataki a kaina ba,daman kullum tana man fadan in daina rashin ji,ko jiya ma saida tace zamu 6ata,yanzu kuma taji wannan asaran da na yiwa d'anta ta uban kudi haka,tabb ai nasan ma ba za tace ya yafe ba,to mima muka had'a da ita da zasu yafe,daga makwabtaka....,ga Hajiya dama ta iya masifaa....mi maye ni Fatuu,na mutu kawae" ta d'ora hannuwanta saman kai kafin ta dago tana kallon Haulat wadda tuni dama ita ta ke ta kallo cike da tausayi,tace"dama nasan ba wata shawara da zaki iya bani,wannan babban abu ne ba irin wanda ki ka saba ban shawara bane,nasan dole sai an kaini gidan yarin" ta kai maganar tana ta faman yin sheshsheka.

A hankali Haulat ta durk'usa kusa da ita ta kalleta tace"duk da haka ina da shawarar da zan baki,kuma ina tunanin Insha Allahu zata yi aiki..." da sauri fatuu tace"kenan kina ganin in nayi amfani da ita ba za'a kaini gidan yarin ba?mutumin zai hakura?" d'an murmushi haulat tayi"tace ehh,in Allah ya yarda zai hakura nike tunani..." fatuu ta k'ara katseta da sauri"toh don Allah fada man abunda zan yi ko minene zanyi indai za'a kyale ni nidai" Haulat tace "saurin mi kike,zan fad'i maki amman sai kin yi mani Alkawarin in dae aka kyale ki bazaki kara aikata makamancin wannan abun da kika yi ba" wani irin kallo fatuu ta juyo tana mata mai kama da harara,can kuma ta dauke fuskarta ta kalli gefen haulat d'in tace "da yake kare mai bak'in baki ne ya cije ni zan k'ara aikata hakan,ko baki ji tun d'azun nace maki nayi dana sani kuma bazan k'ara ba" ta kai maganar tana turo baki,Haulat tace"nasan halinki ne kin iya tuban mazuru,sau nawa kike cewa baki k'ara yin abu kuma kizo ki karan" Cike da gatse Fatuu tace"to gwaggo kiyi hakuri...,don kawae kinga ina neman taimakonki zaki taman maganganu sai kace ni mahaukaciya ce zan sake,ni in zaki fada man abunda zan yi ki fada man lokaci na k'urewa" ta kai maganar tana dan turo baki tana kallon hanya, Karasa zaunawa a kasa Haulat tayi,ta juyo tana kallon fatuu tace"KI JE KI BASHI HAKURI........

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page23⃣*

*Haisam*

Zaune a cikin parloun sa yana operating laptop wadda take mai kyaun gaske jikinta sai shining yake yayin da bayanta ke dauke da tambarin Apple,jin ana k'okarin shigowa cikin parlon kai tsaye batare da anyi knocking ba yasa ya dan waiga ya kalli kopan,

Readers Also Read